Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inta aikin bauta? Allah Sarki kawaye na Indo da Zainab shikenan narabu da Baba Saude nidai gaskia saina koma wajen su Baba Jamra, duk da Sarki Baidulƙais azzalumine so yake ya kasheni amman ai Babata bazata bari ba, can kuma taji hawaye na zarya a kumatunta tace Allah Sarki Umma ta da Abbana ina kewar ku, wayyo Ya Malik dina nasan ya manta da kanwar shi, ni yanzun, koma zan iya gane Ya Malik kuwa, murmushi tayi tace keko Bahijja kin cika zakewa ina baiwa inayin Yaya da Yarima hmm yanzun fa kinsan banbancin ƴayan sarauta da bayi, kwara dai kisan abinda kikeyi sai dai ya zama uban gidan ki Yariman ki kamar kowa.
haka dai Bahijja ta kama sake saken ta na shirme bata san sadda bacci ɓarawo yai awon gaba da ita......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*

*Dedicated this to Samira Bala and Ummu Nanah kuyi yanda kuke so dashi*🥰


_Jinjinar ban girma agareki Nusaiba, Allah yabar kauna_ ❣️



Episode 19&20



_Masarautar Raifasu_



Wajen Sarki Baidulƙais kuwa lamarin duniya ne yai mashi tsaye yana mamakin yanda Sarrilƙus yake fushi dashi akan Bahijja shi kan shi yaso ya kusance da ita kodan kashe kishirwar da ta addabe shi akan Bahijja, shawara ya fara ko yaje dajin Gamki wajen shi susan abinyi wata zuciyar ce tace kaima kasan bazai saurareka ba, amman inko haka ta kasance ai zan shiga cikin damuwa mai yawan gaske, amman bari in saurari sakon Sarki Danwar inji dan nakosa inje intaho da Bahijja kona yi abinda aka umurceni da ita, haka dai Sarki Baidulƙais yai tayin sake saken banza dana wofi harya, gama shirin shi tsaf ya tafi fa'da danjin inda Jaruman shi suka tsaya da abinda ake bukata na kayan yaki.....


Koda ya isa cikin fa'da baki daya Jarumai ne zaune ke saman jiran shigowar shi, yana shigowa kowq ya kike, bayan ya zauna kowa yakai gaisuwa wajen Maimarta ba,sannan suka zauna, shiru ne ya biyo baya, kowa ya kashe kunne yaji abinda Sarki zaice.
shiko baki ɗaya ya shagala da tunani dan kana ganin shi kaga mai damuwa a zahiri, Sarkin Yaki ne yace. "Ranka shidade mungama shirya komai yanzun abinda ya rage mana shine fuskantar abokan gaba sai dai muna da bukatar ma'suna da takubba sun mana karanci."
cikeda gamsuwa Sarki Baidulƙais yace ma Sarkin Yaki su anshi kudi wajen Sarkin taska,duk abinda suke bukata a siya sannan acigaba daba Jarumai gwaji na musamma."
suna cikin fa'danci wata tsohuwa ta shigo, Sarkin fa'da ne yai mata iso wajen Sarki a tare suka gaida Sarki, sannan yace. "Ranka shidade wannan matar tana son ta ganka duk yanda nayi da ita, akan ta faɗi damuwar ta amman tace kai takeson gani."
wani irin kallo yaima ta dan yanda yake jin shi bazai iya sauraron wata karaba a wajen mutanen shi ba dan baida lokacin ɓatawa a halin yanzun, amman gudun karya karya mata guiwa yasa ya bata umurnin magana cewa tayi.
"Ranka Shidade nakawo karar wani ɗan uwana daya anshe mani dukiya ta kuma yahani ni, gashi banda kudi ko hanyar da zanci abinci kuma bai bani komai ba bare insai abinci shine nakawo karar shi ka ansar mani dukiya ranka Shidade."


