Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bazai min hakaba. a !a ! ba Aryan d'ina bane sai dai in wani Aryan d'inne." Ya fada so confused in difficult breathing.
sai ya kuma yi maza ya k'ara zubawa takardar ido ganin tabbas ga sunan wanda ya shigar da k'aran b'oro-b'oro tabbas Aryan d'inshi ne ya shigar da k'ararshi wai ana zarginshi shi yayiwa Zahra fyad'e. Lumshe ido yayi cike da kuna ya furzar da numfashi
wani irin suka ya kuma jin k'irjinshi yanayi yawun bakinshi duk ya k'afe yayi d'aci,
wani irin sarawa kanshi keyi tamkar zai rabe gida biyu,
lokaci d'aya wani zazzafan zazzzabi mai tsanani ya rufeshi,
ji yakeyi inama ya mutu ya bar duniya a kan wannan abu dake shirin faruwa dashi.
haka ya zame kan sofa d'in ya konta rubda ciki sai karkarwa yakeyi.




Aryan kam, bayan ya meda su Hajia Kaka gida,
yana fita kai tsaye court d'in daya shigar da k'arar ya nufa. inda yaje domin yin shirye-shiryen fuskantar zaman da za'ayi a gobe Monday nan mai zuwa.


Abba kuwa Aryan na fita yabi bayanshi da wani irin kallo,
jikin tsananin mutuwan jiki ya mik'e ya nufi bedroom d'inshi,
kan gado ya zaune tare dasa hannu bibbiyu ya tallabe kanshi ya rabga wani tagumi mai cike da abubuwa,
idanunshi sun kad'a sunyi jazir,
ya kasa yin komai sai lips d'inshi daya hade ya taune,
sai ya kuma zubawa k'ofar shigowan idanu ko k'ebtasu baya yi,
yayinda can k'asan zuciyarshi kuwa addu'o'i ne barkatai wanda nima kaina bansan na menene yakeyi ba,
kawai dai na lura kamar yana cikin tsananin tsoro da fargaban gudun wani abu.

