Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah daga dawowata saiki tarbeni da k'orafi don dai ke kece uwar rakad'i."
dariya tayi tare da k'ara ruggumo Auntyn tace.
"O Oyoyo Auntyna to sannu da hanya."
sai ta kuma saki Auntyn ta k'arasa gun Sulaiman tsalle tayi ta ruggumoshi tare da cewa.
"miss you Hamma Culaiman."
dariya yayi tare da janyeta ya rik'o hannunta suna masu ci gaba da tafiya yace.
"Oh Tinan Aunty wato yau kuma kin tuno yarinta,
Hamma Culaiman ko."
dariya tayi tare da gyad'a kai Jafar ne ya matsosu tare da cewa.
"Lokacin kina k'arama ko sau goma zaki cewa Hamma Yusuf, Hamma Yucuf sai ya mauji bakinki ke kuma bakya fasa fad'ar."
dariya sukayi baki d'ayansu yayinda Fa'iq kuwa yaketa yiwa su Mama tsiya, wai sunje sun goge faso a makka,
ita kuwa Zahra sai tura baki tayi tare da murgud'ashi tace.
"Allah ya isana ai, sai na rama."
da sauri Jafar yace.
"Kan waye zaki raman."
cikin k'arfin guiwa da yak'ini kan jarumtarta tace.
"A kanshi mana."
dariya sukayi kawai dan ita da iya gaskiyarta ta fad'an,
suna isa inda suka ajiye motarsu suka tsaya cikin mamaki ganin Abba yana tsaye jikin motar shi yana kallonsu fuskarshi d'auke da murmushi,
ganin sun iso ya koma cikin motar tare cemusu.
"Sannunku da hanya."
yauwa sukace baki d'aya
sai kuma Aunty Amarya ta d'an rusuna tare da cewa.
"Yaya ina wuni?."
"Lfy lau, kun dawo Lfy?."
Alhamdulillah tace tare da mik'e cikin kunya irin ta surkai tunda shi yayan maigidanta ne,
motar Jafar ta shiga ita da Zahra,
shi kuwa Sulaiman ya shiga ta Abba ya zauna a gaba yayinda Mama ta zauna a baya sai Fa'iq daya shiga gefen Mama yana cewa Anty Amarya dake kiranshi yazo gunta.
"A a ke amaryata jeki sai mun had'e a gida bari inga kalar soyayyar tsoffi."
dariya sukasa sannan ya shiga Abba yaja motar tare da cewa.
"Kaji ja'irin yaro".
Mama kuwa tureshi ta d'anyi tare da cewa.
"Matsamin ni karka matseni."
dariya yayi cikin wasa irin na jika da kaka yace.
"Iye Uncle Sulaiman kalli Ango da amarya da goro suke carabke."
dak'uwa Sulaiman ya mishi tare da cewa.
"Kai Fa'iq kan babarka."
haka dai sukayi ta hira da dariya.

A motarsu Zahra kuwa k'awayenta take shaidawa dawowar su Mama da abokanta yan makarantarsu,
cikin tab'e baki Aunty tace.
"Kai Zahra gskya lamarinki fa da gyara,
aboto tsakanin mace dana miji dai ba abune mai fa'idaba."
Jafar ne ya d'an kalleta tare da cewa.
"Aunty a zamaninku ko? ai yanzu abota tsakanin mace dana miji yafi dad'i."
kai ta jinjina kawai tare da tab'e baki madadin ta sawatar tunda ita da kanta tasan tsarin baiyiba,
amman da yake ita yar ko ohoce sai ta share.

