Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sauka dukkansu basuji dadin abinba musamman Sulaiman daya tambayi Ummi take fada mishi yadda abin ya faru da korar da Abba yayiwaYusuf ranar sukuku aka wuni a gidan saboda babu walwala a fuskar kowa.



A asibiti kuwa cikin tausayawa Aryan ya taimakawa Yusuf ya wanke bakin shi.
tea ya hada mishi ya zuba mishi pepper soup din kayan ciki daya koma gida ya karbo a hankali Yusuf yake cin pepper soup din sam bayajin dandanon komai a bakin shi salam haka dai ya tuttura dan matsamishi da Aryan yayi da k'er yasha tea din, mikewa yayi yaji kamar iska zata kadashi Aryan ne ya taimaka mishi ya kaishi har bakin bandaki sannan ya juyo,
saida Yusuf ya watsa ruwa jallabiyar da Aryan ya dauko mishi ya mika masa da gajeren wando ya sako ya fito, lokacin Aryan ya shimfida mishi sallaya tambayar Aryan yayi wacce sallah zaiyi dan baisan tsawon lokacin dayayi a sume ba ,
cikin kula Aryan yace.
"In bakayi magriba ba tom magriba da isha'i zakayi". "ok". a zaune Yusuf yayi duka sallolin harda shafa'i da wutiri sannan ya koma gadon shi ya kwanta ya jingina da pillow lumshe idanuwan sa yayi a sannu ya fara tariyo abubuwan da suka faru acikin rayuwar shi a yau wanda ya jingina hakan a matsayin tashi kalar kaddarar.



Baiyi kokarin hana hawayen zuba ba,
shiko Aryan ganin yana hawaye sai ya matso gareshi tare da fuskantarshi cikin amincin aminai yace.
"Yusuf!!! me yake faruwa ne? hankalina ya tashi dan dazu bayan Daddy ya saka an baka gado na samu Abba na kirashi da wayarka yafi sau 23 bai d'aga ba,
na kirashi da wayata ma bai d'agaba,
saida na kirashi da sabon layina sannan ya d'aga yace
waye ina cewa Aryan ne abokin Yusuf yayi tsaki ya kashe wayar ni abin ya bani mamaki".
Shiru Yusuf yayi tare da rumtse ido lips d'inshi na matse cikin k'unan raining hawaye na bin fuskarsa yace.
"Hmmmm Aryan ai Abba bazai d'auka ba, aida ka san abinda ya faru da bazaka kirashi ba".
cikin rud'u Aryan yace.
"Ban gane ba? Koka mishi laifi ne".
kai Yusuf ya gyad'a a sannu ya fara bawa Aryan labarin abinda ya yake faruwa tiryan-tiryan har zuwa yau, Aryan kam ya girgiza matuk'a amma sai yace.
"Abba yayi laifi amma Yusuf kafi kowa lefi duka fa kuma Hajiya Inna aiko daraja da yawan shekarunta ya sakaka kaji tausayin ta kaki dukan ta".
cikin cije lebe Yusuf ya hadiye wani yawu mai d'aci yace.
"Ni d'anta yake dukarmin tawa mahaifiyar kullum ya medata kamar gangarsa, ko uwa tafi uwa ne?".
cikin fad'a-fad'a Aryan yace. "Haba-haba dai Yusuf tunda kake ka taba tuntub'ar Abba akan dalilin dukan Mama da yakeyi ne?".
kai Yusuf ya girgiza Alamar a a,
cikin yin nasiha Aryan d'in yace.
"Tom ka gani baka da hujja nasan duk taurin zuciya da kafiya irinta Abba daka tareshi kunyi magana ka nuna mishi abinda yakeyi bakajin dadi zai daina saboda yasan kaima ka girma kasan dad'i da daraja da girman mahaifiya kuma zaiji kunyarka, ai abinda harshe bai warwareba to wallahi tokobi bazai warwareshiba Yusuf ka rege zafin zuciya nan taka fa".
a take wani danasani da nadama ya lullube Yusuf, kowa shiru yayi yana saka da warwara a zuciyar shi.



