Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin yadda yaketa kakarin gonin ban tausayi,
cikin jin tausayinshi tace.
"Sannu ko Aryan."
kai ya gyad'a matare da rik'o hannun Ibrahim cikin kakari da son danne yunk'urin da yakejin yace.
"Uncle Ibrahim zan sha ruwa."
cikin tausayawa Ibrahim ya kalli Aunty Amarya tare da cewa.
"Aunty mik'o ruwa in bashi. da sauri ta juya tare da kowa parlour goran faro dake kan firij ta d'auko kana ta fito da sauri,
mik'awa Ibrahim d'in tayi tare da cewa.
"Bashi yasha kad'an kada ruwan ya mishi yawa."
amsa gorar yayi kana ya tallabo kanshi daya manna a k'irjinshi,
cikin tausayawa ya kalleshi tare bashi ruwan ya kuskure bakinshi sannan ya d'an wonke mishi inda aman ya d'an tatta b'ashi sannan ya d'an bashi ruwan ya d'an sha kad'an kana ya janye bakin gorar,
cikin sanyin jiki yace.
"Sannu ko Aryan."
kai ya ya gyad'a mishi tare da yin heg hegy sannan ya lumshe ido cikin k'arfin halli yace.
"Uncle Ibi k'ara min ruwan mana k'ishi nakeji."
cikin sauri ya mik'o mishi gorar sai ya kuma janyeta jin Aunty Amarya na cewa.
"Kadafa ka k'ara mishi zaiyi amayar dashi kaga ya d'ansha wannan bai amayarba."
ba don ya gamsuba sai don uwace baison musu da ita haka yasa ya tsaida Aryan d'in tare da cewa.
"Kayi hak'uri ko Aryana sai anjima in k'ara maka."
kai kawai ya jinjina,
shi kuwa Ibrahim hannunshi ya kamo tare da cewa.
"Zomu je kemis in saya maka mgn."
kafad'a ya mak'e tare da yin rau-rau da ido yace.
"Uncle ibi naji sauk'ifa,
kuma in munje zasumin allura."
kanshi ya shafa tare da cewa.
"Bazan bari suyi maka allura ba, mgni kawai zasu baka."
kai ya rausayar tare da rik'o yatsarda Ibrahim d'in ke bashi alamar ya rik'e su tafi,
badon yasoba yabi bayanshi kana suka fita,
ita kuwa Aryan sai ido ta rakasu dashi haka nan take jin tausayin yaron da sonshi na ratsa mata jiki da zuciya.

Su kuwa suna fita,
da k'afa suka fara tattaki dan akwai wani asibiti kusa dasu,
suna zuwa k'ofar masallacin,
sai ya janye hannunshi tare da cewa.
"Uncle ibi bari inje insa ruwa a butocin masallaci kaga la'asar ta kusa kafin mu dawo an fara al'wala."
ido kawai Ibrahim ya zuba mishi domin tuni ya janye hannunshi yayi cikin harabar masallacin,
gefen dattawan dake cikin rufar ya d'an ratsa tare da cewa.
"Malam liman la'asar ya kusa ko?."
kai ya jinjina tare da cewa.
"Eh Aryan saura 30 minutes za'a kira salla."
da sauri yace.
"To bari in saka muku ruwa a butocin ko."
cikin binshi da ido sukace ta.
"Saka Aryan Allah bada lada."
Amin yace kana ya wuce ya d'auki butocin yabi d'aya bayan d'aya ya d'ud'd'ura musu ruwan kana yaje ya jerasu inda ake al'walan,
sannan yazo ya wuce ta gefensu tare da cewa.
"Bari muje asibiti kafin lokaci ya cika."
to kawai sukace kana sukaci gaba da mgnar nagartan yaron inda Man liman yake cewa,
ai halin mahaifinshi ya gada.

