Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


cikin ranshi yaketa kitsima an cutar da bawan Allah a samar dashi ta hanyar da bata daceba,
ko me zai zama a duniya a nan gaba,
sai an tono tabon cewa shi d'an she gene,
hawayen da suka cika mishi idon ne suka tsiyayo sanadin lumshe idon da yayi,
sanadiyar d'igowar hawayenshi,
dai-dai tsakiyar goshin jaririn,
haka yasa yaron ya k'ara bud'e idanunshi ras,
tare da yin mutsu-mutsu yana kuma wawurar hannunshi yana cusawa a baki alamar yunwa yakeji,
yana buk'atar abincin shi.
Ita kam Zahra sai wasa da yatsunta takeyo so take ta tsaida hawayenta amman abin ya faskara,
haka suna zaune a haka tsawon 15 minutes sannan ya sake d'an d'agowa ya kalleta tare da kanshi idanunshi,
sannan yaja wani nannauyan ajiyan zuciya, ya kuma fesar da numfashi a hankali murya can k'asa tamkar mai yin rad'a yace.
"Ke kad'ai ne aka bari a nan babu mai kula da ke da yaron ki?."
kai ta d'ago a hankali tare da bud'e idanunta,
ta kalleshi ta gefen ido,
a hankali cikin yanayin mgnar wad'anda akawa CS ta bud'i baki da kyar murya na rawa tace.
"Ni da Mama da Tatti ce."
kanshi ya jinjina alamar gamsuwa sai ya kuma d'an d'ago ida nunshi tare da d'an zuba mata su yace.
"Toh ina suka tafi suka barku ku kad'ai?."
yatsa ta d'ago ta nuna mishi window a nan ya hango Tatti a woje tana zaune kan darduba,
dawo da dubanshi yayi zuwa gareta jin tana cewa.
"Doctor ne yace su fita su barni inyi bacci,
Mama kuma taje gida ne Zata dawo."
sunkuyar da kanshi yayi kamar bai jitaba, gaba d'aya ya meda hankalinshi kan jaririn daketa shan yatsun hanunshi.
Hakan yasa shiru ya ratsa tsakaninsu kowa da abinda ke ranshi,
suna cikin haka Affan ya shigo,
gaban Yusuf yaje tare da mik'a mishi ledar hanunshi,
amsa yayi tare da d'ago kanshi ya kalleshi da alamun tambaya,
gane hakan yasa Affan gyad'a mishi kai tare da cewa,
Dabino ne da zam-zam,
yau har kwana uku da haihuwa kaga ya dace ayi mishi hud'uba."
cikin gamsuwa Yusuf ya jinjina kanshi tare da mud'e ledar.
Dabino guda uku ya d'auka tare da fasasu ya cire gwallayen ciki,
sannan ya sasu a baki tare da tattau nesu,
saida yaji yawun bakinshi ya tsastsafo ya had'e da zak'in dabinon sannan ya d'ago yaron tare da tallab'e kanshi shi kuma ya d'an sunkuyo ya had'e bakinshi da na yaron wuri d'aya,
a hankali ya bed'e bakinshi kad'an tare da tarfawa yaron ruwan dabinon,
ai kuwa yaro yana jin d'and'anon dabino sai ya zaro d'an harshenshi yanata lasar ruwan dabinon da aka bashi,
haka Yusuf yayi tayi mishi saida ya bashi ruwan dabino bakwai,
koda ya bari sai yaro ya rink'a turo harshe yana laso lips nashi,
Affan ne yayi dari cikin son yaron yace.
"Kalli abinda yake,
wai shima yasan zak'i ko."
karo na forko da Yusuf ya d'anyi guntun murmushi tun bayan shigarshi furzin,
ita kuwa Zahra ido kawai ta zuba musu still har yanzu hawayenta sunk'i tsayuwa,
shi kuwa Yusuf robar zam-zam d'in ya bud'e tare da kurb'ar ruwan zam-zam d'in a bakinshi sannan ya sunkuyo ya had'e bakinshi da na jaririn ya rink'a d'isa mishi ruwan kad'an-kad'an saida ya bashi dai-dai misalin cikin shi sannan ya d'agoshi tare da azashi a kafad'arshi,
sannan yasa tafin hannunshi yana shafa bayan yaron har saida yaji yayi yar gyatsa irin tasu ta jaririrai sannan ya sauk'oshi ya kontar dashi bisa cinyarshi,
dariya sosai Affan yayi ganin yanata lumshe ido alamun ya k'oshi zaiyi bacci kenan ,
sun kuyowa yayi ya sumbaci goshinshi tare da cewa.
"Masha Allah, Allah ya raka bisa imani."
Amin Amin Yusuf ya fad'i a hankali,
sannnan ya sake d'agoshi yasa bakinshi cikin kunnenshi na dama yayi mishi hud'uba kamar yadda addinin musulunci ya tana dar.
bayan ya gama yi mishi duk abinda ya dace ne,
sai ya mik'e rik'e da yaron yazo gaban gadon tare da mik'a matashi,
ganin yaki kontar dashi yasa dole ta d'ago kanta tana kallonshi da alamun tambaya,
kai ya jinjina mata alamar ta karb'eshi ganin haka yasa ta d'ago hannunta mik'o mishi alamun ya batan,
a hankali ya k'ara matsota sosai har kamar zasu had'u sai d'ai yaron dake tsakiyarsu ya tsare tsakaninsu,
kan cinyarta ya kontar da yaron murya can k'asan mak'oshi ya fara mgn.
"Sunanshi *Aryan* nayiwa *Aryan d'ina tokwara*."
sai ya kuma d'an k'ara sunkuyowa kansu yana gyara Aryan konciyarshi a cinyarta sannan yaci gaba da cewa.
"Ga Aryan nan, amanace Allah ya baki a matsayinki na mahaifiyarshi,
kula dashi da lamuran rayuwarshi,
dole ki zama mai hak'uri domin bashi kulawar data dace,
kada ki bari kyara ko hantarar da mutanen kan iya mishi yasa ki gaza nuna mishi so ko kulawa a matsayinki na mahaifiyarshi domin amanace Allah ya baki kuma amana abin tamb'aya ne,
ki kula da tarbiyarshi."
Zahra kam babu mgna sai hawaye,
Affan kuwa tausayinsu ne fal zuciyarshi.
Ita kuwa Zahra kai take gyad'a mishi alamar gamsuwa da d'aukar nasiharshi.
Yana sunkuye a kansu ita da Aryan k'aramin ,
ya mik'owa Affan hannu wani d'an abu Affan ya d'aura mishi cikin tafin hannunshi,
shi kuwa duk yana sunkuye a kanta idanunshi na kan Aryan k'arami,
hannunshi ya mik'o tare da mik'a mata abinda Affan ya bashin nan,
ita kuwa Zahra bata ganiba domin hawaye daketa kwaranya a ida nunta har saida ya kuma rok'ofowa sosai har tana jin sautin numashinshi,
jin haka yasa ta d'an d'ago kanta,
ganin ya mik'o mata abu yasa cikin rawan jiki ta mik'a mishi hannunta,
ATM nashi ya ajiye mata tsakiyar tafin hannunshi tare da d'an matsawa gefe,
yayinda ya dawo gefen kunnenta cikin sanyin murya yace.
"2212, sune ma bud'an sirrin,
ki kula da rayuwar Aryan ki bashi dukkan abinda ko wanne d'a mai gata ke samu."
idonta ta d'an d'ago ta kalleshi sai ta kuma yi maza ta meda kanta yayinda kuka ya kubce mata.
Da sauri Yusuf ya mik'e tare da juyawa ya fita,
Affan kuwa cikin sanyin murya yace.
"Kiyi hak'uri Zahra ki dena kuka kinga baki da lfy."
kai ta jinjina mishi alamar to.
sannan shima ya juya ya fita.

