Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin girmamawa yace. "Ummu kiyi hakuri ki yafema ɗanki, ki saka mani albarka dan Allah kada kiga laifin Bahijja ko Huzaifa nine silar komai, ba kowa ba." a tsawace tace. "Harka isa ka dinga dan ganta Bahijja dakai inna yi alkawali yanzun na fasa baza tai maka hidima ba, inama ace na kashe jaririyar nan da hannuna, inama ace ban aminta da kaiba da har ka saka mata suna da kanka, kaicona ni Zulaiƙa jinin Sarauniya Yahanazu Jika Sarauniya Maimoon uwa ga Sarki Khamil ɗa ga Sarki Jabbar ɗan Sarki Abdulhamid ni Zulaiƙa yau ɗana MalikusSaif kejin tausayin bayi makiyan mu maciya amana tabbas zan iya wulakan taka Malik akan wannan baiwar Bahijja dan haka ba kai ba Bahijja.!"
shiko ya kasa Komai kanshi ya kulle, su Yazid ko kamar anda sasu cikin ƙaƙƙausar murya tasa Yazid ya kirama ta Fusab wani ba fada ne wanda ke kula da wani wuri wanda ake kai ya'yan sarakai wato jinin Sarauta a cikin wani gida ne ana adana su dan ɓata masu rai, a ganin su duk wanda aka kai wajen kamar anketa mashi rigar mutunci, haka kuwa akayi yana zuwa tace, akaima ta MalikusSaif da Huzaifa ba tasan ganin su a halin yanzun, haka su Malik suka tafi ko magana bai karayi ba dan bacin rai da ya gama kama Malik, Shiko Fusab hakuri yafara ba su Malik a hanya shidai baice komai dan ƴan Masarautar Daborah suna bala'in kaunar Yarima Malik har suke mashi laqabi da Yarima mai adalci, uban marayu mai jinkai, haka ya kaisu cikin wani daki ba abinda babu harda gado, saidai ga jinin sarauta hakan cin fuskane haka ya rufosu ya tafi kamar yanda Sarauniya Zulaiƙa ta umurce shi...



_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 29&30



Koda Fusab ya koma wajen Sarauniya Zulaiƙa zubewa yayi yace. "Allah yakara maki yawan rai Fusab ya cika umurnin ki cikin gaggawa kamar yanda kika bukata." a dakile tace. "Ka kyauta saidai kalubale gareka duk abin da ɗana ke bukata ka tabbata ya samu, nayi hakan ne a gare shi dan innuna mashi so ba hauka bane kwara ya dawo cikin hayyacin shi yasan waye shi ya banbace tsakanin bawa da mai ƴanci kuma Sarkin wannan Masarautar na gobe da yardar Allah." cikin girmamawa yace. "Kwarai kuwa zan kiyaye ba abin da zai nema yarasa ranki shidade ki huta lafiya."
haka ya fita yana mamakin karfin hali irin na Sarauniya Zulaiƙa ya tabbata ba wanda baza ta iya hukuntawa ba a duniya duk yanda take kaunar Yarima MalikusSaif amman zata iya yi mashi hukunci ba tareda ta damuba ko kadan, shi kanshi Yazid ya gama shan mamaki kallan da tai mashi ne yasa shi karasowa ya duka ya gaida Sarauniya sannan yace. "Allah ya huci zuciyarki Ummu, Allah yakara maki nisan kwana nazo ansar mabudi zamu dauki kayan Yaki munakan bada gwaji ne na musamman."wani irin murmushi ta saki shi kanshi yayi mamaki sai kace ba ita bace tagama hukunta gudan jininta ba, bai gama tunani ba kuma yaga ta sake ta haɗe rai sai kace mai jinni a murtuke ta kalle shi tace. "Angaishe ka Yazid a cikin ku kaf yan uwana tundaga ɗana Malik har Huzaifa kafi su kishi na dan haka na jinjina maka ga mabudi kaje kuyi duk abinda ya dace." cikin jin dadi ya karɓi mabudin yayi godiya har zai tashi ya koma ya zauna yace. "Ummu sai dai kisani barin manyan Jaruman mu a cikin gidan kaso tamkar naka sane ga wannan Masarautar tamu, sannan kiyafema su Malik ki fiddosu suma gwarkuwa ne a cikin Masarautar Daborah fiye da tunanin kowa." du kowa tayi kusa da Yazid tace. "Ina ganin girman ka, sai dai korafin ka bai karbu ba amman zan iya fiddo da Sarkin Yaki na dasu Lurwan suko su Huzaifa kabar su ba yanzun ba kaman ta da sunan me muke bata lokacin mu mai mahimmanci muna gwaji duk fa akan wannan dakikiyar baiwar ce Bahijja akan ɗauketa da marar kishin nan yayi ne yasa Sarki Baidulƙais ya aiko mani da wasikar ya kata duk saboda baiwa haba Yazid tunda ka tashi cikin Masarautar nan kataɓa ganin inda akayi yaki irin wannan duk saboda baiwa yar wahala akan Bahijja zan fita cikin mazan fama dan kare martabar Masarauta ta, kaga dole inkara tsanar Bahijja musamman duk wani tsatsan ta, ya zan bari ɗana kamar Malik ya dinga daga darajar baiwa wadda itace silar faruwar komai sannan uwa uba akanta za'a Yaki Masarauta ta kilan akashe mutane masu daraja duk a dalilin BAIWA haba Yazid kasan yanda nikeji a cikin zuciya ta dan haka kata shi kuje kuci gaba da gwajin yakin dake tunkarar ku mai taken *YAƘI AKAN BAIWA!!!."*


