Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikin ta tana tambayarta ko lfy, a kidime take tambayar ta, ɗan murmushi Jakadiya Hajara tayi tace.
"Ki kwantar da hankalin ki Aisha, kinsan ciwon 'ya mace watan tane yakama."ɗan shiru tayi tana nazartar Bahijjar sannan ta sauke ajiyar zuciya aranta ko cewa tayi, lallai kam ashe Yata tazama budurwa kenan Allah ya karemin ke Bahijja, a zahiri ko murmushi tayi tana mai buga bayan Bahijjar cikin sigar lallashi wani irin bankarewa tayi tayi shiru jikin Aisha, sai kuma tafara kuka ahankali, jitayi kamar ta jike a tsora ce wanda har yanzun bata gama sabawa da bakon nata ba tace. "Kitaimakamin irin wannan abun ne ya kuma dawoman.!" ta gama maganar cikeda rauni, matsowa Jakadiya Hajara tayi ta kamata saiko gashi tayi staining, kewaye takai sannan ta nuna mata yanda zata gyara jikin ta haka kuwa tagama shiryawa tabata wani zani ta ɗaura sannan ta kara mata kaya kala ɗaya ta saka, Jakadiya Aisha ce ta wanke kayan da yar tata taɓata ta shanya zaunar da ita tayi gefen ta rike hannun ta cikin kulawa tace.
"Ƴata kinsan wani abu kuwa.?" rausayar da kai Bahijja tayi tana mai maida hankalin ta wajen Babarta, dan tasan intai mata irin wannan kiran akwai abu mai mahimmanci da zata faɗa mata cewa tayi. "Yanzun rayuwa tasake canza miki daga kuruciya zuwa girma na cikar budurci a gareki, ya zama wajibi ki kara kulawa da kanki da duk wani lamarinki da tsabtarki daman ke gwanace, sannan ki kasance mai yawan kamewa, tabbas kingirma Bahijja daman ga yanayin jikin ki, tamkar mai yawan shekaru, inama ace ina taredake danafi kowa farin ciki, saidai yau zamu koma nida Tasi'u."sunkuyar dakan ta tayi tana maijin nauyi da kunya sannan tace. "Insha Allah zan kula sosai, saidai bansan ki koma ke ke sakani cikin tarin farin ciki Ba'ba!" takarasa maganar tana raurau da fuska alamun mai son yin kuka." girgiza mata kanta tayi alamun aaa kada tayi kuka sannan tace.
"Shikenan Bahijja ai muna tare tunda muna kalkashin inuwa ɗaya ta addini kinga bamu da sauran wata fargaba." sake faɗawa tayi jikin Aisha tanajin so da kaunar ta nakara shigarta, cikin kulawa tace. "Ina Umman ki da Abban ki.?"

Wasa tafara da dogayen yatsunta cikin yin kasa da murya tace. "Sunan wajen ayyukan su." rausayar da kai tayi tana maijin tausan su, tace. "Kigaidaman su, wata rana mun gaisa dasu." toh Bahijja tace, daga nan suka cigaba da zantawa cikin kewar junan su.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

_A MASARAUTAR RUNO_

A wajen Yarima Malik ne, zaune kusa da Sarki Abu-Jalal ya sadda kanshi kasa aɗayan gefen haggun shi Matawalle ne kowa yayi shiru a cikin su, cikin kulawa Sarki Abu-Jalal yace. "Abdulmalik." ɗago da kanshi yayi ya kalli Matawalle yace. "Naam." Sarki Abu-Jalal ne yace. "Baffan ka yazo mani da wani batu mai girman gaske yace kunzo nan ne dan ka duba matar aure cikin dangin ka, shine nikeso inji daga gareka, shin da amincewar ka, sannan cikin yan uwan naka mata kaga wadda taimaka kuwa.?"

