Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zabgama Bahijja gabgegiyar bulalar shi sai bankarewa take tsabar azaba shiko Malik baya ya juya masu dan baiji zai iya ganin dukan da akema Bahijja har cikin kokon zuciyar shi yake jin dukan da kowane sashe na jikin shi haka yakejin dukan Bahijja na ratsa shi, itako Sarauniya Zulaiƙa ganin inta tsaya tabbas zata iya yima Bahijja illa yasa ta fita gimbiya Salsabila na maye mata baya, shiko MalikusSaif kamar jira yake mahaifiyar tashi ta fita, ya dakawa Sarkin bulala tsawa, a kidime ya zube bisa guiwowin shi yana neman afuwa yace. "Allah yahuci zuciyar magajin gobe banda wani iko sai abinda Sarauniya ta, ta umurce ni, kasani nima bada son raina na duketa ba!"
wani matsiyacin kallo MalikusSaif ya watsama Sarkin bulala baisan ya ɗauke shi da mari ba cikin muryar shi mai raunin tausayin halin da Bahijja ta shiga yace. "Yimin shiru nima badan ganin girma da darajar wadda tasaka yin wannan dukan ba, wlh da daga kan Bahijja kagama hukunta kowa ne bawa a cikin wannan Masarautar azzalumi, kuji tsoron Allah zalinci bai ɗaurewa! maza ɓace mani dagani tunkan in sauya maka kaman ni!" ganin yanda ran MalikusSaif ya ɓaci saɗaf haka Sarkin bulala ya zille yabar sashen, a hankali ya taho wajen Bahijja yana mai tsananin tausayin ta, tallabo fuskar ta yayi yaga jikin yayi ruɗu ruɗu da shatin bulala da sauri ya fita ya kira wata baiwa yace ta taimaka mata sukaita gida, haka suka ɗauki Bahijja suka fita da ita, jiyake kamar ya kurma ihu dan azaba da yakejin zuciyar shi nayi mashi da dukan sassan jikin shi, ba abinda ke mashi yawo a cikin kwakwalwa sai dukan da akaima Bahijja bataji ba bata gani

Koda gimbiya Salsabila takoma gida iske 'yayan nata tayi cikin falo su da mahaifin su da alama fira suke ɗan taɓawa tsakanin su, yanda sukaga ta zauna jiki ba kwari yasa Huzaifa yafara tambayar mahaifiyar tasu damuwar ta.
"Ummi lfynki miyasa meki?"ɗan karamin tsoki tayi tace.
"Dole raina ya ɓaci abokin ka yasosa mana zuciya nida mahaifiyar shi."
"haba Ummi miyafaru kifaɗaman?" "ace arasa wanda Malik zaiba 'yan kunnen BARRI sai waccen watsatsiyar baiwar.!"
da sauri gimbiya Zahara'u ta mike tana dafe kirji tace. "Lallaima ai duk duniya ba wata 'ya macen data cancanci saka 'yan kunnen barri saini balle kuma wata baiwa."
cikin fushi Huzaifa yace. "Dallah yima mutane shiru sakarar banza kina so maso wani." sai kuma ya maida dubansa kan mahaifiyar su yace. "Gaskia Ummi ina ga baku fahimci MalikusSaif bane taya zaiba baiwa yan kunnen barri inaga yabata ne dan kawai yana nuna tausan ta agare shi kyautatawa ce bawai abinda kuke zato ba."
sanyayen numfashi ta sauke tace. "Haka muke fata ace bawai dan yana sonta ne ya bata yan kunnen Barri ba." murmushi yayi yace. "Ummi kenan in banda abinki ina Bahijja ina MalikusSaif itafa baiwa ce shi kuma Yarima ne, kudai kubar wannan zancen ma."
rausayar dakan ta tayi alamar toh, shiko Dammur ya kasa furta uffan danshi tunda gimbiya Zahara'u tace tanasan MalikusSaif yaji yana son ta aure shi kodan nasabar shi, tashi Huzaifa yayi ya tafi sashen Yarima Malik.....

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Ƙaisu kuwa har Sarkin su yagama haɗa gangamin wa'anda zasuje cin kasuwar Zursu a cikin su harda Sarkin gida sai Sarkin taska da galadima da dagaci da sune zasu wakilci Masarautar su sai hadiman da aka hadasu dasu tare zasu tafi nahiyar Daborah dancin babbar kasuwar Zursu wadda keci a shekara sau ukku, da haka suka ɗauki hanyar tafiya Daborah......

