Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi tare,
hakan yayi maka ko?". murmushi Yusuf yayi had'i da gyad'a kanshi cikin tsananin farin ciki.



Aryan kuwa mik'ewa yayi ya fara rawa yana juyi suma zasuje turai karatu me kuwa Hajiya Kaka da Yusuf zasuyi inba dariya ba.




Duk wani cuku-cukun tafiya karatun su Yusuf an gama inda zasuje South Africa wata makaranta koyar da harkar Polo wacce zaiyita tsawon shekara d'aya *JURASSIC PARK POLO*
in ya gama one year d'inshi zai jona wata jami'ar dan karantar businesses administration.
an kammala komai
visa kawai ake jira ta fito su tafi.



Haka kuma tafiyar su Mama ta gabato dan saura kwana 2 su tafi kuma yauta shirya tanaso su hadu da Yusuf Abba dake shirin fita ta kallah tace.
"Gashi tafiyar mu ta gabato inaso muje nida Auntyn Zarah ta rakani kasuwa nad'an tsinto abinda ba'a rasa ba kuma ya kamata naje nayiwa Iya sallama (Iya mahaifiyar Mama ce) shiru Abba yayi kome ya tuna oho saiya d'auko wrapper d'in 500 ya mik'a mata yace.
"Gashinan kada ku dad'e dad'i sosai Mama taji gudun kada ya ganota saita danne farin cikin ta tace.
"In sha Allah zamu dawo da wuri".
sai data rakashi har bakin mota ya shiga kai tsaye part d'in Aunty Amarya ta wuce a parlour ta sameta cikin zumud'i tace.
"Kiyi maza ki shirya kafin Daddyn Zarah ya fita ya mik'amu gidansu Yusuf". cikin murna Aunty Amarya tace.
"Yanzu kuwa da badan Zarah tana makaranta ba aida mun tafar mishi da ita dan kullum bata da magana saita Hammanta Yusuf".
murmushi Mama tayi tace. "Na rasa wanne d'asawa ce ta shiga tsakanin Yusuf da Zarah a kwanakin nan kuma basu fara shirin ba saida yake shirin barin gidan". dariya Aunty Amarya tayi had'i dayin k'asa-k'asa da murya tace.
"Tunda ya dakar mata Hajja Inna take gadara dashi ai". murmushi kawai Mama tayi da girgiza kanta tace.
"Hmmm yaro yaro ne yaro man kaza."
sai kuma ta juya zata tafi sai kuma ta juyo tace.
"Kiyi maza ki shirya fa".
da "to" Aunty Amarya ta amsa sauri-sauri ta tashi taje part d'in Mama lokacin itama ta gama shiryawa zuwa sukayi sukayiwa Hajja Inna sallama zasuje Kasuwa fatan dawowa lafiya tayi musu,
sannan suka yiwa Ummi ma sallah Daddy ya d'aukesu.

Suka nufi cikin Jimeta,
cikin mamaki Mama ta kalli Daddy ganin inda yayi parking ta kayo tare da cewa.
"...!











*BY*
*GARKUWAR FULANI*
[02/01 12:45 PM] My 2nd Mtn: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣7⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



0005388578 JAIZ BANK AISHA ALIYU GARKUWA
sai number da za a turo katin mtn
09097853276


ASSALAMU ALAIKU
Yan uwana maza da mata ina masu matsaloli rashin wadataccen ni ima musamman mu mata rashin ni ima babbar kalu balene agaremu"saikuga wasu ma auratan sunkasa samun nutsuwa da fuskantar juna"ba wani abubane kejanyo hakan illa rashin gamsar da juna"to kuzo gadama tasamu"
Ni AYSHA ALIYU GARKUWA
Nazomuku dawani babban albishir,dagakanyau kisa aranki har inkin fara amfani dashi to insha ALLAHU kinyi kawa dafarin ciki azaman aurenki...
(Akwai maganin sanyi na maza da namata"irin tsanyi mai kashe gaban dana miji yakasa tabuka komai azaman takewarsa na aure)akwai garin mad'i maikyau Wanda idan kkyi amfani dashi hmm bazance komaiba kedakanki zaki kuma nemata,)sannan kuma "akwai sabulun wanka na amare da man shafawa sanna kuma akwai gunba maikyau yar Niger dana kasar Mali da dai sauransu) gamai bukatar tsaya saiya tuntubeni tawanna lanbar kamar haka
09097853276
Sainajiku ngd🤝🏻