Koda Daddy ya koma gida saida ya kara zuwa ya duba jikin Hajja Inna Abba ya tarar zaune a gabanta ya rafka tagumi ya zuba mata ido shi kad'ai yasan zafin da tukukin da yakeji a ranshi wai har ya haifi d'an da zai iya illata mishi mahaifiya kamar haka, sama-sama ya amsa gaisuwar Daddy dan Daddy dinma haushin sa yakeji yana ganin kamar baiji ciwon abinda Yusuf yayiwa mahaifiyar tasu ba, shiko Daddy yaji zafin abin amman rakin Hajja Inna dariya ke bashi sai nishi take tana zare ido, kuma ya sani sarai da gayya takeyi dan ta dad'a ingiza Abba ne a kan Yusuf shiyasa bai wani damu ba.




Washe gari Daddy ne ya turo kofar d'akin da Yusuf suke, saida kirjin Yusuf ya buga dan tsabar tsoro da firgici wani irin kallo Daddy ke binshi dashi da sauri yayi kasa da kanshi kujera Daddy ya janyo ya zauna a gabanshi hadi da gyaran murya,

cikin sanyi tare da sunkuyar da kai Yusuf yace.
"Ina kwana Daddy".
bai amsa ba illah cigaba da kallon shi da yake,
jikin Yusuf ne yayi sanyi tuni hawaye ya fara zuba a idon shi,
Cikin tsareshi da ido Daddy yace.
"Hmmmm a'ah -a'ah ni bance kayimin kuka ba". Aryan ne ya turo kofa hannun shi rike da basket na break fast d'insu gaida Daddy yayi ya amsa hadi da tambayar shi yamai jiki.
"Alhamdulillah da sauki". Daddy yace.
"Allah ya kara sauki".
Aryan yace "Ameen".
a sannu Daddy ya fara yiwa Yusuf nasiha sannan ya nuna masa irin yadda ranshi ya baci akan abinda ya aikata ashe bai dauke shi uba ba da duk tsahon lokacin nan bai taba fad'a mishi ba Yusuf da Aryanne suka hadu sunata bawa Daddy hakuri daga haka kuma ya sauko, ya huce.



Mama kuwa rayuwa ta cushe mata bata da aiki sai kuka safe rana dare Abba in zai mata maganar duniya ba zata tanka shiba sai kuka hatta da abinci ta daina ci lokaci d'aya tayi wani irin rama inda ka ganta saika zata tayi shekara tana jinya. Abba kuwa duk ya shiga damuwa dan yanason Mama sosai sai dai bayajin akwai wanda ya isa ya tankwara shi ya yarda Yusuf ya dawo gidanshi da zama dama su biyu Allah ya bashi tom ya sallama Yusuf ya cireshi cikin jerin yayansa Zulaihat ta isheshi tunda ita din tanajin maganar shi.



Alhmdllh yau kwanan Yusuf uku jikin shi yayi sauki sosai inda aka sallame shi Daddy da kanshi ya dauke su ya kaisu gidan su Aryan izinin ganawa da Hajiya kakar su Aryan ya nema bayan ya shiga sun gaisa anan ya nemi alfarmar yanaso Yusuf ya zauna a wajensu sabani suka samu da maihaifin sa ya koreshi daga gida kuma zafin rai gareshi kafin a tankwara shi da wuya,
cikin jimami Hajiya kaka tace.
"Ashsha su yara ai ba'a musu haka da lallami da nasiha ake binsu in akace za'a musu dole ba zasuji ba, ai babu komai d'a na kowa ne kuma Yusuf da Aryan
duk d'aya suke a gunmu, ".