A parlour Hajja Inna kuwa bayan Hajiya kaka da Aryan sun tafine,
Maman Yusuf ta matso jikin Zahra da har yanzu batayin mgna sai ido da take zazzarowa alamun har yanzu bata dawo hayyacinta ba,
Aunty Amarya kuwa dage gefen Zahra Kuka takeyi har yanzu ida nunta sun kumbura sunyi sumtun-simtum hatta leb'en bakinta ya kumb'ura yayi jazir gaba d'aya kamanninta ya sauya,
Ummi da take tsaye sai tab'e baki tayi tare dayiwa Aunty Amarya wani irin kallo mai cike da manufofi,
Hajja inna kuwa goronta ta d'an b'alla ta afa a baki tare da gyara zama tace.
"Hmmmm maji ma gani, ai dama ni nasan Zahra ta rina abinda yafi haka,
yoh dama tunda aka saketa kamar bata da ma fad'a ai a tsammaci haka ko?."
Mama kam kai ta sunkuyar cikin zubda k'ollah ta jawo Zahra jikinta,
da sauri ta tallabota jin yadda Zahran ta k'amk'ameta ga kuma hawaye dake kwaranya a idanunta,
Ummi kuwa juyawa tayi ta fita,
lokacin da taga Daddy ya shigo,
domin bata tab'a ganin tsantsar tashin hankali a fuskar mijintaba kamar yau,
gaba d'aya fuskarnan tashi ta tashi daga fara ta koma jazajir tamkar wanda aka watsawa ruwan zafi,
bisa dukkan alamu shima Daddy kwana yayi yana kuka domin idanunshi sun kumb'ura,
gefen Aunty Amarya daketa ruzgar kuka yaje ya zauna,
tare da zuba mata ido,
yana mai jin wani irin tsananin bak'in cikinta da tsanar halaye da d'abi'unta,
can k'asar zuciyarshi kuwa tausayinta yakeji,
domin shi dai Daddy ya yarda cewa wannan k'addararsu ce a zuriyarsu, kuma basu da dama ko dabarar kaucewa rubutaccen al'amarin da Allah ne ya rubuta musu,
tabbas yasan Aunty Amarya bata da kula kan tarbiyar yaranta,
amman duk gidan suna tarbiyartar da kula da Zahra to wannan shine jarrabawa mafi muni da zafi da zuriyarsu ta fuskantar a tsawon tarihinsu,
ido ya rumtse da k'arfi yana jin sautin kukanta wanda dashi ta kwana cikin tsananin kaushin murya yace.
"Maryam ai kin fara kukan da wuri,
da kin adana hawayenki har sai lokacin da kikaga yarki ta zama abin kwatancen mak'otanki kafin ki fara kukan abinda sakacinki ya jaza miki,
lallai sam baki cancanci da a kiraki da uwa ta gariba,
domin baki zama mai kula da kiyaye amanar da Allah ya bakiba,
Allah ya gani ni dai duk wasu hak'k'ok'insu da Allah ya d'auramin na sauk'eshi,
na killaceku na ciyar daku na shayar daku na tufatar daku na jinyaceku na ilimantar daku, dan in baki mantaba kema a gidana kika k'arisa karatunki,
ina bibbiye da lamuran rayuwarku mutanen gida kowa hankalinshi na kan yaranki sabida ke uwace da baruwanta da tarbiya,
ni kuwa dole zan fita nemo mana na rufin asiri babu yadda za'ayi in zauna a gida,
ke kuma da kike gida, na hanaki yin aiki duk da kinyi karatu sannan na ware muku salaries keda abokiyar zamanki ina baku duk wata wai duk don ku kasance a gida kusa da yaranmu a koda yaushe,
amman abu ya faskara harda tsaro aka samar a gidannan amman duk a banza,
toh ga irinta nan rayuwar yarki ta samu tabonda har gaban abadan bazai gogeba."
sai ya kumayi shiru tare da sharte hawayen dake bin fuskarshi har kan geminshi,
Zahra ya zubawa ido na d'an wani lokaci,
sai ya kuma kalli Maman Yusuf yadda itama take kuka kai ya girgiza dan tuno rashin mutuncin da Aryan yazo musu dashi inda shi dai Daddy baram-baram yayiwa Aryan ya kuma gargad'eshi da cewa ko,
turmi da tabarya ya samu Yusuf a kan Zahra to bayi da hurimin shigar da k'ara,
lallai Daddy yaji k'uncin duniya akan fyad'en da akawa Zahra amman yafi jin k'una da bak'in cikin sharrin da Aryan yake son lik'awa Yusuf dan b'ata mishi suna
da yakeda nufin yi,
kai ya juya cikin rumtse ido ya kalli Aunty Amarya sannan ya mik'e yayi taku d'aya ana biyu yace.
*"Maryam kije gidanku na sakeki saki d'aya".*
wani irin zabura Maman Yusuf tayi tare da zubda zazzafan hawaye,
Hajja inna kuwa kai ta juya cikin wani yanayin tausayawa d'an nata dan tasan shi mai hak'uri ne,
ita kuwa Aunty Amarya hannu tasa ta sharte hawayenta cikin disashewar murya ta fara mgna tare da sautin kuka da nadama mara amfani tace.
"Na cancancin duk hukuncin daka yanke min,
tabbas ban zama uwa ta gariba,
ni kaina na tsani kaina domin duk abinda ya samu Zahra sakacinane ke bibiyarta,
Zahra tun tana k'arama nake ganin isharori a kanta,
yayinda ni na haifeta amman Yusuf yaro k'arami shi ya zama Garkuwarta,
kayi hak'uri Daddyn Jafar ka gafarceni,
tabbas nasan na cutar da zuciyarka na zama sanadin da martabar gidanku ya raunata."
sai kuma kuka mai k'arfi ya kwabce mata,
itama Maman Yusuf tuni kuka takeyi mai cin rai tana jin tausayin k'anin mijin nata kuma d'an uwanta d'an kawunta,
uwa uba Aunty Amarya ma sai ta zama abar tausayi domin duk wanda yayi nadama mara amfani tofa ya tab'e.
Hajja innama kalaman Anty Amarya yasa ta d'anji tausayinta,
cikin gida kuwa Mami da Nana suna d'akinsu kuka sukeyi ba mai lallashin d'an uwanshi,
Jafar kuwa yana bakin k'ofar parlour Hajja Inna yana jin duk abinda Aunty Amarya ke fad'i wani irin tausayinta yakeji,
ya tabbatar duk duniya babu wanda zai kaita jin bak'in cikin wannan abun da akayiwa Zahra sai dai gashi sanadin sakacinta yasa Daddy ya yanke hukunci mai tsauri a kanta,
ita kuwa Zahra sai hawaye dake kwaranya a fuskarta tamkar an bud'e igiyar ruwa,
bata fahimtar abinda suke tattaunawa a kanshi,
sai dai ganin Daddynta na kuka cur-cur shi yafi komai d'aga mata hankali,
sannan ga Auntynta ma sai kuka takeyi,
kai ta d'ago tare da kalon Mama sai ta kuma sa hannu ta share hawayen dake bin fuskar Maman,
sannan ta yunk'ura zata mik'e da nufin zuwa gaban mahaifin nata sai ta kuma yi maza ta koma zaune dan azabar da taji ta ratsata,
da sauri Mama ta tallabota ta medata jikinta.