Wani irin mummunan faɗuwar gaba ta dirar mashi take dan danan jijiyoyin kanshi sukai raɗo raɗo dakyal ya saita kanshi ga wani irin kallo Matawalle naima Yarima Malik duk da bata shi yake ba, shiko Sarki Abu-Jalal tsaf yake nazartar MalikusSaif abinka da mutun ne mai saurin ɗago yanayin mutune cikeda kulawa yace.
"Ɗana kayi magana karka boye mani komai faɗi abinda dake cikin ranka ɗana."
sun kuyar da kanshi Yarima Malik yayi yace.......




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 91&92



"Abi aini banda wani zaɓi duk abunda kuka zaɓaman yaim....
ɗaga mashi hannu Abu-Jalal yayi cikin nazartar Malik yace. "Nagane Abdulmalik ba wanda zai maka wani zaɓi da kanka zaka zaɓa." da ido Matawalle yabisu ganin yanda Baffan nashi keson gane abinda ke faruwa kuma yasan muddin yasan zancen soyayyar shi da Bahijja ba makawa zai goyi bayan MalikusSaif ne.
Shiko Malik shiru yayi baice komai ba saima sadda kanshi da yayi kasa, ganin hakane Abu-Jalal yace.
"toh Abduljabbar kaji dai abinda ɗan naku yace, dan haka abarshi saiya shirya sannan duk wadda ya fidda kudubi addinin ta ku goya mashi baya."

Murmushin karfin hali Matawalle yayi dan yasan tabbas Sarki Abu-Jalal ya fahimci komai kuma yasan bazai lamince ba, cewa yayi. "Toh Baffa saidai yaka mata yaje ya gansu duk da haka." rausayar da kanshi Abu-Jalal yayi yace. "Shikenan yanzun zansa Dawud, ya rakashi komai kenan sai mubarma Allah ikon shi."

************************************

A Masarautar DABORAH kuwa yau su Jakadiya suke komawa ita da Tasi'u, suna cikin turakar bayi wajen dangin Tasiu suna gaisawa da iyayen shi, bakaramin farin ciki sukayi ba ganin ɗan nasu yazama cikakkan mai 'yanci yasamu ɗaukaka, haka sukai tayima Jakadiya godiya harda kwallar su, bakaramin dadi Jakadiya Aisha taji ba ganin irin karamci da jindadin da iyayen Tasiu sukayi haka Jakadiya tabasu kudi masu yawa, sannan suka zuwa wajen iyayen Bahijja saidai basu tadda mahaifiyar taba, tana aiki sashen Sarauniya Zulaiƙa, Abdulmajid ne suka iske yana alwalla da alama masallaci zaitafi, koda sukayi sallama tareda Bahijja, amsawa yayi yana kallan su, tashi yayi yaimasu shimfidar tabarma, zama sukayi cikeda sakin fuska yace. "Barka da zuwa." yawwa Jakadiya ta amsa, kallan Bahijja yayi alamun bai ganeta ba, sunkuyar da kanta tayi tana sosa keya tace. "Abba itace Baba Jamra wadda ta rikeni a Masarautar Raifasu."

murmushin farin ciki yayi yace. "Masha Allah kece kukazo da Tasi'u kenan gaskia bamuda bakin da zamu godema ki akan rikon da kikayima Bahijja Allah yasakanta maki da alkhairy, munji labarin ki agareta, kinzama jigo ga Bahijja, saidai muce Allah yakara girma da daukaka."

Cikin jin dadi tace. "Bakomai ai ɗa nakowa ne saidai mugodema dan yarinyar nan itace silar komai agareta ne har Allah yasa muka anshi addinin musulunci kaga mukeda riba, kuma Allah yabiyaku."
Rausayar dakai yayi yace. "Nasamu wannan labarin wajen Tasiu munji dadi Allah yakara hakuri d juriya, yasa mudace, kuma Allah yaɗaura mu bisa daidai baki ɗayan mu."