Godiya Daddy yayi mata sannan yace.
"Inhar mun samu mun shawo kan mahaifin Yusuf din zai koma gida kwanannan insha Allah".
Hajiya tace.
"ai babu komai Allah ya sassauta zuciyar shi ya dai-daita su".
daga haka yayiwa Hajiya sallama su Yusuf ne suka rakoshi cikin sanyin murya Yusuf yace.
"Daddy dan Allah ka fad'awa Mamana inda nake nasan hankalinta bazai taba kwanciya ba har sai taji inda nake".
murmushi Daddy yayi hadi da shafa mishi kanshi yace "In sha Allah, Allah yayi maka albarka".
"Ameen". Yusuf ya amsa.




Koda Daddy ya fad'awa Mama inda Yusuf yake hankalinta ya kwanta kuma nutsuwarta ta dawo jikinta sai dai har zuwa lokacin bata wani sakarwa Abba jikinta ba haka suke zaman kurame in suna zaune a d'aki.



Zarah kuwa tambayar Hamma Yucuf harta gaji dan wataran in Sulaiman zai kaita makaranta saita tubure tace ita Hamma Yucuf ne zai kaita dakyar ake samu ta tafi dan yanzu Aunty Amarya ta dage akan karatun ta, ita kuwa Zahra yanzu fesawa Hajja Inna rashin mutunci takeyi son ranta.


Yauma kamar kullum duk suna tsakiyar gida kowa na hidiman gabansa, Hajja Inna dake gefe a zaune kan carpet da ake fidda mata in yamma tayi ta zauna tasha iska tsaki taja ganin yadda Zahra keta wasa da ruwa duk ta jik'a wurin, cikin fad'a da raki irin na tsofaffi da son a doki Zahra ta tashi tare da zuwa kanta carbin hannunta ta zuga mata tare da cewa.
"Shegiyar yarinya mai kama da ifiritu wato zaki jik'a wurin kalen in sule in karye ko?. "
cikin tsiwa da muryar kuka-kuka tace.
"Ni dai ba shegiya bace ehe, kuma Allah ya isana ,kuma in Hamma Yusuf na ya dawo sai na gaya mishi ya miki duka sai kinyi fitsari a wondonki irin na rannan, ai kin sani sarai."
sai ta kuma fashewa da dariya gami da zuwa gaban Babar yayarsu yar farin Daddy kenan, wacce itace babba akan Yusuf da Sulaiman kuma itama bata shiri da Hajja Inna dan gulma take had'a mata,
dariya takeyi harda rik'e cikinta tace.
"Yauwa Zahra zo ki nuna min yadda tayi da Yusuf na dukanta zan baki wayata kiyi rawanki."
aiko Zahra najin haka tayi fad'uwar yan bori tana
burburwa da gantsarewa tana koikoyar muryar Hajja inna dayin yadda tayi tayi da Yusuf na zaneta, tana.
"Waiyihuhuhuhu..! Yusuf ya kasheni ihuhuhuhu jama'a ku kayo taimako."
aiko Amira, Sulaman ,Ja'afar, Nana, Ibrahim, harda Zeenat auta dariya sukeyi harda tsalensu,
Mama kam dake gefe sai tayi sauri ta koma part d'inta dan gudun kar dariyar ta kubce mata,
Anty Amarya kuwa da Ummee sai suka hau yiwa yaran fad'a suna danne dariyar dake son kubce musu,
ita kuwa sai bambami takeyi tana.
"Wallahi yau sai na had'aku da Abbanku ya tattakaku ya koraku."
Suleiman ne ya samu ya tsaida dariyarsa tare da cewa.

"Wallahi Allah kenan wanda kikasa aka koranma zai dawo bare mu zama daram sai dai ke ki tafi gidan naki uban."
ihu tasa tace ai Sulaiman ya zageta Daddy kam dake sama sai murmushi yakeyi yana mamakin halin tsufa,
su kuwa yara sai dariya sukeyi saida Ummee ta dage ta korasu kowa yaje yayi alwala dan yin sallan maqrib.

