Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wurin su Aryan.

Tofa daga nan suka mik'a kan practical da ake musu babu kama hannun yaro,
yakanyi woya da Zahra akai akai ,
sosoi ya meda kai kan shirye-shiryen gasar da yanzu saura kwana,
biyar a yita.

Yakan kira Maman Yusuf da Abban shi da Zahra yana cewa sufa dage da addu'a in suna son yayi nasara.


Yau ta kama saura kwana biyu gasar,
kuma yau kwana uku kenan basuyi mgna da junaba,
ta idar da sallan isha kenan tana bisa sallaya tanata mishi addu'o'i kiranshi ya shigo woyarta.
saida ta shafa kana ta amsa kiran tare zamewa ta konta bisa sallayar cikin sauk'e numfashi tace.
"Sallam Hamma Yusuf."
cikin shauk'i yace.
"Wayyo Allah na Ummu Aryan na gaji."
a hankali tace.
"Sannu Hamma Allah dai ya baku sa'a."
"Amin Amin." yace tare da cilla polo ball dake hannunshi Affan dake gefenshi ne ya cab'eshi,
shi kuwa Aryan murmushi yayi tare da cewa.
"Ummu na."
shiko Yusuf mik'ewa yayi ya shige bedroom enshi.
nan sukayi ta shan hira.
daga bisani yake ce mata.
"Auren Abdul-kareem d'ina ya kusafa."
a hankali tace.
"A Masha Allah yaushe ne?."
cikin rad'a yace.
"Zaki zo ai tare zamu wuce k'asarsu."
ido ta lumshe tare da cewa.
"Kai Hamma to sai incewa su Mama ina zanje?."
numfashi ya fesar kana yace.
"Kice musu zakije auren abokin mijinki, kuma sai kin biya wurin mijinki,
dan ina son kizo kiga yadda zan buga world polo da idanunki."
murmushi tayi tare da cewa.
"Wato dama shiyasa kasa Ya Jafar ya ya kaini akamin E passport?."
cikin rad'a yace.
"Nayi laifi ko?."
a hankali tace.
"Baka laifi ai." murmushi yayi kana yace.
"jibi ne zaku taso kuma jibin ne da yamma za'ayi
gasar."
"Toh Allah ya kaimu."
tace.
shi kuwa cikin yin k'asa da murya yace.
"Me zaki kawo min?."
"Kayan dad'ihhhhhhhhh zan kawo maka."
ta bashi amsa cikin tada mishi tsikar jiki.
haka dai sukayi ta hirarsu daga bisani sukayi sallama bayan ya shaida mata ai su Mama sun san da tafiyar tata,
dan ya gaya musu.

Toh daga nanfa ta fara shirin fecewa wurin oganta.

Yayinda shima ya shiryawa zuwanta dan ya bar d'akin dake kusa nasu Affan,
ya koma samansu.

A gida Nigeria kuwa yanzu cikin Sakina ya girma,
kana auren Jafar da Dija ansa rana da auren Safwan da d'iyar Goggo Maimuna suna dawowa da wata biyu ne za'ayi bikin.

Tunda wuri Jaafar ya kaita airport dake sai da suka gama Shirin su gaba d'aya Basu wani b'ata lokaci ba aka fara Kiran passingers suka shiga jirgin su ya Lula. Lumshe idanuwan ta tayi ba abinda take sai Allah Allah ta sake ganin Yusuf d'inta Dan ita kanta a yanzu ta gama yarda Yusuf shine farin cikinta, kanta tasa ta jingina da jikin kujera tana tuna rabuwar su dashi murmushi tayi. Jaafar na kula da ita shima murmushin yayi aransa Yana mamakin yanda lokaci d'aya suka maida kansu kamar wasu Laila-majnun, a haka bacci mai Dad'i cike da mafarkin Yusuf ya rufeta. Sun D'an ja lokaci sannan suka isa direct masaukin su Jaafar ya kaisu' akan su shirya Dan lokaci kad'an ya rage a fara tseren a gaggauce ta shirya Dan abinci ma kad'an taci Dan tafi bukatar ganin Yusuf fiye da shi atamfa tasa fara mai ratsin kalar ganye ta nade kanta da laffaya kalar ganyen da ratsin fari ajikinta kadan. abinka da farar fata sai tafito shar ta ita. Jaafar na gaba tana bin sa a baya, suka hau mota zuwa wajen da ake gasar dake ba Nisa da masaukin su nan da nan suka isa.