Da Ameen suka amsa, shigowar Tasi'u ya katse masu firarsu dukawa yai yace.
"Kawu barka da hutawa." "yawwa Tasi'u ance yau zaku koma ko?"
"Eh kawu." murmushin jin dadi yayi yace "gaskia kam kazama dan RAIFASU ko ikon Allah yau ga tsatson Jafar sun watsu har wata Masarautar ta daban Allah dai yacigaba da karemu, kuma yau kune da 'yanci Tasi'u naji dadin wannan lamarin."

Cikin jin dadi yace.
"Kawu aikomai yanada lokaci kowa ya san bayima 'ya'yane." Jakadiya ce tace. "Kwarai kuwa muzamu gaya maku hakan domin bayin sune suka zama fitila a cikin zukatan mu, Allah yakara hade kanmu baki ɗayan mu." da ameen suka amsa sannan suka dunguma shi Tasiu da Jakadiya suka wuce wajen Saifulislam, shiko Abdulmajid masallaci ya wuce, suna isa suka iske Sarauniya Zulaiƙa da Waziri da alamun su kadai suke jira zama sukayi Kangiwa ne yace. "Tasi'u yau zaku koma ko?" eh Tasi'u yace, cigaba da cewa yayi. "Masha Allah ga wannan sakon kukaima Sarki Muhammad, sannan kuce kowane lokaci kofa abude take, ku muke saurare, Yarima yakusa dawowa komai kenan zakujimu muna fatan Allah yasama addinin nan albarka yasa kuyishi cikin aminci mungode sosai, Aisha ga wannan kunyi guzuri a hanya Allah yakiyaye hanya."

ɗan russunawa Jakadiya tayi ta amsa suna godiya Sarauniya Zulaiƙa ce tace. "Allah yakaiku lfy sannan ga yan rakiya nan zamu hadaku dasu sukaiku iyaka Allah ya kiyaye hanya yasa ku isa lfy." Jakadiya ce tace. "Ameen uwar dakina Sarauniya mai adalci mungode maku Allah yabiyaku da aljanna." Waziri ne ya amsa da ameen.

Haka suka kama hanya suka fito baki ɗayan su, a bakin kofa suka tadda Bahijja da sauri ta mike tana mai faɗawa jikin Jakadiya tana kuka itama kukan takeyi, da ido suka rakasu Sarauniya Zulaiƙa ko jitake kamar ta shake Bahijja ta huta, cikin sigar lallashi Jakadiya Aisha tace.
"Haba 'yata kukan nan naki na ɗagaman hankali kidaina kinji kinsan kece farin cikina 'yata." sharemata kwallar idanun ta tayi cikin sarkewar murya Bahijja tace. "Ba'ba kizauna taredani karki barni dan Allah."

Cikin tausayawa Saifulislam yace. "Kibar kuka Bahijja wata rana ai zata dawo gareki." rausayar dakai tayi alamun gamsuwa sannan tace "shikenan Ba'ba Allah yatsare hanya yakaiku lfy, Ya Tasi'u sai watarana, ka gaidaman da Ya Kabir." da toh ya amsa sannan suka kama hanya suka tafi tana ɗaga masu hannu, su Saifulislam masallaci suka tafi shida Waziri, itako Sarauniya Zulaiƙa side ɗinta ta wuce tana mamakin irin shakuwar da Jakadiya tayi da Bahijja, haka ta wuce bedroom dinta, ita kuma Bahijja gida ta wuce ta kwanta tana jin kewar Babarta a cikin zuciyar ta....