Meeting Daddy ya hada na dukansu cikin mahaifiyarsu.
Abba, Aisha, Fatima, Maimuna, Daddy d'in sai autarsu Madina kokarin ganin sun shawo kan Abba ya yarda ya amince Yusuf ya dawo gida dan hannunka baya taba rubewa ka yanke kayar,
to Hajja Inna kuwa sunyi-sunyi su shawo kanta amma ina magana d'aya ce a bakinta in Yusufa ya dawo zai iya kasheta dan yanzu tana matuk'at tsoronshi ko sunashi in an kira sai zuciyarta ta tsinke gashi kuma ita kadai ce zata iya tilasta Abba ya yafewa Yusuf.

Duk zaune suke a parlourn Hajja inna Abba ya shigo bayan an bud'e taro da addu'a, sannan sun gaggaisa gwaggo Fatima ce tace.
"Ammm yaya dama maganar Yus..!".
shiru tayi ta kasa k'arisa maganarta ganin wani irin mugun kallo da ya mata , cikin tsananin kausasa murya da zafi yace.
"Dama yaya me?".
baya tad'an ja murya na rawa tace.
"akan maganar Yusuf ne" mikewa yayi hadi da buga.....................!



*By*
*GARKUWAR FULANI*
[02/01 1:06 PM] My 2nd Mtn: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣3⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Domin samun damar shiga group d'ina na HUKUNCIN ALLAH don karanta littafin zaka/ki turo katin MTN na 200 kacal ta wannan layin 09097853276 ko kuma turo d'ari biyu ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, tabbatar kin turo min screenshot shaidar kin biya kud'in shiga. Dan Allah masu kira kuyi hak'uri da rashin amsawata*




Kada fa ku manta Free page dai sun kusa k'arewa....!


K'arasowa Abba yayi had'i da yin parking d'in motar shin, fitowa yayi da d'an sauri cikin mamaki yake kallon Mama ganin kamar akwai abin daya firgitata, ido ya zuba mata tare da cewa. "Yadai...! me kikeyi a waje?". d'an diriricewa tayi cikin inda-inda da fargaba tace.
"Amm uhmm dama dirin abin hawa naji tom nayi zata kaine , shiyasa na lek'o na gani, sabida nasan ba waya a hannuna to na Zulahat d'inma ba change shiyasa nai tunanin karkazo kaita zaman jirana, to dana lek'on sai kuma naga ashe mai machine ne ya wuce".
ido ya zuba mata tare da matse lip inshi na k'asa alamar yana nazartan Kalamanta
kamar dai yana son gano wani abu da take b'oye mishi, ganin haka yasa ta k'ak'alo murmushin tace.
"Yadai, lafiya kuwa?".
kai ya juya tare da meda dubanshi ga bayansu Yusuf da suka kusa bacewa ganinshi tare da cewa.
"Tohh! su wad'ancan nakan machine d'in su waye ne...!?" dariyar yak'e ta d'anyi tace. "Ikon Allah sai kallo toh ni ta yaya zansan su waye samari nefa suka wuce kila ma ba 'yan unguwar nan bane, nida ko fuskarsu ban ganiba, yadda kaga bayansu nima d'in bayansu kawai na gani". jinta kawai yayi bawai danya yarda da ita bane bayaso ya zurfafa bincike kawai shiyasa yace.
"Okay, toh ya jikin Zulaihat d'in?".
"Da sauki sosai, amma ya akayi ka dawo da wuri kai da kace zaka iyayin awa biyu zuwa uku?".
fuska ya d'an tsuke tare da cewa.
"Shari'ar na d'aga".
cikin mamaki tace.
"Sabida me?.".
fuska ya kuma tsukewa kamar itace mai laifin, a fusace yace.
"Naga alamar k'ulle-k'ulle akeyi anaso a dannewa mai gaskiya hak'k'insa ne, wanda niko bazan lamunci hakanba dan zalumci, da rashin bin HUKUNCIN ALLAH da shariya ta k'indaya mana".
juyawa tayi tare da cewa.
"Allah ya baka nasara ya toni asirin mara gaskiya".
sai taja bakinta tayi shiru dan ta lura a saba'in yake,
tana gaba yana binta a baya suka k'arasa shiga cikin gidan.