Suna fita Tatti na shigowa samunta cikin yanayin kukane,
yasata tayi maza ta matso gareta.
"Zahra Lfy kuwa, meke miki ciwo?
d'inkin ne yake miki ciwo ko wani wuri na jikinki?."
kanta ta kontar jikin Tatti cikin wani irin rauni da tausayi tace.
"Hamma Yusuf."
cikin kad'uwa Tatti tace.
"Me ya sameshi?."
murya na rawa tace.
"Yazo yanzu suka tafi shida Ya Affan,
Tatti Hamma Yusuf yana bani tausayi,
sai kinga yadda ya rame,
ya zama kamar bashi ba."
ruggumeta Tatti tayi cikin zubda hawaye tace.
"Wata rana sai lbri,
insha Allah wata rana zaiyi farin ciki kuma Allah zai saka mishi kan k'azafin da Aryan yayi mishi,
har abadan hak'ar Aryan bazata cimma ruwaba."
suna cikin haka Mama ta shigo tare da Daddy,
ganinsu duk cikin damuwa yasa Daddy tamyar ko jikinne gashi har ana shirin sallmarta,
cikin nitsuwa Tatti tayi musu bayani,
ita kuwa Mama tunda aka kira suna Yusuf ta shege bathroom,
tana shiga ta had'a kanta da jikin gini ta fara wani irin sassanyan kuka tanayi tana mgna.
"Ya Allah ka gani ka fini sanin halin da wannan bawa naka Yusufa yake ciki.
Ya Allah ka jibanci lamuranshi,
ya Allah ka tak'aita mishi munanan k'addarorinshi ka bashi ikon cinyesu,
kayi mishi al'abarka a cikin dukkan lamuranshi."
haka tai ta mishi addu'a tana kuka.

