Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take Abba yace "Tom da izinin wa ta dawo gida".
cikin jin haushi Mama tace "Bangane da izinin wa ta dawo gida ba, ko so kakeyi ta tsaya ya kashemin yar tawa kodan bakai ka haifa min ita ba bakasan zafin nak'uda ba shiyasa".
abinda Mama bata sani ba yau Abba a sama ya shigo saboda shari'ar da yayi yau k'iri-k'iri ga gaskiya akasa ya murdeta dan d'an wani babba ne a kasar nan yayiwa wata yarinya fyade amma daga sama aka turo akace ya kori shari'ar tom da wannan bakin cikin ya dawo gida, toh kuma sai ga Mama tana farfad'a masa maganganu cikin zafin Zuciya dan zamu iya cewa a gurinshi Yusuf ya gado zafin rai, cikin fushi yace.
"Ni kike fadawa wadannan maganganun?".
Mama itama cikin zafi tace "Eh inba haka ba koso kakeyi ace naje na dauko gawar ta". zabura yayi da niyyar kai mata duka da gudu Mama ta tashi hadi dayin kara zata fita da tsautsayi ashe ruwa ya zube akan tile sai kafarta ta zame cikin kid'ima Abba yakai hannu zai tarota amma ina tsautsayi ya riga fata tuni takai k'asa ta gaba ta buga goshi hannunta da takai da nufin ta dogara kuma ta gurde shi a take ya goce kara ta saki had'i da sakin kuka saurin durgusawa Abba yayi danya taimaka mata amma sai tayi saurin janye jikinta bataso ya tab'ata tuni goshinta harya kumbura.



Rigarshi ya saka da sauri ya fita a masallaci ya samo mai gyaran targade saida yayi da gaske Mama ta yadda aka gyara mata gocewar kashin da tayi.



Abba na fita da mai gyaran targad'e Yusuf kuwa daya dauko Zarah daga makaranta suka iso bakin gate d'in da sauri Zahra ta sauka akan machine d'inparking yayi yabi bayanta,
a gajiye ya karasa shiga part d'in nasu, cikin jin wani irin yanayi, ya shiga parlour Mama bakinshi d'auke da sallama,
ganin goshin Mama a kumbure ga dauri a hannunta cikin tashin hankali ya karasa inda take yana.
"Lafiya Mama meya sameki?".
hawayen idonta ta share ganin yadda d'an nata ya shiga tashin hankali a zabure ya mike idonshi harya fara zubda hawaye murya na rawa cikin tsananin zafin zuciya da kuna yace.
"Nasan meya faru basai kin fad'amin ba, kuma wallahi yau sai na rama miki,".
juyawa yayi ya fice a guje jikinshi sai rawa yake kai tsaye part din Hajja Inna ya nufa Hajja Inna dake zaune akan carpet tanajin radio sai gani tayi Yusuf ya shigo yayo kanta gadan-gadan jikinshi sai rawa yake idonshi yayi jajawur da mamaki Hajja Inna ke tambayar Yusuf.
"Lafiya meya faru?" ai bai saurareta ba illah kokarin cire belt da yakeyi, ido ta zuba mishi cikin mamaki, shi kuwa yana gama zaro belt d'in, cikin zafin rai da iya k'arfinshi ya rink'a tsu..................!



