Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake bin kayan dake ciki, rasa abinda zaisa yayi yakai minti ukku a tsaye shi kanshi yai mamaki yasan ba halin shi bane ruwan ido wajen zaben kayan sawa, ɗan rausayar da kanshi yayi kaɗan yana murmusawa a hankali ya jawo wani dankareren farin yadi mai masifar kyau da santsi sannan ya ɗauko wata farar hula ta Sarakai mai ratsin baki baki jikin ta hakama ya ɗauko takalman Sarauta wanda suka gaji da ado ajikin su ya dawo gefen gado wanda ya kafeshi sa fitinan idanun shi ganin an linde shi yasha gyara aran shi yana mamakin yanda Bahijja ta iya aiki har haka ga kamshi yana ta tashi mai ratsa zuciya da gangar jikin mai shakar shi domin yasha turaren daki sai kuma ya gauraye dana jikin shi cikin nutsuwa ya gama saka kayan jikin shi sannan ya ɗaura hular shi saman tausassar suman kanshi a hankali ya saka takalman shi, daga karshe ya ɗaura wata farar agogo ta alfarma wadda glass dinta yake da duhun baki cikin kankanin lokaci MalikusSaif ya zama tamkar balaraben Saudia dan haduwa da ya gaji da yi, shi kanshi yasan yai kyau, mikewa yayi cikin nutsuwa da niyar fita falo dan yasa mu abinda zaici,Bahijja kuwa tana zaune ita kaɗai a cikin tamfatsetsen falon Malik da yaji kayan alatu irin na gidan Sarauta, sai kallan tsaruwar falon takeyi, ta buga uban tagumi tana son ta koma gida tunda tagama aikin ta sai dai ba dama tunda Sarauniya tace sai ta gama aikin yamma zata koma, ganin Jakadiyar Saifulislam tsaye akanta, cikin girmamawa ta sunkuyar da kanta tana mai gaishe da Jakadiya, ɗan ɗaure fuska tayi tace ma Bahijja.
"Tunanin me kikeyi inata sallama bakyaji? Anya zaki iya kulawa da bukatun Yarima.?" sake sunkuyar da kanta tayi tace. "Allah ya huci zuciyar Jakadiya naɗan....katse ta tayi da cewa. "Ya isa anshi kayan shi kije ki jerama shi su cikin wardrofe dinshi daga nan kije madafa inda ake kula da abincin Yarima ki anso mashi nasan Lokacin cin abincin shi yayi ina fatan kin gane." sake jujjuya kanta tayi tana cewa."eh nagane." juyawa tayi da kayan MalikusSaif a hannun ta da alama daga wanki da guga suke dan sungaji da tsaruwa, a hankali take tafiya dasu a hannuwan ta duka biyun sannan ta rungume su a kirjin ta har ta isa kofar dakin, tsayawa tayi tana shawara taya zata tura kofar dakin ga kaya a hannuwan ta kuma tasan da Yarima yana kusa kilan da ya taimaka ya bude mata kofar, dubara ce ta faɗo mata hakan yasa ta saka kafaɗarta da dukan karfin ta tana turawa da kafaɗar ta, shi kuwa Yarima Malik yunwa ce tafara damun shi duba agogon hannun shi yayi yaga har lokaci ya gota mashi, a hankali yasa hannuwan shi masu taushi ya ja handle din kofar dakin da niyar fitowa falo ita kam Bahijja sai kiciniyar tura kofar takeyi da karfi, yana janyowa yaji ta a jikin shi, kayan hannun ta wasu duk sun zube, a ruɗe ta duka kasa da sauri harda yan kwallan ta a idanun ta, tsoro ya addabi zuciyar ta tana tsoran kada Ya Malik dinta yai zatan da biyu take mashi hakan kamar dazun da yake bacci, shi kanshi ya karanci halin data shiga wanda shima yana jin zuciyar shi tana bugawa da sauri da sauri inaga ita da take zatan kilan ma ya hukunta ta daure wa yayi cikin nutsuwa yace. "Ki kula Bahijja kada kiji ciwo." da sauri ta kalle shi kwalla na shatata a saman kyakkyawar fuskar ta, mamaki ya gama mamaye zuciyar MalikusSaif shi awajen shi baiga abin kuka ba yasan bada manufa hakan ta faru ba, rasa abinyi yayi yana san ya lallashi Bahijjar shi wadda yake jinta tamkar wata tsoka a cikin jikin shi sai dai baisan ta inda zai faraba, a hankali ya zura hannun shi cikin aljihun rigar shi ya fito da wani lallausan handkicif ya mika mata, wani irin sanyayen kamshi turaren dake jikin handkicif dinne ya daki hancin ta lokacin daya miko mata shi dai dai saitin fuskar ta a hankali yace. "Share hawayen fuskar ki Bahijjaaah." yanda yaja sunan nata saida ta lumshe idanun kowane sashe na jikin ta saida ya amsa sunan da Ya Malik dinta ya kira dashi duk da ba wani canza shi yaiba amman ta gama imani ba wanda yakai Ya Malik iya kiran sunan ta kamar shi ya raɗa mata sunan da kanshi, cikin sanyin jiki ta amsa, ta kalle shi tace. "Ya Malik dan Allah kayi hakuri ban kulaba." rufe idanun shi yayi zuciyar shi na harbawa lokaci guda yarasa dalilin da yasa idan yana tareda Bahijja yake jin wani yanayi a tareda shi musamman idan ta ambace shi da Ya Malik, wanda yakejin hakan a kowane sashe na jikin shi har yake mata kallan kanwar shi kodan baida kanwa ko kani shiyasa yakejin hakan akan Bahijja? rashin ansar tambyar da yaima kanshi ne yasa ya bude idanun shi ya sauke su kanta take idanun su ya sarke dana juna, da sauri ta sauke nata idan, ɗan murmushi yayi sannan yace. "Kije ki aje kayan, ina falo kisamaman abinda zanci."
yana gama faɗar haka ya fita, cikin takunshi na mutunci da kamala atare dashi ita kuma ta ida kwashe kayan da suka zube sannan tafara jerasu a wardrofe dinshi daga bisani ta fito zuwa falo.....