Bayan an dudduba lfyan Zahra an kwance d'inkin aka sallamesu,
yaro kuma dama lfyarshi lau.


Bayan sun koma gida kai tsaye d'akin Mama aka wuce da Zahra sabida ita Aunty Amarya tace bata son ganin Zahra da d'an shege a hannunta,
suna dawowa Mama ta shiga kitchen tayi mata girkin abinda likitoci suka bata damar taci,
Tatti kuwa tayiwa Aryan wonka ta kintsashi cikin wasu tattausan kaya kalar ja da fari,
wadanda duk cikin sayayyar Jafar ne,
ganin yanata wawure-wawuren hannu alamun yunwa yakeji yasa,
Tatti mik'o mata shi tare da cewa.
"Bashi ya tsotsa."
hannu tasa ta k'arbi yaron tare da rumtse idanunta,
dai-dai da lokacin kuma Ummi ta shigo bakinta d'auke da salati take cewa.
"Oho ya Allah ka tsaremu da fitsarar wannan zamanin yanzu ke Zahra har kinada tsaurin idon da zaki bashi nono yasha?."
Mama dake shigowa ta bayanta ne ta tsuke fuska tare da cewa.
"Toh a barshi yunwa ta kasheshi ne?."
cikin rashin d'a'a tace.
"Yoh in yunwar ta karshi ma ai mun huta da zaman k'azanta a zuriyarmu,
kuma in so kuke ya rayu ai sai ku nemo d'an iskan ubanshi daya bada cikin yazo ya nemo mishi madarar sha."
Tatti kam ido ta zubawa Ummi cikin tsananin mamaki tama kasa cewa komai,
ita kuwa Zahra rumtse idonta tayi yayinda hawayenta ke tsiyaya har kan kumatun yaron,
yayinda can cikin zuciyarta kuwa take tuno nasihar Hamma Yusuf d'in tana jin sautin muryarshi kamar yanzu yake mata mgnar.
"Shi baida laifin komai, kuma shi amanace Allah ya baki,
ina rok'onki da girman Allah kada laifin mahaifinshi ya shafeshi,
dan Allah ki shayar dashi da abincinsa da Allah ya halitta a jikinki,
kada tsonk'omar mutane tasa ki nuna mishi wani halin da zai sashi kuka,
dan Allah kiyi min wannan Al'farmar."
tuno kad'an daga cikin zantukan nashi da ya mata saitin kunnenta a lokacin da ya gaya mata number sirri na ATM d'inshi,
tuno hakan yasa ta tasa hannu ta tallabe kan Aryan ta fara feeding d'inshi cikin jin tausayin yaron da k'aunarshi.