Shi kuwa Daddy part d'inshi ya wuce,
sai Jafar dake binye dashi a baya.

Aunty Amarya gaban Zahra tazo,
tare da kallonta cikin sanyi tace.
"Zahra na ki gafarceni, tabbas ban zamar miki uwa ta gariba,
ban damu da
sa ido kan tarbiyarki ba, uwa uba ban meda hankali kan yi muku addu'a ba,
gashi yau naga sakamakon sakacina."
sai ta juya da sassarfa ta fita kai tsaye bedroom d'inta ta nufa kan gado ta zauna tana wani irin kuka mai cin rai.
Babban d'anta yayansu Zahra kenan shine ya shigo d'akinshi gefenta ya zauna cikin tsanyinshi yace.
"Dan Allah Aunty na kibar kukanan haka,
ya isa kuka bazaiyi maganiba,
dama can haka Allah ya tsara rayuwar Zahra ba saka cinki bane."
cikin kuka tace.
"A a Ibrahim sakaci nane sila kuma dole kowa zai d'ora al'hak'in abinnan kan sakaci nane sanadi,
shike nan Zahra ta rasa martabarta ko?."
kai ya juya mata tare da cewa.
"Aunty Zahra fa ba karuwa bace,
fyad'e fa akayi mata da k'arfi,
kinga ko ashe ba laifinta bane ba kuma laifinki bane,
kuma in dai baki bar kukannan ba to ita kuwa Zahra ya kikeso tayi."
haka dai yayi ta bata baki.