Yusuf tunda Jaafar ya fad'a masa tahowarsu yake cikin farin ciki lokaci zuwa lokaci ya saki murmushi Yana tuna kwayar idonta da ya hango zallar kewar sa da soyayyarsa da ya gani cikin idanuwan ta. Har suka shigo cikin filin bai daina hange hange ba Dan burinsa idanuwan sa sugane masa ita, hawa kan dawakan sukayi nan da nan manyan cemaru suka fara haskosu suna maganganu akansu, wajen ya rude da sowa daidai nan Jaafar ya shigo shida Zahra caraf idansa ya sauka akanta tana tafiya a nutse kanta akatsa murmushi yayi, bai San lokacin dayayi wani zillo ya sauko daga kan dokin ya tako da sauri idanuwan mutane sukayi caa akansa musamman M.Jabir, d'ago Kai tai ta gansa ya tunkarota fuskar sa k'unshe da murna tuni ta manta ta a inda take ta saki fuska tana masa wani irin kallo Wanda ya k'ara jefasa cikin wani yanayi yasa shi gudun dai bai shirya ba tsalle yayi ya haure wajen filin. Yana zuwa ya rungumeta da dukkan k'arfinsa, tun saukar Yusuf cemera ke binsa har zuwansa Gaban Zahra da rungumetan da yayi, mutane suka bisu da kallon birgewa da sha'awa. wannan ya nuna Yusuf na matuk'ar son matarsa y'anmtan dake wajen musamman masu son Yusuf turawa suka had'iyi yawun daya tsaya musu a makoshi

Maman Yusuf da sauran yan gida kowa yaga abinda yafaru tsit falon yayi duk Wanda ka kalli fuskarsa kasan k'asan ransa fal murna da farin cikine, murnan su kasa b'oyewa tayi sai da sukayi dariya Abba fakar idon su yayi ya rad'awa maman Yusuf "yara k'anana sun iya soyayya." Dariya tayi cike da nishad'i da kyafta masa ido d'aya.

Rungumeta yayi tsam ajikinsa Yana mata magana a kunne. Dariya ta zame tana kallon yanda kowa na wajen ke kallonsu, da sauri ta zare ido ta kwab'e fuska.

dariya yasa sosai yace "ki kular min da kanki." Ya juya cikin gudu sosai Yana zuwa ya hau kan dokin aka Fara gasa. Komawa tayi ta zauna jikinta Banda rawa ba abinda yake zamanta ke nan suka Fara gasar.