Ganin haka yasa Ummi tab'e baki ta fita,

Mama kuwa tasa sunkuyo da niyar zama kenan sai ta kuma mik'e da hanzari,
jin gaba d'aya gidan ya rud'e ko ina sai sautin zubar ruwa shaaaaaa,
da sauri ta fito,
a tsakiyar gida taci karo da Aunty Amarya,
ta sauri ta yi kanta tana cewa.
"A a Lfy kuwa naga duk an bud'e pompunan gidan da dams d'in gaba d'aya,
kalli yadda gida duk ya cika da ruwa."
da sauri ta juyo jiyo muryar Hajja inna daga sama tana cewa.
"Ina kuwa Lfy, tunda yau ga d'an shege a cikin gidan,
ai sole duk a zubda ruwan gidan domin ya haramta garemu,
shiyasa yau duk ruwan gidannan sai an zubda shi."
salati da sallalami Mama ta fara murya ciki da kunci tace.
"Yanzu Hajja Inna a bakin wani malamin kika tab'a jin hakane?."
cikin masifa irin ta tsoffi da gadarar ai tanaga uwar Mama k'anwar mijinta ne cikin izaya ta kalli Mama tare da cewa.
"A bakin uwarki naji! ke Wlh Yawuro kifa kiyayeni,
duk wannan iskanci daga gareki ya fito,
shine har zakice a bakin wanne malami naji hakan,
to bari kiji tun iyaye da kakanu haka akeyi yau duk mak'otanmu duk maison tsarkakken ruwa to dole sai ya zubda ruwan rand'unanshi sai dai ya kuma nemo wani ruwan."
jin hayaniyar tayi yawa yasa Tatti fitowa,
ai ido kawai ta zubawa Hajja inna dake tsaye tsakiyar ruwa,
ita kuwa Aunty Amarya juyawa tayi ta kuma sashinta,
ganin haka itama Mama ta koma part d'inta,
tai ta bawa Zahra k'arfin guiwa.
Tatti kuwa bayan Aunty Amarya tabi tai ta mata fad'a kan rashin kulawar da take nunawa Zahra.


Abin al'ajabi hakafa a wannan ranar mafi aka sarin gidajen mak'otansu sukayi ta zubda ruwan randunarsu wai ai an kawo musu d'an shege a unguwa.

Aryan kuwa bashi da lbrin haihuwar domin kab babu mai shiga harkarshi,
sai washe garin suna ne,
da safe yaje parlour Kaka yana zaune ta fito ta sameshi cikin kula da jin haushinshi kad'an tace.
"Yauwa dama kai zan kirawo kazo ka kaini gidansu Yusuf in dubo Zahra da d'anta dan ni bazani sunaba da tsufana."
cikin mmki da k'aduwa ya mik'e tare da cewa.
"Zahra ta haihune, yaushe ta haiku me ta haifa?."
hararanshi ta d'anyi tare da cewa.
"Sai ka bari in muje ka musu tambayoyin."
jin haka ya sashi juyawa tare da cewa.
"Mu tafi."
suna fita kai tsaye Girei suka nufa.


Bayan sun isa Kaka ta shige ciki,
shima Aryan sai yabi bayanta,
ita Kaka Parlour Hajja Inna ta nufa shiko Aryan parlour Mama ya nufa,
domin yanzu baya shiri da Hajja inna a cewarta shi yasa akayiwa jikanta tijara a idanun duniya da kuma yi mishi dukan mutuwa.

Bayan ya gaisa da Mama ne ta shiga ta turo mishi Zahra.