Maman Yusuf tallab'e Zahra tayi suka tafi part d'inta kai tsaye bathroom d'in Maman suka shiga,
nan ta had'a mata ruwan d'umi ta gargasa mata jikinta,
sannan ta kalleta cikin sanyi tace.
"Zahra."
bata amsaba kuma bata kalletaba,
saida ta kuma kiranta karo na uku tace.
"Zahra ki kalleni in kina jina."
kai ta d'ago ta zubawa Maman ido ganin haka Maman ta gane tana jinta kenan cikin tausayawa tace.
"Kiyi niya kiyi wonkan tsarki,
sai kizo kiyi sallolin da ake binki."
kai ta sunkuyar tare da zubda zazzafan hawaye,
dan ita bata tab'a yin wonkan tsarkiba daya shafi hakaba,
tunda har yau bata tab'a yin al'adaba,
itama Mama tasan Zahra bata tab'a yin al'adaba,
fita tayi kai tsaye kitchen ta nufa tea ta had'o mata sannan ta dawo,
dakin ajiye cup d'in tayi sannan taje bakin k'ofar bathroom d'in cikin sanyi tace.
"Goggon Abba fito mana in kin gama."
ita kuwa Zahra tabbas yanzu ta bar jin zafin don alluran da akayi mata ga gasatan da Mama tayi,
zazzab'inma ya sauk'a sai tsananin ciwon kai da takeji,
shiyasa takeyin komai a hankali,
dogon wondon da doguwar rigar da Mama ta kawo mata ta saka sannan ta fito a hankali take tafiya,
sallaya ta d'auka ta shimfid'a da niyar zata biya sallolin dake kanta,
ganin haka Mama ta matso inda take hannunta ta jawo zuwa bakin gadonta,
zaunar da ita tayi,
sannan ta fara bata tea d'in,
ba musu ta fara sha dan wani arin azabebben yunwa da takeji domin rabonta da abinci tun jiya da safe,
don ko na rana bataciba wai sai ta gamawa amarya kolliyarta,
ido ta rumtse dan jin tea d'in tayi kamar da filajin aka tafasashi,
daurewa dai tayi tasa rabin kofin,
sannan ta janye kanta goran rowan dake kan dressing mirror ta d'auka ruwan ta kurb'a ta kurkure bakinta sannan ta matso jikin window ta zuge glasses d'in ta fasa ruwan ta woje,
sannan tazo ta fara sallolin da Mama ta gaya mata ana binta,
bayan ta idar ne Mama ta bata magungunanta tasha sannan ta kontar da ita tare da cewa.
"Kiyi baccinki."
kai ta gyad'a mata alamar toh,
sannnan ita kuma Mama ta fito kai tsaye kitchen ta wuce breakfast ta had'a mai sauk'i,
saida ta kammala ta kaiwa Hajja ina tare dasu iya shatu sannan tazo ta shirya na Abba ta nufi parlour shi,
shiru parlour ba kowa dan haka ta ajiye tiren a kan dinning table sannan ta nufi bedroom,
sallama tayi kusan baki biyu,
jin shiru ba amsa,
yasa tayi sallama na uku tare da kutsa kai cikin bedroom d'in don tasan yau Abba fa sai abinda Allah yayi,
da sauri ta isa inda yake ganin yana zaune kamar wanda aka dasa ya buga tagumi da hannu bibbiyu ga idanunshi da sukayi tamkar zasu amayar da wuta,
bisa dukkan alamu kuwa ya dad'e a zaune,
gafenshi ta zauna a k'asa kan carpet tare da cewa.
"Abban Yusuf! Abban Yusuf..!! Abban Yusuf..!!!."
yana jinta amman ya gaza amsawa sai ajiyan zuciyar da yaja,
da k'arfi ya samu ya rumtse idonshi,
yana jin wani irin tausayinta na ratsashi
shin ya zataji in taji zargin da Aryan ya d'aurawa Yusuf d'in ta,
ita kuwa Maman Yusuf cikin sanyi ta fara magana.
"Abban Yusuf komai yayi tsanani yanafa tare da sauk'i dan Allah karkasa abinnan a ranka."
zamewa yayi ya dawo k'asa kusa da ita jawota yayi zuwa jikinshi,
murya can k'asa yace.
"Maman Yusuf."
kai ta d'ago ta zuba mishi ido jin yadda ya kiratan,
zuciyarta kuwa sai bugawa takeyi da k'arfi,
shi kuwa sai k'ara jawota jikinshi yayi cikin fargaba ya kuma cewa.
"Maman Yusuf."
