Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗauki ruwa daga saman kan Bahijja ta dinga kwarara mata, ana labta mata bulalai ga kafar Sarauniya a saman Binta tana danna mata, ba abinda Binta kecewa sai. "Tuba take uwar dakina wannan girmanki ne an gaishe da mai dole bin umurnin ki wajibi ne Bahijja na tuba Allah yakara girma." itako Bahijja takasa furta uffan sai ambaliyar kwalla da suke ɗawainiya da ita, sallamar da sukaji itace tasa kowa ya maida hankalin shi don ganin mai shigowa, cikin kamun kai na marassa gaskia Sarauniya Zulaiƙa ta mike tsaye tace......





_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم


_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*



Episode 61&62



"Daman yanzun nike shirin zuwa sashen ka Abu Malik." baice komai ba saima karasowa ciki da yayi, cikin nutsuwa ya kalli Bahijja wadda idanun ta sukai jajir dasu yace. "Binta kamata kutafi gida." gaisheshi sukayi sannan takama ɗiyar ta suka tafi, wani kallo ta bankama su kama Bahijja tayi a sanyaye suka fice ya rage dashi sai matar tashi, zama yayi baice komai ba, itama zama tayi kusa dashi tana mai rike hannun shi cikin kula tace. "Abu Malik kayi magana mana bansan wannan shirun naka agareni." zame hannun shi yayi anata ya kalleta yace. "Yanzun naga kina cikin damuwa, kuma inada abinyi, zan koma sashina, domin yau inada baki masu mahimmanci." baijra cewar taba ya mike, itama mikewar tayi cikin rashin gaskia tace. "Anman inzakai baki ana sauran kwana ukku kake sanar dani miya canza hakan.?" "bakomai sabo da ni suka shafa, sai anjima."
jitayi zuciyar ta ta tsinke ta tabbata Saifulislam fushi yake da ita, sai dai dole taimashi uxuri zuwa wani lokaci.

Bayan sati biyu a Masarautar Raifasu kuwa Baidulƙais ne zaune a falon shi ya rasa inda zai saka kanshi yaji sanyi komai na rayuwa ya game mashi yana cikin tunani kawai yaga aljani ɗan tsitu ya bayyana agare shi cikin wata iriyar murya marar dadin sauraro yace "dama ka daina damun kanka ba abinda zai sauya dan haka yau dinnan wa'adin da shugaba Sarrilƙus ya dibar maka ya cika dole kabada zoben dake hannun ka, sannan zamu naɗa sabon Sarki daga cikin jama'ar mu dan cigaba da mulkar wannan daular tamu tunda kai kagaza."

Zaiyi magana kenan yaji kamar an shake mashi makoshi ga wani irin zugi da hannun shi kema shi sai kakkarwa yakeyi cikin tashin hankali yaji kamar anfisgar mashi hannu faɗuwa kasa yayi yana furzar da wani uban nishi kamar wanda yayi artaba da bijimin zaki haka ya dinga kakkarwa yana fidda wata irin kumfa abakin shi, yakai minti talatin yana fama da abu, ɗaya a hankali ya fara dawowa cikin hayyacin shi sai dai abin mamaki ya nemi ajani ɗan tsitu babu shi sama ko kasa, bai kula da hannun shi babu zobe ba, saida yaji zugi ya isheshi ya dubawa yaga ba zoben hannun shi ga wani irin sahun azaba ya dame shi yatsan shi yayi kore dashi, yana ganin haka ya fadi kasa dabas yasaki wani azababban kuka mai sosa rai kamar wani zautacce haka ya tashi da gudu ya faɗa cikin wani ɗaki na tsafin shi, yana neman wani abu da alama abune mai mahimmanci saida bai samu komai ba sai tarin kayan su na surkulle, ya cigaba da gwada sa'ar shi ko zai dace aljani dan tsitu ya bayyana amman ina yana ganin haka yasan baida sa'a Sarrilƙus ya datse duk wata alaka dake tsakanin su yanzun rayuwar shi itace abu na gaba da zasu bukata, anan ya zube yana gunjin kuka mai tsuma zuciya.