Jiki mace Yazid ya tashi yaima Sarauniya Zulaiƙa sallama yatafi dan cigaba abinda yake gaban su cikeda mamaki a ranshi.
Ita ko Bahijja harta daina kuka dan azaba, danko Binta ta gama galabaita danko tun bayi na kallo har sun watse daga su Mairo saifa Bahijja da take ɗaure ko ɗaga hannun ta takasa dan azaba da bala'i......a cikin gidan kaso kuwa Abdulmajid ne labari ya same shi ƴarsa Bahijja tadawo ba karamin murna yakeyi ba yasan zuwa gobe zai iya ganin ta yasan tabbas sai Binta tazo mashi da ƴar lelen ƴarshi yagani dan ba kadan yake jin kewar ta na ratsa mashi dukan illahirin jikin shi ba, hakanan yaji farin ciki ya mamaye mashi zuciya yau zaiga Bahijja a wani sashena zuciyar shi kuwa wani irin kaunar MalikusSaif yaji tana kara ratsa shi lallai maganar Binta ta tabbata MalikusSaif ya zama amintacce ga Bahijja godema Allah yaitayi da Allah ya maido mashi su cikin aminci da walwala, a zahiri ko cewa yake. "Allah gagara misali Sarkin Sarakai mai ansama kowa bukatar shi daman ance mahakurci mawadaci yau ga ƴarmu Bahijja ta sake dawowa a garemu karo na biyu a cikin Masarautar Daborah Allah ka kara tsare mana ita da kariyar ka, Allah nagode maka da wannan ni'imar dakai mana." ranar haka ya yini cikin farin ciki marar misaltuwa.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Masarautar Waisu kuwa zuwa yanzun Yarima Haishir jiki yai sauki sosai har ya fara zuwa gwaji da ake ba Jaruman su duk da sun gama hada komai zuwa gobe zasu tafi Masarautar Daborah kamar yanda Sarki Lahazu ya umurta, yauma kamar marar lakka haka ya dinga sanyin training saidai rabi da kwata ba wanda yake tunawa sai Bahijja yanajin inama ya sake kama Bahijja akaro na biyu

******************************

Washe gari da safe a wajen su Malik kuwa tunda sukayi sallah yake addu'a dan ko bacci gagarar idanun shi sukayi ba wanda yake tausayi sai Bahijja acikin ranshi ji yayi inama wani waje ya ajeta ba cikin Masarautar Daborah da bata shiga cikin wannan fitinar da take ciki ba, a zahiri ko cewa yayi. "Huzaifa kaga yanda Ummu ta ɓata ranta kuwa."? Murmushin yake Huzaifa yayi yace. "Nagani uzuri zamu cigaba dayi mata ranta ne ya sosu sosai." ganin yanda Huzaifa bai nuna damuwar shiba, akan zancen hakan yasa MalikusSaif ya girgiza kai bai sake furta uffan ba dan yaga maganar bata da anfani shi yasa yaci gaba da tunanin shi yana nema ma Bahijja mafita dan ganin ta kubuta daga azabar da take ciki.