Shi kuwa Aryan da sauri yaje ya kamo hannun Ibrahim tare da cewa.
"Muje na gama wannan kam."
to yace kana ya rik'o hannunshi da nufin su tsallaka titin,
sunyi taku biyu zuwa sai ya kuma jin ya janye hannunshi tare da cewa.
"Uncle Ibi ga Daddy ya dawo mu koma gida,
Abeeh na ya aikeni gunshi."
bai jirayi mgnar Ibrahim ba da yake tafiya jiki a mace,
kawai sai ya juya yabi bayan motar Daddy da tuni an bud'e mishi gate ya shiga,
da sauri ya k'arasa inda Daddy yayi parking,
shida kanshi ya bud'ewa Daddy marfin motar kana ya matsa gefe alamar ya bashi hanya,
shi kuwa Daddy cikin k'aunar yaron ya fito tare da mik'a mishi hannu,
kamar wani babban mutun haka ya matso ya bawa Daddy hannu sukayi musabaha,
cikin kula Daddy ya rik'o hannunshi da kyau kana ya kalleshi cikin nitsuwa irin ta manyan doctors yace.
"Kai my aboki baka da lfy ne."
cikin kauda mgnar yace.
"Daddy muje parlour ka da sauri kar lokaci ya k'ure zan fad'a maka aiken Abeeh na."
jawo hannunshi Daddy yayi sannan suka nufi cikin gida kai tsaye parlour Daddy na sama suka haura inda suka wuce Aunty Amarya tana tsaye har yanzu a inda suka barta.

Shi kuwa Ibrahim ganin Aryan bai kuma fitowaba sai yabi bayan motar Jafar dayake biye da Daddy,
kusan a tare suka shiga gidan,
shi Ibrahim gefen Aunty Amarya yaje ya zauna yana cewa bari ya jira Aryan d'in.
Shi kuwa Jafar da sauri-sauri ya shige part nashi da nufin yayi wonka dan Yusuf nata kiranshi ya kai mishi Aryan, so shine dalilin dawowarshi.

Su Aryan da Daddy kuwa suna shiga parlour
kan kujera Daddy ya zauna shi kuwa Aryan tsayuwa yayi ta gabanshi suna fuskantar juna,
cikin rumtse ido yace.
"Daddy Abeeh na ya aikeni wurinka."
cikin tsura mishi ido Daddy yace.
"To gaya min aiken ina jinka."
gyara tsayuwarshi yayi tare yin k'asa da kai murya can k'asa yace.
"Daddy Abeeh na yace wai in baka hak'uri ka gafarceshi,
yace min in ce maka bazai iya had'a ido da kaiba domin yana jin kunyarka,
yaci amanar yardar da kayi mishi."
sai ya kuma kalli Daddy da yayi shiru ya tsura mishi ido yana jin tausayin Yusuf da k'aunarshi da kimarshi na k'aruwa a ranshi fiye da Suleiman da yake d'an cikinshi,
shi kuwa Aryan cikin taune lips enshi ya kamo hannun Daddy kana yaci gaba da cewa.
"Daddy ka yafewa Abeeh na, yace min in ce maka wlh shi ba mazinaci bane k'addararshi ce tazo a haka, dan Allah Daddy ka yafe mishi."
Cikin sanyin jiki Daddy ya gyara zama tare da tallabo fuskar Aryan cikin so da k'aunar yaron yace.
"Na yafe mishi kaji ko Aryan na yafewa Abeehnka ni dama banyi fushi dashi ba, shine da kanshi ya gujeni ya datse duk hanyar da zata had'amu shine kawai abinda ya tsani bak'in ciki duk laifin da zaimin kace mishi kada ya sake gujemin."
cikin jin dad'i yace.
"Abeeh na ya gode kuma bazai sakeba, shina yace kunyarka yakeji shiyasa."
kanshi ya shafa tare da mik'a mishi farar leda da take k'ulle da goro,
kana yace.
"Yauwa gashi maza kaiwa Hajja inna,
nima bari inje inyi wonka inyi al'wala kafin a k'ira sallan la'asar."
Amsar goron yayi tare da cewa to kana ya fita da d'an gudunshi.