"Asibiti kuma! meke faruwa waye ne ba lafiya."
Kai ya juyo da sauri yana kallonta dan jin alamun a firgice take, cikin sauri yace.
"A a kowa lafiya karki firgita magungunan Hajiya kaka ce zan d'auko dan in kaimata shi da wuri."
Ajiyar zuciya ta sauk'e da cewa.
"Aiyo ai wallahi na firgita ainun naji tsoro."
Anty Amarya ma ajiyan zuciyan tayi tare da cewa.
"ai ni ba wanda na tuna sai Tattina." (mahaifiyar Anty Amaryan kena) shi kam Daddy tuni ya shi cikin F, M, C,
bai jimaba ya fito hannunshi rik'e da ledar magunguna motar ya shiga tare janta ya nufi cikin Jimeta.

Kai tsaye bayan p,z, d'in ya nufa,
a bakin gate d'in gidansu Aryan ya tsaya tare dayin hon, da sauri maigadinsu ya lek'o ganin Daddyn ya sashi saurin bud'e musu gate, kai tsaye ya shiga da matarshi a harabar gidan yayi parking, Mama kam jikinta har rawa yakeyi da sauri ta bud'e k'ofar tare da fita, itama Anty Amarya da sauri ta fito,
shiko Daddy yana fita, mai gadin da direbansu na isowa
rusunawa sukayi har k'asa cikin sauri Daddy yace.
"A a Baba tashi mana."
mik'ewa tottijon yayi tare da mik'awa Daddy hannu suka gaisa,
sanna Daddy ya juyo gun direban yace.
"Mutane giadn nan ko."
"Eh suna nan."
juyowa yayi ya kalli Mama sannan yace.
"Toh ku shiga daga ciki."
ai kamar jira take dama a bata umurni cikin sauri da sassararfa suka nufi cikin gidan,
shi kuwa dadi ihsanin kasafin kud'i yayiwa Baba mai gadin da Lado direba tare da tuntub'arsu shige da ficensu Yusuf ba matsala ko.


Suna isa bakin k'ofar Mama tayi sallama tare da d'an bubbuga k'ofar,
Cikin gidan kuwa Raihana dake zaune a parlour tana tsefewa Hajiya kaka kai
kai ta dan sunkuyar ta kalli Hajiya kaka data fara gyangyad'i hannu tasa ta d'an tab'ata tare da cewa.
"Kaka! Kama!!."
cikin d'an magagin gyangyad'in ta d'ago kanta tare da cewa.
"Uhum kin gama ko?."

"A a d'aga min k'afa munyi bak'i bakiji ana buga k'ofaba."

Da sauri ta mik'e tare da jawo kallabinta ta d'aure kanta, cikin bada umurni tace.
"Maza jeki bud'e k'ofar mana Raihana."
da sauri ta juya tare da cewa.
"Toh."
tana zuwa ta bud'e musu k'ogar ganin bak'in fuska sai ta d'anyi murmshi cikin sanyi da tarbiya tace.
"Sannunku da zuwa."
sai kuma ta rab'a gefe tare da cewa.
"Anty ku shigo mana Kaka na ciki."
cikin jin dad'i Mama tayi gaba yayinda Anty Amarya ke binta a baya,
ita kuwa Raihana ta meda k'ofar, kai tsaye kitchen ta nufa ta d'auko drinks da cup biyu sannan ta juyo.