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*Masarautar Waisu*


Gimbiya Ƙamariyya ce zaune saman kyatattar shimfidar ta wadda ta wadatu da kayan ƙawa na musamman kishingiɗawa tayi hadiman ta nai mata fiffita da wasu irin mafittai da suka kawatu da adon gashin ɗawisu, ɗan tagumi tayi kamar mai nazari, jitayi ana sanar da isowar Sarki Haishir, murmusawa tayi tanajin wani irin dadi aranta jin shigowar ɗan nata, baki ɗaya hadiman dake wajen suka zube suna kwasar gaisuwa,a wajewajen Sarki, daga masu hannu yayi hakan ya basu damar tafiy.
tankwashe kafar shi yayi cikin kulawa yace. "Barka sa yamma Umma." murmushi ɗauke a fuskar ta tace. "Angaishe da Sarkin Waisu, ɗa ga Sarki Lahazu jika ga Sarki Humzu barka da hutawa ɗana, ya fama da jama'a.?" cikin jin dadi yace. "Ba'acewa komai Umma." zama ta gyara sannan tace.
Mika yanke game da wannan makiyin Sarkin na Raifasu.?" numfashi mai zafi ya furzar sannan yace. "Ina nan ina shiri so nike indarjaza daular shi yanda ko sunan Haishir yaji sai gaban shi ya faɗi daga baya in halaka shi in dirkake shi daga shi har matar shi." wani irin shu'umin murmushi tasaki sannan tace. "Ni kaina bazan taɓa yafe jinin mijina ba dan haka ka ɗauki abin da mahimmanci cikin kankanin lokaci ka wulakan ta Baidulƙais." "kin san yanzun fa ya zama naka sasshe bare ince inyi fito na fito dashi saidai in halaka shi."
yaka rasa maganar yana wata irin dariya cikin mamaki gimbiya Ƙamariyya tace. "Kamar ya nakasasshe.?" "kinsan Yarima Malik ya sauke mashi hannu ɗaya daya kama wannan baiwar Bahijja, gaskia Umma jayyya dasu MalikusSaif ba dadi."
jinjina kai tayi alamar mamaki cikeda gadara tace. "Sarki Haishir kenan mu yanzun bata su muke ba ga wanda zamu darkake nan! kwara daya datse hannun tsinanne kowa ya huta." matsowa tayi kusa dashi daidai saitin kunnan shi tayi mashi wata magana take ya saki wani irin shu'umin murmushi mai cike da fassararori iri iri itama shi tayi nan sukaci gaba da kudurin su cike da zuciya......


