Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'ofa,
cikin nitsuwa ya kalleshi cikin zubda k'ollah yace.
"Barrister Affan duniya zata so sanin ko kunda k'udurin zaku d'aukaka k'ara,
ko kun mik'a wuya hukinci ya tabbata?."
cikin sanyi Affan yasa tafin hannunshi ya goge hawayen dake zuba kai a gyad'a tare da cewa.
"Bazamu d'aukaka k'araba mun yarda da Hukuncin Allah,
duk da tabbacin da nakedashi kan ba Yusuf bane yayi laifin,
amman tunda ya amshi laifin ya ratayawa kanshi da bakinshi to bani da sauran abin cewa."
cikin sanyi Matawalle ya gyad'a kanshi alamar gamsuwa,
sannan Affan yayi cikin kotun,
Idi kuwa gaban Daddy da Yusuf da Affan da Jafar ya durk'usa wani irin kuka yakeyi,
mgna yakeyi cikin rawan murya yake neman yafiyar Yusuf tare da cewa.
"Nine na cancanci wannan hukuncin nine ya kamata a tozarta ni a idanun duniya ba kaiba Yusuf,
meyasa kayi haka,
meyasa bazaka barni in k'arb'i hukuncin ba,
nine k'ask'anceccen bawa daya dace da hukuncin kisama bama bulaliba,
meyasa za'a tozarta ka kaida kake da mitunci da tsarkaka da kima da daraja."
cikin zubda hawaye Yusuf ya sunkuyo tare da d'ago idi kai ya jinjina mishi tare da zubda k'olla,
cikin takaici Jafar yace.
"Jaka kawai."
jin haka yasa idi ya fice yana kuka,
shi kuwa Daddy hannun Yusuf yaja suka bi ta yar k'aramar k'ofar nan da Abba ya fita ta wurin,
suna fita cikin k'ofar sai gasu cikin wani tamfatsetsen office,
wanda aka k'awatashi,
ga tarin kanta sunfi 5 duk cike suke mak'il da littatafai,
sai wani babban table da yake cike da littatafai,
bisa dukkan alamu nanne ofishin Abba,
sanadin barin k'ofar da Daddy yayi a bud'e shi ya bawa Affan, Aryan, da Jafar samun damar ganin cikin office d'in Abba da kuma abinda ke faruwa,
suna shiga Daddy ya k'ara jawo hannun Yusuf har gaban Abba dake zaune gaban table d'in yana karatun quran,
yayinda har yanzu hawaye ke bin fuskarshi,
Yusuf kuwa suna isa inda Abba yake sai ya zame hannunshi tare da durk'ushewa a wurin yana wani irin sassayan kuka,
shima Daddy durk'ushewa yayi a wurin yaci gaba da kuka,
gaba d'aya sai suka birkita tunanin Abba,
shiyasa yana zuwa k'arshen suratul yaseen ya ruk'e quran d'in tare da yin addu'a,
cikin kuka Daddy yace.
"Ga dai fushinka na forko abinda ya jazawa Yusuf,
ban san kuma me fushinka dana mahaifiyarshi zai jaza mishi a karo na biyuba."
cikin rauni Yusuf ya saki kuka tare da cewa.
"Abba na tub'a ka gafarceni ka dena zubdamin hawayenka."
Aryan kam mik'ewa yayi ya fita domin bazai iya jurar ganin halin da yasa Yusuf a cikiba,
cikin kuka ya figi motarshi ya bar harabar kotun,
Affan kuwa shida Jafar suma fita sukayi suka tafi.