*BY*
*GARKUWAR FULANI*

[02/01 1:06 PM] My 2nd Mtn: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣0⃣

*NA*

*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*WANNAN SHAFIN GABA D'AYANSHI NA SAUDAKAR DASHINE GA DIJA CHIROMA ZAHRA DA YUSUF SUNCE A GAYA MIKI SUMA SUNA SONKI KAMAR YADDA KIKE SONKU, KI BAWA YAN TEAM SIR MOLY HARAFI GOMA-GOMA SABIDA YADDA SUKA NUWA SIR MOLY NAMU SO MUSAMMAN MOM SAYYID&NOOR ITA BATA HARUFA NOGAS DON TAFI KOWA SONSHI, HAUWA A USMAN MAI RASHIN SANI MASOYAN SIR MOLY SUNA YI MIKI FATAN ALKHAIRI*

FREE PAGE


```Hukuncin Allah Fans 2 sabida ku ne nayi posting da sanyin safiya dan naga haqurinku Hukuncin Allah fans 1 rakine garesu 😆shiyasama bazanma tura musuba sai dai su tsinceshi a gefe, ohoho su Sakina Yasir har an cillo min harara, kalli Kubura Sani yadda ta zumb'uro bakinta 😜 Amina lawan harda k'ollah to share hawayenki zan turo muku yanzu, sai daifa yaseen ni ba ruwana in Yusuf ya targad'a tsohuwa```



*Ga masu buk'atar sayan littafin hukuncin Allah zaku turo katin MTN na d'ari biyu kacal, ta wannan layin 09097853276, ko kuma ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, tabbatar ka/kin turo shaidar kin biya ta hanyar yin screenshort sannan in saki a group.Dan Allah masu yi min transfer ta layin etisalat kuyi hak'uri ku bari, katin Mtn zaku turo bana etisalat ba. Sai masu kira dan Allah kuyi hak'uri ku dena kira domin bani iya amsa yawan kiran da nake fuskanta, dama Sadik namiji one ya b'atamin layi ya badashi wa fans shiyasa bani da hutu ko yaushe amsa kira still ga kuma wadanda suketa son samun number sai yanzu suka samu dama shiyasa kiraye-kirayen yayi yawa,yafi k'arfin amsawata, gwara kimin mgn ta what's app zamufi fahimtar juna, sai kuma kunyi hak'uri dani especially fans d'ina na facebook kuyi hak'uri dan Allah da rashin ganin amsata, Wlh ni dai haka nan facebook baya min sam bana iya jurar mgn a can, don Allah kuyi hak'uri*


Belt d'in ya tsula mata da iya k'arfinshi,
kamar a mafarki Hajja Inna taji ya fara tsula mata, k'ara jin ya sake shimfid'a mata belt d'in a lafiyar fatarta yasa ta k'wallah ihu had'i da zabura tare da gantsarewa da yin mutsu-mutsu, cikin azaba da ihu da kururuwa tace.
"Wayyo Allah na! namutu Yusufa ya kasheni, waiyihuhuhuhuuu! jama ku kawo taimako."
ihu takeyi sosai dan ji take kamar da reza Yusuf ke tsarte mata jiki, domin kuwa rebonta da duka ya kai 75 years , sai gashi yau Yusuf na nad'a mata na jaki,
zillo tayi tare da dirowa k'asa kan carpet dan jin yana yi mata wani irin gigitaccen duka kai mata belt d'in yake tako ina, dukanta yakeyi yana kuka tare da yin magana cikin d'aga murya yake cewa.
"Ki hana d'anki dukarmin mahaifiyata, wallahi idan bai dena dukan Mama ba wallah! kullum a kanki zan ramawa mahaifiyata, shima yazo yaji irin k'unci da k'unan rai da nakeji duk randa ya daketa, ai ita ba baiwa bace."
sai kuma ya k'ara tsula mata belt d'in burburwa ta fara tare da sake fitsarin da tun dazu take jinsa,
son jin k'arshen tafsirin da akeyi a radio ya hanata tashi taje ta yisa, sai yanzu ta tsulashi tare da cewa.
"Wayyo Allah shike nan ya kasheni, ihuhuhuhuhuuuu wayyyyyyyyo Yusuf na tuba."
haka Yusuf ya rink'a zaneta ciki da woje bai duba girma da tsufanta ba bare kasancewar ta kakarshi ya zage ya dinga tsula mata belt dinnan, kamar Allah ya aikoshi.