_Bayan kwana_

A Masarautar Runo kuwa yau kwana biyu kenan dayin maganar zaɓen mata da Matawalle yaima Sarki Abu-Jalal, tunda akayi maganar ya sanarwa Galadima hakan yasa aka sanarwa 'yayan 'yan uwa kowa ya shirya dan ba karamin so sukeyima MalikusSaif ba musamman Hafsat tunda ta ganshi taji tana son shi, bayan sallar la'asar ne Matawalle yakira MalikusSaif daman yace suje shida Dawud ya zabi matar aure a cikin su, koda ya faɗa mashi baice komai ba, ganin hakane yasa Matawalle yace.
"Nasan ba zaɓa zakayi ba saidai ka duba halin da kabaro mahaifiyar ka, sannan kasan ko wace kwarya da abokin gurbin ta, Bahijja ba ajinka bace." kallan Lurwan yayi yace. "Kaga Lurwan kuje ku hadu da Dawud yaje ya duba, so nike yana zaɓa ayi baikon sa gobe muwuce gida"
"toh ranka shidade insha Allah." tafiya sukayi direct sashen shi ya shiga ya sake watsa ruwa yasa wani yadi mai taushi cofee da ratsin brown sai yasa hula brown yasaka turare kaɗan, dan ba son zuwa yakeba bare har wata tace tana son shi, wannan dalilin yasa bai waniyi wankan da zaisa har a so shi ba, kallan shi Lurwan yayi yace.
"Haba Yarima kamar ka zakayi wannan shigar?" kallan banza yaima Lurwan tareda zan tsoki yace. "kaike ta wannan Lurwan kallan su nikeyi kaima kasan da manni lokaci kawai nike jira." baijira cewar Lurwan ba ya juya ya fita, shima take mashi baya yayi yana mamakin halin Yarima Malik yanda yake son baiwa, da haka suka isa wajen Dawud daman yagama shirin sa tsaf dan haryafi MalikusSaif ɗaukar gayu, daga sama harkasa yafara kallan Yarima Malik, saidai ya girgiza kai yana ankare da Kawun nashi ya basar yace. "Mutafi ko.?" tafiya sukayi ba inda suka dosa sai sashen gimbiya Yahanasu kakarsu acan ne zai zabi matar cikin 'yayan dangi, yana isa sukayi sallama cikin wani katafaren falo ba kowa a ciki hakan yasa Dawud yace su zauna shiga yayi wani ɗaki bada jimawa yafito tareda wata kyakkywar tsohuwa sanye da jar alqabba, tana isowa suka gaisheta cikin girmamawa kallan MalikusSaif tayi tace.