**************************************

A dajin Gamki kuwa koda aljani dan tsitu ya dawo daga aikin da uban gidan nashi ya sashi saka zoben akayi cikin wata kwallabar tsafi ba abinda ke cikin ta sai tarin jini da wasu irin halittu take zoben ya sauya kala, boka Sarrilƙus ne yasa aka rataye zoben saman wani hannun kuka wanda yake ɗauke da kayan tsafe tsafe iri iri cikin wata iriyar murya ya saki wata irin dariya wanda saida wani haske na tsafi ya dinga tartsatsi a cikin dajin gamki, yace. "Angaishe ka aljani dan tsitu aikin ka yana kyau yanzun abinda ya rage shine rayuwar Baidulƙais tunda ya gaza shayar da dodon gamki daga jinin Bahijja ya gaza ya bamu kunya baida anfani zamu kashe shi, mu tura cikin jama'ar mu su cigaba da mulkin Masarautar Raifasu, hhhhhahhhhh!!! Komai na dajin gamki gilgiza yake jin dariyar da Sarrilƙus keyi wanda yana kwashe sama da shekara kafin yayi irin ta ko makamanciyar ta alamu ya nuna ranshi ya ɓaci matuka kuma zai iya aikata komai akan Baidulƙais dama Masarautar Raifasu baki ɗayan ta


~Aidaman haka rayuwa take duk abinda ba hasken addini a cikin shi lallai bazai ɗaure ba yake watsewa, Allah ya dauwamar damu bisa addinin mu~

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Tunda Bahijja taje aiki wajen Malik take ganin yanda yana yin shi ya sauya da alama yana cikin damuwa marar misaltuwa, hakanan taji itama ta shiga cikin damuwa, saidai bata da hurumin da zata tambayi uban gidan nata damuwar shi, cigaba da aikin ta tayi, shiko MalikusSaif yana kishingide bisa tattausar kujerar shi mai masifar kyau da ado yana tunanin yanda zai bullowa lamarin mahaifiyar shi akan Bahijja, a hankali tazo tana gyara tsakiyar falon dan batasan tai motsi mai karfi da zai jagulama uban gidan nata lissafi dan taga tarin damuwa a cikin kwayar idanun shi dukawa tayi ta wanko wani karamin towel tana goge wani table dake tsakiyr falon, shiko a hankali ya bude idan shi jin zuciyar shi ta buga ranshi ya bashi tabbas Bahijja na kusa dashi dan yafara fahimtar duk sanda Bahijja zata kasance dashi yana shiga wani yanayi ko na shauki ko kuma na son ganin ta akoda yaushe a tare dashi, sai dai yarasa dalilin haka kuma kullin lamarin kara gaba yake ba baya ba, maganar Huzaifa ce ta dawo mashi sabuwa a cikin kunnuwan shi girgiza kai yayi alamun bata yuyuwa sai dai kawai tausayn tane yai tasiri a cikin zuciyar shi kamar yanda mahaifiyar shi take cewa a hankali ya bude baki zaiyi magana sai kuma ya fasa, cigaba da kallan ta yayi ganin yanda take aikin ta cikin nutsuwa da sanin ya kamata, haka ta ida goge ko ina sannan ta tafi.