Yauma Yazid ne zai tafi wajen bawa Jarumai gwaji harya wuce ya dawo baya, shiga yayi sashen Saifulislam iske shi yayi zaune yana karatun alqur'ani, zama yayi harya hama, yana gamawa ya kalli Yazid yace. "Dana kai kadai ko har yanzun abokan ka basu dawo ba insha Allah zasu dawo bada jimawa ba."
murmushi yayi yace."Abbuh sannu da karatu ai sundawo tun jiya da marece saidai ansamu damuwa." mamaki ne ya gama kama Saifulislam a ranshi ko cewa yayi daman har Malik zai iya dawowa ba tareda ya nemeni ba har ya iya kwana bai ganni ba, a zahiri ko cewa yayi." wace matsala ce kodai ba suga Bahijjar ba, fadamani.?" a sanyaye yace. "Aaa Abbuh sun ganta saidai ran Ummu ya ɓaci yanzun haka tasa ankama Bahijja tana turakar bayi tasa anata dukanta tun jiya ake mata azaba har yau ba abari ba, sannan MalikusSaif yaje neman mata alfarma hakan yasa Sarauniya ta mare shi abin tashin hankalin ma yanda tasa aka kama Yarima Malik da Huzaifa aka rufe matasu gidan Huzu, yanzun haka suna tsare." da sauri Saifulislam ya mike yana mamakin irin halin da matar shi keda shi, a zuciyar shiko cewa yayi yanzun miye laifin Bahijja, kuma wannan cin fuskane ace ɗan shi za'a kama, a zahiri ko cewa yayi. "Shikenan Yazid naji da kaga yamani zan san abinyi." godiya yai mashi saidai a darare yace. "Abbuh inane man alfarma wajen ka."? Cikin kara mashi kwarin guiwa yace. "Inajinka." a gaggauce yace. "Dan Allah kada kabari Ummu tasan ni nasar maka."kallon yaro man kaza yai ma Yazid a zahiri ko cewa yayi karka badamu ba zan fada mata zaka iya tafiya." godiya ya sake yi sannan ya tafi shiko Saifulislam yasa akira mashi Sarauniya Zulaiƙa koda mai kiran Sarauniya Zulaiƙa ta tafi iskewa tayi bata nan tana fa'da, haka ta tafi ta gaya ma Saifulislam cewa tana fa'da, rai ɓace yace. "Ai kiranta nace kimani dan tana fa'da ni Kangiwa ba damuwa ta bane kije can ki kiramani ita."
bakaramin tsorata Mairo tayi ba da yake itake kula da sashen Saifulislam, daman tana cikin manyan bayi daga Binta sai ita sai Ladidi sune manya a cikin bayi, ita kuma Ladidi tana kula da sashen Waziri Dammur, hakan yasa Mairo ta tafi jiki sage har fa'da tana zuwa tai sallama Sarkin Zagi yafara cewa. "Ke baiwa mike tafe dake cikin wannan fa'dar mai alfarma? Fa'da ba wajen zuwan bawa bane saida dalili mai karfin gaske da fatan zaki kiyaye gaba." itako dukar da kanta tayi wanda takasa magana kanta a kasa tace. "Allah ya karama Sarauniya lafiya sakone daga Kadimulislam yace yana son ganinki a sashen shi yanzun, Allah yakara girma."
ta gama fadar maganar kanta a kasa dan taki yarda da hada ido da Sarauniya Zulaiƙa wanda ba abinda take aika mata sai mugun kallo, gyaɗa kai kawai tayi ba tareda tace komai, hakan yasa Sarkin Zagi yace. "Sarauniya ta amsa baiwar Saifulislam tana zuwa, fa'da ta sallameki." haka ta tashi tana godema Allah harta isa wajen shi tagaya mashi sakon Sarauniya Zulaiƙa, sannan ta tafi lambun bayan sashen shi tafara aikin gyarawa, itako Sarauniya Zulaiƙa tana can fa'da suna shawara akan Yaki wanda wannan shine zaman karshe da zasuyi kan maganar Yakin dan a lissafin su zuwa jibine za'a kawo masu hari ko kuma zasu fara artaba akan abokan gaba, wani ɓari na zuciyar ta kuwa tana mamakin kiran da Saifulislam yake mata kasancewar yasan tana cikin yanayi bata da cikakken lokaci, wata