"Abdulmalik barkan ku da yamma." cikin girmamwa yace. "Ya jikin tsufa." cikin sigar wasa ta ɗan harare shi sannan tace. "Yarinta dai ai tsufa sai yan zamani"murmushi kawai yayi.
hadimarta ta kira tasa aka fara kawo masu abin taɓawa kama daga kayan marmari da abinci iri iri, haka hadimai suka gama jere masu a gaban su saman wani lallausan kafat na alfarma suna gaidasu suka tafi, itama gimbiya Yahanasu shiga tayi cikin bedroom dinta sannan tasa Jakadiya tai masu kiran su Hafsat, Dawud ne ya fara zubama MalikusSaif dafaffiyar madara mai kamshi tayi kauri da ita, mikama Malik yayi, sannan ya zubama Lurwan, shidai MalikusSaif jujjuya kofin ya dingayi dan baki ɗaya hankalin shi nakan Bahijja, ya matsu ta koma gida, dan bakadan yake kewar taba, jin sallamar sune ya maida hankalin su, kan kofar shigowar, yan matane akalla sunkai su shidda kowace tasha kwalliya iya kwalliya ga kayan alfarma sunsha da kangasu kasan sun gaji da haduwa ga tsabar sarauta a jikin su, kallo ɗaya Malik yai masu ya kauda kai, shima kallan da yaimasu bai wani kalli fuskar suba, da sallama a bakunan su, kowa ya samu waje ya zauna ba abinda ketashi sai kamshi mai ɗan karen dadin shaka, fuska sake Lurwan yace.
"Barkan ku da zuwa." Hafsat ce ta ɗan yatsine fuska kamar batasan magana sai iyayi takeyi tace." yawwa fatan kuna lfy.?" "lfy."yabata amsa danya fahimci ta fiya jijidakai yamasan bazasu shirya da Malik ba, ɗan satar kallan MalikusSaif, Dawud cikin yin kasa da kasa da murya yace. "Abdulmalik yaka mata kugaisa mana." da gefen ido yaɗan watsama Dawud ido sannan ya duba a gogon hannun shiq yaga har biyar da rabi tayi, kallan Lurwan yayi cikin murya kamar mai raɗa ko wanda baisan yin magana yace. "Yaka mata mutafi ko.?" ɗan girgiza kai Lurwan yayi yadan wayance yace. "Eh hakane saidai kugama gaisawa ranka shidade." ɗan hade fuska MalikusSaif yayi zaiyi magana kenan yaji ance. "Ranka shidade Yarima, ai yaka mata agaisa ko.?" a hankali MalikusSaif ya ɗago kanshi ya kalli Hafsat da wutsiyar ido, a ranshi ko cewa yayi.
"Kalleta ahakan zan zaɓi mata wadda batasan darajar kantaba bare ta mutunta jama'a, jibi yanda take wani yaguna, ni bansan mutun mai jijidakai, mtsw." jan tsokin dayai shine ya baiyana a zahiri, baki ɗayan su suka kalleshi, shima kallan sun yayi amman ko ajikin shi, saima cewa yayi. "Sannun ku ko." binsa sukayi da ido ganin kamar ba shine yayi maganar ba, cigaba da murza kofin hannun shi yayi yana ɗan kaɗa kafar shi, ganin hakan ne yasa Lurwan ɗan gyaran murya dan yasan Malik bazaiyi magana ba, yace
"Na fahimci Yarima kamar bakajin dadi, Dawud yaka mata mutafi ko.?" shidai baice komai ba saidai girgiza kai da yaɗanyi dan ya fahimci baki ɗaya bata su Abdulmalik yake ba, akwai abinda yake boyewa, tashi yayi, Hafsat ce tace.
"Baffa Dawud tafiya zakuyi, amman aibamu gaisaba ko." ɗan hararan ta Dawud yayi yace.
"Baki ganin baijin dadi, zamu kuma dawowa." juyowar da zaiyi yaga MalikusSaif harya fita daga falon, a cikin ranshi fal yake da tsanar Hafsat baisan mace marar kamun kai, yana isa sashen Sarki Abu-Jalal, ya shige bedroom dinshi rufe kofar yayi ya shige bathroom yafara watsa ruwa hakan nan yaji ranshi na kuna, yanaji ana koncking, amman yai kamar baijiba Sarki Abu-Jalal ne ya shigo ga mamakin shi yaga Dawud da Lurwan tsaye bakin ɗakin Malik suna bugawa, komawa yayi ya zauna bisa kayatacciyr kujera ta alfarma data dace da Sarakai, a hankali ya kalli amintaccen hadimin shi yace.
"Kiraman su Dawud." tafiya yayi yace. "Ranka shidade, takawa na kiranka." jiyowa yayi ya kalli falon canya hango mahaifin shi zaune yana kallan su, tafiya sukayi, suka zauna kasan kafat cikin girmamwa Dawud yace. "Ranka shidade gamu."

Kallan tsaf Sarki Abu-Jalal yayi masu yace. "Nafahimta Abdulmalik bai bada hadin kaiba ko.?"

Sadda kai yayi kasa yace. "Ranka shidade, gaskia Malik baida bukatar wannan hadin inaga akwai abinda yake boyewa." rausayar dakai Abu-Jalal yayi yakalli Lurwan yace "inaga kai bazaja rasa sanin abinda Abdulmalik yake boyewa ba ko.?" ɗan shiru Lurwan yayi sannan yace. "Eh ranka shidade nasan abinda nasani amman ba duka ba."
Cikin jin dadi yace. "Faɗa mani abin da kasani Lurwan." cewa yayi. "Akwai yarinyar da Yarima keso, saidai ance kowa yanada abokin gurbi, a zahiri yarinyar bata cancani tazama suruka a wajen kuba."