_Masarautar Daborah_


Koda Bahijja ta isa madafa wani wajene na musamman inda ake girka abincin Yarima Malik da iyayen shi, idan kuma ka ƙara shiga daga ciki nanma wajene inda ake girkama sauran yan fada abinci, tana shiga ta iske wata matashiyar yarinya tana jere abinci cikin wani faranti mai ɗan karen kyau, tana gama shirya abincin Bahijja tace. "Ina abincin Yarima." nuna mata baiwar tayi, itako Bahijja ɗauka tayi ta tafi, cikin nutsuwa take tafiyar ta harta isa cikin ƙayataccen falon da Malik yake ciki, tunda Bahijja ta shigo Malik ke kallan ta, musamman yanda take komai cikin nutsuwa da kamala harta iso gaban shi ta tsugunna sannan ta'aje abincin, falat ta dauka ta zuba mashi cikin nutsuwa ta'aje mashi, ɗan kallan shi tayi sannan tace. "Ya Malik ga abincin na zuba." kallan abincin yayi sai dai bai mashi ba, amman baiji zai iya cema Bahijja bai mashi ba, tunda ita ta kawo shi da kanta, ɗan rausaya kai yayi a hankali sannan yafara cin abinci sakwara ce da miyar ganye taji kifi ba kaɗan ta ƙayatu ba, itako Bahijja gefe takoma tana wasa da yatsun hannun ta, cikeda farin ciki daya bayyana a saman kyakkyawar fuskar ta, shiko ɗibowa yayi kadan yakai bakin shi a hankali yake taunawa, ji yayi ya fitar mashi arai, kallan Bahijja yayi wadda ta shagala da wasan da takeyi dan har yanzun Bahijja bata daina wasannin ta na yarin ta ba, shi har mamaki yakeyi idan yaga tana wasa, magana yai mata sam bataji shiba, sake kiran sunan ta yayi wanda idan baka nutsuba ba zakaji me yace ba, hakanan taji jikin ta yabata kamar kallan ta yakeyi, a nuste ta ɗago kanta suka hada ido, saita samu kanta dayin murmushi, sake sunkuyar da kanta tayi, jitayi yace. "Kedai bazaki bar wannan wasannin ba ko? Baki ganin kullin kara girma kike.?" a shagwaɓe ta ya tsine fuska cikin siririyar muryar ta mai ɗan karan dadi tace. "Ya Malik nifa yanzun baniyin wasa, tunda narabu da kawaye na su Zainab da Indo, nan kullin Umma ke hanani wasa dan Allah kasiyoman yar tsana insamu ƙawa."
ta karashe maganar tana cinno ɗan karamin bakin mai masifar ɗaukar hankali da kyau, shi kanshi bugewa yayi yana kallan bakin nata yanda yake juyawa cikin nutsuwa, jin yayi shiru yasa ta kara marerecewa tace. "Dan Allah Ya Malik karkace bazaka siyamin ba." ɗan gyaran murya yayi wanda baisan mitake cewa ba dan yarasa mike damun shi cikin yan kwanakin nan cikin kulawa yace. "Mikikeso asiya miki.?" langaɓar da kai tayi sannan tace."ɗiyar baby nikeso." baisan sadda ya murmusa ba, cikeda shagala yace. "Keko miya haɗaki da ƴar baby yanzun kin girmi wasa Bahijja." batasan ta makale kafada ba, cikin kankanin lokaci ta shagwaɓe kamar yanda takema mahaifin ta dan Abban ta duk da yake bawa amman yana masifar son ƴar tasa da kaunar ta, fiye da zato, cikin shigar shagwaɓa tace. "Dan Allah Amintacce.....sai kuma tayi shiru, take yakara mata kwarjini da haiba, sunkuyar da kanta tayi, kiran sunan ta yayi, a hankali ta ɗago kanta tana kallan shi yace. "Anshi abincin kici." girgiza kai tayi alamar ta koshi, yanda ya tamke fuska yasa ta ansa jujjuya abincin tahau yi, jitayi yace. "Maida hankali kici." ɗiba tayi takai bakin ta cikin nutsuwa take taunawa tana hadewa, wani mugun dadi taji tunda take bata taɓacin abinci irin shiba, lumshe idanun tayi tanajin dadi, Shiko ido ya zuba mata yana karajin tausayin ta, a hankali tace, amintacce kaine farkon wanda yafara ciyar dani jin dadin rayuwa kamar kowane ɗan Adam a duniya, yanda tai maganar azuci saida yajita a zahiri ba tareda ta saniba, shiko a ranshi cewa yayi, Bahijja kenan insha Allah keda iyayen ki sai kunzama mutane masu daraja a idan duniya.....yana cikin sakar zuci kowa da abinda yake sakawa sukaji sallamar su Huzaifa da Yazid lokacin ya ɗauki ruwa a kofi ya bata, ansa tayi tana mai sunkuyar da kanta kasa cikin zazzakar muryar ta tace. "Allah yakara maka girma da nasara Allah yatai maki Yariman Daborah Yarima mai adalci nagode da karamci Allah.....sa hannun shi yayi saman lip dinshi alamun tai shiru, suko su Huzaifa tsaye sukayi suna kallan su, kallan kallo suka dinga yima juna, ganin hakane yasa Bahijja tashi, tayi wani corridor bayan ta gaidasu cikin girmamawa, jitayi yace. "ɗauki abincin nan."dukawa tayi ta ɗauka sannan ta tafi, kallan shi sukayi baki ɗayan su cikin halin ko in kula yace......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*
_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم




Episode 51&52



"Yadai, lfy kuke mani wannan kallon har haka.?" yar karamar dariya sukayi baki ɗayan su, hakan yasa Yarima Malik zauna wa yana kallan abokan nashi da tuhuma, suma sun fahimci irin kallan da yake musu, Huzaifa ne ya ɗauki ayaba yana ɓarewa a hankali yasa abaki ya balla yana mai kallan MalikisSaif daya kafe shi da kallan tuhuma, saida ya haɗe sannan ya kalli Yazid yace. "Yariman Daborah kenan yanzun tare tace haka.?" rausayar da kai MalikusSaif yayi kamar baisan magana yace. "Minayi kuma naga kunai mani wani kallo." Yazid ne ya karɓe da cewa. "Kaima kasani daman Bahijja tafara maka aikin kenan.?" ɗan karamin tsoki yayi kana yace. "Wai daman akan wannan abun kuka tsareni da kallan tuhuma? eh tafara." komawa yayi ya kishingiɗa bai kuma cewa komai ba,mamaki fal a fuskokin su, yanda Malik ya nuna abin kamar ba wani abu bane a wajen shi, cikin kufula Huzaifa yace. "Ohwo nagane anzo wajen shiyasa ka daina bi takan mu, burinka ya cika na shekara da shekaru ko.?"murmusawa yayi ganin Huzaifa ya ɗauki abin da mahimmanci yace. "Huzaifa kenan kuna bani mamaki yanzun akan hadima zaku nuna bacin rai dan ban gaya maku ba.?" "haba MalikusSaif karfa kaman ta baka da abokan da suka fimu kuma a iya sanin mu baka taɓayin hadima ba dan ra'ayin kanka, saikan Bahijja kai kazabe ta kuma kowa yaga yanda akasha artaba akanta, taya baza muji haushi ba, idan baka sanar mana ba."cewar Yazid ya karashe maganar yana kallan Malik, rankwafar dakai yayi ya ɗaura hannun shi saman keyar shi yana ɗan jijjuyawa ya ɗanyi kara kaɗan kas, cikin kulawa da aboki yake ba abokan sa musamman masu mahimmanci a gareshi yace. "Naji amin afuwa Huzaifa maida wukar naga sai hararana kake, kusan wani abu kuwa.?" baki ɗayan su sukace Aaa saika faɗa, gyaran zama yayi sannan yace. "Ni kaina bansan Bahijja zata fara yimin hidima ba, saidai nata shi daga bacci nagan ta harta fara yimin aiki, dan na fidda rai ma daga ita baki ɗaya, shine zakuzo kuna fushi da masoyin ku kuma aminin ku, hakan ba daidai bane." dariya sukayi baki ɗaya ganin yanda ya karashe maganar yana mai nuna damuwa, Huzaifa yace. "Bakomai fa muma harda tsokana, saidai yaka mata ka kara hadimai gaskia, wa'anda zasu dinga gyaran falo da sauran wurare ita kuma Bahijja saitaji da gyaran ɗakuna da abincin ka." saurayar dakai yayi alamun zai duba, "nima abinda ke raina kenan kaga yarinya ce Bahijja ba mamaki aikin yai mata yawa." cewar Yazid, nan ma sake saurayar dakai yayi alamun gamsuwa, ''yaushe zamu shiga kasuwar Zarsu.?" "bansani ba." ya bada amsa atakaice, kallan juna su Huzaifa sukayi sunga komai ya sauya musamman magana sun san hali yan rashin yin maganar sun iso, aran Yazid kuwa cewa yai sai kace mai jinnu, a zahiri kuwa yace. "Yadai kamata muje ran gadi kasan kasuwa ce mai daraja dakeci ashekara kuma kaga kalkashin ikon wannan Masarautar nan take." cikin kosawa da maganar Yarima Malik yace. "Hakane." "shikenan zamu kaima Matawalle gaisuwar ban girma kasan jiya akace yadawo daga tafiya." sake saurayar dakai yayi baice komiba.
"bazabkaje bane kayi shiru.?" cewar Huzaifa, a hankali yace. "Yanzun zakuje ko kuwa.?" "eh mana yanzun shiyasa muka biyo maka." "kubari sai anyi la'asar." sake kallan juna sukayi sannan suka kara maida kallan su akan shi ya kara jadda musu hakan,ta hanyar jinjina kai, da toh suka amsa, sannan kowa yai shiru alamun da abinda kowa ke sakawa aran shi, shiko MalikusSaif tufa yafara ci, suna cikin zaman kurame danma tsakanin Yazid da Huzaifa suna dan taɓa fira kadan kadan sukaji sallamar Bahijja, amsawa sukayi wanda tunda ta shigo kan Malik na kasa bai kalleta ba, suko ita suke kallo harta tsargu, isowa tayi gaban su ta tsugun na cikin nutsuwa tace. "Ya Malik...sai kuma tai shiru tace. "Ranka shidade, daman ina san zanje gida inada uzuri." a hankali ya ɗaura idan shi kanta, gani yai takara mashi kwarjini cikin tausayawa yace. "Saikin dawo." tayi mamaki dan batai zatan samun shi da sauki har haka ba, cikin jin dadi tace. "Nagode, kutashi lfy." harta juya ta tafi suka tsinkayi kiran sunan ta da MalikusSaif yayi, cak ta tsaya sannan ta juyo har gaban shi ta duka tace. "Allah ya taimaki uban gida na gani." mika mata wata leda yayi ba tareda yayi magana sai dai da ka kalli fuskar shi kasan akwai mataki a cikin ta, hannun Bahijja na kyarma ta ansa ta bude baki zatayi magana kenan ya ɗaga mata hannu dolen ta ta hadiye kalaman ta, mikewa tayi ta tafi cikin nutsuwa shiko cigaba da hidimar gaban shi yai, kiran salla sukaji anayi hakan yasa suka mike suka shiga ciki kowa yai alwalla sannan suka dunguma zuwa masallaci.


