Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nigeria. Maman Yusuf tayi fushi dani,
.Abba na yace baya son sake ganina,
mutanen k'asata kowa da Irin kallon da fahimtar yake min,
wasu na tsine min wasu na tsinewa Aryan d'ina, duk da basu san dalilinshi ba,
wasu na farin ciki da abinda ya faru dani,
dole inyi nesa da Nigeria."
shiru sukayi baki d'ayansu ganin wani kekkyawan dottijo tamkar balarabe ya tsaya gefensu cikin sanyi yace.
"Kaje Yusufa, in sha Allah kana tare da nasara,
zakayi dariya wata rana kamar baka tab'a zubda kollaba,
duk da kana da sauran kuka to amman
ka sani Allah yakan jarabci muminai salihin bayinshi ne domin ganin k'arfin imaninsu,
tafi maza jeka, zaka dawo Nigeria a lokacinda duniya duka zatayi al'fahari da kai."
gaba d'aya jikinsu sai yayi sanyi shi kuwa Yusuf ido ya zuwa tsohon domin tabbas ya sanshi a mafatkanshi,
domin shine tsohon daya kwatanta mishi inda za'a dauko mishi wani mgni yace in an kawo yasha to zai rabu da ciwon mararshi,
kuma tunda Affan yaje ya kowo mishi yasha bai kuma jin ciwonba,
ganin Yusuf ya tsaya nazari yasa tsohon sa hannunshi kan kafad'un Yusuf,
wani irin yarr yaji tsikar jikinshi nayi,
sai ya kuma ji k'arfin guiwa ya juyo tare da yiwa su Affan sallama ya juya ya tafi.

Su Affan basu bar wurinba saida suka ga jirginsu Yusuf ya tashi.

Aryan k'ara mi kuwa tunda tsohonnan ya dafa kanshi yayi ta mishi addu'o'i yana cire hannunshi yaro yayi bacci.


Bayan kwana biyu Mama ta kira Aryan take tambayarshi yaushene kam za'a saki Yusuf tunda ya cika shera tun shekaran jiya,
nan Aryan ya shaida mata ai an bud'eshi kuma tunda aka bud'eshi babu wanda ya kuma ganinshi,
tana katse woyar sai tayi murmushi tare da cewa.
"Dan halak kenan ka biyani Yusuf,
Allah ya baka sa'a a duk inda kake,
dan ni kaina ina son ka bar k'asarnan har sai komai ya lafa,
dan shi hijira halal ne."


*****************************

Rayuwa ta tafi lokaci ya juya.
dama baushe yace watan d'aya watan magana watan biyu kuwa watan zagara gari,
tuni mgnar Yusuf tayi tashenta ta kau,
sai kuma tashen mgnar fad'uwar da Team Jahan tayi a world polo,
itama tayi yayinta.

Affan yana yawan zuwa duba Aryan k'arami daga hakane soyayya mai k'arfi ta shiga tsakaninshi da Mami yayar Zahra,
Nana kuwa Aryan Babba ya nuna nacinsa amman Daddy yace ko bayan ranshi bai yarda a bawa Aryan auren yarshiba.
Ana haka kuma
sai ga Sultan da yazowa Mama jajen abinda ya faru da kuma niyar solle Aryan bisa butulcin da yawa Yusuf,
ya had'u da Nana nanfa suma suka fara soyewa,
mgna har taje ga manya,
har an shirya komai na biki.

Bada jimawaba akayi binkin Mami da Affan Nana da Sultan,
yayinda tuni Zeenat ma ta zama yan mata, har ta tsaida mijin aure,
k'awayen Zahra duk sunyi aure, sai Dija da taci gaba da karatu,
ita kuwa Zahra babu ma shinshini sai tarin k'alu balen rayuwa.