A nutse yake nazarta Lurwan kallan dayake mashine ya tabbtar mashi da yana neman karin bayani hakan yasa yace. "Dalili kuwa itadai yarinyar baiwa ce, marar 'yanci." murmushi yayi dan yasan ko Zulaiƙa bazata aminta ɗanta ya auri baiwa ba, bare yanda Masarautar Daborah ta tsani bayi yasan dole Abdulmalik zai shiga cikin damuwa azahiri kuwa cewa yayi. "Hakane, sai dai bawani abu bane dan yana son baiwa, naji dadin jin wannan labarin daga gareka zaku iya tafiya." haka suka tafi danko Dawud mamaki yake kamar MalikuSaif ya buge da son baiwa.
koda Malik yagama wanka kimtsawa yayi ya dawo cikin ash din jallabiya ya kwanta dan hutawa ya kosa zuwa gobe su wuce gida, yana kwantawa yaji an buga kofar ɗakin shi, da kamar bazai buɗ eba sai kuma ya bude, ganin wanda ke bakin kofar ne yasa shi kirkiro murmushi a saman kyakkyawar fuskar ki, zaiyi magana yaji ya kama hannun shi, falo suka nufa bisa 3str ya zaunar dashi gefen shi, ya maida hankalin kaf kan MalikusSaif, a nutse Abu-Jalal yace. "Abdulmalik." murya nadan breaking yace. "Na'am Abi." cikin tausayawa yace.
"Miyasa kake boyemani abubuwa masu mahimmanci a rayuwar ka?" sadda kanshi yayi kasa yana karajin kwarjin kakan nashi yana baibaye shi, cewa yayi. "Kayihakuri Abi, banda wani zabi da yawuce inbarma raina tunda bakin alqalami yariga da ya bushe." murmushin manya yayi yace. "Waya faɗa maka.?"
kallan shi MalikusSaif yayi ya sake maida kanshi kasa, Abu-Jalal ne yace. "Waya faɗa maka? haryanzun a ɗanyan shi yake sai dai wanda Allah ya kaddara, miyasa zakace komai ya lalace dan kawai kana son BAIWA.?"
da sauri MalikusSaif ya kalle shi yana mamakin inda yaji wannan batun abakin kakan shi, cewa yayi "kabar mamaki dan nasan sirrinka ɗana,bayin nanfa suma 'ya'yane." ka nutsu kaji abinda zance maka, karka bari kowa yaji angaya mani wannan maganar, kabar zancen maganar zaben matar da kukazoyi karka damu ba komai kasan ance matar mutun kabarin sa, saidai inka koma gida, kaga abubuwa sunkiyin sauki, ka'aikomin insha Allah Abdulmalik saika auri wadda kakeso, ta hanyar kane bayi zasu zama 'yaya, kuma haske zai sake bayyana a cikin Masarautar Daborah, kada ka karaya ɗana, inaji araina aurenka da baiwar nan akwai alkhairi mai tarin yawa."

Wani sanyi MalikusSaif yaji ya lullube zuciyar shi, yanaji a jikin shi zai mallaki Bahijja, maganar da Abu-Jalal yayi shiya dawo dashi a cikin duniyar tunanin daya tafi, Abu-Jalal ne yace. "Minene sunan surikar tawa." fuskar shi ɗauke da murmushi yayi mashi tambayar, ɗansosa keya MalikusSaif yayi yace. "Bahijja."
rausayar dakai Abu-Jalal yayi yace. " masha Allah kasaki ranka Abdulmalik kaji ni mahaifinka ne, duk abinda bai gimsheka ka aikomin da kaina zanzo." kwantar dakanshi Malik yayi gefen kafadar nashi, yanajin so da kaunar shi na ratsa shi yace. "Nagode Abi Allah yakara girma." da ameen ya amsa, nan sukaci gaba da zantawa