A office d'in Abba kuwa,
cikin rauni da tausayin kanshi da tausayin halin rayuwar da Yusuf ke ciki ya kalli Yusuf cikin zubda hawaye yace.
"Ka bani kunya ka kunya tani a idanun duniya,
kullum alfahari nakeyi da kai ina jin nafi ko wanne uba sa'ar haihuwar yaro nagari,
ashe ban saniba kana nan kana shirin tozar tani,
Yusuf ka kunyatani,
dole inyi kuka,
in banyi kukaba so kake in tsine maka ne ko in jama Allah ya isane?."
cikin sauri da kuka Yusuf ya rink'a jujjuya kai alamar a a,
shi kuwa Daddy tausayin d'an uwanshi ne ya rufeshi ya tabbatar Abba yana son Yusuf tamkar ranshi amman ga yadda k'addarori ke ratsa tsakiyar soyayyarsu,
shi kuwa Abba cikin sanyi yace.
"Toh Allah ya shiryaka Yusuf Allah ya rabaka da k'azantar zinace-zinace Allah ya baka ikon kame kanka,
za'a yi maka bulalin haddinka gobe sannan a goben za'a rufeka sai bayan shekara d'aya zaka fito,
in ka fito sai kayi duk yadda kakeso,
tunda baka da kunya,
kalli yanzu yadda kasa d'an uwana kuka, kuma yarshi ce ka ketawa haddi,
amman da yake baka da ta ido kana bibbiye dashi."
Daddy ne ya kalleshi cikin sanyi yace.
"Ni nasan ba Yusuf bane yayiwa Zahra wannan aikin ba."
cikin fad'a Abba ya kalleshi tare da cewa.
"Tashi ku ficemin daga nan."
ganin fuskarshi ta juye yasa suka fita ba musu,
Daddy ne da kanshi ya kai Yusuf da Kaka har gida domin duk abinda akayi Kaka har yanzu bata tafiba.


Bayan sunje gida Daddy da kanshi yasa Yusuf yayi wonka sannnan ya d'anci Abinci, sannan ya tafi,
Aryan kuwa tunda ya shiga part d'inshi ya rufe kanshi bai kuma fitowa ba.

Mama kam a daren ranar saida Abba ya tausaya mata domin abin tamkar zai tab'a hankalinta,
tayi kuka har hawayenta sun kafe,
sai taita surutu tana cewa.
"Bulali d'ari a fatar Yusuf yaronda duka kad'an ke sashi ya suma,
toh inaga ance bulali d'ari kasheshi kawai za'ayi."
dole fa Abba ya zama mai rarrashinta,
Hajja Inna kuwa da taji lbri dariya tayi tayi harda shewa tace sai yanzu ta huce tunda za'a rama mata bulalin da Yusuf ya shisshinfid'a mata,
Ummi ma a sashinta abin ya mata dad'i,
Aunty Amarya kuwa kuka sosai tayi,
ranar dai gidan babbu farin ciki.


Washe gari da hantsi,
harabar Court d'in Hukuncin Allah ta cika mak'il da mutane domin Safwan ya gama banka d'awa duniya cewa yaune za'a yiwa Yusuf hukuncinshi,
bayan an gama shirye-shiryen da suka kamata,
sai aka nufi wani fili can bayan court d'in inda ake aiwatar da irin wad'annan
hukuncin in jifa nema a nan akeyi in rataya nema a nan akeyi in bulalin nema a nan akeyi,
bayan an gama shirya bulalin mutane sun hallara a wurin kamar yadda shariya ta koyar,
aka bada umarni a fito da Yusuf,
mayan 7 minutes Yusuf ya shigo taron filin kanshi a sunkuye yake tafiya,
yayinda jikinshi ke sanye da farar jallabiya da dogon wondonta fara k'al sai hular tab'a kaji hadisi itama fara k'al,
filin da aka nuna mishi yaje ya tsaya cikin ma'aikatanne d'aya daga cikinsu yazo kusa da Yusuf d'in yace.
"Zaka cire rigarka."
cikin tsananin kunya ya cire,
sannan ya juya ya fuskanci al'k'ibla aka zo aka had'e hannayenshi da jikin k'arfen aka d'auresu,
sannan mai zaneshin ya shigo da zungura-zunguran bilalin rashes tsamiya,
niya yayi tare da yin kabbara,
sannan ya zaro bulala d'aya ya d'agota da iya k'arfinshi ya tak'ark'ara ya zabgawa Yusuf ita a tsakiyar bayanshi,
wanda kafin ya d'agotama shatin wurin yayi jazir,
shi kuwa Yusuf jin wani irin azaba daya ratsashi ya sashi rumtse idanunshi da k'arfi,
Safwan kuwa da sauran yan jarida tuni sun sami abin nunawa duniya da fad'a musu,
al'ummar wurin kuwa sai kabbara sukeyi,
yayinda Daddy da Jafar da Affan kuwa suke kuka da hawayensu a wani sashinma Malam jabir ma ya samu damar halartan wurin a matsayinshi na mumini ya halarci wurin kamar yadda ayar qura'an ta umurci muminai,
shima tuni yake zubda hawaye ganin yadda ake tabkawa Yusuf bulali,
gaba d'aya fatar bayanshi tayi jazir shi kuwa Yusuf tunda ya rumtse idanunshi a bulalar forko bai sake bud'esu ba,
sai karkarwa da jikinshi keyi.