numfashi taja da k'arfi dan duk kiran da yake mata fargaba takeji na rufeta,
saida taji ya yauta kiranta alamun yana son ta amsa mishi,
shiyasa ta muskuta cikin sanyi tace.
"Na'am Abban Yusuf."
jin ta amsa mishi yasa cikin k'arfin hali yace.
"Kunyi mgna da Yusuf ne?."
kai ta jujjuya mishi alamar a a, dan tsoronta ya tsananta,
shi kuwa cikin kauda kai yace.
toh kinyi mgna da Aryan kuwa?."
nanma kai ta juya mishi,
Uhummmmm yace tare da gyara zamanshi suna fuskantar juna cikin tsareta da ido yace.
"Toh ki kira d'anki ki bincikeshi,
domin Aryan yazo min da batun yana zargi ko ma yak'ini cewa wai Yusuf ne yayiwa Zahra fyad'e ba idris bane,
kuma tuni har ya shigar da k'arar Yusuf."
wani irin mik'ewa Mama tayi tare da dafe k'irjinta cikin tsananin firgita da tsoro da tashin hankali,
cikin d'aga murya tace.
"A a ban yardaba in sha Allahu ba dai Yusuf na ba kam sai dai wani Yusuf d'in,
ko kuma in Aryan d'in ya tab'une,
nasanma Aryan bazaiwa Yusuf na hakaba."
hannu yasa ya kamota tare da zaunar da ita sannan ya mata duk bayanin da Aryan ya mishi ya k'ara da cewa.
"Yanzu dai sai abinda court ta bincika ta gano."
sai ya kuma tsuke fuska tare da cewa.
"Kiyi Addu'a dai kar a samu d'anki da wannan laifin,
muddin batun Aryan ya zama gskya to lallai Yusuf zai fuskanci Hukunci na Allah sannan daga nan bani bashi,
dan haka ki binciki d'anki,
ki kuma bashi shawara kada yayi tunanin yin wasa da shari'a,
ki tabbatar ya gaya miki gskya domin wlh in na sameshi da wannan laifin,
ina tausayawa tsokun rayuwar da zai shiga."
gaba d'aya jikin Mama ya mutu wani irin fargaba da tsoro mai tsanani ya rufeta,
a zahiri take ganin bala'i da taurin zuciyar Abba,
a fili take ganin zai aikata fiye da abinda yace a kan Yusuf d'in muddin yatabbata shi aikata,
wasu irin zafafan hawaye netaji suna bin kuncinta
mik'ewa tayi da sassarfa ta fice,
kai tsaye d'akin ta shige gefen Zahra ta zauna wacce ta kasa bacci duk rumtse idon da zatayi sai take ganin abinda ya faru da ita.
a bakin gado Mama ta kife kanta wani irin marayan kuka ta saki mai cin zuciya da ban tausayi,
ita kuwa Zahra sai ido ta zura mata,
cikin tsananin kuka Mama ta kamo hannun Zahra murya na rawa tace.
"Zahra waya miki fyad'e?."
shiru ba amsa Zahra sai ido data zaro,
ita kuwa Mama cikin kuka tace.
"Aryan meyasa zakayi min haka,
me Yusuf yayi maka da zaka bishi da wannan mugun zargin,
Aryan ya zaka tarwatsa min farin cikina,
meyasa sai lokacin da kaga Abban Yusuf ya fara sakewa ya fara mararin Yusuf ya dawo garemu,
meyasa ka zabi ka gayawa Abban Yusuf meyasa baka gaya minba."
sai ta kuma rik'o Zahra cikin tsananin kuka tace.
"Zahra kinji Aryan ko,
yace wai Hamma Yusuf d'in kine ya miki fyad'e sannan ya shigardashi k'ara."
wata iriyar zabura Zahra tayi sai kuma ta rink'a jujjuya kai hawaye masu d'umi na bin fuskarta,
ita kuwa Mama sai ta ruggumo Zahra cikin kuka tace.
"Dan Allah Zahra ki gaya min gskya,
wlh in dai Yusuf ne ya miki fyad'e kada kiji tsoro ki gaya min,
ni kuwa zan gayawa Abbanku,
ayi mishi Hukuncin Allah."
ita dai Zahra har yanzu Allah bai bata bakiba,
domin gaba d'aya tunda abin ya faru sai ta zama kamar ta shiga d'imuwa,
ita kuwa Mama sam bata haiya cinta,
kuka takeyi kamar ranta zai fita.
"Ni na sani Yusuf na ba mazinaci bane,
na sani,
meyasa zaka min haka Aryan,
meyasa Aryan ni na d'aukeka tamkar gudan jinina ina jinka kamar Yusuf."