Mama kuwa ganin yadda ya fito tasan Tabbas wani abin zai aikata, dan haka ta biyoshi amma kafin ta fitoma yayi nisa, sai shigar shi bangaren Hajja Inna ta gani, da sauri ta da kai zata shiga kenan taji ihun Hajja Inna,
ai daskarewa tayi ganin Yusuf ya zage sai dukan Hajja Inna yake, ganin bazai tsaya ba da gudu taje ta wafce belt din hadi da zabga mishi mari da hannunta mai lafiya,
duk da haka Yusuf bai tsaya ba sai nannad'e hannun rigarshi yayi tare bin Hajja Inna ya yaci gaba da dukan ta da hannu, cikin kid'ima da tsananin tsoro da sauri Mama ta tare gaban shi hadi da sa hannunta duka biyu harda mai ciwon ta rink'a jijjigashi tana cewa.
"Kai.! Yusuf! ka dawo hankalin! kasan me kake aikatawa kuwa ? nashiga uku Yusuf koka fara shaye-shaye ne irinna yaran zamani kwakwalwarka ta tab'u ne? !!!".
duk da haka cikin fushi k'ara nufar Hajja inna yakeyi da nufin zaici gaba da dukan, ganin haka cikin d'aga murya Mama tace.
"Yusuf wallahi in ka kuskura ka k'ara tab'ata zan jamaka Allah ya isa!."
yana jin haka sai ya fara yin baya-baya ya koma gaban Mama sai kuma ya rushe da kuka had'i da durkushewa akan kafafuwan sa,
Mama ma kuka ta saka.

Hajja Inna kuwa a gurin ta zube tana makyarkyata tuni zazzabi ya rufeta jikinta duk ya kumbura saboda ba karamin duka Yusuf yayi mata ba,
kuma gashi ya hadu da tsufa.
A part d'in su Zahra kuwa jin Ihunta shiya fito da Aunty Amarya da Ummi daga nasu bangaren, a guje suka shiga b'angaren surkar tasu, lokacin kuma yayi dai-dai da dawowar Abba daga raka mai gyaran targade shima a guje yayi bangaren mahaifiyar tashi jin ihunta da yakeji,
Zahra kuma dake biye da bayan Antynta ganin yadda Hamma Yusuf d'insu ke jibgaar kakar tasu sai ta koma gefe ta tsaya tare da fashewa da dariyar mugunta, dariya takeyi sosai harda rik'e cikinta, cikin tsananin dariya da jindad'i tace.
"Allah shi k'ara hegiya Hajja Inna a dakaki dai, ke ba kullum kin iya kai gulmataba, in kinga ana dukana har dariya kikeyi kina cewa a zaneni da kyau ko? to kema yau zagaye ya isa kanki."
sai ta kuma kalli yadda tsohuwar keyin burburwa da ihu da kururuwa tana gaggantsarewa, sai ta kuma kecewa da dariya harda buga tsalle, tana.
"Yauwa Hamma Yusuf zaneta dai sai itama tayi fitsari a wondo."
lokacin kuma yayi dai-dai kwace belt din da Mama tayi a gurin Yusuf da marinshi amma bai tsaya ba yaci gaba da dukanta da hannu mutuwar tsaye Abba yayi sai jikinshi da yaketa b'ari kamar mazari har zuwa lokacin da Mama ta tare Yusuf, abin yake gani kamar a mafarki wai,
Yusuf ne yayiwa mahaifiyar shi haka.
Cikin tsananin fushi da tafasan zuciya yayi kukan kura tare da sakin tsawa mai firgitarwa,
sai lokacin hankalin Mama dasu Aunty Amarya yayi kanshi dan basu san yazo gurin ba, cikin firgici da tsoro sukayi baya dan sunsan tsauri da zafin zuciya irinna Abba tabbas yau zai iya illata Yusuf koya kasheshi dan ba karamin tattalin lafiyar mahaifiyarshi yake yiba.