Idanun Baidulƙais rufe kamar mai bacci nan ko abubuwane sukai mashi tsaye ya rasa inda zaisa kanshi yaji dadi, shiru ne ya biyo baya daga bisani yace
"Minene sunanki."? "Ranka Shidade sunana Lami."
"toh naji abinda kikace saidai kisani a halin yanzun abubuwa sunyima fa'da yawa akwai muhimman abubuwa dake gaban mu, amman yanzun zan baki kudin da zakiyi anfani dasu, kafin wani lokacin sannan kisani nan da mako biyu kizo keda dan uwan naki danyi maku shari'a in fa'da tasamu sukuni, magatarda ka anshi sunan ta da wanda take kara nan da mako ɗaya ki sake dawowa sannan a bada kudin da zasu isheta har zuwa wani makon."
dukawa tayi ta sadda kanta kasa sai godiya takeyi haka aka ɗauki sunan ta dana ɗan uwanta sannan aka bata kudi tayi godiya ta tafi cike da farin ciki a zuciyar ta......


*Daborah*


A wajen Abdulmajid yau ya tashi da matsanancin ciwon ciki kamar bazai kaiba tsabar azaba da ta gama addabar rayuwar shi, amaine yaita kwarawa sekace zai fiddo da ƴan hanjin shi haka yake ji ga ba abinda yaci dan raban da yaci abinci tunjiya da marece, Ladidi da Binta sai Mairo sune sukazo ganin Abdulmajid daga kullewar da akai mashi suna zuwa, suke iskeshi cikin mawuyacin hali, rai hannu ga Allah a kiɗime Binta tayi kan mijin ta,ta rungumo shi jikin ta batasan sadda ta fara kuka ba mai tsuma zuciya ba, gwanin ban tausayi, tana kuka tana cewa. "Abban Bahijja dan Allah katashi kada katafi ka barni katashi dan Allah kai kadai ke gareni mijina, Mairo dan Allah kuce Abdulmajid yatashi karya tafi ya barni katashi dan Allah." haka ta karasa maganar tana kuka mai tsuma zuciya.
su kansu su Mairo sun kasa ko motsin kirki baki ɗaya jikin su rawa yake musamman da suka ga yanda jikin Abdulmajid ya saki ko motsi baiyi itako Binta tagama fita hayyacin ta, tana cikin kuka ta ɗaura kanta saman kafadar shi, batayi aune ba taji saukar duka na ratsata sake kankame shi tayi tana kuka kamar ranta zai fita suma su Mairo ji sukai anata dukan su, Sarkin bulala ne keta dukan su, basu san hawa ba basu san sauka ba, cikin faɗa yace. "Uban wa yaba ku damar zuwa wannan wajen ko mutuwa zaiyi kubar shi wato ku sarakan tausayi kenan." Mairo ce ta rike kafar shi tafara bashi hakuri dan baki ɗaya ta gama tsorata da lamarin Sarkin bulala haka yai masu korar kare, da kyal suka ɓanɓare Binta jikin Abdulmajid haka suka barshi a yashe kamar ba ɗan Adam, suka tafi sunaji suna gani, shiko Abdulmajid rai hannu ga Allah, koda suka isa turakar bayi haka Binta ta zube kasa sai kuka takeyi ta rasa abinda ke mata dadi a duniya, jitake ina ma ta mutu ta huta, suma su Ladidi gefe ɗaya ta koma suna kuka ba karamin tausayin halin dasu Binta suke ciki su keyi ba, suna cikin alhinin abinda yafaru dasu sai ga wata baiwa tazo tana kiran Binta, ko kallanta Binta bataiba, Mairo ce tace.
"Wake kiranta." amsa ta bata da Sarauniya Zulaiƙa ce, Mairo ce tace gatanan zuwa.
haka wannan baiwa ta tafi, Mairo ce tace. "Kiyi hakuri Binta haka Allah yaso komi makaddari ne daga Allah ki saka dangana a ranki insha Allah Abdulmajid bazai mutu ba, kibar wannan kukan dan Allah."
haka sukai taba Binta hakuri sai ajiyar zuciya takeyi ta kasa cewa komai baki ɗaya ji takeyi kamar zuciyar ta zata fashe, Mairo ce ta kara cewa. "Binta ki daure kije kiran da Sarauniya ke maki karki samu wata matsalar." kallan da Binta taima Mairo kadai saida yasa ta hadiye sauran maganar ta da kyal ta mike ta shiga dakin ta kwantawa tayi jitake kamar zuciyar ta zata fashe, addu'a takama karantowa iri iri ta kama wannan ta saki,wannan haka tai tayi har tafara ji zuciya tafara yimata sauki.
itako Sarauniya Zulaiƙa baiwar na komawa tace mata ina Binta.?" dukawa tayi tace. "Ranki Shidade tana zuwa." ranta ɓace tace. "Banace ki taho kafarta kafarki ba."? A daburce tace. "Ranki Shidade nabarota cikin fushi saidai Mairo tace ince maki tana nan zuwa yanzun."? batakara cewa komai ba, komawa tayi ta zauna tana jiran Binta ta iso taji dalilin dayasa ta aika tazo taki zuwa akan lokaci.......