takarda ce tasa kama hannu sannan ta mike zata tafi wajen Saifulislam saiga Waziri Dammur ya shigo a shitatan yanda tagan shi tabbas ta tsorata shiyasa ta tsaya tana tambayar shi ba'asi, warewa sukayi gefe sannan yace. "Sarauniya yakama ta kizo muje gidan kaso dan fiddo da mutanen mu bai kamata muwuce yau ba ba tareda anfiddo suba." dafe kanta tayi ta rasa mike mata dadi, batai mashi musu ba suka tafi gidan kaso dan fidda su Lurwan, tana zuwa akaita kai gaisuwa wajen ta sannan aka rakata wajen Sarkin Yaki koda ya ganta, kallan ta kawai yayi ya kauda kai sannan ya gaisheta, itama amsawa tayi atakaice sannan tace"Sarkin Yakin Daborah bai kamata ace kunyi kwanaki a wannan wajen ba, yakama ta yaudin nan ku fita dan kusa mu hutu." ɗan murmushi yayi sannan ya kalleta ya kalli Waziri yace. "Hakane Allah yabaki yawan rai saidai ki bari zuwa gobe ko jibi zamu fito kamar yanda kika umurta, dan nan din nafi samun nutsuwa." Waziri ne zaiyi magana Sarauniya Zulaiƙa ta ɗaga mashi hannu alamun yai shiru sake kalln shi tayi tace. "Haka kuke bukata."? Da eh ya amsata, wani shu'umin murmushi tayi tace. "Girmanka ne Mas'ud lokacin da yai maku zaku iya fita saidai kasani fa'da ta sake ku."
tana gama faɗar haka tai tafiyar ta ba tareda taji abinda Sarkin Yaki zaice mata ba, Waziri Dammur ne yace. "Ya kama ta yau kufito zaifi maku amman kayi tunani."shima binta yayi ya tafi, sun fita taima Waziri wani irin kallo tace. "Dammur kagani ko nazo wannan yaron yana neman gaya mani magana wlh koda Sarkin Yaki ko bashi ni Zulaiƙa zan iya kare martabar Masarauta ta, koda kuwa ba Yarima Malik, dan ma ɗana Jarumi ne." "hakane kam amma zasu fito Sarkin yawa shiyasa mukeso ace sun fito yanzun ga su Malik a tsare, bayan kinsan shike tsare mutucin Masarautar nan."
"hmm Waziri tunda nike Malik bai taba min rai kamar wannan lokacin ba amman ba damuwa zan fiddosu." da haka suka tafi, hankalin tane ya koma wajen Saifulislam da sauri take tafiya dan ta shafa'a abubuwa ne sukai mata cinkus, tana zuwa ta iske bai nan hakan taji faruwar gaba, duk dakunan shi ta duba bai nan.
shiko Saifulislam ya gama kulewa hakan yasa ya tafi inda aka kai su Yarima MalikusSaif ya fiddo su, ya kai su har sashen Yarima, cikin damuwa Yarima yace. "Abbuh da kabarmu acan kaga Ummu bata bukatar ganin mu, sannan kuma Bahijja tana turakar bayi ana dukan ta Abbuh zasu iya kasheta."
dafa shi yayi yace. "Kada kadamu yau zansa a sakota." wani irin dadi yai mashi yawa, baisan ya rungume shiba yace. " Abbuh nagode Allah yakara girma da daukaka." tafiya yayi ba inda ya tsaya sai turakar bayi zai shiga kenan mai kula da wajen ya zube yace. "Ranka shidade Allah ya taimaki Kangiwa ba girman ka bane shiga cikin turakar bayi, amatsayin ka namai Sarauta kuma miji ga Sarauniya." wani wawan kallo yai mashi baice komai ba ya shige cikin turakar bayi har inda aka ɗaure Bahijja sadda yaje har angama dukanta duk jikin ta yayi sahun bugu koda Sarkin horo yaga Saifulislam zubewa yayi yana neman afuwa, ko kallo bai isheshi ba haka yasa aka kwance ta aka kaita gida, yasa su Binta suka fara bata kulawa sannan ya tafi yana mamakin irin zalinci na Zulaiƙa, yana komawa ya isketa tsaye taje ta dawo taje ta dawo da sauri ta taro shi tace. "Abu Malik ina kaje ina ta neman ka."? Wani mugun kallo yai mata yace.