Suna isa gida,
Suka samu gida a cike dan su Mami sun dawo,
ga Sharifa yar Adda Zulaihat ma daga school nan ta biyo, sannan Zeenat ma ta dawo makaranta Ibrahim da Sadik duk sun dawo gida,
ga Goggo Maimuna da Aunty Madina duk sunzo
ai suna isa gida ya kacame,
anata farin ciki da dawowarsu Lfy,
haka aka wuni ranar anata hirar yaushe gamo,
sai dere Goggo Maimuna ta koma Aunty Madina kuwa da Zulaihat da Amira kwana zasuyi.
an baje tsaraba kowa yana zab'ar abinda yayi mishi,
har k'arfe goma na dere suna cike a parlour Mama sai Aunty Amarya da tuni tana turaka,
hira suketayi,
Abba kuwa yana parlour shi zaune yanata tsumayin ganin Mama shiru-shiru bai gantaba har sha d'aya,
ita kuwa Mama so take yaran suyi bacci kafin ta tafi,
tasan yaran Zulaihat da d'an karen wayo da surutu,
jin woyarta na ringing yasata mikewa tare da cewa.
"Sharifa mik'o min woyar nan."
Toh tace tare da mik'o mata,
ganin Abba ne yake kira sai ta amsa da sauri tare da karawa a kunne,
shiru tayi tana jin me yake cewa sai ta kuma kalliya yaran da suketa sabgoginsu dan sai take jin nauyin abinda yace har taji tsoron ko yaran suna ji,
shi kuwa jin tayi shirune yaci gaba da cewa.
"Inafa jiranki kema kanki kinsan ina son samun lokacinki,
ba jikokinki kawai keda muradin zama da keba Maman Yusuf, Abban Yusuf ma yana son ganinki kusa dashi."
Murmushin jin dad'i tayi tare da cewa.
"Uhun ganinan zuwa."
Mik'ewa tayi tare da cewa Zahra.
"Ki kashe tv nan dere yayi, Zeenat keda Sharifa ku shiga nan d'akin Zahra ku konta,
kai kuwa Fa'iq tashi kabi Uncle Ibrahim ku kwana can,
Ke Zulaihat bakiga Amira ba tun d'azu gengyad'i takeyi maza tasheta ku shiga d'akina tare da Zahra,
gadon zai ishe ku ai Goggon Abba."
Kai Zahra ta gyad'a tare da mik'ewa tayi gaba waya na mak'ale a kunnenta,
bayan duk sun watse Aunty Madina ma ta mik'e tare da yin dariya tace.
"Hahaha Maman Yusuf Abban Yusuf yayi kirako."
dukan wasa Mama ta kaiwa k'anwar mijin nata kuma dama yar kawunta ne,
ita kuwa zillewa tayi tare da ficewa tana dariya tayi part d'in rigimemmiyar tsohuwarsu.

Tana shiga parlour Abba hannu ya bud'a mata tare da cewa.
"Sati biyun nanfa kamar shekara biyu na jisu Maman Yusuf."
Murmushi tayi tare da rab'awa gefenshi tana cewa.
"Abban Yusuf,
jiya fa nayi mafarkin Yusuf d'inka na cemin Mama kicewa Abba na yamin aure mana."
dariya yayi tsab'anin yadda ta zata,
sai kuma taji ya shafa fuskarta tare da cewa.
"Allah sarki Yusuf d'in Abbanshi,
kice mishi karya damu Abbanshi na sane dashi ina nan ina ta shirye-shiryen yimishi auren."
Ita kam Maman Yusuf wani irin farin cikine ya rufeta sai hamdala takeyi tabbas tasan Abban Yusuf ya sauk'o daga fushin da yakeyi da d'an nasu,
mik'ewa tayi jin yana jan hanunta,
bedroom suka wuce tare sannan ya rufe k'ofar.

Hmmmm masu karatu ya kuke tunani in dai Abban Yusuf tsoho ya iya soyayya haka ya kuke tunanin kabcen Yusuf zai kasance?.

