Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώ
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡sss




*"Alhamdulillah na godewa Allah daya bani rai da Lafiya da nitsuwa da konciyar hankali da damar fara wannan littafin nawa Lafiya, ya Allah ina tawassali da kyawawan sunayenka Allah ka bani ikon rubuta alkhairi da abinda zai amfanar da al'ummar musulmi Allah ka tsaremin Al'k'alami na da rubuta sherri, Allah ka kawarmin da Yatsuna da tunani na da idona akan rubuta abinda zai zamo guba ga Al'umar Annabi, ya Allah ka tsareni daga sharrin mutun da Aljani Amin Amin Ameeeeeeeeen ya rabbil izzati."*



*K'warai-K'warai na gane duniya mai sonka shikeyi maka hiddima, tabbas wannan haka yake masoya na naga zahiri ashe dai nidin ce kuke so ni Aysha Aliyu Garkuwar kuke so ba novels na ba, domin da novels nane a zaman da nayi ina hutawar nan da kun mance dani sai gashi wallahi abun mamaki kunfi nunamin kulawa a yanzu fiye da in ina typing Ana kyawun tare masoya na dan nida ku ba mugun tare akeba a,a kyawun tare muke shiyasa gani gareku da wani sabon salon tukuicin ku, sai dai fa ga shawara gareku Reeders duk mai son karanta littafin nan to ta/ya Tarawa kanta/kanshi dan in nayi koda 5 page ba wacce zan Turawa ta Prvt chartπŸ˜‰πŸ˜πŸ˜˜πŸ€πŸ»*








*Z*ahra! Zahara!, sauri ya k'arayi ganin duk kiran da yake mata bata jinshi, dan ta daddage sai rawa takeyi d'an guntun siket d'in dake k'ugunta sai bud'uwa yake, wanda yafi dacewa da a kirashi da sunan tayani tsalle sai 'yar rigarta wacce tayi cib da jikinta kanta a kitse an tubke cukun a tsakiyar kanta amman duk kitson ya tuttujare dan tsufa da yayi.

Sai sautin wak'ar nan mai taken,
Zahra-Zahra kece tauraruwa zahra-zahra kekkyawa kina da kyawu,
na sura,
dake tashi da kind'in daya cika illahirin unk'uwar,
Matasan kuma da ke zaune a bakin d'an Shagon charging sai dariya suke ganin yadda Zahra keta rawa sunata mik'a mata sweet tare dayi mata tafi.

Sauri sosai Yusuf ya keyi har kamar zaiyi tuntub'e yana isa wurin,
ita kuwa tana juyowa ganin yadda ya nufota haik'an k'adaran yasa ta faraja da baya-baya tare da rumtse idanun ta tana sauraron ta ina mari zai sauk'a a fuskarta,
shiko yana isa gareta yatsunshi biyu yasa ya kamo kunnenta ya matse da k'arfi sannan ya juya ya nufi bakin get d'in shiga gidan su da ita,
itako tuni ta saki k'ara tare da yarfa hannu tana kiran.
"Aunty na! Aunty na! Hamma Yucuf a cire min kunne na".
shiko janta yakeyi da iya k'arfin shi dan yana jin zafin yadda k'arfi da yaji ake sake Zahra take abunda ranta keso yarin k'arama amman duk wata rawa ta iya ga bibiko ita ko yaushe tana cikin maza sannan in an gayawa Aunty bata daukan abun da mahimmanci.

A haka suka shiga cikin gidan kai tsaye parlour Auntyn ya nufa da ita,
yayinda Mama kuma ke binsu a baya tana.
"Kai Yusuf sake mata kunne zaka jawo mata ciwon kunne fa."
Shiru yayi har suka shiga parlour inda Aunty take zaune tana jinsu,
suna shiga tace kai.
"wallahi kai dai Yusuf ka sawa Zahra ido,
ai yarinta ce kowa da irin tasa,
ka bar 'yarinya ta huta, in ta girma ai zata bari."