Bayan wasu awanni MalikusSaif ne ya gama wanka ya shirya cikin wasu kaya masu masifar kyau da daukar hankali na gidan Sarauta wanda ya wanci ba masu amfani dasu sai Yarima, shima Yariman wanda ya ansa sunan sa ma'ana Yarima mai jiran gado a hausan ce magajin Sarki, ba karamin kyau da karbuwa kayan sukai ma MalikusSaif ba Maroon color ne sai ratsin golden yasha ado da zaiba itama golden sai takalman shi suma golden sai agogon hannun shi masu asirkar golden haka dai gayama kimtsawa ya fito sak a MalikusSaif dinshi, fitowa yayi falo ya zauna, iske Bahijja yayi ta jinjina jikin bango da alama ta gaji ga ɓarawo bacci na neman ɗauketa, shiko murmushi yayi a ranshi ko cewa yayi kuruciya kenan jibi yanda take gyangyadi daga zaune maimakon ta koma gida ta huta, komawa yayi saman kafat dake linde a gyare yasha kayan alatu iri iri ɗan gyaran murya yayi a firgice Bahijja ta ware idanun ta, ganin shi tayi zaune yadan kishin giɗa tashi tayi a nutse taje ta duka ta gaida shi, fuska a sake ya amsa, tashi tayi taje tafara kawo mashi kayan abincin shi a nutse ta aje, cikin kulawa ta ɗauki flat tace. "Ranka shidade mikake bukatar ci.?" girgiza mata kanshi yayi alamun ya koshi, cikeda da damuwa tace. "Ya Malik daga gani akwai abinda ke damunka dan Allah miyasa meka.?"
yaji dadin yanda Bahijja harta fara gane yanayin shi, cikin kulawa yace. "Bakomai kanwata karki damu, ke kinci abinci.?" da zatace aa sai kuma ta tuno da abinda Sarauniya tai mata, a hankali tace eh naci, sai kuma takara cewa. "Dan Allah indai ba abinda ke damunka kaci abincin?" badan yana son cin komai ba sai dai baisan tashiga cikin damuwa, gyada kai yayi, hakan yasa tace. "Mikakeson ci?" a atakaice yace. "Duk abunda yai maki ina son shi." bude farfesun yan ciki tayi sai farar shinkafa ta zuba mashi ɗan kima sannan ta zuba mashi ruwa a kofi, a hankali ta miko mashi, murmushi ya sakar mata, yasa hannu zai amsa kenan sai yaga hannun ta wani irin sahu ga jini ya kwata sosai, baisan sadda ya rike hannun ba, cikin damuwa yace. "Bahijja miya sameki a hannu?" da sauri ta girgiza kai alamun ba komai, itako yanda ya rike mata hannu cikin tattausan hannun shi saida taji wani iri har cikin kwakwalwar ta, da sauri ya sake ta ganin ta zubama hannun nashi ido, hakanan ya samu kanshi dajin haushin kanshi, daya riketa, still yana tambayar kanshi abinda ya samu Bahijja a saman hannun ta, a hankali yafara cin abincin badan yanajin ddin shi ba, itako gefe ta koma tanajirn uban gidan nata yagama cikeda da tunani a cikin ranta,shima sake saken zuci ya dingayi.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