Washe garima haka gidan ya cika da yan uwa da mak'ota
duk k'annen Abba sun zo,
bayan sallan Azahar sai ga k'awayen Zahra ma su uku sun zo,
parlour Mama ta fara kaisu suka gaidata sannan wurin Aunty daga nan suka fito suka gaida Ummi da Hajja Inna,
sannan suka koma d'akin Zahra dake part d'in Mama,
hira sukayi tayi irin tasu ta k'awayen da k'uriciya da balaga ke tsaburarsu,
har la'asar tayi,
Dija Chiroma ce ta fara mik'ewa tare da cewa,
"La'asarfa tayi tun tuni."
Salima yar Aunty Fadwa ce tace.
"Hahaha ai ni nayi da mutanen saudia."
gyara zama Safiyya ma tayi tare da cewa.
"Nima ina hutu."
Ido Zahra ta zuba musu tare da cewa.
"Uhum kunji dadinku ni dai har yau ban fara wannan fashin sallanba."
da sauri Dija ta koma ta zauna tare da cewa.
"Kai haba dai Zahra har yanzu baki fara yin Al'adaba?."
Cikin alamun tsoro tace.
"Wlhi kuwa ni abin yama fara damuna fa, kinga su Mami da Nana tun suna da shekara 13 suka fara,
amman ni har yau shiru."
Salima ce tace.
"Gsky kam ko mutanen da d'in ma yawanci shekara 14 dai zuwa 15 suke farawa."
cikin sauri Zahra tace.
"Toh bare yanzu da ake cewa muna farawa da wuri, amman ni shekara 16 ace ban faraba."
ta k'arishe maganar cikin d'an karaya,
sai ta kuma kalli Safiyya da ke cewa.
"Ke Zahra wata k'il fa kina cikin irin matan nanne da basa al'ada."
ido ta zaro tare da cewa.
"Na shiga uku kenan fa bazan tab'a haihuwaba ko? tunda sai da al'ada ake gane shigar ciki,
toh ko dai bani da mahaifane a cikina?."
ta k'arishe maganar tana shafa cikinta tare da zurawa Dija ido,
yayinda Salima da Safiyya kuwa suke tayata zaro idon
dariya Dija tayi sannan tace.
"Ke babu komai fa wata k'il sai kin cika sha bakwai zaki fara."
Safiyya ce tace.
"Eh gsky ba mamaki amman dai kije kiga gaining doctor."
cikin gamsuwa da shawarar Safiyya sukace.
"Eh kam gsky hakan yafi."
kai ta jinjina tare da cewa.
"Insha Allah sai bayan bikin Aunty Raihana zanje inga doctor dan haka Adda Zulaihat ma tace min, har tace zama ta rakani ko kuwa ta had'ani da Abban Fa'iq da yake shima doctor ne."
Haka dai sukayi ta tattauna matsalar tata ,
basu ankaraba sukaji kiran sallan magrib,
ido Dija da Zahra suka Zahra tare da mik'ewa a tare suna cewa.
"Subahallahi Zahra kinga mun biye musu bamuyi sallaba."
"Wallahi kuwa kinga shiga nan kiyi al'wala ni kuwa bari inje toilet d'in Mama".
to tace tare da shiga bayan sun fito sunzo suna sallan Salima da Safiyya kuwa suka shishshiga dan kimtsa jikinsu.

Bayan sun idar da sallan Zahra ta shiga kitchen ta kawo musu d'anwaken da tasa Zeenat tayi musu,
tare da yankekken salad da tomato da d'an albasa, sai dafeffen k'wai, da yaji tare da man k'uli,
ajiye musu tayi a tsakiyar d'akin sannan ta juya ta koma parlour firij ta bud'e tare da d'auko musu drink's mai sanyi,
zubewa sukayi a kan carpet sunaci suna hirar yadda bikin birthday Dija da suke shirin yi zai kasance,
suna gama ci ta tattare wurin,
sannan Zahra taje d'akin Mama gefenta ta zauna tare da d'aukan takalma k'afa uku sannan ta d'auki zam-zam da dibino da gabaruwa shima tayi k'ulli uku manya sannan ta kalli Mama dake jan carbi cikin tonk'oshe kai tace.
"Ayyah Mama zan d'auki sallaya d'aya zan k'ara da biyun dana d'auka gun Anty da Ya Sulaiman zan bawa su Safiyya su kaiwa su Mamansu."
kai ta gyad'a mata alamar to.

Haka ta had'a musu kowa takalmi da sallaya sai su zam-zam,
sannan ta rakasu har bakin titi suka shiga taxi da zai kaisu cikin jimeta tare da biya musu kud'in motar,
taxi d'in na barin wurin taga wani taxi d'in ya kuma tsayuwa gabanta,
har ta juya sai ta kuma tsayawa jin muryar Fadil na ce mata.
"Hi Girei."
da sauri ta juyo dan tasan abokanta ne kawai ke kiranta da Girei,
su Fadil kuwa su 4 suka fito tare da cewa.
"rakiya kikayi."
"Kai ta gyad'a alamar eh sannan tace.
"Su Dija chiroma nefa gsky naji haushi dabaku haduba, ko d'azu Salima ke cewa robonta daku tun randa muka gama last page d'inmu."
haka suka jera tana tsakiyarsu sunata hira da dariya yayinda duk inda suka wuce ba'a zatawa Zahra al'khairi
wasu tsoffin da suka wuce yanzune d'ayan yace.
"Kai wannan yarinya sai shiriyar Allah yanzu da deren nan tana yawo a titi tsakiyar matasa har 4 ai duk abinda sukayi mata ita ta jawo."
cikin halin son bin d'an adam da mummunan zato d'ayan yace.
"Toh bakaga ita bata wani tsoron mazaba ka manta tun tana k'arama maza ke tsakurarta,
dama wannan yaron Yusufa kawai take tsoro to shiko ubanshi ya koreshi a gidan ba sai tayi abinda take soba."
haka dai sukayi ta gulmarsu.