Turata yayi kan kujera sannan ya wuce bedroom yana zuwa durowa ya bud'e wurin kayan ta yasa hannu ya jawo d'an hijabinta, sannan ya fito parlour yana zuwa ya zura mata hijabin sannan ya kalleta cikin tsuke fuska da zaro ido yace.
"Maza b'acemin da gani yanzu d'auki Allonki ki tafi bappa jangird'e in kuma na fito na sameki a wurin Idi mai charge kina rawa sai na karya miki k'afa inga dame zakiyi rawan."
Simi-simi ta fice tana ruggume da Allon nata,
tana fita kamar kullum yadda ta saba in zata tsallaka titin k'ofar gidan nasu sai ta jawo rigarta ta rufe fuskarta sannan ta tsalla ka,
ita in ana duba hanya kafin a tsallaka to ita sai ta rufe fuskarta kuma hon d'in mota ko keke napep baya sata ta bud'e ido bare ta kauce musu,
a hakan cikin sa'a ta samu ta tsallaka ta wuce makarantar Allon nasu.

Tana zuwa ta shiga cikin taron yaran ta zauna sannan ta fara juye-juye tana wani kakkane ido alamar neman rigima aiko tayi tozaki da Amira yar malamin allon nasu
ido ta tsura mata tare da yamutsa fuska ta kuma kalli k'afar Amiran dake da gyambo ga k'udaje sun cika kan ciwon,
yawu ta tsirtar cikin harara da tsiwa tace.
"ke Amira ki rufe ciwonki ni bana son gani."
itama Amira a tsiwace tace.
"bazan rufeba ciwonki ko ciwona."
ganin suna surutu ne yasa bappa jangirden yayi musu tsawa tare da cewa.
"NJange-NJange, be! sini! mimarra! alifi! lallamu! hasakeri!".
sannan ya d'ago bulalan hannunshi tare da juyata kan taron d'aliban nashi,
lokaci d'aya wurin rud'e da karatun yara da 'yan mata da 'yan samarin,
rud'eqar wurin yasa Amira ta d'an matso jikin Zahra har ta d'an goga mata gyambon k'afarta a jikin Zahran,
Itako Zahra tana jin ciwon ya gogeta ta kalli Amira cikin tsiwa ta zaro takalmin robar dake k'afarta sannan ta daddage da iya k'arfinta ta zuba mata takalmin a kan gyambon har saida k'udajen dake kan gyambon suka mace tare da narkewa a cikin ciwon,
wani irin sanda rewa Amira tayi tare da mimmik'ewa ta cillara k'ara mai cike da azaba,
cikin tsoro Bappa jangirde yayi kansu dan duba me ya samu d'iyar tasa,
itako Zahra tana ganin yayi kansu ta mik'e tare da cilla allonta gefe ta cire d'aya takalmin dake k'afarta sannan ta arce a saba'in ta nufu gidan su.


A gidan kuwa tana fita Yusuf ya kalli Antyn cikin yin magana Kai tsaye yace.
"Anty sufa yara amanace ga iyayensu kuma abun kiyayewa ne,
fisabilillahi ya za'ayi ace,
komai Zahra tayi ke bata laifi a gareki,
kullum ita tana cikin maza,
sam bakya kula da suwaye take mak'alewa,
in anyi magana sai kice yarinta ce,
to wallahi in bata nitsuba bazan dena sa mata idoba".
yana fad'in haka ya fice ya haura sama inda d'akinsu yake,
sauri-sauri ya cire uniform nashi dan yaji an fara kiran sallan la'asar a masallacin k'ofar gidan nasu,
A parlour Anty kuwa yana fita,
Mama ta kalli Antyn cikin nitsuwa tace.
"Antyn yara ke kinaga zancen Yusuf shirme ne ko?
to wallahi gaskiya yake gaya miki,
domin kuwa Allah ya kawomu wani zamanin da idan kayi sakaci da lura da yaranka to tun suna k'anana wani gardin banza zai lalata miki 'ya sannan ya rabata da budurcin ta da nitsuwarta
tabbas iyaye sai an sanya lura a kan yara dole kisan shige da ficen 'yarki ko d'anki. "
murmushi tayi tare da cewa.
"Kai Mama insha Allahu ba komai Allah zai tsare mana su."
Ficewa Mama tayi ganin bazata fahimci abinda ake guje mataba.