Cikin k'warewa yusuf ke sarrafa dokin sa kana gani kasan yasan takan gasa, k'in kula polo ball d'in yayi Dan shi yasan irin dabarar daya tanadarwa kansa. hakan yasa M.Jabir ya Mik'e Yana nunawa Yusuf d'in ya amsa murmushi yayi ya cigaba da sarrafa dokinsa har sai da lokacin daya sa yayi daidai da amsar yasa ya k'ara kaimi Yana zuwa abokin gasar ya buga ball d'in sama Yusuf yasa stick dinsa ya tare cike da k'warewa ya shawo kan dokin ya cigaba da bugata Yana k'ara kaimin cigaba da gudun. da mamaki mutane ke kallonsa Dan gudun da yake da kuma sarrafa ball d'in hakan abune Wanda mutane ke ganin bazaiyuyu ba. Nan da nan ya Basu tazara hakan ya tunzira abokan karawar sa suka k'ara kaimi wajen ganin sun kamosa amma ina nan da nan wajen ya rud'e da sowa ta ban mamaki cikin gwaninta yake buga ball har Yana Wasa da ita da stick d'in hannunsa mutum biyune suka cimmasa da matsiyacin gudu Yana ankare dasu suna isa inda suke ya cilla ball d'in ya bita cikin mugun gudu ya cafeta da stick dinsa ya kara kaimi wani ihu yan Nageria suka sa suna mamakin Yusuf shi kam ganin Zahra dayasan tana gabansa. ya k'ara nuna kwarewarsa da zafin namansa, ilahirin jamaar wajen cike suke da mamakin irin salon da Yusuf yake fuskar sa cike da annuri Kai bakace a wajen gasa yake ba sassautawa yayi da gudun hakan yasa abokansa suka kusa cimmasa ganin sun kusa yasa shi zabura da shida dokin Wanda sai da sukayi tsalle suka dire ya zuga aguje Yana jefa ball har suka isa lined ending buga stick din yayi daidai lokacin ya saki limzamin cike da gwaninta dokin yayi tsalle hakan yasa mutane ihun murnan Yusuf yaci gasa, tsallen da dokin yayine cikin k'ank'anin lokaci Yusuf ya fad'o, dokin ya sauke kofatonsa kan hannun Yusuf ya yankesa sosai hakan yasa Yusuf wata k'ara nan nan da nan jini ya balle. Arazane Zahra tasa ihu tana kallon Yusuf na rik'e da wajen da jinin yake zuba Yana runtsa fuska da gani kasan Yana matuk'ar jin zafi. Cikin azama ta k'walla masa Kira cikin kuka da Firgici tace.
"HAMMA YUSUUUUUF!!!" a guje tayi cikin filin tana kukan kiransa Dan daga k'arshe ma bajewa yayi ak'asa Yana maida numfashi mutanen wajen abinka da turawa jin ta ambaci sunansa yasa Suma suka rud'e da Kiran sunansa suna jinjinawa. Cikin lokaci kankani ta isa kansa had'e da mannasa a jikinta sosai, tana kuka da sauri masu kula da marasa lafiya na wajen suka isa da kyar suka b'anb'are Yusuf a jikinta Dan cukukuyesa tayi tana kuka ka shirb'an kamar zaa kwace matashi.

Maman Yusuf ma Mik'ewa tayi da sauri jikinta na karkarwa Dan cemeras sun hasko ciwon da Yusuf d'in yaji duk da cewa shine yaci gasar rintse idanuwan ta Mama tayi tana jin ciwon kamar a cikin ranta shi kansa Abban ya tsorata sosai ta maza yayi ya rarrashesu aransa kam shiyake ganin yadace a rarrasa Dan shikad'ai yasan zafin dayaji.
Media kam ta dauka Dan tuni vedion da abin ya faru ya cika media jikin kowa yayi sanyi duk da ana murnar nasarar da aka samu sai dai fad'uwar da Yusuf yayi da ciwon yasa tausayin su harda na Zahra kamasu Dan ita kuka take sosai jinin Yusuf d'in ya bata duk jikinta.

Cikin fili kuwa ya rude da Kiran "YUSUF ! YUSUF !! YUSIF!!!".
Yana jin su kaf aransa, Yana murna da kuma godewa Allah akan nasarar da ya samu uwa uba Yana jinsa kwance jikin Zahra Dan k'in yarda tayi su rabata dashi a jikinta akayi masa dressing. Ana gamawa ya kalleta had'e da kashe mata ido d'aya idonta ya cicciko da hawaye da sauri ya Girgiza mata Kai k'ara rikesa gam tayi tana kyafkyafta ido. mutane ne sukayo caa kansa suna tayasa murna da kuma masa sannun ciwon dayaji kowa awajen son ganin Yusuf yake, da son d'aukan sa hoto hakan yasa yan team d'in su fita da Yusuf d'in Dan mutane sunyi masa yawa kodan ciwon da yaji yasamu relief.

Nageria kam ta hau sowa da ihu musamman media kowa ya manna hoton Yusuf da Zahra lokacin data shigo filin ya rungume ta, ba abinda kakeji sai murna da sowan mutane kowa na adduar Allah ya bawa Yusuf lafiya.
Turawa kam gidajen tv nasu ba abinda suke sai tattauna gwanintar Da Yusuf yayi da kuma salon wasan da yayi yau, Wanda baa tab'a kwatanta irinsa ba wannan yasa duniya na masa kallon wani mutum na dabam me hikima da iya wasan polo Wanda baa taba samun kamarsa ba.