jin ana sanar da shigowar mai girma Matawalle gyara zaman shi yayi Yarima Malik yayi, koda yazo zama yayi kusa da ɗan na shi, cikin sakin fuska ya gaishe da kawun nashi cikin girmamawa, Matawalle yace.
"ɗana gani nazo da kaina, naga lokaci ya nata kurewa abubuwa suna karaja baya, kuma kai bakace komai ba, har zuwa yanzun ya ake ciki akan maganar fidda mata?"
da sauri Bahijja dake can gefe ta kalli Matawalle samun kanta tayi dajin faɗuwar gaba, shima Malik ita ya kalla wadda ta kasa ɗauke idanun ta akan shi, kallan Matawalle yayi ya sadda kanshi kasa cikin ladabi yace. "Allah yataimaki Matawalle daman ina son nan da kwana ukku inzo maka labarin da kaina inba dam....katse shi Matawalle yayi yace. "Wane irin kwana ukku Malik? Dafa sati nabaka, shine kaki maida hankalin ka akan lamarin nan ya kake so ayi yanzun?" gyara zaman shi Malik yayi yace. "Eh na fidda Kawu kawai dai inajiran nagama tantance wani abune shiyasa." "Aaa Malik ya isa haka ka shirya jibi zamuje wajen Kawun mu Masarautar da tasan kima da daraja ta dan Adam daular musulunci sai ka zaba matar aure a can hakan zaifi." Bahijja dake jin duk abinda ake faɗa tashi tayi ta shiga ciki, jitayi wani irin kasala da ciwon kai ya dirar mata, zuwa tayi ta zauna wajen wani corridor tanajin zafin maganar da Matawalle kema Yarima Malik.
"Dan haka ka shirya bansan musu, nasan nan ba wadda zaka fidda amman nasan can muddin kaga zuri'ar shi akwai addini zasu shiga cikin zuciyar ka sosai, fatan Allah yai mana jagoranci." da ameen Malik ya amsa dan baisan yana musu da Matawalle kodan so da kaunar da yake nuna mashi kamar dan cikin shi, bai jima ba yaima MalikusSaif sallama ya tafi kasancewar yana sauri akwai wani taro na yan kasuwa da zai halatta, yana tafiya Malik ya tashi yaga ba Bahijja a tunanin shi ta tafi gida tafiya yayi zai shig lambu dan hutawa, can ya hangi Bahijja ta zauna kamar mai tunani cikin kulawa yace. "Mikikeyi nan?" a daburce tace. "Bakomai, daman inasan zanje gida Ya Malik banjin dadi." cikin tausayawa yace. "Miya sameki?" "kaina ke ciwo." dan shiru yayi sai kuma yace. "Allah yabaki lfy kije ki huta." godiya tai mashi sannan ta tafi jitayi baki daya sashen na Malik ya fitar mata arai haka ta koma gida ta kwanta lokacin bata tadda kowa cikin gidan ba, sake sake ta dinga yi a cikin zuciyar ta tana tambayar kanta batasan tanayi a zahiri ba tace. "Wai shi wannan mutumin mi ruwan shi da wadda Ya Malik zai aura, wannan wane irin abune, shi ba wadda, zai aura amman andami mutun mtsw, sai kuma tace keko Bahijja mi ruwanki da wadda Ya Malik zai aura ba Abba yace kidaina shiga sabgar da ruwanki ba? abin haushi ma......jitayi Mairo tace. "Ke Bahijja mi ruwanki da wadda iyayen Malik zasuyi mashi zabi, ba ruwanki 'yata kidaina damuwa da duk abinda bai shafeki ba." murmushin karfin hali tayi tace. "Inna ba haka bane inaga kamar dole sukeso suyi mashi." "keji beki dan Allah da karam bani ba ruwanki da wadda ta dace da rayuwar shi kibarma wannan maganar kada Abbanvki yaji ki." dan taɓe baki Bahijja tayi sannan suka kama wani labarin ita da Mairo sunajin dadin su, take ta nemi ciwon kan da take fama dashi ta rasa.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

A Masarautar Raifasu kuwa Jakadiya ce a cikin gidan yari, sai dai ba abinda ya sauya dangane da addinin ta, kullin sai tayi sallolin ta da duk abinda takeyi a boye yanzun kuwa a bayyane takeyin shi hakan ba karamin sosa masu rai yakeyi ba, saidai basu da wani zabi da yawuce su samata ido tunda Sarki Baidulƙais ya hana abugeta ko musguna mata, a wajen Sarki Baidulƙais kuwa tashi yayi ya shirya cikin kayan shi na Sarakai ya doshi dajin Gamki wajen Sarrilƙus dan nemama kanshi masalaha a wajen uban gidan nashi yana shiga uban dajin na Gamki bai ganin komai sai duhu sai dai zaka iya ganin gaban ka yana cikin tafiya a cikin shi yaji wata irin kara a wajen da yake, juyawar da zaiyi yaga wani abu ya tunkaro shi a guje da sauri yai.....