Washe gari da safe ranar ne su MalikusSaif zasu dawo gida, tunda suka gama shiryawa suke zaune cikin falon Sarki Abu-Jalal basujima ba sosai ya fito cikin kayan alfarma na Sarakai kallansu yayi yana mai mikoma Abdulmalik hannu, tashi yayi yaje wajen kakan nasu rungume shi yayi yanajin kewar shi na ratsa shi ta kowane kofan gashi da yake cikin jikin shi, atare suka zauna, Matawalle ne da Lurwan suka gaishe da Sarki Abu-Jalal, cikin sakin fuska yace. "Abduljabbar." Matawalle ne ya amsa da. "Naam." cikin kula da uba kebawa 'yayan sa yace. "Kaga bamu samu matsaya ba, saidai inajan kunnen ka kaida Zulaiƙa ban lamunce a takura Abdulmalik ba, duk wadda yakeso a lamince ya aureta banda auren hadi." mamaki ya kama Matawalle, sake kallan Baffan nashi yayi zaiyi magana, Sarki Abu-Jalal ya ɗaga mashi hannu yana girgiza kai yace. "Umurnina ne ba shawara ba Abduljabbar, inafatan Allah yakaiku lfy." "Ameen ya rabbi." cewar Matawalle, kanshi yagama kullewa dan kamar gargaɗi Baffan nasu kemasu alamin yasan komai, to ta yaya? baida amsa tambayar shi jiyayi ya kuma cewa. "Abdulmalik kakulaman da kanka zanyi kewar ka ɗana." murmushi yayi yace "insha Allah Abi nima ina kewarka." da haka suka gama abinda zasuyi sannan kowa ya hau dawakan su, sukai masu rakiya zuwa iyakar gari sannan suka tafi Sarki Abu-Jalal yana ɗaga masu hannu, jiyake inama Abdulmalik yadawo wajen shi baki daya saidai suka ɓacema ganin su sannan suka koma cikin Masarautar Runo...


_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 93&94



Masarautar Raifasu, Sarki Muhammad ne dasu Tasi'u suke bashi sakon Saifulislam kasancewar saukar dare sukayi shiyasa tun jiya basu gabatar mashi da sakon ba sai da safe, saida suka gama kwashe komai da yanda aka tarbesu aka karramasu suka faɗa mashi ba karamin daɗi yajiba dan bai tsammaci hakan daga garesu ba, sai dai daya dubi alfarma irin ta addinin daya haɗasu sai yaga ba abin mamaki bane, wani murmushi yayi sannan ya bude wasikar yafara karantawa.

_Assalamu-alaikum_

_Inafatan mun sameku cikin aminci, sakon ka ya riskeni inamai farin cikin jin wannan labari mai_ _dadin sauraro, inai maku albishir akan duk wani taimako da kuke bukata kofa a buɗe take, sannan maganar Sarrilƙus kada kudamu kanku kuyi addinin ku cikin aminci_
_duk abinda kukaga baku gamsu dashi ba, ku sanar mana, Allah yakara hade kanmu alfarmar annabi da alqur'ani,_ _daga Saifulislam Daborah, zuwa ga Sarki Muhammad Raifasu._

Nauyayyan ajiyar zuciya ya sauke yana maijin daɗin wannan sakon, kallan Jakadiyar sa yayi yace.
"Ina ƴarki kingan ta kuwa." murmushi tayi aranta ko tace Allah Sarki shugabana kai dai kana son Bahijja, azahiri ko cewa tayi.
"Naganta ina ruwan Bahijja anzama yan mata, lfyrta lau." ajiyar zuciya ya sauke a sirrin ce yace. "Ina ruwan 'yata Bahijja, gaskia kam addinin musulinci addini ne mai daɗi, yanzun nakara banbance tsakanin ilimi da jahilci, yanzun haka inajin kunyar abinda na aika tama Bahijja, sai dai a yanzun inama Bahijja kallan 'yata ta cikina! Allah nagode maka daka fiddani a cikin tsantsar jahilci da duhun da nike ciki, Allah ka kara tabbtar damu a cikin wannan addinin mai dinbin daraja da rahama." baki dayan su suka amsa da amin, yana karajin kaunar Bahijja a cikin zuciyar shi....