Tana fitowa parlour,
can ciki-ciki tayi sallama,
sam Aryan bai jitaba sabida ya shiga duniyar tunani,
gefe can ta zauna tare kauda kanta tana kallon gefen window,
wani irin tsana da haushin Aryan takeji yana ratsa zuciyarta da dukkan gabban jikinta,
ganin baima san tazoba yasa taja gajeren tsaki,
tare dayin mgnar zuciya,
mugu kawai azzalumi mahinci,
hararnshi tayi ta gefen ido,
dai-dai lokacin Aryan k'arami yayi kuka hakan ne ya jawo hankalin Aryan babba,
firgigit ya dawo haiyacinsa cikin sauri ya d'ago kanshi tare da zuba musu ido,
itama kanta ta d'ago ta zuba mishi hararar data jikinshi yayi mugun mutuwa kunya mai tsanani ta rufeshi,
cikin k'arfin hali yace.
"Ashe kin haihu, wlh bani da lbri sai yau me muka samu?."
tsaki taja tare da murgud'a baki cikin kunk'uni tace.
"Me ruwanka da abinda aka samu,
inji dai kai kam kayi abinda zakayi na cin amana."
ya jita sarai hakan ya sashi kauda mgnar tare da mik'o hannunshi tare da cewa.
"Kowa Baby."
k'in kulashi tayi sai k'ara ruggumeshi da tayi,
ganin haka ya taso a hankali ya nufi inda take domin ya sani a duniya babu wanda Zahra zata tsana sama dashi,
gabanta ya d'an sunkuyo tare dasa hannu zai k'arbi yaron,
cikin kauda kai tace.
"Ka barmin yarona."
cikin k'arfin hali yace.
"Nima ai d'anane."
wani irin mugun harara ta cillamishi tare da taune lips enta,
shi kuwa hannu yasa ya d'ago yaron,
sannan ya koma gefenta ya zauna cikin sanyi ya rink'a yiwa yaron addu'o'i,
sai da ya gama ya d'ago kai tare da cewa.
"Wanne suna za'a samishi?."
tsaki taja tare dasa hannu ta d'auke yaron sannan ta mik'e tsaye tayi taku biyu zuwa na uku tace.
"Garkuwarmu ya rigaka yazo yayi mishi hud'uba tun randa ya cika kwana uku,
duk da bai nemishi shawarataba,
na kuma hak'ura nabi hukuncinshi duk da ya sawa yaron sunan da nafi tsana a raina,
amman nayi na'am da haka ko dan cikar imanin wanda ya rad'a sunan."
cikin mamaki Aryan ya mik'e tare da cewa.
"Waye kuma Garkuwarku?."
cikin d'an d'aga murya tace.
"Wanda ka tozarta,
koda yake nasan yanzu kanka baya tunoshi gwara in na gaya maka sunanshi,
Hamma Yusuf nake nufi."
kai ya jinjina cikin alamun gamsuwa yayinda idanunshi sukayi jazir murya na rawa yace.
"Wanne suna ya sawa yaron?."
a hatsale da d'an d'aga murya irin ta wadanda akawa CS tace.
"Aryan, wai kai yayiwa mai suna,
da yake shi ya iya saka al'khairi akan wanda ya mishi sharri."
wani irin mik'ewa Aryan yayi cikin rawan jiki,
yayinda hawayen da yake dannewa tuni suka zubo cikin sanyi sauti yace.
"Kiyi hak'uri Zahra ku gafarceni,
ki nema min yafi a cikin dukkan family enku,
ban san da idon da zan k'ara ganin Yusuf ba,
nayi kuskure mafi muni a rayuwata na cutar da wani tsagi na jikina,
domin Yusuf tsagin jikinane,
kaitona ni Aryan."
sai ya kuma juya ya fice yana mai zubda hawaye,
itama Zahra shiga tayi tana kuka yayinda ta samu Mama kukan takeyi.