Aryan k'arami ya girma sosai yanzu,
ya canza kamanni ya zama tamkar mahaifinshi da ka ganshi kaga mahaifinshi,
in da mai son gane waye mahaifinshi ya shirya yaje Girei ya ganshi domin Aryan lake farther ne,
komanshi irin na mahaifinshi ne,


Yusuf kuwa tuni Argentina suka k'arb'eshi,
a team na Ellistiner johor polo team d'insu da yafi tashe da sanuwa,
cikin k'ank'anin lokaci nasara mai tarin yawa ta rink'a riskar rayuwar Yusuf yayinda ko wanne teams da dama nak'asashe keta kawo mishi takardar gayyata,
so sukuwa Argentina sun kasa sun tsare,
ana bashi farashin gayyata sai su ninka mishi,
lokaci d'aya ya meda gurbin asarar da yayi nasa k'udinshi a neman shiga gasar world Polo na 2015 inda suka tatikeshi bayan nan kuma iftila'i yayi ta biyoshi.
Duniya ta d'auka ta amsa duk gasar da ya shiga sai yayi nasara,
yayinda ko wanne team suke harinshi,
ya zama abin alfaharin duniyar polo,
inda yan Nigeria suke gani k'iri-k'iri d'an k'asarsu yafi k'arfinsu,
team jahan kuwa tuni ta mace,
ko a nan cikin gida Nigeria ba'a wani sata a sahun manyan teams,
sai dai in an bud'e shafin baya ace da shine team da yafi ko wanne,
shaharar Yusuf tasa babu wanda zaice ga taka maimain inda yakeda zama,
tunda ko wacce k'asa tana damawa dashi,
hotunanshi kuwa duniyar yanar gizo-gizo su kad'ai ke kashe zuciyar magautanshi,
to k'asarma da kanta bata samu damar ganinshi ba.
wannan kenan


Raihana kuwa sai yanzu Allah ya bata aihuwa dan har su Mami ma sun rigata haihuwa.

Aryan ya girma tuni yayi nisa a karatunshi,
kasancewarshi yaro mai kaifin basira da hazak'a yasa tako wanne sashi a first class yake fita,

Aryan Babba kuwa dole ganin an aurer da Mami ya hak'ura ya k'arb'i tayin da Kawunshi ya mishi ya auri Rafi'a.

Yau Jumma'a kamar ko yaushe ana yin assalatu,
Zahra ta tashi Aryan kasan cewar ya saba ba gardama ya tashi wonka ta fara yi mishi da burosh sannan yayi alwala sannan ya fito,
mai ta shafa mishi tare da d'auko mishi,
farar jallabiya ta zura mishi tare da fesa mishi turarenshi,
sannan ta d'auko yar hularshi ta saka mishi,
cikin nitsuwa ya juya yayi hanyar fita tana binshi a baya,
a bakin k'ofar parlour ya tsaya,
ita kuma ta bud'e mishi k'ofa tare da cewa.
"Yauwa yi sauri kaga gacan Daddy ma yanzu zai fita zuwa masallacin."
Kai ya gyad'a mata tare da cewa.
"Toh Ammi kije kema kiyi salla karki manta kiyi min addu'a in samu nasara a gasar qura'an da zamuyi next week."
kai ta jinjina mishi tare da cewa.
"In sha Allah zakayi nasara,
ai nasara a gasa gadon jininka ne in dai ka cika jikinshi to bazakayi gasa ka fad'iba in sha Allah."
cikin jin dad'i ya fita tare da cewa toh.

Ita kuwa cikin lumshe ido ta koma bedroom d'in Mama tayi shirin sallanta,
bayan ta idar tayi azkar,
ta mik'e ta shiga kitchen domin shirya mishi breakfast enshi dan yanzu kab gidan shine yaro.

Shi kuwa Aryan tare suka fita da Daddy yayinda Abba ke binsu a baya,
yana kallon dukkan motsin yaron, da yadda yake abubuwanshi yana tuna mishi k'uruciyar waninshi,
bayan an idar da salla nayi matuk'ar mmaki ganin nitsuwa irinta Aryan tamkar babban mutun azkar yakeyi cikin zazzak'ar muryarshi irin ta mahaifinshi,
sai kusan k'arfe bakwai su Abba da Daddy suke tafiya gida yayinda shima Aryan yake biye dasu a baya.