Ita kuwa Zulaihat jin Abba ya sata had'iye kukan nata dan dole, sai jan da idanuwan ta sukayi, bayan sun gaisa Abba yayi mata ya jiki, 20k ya bata sannan sukayi mata sallama, har k'ofar gida ta k'ara rakasu tana dad'a yiwa Abba godiya.



A hanya kuwa Yusuf dake tuk'asu, dan yanzu an samu canjin mai tuk'in shine yaja wata doguwar ajiyar zuciya saboda suna cikin layin su Zulaihat ya hango motar Abba ta shigo layin ta mirrow din machine d'in Aryan kuwa da baisan dalilin daya saka Yusuf din k'ara gudun machine d'inba shine cikin fad'a yace.
"Kai Yusuf kana da hankali kuwa? ko zubar damu kakeso kayi ne a titin ? koka manta wannan ba badsha d'inka bane kake gudun ganganci damu?".
(badsha sunan dokin Yusuf ne) tsaki Yusuf yayi cikin fushi shima yace.
"Ni dad'ina dakai wutar ciki wallahi a maimakon ka tambaye ni dalilin gudun amma sai mita, da raki ga d'an banzan tsoro kamar mace".
Allah sarki Aryan saukin kai gareshi da hak'uri kamar me shiyasa abotar su da Yusuf tayi k'arko har yanzu,
murmushi yayi tare da cewa. "Toh naji bar min sababi meya sakaka yin gudun?". saida Yusuf ya taune leb'en shi na k'asa danya zame masa al'ada da kuma gado cikin kunar zuci yace.
"Hmmm uhummm Aryan motar Abba na gano ta shigo layin dabadan nayi hanzari mun fita a layin ba babu abinda zai hana ya gammu kuma bawai ina tsoron ya ganmu bane a'ah matsalar da zasu samu da Mama sannan zai iya shafar har Adda Zulaihat d'inma shiyasa nayi hakan".
cikin tausayawa Aryan ya gyad'a kansa alamar gamsuwa, da tausayawa aminin nashi har sukaje gida suna tattauna matsalar da tunanin yadda insun dawo zasu tunkari Abba ko zai hakura ya yafewa Yusuf d'in har suka isa gida,
horn Yusuf yayi mai gadi ya bud'e musu suka shiga parking Yusuf yayi suka sauka sunkuyawa yayi had'i da rik'e gwiwowin sa duka biyu, tare da rumtse ido had'ida fesar da numfashi da kuma cije lips nashi duka biyu,
cikin wasa irin ta abokai kuma aminai Aryan yace. "Yadai ko jarabar ta motsa ne Barade".
naushi Yusuf ya kaiwa Aryan ya goce yana dariya shakiyan ci yace.
"Kasan Allah wannan halin Abba ka d'auko gaba dayan ka, zafin rai ba sassauci kuma wai kake cewa Abba nada zafi, kuma kai kama fishi zafi dan kai bala'ine ma da kai, banza *Ayu* kawai". yana kaiwa nan ya juya ya kwasa a guje zuwa gida,
ai a zabure Yusuf ya mara masa baya har parlour suka shiga a guje,
Hajiya Kaka da take zaune tana dama fura tare da zuma a madadin sugar cikin farin ciki da son jikokin nata tace. "Uhmm hmm kun fara ko waiku sai yaushe zaku girma ne bakwa rabuwa da rigima inaga inkun tafi gurin gasar ma hakan zakuyi tayi ko?". kwafa Yusuf yayi tare da motsota yasa hannun ya jawo d'an k'aramin k'warya mai cike da zumar ya fara lasa tare da cewa.
"Allah Hajiya Kaka Aryan ne dan rainin wayo ya fiya tsokana".
dariya Aryan yayi yace. "Allah Hajiya Kaka ba haka bane waifa dagayin magana shine ya zuciya ya biyoni a guje".
dariya tayi tace.
"Allah ya shiryaku ni babu ruwana ba'a shiga fad'anku saiku shirya kubar mutum dajin kunya".
dariya sukayi tare tafawa,
Raihana da shigowarta kenan jakarta islamiyarta ta ajiye gaban Yusuf cikin nitsuwa tace.
" Hamma Yusuf bari in biya haddana kaji in yayi dai-dai in baiyiba ka gyaramin kar inje a zaneni".
cikin kula ya juyo gareta yana lasar zumar tare da lumshe ido yace.
"Hmmmhm bisimilla".
zama ta gyarra tare da fara rera karatu cikin sauti mai dad'i take karanto suratul yaseen daga forkonta har zuwa tsakiyarta, inda nan aka tsaidasu sai yau in sun bada wannan za'a k'ara musu,
murmushi yayi tare da yin kabbara yana jinjina mata sannan ya k'ara mata, tayi ta biyawa har lokacin tafiyarta tayi ta fita ta tafi,
suko nan suka zauna kuma suka daura hira daga haka suka shirya suka manta abin daya korosu.