Shiko Yusuf har ya juyo zai fito d'akin nasu ya sauk'o k'asa ya tafi masallaci sai ya hango Zahra da take gudu da iya k'arfinta ta nufo gida,
k'ara matsowa yayi jikin window nasu yana kallonta har ta tsallako koltan sannan tana shigowa cikin gidan,
ta ratsa gefen get d'in inda aka jera kan pompo
inda yaran mak'ota ke jere suna d'iban ruwa,
tana isa wurin ta tsund'uma hannunta cikin bokatin wani yaro ta fara wonke inda Amira ta manna mata gyambon,
yaro yana ganin haka ya janye bokatin yana.
"Kai Zahra wallahi kin raina min wayo."
bata kulashi ba sai kuma tayi kan sauran yaran ta rink'a tsutstsuduma musu hannu da k'afarta a cikin ruwansu,
suko sai binta suke da harara suna zare mata ido dan suna tsoron dukanta tunda a gidansu suke d'iban ruwa kullum,
gaba d'aya ta jik'a jikinta jigib da ruwa sai d'iga take tol-tol,
Kai ya girgiza cikin Al'ajabin hali irin na Zahra sannan ya sauk'o da sauri-sauri gudu-gudu
a k'asan step d'in sauk'a ya tarar da Anty,
wuceta yayi da sauri,
binshi tayi da ido tare da yin murmushi tace.
"ohoho Zahra am kinga ta kanki,
dan na sani sarai,
yanzu haka wannan saurin da yakeyi ke zai jibga."
Mama dake Bak'in k'ofar parlour tane ta tab'e baki gami da cewa.
"In anbi ta taki a kan Zahra haka zata zama saggartaciya."

Hajja Inna ce ta kallesu cikin yanayin fad'an tsofi tace.
"ai Zahra kam an bonu da ita yarinya sam batajin magana."

ita dai Anty sai Murmushi tayi dan bata fushi kan duk abin da ake cewa a halin Zahra.


Shiko Yusuf yana isa inda suke ya karyo bulala a cikin fulawin dake jere a wurin,
sannan ya rink'a caud'a matashi a sharabanta,
ihu tasa tana tsalle siket d'inta tayani tsalle shima yana tsallen a haka ya rekota har cikin gida,
da gudu ta koma bayan Antyn ta nata kuka tana.
"Hamma Yucif a kasheni
Anty a mutu fa."
hannu tasa ta d'agota ta d'aurata kan cinyarta tana dariya tare da cewa.
"Kai amman dai Yusuf baka da ta ido,
ai ko mutuwa tana kunyan idon uwa."
Hajja Inna kuwa dariya tayi cikin jin dad'i tace.
"ai da kin mutu da bakiyi magana ba,
shegen baki kamar window da bak'ar fuskarki kamar mutanen koma."
shiko Yusuf harara ya watsa mata tare da ficewa ya nufu masallacin.



Da dere bayan anyi sallan ishah,
Yusuf da Sulaiman suka shigo cikin gida yayin da Abba da Daddy ke binsu a baya
suna shiga Yusuf ya jawo kujera a tsakiyar gidan ya zauna cikin d'aga murya yace.
"Zahara! Zahra! ."
da gudu ta fito tazo ta tsaya a gaban shi
cikin tsawa yace. "zauna."
ba musu ta zauna
cikin yanayin nasiha yace.
"Zahra! ."

"Na'am."

"kina jina ko?."

"uhmm."

"Yauwa to Zahra ki nitsu ko,
ki saurareni, dan Allah ki dena fita yawo,
kibar bin maza, ki rink'a zuwa makarantar allo,
kuma in kinje ki dena dukan sauran d'alibai, ki dena neman tsokana, kibar cin zali,
kuma kar in sake ganin kinje bakin shagon Idi mai chargi karki yarda kina yin rawa in yasa wak'ok'in shi,
ki rink'a yin karatu kar kina gudowa,
in kinje ki dena dukan Amira,
kinga d'azuma da kika gudo da naje in tabbayi meyasa kika gudo,
Bappa jangirde yace min Amira kika famewa ciwon ta,
ki kiyayeni karki k'ara."
cikin jujjuya kai ta rink'a cewa.
"a k'ara, a k'ara."
ita a nufinta zatace bazan k'araba a gwarancin ta kuma ya fito kamar cewane take zata k'arane,
hakan kuma yasa Yusuf
kamo kunnenta yana matsewa tare da cewa.
"Sai na karya k'afafun kuma in tsinke kunnen."
da sauri Mama tasa hannu ta jawota tare da buge hannun Yusuf cikin fad'a tace.
"Kai Yusuf cewafa tayi bazata k'araba wallahi kana yawan cin zalin Mama nan tawa."
Mik'ewa yayi tare da cewa.
"Gobe a tsefe miki kai, kuma in naji kina kuka nida ke kuma ni da kaina zan kaiki kitson."
ita dai Zahra da haka tayi bacci.