A parlour Mama ya samesu gaban Mama yaje tare da zama gefenta cikin nitsuwa yace.
"Maman Yusuf ina kwana."
cikin jin dad'i da tsananin k'aunar yaron tace.
"Lfya lau Aryan, maza matso ka karya ko."
to yace tare da zama ya tonk'oshe k'afafunshi yana fuskantarta,
yayinda ita kuwa take had'a mishi tea,
tana gama had'a mishi ya karb'a tare da yin bisimillah ya fara sha tare da cin soyayyan doyan,
cikin nitsuwa Zahra ta fito da jakarshi da takalminshi da uniform nashi a hannu gefenshi ta zauna cikin kula ta jawo k'arfarshi dake kama data mahaifinsh hatta faratunshi,
safa ta fara samishi tare da cewa.
"Maza kayi sauri Babana kada a tareka letting kasan bana son a zane min kai."
kai ya gyad'a mata alamar to,
ita kuwa ci gaba tayi da kanshi yayinda Mama ta zuba musu ido tana mai jin tausayinsu,
saida ya gama karyawa sannan ta kimtsashi cikin uniform ensu mai blue and white collar,
kasan cewar akwai irin d'an sanyin forkon damuna yasa ta samishi suwaita a sama,
lunch box nashi ta mik'a mishi tare da cewa.
"Muje in kaika makaranta."
fuska ya d'an kwabe cikin yin rau-rau da ido murya can k'asa yace.
"Ammi sai yaushe Uncle Jafar zai dawone?."
Kai ta kawar dan tasan abinda zaice kowa babanshi ke kanshi shi kuma tunda uncle Jafar ya tafi bautan k'asa ita ke kanshi sai wasu lokutan Daddy ke kanshi,
muryashice ta katse mishi tunani.
cikin raunin murya da kuka yace.
"Maman Yusuf ai jiya na gaya miki abinda Salim Adam ya fad'a min ko?."
cikin jin tausayi Mama ta gyad'a kanta alamar eh.
shi kuwa hawayenshi ya share tare da cewa.
"Toh ki gayawa Ammi na mana."
jin haka yasa Zahra sunkuyowa dai-dai tsawonshi cikin sanyi tace.
"Me Salim d'in yace maka?."
kaishi ya d'ago ya zuba mata ido cikin rawan murya yace.
"Cemin yayi wai bani da baba ni d'an shege ne wai shiyasa kowa Babanshi ke kanshi school wai ni kuwa sai uncle na da kakana sai kuma ke,
Ammi waye babana tunda kince inada Baba nima."
zuwa yanzu hawayenta sun zubo cikin k'arfin hali tace.
"Muje zan gayawa Atynku ta mishi fad'a."
jin haka ya d'an share hawayenshi kana suka fita.


A bakin titin k'ofar gidansu ta tsaya,
tare da gyara nik'abin fuskarta,
wani keke napep da ta tsaida ne ya tsaya gabansu cikin sanyi tace.
"Makarantar Aslaimin."
kai mai keken ya juya tare da cewa.
"50 ne."
wata matar mak'o tansu dake cikin napep d'in da alamar gwari zataje sarowa dan sana'arta ce,
to sai an wuce Makarantarsu Aryan d'in za'aje wurin sarin nasu,
cikin gyatsine matar tace.
"Ni bazan zauna da najasaba a kusa dani."
cikin mmki mai napep d'in ya juyo ya kalleta tare da cewa.
"Najasa kuma kamar yaya."
cikin tijara tace.
"Yoh d'an shege nefa data samo cikinshi a karuwanci."
tsaki mai napep d'in yaja tare da cewa.
"Toh ki fita mana,
mutane sai iya sawa k'addarar wani ido da son yi musu dariya da tijara,
kalleki in an ganki kamar mutuniyar kirki amman shine kike tona asirin wata,
shin yanzu ke kinsan k'addarar da kan iya riskarki ne?."
cikin tashanci tace.
"Tsaya ni karka min mugun fata,
Allah ya yayemin yayana su zama karuwai mazinata."
ai a zafafe mai napep d'in ya rink'a masifa tare da cewa ta fice mishi a keke,
dole ta fita tana masifa wai ya mata rashin adalci wai ai ita ya fara d'aukowa,
ita kuwa Zahra tuni hawaye ya jik'a nik'abinta,
shima Aryan hawayen yake zubda cikin jin tausayinsu mai nefen yasa hannu ya kamo hannu Aryan tare da cewa,
"Zo aboki na karkayi kuka."
sai ya kuma kalli Zahra cikin sanyi yace.
"Toh kema kina kuka shi kuma yaro ya zaiyi,
shiga muje dan Allah karkisa yayi letti a dakeshi a banza."
Cikin sanyi ta shiga,
Suna tafe yana jan Aryan da hira har yaro ya sake,
nan yake cewa Zahra karta damu zai rink'a zuwa kullum ya kaishi.