haka dai Mama tayi ta kuka da suru tai.


Aunty Amarya kuwa har ta had'a kayanta zata koma,
gidansu
Hajja Inna tace babu inda zataje,
ta koma d'akinta ta zauna ko Daddy bazai meda itaba ta zauna zaman iddarta a nan,
dole Aunty Amarya ta koma ta zauna
Mami kuwa tayi kuka har ta godewa Allah abu biyu ya had'un mata anyi k'anwarta fyad'e an kuma saki mahaifiyarsu.

Abba kuwa Mama na fita,
shima ya shirya ya fita,
kafin ya fitane ya haura sama wurin Daddy,
a parlour ya sameshi shida Jafar,
zama yayi gefen Daddy cikin fiddo true color inshi yace.
"Toh Aliyu ka ji batun da Aryan yazo min dashi ko,
dan yace min ya gaya maka, ka zazzageshi da yake baka son gsky."
cikin tsuke fuska da tsananin tashin hankali Daddy yace.
"A dai wannan karon to sai dai kayi hak'uri Yaya Muhammad wlh abinda kake shirinyi kaida Aryan bada yawuna ba."
A fad'ace Abba ya mik'e tare da cewa.
"Toh ni da yawuna za'ayi, kuma ni ina bayan binciken Aryan,
kuma wlh muddin aka sameshi da laifinnan sai duniya ta sani."
kafin ma Daddy yayi wani yunk'uri Abba ya fice,
shi kuwa Daddy komawa yayi zaune cikin tashin hankali
Jafar ne ya zuba mishi ido cikin tausayin mahaifin nasu da tsoro abinda wannan sabon al'amari zai haifar a familyn nasu cikin sanyi yace.
"Daddy kayi hak'uri in sha Allah, Hamma Yusuf bazai tozarta ba,
domin bai aikata laifin da ake zarginshi da Shiva,
kawai dai sharrine irin na mugun abokin da kai kuma ka rik'e da amana,
dama ance kaji tsoron sharrin wanda ka kyautatawa."
cikin tashin hankali Daddy ya nisa tare da cewa.
"Ya Allah ka kawo mana sauk'in wannan mummunan lamari."
sai ya kuma kalli Jafar cikin karaya yace.
"Jafar ya zanyi in bawa Yusuf kariya akan wannan mugun k'ulli ya zanyi in fiddashi?."
Cikin sauri Jafar d'in yace.
"Daddy nimafa shaidane lokacin da abinma ya faru Hamma Yusuf baya gidan mafa,
muna tare dashi a gidan mai, tare muka koma gidan lokacin da labarin abin ya riskemu,
Daddy ni zan zama shaidar Hamma Yusuf in sha Allah burin Ya Aryan bazai cika ba."
haka dai sukayi ta tattauna yadda abun zai kasance.

Abba kuwa yana fita ya nufi harabar gidan wurin parking lot nasu,
tafiya yakeyi cikin tsananin fushi da tashin hankali,
Adda Zulaihat da yanzu mijinta ya kawota dan duba lfyar jikin Zahra,
bayan Abban tabi cikin rauni tace.
"Abba barka da safiya."
ina sam bayaji baya gani sai tsantsar tafasar da zuciyarshi keyi,
baki uku tana gaidashi bai kula taba,
saima figar motarshi yayi ya fice da gudu,
ganin haka yasa hankalin Zulaihat tashi,
da sassarfa ta shige cikin gidan.