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*

_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



Episode 31&32



"Naje na biyama kaina bukata tunda nina damu da abin da zanyi dan haka kije kiyi uzurin gabanki.!"
ya gama maganar ya shigewa bedroom dinsa itama binshi tayi ta iske shi zaune a gafen gado, itama zama tayi gefen shi cikin sanyin murya tace.
"Haba mijina karkayi fushi mana, ina ta ujilar inzo gareka, abubuwa ne suka shamin kai shiyasa."
murmushin mugunta yayi yasan abin daya aikata mata kadai ya isheta hukunci! rausayar da kanshi yayi yace. "Hakane kam nima abubuwan suka shamin kai shiyasa na manta da nasa a kiramin ke ba damuwa zaki iya tafiya hidimomin gaban ki, dan haka ina bukatar hutu." sake marerecewa Zulaiƙa tayi cikin damuwa tace. "Ai nagama daman naje gidan yari dan fiddo Mas'ud dasu Lurwan sai dai sunce zuwa gobe zasu fito." shiru yayi yana ɗan nazari a zahiri ko cewa yayi. "Daman baki fiddasu ba sai yanzun? anya kina aiki da tunani Zulaiƙa? wai miyasa ku mata kuke abu yanda kuka ga dama yanzun ko wane lokaci za'a iya kawo ma Masarautar ki hari har yaushe kika fiddo suka huta balle su tallafa maki da karfin su? Koda yake yanda kika gani haka zakiyi! ba wannan ba, nima naje na fiddo Ƴaƴana da kikasa aka kullemani su yanzun haka Yarima yana sashen shi." waro ido tayi tana kalan shi cike da mamaki tace. "Ka fiddo sufa kace.?"
kallan rainin hankali yai mata yace.
"Mikike nufi sai in zuba maki ido ina kallan ɗana a kulle bayan ya gama shan wahalar nemo yarinyar nan maimakon ki jinjina mashi akan namijin kokarin da yayi kawai sai inji dana a kulle kema kinsan kan Malik zan iya komai shi kadai na mallaka a duniya dan haka bazan saka ido ba ina ganin ɗana cikin damuwa ba! dan haka yana can nace su huta shida Huzaifa."
ya gama maganar yana kishingiɗawa saman gado, rasa mi zata cema Saifulislam tayi, dan taso ta kara ɓatama Malik rai kamar yanda ya sosa mata nata ran, dakewa tayi tace. "Yanzun har Malik yayi abin yabawa dan ya tafi ɗauko baiwa? Haba ai wannan abin kunya ne, bama gani kadai ba harda Masarauta ta baki ɗaya, kaga dole in hukunta shi."
ranshi ne ya gama ɓaci baisan ya zauna ba yace. "Kada kigaya mani ba dadi Zulaiƙa ina laifin wanda ya ceci naka ko kin manta iyayen yarinyar nan haka suka sadaukar da ƴarsu kan danmu? suma ba mutane bane? ko an gaya maki tashi kawai sukayi suka tsince ta! ita haifata akayi kamar kowa! da anyi mgana sai kice baiwa baiwa itama mutunce kamar yanda kike ta kama kema mutun ce! sannan MalikusSaif ya cancanci yabo tunda har yasan halacci kuma ya sakan ta ma mutanen da suka yi mashi aikin alkhairi, gaskia kin zama butulu Zulaiƙa."