A gida kuwa cikin rashin sa'a Mama ta lek'a parlour Hajja Inna da nufin ta kira Zahra tazo taci abinci,
sai ta samu tv Hajja Inna a kunne inda kai tsaye ake nuno Hukuncin da akewa Yusuf,
inda Zahra ta tasa tv a gaba tana kuka mara sauti,
Ummi na gefe tana ta murmushin mugunta Hajja inna kuwa fuska ta kwab'e tare da mita tana cewa.
"Wannan mai dukan ya cika mugunta ji yadda yake dakarmin jika kamar shi ya haifa min shi,
wai ko dai kasheshi ne yakeda niyar yi?."
da sauri ta zabura ta mik'e lokacin da aka zubawa Yusuf bulala ta 58 wacce tayi sanadin fashewar fatarshi jini ya fara zuba,
bayanshi zuwa kafad'arshi zanen bulali sunyi rud'u-rud'u kuka Hajja inna ta saki da k'arfi ganin ya wurgar da wannan bulalar dan ta gutsustsure sai ya d'auko wata,
ai kuka ta farayi sosai tare da mik'owa Zahra wayarta tana cewa.
"Wayyo Allah zasu kashe min Yusufa,
ke Zahra maza ga wayata kira min Abbanku."
rumtse ido Zahra tayi da k'arfi lokacin da aka tsula mishi wata bulalar da saida jini ya rink'a bin bayanshi har zuwa k'afafunshi,
cikinta ta dafe jin wani irin juyi da harbawa da cikin yayi cikin sauri ta mik'e tare da cewa.
"ai gwara ki bari a kasheshi tunda kin tsaneshi,
in kin gama dashi sai kin dawo kaina tunda dama mu biyu kikafi tsana."
tana fad'in haka ta fice a guje,
ganin haka Mama ta juya tana kuka tabi bayanta,
Hajja Inna kuwa kuka takeyi sosai Mami da Zeenat suna tayata.

Aryan kuwa tunda ya rufe kanshi jiya sai yanzu ya fito da yaji yunwa zata kasheshi,
yana zuwa parlour Kaka ta sameta ta tasa TV a gaba tana kuka,
ganin abinda akeyi a tv ya sashi zamewa a gaban Kaka shima ya bud'e sabon shafin kukan,
a nan yake yiwa kaka bayanin abinda ya sa yayiwa Yusuf komai,
ai nan sukaci gaba da kuka nan tausayin Aryan ya kama Kaka tasan tabbas babu wanda zai fahimci Aryan a duniya dan ko ita sai yanzu ta fahimceshi da ya mata bayani.