Tafiyarsu tanata karatowa yauma kamar yadda suka saba Yusuf da Aryan suka fito zasu tafi training kai tsaye d'akin da dawakan su suke ciki suka nufa, suna k'arasa shiga kamar yadda suka saba dawakan suka fara haniniya alamar sun ganesu murmushi Yusuf yayi tare da kallon Aryan yace.
"Aryan yau muyi canjin doki mana nahau naka kai kuma kahau nawa".
Aryan kuwa zaro ido yayi had'i da kad'a kanshi yace.
"Wa d'in! tab a'ah kam Yusuf ina tsoron dokin ka bazan iya controlling d'in Badsha d'inka ba kayi masa horon dakai kad'ai zaka iya amfani dashi, abu in yana gudu kamar zai tashi sama".
dariya Yusuf yayi yace.
"Toh ai inaso kaima ka iya gudu da doki ne kamar yadda nake yiwa nawa ya zamana inba daya daga cikin muba babu wanda zai iya amfani da dawakan mu, kuma wata ran in bana nan wa zai kula da Badsha d'ina?".
kai Aryan ya juya yace.
"Toh naji amma ban yarda ba kai dai kahau naka, ni nahau nawa, babu inda zakaje ko yaushe kana tare da Badsha d'inka".
Cikin son juna Yusuf yace. "Haba dai brox try mana ai sai an gwada akan san na k'warai, matsoracifa bayi zama gwani".
shi kam Aryan kai ya kad'a had'i da kallon Badsha ido cikin ido da nufar shi da niyyar kama linzamin sa dan yahau,
wani irin haniniya Badsha yayi had'i da harbin iska da kad'a jelarshi,
dariya Aryan yayi tare da komawa baya yace.
"Ka gani ko shima yafiso uban gidanshi yahau kanshi ya horu da sukuwar wahala". Dariya sosai Yusuf ma yayi had'i da tahowa yana shafa gashin dake goshin dokin cikin kirarin daya saba yiwa Badsha yace.
"Badsha dokin Yusuf bani sai dakai bana bada aronka ni dakai mutu ka raba".
had'i da sumbatar goshin Badsha haniniya Badsha ya k'arayi had'i da d'aga k'afafuwan shi na gaba duka biyun alamar sarawa Yusuf d'in da jin dad'in kirarin, zagayawa Yusuf yayi yahau kan dokin shi,
cikin sha'awa da burgewar sabon dake tsakanin Yusuf da Badsha Aryan yayi murmushi had'i da zagayawa shima yahau kan nashi dokin yana.
"Nima Allah ya nunamin randa zanyi sabo da nawa dokin kamar haka".
dariya Yusuf had'i da cewa.
"Sai ka rege tsoronshi."
murumushi Aryan yayi sanan suka fita daga d'akin dawakan,
mai gadi ya bud'e musu gate suka fita, yana musu addu'ar dawowa lafiya da mamakin yadda kan yaran yake a hade komai zasuyi tare sukeyi.