_Danjin Gamki_


Sarki Baidulƙais ne gurfane agaban babban dutsin saman kuka da ka ganshi zakasan akwai tarin bakin ciki a cikin zuciyar shi kuma yana cikin alhini a saman fuskar shi, wani abune gafen shi girke shidai ba mutin ba kuma ba aljan ba, sai wani zabgegen bindin shi a shinfiɗe, kallan saman dutsen yayi yana al'ajabi wai yau shine kasan dutse saɓanin da daya ke hawa har sama baida shamaki dashi, wata iriyar amon magana yaji a cikin kunnuwan shi yaji ana cewa. "Ka tashi kabar wannan wajen bakada anfani a wajen mu, tunda kagaza samamawa dodon Gamki jinin Bahijja ta hanyar kusantar ta, ka gaza Baidulƙais." hannun sa guda ya toshe kunnan shi dashi ya jujjuya kai alamun aaa cikin sanyin murya da kaɗuwa yace. "Kada kaimin haka ya shugabana kai kadai karagemin arayuwa, na rasa Bahijja na rasa ɗana na rasa sashe na garkuwan jikina kuma yanzun kace zaka barranta agareni katai....
cikin tsawa wadda hartar watsin wuta ke fita abakin Sarrilƙus yace. "Kaimin shiru maganar ka bata tasiri a cikin kunnan Sarrilƙus dan haka kayi gaggawar maido mana zoben hannun ka, sannan dole kasauka bisa karagar mulki sannan, rashin bin wannan umirnin zakaga abinda bakai zato ba, kasan abinda zan iya hakama kasan abinda bazan iya ba, ɓaceman da gani." zaiyi magana kenan Sarrilƙus yasa aljani ɗan tsitu mai kula da zoben hannun Baidulƙais ya ɗauke shi, saidai ya waiga ya ganshi cikin wani ɗaki na tsafi wanda yake cikin Masarautar Raifasu, wani uban gunji kuka ya saki yarasa abinda ke mashi dadi a duniya, wannan kenan