Sukuwa Fadil, Hafiz, Ayman, Harus sai bayan isha'i suka tafi.


Washe gari da hantsi Aryan ya kawo Kaka da Raihana,
tare suka shiga har cikin gida domin yanzu Abba ya barshi yana shiga cikin gidan,
a parlour Hajja inna suka yada zongo nan akayi ta hira bayan Mama ta basu jakar tsarabarsu sannan ta mik'awa Raihana laptop d'inta tare da cewa.
"Ga wannan kuma Hammanku yace in kawo miki."
cikin farin ciki ta karb'a tare da cewa.
"Allah sarki Hamma Yusuf ngd Ngd Ngd matuka Allah ya bar zumunci ya k'ara bud'i."
Amin Amin sukace baki d'aya,
Aryan ne ya d'an gyara zama tare da cewa.
"Mama ki k'ara yima Raihana godiya fa wurin Yusuf, dan satin daya gabata sakon kayan d'akinta da ya saya mata duk sun iso,
dan Allah ki kuma yi mishi fad'a yafa rege k'ona kud'i a banza."
cikin sauri Mama tace.
"A a Aryan karka kuma cewa haka shida yar uwarshi ai ba k'onawa a banza bane sannan ai tsakaninku da Yusuf ba godiya."
tura baki Raihana tayi tare da cewa.
"Ato gaya mishi dai kam Mama haka Kakama tayi ta fad'a wai ya dena biyewa shirmena."
"Yoh ai gskya na fad'a ai."
cewar Kaka.
Shi kuwa Yusuf i v ya mik'awa Mama kusan guda 40 yace gashi.
"A bawa Abba da Daddy da Sulaiman na d'aurin aurene in Allah ya kaimu."
amsa tayi tare da cewa.
"Ashe abin yazo, to Allah ya kaimu ya sanya al'khairi."
cikin jin kunya Raihana ta kalli Aunty Amarya tare da cewa.
"Aunty zaku bani aron k'anwata Zahra ko tayi mana makeup d'in biki nida k'awaye. "
cikin sakin fuska tace.
"Keda yar uwarki me zai hana."
murmushi Zahra tayi tare da cewa.
"Wow Aunty Raiha Allah ya kaimu bikinnan sai na miki kolliyar da ban tab'a yiwa kowaba a duniya."
murmushi tayi tare da rik'e hannun Zahra tace.
"Shiyasa nake sonki tawan."
Mami da Nana ce suka had'a baki wurin cewa.
"ai Wlh dama Aunty Raiha kinfi son Zahra a kanmu."
dariya sukayi baki d'aya banda Hajja inna data harari Zahra dake jijjiga k'afadu da k'ijinta tanayiwa su Mami gwalo,
haka dai akayi ta hira saida sukayi azahar suka tafi.