_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*



Episode 63&64




yai wani uban tsalle ya koma gefe yana fidda wani uban gumi ga tsoro daya gama addabar rayuwar shi dandanan numfashin shi ya fara daukewa, jiyayi anyi wurgi dashi bisa wani dutsi, yunkurawa yai zai tashi yaga wata bakar guguwa ta tunkaro shi bai kuma sanin inda kanshi yake ba, sai dai ya ganshi gurfane a gaban Sarrilƙus ga wasu irin tafkatafkan macizai da kunamai kamar na karfe tsabar bakin da suke dashi daga gefe kuma ga wata halitta nan rabin kanta na mutun rabi kuma na dabba, sai bindin ta na dabba amman kafarta ta mutunce, a tsorace ya kalli Sarrilƙus wanda ko kyan gani baida shi, yayi bakikkirin da kagan shi kasan baida digon imani ko kadan, cikin wata muguwar murya wanda duk wanda ya saurareta yasan ba sauki cikin lamarin yace.
"Kai Baidulƙais waya baka ikon shigowa dajin Gamki na fahimci yanzun ka manta matsayin ka a wajen mu ko? yanzun zaka banbance tsakanin aya da tsakuwa." kallan aljani dan tsitu yayi, yace. "Koya mashi hankali."
buga tsalle yayi ya ɗane saman jikin Baidulƙais ya kafa kanshi jikin wuyan shi yafara sha mashi jini shiko cikiniyar anshewa yafara amman ya kasa sai kakkarwa jikin shi keyi, ba abinda ya fado mashi arai sai maganar Jakadiya, sannan ya tuna da Bahijja lokacin da yaji ta fadi wata kalma, daya tambaye ta sai tace ba komai, jikin shi na tsuma ya furta kalmar da yaji Bahijja ta ambata yace. *"A'uzubillahi minasshatanir rajim."*
da sauri aljani dan tsitu ya fasa uwar kara ya sauka saman Baidulƙais shima Sarrilƙus jiyayi kujerar shi ta gilgiza tsoro da fargaba suka mamaye su cikin kankanin lokaci, cikeda mamaki ya kalli Baidulƙais yace. "A haka kake so mu yafe maka bayan ka bar addinin mu?"
shi kanshi Baidulƙais din mamaki yake dan ya fadi wannan kalmar duk bala'in aljani dan tsitu amman ya gudu, cikin dakewar murya yace.
"Ya kake so inyi bayan na baku hakuri na nemi afuwa agreku kun juyaman baya nazo dan inyi mubaya'a ku maido mani da zoben mulkina amman kunki nema kuke ku kasheni kenan?." wata uwar tsawa Sarrilƙus ya kwaɗama Baidulƙais har wata tarwatsin wuta ke tashi a cikin bakin shi ga idanuwan shi sunkoma tamkar garwashin wuta ba kyan gani yace.
"Yau saina kashe ka tunda harka rage karfin alkadarin tsafina ta hanyar ambatar wannan kalma kasa kwatan duhun dajin nan na Gamki ya rage ka tozartani kaci amana ta ya zama dole yau din nan ka bakunci barzahu." hannu yasa ya nuna macizan nan da sauri suka kaima Baidulƙais wata irin cafka, saida ya tsorata har wani sauti suke fiddawa suna kiran shu shu shu, haka suka biyo shi ga kunamu suna ta halbin iska sai ja yake da baya baya, tunawa yayi sadda suka kama Sarkin Burga na Ƙaisu yaga yanda wa'annan kunamun da macizan sukai mashi raga raga, wani irin tsoro ya sake rufe shi ga wata zufa dake tsattsafo mashi ganin sun kusa kama shi ya rufe idanun shi yana kiran.
*A'uzubillahi minasshatanir rajim!*" Abinda yake ta fada kenan, wata uwar tsawa Sarrilƙus ya saki macizan suka dinga komawa baya suna bacewa da kunamai, shi ko Sarrilƙus sai gabza ihu yake ganin alkadarin shi na neman lalacewa ya fasa wani irin sauti saiga wani bakin aljani ya baiyana nuna mashi Baidulƙais yayi wanda zuwa yanzun idanun shi abude yake yana ganin abin mamaki yanda suke ihu duk sun fita cikin hayyacin su, wata bakar guguwa ce ta figeshi gani yai anyi wurgi dashi cikin cibjin yayi kusa da dokin shi cikin tashin hankali wannan aljani yace.
"Kul karka sake shigowa wannan dajin mun barrantaka a cikin mu, inba hakaba zamu halaka, huhhhhhahh!" ya bace shima a sanyaye ya hau bisa dokin shi ya nufi hanyar Masarautar shi yana mamakin yanda a da baijin tsoro ko shakkar dajin Gamki amman yanzun ya razana ko dan baida zoben Sarrilƙus a hannun shine ashe haka mutane keji idan suka shiga cikin dajin Gamki? da wannan tambayar ya kama hanyar komawa Masarautar Raifasu cikeda al'ajabi mai tarin yawa a cikin zuciyar shi.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Cikin Daborah kuwa Yarima Malik ne wajen mahaifin shi suna tattaunawa yana mashi tambayoyi cewa yayi.
"Malik yaka mata ka fidda matar aure kamar yanda muke bukata ka tsaya ka fidda wadda kasan kana so, ɗana kada ka bari lokaci ya kure maka, inkana ganin baka iya fada mana wadda kake so ka sanarma Huzaifa mana." sadda kanshi MalikusSaif yayi yana saka abubuwa a cikin ranshi cikin girmamawa yace.
"Abbuh inaji kamar akwai abinda ke bibiyata dan ina narasa sukuni lokacin da wani abu mai mahimmanci ke tare dani sai insamu kaina cikin fargaba da yai nisa dani kuma Abbuh sai inji ina tausayi da kewar abun sai dai har yanzun zuciya ta tana karyata hakan duba da rashin kima ko darajar abin a idanun mutane masu daraja, saidai Abbuh kullin ina nafilfili ina mikama Allah kukana yaimani zabi da mafita akan wannan al'amarin wanda wasu kema wata fassarar ta daban."