Sai yamma liss suka isa masaukin su hannunta rik'e da kit din da aka bata akan ta dinka wanke masa ciwon da yaji tana canza bandage d'in da aka sa masa. M.Jabir tafiya yayi ya barsu Affan, Aryan da Jaafar a gabansu take nan nan dashi shi kansa Yana matuk'ar jin dad'in kulawar data ke bashi agaban kowa hakan yasa yake nuna mata ba komai Dan hankalinta amatuk'ar tashe yake rakiyar su Aryan ma da kyar ya lallasheta ta barsa ya fita.

Fitarsa yasa ta shiga wanka ta canza da rigar bacci me kyau marar hannu kalar ja me ratsin Baki ta d'auko kit tana jiran shigowar sa. Da sallama ya shigo ta amsa idonta akan ciwon nasa ganin bandage d'in jini ya jikasa, yasa ta k'arasa da sauri ta rik'o hannunsa ta zaunar dashi gefen gadon da suke a hankali ta Fara warware bandage d'in, Yana sane yace. "washhhh!" Idonta ya cicciko da hawaye nan da nan ya Fara zuba. ta d'auko swab ta sunkuyar da kanta ta Fara goge ciwon k'amshin turaren da kanta yake da roll d'in data shafa ya fisge sa ya Fara shinshina gashin a yunwace Yana kissing din su had'e da wuyanta Yana k'ara sunne bakinsa daidai kunnanta kissing din forehead d'inta yayi ta d'ago Kai suka had'a ido idansa yayi jajur Dan wajen na masa suka sosai. A haka ta gama idonta na zubda hawaye. Mik'ewa tayi da mayar da kit d'in a tsaye ta gansa ya zuba mata idanuwa Yana mata wani mayen kallo kusa dashi ta tsaya hannunsa ya me lafiya ya janyota kusa dashi Yana shafa kanta, hawayen daya mak'ale ya sauka da sauri cikin kulawa ya ya sa harshensa ya lashesu Yana Girgiza mata Kai cikin wata rikitacciyar murya ya Fara magana cike da lallashi "bana San kukan nan naki, nifa lafiya nake kawai y'ar kurjewa ce, kin gani lafiya nake ba abinda zai samu Yusuf d'in ki kinji" sunne kanta tayi a k'asa tana jinjina Kai d'ago da kanta yayi Yana murmushin karfin hali Yana kallon jikinta da rigar da tasa ta fito da surorin ta musamman kirjinta lura tayi ta juya da sauri janyota yayi Yana dariya cikin kunnanta ya rad'a mata.
"Yaufa lilon da zanyi na musamman ne dan k'ishi ya kusa kasheni dan haka ki..." Bai k'arasa ba ta rufe masa Baki da hannunta tana zare ido fuskarta a sake duk da idonta jajir yake sbd kukan data ci.
"Uhm" kawai tace rungume ta yayi yana jin wani iri har cikin k'asan ransa itama matseshi tayi gam aranta tana jin d'umin jikinsa a cikin jikinta. Tausayin sa ya kamata d'ago da kanta tayi suka kalli juna matsowa tayi da bakinta da alama kissing d'in sa take sonyi wani zillo yaji jikinsa yayi da sauri ya tarbi lips d'in ta yai musu masauki cikin bakinsa Yana shansu hannunsa me lafiyan ya cusa cikin rigarta Yana matsa sassan jikinta itama hannunta tasa cikin rigar sa tana shafa kirjinsa had'e da matsa nipple d'in sa rikita shi tayi tsayuwa ta gagaresu suka kwanta bisa k'aton gadon d'akin da kanta Zahra ta cire masa riga ajiyar zuciya ya sauke da k'arfi ya zame rigarta idanuwan sa suka ci karo da lollipop d'in sa da sauri ya Kai bakinsa ya Fara zuk'arsu k'ara bank'aro k'irjinta tayi hakan ya k'ara masa k'aimi har ya Kai inda yake son cimma tare da gudun mawarta Dan yau ta bashi had'in Kai fiye da yanda yayi zato Banda sa mata albarkaba abinda yake,