Washe gari ya kama asabar ba makarantar Boko
dan haka ana idar da sallan asuba Yusuf da Sulaiman suka haura sama suka shige d'akinsu suka rufe sannan suka koma baccin dan hutun weekend.

a K'asa kuma Mama ce taketa koran yaran su tafi makaranta karsuyi Letti kasan cewar makarantarsu Arabic da Boko ne su Al'hamis da jumma'a suke hutunsu dan hanka yanzu gaba d'ayan su suka tafi,
ita kuwa Zahra sai tsallenta taketayi bayan Anty ta gama komai tayiwa Zahra wonka ta wonke mata kai sannan ta shirya ta cikin irin 'yan guntayen siket d'inta,
da suke k'ara mata rigima
sannan ta shimfid'a taburma a tsakiyar gidan ta kamo Zahran da nufin fara mata tsifar kan nata
aiko ta fara tirje-tirje da koke-koke tana jada baya,
sanin halinta sarai ba yarda zatayi ayi tsifan da sauk'iba,
yasa ta fizgota ta fara mata tsifan,
aiko ta daddage ta b'are baki sai kuka da ihu take,
duk ta damula fuskarta da hawaye da majina,
ganin Antyn nata bata da niyar saketa yasa ta daddage ta takafa hak'oranta a cinyar Antyn ta kafa mata cizo,
da sauri ta saketa tana shafa inda ta cijetan,
ita kuwa ana saketa tayi bakin gate a guje ta bar gidan ,
tana fita da kai rabi a tsefe rabi a kitse tayi bakin titin inda taron matasan unguwar dama na wasu unguwannin suke taruwa.


ita kuwa Anty cikin ko in kula taci gaba da harkokinta,
har zuwa k'arfe goma na safen Amman ko a jikinta batama yi cekiyar ina d'iyarta mace ta shigaba bare tasan da su waye take tare ba,
Ammi ce ta d'an lura da dad'ewar da Zahra tayi bata shigo gidan ba sannan ta kalli amaryar tata cikin ganin sakacinta tace.
"Wai yanzu bazaki binciki inda Zahra ta shigaba ba ko."

cikin ko gezau tace.
"Ya wuce tana shagon Idi ne,
ko tayi bacci a can."

"kin tabbatar tana can d'in kenan? sannan inma kin tabbatar d'in,
shi Idi kina da tabbacin halinshi ne da d'abi unshi ne? ke yanzu ranki ya gamsu da kibar 'yarki mace a tsakiyar Maza?."

ta bud'e baki da niyar zatayi magana kenan suka jiyo kukan da Zahra takeyi tare da ihu,
da sauri suka juyo gareta
Cikin tsoro Ammi ta nufi inda take ganin yadda take tafiya tana tangad'i da layi,
sannan ga pant da siket d'inta a hannu duk an tub'e matasu,
cikin zaro ido Ammi tace.
"Ke Zahra waya tub'e miki kayanki harda pant d'inki?. "
cikin wani irin sautin kuka tare da yarfa hannu tana shafa k'ugunta tace.
"Id........!!!



πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 2⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡




*DEDICATED to Aisha Aliyu Tsamiya*






*"I*di ne a ciremin." ido Ummi ta kuma zarowa cikin wani irin yanayi ta kalli Antyn dake zaune a gefensu ta tsura musu ido da yanayin rashin karaya a tattare da ita,
tsaki ta d'an ja sannan tace.
"Zahra am komai ya faru dake da sakacin mahaifiyarki domin ita sam bata d'auki kula da tarbiyar yara da wani matsayi mai girma ba sam bata lura da zamanin da muke ciki na yawaitar *Fyad'e* akan yara k'anana ba."
sai kuma ta jawo Zahran wacce take ta layi da lumshe ido,
K'ugunta ta tsurawa ido ganin yadda take ta sosa wurin,
ganin duk ta birkice da kuka yasa Ummin ta fara haurawa saman step d'in da da zai kaita sama inda Daddy dasu Yusuf suke,
haurawa take tana kiran.
"Yusuf! Yusuf! ina kake ? maza fito kazo kaje gun Idi mai shago, ka tabbayeshi dalilin me zai cirewa yarinya suturarta?
kuma ya shirya abin da zai cewa Daddyn ku."
Shiru tayi ganin Yusuf daya fito daga part nasu ya nufo gunta,
cikin muryar bacci yake magana tare da tsuke fuska ya kalli Zahra dake ta kuka,
mik'a ya d'anyi sannan ya kalli Ummin tare da cewa.
"Ina ganinta ta window tun d'azu,
ina kallonta taje shagon Idi tayi tayin rawa,
suna bata sweet, ta zauna shan sweet d'inne tayi bacci a wurin,
so bata jima da yin baccin ba, naji tana kuka,
so nadai ji Idin yana cewa mai gadi wai cinnaka ne ya cijeta."
tsaki ta kuma ja cikin jin haushin sakacin da Anty keyi da d'iyarta sannan ta tura Zahra tare da cewa.
"Kuma dan cinnaka ya cijeta sai ya cire mata kayanta."
ratsawa gefen Ummin yayi yana sauk'owa k'asa tare dabin Zahran a baya yana mai cewa.
"Ato ya muka iya, tunda ita Zahra mazane abokan zamanta sannan an sata a makaranta Anty ta dage ta hana wai tayi yarinya,
ai tana wahala sai randa sukaga dama take zuwa, toh gashi a gidan bata da aikin yi sai rashin kunya da yawo rawa kamar mazari,
sannan a madadin a rink'a korata makarantar allo hakan ya gagara,
sai in an tab'ata,
ace an samata ido."
hannunta ya fizo dai-dai lokacin daya isa inda take,
gaban Antyn ya ajiye ta tare da kamo kunnenta ya murd'a cikin fad'a yace.
"Wallahi in naga kin kuma shiga shagon Idi sai na miki shegen duka,
kuma yanzu za'a tsefe miki wannan buyagin kitson naki,
in kika kuskura kikayi mana kuka sai na yage bakin naki."
hannu tasa ta rufe bakin nata dan danne kukan da take yin,
shiko juyawa yayi ya shiga parlour kakarsu Hajja Inna
kan kujera ya konta tare da lumshe ido alamar zai kuma yin baccin,
Hajja Inna namai magana amman yayi shiru kamar bai jita ba
dan bai samu yayi baccin ba tun kukan tsifan da Zahra tayi ya tashi daga baccin da yake.

itako Zahra ganin inda ya shiga ba nisa yasa tayi tsilli-tsilli da ido har aka gama tsifar,
sannan aka tubke kayin tare da goge mata fuskarta data cab'ule,
kallon ta Anty tayi tare da mik'a mata dari 200 tace.
"Hin karb'i kud'in kitson naki,
kije Hamman ku zai kaiki gidan kitson."
kai ta karya tare da tura bakinta tace.
"Hamma ayi bacci fa,
Anty aje ni da aina."
Murmushi tayi tare da cewa.
"Yoh ai dolenki kije dashi tunda duk wanda ya kaiki sai kinyi ta ihu sai in shine ya kaiki kike tsayuwa ayi mai kyau."
wurgar da kud'in tayi tare da cire hijabin da aka samata sannan ta nufi part d'in Antyn nata,
tana cewa.
"Anty na ni ayi bacci."
Mama dake bayan tane ta rik'o hannunta tare da cewa.
"Yusuf fito ka kaita gidan kitson an gama mata tsefe kan."

Fitowa yayi tare da kallon inda take ba magana,
ganin kallon da ya mata kawai yasa tasa hannun ta d'auki hijabin tasa sannan tayi gaba,
binta yayi a baya suka fice,
Dariya sosai Hajja Inna tayi tare da cewa,
"Kurama tasan gidan mai babban sanda."
dariya sukayi,
itako Anty sai cewa tayi.
"Ba dolenta ba yadda yake cin zalintan nan. ga fuska kamar ta tsohon soja,
ai koni uwarta in Yusuf ya tsuke fuska sai yabani tsoro."

"ai shine maganin ta." cewar Ummi.




Suko suna fita tana gaba yana binta a baya har k'ofar gidan masu kitson
sannan ya tsaya tare da yin sallama,
mai gidan da kanshi ya lek'o sannan suka gaisa.

"Baba dama Zahra ce na kawo ayi mata kitso."