Kai tsaye bedroom d'in Mama ta wuce dan tajiyo sautin kukanta a can,
tana shiga tayi gaban Mama wacce take kuka mai cike da ban tausayi
Ummi kuwa da Aunty Amarya wacce itama kukan takeyi, sautin kukan Mama suka ji shiyasa suka shigo,
tashin hankali gidan ya k'aru a lokacin da Mama takeyi musu bayanin abinda Aryan yakeda nufin aika tawa,
gaba d'aya sun shiga rud'ani
lallashin Mama sukeyi da bata k'arfin guiwa,
Hajja inna kuwa baki ta tab'e ta kalli Zulaihat data rud'e take ta tambayarsu meke faru,
k'ara tab'e baki Hajja Inna tayi tare da cewa.
"Yoh ai dama sa rina, me abin mamaki da k'aryatawa ni ko yan mata dozin akace min Yusufa yayiwa kaciya zan yarda,
ai kuma kun sani zai aikata abinda yafi haka,
yaron da yakejin kanshi kamar doki,
yana ji da k'arfi ga kud'i ga rashin mafad'i,
to ai dama kunsan abinda ya karanto a k'asar wojen,
ai in dai fyad'ene to yanzu ya fara,
in kunga ya bari dai sai dai in nasa Abbansu ya dandatse d'an iska ya medashi kamar taure."
tsorone ya k'ara rufe Zulaihat domin bata fahimci mgnar kakar tasuba,
cikin zubda hawaye ta kalli Ummi wacce ita idonta k'amas ba d'igon hawaye tace.
"Dan Allah Ummi meke faruwa ne?."
nitsawa tayi tare da cewa.
"Uhum ke dai bari yaran yanzu sai a hankali,
kaga yaro sunu-sunu kamar na Allah,
amman aiyu kanshi ko dujal sai ya sara mishi ki gafa fyad'en da akayiwa Zahra ashe Yusuf ne ya mata muna fukin Allah ta ala,
sai Aryan yaron kirki shine ya fidda gskya."
wani irin zabura da kuka Zulaita ta saki tanayi tana jujjuya kai tare da cewa.
"Shi dai ba munafuki bane kuma Yusuf bazai aikata hakaba,
k'azafi za'ayi mishi,
yanzu Ummi ke kin yarda kenan?."
cikin ko in kula tace.
"Kwarai kuwa na yarda,
to me zai hanani yarda amininshi nefa ya fad'a
wanda suke rayuwa a tare ai komi Aryan ya fad'a a kan Yusuf duniya zata yarda."
tana fad'in haka ta fice da alamar abin ya mata dad'i,
bayanta Hajja Inna tabi,
ita kuwa Zulaihat cikin kuka tace.
"Mama ki kira Yusuf mana wata k'il zai amsa kiranki,
muji ta bakinshi, dan ni tunda asuba nake kiranshi baya amsa kiran."
cikin kuka Mama ta sharte hawayenta tare da cewa.
"Na kirashi yafi sau 35 baya amsa kiran, ban san wani hali yake cikiba."
jin haka gaba d'aya sai tashin hankali su ya k'aru,
Aunty Amarya ce ta nisa cikin disashewar murya tace.
"Toh ke Zulaihat ko zakije ki dubo lafiyarshi,
domin tunda kikaga kun kira bai amsaba gskya ba Lfy."
kai Mama ta jinjina alamar gamsuwa da shawararta,
cikin kuka Zulaihat tace.
"Bari inyi salla sai in tafi."

Wunin wannan rana wannan gida sun yishine cikin tashin hankali da k'uncin rayuwa,
fad'in halin da Mama ta shiga ba mai iya misaktashi,
Zahra kuwa tausayin Mama ke sata zubda hawaye time to time.

Ummi kuwa abin nema ya samu,
Credit ta aika Zeenat ta sayo mata na 3k ta lodashi a wayarta,
ta rink'a bin d'angi da mak'ota wanda ya dace da wanda bai daceba tana gaya musu,
kai tsaye take cewa Yusuf yayiwa Zahra fyad'e,
lokaci d'aya mgna ta bazu a dangi da mak'ota,
kafin kace kobo wasu mak'otan sun fara shigowa dan tabbatar da zancen,
nan Hajja inna kuma zata zage tayi musu bayani,
ta kuma kaisu d'akin Mama a cewarta ai sunzo duba Zahra da jikine.