Yana sauk'owa ya kalli inda Ibrahim ke zaune cikin gudu-gudu yace.
"Uncle ibi bari in kaiwa Hajja inna aikenta inji Daddy."
kai ya gyad'a mishi alamar to.

Shi kuwa yana shiga ya samu Hajja inna na zaune bisa sallaya,
matsota yayi a hankali kana ya mik'a mata ledar sannan yace.
"Gashi inji Daddy."
cikin jin dad'i tasa hannu ta Karb'a tare da cewa.
"Yau kai ngd matuka Allah yayiwa Daddy al'barka da ya saya min goro kaima daka kawo min Allah ya maka al'barka."
cikin jin yar gajeriyar dariyar jin dad'i yace.
"Amin Am....!
sai ya kuma yi shiru tare dasa hannunshi duka biyu ya toshe bakinshi kana ya juya da gudu ya fita bak'in barandar,
tuni aman ya k'ubce mishi wani irin kakari yakeyi da azaban k'arfi yanayi yana rumtse ido,
da sauri Ibrahim ya taso tare da kamoshi,
itama Aunty Amarya cikin sassarfa ta iso inda yake.

Mama kuwa cikin bacci daya fara saceta ta jiyo yunk'urin amanshi yanayi tare da kuka k'asa-k'asa cikin sauri ta fito,
da sassarfa ta isa inda suke,
ganin sai yunk'uri yakeyi tamkar zai amayar da ranshi,
cikin sauri Hajja inna data iso wurin yanzu tasa hannu ta k'arb'eshi daga hannun Ibrahim kana ta zauna dirsham a kan barandar cikin kauda kai tacewa Aunty Amarya,
"kawo ruwa a bashi."
da sauri ta nufi d'akinta dan kawo ruwan,
shi kuwa Ibrahim cikin tsoro yace
"Mama karb'eshi mu tafi asibiti."
itama Mama jiki na rawa ta iso inda suke cikin tsuma tasa hannu ta Karb'eshi daga jikin hajja inna dan gaba d'aya karkarwa takeyi ganin Allah yana ikonshi cikin lokaci d'aya yaro ya birkice.
shi kuwa Aryan ganin Mama ta Karb'eshi cikin kakari da gala baita yayi luuu da kai ya manna kanshi a k'irjinta cikin rawan murya yace.
"Mah Mama Maman Yus Yusuf, Ammi na."
sai ya kuma kalli Jafar da yanzu ya shigo cikin lumshe ido yace.
"Uncle Ja Jafar kaini wurin Abeeh na zai bani ruwa in sha."
cikin tsananin karayan zuciya Jafar ya matsoshi tare da rik'o hannunshi zai mgna kenan kiran Yusuf ya shigo woyarshi,
jiki na rawa ya d'a,
shi kuwa Yusuf cikin tsananin fad'uwan gaba yacewa Jafar.
"Kai Jafar ni gani a bakin masallacin k'ofar gidanmu fito min da Aryan mu tafi."
cikin firgita Jafar ya kalli yadda wuyan Aryan yakeyi murya na rawa yace.
"Hamma Yusuf ka shigo cikin gida Aryan baida Lfy fa sai kaga yadda ya zama."
bai k'arishe mgnarba ya ji an katse kiran,
Ita kuwa Zahra tana cikin baccin tashin hankalin da takeyi taji wayar da Yusuf ya bawa Aryan yayi ta nad'ar duk mgnar da sukeyi,
shi kuwa Aryan da zai fitane ya cusa wayan a k'asan pillownta,
so jin wayar na ringing a k'asan pillow da take konce dashine yasata farkawa,
cikin firgita ta mik'e tare da lalubo wayar,
amsa kiran kawai tayi dan a zatonta wayarta cema,
sabida cikin mgagin bacci take,
amsa kiran tayi tare da karawa a kunne cikin sanyin murya tace.
"Sallamu alaikum."
ina Yusuf kam Allah bai bashi ikon amsa sallamartaba sai cewa yakeyi.
"Ina Aryan ina Aryan ki bashi wayar."
cikin sauri da rawan jiki ta d'iro daga kan gadon kana nufi woje tana mai ce mishi.
"Hamma Yusufy Aryan baya kusa dani fa bari in duboshi ko yana wurin Mama."
cikin fargaba yace.
"Ina kika barmin yaro me ya sameshi me kukeyi da bakima san halin da d'anki yake cikiba."
tana rik'e da woyar ta fito parlour sai kuma tayi woje da sauri jin muryar Auntynta tana cewa.
"Innalillahi wa Inna'ilaihi raji'un Maman Yusuf wuyanshifa baya tsayuwa."
jin haka yasa ta fita da gudu cikin tsananin rawan jiki,
da gudu ta isa inda suke tana zuwa,
ta durk'usa gaban Mama tare dasa hannu ta tallabo kanshi da yayi lagai,
cikin tsananin firgici da tsoro tace.
"Wayyo Allah na wayyo Aryan d'ina wayyo Hamma Yusuf kazo kaga yadda Aryan d'inmu yake."
kasan cewar bata katse kiranba shiyasa Yusuf yaji duk abinda take fad'i,
shiyasa cikin fargaba ya b'alle marfin motar ya fito cikin tsananin fargaba da tsoro ya nufi bakin gate d'in gidan nasu,
yana zuwa bakin mashigar cikin fargaba da tashin hankali ya d'aga kafarshi tare da kusa kai cikin gidan,
daga bakin gate d'in yake jiyo sautin kukan Zahra tanata kiran Aryan.
Cikin zafin nama ya nufi cikin gidan da ya barshi tsawon shekaru goma sha,
Daddy ma dake bathroom gaba d'aya jikinshi rawa yakeyi sauri yakeyi ya fito dan jiyo kukan Zahra.