Koda suka shiga cikin makarantar,
albarkacin ganin idon uwa ba'a zaneshi ba,
sai Zahra ta nemi Antynsu Aryan tai mai mgnar dan Allah a yiwa Salim Adam fad'a amman bud'an bakinta sai cewa tayi.
"Toh k'arya yayine naga dai d'an shegen ne ko?."
ko kunsan waye Antynsu Aryan Amira ce yar malamin makarantar allonsu Zahra wanda suke yawan fad'a da Zahra lokacin suna yarinta,
kuma Salim Adam d'anta ne.
jin abinda tace yasa,
Zahra juyawa ta fita tana zubda kollah.


Haka dai Aryan yake fuskantar k'alubale yayinda Zahra kuwa take yawan shiga tashin hankali.

Ya Sulaiman kuwa yana ta faman nacin son Sakina A, S butu,
yayinda ita kuwa tayi burus dashi domin a cewarta Yusuf d'inta take jira.

Safwan kuwa har yanzu baiyi aureba,
ace warshi bai samu kalar matar da yake soba.

Yauwa asabar tun da sanyin safiya Raihana ta kira Maman Yusuf ta shaida mata ta haihu,
hakan yasa Mama tace Zahra ta shirya gobe taje ta dubo yaro,
haka kuwa akayi.


Washe gari da misalin 10:00 Am,
Zahra ta shirya ita da Aryan cikin shiga ta alfarma.
Atampa mai kyau da tsada riga da zani domin yanzu Zahra ta dena shigen k'ananan kaya,
bayan ta gama shiryawa cikin atampar sai ta kuma d'auko wata lappaya mai azabebben kyau,
yane jikinta tayi tare da jawo fuskarshi k'ad'an ta d'an rufe fuskantar,
kyau iya kyau dai tayishi domin kusan yanzune Zahra take kan ganiyar k'uruciyarta a yanzune zata amsa sunan budurwa mai cikar zati da halitta,
duk da yanayin k'uncin rayuwa da take ciki bai hana wasu sashi na jikinta hab'aka ba,
babu mai ganinta ace mishi ita ta haifi Aryan ya yarda,
domin ta murje tayi cib-cib shekarunta da surarta suna tafiya reras.

Juyowa tayi ta kalli Aryan dake rik'e da wayarta yanata karatun qura'an,
muryarshi sak ta mahaifinshi,
gefenshi ta zauna tasa kafad'arta ta d'an tab'ashi tare da yi mishi alamar ta gama,
jin haka ya sa da yaje k'arshen surar yayi addu'a tare da cewa.
"Ammi nayi bitar hadda nane, shine na sake dubawa,
kuma Alhamdulillah ban b'ataba."
cikin lumshe ido ta kamo hannunshi tare da cewa.
"In sha Allah ai bazaka b'ataba."
kai ya jinjina tare da cewa.
"Yauwa Ammi kina min addu'ar Allah yasa inzo na d'aya ko?."
kanshi ta shafa tare da cewa.
"Sosai ma kuwa, kuma insha Allah zakazo na d'aya domin jininka jinin nasarane,
mahaifinka bai tab'a shiga gasa ya fad'i ba sai dai in bai samu damar shigaba."
murmushi yayi tare da cewa.
"Yauwa Ammi, jiya nayi mafarkin mahaifina yana cemin wai ya k'usa zuwa garemu."
ido ta lumshe tayi kamar bata jishiba domin tasan yanzu zai tsareta da da tarin tambayoyi,
suna fitowa tsakar gida suka samu su Mama,
sallama tayi musu sannan ta tafi.