Yusuf dake durkushe kan kafafun sa kanshi a k'asa yanata ambaliyar kuka bai d'ago kanshi ba tuni ya farajin duka tako ina dan belt din da Mama ta k'wace ita Abba ya dauka ya fara dukan shi kuma da gurin karfen duka yake kai mishi tako ina yana had'a mishi da gula da k'afa dukan shi yakeyi amma Abba bayajin dukan da yake mishi ya wadatar dan haka yasa hannu ya shak'o wuyanshi tare da fara tattakashi,
Yusuf kuwa sarkin zuciya daman yau zuciyar shi ta gama hawa baya ji baya gani baya tsoro da shakkar komai yau ya yadda ya dauki duk wani hukunci daga mahaifin nashi dan ya gaji dacin kashin da yake yiwa mahaifiyar shi,
Ita kuwa Zahra cikin tsananin firgita ta saki ihu ganin irin dukan da Abba kewa Hamma Yusuf d'in nata, kuka takeyi tare da rik'o hannun Antyn ta tana janta zuwa gun da Yusuf din ke durk'ushe cikin kuka tace.
"Wayyo! Anty na Abba zai kashe Hamma Yusuf,
Anty, Ummee, ku hana Abba dukan Hamma."
sai ta kuma sakin ihu, ganin ta firgita yasa Antyn ta jawota ta rugumeta tare da sakin
ihu,
ihun su Aunty Amarya sukeyi ganin tuni jikin Yusuf ya farfashe yanata fidda jini amma hakan bai saka Yusuf yayi kokarin guduwa ba kuma hakan bai saka Abba ya tsaya da dukan shiba Mama ce tayi kukan kura had'i da tare gaban Abba cikin tsanani firgita da kuka tace. "Kasheshi kakeso kayi ne?
zaka kasheshi ne? ka kasheni ni dan dalilina yasa yayi haka, sau nawa nake fad'a maka ka guji randa Yusuf zaizo daukar mataki akan dukan da kakemin, amma kayi biris, shekara nawa na dauka ina shan duka daga gurin ka yanzu karfin d'ana ya kawo yanajin dai-dai yake da duk wanda ya dakar mishi mahaifiya!!".
tunkudeta Abba yayi had'i da jifanta da wani mugun kallo cikin haki yace.
"Ashe kece kika saka yazo ya illatamin mahaifiya ta? toh ki fad'awa d'an iskan d'an naki yayi maza-maza ya bar gidannan tun kan fushina ya sauka a kanshi ya tattara ya nasa ya nasa yabar min gida kuma duk randa ya yadda yazo gidana ko yaje gidan wani daga cikin k'annena naji labari kona gani ranar a bakin auren ki, kuma ko gawata ban yadda yazo kanta ba inhar yazo ban yafe masa ba".
cikin matsanaicin kuka Mama tace.
"Wallahi tun yanzu zamu bar maka gidan dani dashi, sai dai mubar maka gidan naka dukan mu amma ba zaka kori d'ana ba alhalin akan gaskiyar sa yake."
sai zuwa lokacin Yusuf yayi magana da wata irin murya ta tsantsar b'acin rai da k'una yace.
"A a Mama ba zamu tafi tare ba zanbar mishi gidanshi saboda dama kullum cikin bacin rai da bak'in ciki nake a zamana a gidannan saboda abinda akeyi miki, amma wallahi!!! ki sanar mishi duk randa ya k'ara dukan ki zan dawo na rama miki akan mahaifiyar shi!".
saroro Abba ya bishi da kallo haka ma Mama dasu aunty Amarya ba karamin mamaki da tsoro furucin Yusuf ya basu ba yadda yayi maganar da kwarin gwiwar shi babu wani tsoro ko danasani.



Hajja Inna data sandare ta sume shiya dawo da Abba hankalin sa yayi kanta yana jijjigata,
Allah sarki Maman ce ta tafi da gudu ta debo ruwa ta shafa mata a sannu numfashin ta ya dawo, Daddy da Aunty Amarya ta kira shine ya shigo a guje nan ya fara bawa Hajja Inna taimakon gaggawa a sannu numfashinta ya dai-daita bacci ya kwasheta.



Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa.
"Toh yanzu ina Yusuf d'in?" Mama ce ta share hawayen daya zubo mata tace.
"Ya koreshi".
Cikin takaici yace.
"Haba-haba Yaya in rai ya b'aci ai hankali ke nemo shi ba'a yanke hukunci cikin fushi bai kamata ka kori Yusuf a wannan shekarun nasa ba ai yayi kankanta da yawa, yanzu kasan ina zai shiga? kasan wani hali zai fad'a? kasan irin rayuwar da zayyi? kasan irin matsalar da hakan zai iya jawowa nan gaba!!!? masalaha ya kamata a nema ba aiki da zafin raiba".
wani banzan kallo Abba yayiwa Daddy had'i da cewa "K'ank'anta! K'ank'anta fa kace!! inhar shid'in karamine mai zai saka yayiwa mahaifiyar mu irin wannan dukan, in tafiya tayi tafiya wataran ni zaice zai daka ai kanaga yaro ya zama dan daba d'an ta adda kace in barshi a cikinmu".
cikin jin takaici Daddy yace. "Toh shikenan nizan nemi Yusuf d'in ni nasan har abadan bazai dakeni ba yanzu zan nemoshi muyi magana".
a zabure Abba yace.
"Kul!!! kada ka sake inhar kayi gangancin aikata hakan ina mai tabbatar maka zaka hadu da fushina mai tsanani, wallahi matuk'ar ka nemoshi bani ba kai har abadan".
nan Abba ya tashi ya fice daga dakin cikin fushi, gaba d'ayansu da ido suka bishi Mama kuwa fashewa tayi da wani irin kuka mai tsuma zuciya,
a sannu Daddy ya dinga bata baki da ban hakuri yana nuna mata cewar insha Allah zai samu ya shawo kan Yaya harya yarda Yusuf din ya dawo gida,
anan yake tambayar ta mene sababin faruwar abin tiryan-tiryan ta fara bashi labari tun daga farko har karshe sosai yayi mamaki da al'ajabi a shekaru da ilimin da dottaku yayansa bai zaci zai iya dukan iyalin shiba ashe ba'a iya zafin zuciya ya tsaya ba harda duka hakan kuwa sam bai kamaci babban mutum mai shekaru irinsa ba , bai kamaci dukkan namiji mai cikar nagartaba. (kalubale a gareku iyaye maza kubar ganin kuna ware kwanji ku jibgi matan ku son ranku tom a sannu ranar biya zatazo dan da zarar yaranta sun tasa burinsu su kwaci mahaifiyar su su rama mata dukan da ake mata) kuma abin al'ajabi da mamaki duk wannan dukan da Abba ke yiwa Mama yan gidan babu wanda ya sani daga Zulaihat sai Yusuf kadai suka sani dan tana b'oye sirrinta suma su Yusuf bata tab'a ajiyesu ta gaya musuba gudun kar tasa musu tsanar mahaifinsu, sai Anty Amarya da Ummee wanda suna fahimtar dukan da Abba ke mata, musamman Anty Amarya da Yusuf ke koka mata matsalar.



Shi kuwa Yusuf yana fita d'akinshi yaje duk da jini na zuba a jikin shi hakan bai dameshi ba abubuwan da suke da amfani a rayuwarsa ta duniya da lahirarsa kama daga, Qur'an d'inshi takardun makarantarsa dana aikin Pollonsu da dai sauransu ya tattara a karamar jaka sannan ya fito daga d'akin,
part d'in Mama ya nufa cikin jan k'afa a parlour ya tadda ita, tana kuka kamar ranta zai fita, Anty Amarya da Ummee sun tasata gaba suma kukan suke tare da lallashinta,
gabanta yaje ya durk'usa tare da d'ora kanshi bisa cinyarta, cikin rawan murya yace.