Ita kuwa Zahra cikin rawan jiki ta karb'eshi daga hannun Mama da tuni hawaye ke bin fuskantar,
domin gaba d'aya Aryan ya juye kamanninshi duk sun sauya ya juye yayi fari tas sai idanunshi da sukayi luu suka lumshe tare da yin yar yana-yana da hazo,
Hajja inna ma tuni tausayin Zahra ya rufeta domin Aryan bashi da sauran hayaci a jikinshi sai hak kak yakeyi.
cikin firgici Zahra ta yunk'ura dashi dai-dai lokacin da Yusuf ya iso gabansu,
sai kuma ta kasa sabida duk jikinta rawa yakeyi,
gashi shi kuwa Aryan tuni ya saki jikinshi yayi nauyi,
komawa tayi dirsham ta jingina da jikin k'ofar parlour Hajja inna sai hannu tasa ta kamo hannun Hamma Yusuf d'inta da yaketa karkarwa tattaro sauran k'arfinta tayi tare da jawoshi ya durgusa gabansu,
cikin tsananin kuka tace.
"Wayyo Allah na wayyo Hamma Yusuf wayyo Aryan na."
Dai-dai lokacin da ya zauna Aryan yayi wani yunk'uri tare da bud'e baki a hankali murya can k'asa baki a bushe yace.
"A.. Ab.. Abeeh, ka.. ce. Am... Amm.. Ammi ta ba.. bar ku ka."
sai ya kuma ya mik'a tare dasa hannu ya shafi fuskar Yusuf da tuni ta jik'e da hawaye
so yake ya karb'e Aryan ya tafi dashi asibiti amman duk gabbanshi sai rawa sukeyi suna sakewa,
shi kuwa Aryan cikin magagin fitar rai ya bud'i baki a hankali yace.
"Abeeh zansha ruwa."
Cikin jin fargaba yasa hannu ya zare goran ruwan dake hannun Aunty Amarya cikin rawan jiki ya manna mishi bakin goran a bakinshi ido ya lumshe tare taune lips enshi kana yafara shan ruwan kurb'a uku yayi ana hud'u sai ruwan ya kasa tafiya sabida jijiyonyin sun had'e rabonshi ya k'are,
sai ji kukeyi jijiyonyin wunshi na dark'afewa,
sai kuma ida nunshi suka tafi tare da k'afewa kana yayi wata yar mik'a dasa hannunshi ya sauk'a kan hannun Zahra dake rik'e da hannun Hamma Yusuf,
sai kanshi ya tafi luuu,
wani irin firgita Yusuf yayi lokacin da yaga rai ya bar gangan jikin Aryan,
wani irin kukane mai tsananin ciwo da k'una ya subuce mishi cikin firgita yasa hannu ya jawo Zahra ya had'e da gawar Aryan ya ruggumesu da k'arfi kana ya saki kuka mai cin rai tare da jingina kanshi da jikin Mamanshi.