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Waisu kuwa, Sarki Haishir ne da jama'ar shi, suke shawarar mutanen da zasu zaɓa domin zuwa cin kasuwar *Zursu* dake cikin birnin *Daborah* , cikin izzah ta sarauta dake ɗawainiya da Haishir yace.
"Sarkin taska da uban bayi, sai galadima, zaku jagoranci jama'ar mu zuwa kasuwar Zursu sai dai fa'da bata lamunce ba daidai da cacar baki ta haɗa ɗaya daga cikin ku da jama'ar Sarauniya Zulaiƙa, cin arziki mukaje shi yaka mata muyi mu dawo gida, zuwa yanzun kowa yasan ba Masarautar Daborah bace damuwar muba tunda suma batamu sukeyi ba, anyi walkiya munga haske zuwa yanzun wanda ya dade yana ikirarin shine masoyin mu ashe shine matsalar mu kuma ashe makiyin mune, wannan kuwa lokaci kaɗan na dibar mashi cikin doron duniya zan kawar da rayuwar Baidulƙais da karfin ikona da izzah ta da gadara ta karagar mulkin Waisu nasan kowa ya gane karatun? kazu iya tafiya zuwa gobe dan kuje da wuri ku dawo da wuri, ina fatan Gurfanai yatai makeku." cikin jin dadin kwarin guiwar Sarkin nasu suka tafi kowa yanajin dadi a cikin ranshi.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Kodasu MalikusSaif suka gama sallar la'asar ba inda suka wuce sai wajen Matawalle wanda yake aboki kuma amini ga Kangiwa wato Saifulislam, shima shararren ɗan kasuwa ne fatauci yakeyi kasa kasa kamar Saifulislam, dan dai shi Saifulislam yana hutu sai dai ya tada yaran shi suje sunai mashi kasuwancin kamar yanda suka saba. suna shiga cikin kayataccen sashen Matawallen wanda ya gaji da haɗuwa musamman na kayan alatu na more rayuwa tayau da kullin, Matawalle ya kasance ɗane ga kanin baban Sarauniya Zulaiƙa wato Abdulhamid, sai dai shi Matawalle bai taɓa haihuwa ba wannan dalilin yasa ya ɗauki so mai girman gaske ya ɗaura akan MalikusSaif wanda yake jikin shi tamkar ɗan da ya haifa na jinin shi, koda suka shiga hadimai ne ketakai gaisuwa wajen Yarima Malik da abokan sa, zama sukayi cikin falon,Matawalle cikin kamala, baiwar shi tazo tagaida su Malik sannan ta sanar ma matawalle zuwan su MalikusSaif, cikin kankanin lokaci ya fito daga cikin dakin shi yana mai ware hannayen shi hakan yasa Yarima Malik mikewa yaje ya rungume kawun nashi cikin tsantsar so da kauna irin ta dangin uwa da suke ma ɗan ƴar uwar su.
sunkai sakan shabiyar ahaka sannan suka dawo suka zauna a kujera ɗaya shi da MalikusSaif, ɗan rankwafawa su Huzaifa sukayi suka gaida Matawalle cikin sakin fuska da aminci irin na mutanen kirki ya amsa yana mai tambarya su Huzaifa ya mutanen gida, suka amsa da kowa lfy sake maida kallan shi yayi kan ɗan nashi wato MalikusSaif cikin kulawa yace. "Tabbas ɗana ya girma yanzun abu ɗaya ya rage maka Yarima."sadda kanshi MalikusSaif yayi yana murza zoben azurfar dake hannun shi, cikin kulawa matawalle yace. "Yakai shiru Yarima." sosa