"Lale marhabin, marabanku, ku iso bisa kujera."
Kaka fad'i fuskarta cike da fara da alamun daddatu da son bak'i,
suma cikin girmamawa da jin dadi suke amsawa da.
"Yauwa Hajiya."
tana ta nuna musu kan kujeru su zauna amman fir sunk'i
sai zama sukayi a gefenta kan tattausan carpet d'in da take zaune,
cikin girmamawa Mama tace.
"Ina kwana."
shiru tayi tare da tsurawa Mama ido cikin yin murmushi tace.
"Maman Yusuf ko."
kai Anty Amarya ta gyad'a mata tare da gaidata,
amsawa tayi cikin tsananin jin dad'i baki ta bud'e da d'aga murya tace.
"Raihana maza zokije ki kira su Hammanki yau ga Mamansu tazo."
dariya Raihana tayi had'ida ajeyi tiren drinks d'in a gabansu cikin fara ta nufi gaban Mama yayinda tace.
"kai Kaka irin wannan kira da k'arfi."
ta k'arishe maganar tana rab'ewa jikin Mama,
cikin jin dad'in hakan Mama ta jawota jikinta tana cewa.
"Yau dai gani ga d'iyata Raihana."
dariyar jin dad'i kaka tayi had'i da cewa.
"ai kam Alhamdulillah yau Yusuf da Aryan farin ciki ya k'aru."
jin haka Raihana ta mik'e tare da cewa.
"Yauwa Mama barin inje in musu albishir."

bata tsaya jin me za'a ceba ta fita da gudu kai tsaye parlour su ta nufa Aryan ta samu a parlour cikin zumud'i take cewa.
"Ya Aryan ina Hamma Yusuf."
tsaki yaja tare da- daka mata tsawa.
"Ke biki da hankali ko? baki iya sallama bane, ji tsabar rawan kai baki ganshi bama."
juyowa tayi ta kalli inda Aryan d'in ke nunawa sam bata lura dashiba
ko dan konce yake a k'asa bisa carpet yasa laptop enshi a gaba, shima bai jitaba dan yayi nisa a binciken makarantar da zaije d'in *Jurassic park polo, South Africa* yana kallon irin dawakai da ake amfani dasu da hostels nasu da wuraren tsare dake ciki da irin Holls nasu inda ake d'aukar darasi da duk wani tsare-tsare da dokar makarantar
har cikin d'akunan kwanan students d'in duk gasu yana gani bisa yanar gizo-gizo, shiyasa sam baiji shigartaba sai tsawar da Aryan ya buga mata,
shisashi d'ago kanshi ganin ta k'wab'e fuska ta tura baki yasashi saurin mik'e tare da cewa.
"No karkiyi mishi kuka, zo nan ki gaya min me aka aikoki."
dan ya sani bata zuwa part inba aikota akayi ba,
murmushi ta d'anyi tare da cewa.
"Mama ce tazo."
tashi zaune Aryan cikin son ta tabbatar mai da zatonshi yace.
"Wacce Mama d'in?."
juyawa tayi tana k'ok'arin fita tare da cewa.
"Maman Hamma Yusuf."
ai kusan a tare suka mik'e sauri-sauri gudu-gudu sukabi bayanta, ita kuwa a guje ta shiga parlour kan cinyar Mama ta rab'a tare da k'elk'elewa da dariya tana.
"Aha yaseen na rigaku."
a tare suka shigo ai cikin tsananin happy suk'a had'a bakin cewa.
"Mama oyoyo."
gefenta suka nufa da nufin su rab'a jikinta, ai da sauri suka tsaya jin d'an ihun da Raihana tayi.
"Wayyo Allah Mamana zasu karya miki cinya, Allah ko Mama hanasu matsowa sunyi k'atti fa nice dai-dai d'in konciya a cinyarta ko Anty."
ta k'arishe maganar tana kallon Anty Amarya,
dai-dai lokacin kuma Kaka ta shigo dan Daddy ya turo mai gadi ya mishi sallama da ita shine taje suka gaisa, so sai yanzu ta shigo,
ido ta zuba musu cikin sha'awa ganin yadda suka sake da juna anata hira da dariya,
Aryan ne ya fara jan Raihana tare da cewa.
"Hegiya ai kema kinyi k'atuwa da zama a cinya kina 14 year ai kin girma."
Yusuf ne yayi dariya tare da cewa.
"Aryan barta ta d'ana ai mu mun saba."
sai ya kuma kalli Anty Amarya cikin shak'uwa yace.
"Anty Sulaiman fa?."
dariya tayi tace.
"Sai gobe zaizo dasu Amira, Nana, Zeenat, Mami, Ibrahim, Ja'afar, Sadik, Zahara, da Ummeenku wata k'il harda Hajja Inna da."
murmushin jin dad'i yayi tare da cewa.
"Tab Hajia Kaka gobe kinada manyan bak'in askarawa kenan."
cikin jin dad'i Hajia kaka tace.
"ai naji Dad'ina Allah ya kawo minsu lafiya."
Aryan ne yayi dariya gamida cewa.
"Amin Amin, saiko ki shirya reba dambe tunda harda aganniya Zahra za'a zo."
dariya sosai Sukey su duka, Anty Amarya ce tace.
"Kai Aryan banda sharrifa Tinana ta girmafa yanzu ta rege tsokana."
jinjina kai Yusuf yayi tare da cewa.
"Da kamar wuya."
Hajia kaka ce ta zauna gensu tare da cewa.
"Yusuf Aryan kuje Daddy na jiranku zaku gaisa."
to sukace tare da mik'ewa sukaje harabar gidan suka gaidashi, albarka yasa musu tare da yi mutsu nasiha mai ratsa jiki sannan yace.
"Bari ni zan shiga Asibiti kucewa su Maryam d'in su shirya da wuri k'arfe biyar zan taho mu tafi."
cikin girmamawa sukace.
"Toh Daddy Allah ya kiyaye hanya sai ka juyo."
"Amin Amin."
yace tare da shiga mota ya fita,
suna tsaye har ya fita,
sun juya kenan zasu shiga cikin gida sukaji muryar Zulaihat tana cewa.
"Yauwa ashe zamu gane gidan."
da sauri sukayi gunta cikin happy kulolin hannunta suka amsa tare da cewa.
"Keda waye?."
"Nida Abban su Afnan ne, yana gaisawa da Daddy ne, ai Allah yasa muna karyo kona Daddy kuma na fitowa."