Allah sarki rai bak'on duniya Aryan ya tafi kamar bai zoba.

Ita kuwa Zahra cusa kanta tayi cikin k'irjin Hamma Yusuf d'in kana tasa hannu ta mik'e hannunshi dana Aryan gam, sai ta kuma saki alamar ta sume a k'irjinshi.

Jafar kuwa shima kife kai yayi yana kuka mai ban tausayi.
Hakama Ibrahim sai zamewa yayi k'asa dirsham tare da sakin kuka tausayin Yar uwarshi da Hamma Yusuf na ratsashi.

Mama kuwa abu ya taru ya mata yawa sai kawai ta zama mutun mutumi,
ita dai tasan yau ga Yusuf d'inta a gabanta kuma yana kuka ruggume da Aryan da Zahra,
Aunty Amarya kuma duk jikinta rawa yakeyi,
yayinda Hajja innama tausayin jikokinta yasata kuka cur-cur.

Daddy kuwa yana sauk'owa k'asa ganin yadda duk suke kuka ga Yusuf ruggume da Zahra da Aryan sai kawai jikinshi ya kama rawa,
dai-dai lokacin kuma Abba ma ya iso tsakiyar gidan ganin yadda gaba d'aya gidan suke tare a wurin suna kuka ga Yusuf ruggume da Zahra wacce take sume ga kuma gawar Aryan a tsakiyarsu cikin firgici Abba ya matso tare da kallon Hajja inna cikin rawan baki yace.
"Hajja inna meke faruwa."
murya na rawa tace.
"Aryan ne."
sai ta kuma kasa k'arisa mgnar taci gaba da kuka.
shi kuwa Abba cikin wani irin yanayi ya juyo ya Kalli yadda Yusuf ke ruggume da Zahra,
cikin taune lips da sasaarfa Abba ya iso garesu cikin wani irin ya d'ago hannunshi tare da......!




By
*GARKUWAR FULANI*
[29/01 10:11 PM] My 2nd Mtn: *HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 17*

Na
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


Kamo hannun Aryan da yaketa rito, babbar yatsarshi ya dannan kan
jijiyar hannunshi, sai ya kuma mik'ewa cikin wani irin bak'on yanayin da bai tab'a riskar rayuwarshi ba,
tun bayan rasuwar mahaifinshi,
ido ya rumtse da k'arfi kana ya juya ya nufi part nasu,
kai tsaye bathroom ya nufa,
al'wala ya farayi tare da nemo jarumta ya sawa ranshi amman ina abin yaci tura,
yanayi hawaye na bin fuskarshi,
lokacin daya fito kuwa sai abin ya tsananta jiyo sautin kukan Yusuf can k'asa,
zamewa yayi bakin gado ya zauna tare dasa hannu bibbiyu ya tallabe kanshi wani irin kuka mai cike da rauni da tausayawa ne ya kubce mishi,
lallai kam ya tab'a d'and'ana zafin mutuwar mahaifinshi,
ya kuma shiga k'uncin rayuwa lokacin da iftila'i ya fad'awa rayuwar Yusuf domin sune manyan k'una daya tab'a ji a rayuwarshi, sai yau kuma da rasuwar Aryan ta daki zuciyarshi fiye da zaton mutun,
kuka yakeyi sosai cikin sanyin sauti.