Jerawa sukayi suna tafiya suna hira,
yayinda duk majalisar samarin dasu Yusuf zasu wuce saisun musu kirari saboda sunsan sune zasu wakilcesu Jahan team a kasar da za'ayi ta kasa.



Dai-dai zasu shiga airport d'in kenan safwan ma ya k'araso daga kan dokin sukayi musabaha suka karasa shiga,
olready Affan da cotch d'insu Malam Jabeer suna cikin airport d'in,
suna isa inda suke suka diro daga kan dokin suka kai gaisuwa ga cotch,
babu wata-wata cotch jabeer ya fara nuna musu wasu sabbin hanyoyin cin tseren doki sannan ya basu umarni suka hau dawakan had'i da busa k'usur suka kwasa a kuje, gudu sukayi sosai kamar yadda suka saba tamkar zasu tashi sama,
Yauma Yusuf ne yazo na d'aya,
toh daga nanfa Safwan ya fara jin haushin Yusuf dan a kwanakin nan indai anyi shikeyin na daya bayan kuma shiya kamata yana zuwa ana d'aya tunda shine dan gado ba taka haye ba amma dai bai nunawa Yusuf d'inba tunda daga yau sun gama zuwa training d'in sai ranar tafiya kuma tunda saura kwana 3 tafiyar tasu.



A gajiye suka k'arasa gida kamar yadda suka saba maida dawakan nasu sukayi d'aki suka fito alwala sukayi a fanfon waje saboda kiran sallar magriba da ake tayi nan suka isa masallaci.



Bayan an idar da sallah zama sukayi suna sauraron wa'azin limamin masallacin kamar yadda ya saba duk ranar juma'a yanayin wa'azi daga sallar magriba zuwa isha'i in anyi sallar isha'i kuma sai su tafi gida dan basa yawon dare.



Yau liman wa'azi yayi mai duka da ratsa zuciya akan illar zina sosai ya tsoratar da kalolin azabar da Allah ya tanadarwa duk wani mazinaci da mazinaciya sannan ita zina bashi ce tun kafin aje lahira ake fara biyanta a duniya dan in kayi da uwar wani sai anyi da taka, in kayi da k'anwar wani sai anyi da taka, sannan in kayi da yar wani sai anyi da taka haka kuma in kayi da matar wani sai anyi da taka in kuwa baka da kowa acikin wadannan tom sai anyi da katangar gidanka ga azabobi da Allah ya tanadarwa duk mazinacin dabai tuba ba ranar alkiyama.



Sosai zuciyar Yusuf tayi rauni yaji yana k'ara kyamar zina ina amfanin yaje yayi ace za'ayi da Mama ko Zulaihat ko Zarah damm gabanshi ya fad'i tunowa da yayi da Zahrah dan a kwana biyun nan yadan rage tunaninta a haka dai Malam ya karasa wa'azin saboda lokacin sallar isha'i yayi bayan an idar da salla suka fito suka nufi gida.




Aryan ne yaga jikin Yusuf yayi sanyi tun suna masallaci tafe suke zasu karasa gida Aryan yace.
"Nifa naga jikin ka duk yayi sanyi ko wani abune ya faru ko baka da lafiya ne?". murmushin yak'e Yusuf yayi yace.
"Babu komai".
shan kunu Aryan yayi yace. "Waito har sai yaushe zaka d'aukeni kamar yadda na dauke kane nifa inajin ka a raina tamkar mun fito ciki d'aya ne amma kai ina ganin kamar ba haka bane?".
cikin damuwa Yusuf yace. "Aryan kenan wato har yanzu kana haufi kan yadda ni

Please Login or Register in order to submit comment