Bayan ta isa gidan Raihana tun a harabar gidan taga alamun akwai bak'i hakan yasa ta k'ara gyara rufuwarta tare da rik'e hannun Aryan da kyau,
a hankali take tafiya kanta a sunkuye har zuwa cikin gida,
a bakin parlour ta d'an tsaya tare da yin sallama,
yayinda cikin parlour yake cike da Affan da Mami da suka had'u da Safwan gidan,
sai kuma Rafi'a da Aryan babba,
sai mai gida Faisal.
cikin sanyi ta shiga bayan sun amsa sallamarta,
tana shiga gefen Raihana ta zauna,
yayinda Aryan kuwa tuni ya nufi wurin Affan,
shima Affan tuni ya bud'e mishi hannu da gudu ya k'arisa gareshi tare da d'ale jikinshi,
ita kuwa Zahra cikin sanyin murya tayi musu gaisuwar yan kasuwa,
bi ma'ana tayi musu gaisuwar jam'i shima murya can k'asa tace.
"Ina kwananku."
Affan ne yaketa hararan Safwan ganin yadda yake kallonta tamkar zai had'iyeta shi kuwa Safwan,
wani irin dad'i da shauk'i yakeji domin yau dai yaga kalar matar da yakeso,
gaba d'aya ya meda hankalinshi kanta,
cikin ganin yanayin da ya shiga Faisal ya d'an harareshi tare da cewa.
"Kai malam gyara rik'on da kayiwa yaron nan karka yarmin da yaro dan nasan baka san zafin haihuwaba."
mirmushi sukayi dan yadda Faisal yayi maganar bil hakk'i da gskya,
Mami kuwa wani irin dad'i takeji,
Allah Allah takeyi inama zarginta ya tabbata Safwan yace yana son Zahra ko ba komai in tayi aure wasu abuban zasu ragun mata.
Aryan babba kuwa shi sai mik'ewa yayi tare da kamo hannun Aryan k'arami cikin nuna isa da sabo da yaron yace.
"Aryan zo muje wojeko."
hannu Aryan ya mik'o mishi tare fara zamowa daga jikin Affan.
Ganin haka Affan ya d'an sunkuyo tare da tsuke fuska yacewa Aryan k'arami.
"Bazaka jeba."
aiko sai ya koma ya zauna tare da kallon Aryan Babba cikin tarbiya yace.
"Sorry Daddy karkayi fushi, Uncle Affan ya hana."
cikin tsananin mololon bak'in ciki Aryan ya fice.
shi kuwa Affan kanshi ya sunkuyar tare da kallon Aryan cikin rad'a-rad'a yace.
"Waya saka kake kiranshi Daddy?."
cikin sanyi shima yayi mgna rad'a-rad'a fahimtar da yayi Affan baya son wasu suji mgnar bakinshi ya d'an kawo kusa da kunnen Affan murya can k'asa yace.
"Shine yake cemin in rink'a kiranshi Daddy,
wai shi Daddy nane."
jin mgnarsu da yaron bazata yiwu a wurinba ya sashi kamo hannunshi ya mik'e dashi tare da mik'owa Mami hannu alamar ta bashi Asina yarsu kenan yar wata uku,
mik'o mishi yar tayi tare da cewa ina zuwa,
kai ya d'an jinjina tare da cewa.
"Mgnar sirri zanyi nida yarana."
har yaje bak'in k'ofa sai ya kuma juyo ya kalli Safwan dake kallon Zahra tamkar zai had'iyeta,
ita kuwa sai kanta ta sunkuyar tare dayin wasa da 'yan yatsunta,
cikin harara yace.
"Wai kai Safwan yaushenene zaka tafi,
kafa rigamu zuwa nan dukanmu,
ka zauna sai yawan kallo kamar tsohon maye, mitsss."
yaja dogon tsaki sannan ya fice dan ganin Safwan bai bi ta kanshi ba,

yana fita Mami da Rafi'a suka mik'e sukayi cikin bedroom don lokacin salla yayi.