Kwance suke sai maida numfashi suke hannunsa yasa Yana shafar jikinta santsi da laushin fatarta na sashi lumshe ido a hankali hannunsa ya sauka kan cikinta hannunshi ya kuma mannawa kan cikinta jin cikinta yayi d'as dashi a cikin dariya ya k'ara tab'awa jin tabbas wajen a cike kana yayi tauri ga kuma cikin ya d'an taso wurin kuma ya d'anyi d'umi sai d'an harbawa da wurin yakeyi da sauri ya Mik'e jiki na rawa ya kallenta cikin blanket d'in.
sai ya kuma janye blanket d'in.
tashi tayi da sauri tana kallonsa tare da kare k'irjinta. K'urawa k'irjinta ido yayi ganin duk da karesun da takeyi basu karuba sunyi lumtsum lumstum dasu sun k'ara girma da cika wani irin kad'uwa yayi sam, ya manta da ciwon hannunsa ya rarumeta ya d'agata Yana zagaye da ita cikin d'akin cike wata iriyar murna da tsananin farin cikin da Zahra bata tab'a ganinsa ciki ba direta yayi Yana kallon k'irjinta Yana lashe lips ensh dariya tayi ta tafi da sauri zata rufe jikinta ya bita ya rik'eta yana Girgiza mata Kai cikin dariya da zallan farin cikin da Shauk'i yace.
"Wayyo Allah na Ummu Aryan tsaya! yanzu bake kad'ai bace, wannan gudu sai ki motsamin tattalina ki wahalmin da gudan jinina." Cikin jin kunya da jin dad'in yadda ya shiga farin cikin ganinta da jikinshi,
dan dama tak'i gaya mishine dan tafi son ta mishi ba zato ba tsammanin in ya kuma Nigerian ya ganta da cikinshi wanda ko su Mama basu san da shiba dan ita ba mai halittar laulayi bane,
to kuma sai gashi yasa an kawota,
kallon shi tayi cikin kunya rufe idonta tare da kamo hannunshi ta d'aura kan cikinta,
gyara zamanshi yayi ya d'orata kan cinyarsa yana cigaba da karewa k'irjinta kallo kwab'e fuska tayi tana magana.
"Nifa Hamma Yusuf.." cikin kwaikwayonta shima Yance. "Nifa Hamma Yusuf."
dariya ya bata ganin yadda yayi,
sai ta kuma kalli inda yaji Ciwo har bandage d'in yayi jini cikin tausayi ta sa bakinta tana hura wajen,
rungumeta yayi yana tuna rabon shi da ita.
Ashe har Allah ya sake basu wani d'an k'ara k'ank'ameta yayi cikin murna ya da zallan farin ciki yace.
"Alhamdulillah, Allah na gode maka da kyautar da kaimin ya Allah ka sauk'i Ummu Aryan d'ina Lfy,
Zahra Allah ya miki al'barka."
Cikin jin dad'i tace.
"Amin Abeeh Aryan." cikin ruggumota tambayeta. "Yaushe ne last period d'in ki?".
bazata taji tambayar shiru tayi tana tunani dan ita tunda tayi jinin haihuwan Aryan bata kuma yin jiniba saida,
yayi tafiyarnan da wata d'aya hakanne yasa ta gane wato ita sai in tanada ciki take al'ada.
jin tayi shiru yasa shi murmushi Yana mamakin shirmenta da wawtarta kenanma bata san watannin cikin ba,
ganin yana mata kallon yarintane yasata cewa.
"Cikin wata ukune ya d'an shiga na hud'u."
sai ta kuma tura baki tare da cewa.
"Ni bana bin wota sai kayi lilo ne sai inga na fara, hakama yamin a cikin Aryan."
ruggumota yayi cikin tsananin farin ciki yace.
"Baby dole in k'ara kud'in sadaki dan ked'in ta dabance, irin wannan kayan harka babu fashin k'arshen wota ai ni Allah yamin rahamomi da yawa."
cikin begen juna suka kuma ruggome juna suka koma ruwa.


Daren ranan kam, Yusuf fur ya zage kamar zai maida ta cikin jikinsa daga ita harshi duk sunyi farin Daren da kuma jinsa na musamman a wajensu Dan itama Zahran ji tai sam bata gajiya dashi Dan haka cikin jikin juna suka kwana.