Murmushin manya Saifilislam yayi yana maijin dadin abinda ɗan nashi ya fada duk da shima yana fargabar al'amarin cikin kulawa yace.
"ɗana Malik ka rufe sirrin zuciyar ka gudun matsala duk da har yanzun bakasan matsayin lamarin nan a cikin zuciyar kaba, saidai mubarma ikon Allah komai, namu addu'a saidai duk da haka ka duba mata a cikin jama'ar mu na daga yan uwa abokan arziki da saran su." "toh Abbuh insha Allah, saidai Matawalle yasake yimin maganar da kanshi ni kuma ina jin nauyin Matawalle."
"Karka damu Yusuf baida matsala, kuma zai zama jigonka a cikin al'amarin ka yana da saukin hali karka damu, saidai duk abinda zakayi ka duba yanayin mahaifiyar ka, ka kara yimata biyayya." rausayar da kanshi yayi yace. "Toh Abbuh nagode." itako Sarauniya Zulaiƙa tunda suke maganar tanajin su a yanzun ne takaraso da sallamar ta saidai tana mamakin al'amarin da ɗan nata yake boyewa ko kuma shige mashi duhu da yake ikirarin yayi a nutse tace. "Ɗana karabi da zuwa sashena ko lfy?" "bakomai Ummu zancen Matawalle ne ya shamin kai." murmushi tayi cikeda jin dadi tace. "Yaka mata ai kasan yaya, na son yaga kayi auren nan, shiyasa."
shima murmushin karfin hali yayi yace "insha Allah ina kokari." da haka kowa yai shiru na sakanni, nan MalikusSaif yaima iyayen nashi sallam ya fita cikin nutsuwa yake tafiya

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Koda Baidulƙais ya koma gida direct kewaye ya shiga yayi wanka ya dawo yarasa abin yi ga wani zazzabi da yagama rufe shi lokaci kalilan cikin ranshi ko yana mamakin addinin su Bahijja gaskia akwai abu mai girman gaske a cikin wannan addini, mikewa yayi ya tuna da maganar Jakadiya tai mashi da sauri ya saka riga fitowa yayi ya kalli mai kula da shige da ficen shi yace. "Zanje gidan yari yanzun nan."
take mashi baya yayi shida wasu dogarawa suka nufi cikin yarin Masarautar Raifasu.