Ita kuwa Zahra cikin sanyi ta d'an d'ago ta kalli Raihana tare da cewa.
"Aunty Raiha ina Babyn?."
cikin kula da tsananin tausayin yadda rayuwar Zahra ta juya komanta ya zama sanyi-sanyi kamar ba itace Zahra mai rakad'i da surutu da mazarin nanba,
cikin kulata tace.
"Toh baki d'ago kankiba ya za'ayi kiga inda yake."
murmushi tayi tare da d'ago kanta,
ganin haka Safwan ya mik'e tare da matsowa inda take a gabanta ya d'an rusuna tare da mik'a mata yaron,
hannu tasa ta k'arbeshi,
ba tare da ta kalli Safwan d'inba,
shi kuwa Safwan cikin wani irin salo murya can k'asa yace.
"Gimbiya kike d'an d'aga kankima mana,
ki taimaki rayuwar bawanki Safwan yaga kwayar idaunki ko zan samu cikekkiyar nitsuwa."
yaron ta k'ara ruggumewa dan kalaman Safwan sun buga mata zuciya,
Raihana kuwa tuni tabi bayansu Mami.
shi kuwa Safwan ganin haka ya koma gefen Zahra inda Raihana ta tashi,
zama yayi tare da kallon Faisal cikin taushin murya yace.
"To ni dai Alhamdulillah Faisal yau dai nayi farin gani a gidanka,
na samu matar aure."
cikin jin dad'i Faisal yace.
"Alhamdulillah dama zamanka haka ba aure ya ishemu".
a tak'aice dai anan a wannan ranar Safwan ya isar da sak'on zuciyarshi ga Zahra yayinda Faisal Mami Raihana sukaji dad'in haka,
Affan kuwa tamkar yaje ya shak'e Safwan yakeji,
domin yasan su Mami basu san waye Safwan ba tunda shi k'iyayyar daya nunawa Yusuf a wayance take kowa zai d'auka kawai yanayin sana'arsace.

Da forko Zahra tak'i amince mishi,
to amman daga baya dole ta amince mishi sabida yadda Aunty tayi ta zaginta,
harda cewa.
da tayi sa'a ma ta samu wanda ke sonta kuma saurayi,
tai mata misali da itafa yanzu matsayin bazawara take,
gashi an gaya mishi abinda ya faru da ita da cewar Aryan d'antane,
toh shi Safwan sai da aka gaya mishi ya gane Zahra,
ya kuma amince zai aureta a hakanta,
domin shi randa ya ganta a gidan Faisal yayi zaton Aryan k'aninta ne.

Toh a haka dai sabo ya shiga tsaka ninsu shi kam Safwan sosai yake sonta,
tuni ya kai mgnar ga iyayenshi har anje anyi tambaya an gama mgnar komai,
har lefe an kai,
so sai yayi tunanin ya gayawa mahaifiyarshi gskiyar lamari akan Zahra domin kar tajiyo jita-jita,
ai kuwa Hajia Yabi tana jin wannan tabo na zara tayi tsalle ta dire tace wannan auren sai dai bayan ranta,
nanfa aka fara tattaburza Safwan kamar zaiyi hauka,
gashi Allah ya jarabceshi da son Zahra tamkar ranshi.


haka dai mgna ta zama ciniki gaba baya tsada.

Affan kuwa da yaji wannan lbrin gaba d'aya hankalinshi ya tashi,
cikin kwanakin ya rink'a azalzalar Yusuf da batun ya dawo gida ba lafiya,
domin shi dai Affan burinshi Yusuf ya auri Zahra.


Yauma kamar kullum Safwan ne zaune gaban Hajia Yabi cikin sanyi ya kalleta tare da cewa.
"Dan Allah Mommy ki taimaki rayuwata wlh ina son Zahra itace kalar matar da nakeso."
Tsaki taja tare da cewa.
"Wallahi Safwan ka bar min zancen wannan yar iskar mai d'an shege,
wlh na gaya maka in kaga ka aureta sai dai bayan raina."
murya a raunane yace.
"Mommy wlh Zahra ba k'aruwa bace,
k'addararta ce tazo mata a haka, dan Allah ki dena ce mata karuwa."
harara ta watsa mishi tare da mik'ewa ta fice ta bar mishi wurin.