*****************************

Washe gari da safe Bahijja ce ta tashi daga bacci ta shirya ba inda ta nufa sai ɓangaren Yarima Haishir tana zuwa tafara gyaran falo kamar yanda ya umurceta sannan taje bakin kofar dakin su Malik da zata kwankwasa masu kofa sai kuma ta fasa, hakan yasa takoma falo ta zauna wata zuciyar ce tace mata ai kwara ta ida aikin ta, wannan shine hutun jaki da kaya, wannan karan dakin Yarima Haishir ta shiga kwance ta iskeshi yayi ruf da ciki sai bacci yakeyi ɗan gutun tsoki taja tace. "Hakadai za'a kare ba sallah ba salati sai bacci kawai akasaka agaba inama anfani." shiga tayi cikin kewayen dakin ta cigaba da wankewa tagama sannan ta share tsakar dakin ta rufe kofa ta koma falo, ɗakin su Malik ta wuce tana isa ta kwankwasa kofar tsaye take tanajira taji anbude mata kofa wata zuciyar ce tace kodai basu tashi daga bacci ba, sai kuma tace aiba abin mamaki bane tunda ba wani sahihin addini ne dasu ba banda na bacci, bata ida sakar zucin da take ba sai ta ɗan jingina da kofar dakin kafin abuɗe mata ta riga shagala a tunani, ji tayi anbude kofar gashi ta gama sakin jikin ta a jikin kofar baya baya tayi zata faɗi bakaramin tsoro bane ya mamaye mata zuciya ba harta fidda rai tasan inta faɗi zatayi rauni marar kyau, ji tayi an tarota ta faɗa saman mutun, wani irin sanyayyen kamshi ne ya ziyarci illahirin hancin ta har cikin kwakwalwarta, rufe idanun ta tayi ta kasa ko motsin kirki, shiko Yarima Malik ya kafeta da razanannun idanun shi, yana mamkin kalar kyau da girman da Bahijja tayi har haka, jin shirun yai yawa hakan yasa ta bude idanun ta ta azasu asamn fuskar shi wani irin mummunan faɗuwar gaba taji ya da baibayeta da kyal ta iya zamewa a hannun Malik, da sauri ta duka kasa tace. "Tuba nike ranka shidade banyi zatan kuna kusa ba kuma bansan na saki jikina ba a kofar kaimin aikin rai."? Murmurshi ya sakar mata wanda ya tafi da imanin Bahijja ganin kyau da irin halittar da Allah yaima Malik wanda tai mashi kallan tsoro sai yanzun take kara ganin kyaun shi, saidai baki ɗaya kanta ya kulle tarasa gane inda tasan wannan fuskar koma a inane tasan wannan kamanni, shima kallan ta yakeyi yasan nazari takeyi inda ta sanshi, shiru yayi ya nasan yaga kota gano wani abu dangne dashi ganin yanda ta shagala da kallan shi sai dai da alama bata tuna komai ba, a hankali kamar wanda baisan yin magana yace. "Bakomai karki damu, mi zakiyi nan."?
duk daburce tarasa abin cewa tace. "Aiki aiki ne Yarima Haishir yasani ingyara maku masaukin ku." jitayi yace. "Toh bissimillah."
jitayi kirjinta na dukan tara tara cewa tayi daman wannan mutanen sunsan kalamar bissimillah kenan?
Ai nasan wannan addinin mune damn a wannan Masarautar akwai wanda yasan bissimillah a zuciya take maganar ta batasan ta fita filiba, shiko Malik dariya tabashi kunshewa yayi ya kalleta yace. "Ko bakiyi niyar farawa bane."?
Da sauri tace"aaa zanyi gaba yayi ta bishi baya, sai satar kallan shi takeyi tana shiga tafara gyaran gadon dakin Huzaifa ne ya fito daga kewaye da alama alwallah yayi cewa yayi. "Yarima ina littafin nan bani zanyi sallah.....ganin Bahijja yasa bai ida sauran zancen suka makale mashi a baki ba, gaidashi tayi, saidai bai amsa ba itako ko ajikin ta ba abinda ke damunta irin ganin wannan saurayin da tagani ta rasa inda tasan fuskar shi, ganin yanda kowa yai shiru hakan yasa MalikusSaif yace. "Duba waccen jikar yana ciki, haka kuwa akayi ɗaukowa yayi taga ya kabbara sallar shi yana tayi sai ya zamar ma Bahijja hoto haka ta shagala tana kallanshi taga harya fita iya sallar ma saida ya gama sannan tafara shara, har tagama gyara ko ina, dukawa tayi taimasu sallama zata tafi.
tsaida ta Malik yayi ya bata abincin da aka kawo masu kalaci dan shi koci baiba daman Huzaifa ne yadanci shima ba sosai ba, cewa tayi ta gode, wani irin kallo yaimata hakanan taji yaimata kwarjini kuma bazata iya musu dashi, batasan ta ƙarɓa ba, godiya taimashi ta tafi, tana mamkin irin mutuncin shi a zuciyar ta gashi mutun mai daraja da arziki wanda ya gaji mulki ga kyau saidai yasan darajar dan Adam koda yake ba abin mamaki bane kasancewar shi musulmi, karo na farko kenan da mutum mai daraja a cikin jerin mutanen da ta haɗu dasu yai mata mutunci wani irin dadi taji yana ratsa mata cikin zuciya komawa tayi falo ta faracin abincin ta cikin jin dadi danko ba abinda dake mata yawo a idanun ta sai Kyakkyawan Saurayi sunan da taba Yarima Malik kenan a zuciyarta......