Cikin jin dadi suka k'arisa parlour da manyan kulolin a hannunsu,
suna ajiyewa suka fita suka gaida Abubakar mijin Zulaihat sannan suka dawo cikin gidan.

Hira sukeyi sosai cikin nishad'i da k'aunar juna Raihana sai juyi takeyi a cikinsu,
Allah sarki bata san uwa da ubaba gwara Aryan ya sansu, basu da kowa sai Hajia kaka dan dama itama Babansu ne d'anta k'waya d'aya tal kuma ya rasu,
sai mahaifiyarsu kuma itama su biyune rak a cikin iyayensu
ita ta rasu Uncle Adam d'insu kuwa bai samu mace ta gariba, shiyasa basa zuwa, sai dai yana tsananin k'aunarsu da tausayinsu shiyasa yake musu duk abinda suke but'ata.

suna cikin hira Kaka tace.
"Kai Raihana tashi mushiga kitchen muyi aikin abinci ma tasasu da surutu ne ba abinci."
cikin tsokana irin ta kaka da jika Zulaihat tace.
"Toh a cici kontar da hankalinki na mana girki yau wunin hirane kawai, ke Raihana muje inga kitchen d'in naku in kina gyarawa mu d'auko pellets and spoons muzo muyi lunch gaskiyar sohuwarnan rana ta tsala."
mik'ewa sukayi suka shiga kitchen d'in.

Aryan, Yusuf, Aunty Amarya, Mama, Kaka, sukuwa hira sukaci gaba dayi cikin hirar Mama ta kalli Yusuf da Aryan tace.
"Jibi fa mu kam zamu tashi zuwa saudia, ku kuma sai yaushe?."
cikin sanyi Yusuf yace.
"Mu kuma gata zamu tafi."
Anty Amarya ce tace.
"Toh Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya."
Amin Amin suka amsa baki d'aya,
abincin da Zulaihat ta kawo musu bana wasa bane, tayi sokwara da miyar dege-dege sannan tayi tuwon semo da miyar d'anyar kubewa ga soyayyun kaji da snacks and drinks with cuucus.
sunci sunyi tim sai hira da raha,
ranar Raihana bataje islamiya ba,
3:35 pm Abubakar ya dawo zai d'auki Zulaihat,
rau-rau tayi da ido alamar zatayi kuka cikin sauri Yusuf yace.
"Gobe zamuzo miki da yamma."
cikin jin dad'i tace.
"to." tare da share hawayenta.