Haka yayi ta zama a wurin har saida yaga dere ya fara nisa sannan ya mik'e ya nufi part nashi.

Bayan ya gama shirin baccinshi ne,
ya konta tare da Jawa woyarshi ya kira Zahra.

Ita kuwa Zahra tana konce yayinda Aryan ke kan k'irjinta,
inda ya kasance nanne makoncinshi haka suka saba koya zatayi sai ya d'aura kanshi a k'irjinta yake bacci itama kuma bata iya bacci sai in har ta jawoshi jikinta,

jin woyarta na ringing ne yasata d'agawa da sauri dan kar sautin ya tada Aryan d'in,
ido ta lunshe jin muryar Safwan tamkar zai kuka yake cewa.
"Zahra na kasa bacci."
cikin sanyi tace.
"Meyasa?."
murya can k'asa yace.
"Cikar burina nake tunanin ta yadda zai samu gareni."
murya a sanyaye tace.
"Komai nufine na Allah kuma komai yanada lokacinshi,
matar mutun k'abarinshi,
please ka kontar da hankalinka dukkan tsanani yana tare da sauk'i."
gyara konciyarshi yayi yana jin sautin muryarta na ratsa mishi jiki da zuciya.


A haka bacci ya sacesu baki d'ayansu.


Can cikin duniyar bacci Safwan ya shiga duniyar mafarki.
inda ya ganshi a farfajiyar wani gida ya fuskanci gabas yayinda gidan yake bayanshi,
yana tafiya hannunshi rik'e da wata yar kekkyawar fulawa irin ta masoya,
wani irin sauri ya k'ara harda d'an gudu-gudu sabida hango Zahra da yayi cikin shigar k'ananun kaya,
cinyoyinta duk a woje,
gaba d'aya burinshi ya isa gareta,
dan haka ya k'ara saurinshi,
yazo gab da ita kenan,
sai yaga Yusuf ya iso gareta tamkar gilmawar walk'iya,
yana zuwa ya ware mata hannu ba musu itama sai ta d'ago hannunts tare da ruggumeshi.
wani irin bak'in cikine ya rufe Safwan haka ya sashi,
meda hannunshi baya saida ya d'an wucesu ya cilla fulawar tare da kwabe fuska tamkar zaiyi kuka.

yana cilla fulawar ta gefenshi sai ga Dija ta cab'e fulawar cikin sauri tabi bayanshi,
tare dasa fulawar ta d'an bugi kafad'arshi,
jin an tab'ashi ya sashi juyowa,
ganin zuk'ek'iyar mace a gabanshi tana mik'a mishi fulawar fuskarta d'auke da murmushi,
baisan lokacin da yayi wani irin mumurmushi tare da sauk'e numfashi,
dai-dai nan ya farka tare da tsananin fargaba da tsinkewar zuciya a fili yace.
"Toh kuma me wannan mafarkin yake nufi,
wannan mai jajayen kunnuwan me yake so danine kuma nifa ina tsoron mafarki a kan Yusuf, dan mafi akasari yakan zama gskya?."
sai ya kuma koma konce tare da lumshe ido,
yana sak'a da worwora.


Washe gari da safe.
Cikin masarauta Affan ne durgushe gaban,
M Jabeer,
suna tattaunawa abinda ya shafi masarautarsu
jin wayarshi na suwane ya d'aga tare da mik'ewa ya bar wurin,
cikin mmki M Jabeer ya bishi da ido domin yasan ko wacce iriyar wayace Affan kan yishi a gabanshi,
shi kuwa Affan ganin Yusuf ne ya sashi barin wurin.