Washe garin suna a cikin masallacin masarautar fadar jiha Affan yasa akayi addu'a wa jariri,
inda aka sha rabiyar dabino da goro,
sannan duk wani abinda uba zaiyi Affan ya yishi,
domin cika mota yayi mak'il da kayan buk'atun rayuwa na uwa da d'anta yasa aka kai gidansu Yusuf,
motar da ta kawo kayan da Affan ya musu tana tafiya,
Aryan ya iso tare da Rafi'a inda shima yayi dukkan abinda uba zaiwa d'anshi.
Hajja inna kuwa ranar ta zuba tijararta son ranta wai ba' isa ayi musu taron sunan d'an shegeba a gidansu,
to da yake babu wadansu bare da suka zoma sai Zulahat, Amira, Goggo Fatima,
Goggo Maimuna sai Aunty Madina sai kuma Raihana,
sai Dija Chiroma k'awar Zahra,
da dai sukaga tijarar tayi yawane,
Autar Hajja Inna Aunty Madina kenan taje tayi tawa Hajja inna magiya kan dan Allah ta bar abinda takeyin,
tofa sai tayi kamar ta nitsu angina kad'an kuma zata kuma ci gaba daga inda ta tsaya,
haka dai akayi wunin ranar aka watse.

Hakafa al'amarin rayuwa yayi ta gudana,
mafi akasarin ranaki Zahra sai tayi kuka,
duk gidan babu mai kula da lamuranta da d'anta sai Mama da Daddy sai Ya Jafar d'inta,
sai Mami da Zeenat duk sauran da zaiyi kuka har ya mace babu mai kulata a kanshi,
haka rayuwa tayi ta tafiya lokaci yaja,
Affan yakan zo duba Aryan k'arami yayinda shima Aryan babba yakanzo,
hakama Raihana da Faisal d'inta sukanzo.

Yanzu Aryan ya cika wata takwas,
wanda hakan yayi dai-dai da cika shekarar Yusuf d'aya a furzin,
yaro ya girma sosai yayi d'an lukuti dashi gashi fari k'al son kowa k'in wanda ya rasa,
gashi da nitsuwa sam bashi da yawan fitina ko gagara irin ta yara gashi da d'an karen wayo,
duk da yana yaro yasan masoyanshi ya kuma san wad'anda suke zare mishi ido in yaje kusa dasu mu samman Hajja inna mai zugeshi da carbi.

shiyasa baya zuwa inda suke,
tuni kuma ya fara tattaki.

Yau jumma'a da sanyin safiya Zahra ta shiga kitchen ta gama musu aikin breakfast,
bayan ta gama ne ta fito parlour inda ta samu Mama da Aryan suna zaune sai tsalle yakeyi a jikin Mama,
ganin Zahra yayi saurin sauk'a yabi bayanta tare da d'aga mata hannu alamar ta d'agashi cikin
lumshe ido ta sunkuyo ta d'agashi tare da cewa.
"Wash Aryan kayi k'atofa, yanzu na kusa in dena d'agaka."
Jafar ne da ya shigo yanzu yace.
"Uhummm gashi ke kuma kullum k'ara ramewa kikeyi duk kin canza yanayin rayuwarki ,
sam banajin dad'in abin."
Mama ce ta mik'e zaune cikin kula ta kalli Jafar d'in sai ta kuma kalli Zahra tare da cewa.
"Gata nan Jafar mafi akasarin ranaku sai tayi kuka,
ni kuwa damuwarta ke sani damuwa gata nan ko k'ofar gida bata fita tunda samu wannan matsalar."
ita kuwa Zahra kumatun Aryan taja wanda yaketa cewa.
"Mammama."
wai ta goyashi kenan.
kai tsaye bathroom ta wuce dashi,
wonka tayi mishi sannan tazo ta shiryashi cikin riga da wondo mai azabar kyau,
rigar orange wond'on kuma blue,
mai d'an ratsin orange daga can k'asan k'afafunta,
sai takalmanshi booth irin na yara masu azabar kyau,
mai ta tsiyayo a tafin hannunta ta k'ara shafawa suman kanshi datayi lib-lib,
shi kuwa turarenshi yaketa mik'o mata alamar ta sa mishi,
hannu tasa ta k'arba tare da fesa mishi sannan ta d'auko sabuwar wayarda Affan ya kawo mata jiya,
hotuna ta rink'a yi mishi,
shiko sai dariya yakeyi,
kiss ta manna mishi a goshinshi tare da cewa.
"Kaine farin cikina Aryan ina sonka,
domin nasan baka da laifin komai,
aka yadda kazo duniya."
murmushi yayi kamar yasan me take cewa.