da sauri ta mike tace. "Kana ta fadan munanan kalamu a kaina saboda baiwa! ɗan naka yayi abin kunyar shine kake goya mashi baya ko kamanta shi Yarima ne." dan karamin tsaki yayi yace. "Ita baiwar da kikasa aka ɗaure kina san kiga gawarta ne? kasancewar ta mutun mai jini a jiki kamar kowa shiyasa naje da kaina har cikin turakar bayi nasa aka kwanceta na dan kama mahaifyar ta zata cigaba da bata kulawa ta musamman dan Bahijja bata cancanci wulakanci ba, amman in har kinsan halacci."
Wani irin mummunan faɗuwar gaba ne ya riski Sarauniya Zulaiƙa ba tasan taja baya tana dafe kirjin ta dake dukan tara tara kamar zai faɗo kasa, jikin ta ne yafara rawa kamar mazari, hakan yasa ta duka kasa wasu kwalla masu ɗumi suka wanke mata fuska, muryar ta na rawa tace. "Saifulislam!!! da kanka kashiga turakar bayi kana mijina uban dana magajina, ka shiga turakar bayi ka kwance baiwa yar bayi."?
Take yaji wani irin sanyi aran shi yasan yasha da Zulaiƙa raban daya ga tayi kwalla har ya manta a rayuwar shi ta duniya mikewa yayi yace. "Kwarai kuwa da hannu na, nasa aka kwance Bahijja sannan dani aka kaita har masaukin iyayen ta, kuma na dawo ɗaki na, duk nine nayi wannan aikin saboda ɗan Adam ba abin wulakan tarwa bane ki saka wannan a ranki Ummu Malik."
bata san ta rushe da kuka ba mai cin rai tace. "Baiwa baiwa baiwa!!! Kaje ka kwanto kana mijin Sarauniya yau kaine kafarka ta taka turakar bayi lallai Abu Malik ka karya doka mai girman gaske ka watsa mani kasa a ido, ga idanun kuwa duniya za'a ce mijin Sarauniya Zulaiƙa ua shiga turakar bayi ya kwanto baiwa!
daman haka ɗanka ya gudu yaje ya ɗauko baiwa yau gashi an wayi gari Kangiwa uban MalikusSaif ya shiga turakar bayi ya kwanto baiwa! ina ace dukana kai tayi da yafi mani sauki akan wannan abin kunyar da kuka jefani kai da ɗanka! tabbas Saifulislam badan kana mijina ba kuma ina kalkashin ikon ka, wlh dako Malik ya aika ta mani irin wannan abin da ka aikata mani ni kaina basan kalar hukuncin da zan mashi ba saidai kaci darajar aure, amma ka zubda mani ƙima da daraja ta, tabbas Bahijja kinzo da kalubale iri iri tunda ga haihuwar ki har zuwa lokacin da ɗana yaje ɗauko ki! yau gashi a kan ki za'ayi Yaki kina baiwa za'ayi yaki kanki, gaskia Bahijja kin shiga cikin gona ta! wanda ba mahalukin da yata yima Sarauniya Zulaiƙa kutse saike, ke din ma baiwa ƴar bayi.!"
Haka ta karasa maganar tana rushewa da matsanan cin kuka mai taɓa zuciya.
koda Saifulislam yaga Sarauniya Zulaiƙa tana ta zance kamar wata zautatta baisan ya zauna ba yana kallan ta yasan tabbas ranta ya gama ɓaci dakewa yayi yace. "Tabbas Bahijja baiwa ce kuma baiwa ce wadda ta kafa tarihi a rayuwar Masarautar Daborah kuma baza'a taɓa mantawa da ita ba, sai dai ina so ki kara sawa a cikin ranki BAYIMA 'YA'YANE! matat."
yana gama faɗa mata haka ya tashi ya shiga bathroom danyin wanka ita ko saman kafat ta kwanta tana kwalla masu zafin gaske ji take kamar ta fiddo zuciyar ta ta huta da azabar da take ji a cikin kirjinta.......