A can kuwa kafin a yiwa Yusuf bulali 86 ya suma ,
amman ba'a gane ya sumanba yabida mafi akasarin wurin kuka sukeyi Affan da Daddy da Jafar sune suka gane ya suman,
sai Aryan da yake kallo a tv shima ya gane Yusuf a sume yake,
yayinda Abba ma ya gane Yusuf d'in ya suma,
yana shirin ya sanar dasu kuma sai yaga alamun ya farfad'o,
haka akaci gaba da yimishi *Hukuncin Allah* har saida aka gama bulalin kab,
sannan aka kunceshi,
cikin ganin duhu da jiri ya fara sauk'owa daga inda yaken yayinda duk inda ya taka k'afarshi sai ya bar shaidar jini,
tafiya yakeyi yana daddafe dan guntun bongon,
ida nunshi a lumshe dan jirin da yake gani yayinda hawaye ke bin fuskarshi still kuma fuskarshi d'auke da murmushin jarumta da sauri Daddy yayi kanshi,
yana zuwa ya ruggumeshi tare da tallafa mishi suka fara tafiya,
nanfa gaba d'aya akabi bayansu,
suna zuwa harabar court d'in motar furzin na isa wurin,
abinda yayi matuk'ar k'ona zuciyar masoyan Yusuf ya sasu kokawa magautanshi kuwa sukayi farin ciki,
ba yadda Daddy baiba a barshi suje asibiti a motarshi sam hukuma sunk'i dole akasa Yusuf a motar furzin,
sannan sukaje asibitin su Daddy yayinda hukuna suka kasa suka tsare,
kwanan Yusuf biyu a asibintunsu Daddy kula dashi sosai,
randa za'a wuce dashi furzin dashi kuwa
a harabar asibitin suka samu cincirindon al'uma masoyanshi da magautanshi,
yayinda yan jarida sukayi mishi caaa a kanshi,
duk da kakkareshi da ma'aikatan furzin d'in keyi suna tuture mutane domin su samu hanyar wucewa hakan bai hana wasu daga ciki matsowa inda Yusuf yakeba,
sun zo daf da motar har an bud'e mishi mota zai shiga sai ya kumo juyo fuska a d'an sake yayinda zuciyarshi ke harbawa yana ganin zallar soyayyar masoyanshi inda kuma yake ganin k'iyayyarshi a fili a kan fuskar magautanshi,
ido ya rumtse jin muryar Safwan yana maimaita mishi tambayar da yayi mishi.
"Duni zasu so su san ya kaji a lokacin da aka yanke maka hukunci a matsayinka na k'azami kuma mazinaci, maso yanka zasu so su san yadda ka tsani kanka tunda wata hud'u baya ka shaidawa duniya ba abinda kafi tsana kamar zina da mazinata,
in baka manceba in tambayeka me kafi kyankyamin, a lokacin cikin izza kace ba abinda kafi kyama sai zina da mazinata inda ka k'ara da cewa in dai kasan mutun mazinaci ne baka cin abin hannunshi koda kuwa fura da nono ya baka,
to dan haka masoyanka na son jin ta bakinka?."
murmushin k'arfin hali yayi tare da taune lips enshi tsayuwarshi ya gyara tare da yin gyaran murya cikin iya sarrafa harshe yace.
"Masoya na, ku tayini addu'ar Allah ya bani damar cinye wannnan jararbawar,
nasan masoyana na gskya sun san Yusuf ba mazinaci bane,
kuma ba k'azami bane,
k'addarar rayuwatace tazo a haka."
dariyar jin dadi Dafwan yayi lokacin da yaji wasu yan tsirarun matasa sun fara cewa.
"K'aryar banza mazinacin banza,
ai dama mugu shi yasan makoncin mugu in ba hakaba ya za'ayi kasan mazinaci har kace bazaka ci abin hannunshi ba,
in dai ba tare kuke holewarku ba."
sai kuma suka rink'a ciro takalmansu suna jifarshi dasu,
shi kuwa Yusuf kauda hankalinshi yayi tare da juyowa gun da Matawalle ketsaye yana mishi tambayar mutunci cikin tausayin Yusuf d'in yace.
"Wata hudu zuwa na biyar da suka wuce ka shaidawa duniya,
dukkan nasara da d'aukaka tana tare da k'alubale,
yayinda nace da kai shin ka tab'a fuskantar k'alubale,
a lokacin kace dani baka tab'a fuskantaba sai dai zuciyarka na cike da fargaba domin kasan dole ita nasara tana tare da k'alubale."
sai ya kumayi shiru yana k'ok'arin maida hawayenshi, shi kuwa Yusuf murmushi yayi still kuma hawaye na tsiyaya a idanunshi,
hakan yasa Matawalle yaci gaba da cewa.
"Mosoyan sun koka da irin zazzafan k'alubale da ka fuskanta,
ta sanadiyar aminka abokinka barrister Aryan,
na lek'a shafu kanka na yanar gizo-gizo kama daga Facebook, instagram, You tube, what's app duk inda na shiga babu abinda ke yawa sai maganarka,
hakan yasa cikin wattannin hud'unnan naga k'arin masoyan da ka samu a instagram sama da dubu 60 hakama duk a sauran shafu kanka naga ka samu yawan masoya harma da mak'iya domin mafi akasarin shafukan naka fad'ace-fad'ace akeyi wasu na zaginka wasu na kareka,
yayinda mafi akasari sukebin Barrister Aryan da tofin Allah tsine,
duk da basuji ta bakin kaba,
amman sun matsu da su san matsayin Aryan a wurinka?."
ido ya lumshe tare da bud'esu cikin tattausan lafazi yace.
"Aryan ba abokina bane shi d'an uwanane Aryan aminine kuma shak'ik'inane,
duk mai sona yaso Aryan domin Aryan shiya assasa Yusuf Aryan ne ya samar da Yusuf,
duk mai k'ina to tabbas yak'i Aryan,
masoya na kunji matsayin Aryan a gareni bai samu rauniba."
Aryan kuwa dake jin kalaman Yusuf a radio Baba mai gadi kife kanshi kawai yayi tare da zubda hawaye,
dama yasan ko duk duniya zasu manana mishi zato to Yusuf zai kyautata mishi zato.