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

_Masarautar Daborah_

Sarauniya Zulaiƙa ce zaune saman kujerar alfarma da tasha adon Jawhar ta dan jinjina kanta tana mai ɗan jujjuyawa kanta tai sama tai kasa, sai dai baki ɗaya hankalin ta bai jikinta, jin ana sanar da shigowar gimbiya Salsabila ya dawo da ita a duniyar tunanin ta, zama tayi tareda gaishe da Sarauniya Zulaiƙa, juyowa tayi ta kalleta ba yabo ba fallasa, gimbiya Salsabila ce tace.
"Ranki shidade har ankai wani matsayi da wannan baiwar Bahijja zata wulakanta Zahara'u."

Kamar baza tayi magaba sai kuma tace.
"Kamarya wulakanci.?" "ehmana naji bakice komai shiyasa nace bari inbiyo ba'asi, kan wanna aurakar har marin Zahara'u saida Abdulmalik yayi." a hankali Sarauniya Zulaiƙa ta ɗago daga kishingidar da tayi tace.

"Bahijjar banza da wofi harta isa ta wulakan gimbiya Zahara'u dani take zancen yarinyar nan ta zame mani karfen kafa ta isheni tana shiga cikin gona ta zan iya halaka wannan matsiyaciyar baiwar!" Binta ce ta shigo ta dawo daga shanya bayan sashen Sarauniya Zulaiƙa da alamu wanki tayi, cikin gadara Sarauniya Zulaiƙa tace. "Ke zonan." da sauri ta iso zata duka Sarauniya Zulaiƙa tace.
"Tashi munafuka yar manufukai, kije kice matsiyaciyar 'yarki taimaza tazo ina neman ta." jiki sanyaye Binta fita tana share kwallan idanun ta, dan tafara gajiya da irin wulakancin da Sarauniya Zulaiƙa ke mata, haka ta isa cikin madaidaicin gidan nasu wanda ya zarce kowane gida na bayin dake cikin turakar bayi kasancewar sune iyayen bayi, isketa tayi tana karatun alqur'ani tana karanta suratul Mulk, gefe ta tsaya tana kallon 'yar tata, sai dai tana mai tausayin halin da zata shiga, tana kai aya ta kalli mahaifiyar tata wani irin mugun faduwar gaba ne ya lullube Bahijja ganin mahaifiyar ta, tana kuka sharbe sharbe da hawaye, cikin raunanniyar fuska Bahijja tace.
"Umma lfy kike kuka dan Allah mi akaimaki ko baki lfy.?" rausayar da kanta tayi tana jin tausan Bahijja cewa tayi. "Bahijja haka zakita hakuri akan kaddararki da,da hali da kin gudu kinbar wannan Masarautar dan tsira da rayuwarki da alama Sarauniya Zulaiƙa itace zatayi ajalinki 'yata dan haka taki ta sameki Bahijja, yanzun haka ita ke kiranki." dafe kirji Bahijja tayi tana salati cikin kuka tace.
"Umma nidai kukan kine banso, kuma wuya bata kisa, sai dai ta sani indai akan ɗanta ne na hakura ban son shi Umma." murmushin manya tayi tana kalan kuruciya a kan fuskar 'yartata tace. "Bahijja kenan bakin alqalami ya riga ya bushe wuce muje saiki ɗauki

Please Login or Register in order to submit comment