Suna dawowa rakiyar Zulaihat Mama ta tasasu gaba cikin sanyi da alamar tsoro tace.
"Toh Aryan kaga inda Allah yake shirin kaiku kaida Yusuf,
dan Allah ki rik'e addininku da mutunciku da kimarku a matsayinku na musulmai ku sani duk inda kuke Allah na ganinku kuma shine ya haneku da aikata duk wani alfasha ku zama 'yaya na gari abin alfahari ga k'asarku da mu iyayenku, Allah muku albarka ya shiryaku ya raya mana ku bisa imani ya tsare mana gabbanku daga aikata haram."

cikin nitsuwa da jin nasiharta da Addu'arta na ratsasu suka amsa da Amin Amin.

biyar dai-dai Daddy yazo ya d'aukesu, har bakin gate suka rakasu harda Kaka in da Daddy ya bata kud'i da magungunanta daya mance d'azun bai bataba,
godiya tayi sosai sannan suka tafi.


********


Washe gari Sulaiman ya kwaso su Imminent da sure Amira baki d'aya sai Zahra da zazzab'i yana su taho tare
Suma sun jima sosai amman basu wuniba, anayin azahar suka koma, suna kewan juna.


Da yamma Yusuf da Aryan suka shirya suka fita,
kai tsaye gidan Goggo Aisha sukaje suka mata sallama daga nan sukaje gidan Goggo Fatima da Maimuna, sannan suka gangara gid'an Anty Madina anan sukaci abincin dere,
sannan sukayi fadar mai martaba sarkin Adamawa dan amsa kiran da malam Jabeer ya musu,
suna shiga cikin masarautar Affan suka nema yana zuwa ya mik'a musu hannu suka tafa tare da gaisawa sannan yayi gaba suna binshi a baya har zuwa cikin wani tamfatsetsen parlour cikin sanyi sukayi sallama tare da isa inda suka hank'o ogan nasu da Saran da mahaifinshi a gefe,
murmushi yayi musu tare da nuna musu wurin zama.

Cikin girmamawa suka gaidashi, tare da Baban Safwan sannan suka mik'awa Safwan d'in hannun dan yin musabaha Amman sai ya sharesu ko inda suke bai kalla ba,
Shi kuwa Malam Jabeer
nasiha yayi musu mai ratsa jiki da zuciya sannan yayi musu addu'a tare da fatan nasara da alkhairi,
Affan ne ya kallesu cikin sha'awa sai ya kuma juyawa ya kalli d'a uwan nashi baki ya d'an zumbura tare da yin magana k'asa-k'asa,
murmushi malam Jabeer yayi dan yasan matsalar Affan, shi dole shima woje zaiyi karatu,
shi kuwa ya hana dan rawar kanshi tayi yawa, shiyasa ya samamar gurbin karatu anan inda yake aiki cikin Abti American university of Nigeria,
shiyasa yaketa k'unk'uni cikin sanyi yace.
"Wai Affan kam me kake cewa ne?."
cikin tura baki yace.
"Cewa nayi sunji dad'in su."
dariya sukayi baki d'aya dan ganin yadda yayi maganar yana wani Longon'bar da kai kamar marigayin zakara.


9:00 pm suka isa gida a gajiye suke dan haka shirin bacci kawai sukayi suka konta.