Matawalle kuwa cikin yarda da tsarkakar zuciyar Yusuf yace.
" Toh har lau masoyanka zasu so sanin matsayin barrister Affan a gareka?."
Murmushi yayi saida hakwaranshi suka bayya baki d'aya sannan hawayenshi suka zubo cikin tank'oshe kai bisa kafad'arshi yace.
"Barrister Affan wani sashine daga cikin shasukan jikin Yusuf,
Affan da Jafar sune Garkuwar Yusuf,
Affan wani jigone na tabbatuwar farin ciki da darajar Yusuf,
shi Affan shine laimar dake kare Yusuf daga dukan ruwa ko tsananin rana,
Affan ngd matuka Allah bar zumunci da qauna a tsaka ninmu."
ya k'arishe mgnar tare da zubda hawaye,
da yawa mutanen wurin zuk'a tansu sun raunata yayinda tuni wasu sun zubda hawaye,
ganin haka d'aya daga cikin gandu robobin ya bud'ewa Yusuf mota tare da cewa.
"Mu tafi."
juyawa yayi har yasa k'afa zai shiga motar sai yaji tambayar da Matawalle keyi mishi ya cancanci a bashi amsa cewa yayi.
"A hirar da akayi da Malam Jabeer jiya bayan yanke hukunci da kotu tayi,
ya shaidawa manema labarai cewa,
ya koreka daga team d'inshi ya kuma k'ara da cewa baza'a baka damar asassa team naka na kankaba ya kuma ce babu team da zata kuma k'arb'arka aiki a fad'in k'asar nan,
shi me gskya lamarin sannan wanne mataki zaka d'auka?."
cikin sunkuyar da kai alamun girmamawa yace.
"Abinda shigubana ya fad'a hakane na kuma cancanci ko wanne hukunci daga gareshi,
kuma zanyi k'ok'arin inga abinda duk ya fad'in ya tabbata,
ko dan in bawa magautana damar suje su gwada tasu bajintar."
yana fad'in haka ya shiga mota,
yana shiga direba yaja suka tafi,
Matawalle kuwa cikin jin dad'i ya juya ya tafi domin ya fahimci amsar Yusuf ta k'arshe da Safwan yake bi ma'ana Safwan yaje ya gwada iyawarsa a gasar would polo da za'ayi wata biyar masu zuwa.