Bayan sun fito parlour ne ta samu Jafar nanan har yanzu yana ganisu ya mik'owa Aryan d'in hannu cikin sauri ya zamo daga hannun Zahra da gudu ya nufi inda Jafar yake,
yana zuwa ya d'agashi sama tare da d'aurashi kan wuyanshi,
yayinda shi kuwa Aryan yasa hannu biyu ya rik'o kan Jafar d'in,
yanata kerketa dariya,
shi kuwa Jafar hannunshi yasa ya rik'o k'afafunshi,
sannan ya kalli Mama cikin kula ya kuma kalli Zahra yace.
"Zamu fita da Aryan,
zan saya mishi wasu kaya da na gani sabbin samfuri."
kai Mama ta jinjina alamar to,
ita kuwa Zahra cikin sanyi tace.
"Toh bari yasha kununshi kar yaje ya ta maka ihu."

to yace sannan ya sauk'oshi ya mik'e mata shi ya juya zai fita yana cewa.
"OK to kiyi sauri bari inje in gaida Ummi sai inzo mu tafi."
yana fad'in haka ya fice ya tafi yayi part d'in Ummi,
shi kuwa Aryan zamewa yayi tayi tare da k'ananun kuka alamun shi dai a barshi zaibi Jafar,
haka yasa dole ta sakeshi,
cikin tafiyarshi da bata gama nunaba yabi bayan Jafar wanda tuni ya shiga part d'in Ummi,
shi kuwa yana haura saman barand'ar takiyar gidan yayi tangak-tangal ya fad'i,
wani irin ihu yasa da k'arfi,
Aunty Amarya da Hajja inna da Nana da suke tsakiyar gidan ko inda yake basu kallaba,
ita kuwa Zahra da Mama kusan a tare suka fito,
jin ihunshi nan suka samu Zeenat ta d'agashi tana kad'e mishi jiki domin baiji ciwoba kukan tsorone kawai yakeyi,
da sauri Mama ta k'arbeshi ita kuwa Zahra sai kallon Aunty Amarya da tayi ko a jinkinta,
ita kuwa Mama Zahra ta mik'awa shi tare da cewa.
"Karb'eshi ki bashi nono."
amsarshi tayi tare da zamewa ta zauna kan bakin barandar ta fara fiddling inshi,

shi kuwa jiyo muryar Jafar ya sashi sakin nonon tare da zamewa ya sauk'a ya nufi wurin Jafar,
cikin kula ya d'agashi ya ruggumeshi tare da cewa.
"So sorry my boy."
yana fad'in hakane yayinda yake fita dashi ita kuwa Zahra sai hannu tasa tana share hawayenta.


Shi kuwa Affan kai tsaye Airport ya nufa,
ni kaina Garkuwa mmki nakeyi ko me zaije yi a Airport,
shi kuwa bayan ya isa cikin Airport d'in ne kai tsaye inda matafiya suke zaman jiran jirgi ya nufa,
daga bakin wurin naga masu jajayen kaya da alamar akwai jinin sarauta a wurin,
yana k'ara gaba sai ga Affan a gabanshi,
cikin kula Affan ya mik'a hannu ya karb'i Aryan da yaketa sauk'e ajiyan zuciya,
bisa dukkan alamu Aryan ya saba da Affan dan ba musu yazo gareshi,
sai kuma suka juya suka nufi wani sashi na musamman inda manyan matafiya suke zama in basa son hankalin mutane ya dawo garesu,
can gefe suka je kan wasu kujeru masu kyau,
Yusuf na zaune cikin shigar k'ananan kaya wad'anda kalarsu d'aya dana Aryan, yayi kyau sosai sai dai yanayin rama da k'uncin rayuwa dake tare dashi,
suna isa Affan ya mik'a mishi Aryan k'arami,
hannu mik'o tare da zubawa yaron ido,
shima Aryan ido ya zubawa Yusuf cikin gwaranci yayi dariya tare da cewa.
"Abeeh."
gaba d'aya Jafar da Affan dariya sukayi mai cike da mmaki,
shi kuwa Yusuf k'arb'arshi yayi tare da ruggumeshi gam a jikinshi sannan ya juya nufi hanyar da zata sadaga da inda jirgin yake...!