Kai tsaye cikin motarshi ya shiga,
saida ya gyara zamanshi sannan yace.
"Kai ba doguwar gaisuwa nake soba,
yaushe zaka dawo?
na dai gaya maka Mama bata da lafiya ko."
cikin sanyi Yusuf yayi gyaran murya tare da cewa.
"Nanda kwana uku za'a buga world polo,
kuma team Ellistiner bazata sakeni ba,
dole sai an buga gasar,
so ana gamawa zan taho."
cikin jin dad'i Affan ya sauk'e numfashi tare da cewa.
"Masha Allah,
toh Allah ya bada sa'a."
"Amin Amin."
Yusuf yace tare da katse kiran,
dan ganin kiran shugaban qungiyarsu ta shiga wayarshi.


A Girei kuwa ana kiran sallan azahar Aryan yayi alwala tare da bin bayan Jafar da ya dawo wata d'aya daya gabata,
suna zuwa harabar masallacin,
Aryan ya d'auki butocin ya fara ciccikasu da ruwa yana ajiyewa gefen da ake al'walan,
yakai buta ta uku wanda tuni har wasu sun k'arba suna Al'walan ya d'auki buta ta hud'u ya koma jikin pompon ya sunkuyo da nufin bud'e bakin pompon sai ya kuma mik'ewa da saurin,
jin wani irin azaba ya ratsashi,
yana dagowa dottijon ya kuma zuba mishi carbin hannunshi,
cikin fad'a yace.
"Matsa daga nan shege d'an mazinata,
zaka zo kana mana wasa da ruwan al'walanmu mai tsarki."
shi kam Aryan gaba d'aya jikinshi rawa yakeyi tuni ida nunshi sun cicciko da hawaye,
kuka mai k'arfi ya danne mishi harce,
jin ya sake tsula mishi carbin ne ya sashi sakin wani irin gigitaccen k'ara,
wanda saida Zahra dake cikin gida ta jishi,
Yusuf kuwa dake can k'asar Argentina a mafarki Allah ya nuna mishi dukkan abinda ke faruwa da Aryan,
zuba mishi carbin da aka kuma yine yasa Yusuf farkawa tare da cewa.
"Aryan ka gudu kar ya illatamin kai."
shi kuwa Aryan ya kasa matsawa gaban wannan tsoho sai karkarwa da jikinshi keyi, tuni wuyanshi yayi jazir,
Jafar kuwa jin ihun Aryan ne ya sashi fitowa da gudu yazo ya d'agoshi tare da ruggumeshi cikin k'unci yace.
"Haba dai Bappa jangirde me wannan yaron ya maka da zakayi ta zaneshi da carbi."
kun tuna bappa jangirde malamin allon makarantarsu Zahra tun tana k'arama kunsan dama baya yin Zahra,
cikin rashin tausayi ya kalli Aryan daketa kuka yacewa Jafar.
"Wallahi da inada damar hana yaron nan zuwa,
masallacin nan wallali dana hanashi zuwa,
haka kawai sai kuyi ta kawo mana najasa a cikin matsallaci."
cikin tsananin takaici Jafar ya sauk'e Aryan tare da tsugonowa dai-dai tsawonshi tafin hannunshi yasa yana share mishi hawayen daketa zuba,
cikin taushin lafazi yace.
"Kada kayi kuka Aryan,
kaifa ba rago bane,
kai jinin jarumine kuma tsarkakkeke mahaifinka ba d'an iska bane,
kuma kai ba najasa bane,
duk mai ce maka najasa yaje ya binciki gidanshi,
kayi murmushi kaji ko yarona,
haka mahaifinka yake duk tsananin wuyar da yake ciki yakanyi murmushin jarumta a fuskarshi."
wani irin murmushi Aryan yayi still hawaye na bin fuskarshi,
shima Jafar murmushi yayi tare da cewa.
"ehye-ehye like father like son."
sai ya kuma kamo hannunshi yace.
"Muje muyi salla mu bazamuyi fad'a a masallaci ba."
har sunje bakin mashigar masallacin Aryan d'in ya juyo tare da cewa.
"Bappa njangirde na yafe maka zalina da kaci."
shi kuwa Bappa njangirde a take kunya ta rufeshi,
sai tausayin yaron ya kamashi,
tabbas yasan bai kyautaba.

Bayan an idar da salla sun koma gida

Please Login or Register in order to submit comment