A tsakar gidan kuwa cikin rauni da tausayin Zahra Daddy ya iso inda suke zama yayi gefensu kana yasa hannu,
ya kamo hannun Zahra da nufin janyeta daga jikin Hamma Yusuf amman ina domin ba k'aramin rugguma Yusuf yayi musuba,
gashi ya jingine kai a kafad'ar Mama yana wani irin kuka mai cin rai da zuciya,
cikin sanyi da zubda kollah Daddy ya kalleshi tare k'ara matsoshi kana yace.
"Yusuf kayi hak'uri kayi addu'a kaji ko,
sakesu, kaga Zahra a sume take."
shi kuwa Yusuf rumtse ido yayi sai ga wasu zafafan hawaye suna bin kumatunai,
kallon Daddy ya kumayi murya can k'asa yace.
"Daddy wai da gaske Aryan ya rasu, ya tafi ya barmu?."
kai Daddy ya jujjuya kana yace.
"To kawoshi in dubashi."
ganin ya d'an sassauta rik'on da ya musune sai Daddy yasa hannu ya tallabo Zahra kana ya juyo ya kalli Jafar daketa zubda hawaye cikin sanyi yace.
"Jafar d'auki Zahra kaita parlour Hajja inna."
cikin tausaya musu Jafar ya d'auketa yayi parlour kakarsun da ita.
shi kuwa Daddy hannun Ibrahim ya kamo tare da cewa.
"Zo d'auke gawar a jikinshi."
jin haka Yusuf ya k'ara tabbatarwa shike nan Aryan d'inshi ya tafi,
gashi tuni sunanshi ya bar jikinshi,
dole an ambaceshi da kalmar gawa."
shima Ibrahim kuka yake mai cike da tausayi da tsoron Hukuncin Allah kalli k'udurar ubangiji yanzufa Aryan na raye suna hira dashi suna tafiya tare dashi,
gashi one second ya rabashi da rayuwar duniya,
sunkuyowa yayi ya ruggumo gawar kana ya kalli Daddy tare da cewa.
"Ina zan kanshi?."
"Parlour Hajja inna."
Ya bashi amsa a tak'aice kana ya mik'e tare da jawo hannun Yusuf kai tsaye sama suka haura,
har cikin bedroom d'in Daddy bakin k'ofar bathroom Daddy ya tsaya dashi tare da kallonshi cikin d'anne kukanshi dan baya son kukanshi ya kubce dan kukanshi zai tsananta na Yusuf,
cikin kula yace.
"Shiga kayi al'wala kaji an kira salla."
kai ya gyad'a kana ya shiga bathroom d'in.
Shi kuwa Daddy juyawa yayi ya koma jikin durowarshi, robar zam-zam ya d'auko tare da kolban turare kana ya sauk'a k'asa,
inda ya samu Mama da Aunty Amarya suna kuka mai sanyi,
cikin kula ya kalli Mama tare da cewa.
"Kawo mana mazubin ruwa."
cikin sanyi da mutuwar jiki ta mik'e kana ta nufi part nata,
kai tsaye bedroom d'inta ta nufa wani kwarya babba da d'an k'arami ta d'auko.
shi kuwa Daddy Jafar ya kalla tare da cewa.
"Kayi maza kaje ka seyo likkafani ka kawo,
mu shiryashi kafin a k'ira sallah."
har ya juya zai fita sai ya kuma dawo jin Aunty Amarya na cewa.
"Akwai sauran na Yaya Gombo inaga na taho dashi harda ganyen magarya ma bari in kawo."
tana fad'in haka ta juya yayi sashinta,
ba jimawa suka dawo ita da Mama,
dai-dai lokacin kuma Yusuf ya sauk'o,
kusa da Daddy yaje kana suka shiga parlour Hajja inna a tare yayinda Jafar ke binsu a baya,
suna shiga Ibrahim ya kalli Daddy cikin rauni yace.
"Daddy Zahra fa bata farfad'o ba har yanzu."
cikin sanyin sauti yace.
"Eh barta sai an anyiwa gawar sutura tukun."
nad'e carpet d'in parlour suka kana Yusuf ya zauna shida Daddy,
sukayiwa gawar wonka kamar yadda shariya ta koyar damu,
Allah sarki Yusuf yanayi yana zubda kolla yanaji yana gani akayiwa Aryan d'inshi suturar da dukkan musulmi yake samu a k'arshen rayuwarshi,
shida kanshi ya karb'i auduga a hannun Hajja inna ya rink'a yaga kad'an-kad'an yana toshe wasu sashi na jikinta gawar kamar su k'ofofin hanci da kunne,
sabida kal gawar ta k'andare ta bushe,
bayan sun gama mishi komai ne sai aka kontar dashi a
can gefe a k'asa.
kana Daddy matso wurin Zahra cikin 4 minutes yayi mata yan dabarunsu na likitoci sai gata ta farfad'o.