suna isa cikin gidan Yari mai kula da gidan Yarin ne ya rugo da gudu, ya tari Sarki Baidulƙais kujera ya kawo ya aje mashi yana mashi sannu da zuwa, Sarkin Zagi ne ya fara koda Sarki Baidulƙais, yana cewa. "Gyara zaki, gyara zinki ranka shidade Sarkin Raifasu barka da zuwa gidan Yari mai tarin tarihi, gurfanai ya taimakeka."
wani mugun kallo ya bankama Sarkin Zagi cikin dakewa yace a fiddo mashi da Jakadiya, koda aka fiddo da Jakadiya wani irin dadi taji ya kama ta, dukawa tayi a gaban Sarki Baidulƙais tace. "Ranka shidade barka da zuwa Jamra na gaisuwa." gyada kai yayi cikin kulawa yace "Jamra ina neman afuwarki akan abinda naimaki tabbas Jamra na tabbata kece kadai wadda zata kawo mani haske a cikin rayuwata sanadiyar Bahijja, anyi walkiya naga haske Jamra kowa ya gujeni harta Sarrilƙus, ya juyaman baya Jamra ina cikin tashin hankali marar misaltuwa."
cikin jin dadi da samun cikakkiyar kwarin guiwa tace. "Tabbas Bahijja tayi gaskia addinin musulunci addinine na gaskia kuma yana tareda nasarori iri iri tabbas naji dadi da Allah ya tashi daukaka addinin shi sai yafara ta wajen ka, a matsayin ka na shugaba, kasani daman tsakanin gaskia da karya akwai shamaki mai karfi da nisa mai yawa kamar yanda gabas da yamma sukeda nisa da juna ta yanda bazasu taɓa hadewa ba to hakan take ya shugaba na." murmushi yayi yace. "Hakane Jamra gaskia naga banbancin dake tsakanin gaskia da karya a lokacin da naje dajin Gamki, boka Sarrilƙus yana son ya kashe ni amman dana fadi wata kalma da naji Bahijja ta fada lokacin da takawo mani abinci nima nayita lokacin ina cikin tashin hankali, ba wata kalma bace face, *A'uzubillahi minasshatanir rajim!* tabbas naga alfanun wannan kalma ta ceceni Jamra, dan haka na barranta akan abinda muke bautamawa aikin banzane Jamra nayi imani da ubangijin dakike bauta mawa Jamra."
duk wadan da ke wajen kallan juna suka dingayi sunaji Sarkin su na wani yare ko kuma ince kurman yare a wajen su, sannan Jakadiya tace. "Tabbas ya shugaba na, kalmar da kafada ba karamar kalma bace domin Bahijja ta fada mani ma'anarta tana nufin ina neman tsarin Allah daga shaidan la'ananne abin korarwa." cikin gamsuwa yace. "Gashi ta zama hijaba a tsakanina da shaidanun da suka baibayeni Jamra naji dadi da gaskia ta bayyana a cikin wannan Masarautar tawa ta Raifasu, dan haka Jamra ki sakani cikin wannan addinin naki." wani irin sanyi Jamra taji da dadi cikin sakin fuska tace duk abinda na fada kaima kafada ya shugaba na, tace kace.


_*Asshahadu alla ilaha'ilallahu, wa'ashhadu anna Muhammadur rasulillahi."*_
tana fada Baidulƙais yana furtawa hakama makarraban da suka rako shi suma suna furta wannan kalma harda Sarkin gidan yari wani irin dadi Sarki Baidulƙais yaji ganin mabiyan shi basu mashi bore ba akan abinda yake tafe dashi, itako Jamra wani irin dadine ya baibaye ta cikin kulawa tace. "Wannan kalma tana nufin na shaida babu abin bautawa da gaskia sai Allah kuma annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma manzon sane."
Sarkin Zagi ne yace. "Jakadiya waye *Annabi* *Muhammadu* kuma?" murmushi Jamra tayi tace. *"Annabi Muhammadu* mutun ne kamar kowa sai dai yafi kowa daraja domin duk abinda muke samu na rayuwa albarkacin shi mukeci, Allah ya aiko shi da wannan addinin na musulunci domin ya zama rahama ga talikai, ma'ana mu bayin Allah, *Annabi Muhammadu* ya

Please Login or Register in order to submit comment