"Ki gafarceni Mama ki yafe min ki jik'aina kisamin albarka, ki dena zubda hawayenki a kaina."
cikin kuka tace.
"In banyi kukaba Yusuf me zanyi? yanzu ina kasan zaka shiga a fad'in duniyar nan tunda ya hanaka zuwa gun yan uwanshi, nima kuma yan uwanshin sune yan uwa, yau da ace ba zuriyarmu d'aya bane da Abbanku da nasan yan uwana zasu rik'emin kai gashi duk family shine babba babu wanda zai tonk'orashi, Yusuf me zanyi in banyi kukaba ina tsoron lalacewar tarbiyarka."
kai ya kuma kontarwa bisa cinyarta tare da rik'e tafin hannunta Yance.
"Mama Addu'a zaki min ba kukaba Mama nayi miki Al'k'awari zan zama d'a nagari zan kasan ce miki Al'waladul saliha insha Allah bazaki kunyata ba akan tarbiyar da kika bani, Mama duniya da fad'i zan tafi kuma duk inda nake muna tare."

Murya na rawa ta dafa tsakiyar kanshi tare da cewa.

"Allah yamaka Al'barka ya shirya min kai ya tsaremin gabanka da bayanka ya Allah ya tsare min imaninka da gabb'an ka daga aikata aikin ashsha Allah ya baka sa'a ya huci zuciyar haifihaifinka in samu ka dawo garemu."

"Amin Amin Ameeeeeeeeen ya rabbil izzati Ngd matuka Mama. "
yace tare da mik'ewa gaban Ummee yaje ya nemi gafararta sannan ya dawo gaban Anty Amarya da take kuka kamar ranta zai fita ta kasa magana sai jujjuya mishi kai takeyi kuka ta saki da k'arfi jin abinda yake fad'i mata.
"Dan Allah! Dan Allah!! Dan Allah!!! Anty ki kula da Zahra, Anty ki kula da amanar da Allah ya dank'a miki a matsayinki na mahaifiya Anty ki rufa mana asiri kar sakacin ki akan Zahra ya jazawa Familynmu zubewar mutunci da k'ask'anci, dan Allah Ummee, Anty, Mama ku kularmin da tarbiyar k'annena wallahi ina jin tsoron kar rayuwarsu ta cutu ina fargaba akan k'annena."
yana kaiwa nan ya fice da sauri yana mai zubda hawaye,

ita kuwa Anty Amarya da sauri tabi bayanshi tana kuka tare da cewa.
"Dan Allah Yusuf ka tafi gidanmu karkaje wani wuri kaje gidanmu wallahi nasan Mahaifiyata da yan uwana zasu rir'eka iya rai da mutuwa."

Yana jinta amman sai ya fice daga gidan da saurinshi,
ita kuwa komawa tayi part d'in Mama sukayi ta kuka.

Tafiya yayi mai nisa har ya fice daga yankin Girei , da k'afa ya shigo har cikin Jimeta.
Kai tsaye bayan P, Z ya nufa dai-dai k'ofar gidansu Aryan jiri ya fara d'ibanshi saboda jinin daya zubar sai kuma ya tafi luuuuuuu...............



*BY*
*GARKUWAR FULANI*
[02/01 1:06 PM] My 2nd Mtn: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣2⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*Ga masu buk'atar biyan kud'in karanta littafin k'ofa a bud'e take, turo katin MTN na 200 kacal ta wannan number 09097853276 ko kuma turo 200 ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, kadafa ku manta free page ne kuyi k'ok'ari ku biya domin free page d'in sun kusa k'arewa*



Mik'ewa Abba yayi had'i da yi mata wani irin mugun kallo tare da jan dogon tsaki cikin kaushin murya da nuna isarsa a matsayinshi na shine baba a kansu baki d'aya cikin tsawa da tsuke fuska yace.