Rayuwa dai taji gaba da tafiya yau fari gobe tsumma,
wata rana farin ciki wata rana akasin haka,
Yusuf dai yana can yana rayuwar furzin cikin salama,
domin ba duka ba zagi sai d'ai k'uncin zuciya,
Affan na yawan kai mishi ziyara,
hakama su Daddy, Jafar, Faisal, Raihana, Hajia Kaka, Uncle Gambo, da Tatti mahaifiyar Aunty Amarya kenan in tazo tayi ta kuka.

Raihana kuwa kwata-kwata tak'i ta saurari Aryan fushi takeyi dashi sosai,
Aryan kuwa kunya ta hanashi zuwa gun Yusuf.

Idi kuwa ya d'auko Mahaifiyarshi wanda yawanci tare suke zuwa wurin Yusuf itama tayi ta kuka tana bashi hak'urin jarrabawarshi domin idi ya gaya mata gskyar lamarin.

Zahra kuwa rayuwa tayi tsanani tako ina tana fuskantar illar da matsala da wad'anda tsautsayin fyad'e ya far musu,
domin ko motsin kirki tayi sai Ummi ta yab'amata bak'ar mgna,
a d'aya gefen uwar data haifeta da kanta ta tsaneta domin ido da ido Aunty Amarya ke cewa in taga Zahra da cikin jikinta ji take kamar ta fad'i ta mutu dan bak'in ciki da tsanar cikin,
haka nan Abba ma yakejin ya tsani abinda ke cikin nata tun kan a haifeshi,
Hajja Inna kuwa sai abinda ya k'aru kunsan camfin mutane wai in akwai mai cikin shege a wuri wai mala'ikun rahama basa zama wurin,

Mama da Daddy da Jafar da Mami da Zeenat su kad'aine ke tausayawa Zahra domin Ya Sulaiman da Nana ma layin Ummi suke,

Zuwa yanzu cikin Zahra ya girma tirtsi-tirtsi dashi,
tayi wani irin fari da rama mai yawa,
sai k'aton cikin,
Adda Zulaihat na yawan zuwa hakama Amira itama irin Jafar ce tana son Zahra da tausaya mata,
kamar kullum,
yau da sassafe Ummi tazo part d'in Mama inda ta samu Zahra na konce kan 3 str Mama na zaune ta wurin k'afafunta,
ta d'aura k'afafun Zahra kan cinyarta tana d'an mammatsa mata dan kumburan da sukayi,
ganin Ummi yasata zuba mata ido,
ita kuwa Ummi cikin tab'e baki tace.
"Ke uwar d'an shege ai sai kin fito kiyi mana sharar tsakiyar gidan,
domin Nana cikinta ke ciwo, Zeenat kuwa tayi sammako ta tafi makaranta,
kinga Mami kuwa bata nan."
da yake tunda Amira ta haihu Mami taje gidanta yanzu wata kusan uku kenan tana can da take CS akawa Amiran,
cikin sanyin rayuwa data koma yanayin Zahra ta yunk'ura ta tashi tare da gyara zaman wuyan hijabinta cikin sanyi tace.
"Toh Ummi bari inje inyi fitsari sai inzo."
cikin fad'a tace.
"Bana sun muna furci fitsarinki da baya k'arewa bini-bini kinje yin fitsari,
ni kiyi maza ki fito kiyi mana sharar."
lips dinta ta taune tare da zubda k'ollah tace.
"Toh."
Mama kuwa cikin tausayinta tace.
"Bari inje inyi mana sharar."
cikin tsaurin ido Ummi tace.
"A lallai kam kakar d'an dakan kuka,
ai aikin ba naki bane itan dai zata zo tayi mana."
kai Mama ta jujjuya alamar ba matsala,
ita kuwa Zahra fitsarin taje yayi sannan tazo ta fara sharar tsakiyar gidansu da yake cike da intalos mai zane-zane kunsan shareshi da azabar wuya,
bata dad'e da farawanba wani irin azabebben k'warnafi ya rufeta ji takeyi cikin k'irjinta kamar wuta keci,
sai kuma tari a haka ta rink'a sharar tana d'aga k'afarta da keret,
tana zuwa d'ai barandar Hajja Inna amai mai bala'in zafi ya rufeta,
aman takeyi baji ba gani,
ai cikin rashin mutunci Hajja inna ta fito tare da cewa.
"To Wlh maza kizo ki wonke k'azantarki shegiya muguwa ki rasa inda zaki amayar da dafin kwaranafin d'an shige sai a k'ofata."
jin hargowar Hajja Inna ne yasa Mama fitowa,
Daddy kuma yana sama yana ganin abinda ke faruwa,
Mama kuwa tana zuwa ta k'arb'e tsintsiyar ta jefar sannan ta jawota gaban pompo ta rink'a sa mata ruwa tana wonke k'afafunta da aman ya tattab'a,
tare da kuskure bakinta,
sannan taje ta wonke wurin ita kuwa Zahra sai hawaye ke bin fuskarta zabida zafi da zuciyarta keyi,
Daddy ne ya sauk'o zuwa inda suke cikin tausayawa yace.
"Goggon Abba daga yau karki sake yin shara kinji ko sai kin samu Lfy."
kanta ta gyad'a tare da goge hawayenta,
Hajja Inna kuwa sai masifa takeyi.