Atishwa tayi ta jerewo har guda uku,
kana tayi hamdala cikin tsoro ta rink'a binsu da ido,
ganin babu Hamma Yusuf da su Mama ne sai ta sauk'e numfashi tare da cewa.
"Daddy ina Aryan mafarki nayifa wai ya rasu har Hamma Yusuf yazo."
cikin tsananin tausayinta ya jujjuya mata kai tare da cewa.
"Jekiyi al'wala kizo kiyi sallan la'asar kinji yanzu za'a shiga salla."
yana fad'in haka ya juya ya fita.
yayinda tuni Yusuf kam ya fita tare da Jafar da Ibrahim.

Ita kuwa Zahra ido ta rumtse da k'arfi tare da Katlin hajja inna dake zaune gefenta cikin tunani da tsoro tace.
"Hajja inna ai ba'a nan nayi bacciba meya kawoni nan?."
sai ta kuma mik'e tsaye tare da cewa.
"Toh ina Aryan?."
cikin kula Hajja inna ta sunkuyar da kai dan
bata son Zahra taga hawayenta murya na rawa tace.
"Kinsan Aryan bazaiji ana kiran salla yana gidaba,
yanzu ya tafi."
kai ta jujjuya cikin rashin gamsuwa kana ta nufi bedroom d'in Kakar tasu al'wala tayi bayan fitone ta nufi part d'in Mama,
tana shiga kuma ta jiyo sautin mgnar Mama da tun d'azu ta shiga wurin Abba da yaketa kuka tamkar mace,
cikin tausayawa Mama take bashi baki domin a iya zamanta dashi yaune karo na hud'u data ganshi yana kuka cur-cur da hawayenshi ranar da mahaifinsu ya rasu,
sai ranar da ya kori Yusuf domin a ranarma yana dukan Yusuf ne still kuma yana kuka,
sai kuma randa akayi shariyar k'arshe da Yusuf yace shine yayiwa Zahra gyad'e nanma yana mgna yana kuka sai yau kuma data riskeshi yana kuka sosai.
cikin sanyi da rawar murya tace.
"Abban Yusuf kukan nan ya isa haka,
wlh ni a zatona kaine zaka bani k'arfin guiwar yadda nima zan k'arfafawa Zahra guiwarta ta ruggumi k'addararta,
sai kuma gashi kaida kanka ka gaza daurewa."
lips enshi ya taune tare rumtse idonshi murya can k'asa cikin rawan murya yace.
"Lallai mutuwar yaron nan ya daki zuciyata,
tun bayan rasuwar Babanmu ban kuma jin mutuwar data raunatani ba sai ta Aryan."
sai ya kuma Kalli Maman Yusuf cikin rawan murya yace.
"Maman Yusuf, kinsan waye Yusuf a gareni duk duniya bani da kamarshi,
ina jin tausayin Yusuf shin har sai yaushe shi kuwa zaiyi farin ciki a rayuwarshi,
tun yana k'araminshi yake fuskantar k'alubalel da nine sanadi,
gashi nasara na bibiyarshi ga kuma tarin k'alubalen rayuwa,
yaro k'arami dashi ya shiga hau ula'i daban-daban,
zaman Yusuf a kurku nan fa fansane ga rayuwarshi,
da Aryan Babba baiyi nacinda aka kai Yusuf gidan yariba da tuni magautanshi sun kasheshi,
sanin bashida kariyar da zai iya bawa Yusuf ne yasashi fallasa k'addarar Yusuf da tazo a gab'ar da ake neman rayuwarshi,
me Yusuf na ya tsare musu,
su barmin rayuwar yaro mana shima yaji sauk'i,
sun gigita duk masoyanshi, wannan yaro Malam Jabeer haukane kad'ai baiba lokacin da suketa farautar rayuwar Yusuf,
sun tasashi a gaba shida Aryan babba ala dole sai sun kashe Yusuf."
ita dai Mama idanu kawai ta zama mishi domin sam bata gane inda maganganunshi suka dosaba ta dai gane mutuwar Aryan ta dakeshi,
kuma tausayin Yusuf shi yake sashi zubda hawaye da surutai,
ta kuwa gane mutuwar Aryan daga Allah ne bata da alak'a da magautan Yusuf.
ganin yadda yaketa kuka yasa ta koma parlour ruwa mai sanyi ta d'auko kana ta dawo inda yake,
cikin tausayawa irin ta mata da miji ta mik'e mishi ruwan
ba musu ya amsa yasha,
a hankali ya rink'a sauk'e ajiyan zuciya kana,
yasa tafin hannunshi cikin kofin ya d'an d'ebo ruwan fuskarshi ya d'an watsawa ruwan sannan ya mik'e ya fita jin an fara tatta ik'ama a masallacin.