washe gari ta kama ranar tafiyar su Mama,
shiyasa su Yusuf suna dawowa sallan asuba cikin sanyi Yusuf ya kira Daddy a waya,
cikin girmamawa ya gaidashi tare da cewa.
"Daddy Mama fa?."
kai ya jinjina tare da cewa.
"Ayya Yusuf Allah bai k'addara zakuyi sallama ba da tafiyar tasu ance uku na yamma ne sai kuma kwatsam aka kirasu cewar k'arfe uku na asuba zasu tashi,
so a deren muka rakosu airport, tuni sun tashi ma."
cikin sanyi tare da zubda hawaye wani irin k'unci da kewar iyayen nashi yakeji tamkar yayi fiffige ya fire ya bisu, ji yake kamar bazasu sake ganin junaba sun rabu kenan har gaban abadan cikin tsananin k'uncin zuciya yace.
"Allah ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya."
sai kuma yayi shiru tare dasa bayan tafin hannunshi yana share hawayen dake bin fuskarsa ba k'ak'k'autawa ajiyan zuciya yaja sannan yaci gaba da cewa.
"Amman Daddy banyi sallama da Mama bafa, ga Abba yana fushi dani Daddy ya zanyi da raina?
naso inga tafiyarsu su ganni in gansu"
sai kuma muryarshi ta fara carkewa cikin zubda hawaye ya rink'a cewa.
"Daddy sai yaushe zan sake ganin Mama sai yaushe Abba zai yafe. min."
Cikin jin tausayin shi yace.
"Yusuf tafiya ai ba mutuwa bace, Mamanka zata dawo nanda d'an wani lokaci kaima zaka gama karatunka ka dawo, na tabbatar kafin nan Abbanka ya huce ya yafe maka,
karka damu Yusuf komai yayi zafi maganinshi Allah please karkayi ta kuka, in Mamanka taji hankalinta bazai kontaba, gashi itama ta tafi tana kuka tana ta barmin amanarka, karku taru ku raunata min zuciya mana kaifa namiji ne."
haka dai yayi tamai nasiha da k'arfafa mishi guiwa da kontar mishi da hankali
"To Daddy in sha Allah na bari, Ngd matuka Allah ya bar zumunci yae k'ara girmada wadata sai anjima."
yana jin Daddy ya amsa da Amin, ya katse kiran
kawai
yana mai matuk'ar jin kewar iyayen nashi,
da ker Aryan da Kaka suka samu suka sashi ya d'an sake a wannan wunin har sukayi d'an shirye-shirye su tare.



********************

Washe gari suma jirginsu ya d'aga,
sai Babban birnin South Africa,




*Wasa farin girki. yanzu aka fara shiga cikin labarin fa ku dai ku biyoni a sannu zakusha Mamakin salon wannan littafi*








*By*
*GARKUWAR FULANI*
[30/12/2019 11:38 AM] My 2nd Mtn: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣8⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*





🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*Laifin dad'i k'arewa ! toh haka dai mgnar take, so daga yau free page sun k'are. Ga masu buk'atan ci gaban littafin har k'arshe k'ofa a bud'e take, turo katin MTN na 200 kacal ta wannan layin. 09097853276, ko kuma ta asusuna kamar haka 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, tabbatar kin turo min screenshot shaidar kin biya kud'in samun damar karanta littafin har k'arsh*

*Kada ki bari a barki a baya Hukuncin Allah labari ne mai cike da darrusan rayuwarmu a yau karanta Hukuncin Allah kan 200 kacal littafi mai k'unshe da ababen al'ajabi, fadakarwa, nishad'antarwa, dariya, kuka, tausayi, nishad'i*


*Wannan shafi nakine FIDDAUSI SODANGI kekkyawar marubuciyarmu, idan nace muku kekkyawa tofa kyawun ya shahara duk da wasu makaranta na zagin marubuta wai sun fiye zuzuta kyawun jaruman littatafai, wai ai in anga wata marubuciyarma sai an gudu dan tsabar muninta ko? to ni kuwa nace in dai munada kyawawan marubuta irisu Feedo me zai hana muyi ta zuzuta kyau tunda muna ganin kyawun yana tare damu, kowafa na son kyau sai dai in bai samuba👌🏻😊😘 Feedo kekkyawar marubuciyarmu ni Garkuwa*
*inayi miki fatan al'khairi a rayuwar aurenki Allah ya baku zaman Lfy yasa iya rai da mutuwa ne Allah ya baku zuriya d'aiyiba Allah ya kawo mana Maryam nanda shekara d'aya mai zuwa, Allah ya kad'e fitina ya sanya al'khairi, Allah ya tabbatar da farin ciki a rayuwar aurenku.*