By
*Garkuwar Fulani*


[1/16, 1:43 PM Jnywl






Yana fita farfajiyar wurin sai yayi gefe,
k'ark'ashin wasu tsirrai inda aka jera kujeru na alfarma,
zama yayi tare da ajiya Aryan kan cinyarshi cikin kulawa da cikar imani da tausayawa da jin k'aunar yaron na ratsashi ya had'e goshinsu wuri d'aya,
idanu ya lumshe tare da d'an d'ago kanshi ya manna lips enshi a goshin Aryan tare da sake mishi wani irin tattausan sumbata,
cikin sanyi yace.
"Aryan."
kai ya d'ago ya zuwa fuskar Yusuf ido sai ya kuma sa hannunshi cikin haljihun gaban rigar Yusuf ya zaro wata sabuwar waya da Affan ya had'a mishi,
cikin gwaranci yace.
"Abeeh ceffi."
wani irin farin ciki ne ya ziyarci ruhin Yusuf har saida ya murmusa tare dasa hannu ya kamo kumatun Aryan din cikin sanyin murya yace.
"Au selfie kakeso muyi."
shi dai yaro sai dariya yayi tare da sa bakinshi a kumatun Yusuf kamar yadda Jafar da Zahra da Affan suka koya mishi,
ganin haka yasa Yusuf yin murmushi tare da amsar wayar ya fara yi musu hotuna,
abu da babbar waya ta manyan yara sai ga hotunannan tamkar ka kirasu su amsa.
Affan da Jafar kuwa gefe suka koma suka tsaya sunajin tausayin bayin Allah nan,
shi kuwa Aryan hango Jafar da Affan ya sashi zamewa daga jikin Abeehnshi da fad'i ya fara tattaki yanayi yana juyowa yana kallon Yusuf daya hard'e hannu a k'irji ya zubawa yaron ido,
yana isa wurinsu yaje gaban Affan ya tsaya tare da bud'e hannu alamun a d'agashi hakan yasa Affan sunkuyowa ya d'ashi tare da cillashi sama,
dariya sosai ya rink'a kerketawa,
ganin haka Yusuf ya matsosu fuska k'unshe da murmushi Jafar kuwa hoto yayi musu dukansu.
Dai-dai lokacin kuma aka fara kiran passengers dan shiga jirgi lokacin tashi yayi,
jin haka Affan ya ruggumi Yusuf cikin sanyi yace.
"Yusuf zamuyi missing enka,
ji nake gaba d'aya bana son tafiyar nan,
sai dai don itace mafita."
Jafar kuwa lip enshi ya taune tare da cewa.
"Ni dai banso Hamma Yusuf ya tafiba naso ya zauna muga me Allah zaiyi."
cikin sauri Affan yace.
"Tafiyarshi itace mafi dacewa,
domin burin magautanshi ya hallaka,
to kuma idan rana ta fito tafin hannu baya kareta,
ci gaban Yusuf shi zai fasa zuk'atan magautanshi.
Dole Safwan sai yaga ci gaban Yusuf in sha Allah.
Aryan zai gani da ida nunshi sai duniya kab tasan da Yusuf sam bazai durk'usheba,
koda ko zan rasa komai nawa in sha Allah Yusuf sai yayi zarra a World polo in sha Allah,
sai mutanen da suka k'ishi sun dawo suna nemarshi tamkar yadda yabanya take neman damshi,
in sha Allah Hamma Jabeer sai yayi barar Yusuf ya dawo Jahan polo team a lokacin da Yusuf yafi k'arfinsu."
shi kuwa Yusuf kanshi ya sunkuyar murya can k'asa yace.
"Jafar zan tafi,
dole in tafi me zan zauna inyi a

Please Login or Register in order to submit comment