tana cikin cin abincin ta rabi, ba komai take tunani ba sai Yarima Malik jitake kamar akwai wani abu a tareda shi, musamman da taga ba kalar addinin Masarautar Waisu sukeyi ba, tambaya tafara yima kanta miyasa suke boye fuskar su idan suna cikin mutane, jitayi tace kema dai Bahijja miye abin mamaki baki ganin kalar kyaun shi, sai kuma tace Aa anya kodai akwai abinda sukazo nema a wannan Masarautar ne? Kai kuma aida Yarima Haishir bai basu masaukiba a cikin sashen shiba, kuma yace abokan shine, wata zuciyar ce tace mata keko ina ruwanki da damuwa da wadan nan bakin karfa ki ajama kanki halin da baki dashi na saka ido akan rayuwar wasu, tana ta tunani taji an hankaɗar da abincin dake hannun ta afusace Yarima Haishir yace. "Wato raini ya shiga tsakanina dake ko abincin bakin nawa zaki zauna kinaci sannan uban wa kika bari zai gyara maki gadan ɗakin nawa."
baki daya jitayi jikinta yai sanyi cewa tayi. "Nice zan gyara daman jira nayi kagama bacci tukunna sannan kuma sune suka bani.....kifa mata mari yayi yace. "Suka baki ubanki, yau saina ɗebe rainin daya shiga tsakanina dake."
fara dukanta yayi wani mugun zafi taji ya ratsata batasan ta kurma ihu ba shi kanshi Yarima Haishir saidai yai mamaki yasan taurin kanta bazai bari tayi kuka, tundaga dakin su Malik suka jiyo karar ihu, da sauri ya mike yace wannan wane zalinci ne kowace Masarauta dai bayi basu da ƴanci, bari inga wa'akema wannan bugun har haka." rikeshi Huzaifa yayi yace. "Karkaje Yarima kaga dai ba Masarautar mu bace kuma ya kamata ka rufe fuskar ka, dawowa yayi ya rufe fuskar shi har ya zauna ya kuma jin wani ihun kukan hakan yaji zuciyar shi na duka, baisan yakara mikewa ba yace.
"Anya kamar Bahijja bazan mance da wannan muryar ba Huzaifa baijira cewar shiba ya fita da sauri shima maye mashi baya yayi yana zuwa ya iske Yarima Haishir yana dukan Bahijja har kwallo yakeyi da ita wani irin bacin raine ya dabaibaye zuciyar MalikusSaif baisan sadda yai kukan kuraba ya ingije Haishir ba har saida ya kusan kifewa kas, a tsorace ya kalli Yarima Malik wanda tuni idanun shi sun sauya kala tsabar bacin rai, itako Bahijja da sauri ta koma bayan Malik duk jikinta ya kama kyarma kamar zata faɗi, shiko Haishir mamaki yakeyi miya haɗa Yarima Ƙamar da Bahijja harya nuna fushi dan anbigeta buɗa baki yayi yace.......