Airplane d'in na sauk'a a airport d'in babban birni South Africa d'in,
jim kad'an passengers suka fara fitowa a hankali cikin nitsuwa da wayewa, sai da a k'alla mutun sama da 23 suka fito sannan, Aryan ya fito Yusuf na biye dashi a baya, cikin shigarsu ta matasan polo daga ka gansu kasan shahararrurene kuma sanannun a harkar polon,
kyau sosai Yusuf yayi cikin rigar polo d'insu orange color mai farin rubutu a jiki wanda aka rubuta Nigerian polo club, a gaban rigar a baya kuma an rubuta Jahan team a sama dai-dai kafadunshi kuwa an rubuta Yusuf 1 a k'asanta kad'an kuma sai akasa Baraden Adamawa da tambarin zanen doki da mutun akai yana rik'e da sword cup tare da d'aga polo stick enshi sama, sai wandon jeans blue color sai d'an rasin fari-fari a dai-dai cinyoyinsa, sai hular p carp shima orange color an rubuta Jahan team a gaban goshinsa, sai ida nunshi dake manne da wani d'an siririn glasses mai ruwan garai-garai, sai takalmin boot shima orange color sai igiyoyinshi farare, sai hannunshi dake daure da agogon gucci fari k'al, hannunshi na rik'e da logadge.

Cikin wani irin yanayi ya lumshe ido tare da shak'ar iskar k'asar, sassanyan numfashi ya fesar cikin jin wani irin yanayin k'asar na ratsa jiki da jininshi har cikin k'ahon zuciyarshi yakejin sassayanyar iskar na ratsashi tako wacce k'ofar gashin jikinshi,
a hanakali yake motsa lips enshi alamar yana addu'ar neman shiga lafiya da farawa lafiya da gamawa lafiya,
cikin nitsuwa ya fara taka steps d'in one by one yana bin bayan Aryan da ke gabanshi,
kai tsaye harabar inda passengers ke zuwa su tsaya dan duba masu d'aukarsu suka nufa,
suna zuwa suka shiga cikin taron jajayen kunnuwa inda suma suka saje dasu, gaba sosai suka shiga inda suka tsaya gaban igiyar da tayi katanga tsakanin masu d'auka da wad'anda za'a dauka,
jim kad'an shiru basuga wanda yazo d'aukarsu ba, Aryan sai raba ido yakeyi, shi kuwa Yusuf wayarshi ya zaro cikin aljihun jeans enshi ya fara d'an latse-latse, sai tsaki da yake d'an ja k'asa-k'asa yayinda kowa harkar gabansa keyi a wurin ba ruwan wani da wani, yana cikin latsa wayar yaji, Aryan na cewa.
"Yauwa Yusuf gacan mai zuwa d'aukarmu shima yanata baza ido."
kai ya d'ago tare da lumshe idonshi ya bud'esu kan d'an k'aramin katakon da maturen ke rik'e dashi yake ta jujjuyawa wanda a gaba an rubuta Nigerian polo, a baya kuwa ansa Jahan team,
kafin ya ankara sai jin muryar Aryan yayi yana cewa.
"Hi Nigerian polo."
aiko da sauri baturen ya juyo cikin sakin fuska yazo wurin tare da karb'ar logadges insu tare da cewa.
"Ur welcome." cikin sauk'e numfashi da d'an sakin fuska Yusuf yace.
" thanks." kai tsaye motar sukaje suka shiga inda suka kama hanyar makarantarsu Aryan University of Cape Town, dan shi bazaiyi na polo ba,
shi kuma Yusuf sai next year zai koma makarantarsu Aryan d'in yayi digiri insha amman yanzu kam Jurassic Park polo South Africa zai fara.

"Ya subahanallah."
Yusuf yace lokacin da suka kutsa kai cikin jami'ar da duk South Africa ake ji da ita, kai ya maida jikin kujerar ya lumshe idonshi tare da sauk'e numfashi, Aryan kuwa sai sauk'e ajiyar zuciya yakeyi akai-akai dan tsaruwa da had'uwar jami'ar ta zarta zaton mai karatu, duk abinda zance bazan fidda tsarin had'uwarsa ba sai mazauna can zasu gane me nake nufi,
makaranta ce mai cikar tarihi daci gaba wanda kan dutse take yayinda tsirrai da itatuwa sukayi

Please Login or Register in order to submit comment