keya yayi yace. "Ranka shidade kai nike saurare."cikin jin dadi yace. "Kayi aure shine cikar kamalar ka da mutuncin ka akalla kakai talatin a duniya Malik bai kamata....jin tarin da Yarima Malik keyi shine ya katse ma Matawalle maganar shi da sauri ya zuba ruwa a kofa ya bashi da hannun shi yasha, cikin kulawa da tausayin ɗan kanwar tashi yace. "Sannu ɗana nadame ka da dogon surutu harka kware ko? namanta dan nawa bai cika son dogon magana ba." yakara she maganar yana shafa kwantacciyar suman kan Malik dake kwance gwanin ban shi'awa, ɗan kaɗa kanshi yayi sannan yace. "Bahaka bane Kawu kwarewa nayi insha Allah za'ayi hakan." suko su Yazid dariya ce suke danne sun tabbta ba karewar da Malik yayi kawai baisan zancen ne shiyasa ɗazun yace sai anyi la'asar zasu zo wajen matawalle dan bai tunanin zasu tadda shiba yasan kilan yana wajen mahaifin shi, kallan su Huzaifa Matawalle yayi yace. "Huzaifa nasan kunsan komai akwai wadda ɗan nawa yake nema." shiru Huzaifa yayi kanwar shice tafaɗo mashi arai saidai yasan shi Malik bai san Zahara'u nason shiba saidai yanai mata shiawar kasancewar shi mijin ta, amman yafison sai MalikusSaif din yana bukatar hakan, a zahiri ko cikin sanyin rai yace. "Allah yataimaki mai girma Matawalle babu gaskia sai dai kilan ko daga baya." cikin jin dadi yace."ka shirya sati mai zuwa zamuje wajen kanin mahaifin mu ka zabi matar da zaka aura, a cikin daular musulunci Sarki mai adalci da sanin yaka mata." zaro idanu Malik yayi waje cikin kiɗima yace. "Kawu akwai, kada mukai ga haka na fidda ta." baki ɗayan su suka haɗa baki wajen cewa wacece.?" shiko Matawalle dadi yakeji Malik yana da wadda zai aura suko su Huzaifa mamaki suke yaushe Malik yafara soyayya kowa da kalar abinda yake sakawa aranshi, shiko MalikusSaif mamaki yake taya harya furta wannan kalmar, cikin tuhuma Matawalle yasake cewa."kai muke saurare Yarima wacece surukar tawa?" baki ɗaya jikin MalikusSaif yai sanyi cewa yayi.......



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم




Episode 53&54



Yan kame kame Yarima Malik ya fara sannan yace.
"Hmmm daman ina nufin...jin sallamar da Saifulislam yayi shida matar shi wato Sarauniya Zulaiƙa yasa suka maida hankalin su kan kofar tareda amsa sallamar tasu, cikin ladabi suka sauka saman tausassan kafat dake shimfiɗe cikin katan falon Matawalle, suka zauna tare da tan kwashe kafar su, shima Malik ganin abokan nashi kasa yasa shi yun kurawa zai safko kasa, Matawalle ne ya rike mashi hannun cikin nashi da kallo suka bishi komawa yayi ya zauna gafen kawun nashi cikin girmamawa su Yazid suka gaishe su, amsawa sukayi Sarauniya Zulaiƙa take tambayar ƴaƴan ta nata lafiyar su, cikin girmamawa suka ce. "Lfy lau Ummu."
Saifulislam ne ya mikawa aminin nashi hannu

Please Login or Register in order to submit comment