Da yamma duk suna tsakiyar gidan Suleiman ya shigo,
gefen Amira ya zauna tare da cewa.
"Ke tashi zaune ki gyara zamanki,
wai anyama Amira bazan soke sunanki a cikin list d'in masu zuwa aikin hajinnan kuwa ba."
cikin zafi ta mik'e tare da cewa.
"Jakar uwar ubanka dan me zaka sokeni d'an bak'in ciki."
baki ya tab'e tare da cewa.
"You gani nayi kinci wake ina zaki je da k'wajejen cikin nan."
cikin jin kunya tace.
"Toh ai kafin nan zan haihu fa."
dariya sukayi mata baki d'aya,
sannan Sulaiman ya kalli Hajja Inna tare da cewa.
"Yusuf ya bada kud'in kujerun makka takas yace a saka wandanda suka dace,
so ni na zab'i wadanda suke sonshi,
Goggo Maimuna da Goggo Aisha tare da Anty Madina sai Adda Raihana da Amira sai Tatti maman Anty Amarya sannan Raihana sannan malam liman na masallacinmun nan."
baki ta tab'e tare da cewa.
"Allah dai yayi kafin a haifeshi ma da hak'orin makkata ya ganni,
ya biyawa wasu ni na yafe."
habawa su Goggo Maimuna kuwa farin ciki kamar zai kashesu,
Adda Raihana kuwa tun randa Sulaiman ya gaya mata sai tayi ta kuka burinta bai wuce d'an uwanta ya dawo kusa da suba,
tana jin tsanar Garzali a ranta in ta tuna shine sanadin komai.

Haka sukayi ta farin ciki da yamma duk suka koma gidajensu da al'bishir mai dad'i.


Mu lek'a can dubai kuwa

Dubai cikin yankin nahiyar Abu Dhabi jumairah etihad towers,
anan su Yusuf sukayi masauk'i yayinda tun deren da suka isa suketa k'anan tarukan tattaunawa da teams na sauran sasan duniya,
Randa suka cika kwana 7 da zuwa kuwa a ranarne zasuyi zama na musamman da dukkan teams da suka samu damar shiga gasar world polo da za'ayi,
Yayinda Ghantoot racing and polo club suka shirya zaman cikin farfajiyar shi'ar tasu,

Tun misalin goma na safe suka hallara cikin babban hall d'in yayinda ko wanne k'asa suke sanye da kaya mai kalar tutar k'asarsu,
sosai Yusuf da Malam Jabeer sukayi kyau cikin shigar green white green,
sun fito ras tamkar larabawan.
Yayinda Indian, Argentina South Africa Amiraka Pakistan da dai sauran k'asashen duk suke cikin shigar shiri jira kawai suke lokacin farawa yayi su hallara kan kujerunsu da aka tanada na musamman.

Malam Jabeer ne ya kalli Yusuf wanda zufa ke tsatstsafo mishi duk ta inda gashin jikinshi yake,
duk da sanyin A, C dake ratsa wurin amman saida ya jik'e lips inshi ya taune da k'arfi tare dasa hannu ya damk'i cinyar Malam Jabeer dake gefenshi,
cikin tsananin azaba yace.
"Ma... Mala... Malam! marata azaba zai kasheni."
da sauri Malam Jabeer ya roggofo kanshi dai-dai lokacin da yaga yana k'ak'k'ame shi tare da jan wani irin dogon numfashi sai kuma yaga ida nunshi sunyi luuuuu alamar sum......!







*By*
*GARKUWAR FULANI*

[04/01 9:01 PM] My 2nd Mtn: Garkuwar Fulani: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

*Assalamu alaikum, masoya na masoyan littafaina, ina mik'a sak'on gaisuwata a gareku tare dayi muku Al'bishir d'in gani na dawo gareku da sabon littafina mai suna HUKUNCIN ALLAH, wanda na shiga Nazari tunani bincike hangen nesa na zak'ulo matsalolinmu a yau tare da kuma samo Garkuwar da zata tsira damu da yaranmu k'annenmu daga fad'awa halin dana sani,*
*HUKUNCIN ALLAH*
littafine dake tafe da sak'onni masu tarin yawa. *tuna sarwa, tsorotarwa, jan hankali, fadakarwa, tare da zaburarwa da bada k'arfin guiwa da zamu had'u mu yak'i k'alubalen dake addabar al'ummar mutanen wannan k'arni da muke ciki. sannan akwai nishad'antawa tare da ban dariya hakan kuma* kunsan salo nane ban tausayi mai ratsa zuciyar ma abocin imani da tausayi, duk suna cikin wannan littafinawa mai suna *HUKUNCIN ALLAH,* domin samun damar karantashi zaku iya bibiyata a manhajar what's App a number wayata kamar haka 09097853276 kan farashi mai sauk'i yi register da naira d'ari biyu kacal damin samun damar karantashi daga forko har k'arshe littafin *HUKUNCIN ALLAH* ko katin waya na layin MTN wanda za'a turo shi ta wannan number 09097853276 ko tur'a d'ari biyun ta asusuna na 0005388578 JAIZ BANK AISHA ALIYU GARKUWA,
kada ka/ki manta turo min shaidarki na tura kud'in a dai wannan number 09097853276 ina maraba daku masoyana tare da kuma yi muku al'bishir da yin posting a kai a kai kada ka/ki sake a baki labari, sai kunzo.......!!!