Abun duniya dai ya taru yayiwa Mama da Aunty Amarya yawa,
wuni d'aya sun fita haiyacinsu,
Daddy kuwa yana jin duk abinda ke faruwa to amman ya zaiyi da tsohuwar nan
yasan yana yin mgna zasa kuka tace yafi son yarshi da ita,
zata kuma gayawa Abba in ba sa'a ba suzo rai ya b'aci.

Raihana kuwa tunda gari ya waye take cewa Faisal ya kaita ta dubo Zahra,
amman sai yace mata ai Aryan yace kar ya kaita ko ina,
tayi ta kiran wayar Aunty Amarya kuwa dan jin ya jikin Zahra amman bata amsawa,
time to time in ta faki idon bak'i dake shigowa a kai akai takan tsare Faisal da kuka da magiya dan Allah ya kaita ta dubo Zahra,
Shi kuwa Faisal sai dai ya bata hak'uri dan Aryan ya hanashi kaitan,
ta dai kira Kaka sun gaisa ta gaya mata jikin Zahra da sauk'i.


Tsakanin azahar da la'asar ne Zulaita ta iso gidansu Aryan,
kai tsaye parlour Hajiya kaka ta shiga,
inda ta samu daga ita sai matar kawunsu Aryan,
bayan sun gaisa ne sun jajantawa juna abinda ya faru da Zahra ne Zulaihat tace.
"Dama nazo wurin Yusuf ne,
domin muji ta bakinshi kan abinda Aryan yace."
cikin rashin fahimta Kaka tace.
"Ta bakinshi kuma?
me Aryan d'in yace."
da sauri Mommy ta matso inda Zulaihat take ganin daga tambaya sai hawaye car-car,
cikin firgici Kaka tace.
"Subahanallah Zulaihat make faruwa kuma?."
cikin kuka Zulaihat ta shaidawa Hajiya Kaka abinda Aryan yace da kuma shigar da k'arar da yayi ta k'arishe mgnar da cewa.
"Kuma tunda gari ya waye kiran Yusuf mukeyi amman baya amsawa, shine Mama tace inzo in duba Lfy kuwa."

Allah sarki Hajia Kaka lokaci d'aya ta birkice kunya mai tsanani ta rufeta fad'a takeyi kamar zata ari baki kuka mai k'arfi ya kubce mata,
cikin kuka tace.
"Innalillahi kaito Aryan bakayi mana adalciba,
Aryan yaci amana,
ko dai Aryan ya fara shaye-shayene ban saniba,
Aryan ka kunya tani a wurin wadd'annan bayin Allah."
sai ta kuma koma kan kujera tare da tsiyayar da hawaye masu zafi,
ita kuwa Mommy sai salati takeyi tana kuma kiran Aryan a waya amman bai amsaba,
Zulaihat kuwa zuwa yanzu sai dai hawaye,
ita kuwa Kaka sai kuka takeyi tare da cewa.
"Ashe shiyasa yau tunda gari ya waye Yusuf bai shigoba, maza tashi muje mu dubashi."
A jere suka nufi part d'in Yusuf kai tsaye suka kutsa kai cikin parlour don a zatonsu yana bedroom,
da sauri sukayi gaban 3 str inda yake konce kiran woyarshi da akayine ya nuna musu yana wuri,
da sauri Mommy taje ta kunna wutan parlour,
a take haske ya mamaye wurin,
cikin sauri Zulaihat ta zauna gabanshi ganin yana zaune ya kafa guiwowin hannunshi kan cinyoyinshi yayinda yasa hannu biyu ya tallabe kanshi,
ida nunnan nashi sun kad'a sunyi jazir,
gaba d'aya jijiyoyin kanshi sun taso sunyi rud'u-rud'u,
jijiyar kan hancin shi tamkar zata harbo ta fito sarari,
wani irin rawa jikinshi yakeyi tamkar mazari,
cikin firgita Zulaihat tayi ta kiranshi,
amman ko idonshi bai d'ago ya kalletaba bare yayi mgna,
sai kamo

Please Login or Register in order to submit comment