Kwanakin da sukayi ya zame musu kwanakin da bazasu manta dasu ba arayuwar su Dan kowa na kaffa kaffa da d'anuwansa tamkar zasu cinye juna Dan tausayi da soyayya. Anan America y'ar k'aramar walima akayi saboda ciwon da Yusuf d'in yaji acewar su kwara abarsa ya huta hakan tasa baa wani tsawaita walimar ba akayi aka gama tare da manyan team d'insu wakilai da manyan mutane na nan America,

Bayan an gama ne su Jaafar da Safwan suka hau shirye shiryen komawa 9ja su kuma su Affan da Aryan zasu bi su Yusuf Egypt wajen bikin Abdulkarem.
A jirgi ma Yusuf rungume yake da Zahran sa Dan tuni ya Bawa su Affan Baya Suma suna bayansa suna masa shak'iyancin Wai "aiki yazo ga ma'iya." sai dare suka sauka Egypt, sun samu tarba daga k'asar Dan Kai kace da Rana yazo yanda kowa na wajen ke son had'a hannu da Yusuf da kyar Abdulkarem ya sasu a mota shida Zahra ya Kai su masaukinsu. Bayan sun saukaa kayataccen d'akin su shi da kansa yaiwa Zahra wanka Dan yace bai son ta wahalar masa da tattalinsa. Itakam tunda tazo America taga Yana matuk'ar kula da ita. ita kanta tana matuk'ar son zama ajikinsa ga yawan son kasancewa da take dashi tarasa dalili Dan kullum ita tashi kamar su had'iye kawunan su.

Washegari shine ranan da zaayi walima. Doguwar riga tasa milk colour tayi Rollin din kanta da gyalen rigar Wanda yafi background din rigar duhu yayi sak kalar kwalliyarda akayiwa rigar da stone daga kasa daidai forehead dinta tasa rings flower ya zagaye goshinta bayan ta ci kwalliya kallon sa tayi yasaka riga Fara tass ya Dora riga blue asama mai yankakken hannu ya sa blue din tuta asaman riga "mashaa Allah." Ta fad'a fuskarta da murmushi tana kallon sa shima kallonta yayi cike da so Yana kallon tsantsan kyan da tayi driver ne yazo ya d'aukesu Dan su Affan tuni suka kyalesa a cewar su kwara su kyale su, su cinye kansu, su huta.

Isar su wajen yasa hankalin kowa yayi kansu Dan a yanzu duniya ta k'ara sanin Yusuf. da sauri Abdulkarem ya k'araso ya nuna musu wajen zama.
yayinda y'anmtan wajen sai kallon Yusuf d'in suke tamkar su kwace shi ya zamo jisinsu wasu 'yan matane sukayo kansu sunci kwalliya da mamaki suke kallon sa had'e da mik'a masa hannu kallon Zahra yayi datayi kicin-kicin da fuska sallama yayi musu ba tare da sun had'a hannu ba, neman izinin zasu dau salfie tare sukayi kallon Zahara yayi ta wutsiyar ido cikin kauda kai ya basu dama, suka matsowa kusa dashi sukayi tamkar zasu ruggumeshi hakan ya tunzira ran Zahra cikin tarin takaici ta Mik'e da sauri zatabar wajen dan wani irin abu da taji ya ya taso mata a zuciya zuwa mak'oshinta, karaf ya rik'e mata hannu tare da cusa yatsarsa tsakiyar tafin hannunta yana mata wani salon kana kuma bai ko kalli gefen da takeba sai wani tsadedden murmushi da yakeyi hakan yasa ta Janye hannunta tayi k'ofa da sauri. gyara zamannshi yayi. sai ya kuma mik'e da sauri tare da binta da sassarfa yana kiranta dan gani yayi ta.......



*BISA DUBA K'ORAFE-K'ORAFENKU DA YAWA SUN BINI PC DA HAD'ANI DA ALLAH KAR INYI AIKIN GAGGAWA IN BI TYPING DAKI-DAKI KUNCE KU BA GAGGAWA KUKEYIBA KAR INCE ZAN TAKURA KAINA IN GAMASHI RANA D'AYA KUNFI SON IN BISHI A YADDA NA SABA TO ALHAMDULILLAH K'ORAFINKU YA KARB'U ZAMUCI GABA DA POSTING YADDA MUKA SABA HAR K'ARSHE*


page d'inga ba editing zakuyi fama da typing errors sai hak'uri.