Yusuf kuwa tunda sukayiwa Aryan sutura ya wuce cikin masallacin da yafi shakara goma bai shigaba,
Qura'an ya d'auko ya fara karatu dan nemawa zuciyarshi sanyi,
kuma Alhamdulillah yaji sauk'in azabar da zuciyarshi ke mishi.

Daddy kuwa kafin ya fitane ya d'auki ledan goron da ke gefen Hajja inna,
kana ya haura saman kai tsaye cikin bedroom nashi ya wuce,
kan mirrornshi ya nufa hannu yasa ya d'auki ledan sweets guda biyu da aka bashi wurin sauk'an karatun da yaje shekaran jiya,
cikin aljihunshi ya zurasu gaba d'aya,
kana ya fito yana fita a bakin masallacin yayi arba da motar Malam Jabeer,
yana shiga cikin masallacin kuma ya hangeshi yana al'wala.
gaisawa sukayi a tsastsaye kana suka shiga cikin masallacin jin an tada ik'ama.


Abba kuwa sai lokacin ya fito gida.

da sassarfa ya shiga cikin sahu dan kar a kere mishi.


A cikin gida kuwa dama Zahra tunda taji kalmar da Abba yayi ta rasuwan Aryan,
sai ta wuce bedroom d'inta,
sallaya ta shimfid'a kana ta zumbula hijabinta,
ta fuskanci gabas,
da fari tana cikin haiyacinta tayi sallan la'asar
d'in amman bayan ta idar da la'asar d'in sai kawai ta mik'e taci gaba da jero nafilfili tanayi tana zubda hawaye duk sujjadar da zatayi sai tayi ta kuka tana rok'on Allah yasa har yanzu mafarki takeyi.
shiyasa Maman Yusuf bata san abinda ke faruwa ba.

A masallaci kuwa bayan an idar da salla ne Daddy ya gyara zama tare da kallon Malam liman cikin sanyi yace.
"Man liman a tsada mutane akwai d'aurin auren da nakeso a gabatar yanzu."
cikin d'an mmki Liman yace.
"Alhaji Aliyu d'aurin aure kuma,
da yamma-yamma?."
kai Daddy ya jinjina mishi.
ganin kamar Daddy baison binciken da yakeson yid'inne ya sashi gyara zama tare da rik'o abin mgnar cikin gyaran murya yace.
"Jama'a

Please Login or Register in order to submit comment