"Idan harku! bakusan ciwo da darajar mahaifiyar kuba tom ni nasani, idan ku baku da tausayi da jink'an mahaifiyarmu toni, bazan iya jure koda cizon cinnakane a kanta bare dukan Yusuf, wanda k'arfi yake k'arawa da girma, ta yiwu wata ran in dawo in samu ya kashe min uwa, tunda yana da zuciyar da zata iya bashi shawarar dakar min ita,
kuma wallahi Allah kenan ku sani duk wanda yaci gaba da yimin maganar Yusuf tamkar ya nemi mu raba hanya ne dan akan Hajja Inna zan iya sallama kowa! zan iya raba zumunci da kowa! so daga yau duk wanda ya kuma min maganar Yusuf Hmmmm!".
sai ya k'arashe maganar a zafafe hadi da sar k'afe yatsun hannunshi ya tonk'orasu saida suka bada sautin k'aras-kararas, sannan ya ficewa a fusace.
Shiru sukayi kowa da abinda yake tattaunawa a zuciyar shi yayinda Goggo Madina autarsu Abba taketa kuka, dan tana matuk'ar jin tausayin raba uwa da d'a da Abba yayi, cikin kuka tace.
"Inba mutuwa ba wake raba tsakanin uwa da d'anta, meyasa Abba yake son zama azzalumin shugaba akan iyalansa, dan Allah Yaya Aliyu kayi wani abu a kai."
ta k'arishe maganar tana kallon Daddy,
Goggo Aisha kuwa mik'ewa tayi tare da cewa.
"Ni bazan kuma cewa komai ba, dan inna nace zanyi mgna abin bazaiyi dad'iba, shi Abba mu kanmu gani yake kamar bama son uwarmu, bai saniba mun fishi sanin zafin haihuwa da darajar uwa da wahalarta a kan d'anta, shiyasa muke gudun karya raba Yusuf da uwarsa, Amman tunda yak'i to shiyasa sani, kuma Wlh Allah duk abinda Yusuf ya zama koya aikata to korarsa da Abba yayi shine sanadi! kuma shike da laifi."
tana fad'in haka ta juya ta fice, Goggo Maimuna kuma, Hajja inna ta fuskanta wacce taketa kumbure-kumbure cikin sanyin murya tace.
"Dan Allah Hajja Inna kisa baki Abba ya janye k'udirinsa".
ido ta zaro tare dayin zuru-zuru dasu tace.
"Tab! wa d'in!? nida Yusuf a gida d'aya, ai wallahi iya dawowa zan bar gidannan, yaseen nama lura so kuke ya kasheni, yaronda in ya juye kamar sojan zaki yake zama, duka nafa yayi tayi kanar ya samu abaran jaka bugun gardifa yami".
jin haka yasa duk suka mik'e suka fita sai Anty Madina da Goggo Fatima su suka zauna wai dan shawo kanta, amman ina sunyi-sunyi tsohuwarnan tak'i k'arshema kuka tasa musu.



Mama kuwa dake zaune kuka ya zame mata sana'a bata da aikin yi lokuta da dama sai ta zauna tayi ta kuka,
yanzuma zaune take tana sharar hawayen dake sinti a fuskarta tare da sauk'e ajiyan zuciya, a hankali ta juyo ta kalli wayarta da taji tana ringing cikin sanyin jiki ta dauko wayar,
ganin mai kiranta tuni annuri ya game fuskarta jikinta har rawa yake ta d'auka ta saka a kunne cikin tsananin bege da kewarsa tace.
"Hello Yusuf kaine? Yusuf kana ina? kana lafiya dai kam ko Baba na?".
murmushi yayi mai sauti, yace.
"M..!". wuff taji an wafce wayar had'i da dokata da k'asa lokaci d'aya ta tarwatse a zabure ta juyo Abba ta gani yanata huci tare da murtuk'e fuska cikin mada umurni da zancen kaifi d'aya yace.
"Wannan shine gargad'i na k'arshe da zanyi miki nace babu ke babu Yusuf idan kunne yaji toh...............". sai kuma ya

Please Login or Register in order to submit comment