"Toh Yusufa yau kuma an kawo Zahra'u ne, ba matsala. "

Kallon ta yayi tare da cewa.
"Shiga ayi miki kitson, ina jiranki a nan."
ya k'arishe maganar tare da nuna d'an dakalin dake k'ofar gidan."
shiko Baba hannu ya mik'a mata yana.
"taho mu tafi ko Zahra'u."
binshi tayi tana kele baki alamar zata fara kuka,
ganin haka yasa Yusuf cewa.
"Baba in tayi kuka a turata d'akin *Biri* ya mata kitso."
tana jin haka tayi sit da bakin ta,
suna shiga Goggon Biri matar dake mata kitson ta fara mata kitson,
da tayi motsi alamun kuka sai matar tacewa 'yarta Ladiyo.
"Ladiyo bud'e birin yazo ya d'auketa."
a haka suka samu sukayi kitson tanata cure-cure har tayi bacci kafin a gama,
koda suka gama Baba da kanshi ya ciccibota ya fito k'ofar gida inda Yusuf ke zaman jiranta,
hannu yasa ya karb'eta tare da sab'ata a kafad'ar shi,
sannan yayiwa Baban Ladiyo godiya da sallama ya nufi gida.

Suna isa cikin gidan nasu Yusuf ya tsaya cak a tsakiyar gidan tare da zubawa part d'in Mama ido dan jiyo sautin sheshshek'ar kukan da takeyi k'asa-k'asa sannan yana jin sautin marin da ya tabbatar mishi Abba ne keyi mata shi.

Shiru ya tsaya a wurin sai jikin shi dake rawa lips inshi ya kamo ya cija ta ciki lokaci d'aya
ida nunshi sukayi jazir gaba d'aya jijiyan dake goshinsa ya taso sama,
ya kasa yin gaba ya kasa yin baya
sai Zahra dake kan kafad'arsa ya k'ara tallab'e kanta,
yana tsaye a wurin har Abban ya fito yana tafe kamar zai bugi babu fuskarnan a murtuk'e, yana ficewa shiko ya nufi part din Maman.

A parlour ya sameta zaune bisa kujera ta kife kanta kan cinyoyinta tana kuka mai cike da cin rai,
da sauri ya kontar da Zahra kan 2 str,
idon shi cike da k'ollah ya durk'usa gabanta sannan yasa hannun shi kan guiwowinta cikin cushewar murya yace.
"Mama yauma dukanki Abba yayi ko?
Mama me kikayi mishi? ."
Da sauri ta d'ago kanta dan bata san da shigowarshi ba hannu tasa ta share hawayen ta ajiyan zuciya tayi tare da cewa.
"Kai Yusuf duka kuma?."

"Eh mana Mama inba haka ba meya saki kuka?".

kauda fuska tayi cikin son b'oye abinda yaron nasu ke son ganowa tace.
"Har yaushe zanci gaba da cema Miji baya dukan matarsa, domin hakan ba halin mutanen k'warai dana kirki bane,
Abban ka kuma kai shaidane mutun ne managarci mai daraja da mutunci ko mak'otanshi da mutanen gari zasuyi shaidar dottakun sa da mutuncinsa,
a kullum ina shaida ma ni Abban ka bai tab'a koda muntsili na ba,
Kukan da kaga inayi,
rasuwa akayi mana, shine daya gaya min na kasa tsaida hawaye na."
girgiza kai yayi cikin rashin gamsuwa da zancen mahaifiyar tashi
ya dad'e da sanin boyemai laifin mahaifinshi takeyi,
a fili kuma sai tsura mata ido yayi yana kallon fuskarta da tayi jazir alamun marukan da aka yayyarfa mata,
idon shi ya rumtse da k'arfi cikin rawan murya yace.
"Kiyi hak'uri Mama komai yayi tsanani zaiyi sauk'i komai yanada iyaka watarana sai labari,
insha Allah Mama zakibar kukan wannan rasuwan da akeyi miki lokuta da dama duk da bansan wad'anda suke rasuwan ba,
amman kiyi hak'uri domin Mahak'urci mawadaci."
hannu yasa ya share mata hawayen nata cikin sauk'e numfashi mai nauyi yace.
"Mama insha Allah hawayenki zasubar zuba zan saki dariya a madadin wannan kukan, zan cire k'unci a ranki zan samar miki farin ciki."
Murmushi tayi cikin jin sanyi a ranta kanshi ta dafa tare da cewa.
"Allah

Please Login or Register in order to submit comment