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Raifasu kuwa sun gama shirin su tsaf dan kowa ne Jarumi yagama duk wani abun da zaiyi kowa ya hau saman dawakan su sunbi layi suna jiran abada izinin tafiya kasancewar akwai tafiya tsakanin su da Masarautar Daborah, shi yasa suka gama shirin su basu san sukai gobe ba tareda sun isa ba ko kuma su ɗauki lokaci mai tsawo, a cikin sashen Sarki Baidulƙais kuwa shida Jamra ne sai bayi guda sha hudu da za'ayi tafiyar dasu dan ba Jarumai kulawa bakwai mata bakwai maza, sun gama shirywa tsaf da kayan guzuri a hannun su, suka fito shima Sarki Baidulƙais fitowa yayi cikin shiga ta alfarm ta kayan Yaki ba inda ya nufa sai wajen Sarki Danwar shima ya gama shirin nashi shida Jakadiyar shi suka fito baki ɗayan su suka hau dawakan su, inda Sarki Baidulƙais yayi sallama da gimbiya Yazira sannan suka dunguma dan tafiya, Sarkin Kofa ne ya bude masu Kofa suka tafi, sannan suka ɗauki hanyar tafiya Masarautar Daborah

_DABORAH_

wajen su Binta kuwa sai kulawa take ba yarta tanajin dadi yau gata ga Bahijja a tareda ita, itako Bahijja bacci takeyi da kagan ta kasan na wahala ne takeyi sai su Mairo sun kewaye ta sai kallan ta sukeyi kamar wata bakuwa haka ta koma masu.
Danko Sarauniya Zulaiƙa da kyal ta koma sashen ta tana zuwa wanka kawai ta iyayi baki daya hankalin ta yai matukar tashi inta tuna da Saifulislam ya shiga turakar bayi, sawa tayi akai mata kiran Binta zuwa yanzun kiyayyar ta kaf ta rataya akan Bahijja gani takeyi duk wani farin cikin ta Bahijja kemata barazana dashi, saman wata kujera ta zauna ta alfarma ta rufe idanta kamar mai bacci saidai kana ganin ta kasan tension ne yai mata yawa sai lula kujerar takeyi tana tunani iri iri a cikin zuciyar ta koda kiran Sarauniya Zulaiƙa ya iske Binta lokacin Bahijja ta farka daga bacci a hankali ta dinga bin mutanen dake wajen da kallo takai minti ukku tana aikin kallan su sannan ta kalli Binta bata san sadda ta faɗa saman ta ba bakin ta na kyarma tace. "Umma na dan Allah ki gudu dani wlh kasheni zasuyi duk inda naje basu kauna ta so suke su lahanani Umma na dan Allah kitaimaka mani." sake riketa tayi tace. "Ki kwantar da hankalin ki Bahijja ko kin manta kedin baiwa ce wuya bata kisa, karki manta tin kina kankanuwar ki nasha faɗa maki baiwa bata san gata ba ko jin dadi wahala kawai tasani miyasa zaki yaudari kanki inasan a duk inda kika kasance kisa aranki ke baiwa ce, sannan ki rike matsayin ki da darajar ki, Ƴata ki daina faɗar wannan maganar daga yau kisani zakaran da Allah ya nufa da cara komai wuya sai yayi, kinji Ƴata kiyi hakuri haka Allah yaso ya ganki insha Allah zaki zama mai daraja koda bamu raye kinji yanzun ki kara hutawa zanje kiran da uwar dakina kemani."
Gyada mata kai tayi alamar to.
har zata tafi Bahijja ta sake rike hannun Binta tace. "Umma daman wannan

Please Login or Register in order to submit comment