*BY*

*GARKUWAN FULANI*
[18/02 5:30 PM] My 2nd Mtn: *HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 29*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

~Page d'in yauma dai ban samu daman yin editing kamar na jiya~


Ta nufi hanyar fita da alamun tafiya zatayi,
murmushi yayi tare da saurin mik'o hannunshi ya kamo nata.
cikin tsananin tsuke fuska da fushi ta fizge hannunta kana taci gaba da tafiya,
ido ya lumshe tare da yin mgnar zuci.
"Hmmmm Ummu Aryan rigima."
sauri ya k'ara ganin tana gab da fita cikin hall d'in,
jawota yayi tare da ruggumota irinyar ruggumar gefe d'ayan,
woyarshi ya d'ago tare da fara yi musu selfie,
ganin tayi kici-kici da fuskantar ne ga alamu kuka zatayi,
sai ya d'an sunkuyo kanta tare da manna mata kiss kana ya rad'a mata.
"Wai me akayi miki ne?."
ido ta tsura mishi kana ta jujjuya kai a fili tace.
"Hmmm wato baka ma san abinda akayi min ba?."
cikin tsare gida ya d'aga mata girarshi. kai ta jinjina kana tace.
"Uhummm."
a ranta kuwa tace OK zaka sani ai.
jan hannunta yayi suka koma mazauninsu,
yayinda tuni yan matannan kuma sunsha jinin jikinsu ganin ya wani sharesu ya mance dasu yabi Zahra,
haka yasa suka bar wurin.

Anyi liyafar Lfy an tashi Lfy. kusan k'arfe sha biyun can suka koma gida,
suna shiga Zahra ta zame ta shiga bathroom wonka tayi kana tayi shirin bacci.
tana fita shima ya shiga,
bai wani dad'eba ya fito tare da kimtsawa bai damuba ganin bata bedroom d'in dan a zatonshi tana parlour,
saida ya gama kimtsawa ya fito parlour nanma shiru babu ita,
zama yayi bisa kujera kana ya k'ira woyarta,
wayar tanata ringing ba'a d'agawa,
mik'ewa yayi ya lek'a wurin dinning area nanma bata nan sai wayarta dake kan dinning table d'in.
kai ya jujjuya gabas da yamma kudu da arewa duk bata nan,
da sauri ya juya ya nufi bedroom d'in dake gefen wanda suke ciki,
inda nan akace su Sultan su zauna su kuwa sukace a a gwara subar Yusuf da Zahra kad'ai a gidan a cewarsu basu shiryawa ganin tab'ara ba,
so shiyasa ya zama su kad'aine a d'an gidan,
yana zuwa ya murd'a marfin k'ofar ya jita gim a rufe,
cikin d'an d'aga murya yace.
"Ummu Aryan! Ummu Aryan!! Ummu Aryan!!!."
tana jinshi tayi shiru kamar bata jishiba,
don har ranta take jin haushin yadda ya wani biye yan matan nan wai zasuyi hoto harda kuma wani cewa wai me akayi mata.
shi kuwa Hamma Yusuf fita yayi ya zagaya ta inda windows din d'akunan suke,
da sauri yasa hannu ya ture glass d'in kana yasa hannunshi tsakankanin k'arafun ya d'an janye labuyen.
konce ya ganta tana fuskantar ta inda yake,
ganin shine yasa ta k'ara tsuke fuska kana ta juya mishi baya ta meda kanta gefe.
Cikin sauk'e numfashi yace.
"Ki tashi ki bud'e k'ofar nan."
shiru bata kulashi ba,
cikin had'e murya yace.
"Ummu Aryan kina jina ki medani bawanki ko,
ina woje sanyi na neman illatani kina sane da bazan iya jurewa ba kam."
still kamar bata jishi ba,
saima gyara konciyarta da tayi tayi balance ta wani mirginawa kamar wahainiya.
ya dad'e a wurin yana mata mgna cikin bada umarni da fad'a-fad'a,
ganin da gskefa takeyi sai ya

Please Login or Register in order to submit comment