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



_Fatan alkhairi a gareki masoyiya ta Deeymusah ina fatan Allah yakara maki lfy mai anfani, kaunar ki a gareni ta musamman, my Deejah Allah yabar tare_ 🤝🏻




Episode 21&22




"Zaki fito daga bayan shi ko kuwa saina canza maki kaman ni."?
Juyawa Yarima Malik yayi yaga yanda jikin Bahijja ke kyarma duk tsoro ya gama addabar rayuwar ta, ta gama tsurewa.
kallan Yarima Haishir yayi yace. "Kai ko miya ja maka dukan mace?kake ta kumfar baki sai dai kace ka haɗu da Jarumi irin ka!? waima mi tayi maka har haka."?
Ya karasa maganar da siffar zolaya, ajiyar zuciya Yarima Haishir ya sauke sannan yace. "Miya haɗa ta da abincin ku, ku sa'annin tane daman wannan yarinyar ba kunyar kirki tasani ba da kabarni na ɓallata tunda bata hankali."
dafa kafardar Haishir yayi da karfi saida ya kalli Malik dan ba kadan yaji cafkar da MalikusSaif yaima shi ba, cikeda da ƙaƙƙausar murya Yarima MalikusSaif yace.
"Haba abokina maida wukar nine nace taci kuma ma miye a ciki dan na bata abinci? ba hadimar ka bace."?
Yaso yaima Bahijja kaca kaca saidai kwarjinin da Malik yaima shi bazai barshi ba ya ida abinda yai niya ba, saiya samu kanshi da cewa. "Shikenan badamuwa tunda kaine ka bata, ke kuma daga yau idan kikazo aiki kiyi abinda ya kamace ki, inafatan kin fahimta, yanzun kije ki gyaraman ɗakina."
Jiki sanyaye Bahijja tayi hanyar dakin shi da ido suka bita shiko Yarima Malik cigaba yayi da tunani kamar ba abinda ya faru kowa yana sakar zuci wanda tambayoyi iri iri suka addabi Yarima Haishir saidai baida amsar su, ba abinda yafi ɗaga mashi hankali yanda Yarima Ƙamar ya nuna fushi dan ya bugi baiwa ko shima dai ya kamu da son Bahijjar ne, kai daga ganin ta, ban tunanin zai sota, wanda a zahiri yake zancen duk da baisan ya fita, Huzaifa ne ya kalli Malik, jin abinda Yarima Haishir ke cewa itako Bahijja tana gyaran gado tana kwalla ta tsani Yarima Haishir mugune dan taci abinci shine yake neman illata ta gaskia baida imani, badan Kyakkyawan Yarima yazo ba da shikenan yau saiya lahanata haka ta ida aikin ta sannan ta fito ta tafi masaukin su, ta kwanta kafin ta koma aikin marece......