Dan Allah banda kira
*HUKUNCIN ALLAH*

*AMFANIN SOYAYYA*
*aure*






*NA*



*25*


ahankali yake takawa har ya karaso cikin Parlour zubewa yayi akan kujera wayan sa ya zaro dak'er yake dannawa saboda yanda idon sa da yake neman rufewa saboda bacin rai Sahal ya shiga kira amma bai dauka ba har wayan ta gama ringing tsaki yayi dan kayan sawa yake son Sahal ya kawo masa saboda dama duk kayan sa yana part din Halima kuma
har boxers dan sa yakani ajikin kwarton ta bazai iya cigaba da amfani da su ba ko part din baya son kallo tunda ya dawo daga tafiya gashi ya nason fita sake kira yayi
Hamrah da wayan yake hannnuta tun kiran farko taki ta dauka saboda tsoron me kiran da yasake kira tayi shahadan d'agawa dan tasan rashin daukan ma wani lifine
"dalla malam kawomin kayan da zansa namamajo kafito ma agida ya gagare k...
"Yamall yana toilet zan..
dif taji an kashe
dai dai lokacin shima Sahal yafito
tana dariya ta fada masa ido ya waro "to ke meya kai ki daga wayan sa.?
Hamra tace karanbanin akuya mana gaida kura
kiranshi Sahal yayi tayi bai dauka ba sai da yaga dama ya d'aga."

"Please ka sanarwa matar ka ba amin haka yazama shine na karshe da zata dagamin waya."
dariya sahal yayi yace
"naji har sakon namamajo wane irin kaya kake so."
"yadi banason red ko green."
Sahal yace "gaskya bani da cooler dinka violet ko black dan duka na Kai ma su Kai ma kaya kala goma cikin kwanaki 4 kagama dasu to nide bazan iyaba idan bazaka fita ka nema ba kasa wanda kazaman suka saka...
yana magana yana dauko masa kayan duk acikin ledansu bai taba sa suba kaman Kala 5 yafitar ya dauka yafita dan ya mek'awa masa
Sahal kallon Mall da yaketa fushi yayi meyasa wai hamrah ta daga masa waya yayi yace "banda kai ma wllh habibita zata iya magancema matsalan ka kanemi fada awajenta tama isa har zuciyar madam basai kaje kana kananun murya awajen tsohuwa ba dan wllh zakasha tijara ".
bai ko kalli inda yake ba ya dauki kayan yayi sama

*BARNO YARWA*

yana zaune a kujera 3siter kanta akan kafatuwan sa sai faman murmurda mata Kai yake wai bai yarda baya kisuwa ba amma yana saki yar zai zubo kuma ya ware dariya take masa yanda ya dage ko gajiya bayayi tace " dan Allah ka bari na tashi yau fa ba nice da kai ba ina tsoron aunty fanta ta shiko ta ganmu a haka wllh tana da kima a idona inason kadin ga boye yanda kake nuna kulawa sosai akaina agabanta abin yayi yawa tana da hakuri ma ....
aiko bata rufe baki ba sai ga Fantan ta shigo da saurinta batayi mamakin yanda ta samesu ba Dan ba bakon abu bane awajenta amma yanda suka ganta kamar a firgice yasa Ayya ta mek'e "tace Aunty Fanta lafiya" ?
kofa take nuna musu da hannu Grema ya mek'e yafita shima cak ya tsaya gani de shi yabar Ayya adaki amma ga wata Ayyan tsaye rik'e da yaran larabawa a tsakiyar parlour tunowa da Ayya tanada yan uwa yasa yayi murmushi cikin harshe larabci yace ku zauna kafin bakuwar tayi magana sai ga Ayya da Fanta sun fito Ayya cak ta tsaya tana kallon ta hawayen da yacika mata idon shiyasa take gani dishi dishi ita ma bakuwar mek'ewa tayi da gudu tayi inda Ayya take cikin wani irin sauri suka rumgumi juna da sauri ta saki Ayya tafita da gudu sai gashi ta shigo rike da wani namiji k'ato ba tambaya Ayya tagani shine namjin dan uwanta duk suka rungumi juna kuka sosai sukayi Mai isarsu suka zube Ayya ce tafara magana cikin harshe larabci dan balefi zaman tada Ruwaida ta meda hankali ta koya ashe mama da gaske takeyi ina da yan uwa meyasa tun da baku neme niba." ?
Namijin ne yayi karfin halin cewa "bamu sani ba sai kwanan na mama surayya take gaya mana da baban mu yarasu kakan nimu ma sun rasu bamu sha wahalan neman kiba ta hanyan tsohon Lawyer ki da baba ya bawa document na dukiyar ki shine yamana jagora ashema d'an sa kike aure ni sunana Abdullah banyi aure ba sai y'ar uwata Zayner ita tayi aure yaranta biyu gasu yanuna yaran nan aka sake sabon gaisuwa atake takira hamrah take gaya mata itama hamrah harda kukanta da alkawarin zata biyo idan ta tashi a adamawa sai data basu waya suka gaisa da hamrah ta harshe turanci sukayi sallam