Haka dai abin yayi ta tafiya,

Yau ta kasance ranace ta musamman a tarihin Safwan domin shi aka saka a madadin Yusuf d'in,
sunje da kyar aka yarda,
cikin rashin sa'a kuwa tun a zoggon forko aka koro Nigeria gida,
inda wannan abu yasa al'ummar k'asarmu kuka,
mosoyan Yusuf begensu garshi ya taso,
mu samman cikin jihar Adamawa duk anbi anata yayyage kalandu Safwan da aka lillik'a.


Bayan kwana biyu da faruwar lamarin.

You Zahra ta tashi da zazzafan nak'uda,
abin tun asuban fari,
amman har zuwa azahar abu yaci tura,
Daddy da kanshi ya turo masu karb'ar haihuwarta daga asibiti domin baya son mgnar haihuwar ta bazu yanzu yan jaridu zasuyi musu caa a kai,
Mama kam gaba d'aya ta rud'e domin ga nak'uda gadan-gadan sai yaro ya k'asa sai ya kuma komawa sama kan k'irjinta lokaci d'aya numfashinta sai ya fara fizga,
ga jini da yaketa zuba,
ganin hakaba Mama ta kira Daddy ta gaya mishi,
halin da ake ciki,
ba b'ata lokaci ya kira Jafar yace maza yaje ya daukosu ya kawosu asibitin su,
haka kuwa akayi.

Bayan sun isa ba jimawa aka shiga da ita d'akin tiyata tare da manyan likitoci,
cikin sa'a aka samu nasarar ciro yaro na miji fari k'al dashi kama da Zahra sak da sak,
cikin k'ank'anin lokaci aka kimtsata ita da yaro cikin ink'antacciyar kulawar manyan likitoci.

Kafin zuwa dare labarin haihuwar Zahra ta bazu ko ina cikin d'angi da mak'ota.


Affan kuwa tunda yaji lbrin haihuwarta yaketa cuku-cukun yadda zai samu a b'ar Yusuf suje asibitin,
shine bai samu wannan damarba saida ya kakanshi sarkin Adamawa yasa baki sannan aka basu daman zuwa inda aka basu awa 3,
sannan aka had'asu da gand'u robobi 2 yan rakiya,
ba yadda Affan baiba akan a bar Yusuf ya canza kaya amman sunk'i.