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Sarauniya Zulaiƙa ce wajen Saifulislam kowa yayi shiru da alama ransu ne a ɓace, saboda fuskokin sune suka bayyana hakan, ganin yanda Saifulislam ya nuna bacin rai a fili hakan yasa Sarauniya Zulaiƙa tace.
"Haba Abu Malik banyi tsamma nin wannan abun zai ɓata maka raiba, narasa dalilin dayasa akan bayin nan kake nuna damuwarka a zahiri, bayan duk abinda ke faruwa sune sila kai kuma baka ganin laifin su."
baisan sadda ya daka mata tsawa ba da karfi yace. "Yimin shiru Zulaiƙa karki saka raina ya ɓaci a banza a wofi abinda kikeyi a cikin Masarautar nan ya wuce gona da iri yanzun jibi yanda kikasa ana azabtar da bayin Allah, ina ruwan Abdulmajid dan MalikusSaif yatafi neman Bahijja ai basu suka aike suba, shine zakita yimasu azaba wlh ina gaya maki ki guji sakayyar ubangiji wannan dalilin yasa ko kusa ban shiga cikin sabgar mulkin ki gudun ɓacin rai dan haka kada insake jin bakin ki kije kiyi duk abinda kikaga dama damuwar kice, kada kisaki tunkarata da kalar wannan maganar aikin banza aikin wofi.!"


Baki ɗaya idanun Sarauniya Zulaiƙa sun sauya dan ɓacin rai tarasa mi zatace ma Saifulislam ganin yanda ranshi yai mugun ɓaci hakan yasa ta fita daga sashen shi ta tafi nata, tana zuwa ta iske Binta na share share tunda taga yanda Sarauniya Zulaiƙa ta shigo takara kama kanta gaidata tayi wani wulakantaccen kallo ta azama Binta batasan ta sadda kanta kasa ba, shiga tayi dakinta ta rufo kofa saman gado ta faɗa ta rasa abinyi sai tunanin maganganun Mijinta takeyi wani ɓagaren na zuciyar ta kuwa cike take da jin haushin Yarima MalikusSaif tasan shine ya jaza mata duk abinda ke faruwa.....

A gidan yarin Daborah kuwa ba abinda ya sauya tunda ciwon ciki ya turnike Abdulmajid haka aka barshi wanwar sanyin marece ne ya busashi hakan yasa ya tashi jiki ba kwari duk ya mutu, kallan mutanen wajen ya dingayi Sarkin bulala ne ya bashi aikin gyaran wajen dawakai, haka ya dinga kwasar kashin dawakai shida Ashir, shima ba wani ragi da yake samu saima abinda yayi gaba kullin sai anmashi bulala sama da hamsin, duk yabi ya lalace ya susuce idan ba sanin kirki kaima Ashir ba bazaka iya gane shi ba.