Ayya Allah Allah take su Kharajina suzo suga yan uwan ta dan suntafi gidan gyaran jiki har Bilkisu k'anwar ta wanda dama ta shiryu nan danan aka shiga cika musu gaban su da abinci
kwanan su 4 suka juya da alkawarin zasu zo bikin su kharajina hamrah de tazo sun hadu tunda tana adamawa Ruwaida cede sai awaya suka gama gaisa dan da tace zata zo malama tayi ta mata nasiya akan ta gayawa mijinta itako da tagaya masa gwara ta fasa sa hadu a bikin idan sunzo


*KADUNA GIDAN ME KWANO*

Ismail agaban Umma Umma yanzu kina nufin in barsu wllh ina bukatar matata."
Umma "tace ai shikenan Yi musu maganan kaga baka san halin hajja ba idan tasan ka damu da jikar ta ta zaka sha wulakanci jiya nima ba irin gorin da bata min ba tana cewa yayata da bani da kamarta ta kasa rikemin y'ata Kai zagi har dana rabawa da y'an uwa ka manta dasu Kawai na kwanaki kad'an kaji yaron Umma bana son su wulakanta min kai ne."

ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace "Umma ba zaki gane bane wllh Umma ina son Aisha inason bata hakuri."
dariya Umma tayi tace "haba me abin basu hakuri idan sunki ga Ameera sai na baka." amira da hajara suka Sa dariya shima Mall murmushi yayi yace "tom amma Umma ai ko ganinta nayi ko ."
"izaman ka anan zata zo gaisheni dan bata shigo ba amma dan Allah kar ka ba damu ka kame kar ka sakar mata kofa
Murmushi yayi yana daukan kofin gabansa

Ruwaida part din ummusulem ta fara shiga ta gaisheta sai na malama Malama tasan da zuwan Mall kuma tasan ita Ruwaida bata sani ba ta kalleta cikin wani riga da siket dukda yamata kyau amma malama tace Yawwa y'ata dama neman ki nake wllh wani dogon riga na sayo miki a wajen hajiya Fatima jiya nake son ki gwada ko zai miki kyau akaro wasu."

cikin murna Ruwaida tace "Yawwa malama muganshi kamar kinsan wllh ba azomin da kayana ba daga asbiti fa muka yiwo nan din hannunta mlm ta kama suka shiga har cikin bedroom dinta tace "shiga bathroom ki dan sake jirje jikinki sai kisa zaifi kyau ko sabbin wayoyin da Abba ya saya mata ta ajiye a kan mirror ta shiga ruwaida tayi kyau cikin rigan me dan karan kyau Ash colour bawani makeup tayi ba powder kawai ta shafa sama masa sai lip glow na oriflame da ta dan shafawa dan malama tana amfani da kayan orilame ne tana fitowa parlour mlm tace "kai Masha Allah sai ina kuma.
zanshiga wajen Abba mugaisa sai na k'arasa wajen Umma."
Mlm tace "Abban ki yafita gidan gona."
"Allah yadawo dashi lafiya amma malama dan Allah ki

Please Login or Register in order to submit comment