Da yammacin ran jumma'a suka samu damar zuwa asibitin a motor furzin yayinda motar Affan da fadawanshi ke biye dasu a baya,
suna fita kai tsaye d'akin da Zahra take suka nufa,
suna zuwa duk sauran suka tsaya sai Affan da Yusuf d'inne suka shiga,
a hankali suke tafiya har zuwa bakin k'ofar mashigar inda gadon nata yake,
Affan ne a gaba dan haka shi yayi sallama tare da turo k'ofar suka shiga,
ita kuwa Zahra tana konce kan gadon a rigingine,
tana kuma fuskantar hanyar shigowar,
gefenta kad'an kuma jaririn ne a konce an shiryashi cikin wasu fararen kayan sanyi masu taushi da tsananin kyau yanata baccinshi,
jin sallamar da akayine ya sata d'ago kanta daga kallon jarin,
ta maida ida nunta kan k'ofar,
Affan ta fara gani hakan yasa ta gyara zan siririn gyalen daya sub'ale yabar gashin kanta a woje,
ta d'ago kai da nufin yi mishi sannu da zama kenan,
tayi ido hud'u da fuskar Hamma Yusuf d'insu cikin shigar fursunoni,
wani irin bugawa k'irjinta yayi lokaci d'aya hawaye suka cicciko mata idanunta,
kanta ta sunkuyar yayinda tuni hawayenta suka fara kwaranya,
Affan ne ya zauna kan kujerar dake wurin,
cikin jin tausayinsu ya kalli Yusuf tare nuna mishi bakin gadon kusa da yaron a hankali yace mishi.
"Ga wurin zama."
shiru Yusuf bai kulashiba itama Zahra bata kuma d'ago kanta ta kallesu ba,
ganin hakka Affan ya mik'e da juyawa ya fita yana cewa.
"Bari inje wani wuri ina zuwa yanzu,
kayi maza kasan awa 3 aka bamu."
dukansu ba wanda yayi mgna shi dai Yusuf sai ido ya bishi dashi,
har saida yaga ya fita ya jawo k'ofar ya rufe,
sannan ya juyo kan Zahra wacce take sunkuye da kanta tana zubda k'ollah tare da murza yatsun hannunta,
shi kuwa Yusuf idanu ya zuba mata na tsawo 2 minutes sannan ya fara taku a hankali har zuwa gaban gadon,
yayinda bugawar zuciyarshi ke tsananta,
itama Zahra a gefenta haka abun yake,
shi kuwa hannunshi yasa ya d'auko yaron ya ruggumeshi cikin tsananin bugawar zuciya,
sannnan ya jawo kujerar da Affan ya tashi a kai yanzu,
ya turota kusa da gadon,
zama yayi tare da zubawa jaririn ido,
shi kuwa jaririn tunda Yusuf ya kai hannunshi jikinshi ya bud'e ida nunshi rakwal dasu sai mutsu-mutsu yakeyi,
shi kuwa Yusuf kanshi ya sunkuyar ya sumbaci goshin yaron tare da medashi jikinshi ya ruggumeshi,
yana jin tausayin yaron na ratsashi,
kanshi ya d'ago ya zuwa Zahra idanu wacce itama su take kallo ganin ya d'ago kanshi ne yasa ta kauda kai,
cikin nitsuwa ya gyara zama tare da tsura mata ido murya can k'asan mak'oshi cikin kasala da sanyi ya bud'i baki a hankali yace......!




By
*GARGUWAR FULANI*


Jttwl







"Ya jiki?". kai ta k'ara sunkuyarwa tare da rumtse idanunta,
nan hawayenta suka samu damar zubowa baki d'aya,
shiru tayi kamar bata jishiba shi kuwa ido ya kauda a kanta tare da meda kallonshi kan yaron,
wani irin tausayin jaririn yaji yana ratsa zuciyarshi dako wanne sashi na jiki da ruhinshi,

Please Login or Register in order to submit comment