Koda Sarauniya Zulaiƙa ta fito daga dakin ta kiran Binta tayi tana zuwa ta duƙa ta gaidata kanta a kasa, shiru tayi tana jiran taji mi uwar dakin tata zatace mata.
"Ke baiwa ƴar bayi ta taɓa kunnan bayi uwa ga bayi, ubanwa yabaki damar da zan aika kiranki kiki zuwa sai yanzun da kika ga dama."?
Rasa abin cewa Binta tayi duk da tasaba jin wukakancin da Sarauniya Zulaiƙa ke mata, cikin rawar murya tace. "Ranki shidade banda lafiya a lokacin shiyasa.....kifamata mari tayi har ukku sannan tasa ƙafa ta halbata har saida ta faɗi kasa kanta ya bugi kasa jinine ya fara zuba, kwalla kara tayi ko motsin kirki batayi, haka Sarauniya Zulaiƙa taci gaba da yimata masifa ganin bata motsi,kiran wata baiwa tayi tasa aka ɗauketa kamar marar rai sawa tayi aka fidda Binta waje sai kace dabba su kansu bayin da sukayi jifa da Binta saida sukayi kwalla, wata baiwa ce Hansa'u taga abinda akaima Binta haka ta ruga ta kira Mairo a sashen Saifulislam ta gaya mata halin da Binta ke ciki, da gudu suka iso dukawa tayi ta riko hannun Binta jin bata motsi taji gaban ta yayi mummunan faɗuwa, da sauri tasa aka ɗebo ruwa aka yayyafa mata farfaɗowa tayi, kamata sukayi suka maida ta turakar bayi, sukai tayi mata fiffita ko magana Binta ta kasa yi saidai kwalla da suketa sunturi a saman fuskarta sai ƙarƙaɗa kai takeyi tana kwalla tana san tayi magana, amman jitake zuciyar ta zata iya fashewa, Mairo ce ke goge mata kwalla tana bata hakuri, da sauri Ladidi ta faɗo itama kukan ne ta fashe dashi tace. "Binta miyasa meki kanki ke jini?
Mairo miyasa mu Ummu Bahijja dan Allah kuyi mani magana." ranar haka sukaita kuka kowa ji yake zuciyar shi ba dadi, musamman Binta da takasa furta ko kalma ɗaya dan ɓacin rai daya addabi zuciyar ta......

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Raifasu kuwa Baidulƙais ne kwance saman gadon shi cikin mawuyacin hali wani irin shi'awar Bahijja ne ya addabi rayuwar shi ko motsin kirki ya kasa ga zufa na tsastsago mashi yayi sharkaf sai juyi yakeyi ya rike marar shi sai murɗama shi takeyi tun yana saman gado har saida ya faɗo kasa, numfashin shine yafara ɗaukewa kamar zai mutu, da kyal ya rarrafa ya isa banɗaki ruwa ya ɗiba ya dinga shekama kanshi ruwa ko yaji sanyi amman feeling ke kara addabar shi hakan yasa ya diɓe kayan shi yafara wasa dick dinshi kamar karama kanshi bala'i yakeyi fashewa yayi da kuka mai cinrai yana kiran sunan Bahijja tun yanayi a zuciya harya fara kiran sunan ta da karfi, samun wani tsumma yayi yai mashi rami yasa dick dinshi yana dukan wajen amman a banza ranar haka Baidulƙais ya yini cikin daki yana kwasar azaba da bala'in da baitaɓa jin irin shiba baisan sadda ya shiɗe wajen ba wanwar kasa a sume cikin bathroom haihuwar uwar shi a wulkance....



*Niko ƴar mutan kankia nace ai Allah ba azzalumin bawa bane duk abinda mutun zai aikata karshe kanshi ke karewa*


Itako Jakadiyya shigowa tayi falon Sarki Baidulƙais tasa bayi aka fara gyara shi, jin shiru bai fito ba hakan yasa ta tashi ta shiga dakin shi ta fara kwankwasa kofa takai minti goma bataji yayi magana ba,tana turo kofa taga ta buɗe, shiga tayi taga gadan duk ya ya mutse kamar anyi kokowa a saman shi bin dakin tayi da kallo ba taga komai ba, har zata fita taji kamar gurnani a ban daki, gabanta ne ya faɗi a hankali ta nufi ban dakin taga kofa a bude alamun ba kowa, a cikin kewayen harta juya sai tace bari ta rufo kewayen tasa baiwa ta gyara dakin taga duk yayi datti da yawa, tana shiga zataja kofa taji wani abu ya tokare kofar dubawar da zatayi taga Sarki Baidulƙais kwance haihuwar uwar shi, bata san sadda ta saki ihu ba rufe bakin ta tayi ta rufe idon ta bakaramin tashin hankali ta shiga ba, ko kallan shi takasayi, ganin alamun bai motsi yasa ta dibi ruwa ta zuba mashi ajiyar zuciya ya sauke, tai saurin barin kewayen, shi ko dukan kanshi

Please Login or Register in order to submit comment