************************************
Koda Huzaifa ya shiga sashen Yarima Malik iske shi yayi kwance ya zurama sillin ido kamar mai bacci, zama yayi gefen abokin nashi yana nazarin shi, ya lura bai san ya shigo ba hakan yasa ya dafa shi a hankali ya waiga yaga Huzaifa, sakar mashi murmushi Huzaifa yayi, sannan Malik ya zauna yace.
"Ina cikin mawuyacin hali Huzaifa.?"
cikin kulawa da aboki kebama abokin shi yace. "Miya sameka Yarima.?" numfashi ya sauke mai zafi sannan yace. "Bahijja ce Huzaifa, Ummu tasa andaki Bahijja kan laifin da bataji ba, bata gani ba, karkaga yanda tasa akaima ta."
jinjina kai yayi ya sake kallan shi sannan yace. "Hakanan Ummu zatasa adaki Bahijja.?" "aaa nabata yan kunnen BARRI ne shiyasa tasa akaci zarrafin ta."sake cewa Huzaifa yayi "kasan wani abu kuwa.?" "inajinka ya bashi amsa atakaice, cewa yayi "ina zatan kafaɗa tarkon son Bahijja Yarima sai dai kai har yanzun bakasan kana sonta ba, kadauka tausayin ne kawai kakeyi."
mikewa Yarima Malik yai yana girgiza kai sannan yace.
"Huzaifa da badan kai kayi wannan maganar ba wlh da saina hukunta duk wanda yai mani ita!" murmushi Huzaifa yayi yace. "Haka kafada daga nafada maka abinda na gani a zahiri shine zakace haka? Inanan wata rana dakan ka zakazo kasa meni da wannan maganar!" shima MalikusSaif din murmushin yayi yace. "Shikenan yanda kace mungani." da haka suka canza wani labarin mafi akasari akan yanda kasuwar ta Zursu zata wakana ne suke tattaunawa akai kafin zuwa gobe zasu shiga kasuwar, da haka Huzaifa yaima Malik sallama yatafi sai dai aran shi yana mamakin musu irin na abokin nashi.

A turakar bayi kuwa Bahijja ce kwance su Mairo na gasa mata jikin sai sannu suke jero mata, shiko Abdulmajid ya gama kufula ganin halin da 'yar tasa ke ciki, cewa yayi. "Sannu 'yata shiyasa kullin nike yawan gaya maki ki tsaya matsayin da Allah ya ajeki, kinga abinda Sarauniya tasa akaima ki MalikusSaif ne kadai kejin tausayin ki ina tausayin halin da zaki dinga fuskan ta a cikin wannan Masarautar 'yata." itako Bahijja wasu hawaye ne masu dumi take sharewa cikin disasshiyar muryar ta tace.
"Abba miyasa Sarauniya Zulaiƙa, bata sona ta tsaneni!?"
rausayar dakan shi yayi cikeda da tsantsar tausayin 'yar tashi yace. "Bake kadai ba 'yata kaf zuri'ar Jafar, Sarauniya bata son su ko kaunar su." sake yima mahaifin nata tambaya tayi tace. "Miyasa hakan ke faruwa?" cewa yayi. "anata dalilin tace bayi munafukai ne, bamu da amana!"
wasu kwallan Bahijja ta sake sharewa tace.
"Ita bata ganin ba duka aka taru aka zama ɗaya ba." murmushi yai na manya yace. "Ai daman wake ɗaya shike ɓata miya, kinsan mi 'yata?" cewa tayi aa Abba." "kada kisake ki shiga abinda baida meki ba, sannan ki guji karɓar kauta daga hannun mutane masu daraja, saboda daga inda suka fahimci ke fakiriya ce baki da wata daraja a idon su, abin zai zame maki baraza na adin ga cin zarafin ki ana kaskantar dake, 'yata ki kasance mai wadatar zuci, idan kika godema Allah akan ni'imar da yai maki zai kara maki, Bahijja kisa aranki ke baiwa ce, amma kuma ba kaskantacciya ba, ke mai daraja ce wajen ubangijin ki da mutane masu mahimmanci da suka san darajar dan Adam, 'yata ki guji shigema rayuwar Yarima Malik, kodan mahaifiyar shi, kullin kikara zama baiwar sa, kada ki bari yazama kina mashi kallan wani dan uwanki ko kuma makusancin ki, dan hakan zai iya zama matsala agreki, kisaka wannan aranki 'yata, watarana insha Allah zaki zama mai daraja a cikin wannan Masarautar dama kewayen ta."

Numfasawa tayi tace.
"shikenan Abba na zan kiyaye, saidai Abba ina nasamu wannan sunan da naji Sarauniya Zulaiƙa na wulakanta shi?" girgiza kai yayi yace. "Yata duk abinda bai shafeki ba baruwan ki dashi saidai kinyi tambaya mai kyau, wannan sunan 'yata kinci darajar mai daraja, Yarima Malik shida kanshi ya raɗa maki wannan sunan, sabida badan Allah yasa ke mai tsawancin rai bace da damu dake tuni bamu a doron kasa kilan sai dai labarin mu, MalikusSaif ne ya fanshemu wajen mahaifiyar shi."
wasu kwalla taci gaba da fiddawa masu zafi tace. "Abba kamar ya fansa mikukayi mata ne?" "bakomai dan Allah yabamu karuwa mun haifeki shiyasa, mukai laifi kasan cewar mu bayi har yanzun 'yata ta haramtama bayi haihuwa a cikin Masarautar mu, shiyasa kika kasance karama kuma auta a cikin bayi."
rike hannun shi tayi tace "Abba batasan Allah keyi ba." "tasani 'yata kawai dai son zuciya ne na dan Adam da mantuwa irin tamu da ajizanci." "hakane Abba, shiyasa Ya Malik ya saka mani suna."
"kwarai kuwa agaban mahaifiyar shi yace abarki kinzama kanwar sa kuma ya saka maki suna Bahijja kinji ainahin sunanki 'yata." shiru tayi su Binta ko kwalla suka share tana tuna irin azabar rayuwa da suka fusknta a cikin Masarautar Daborah, itama Bahijja tunani ta shiga yi sai kuma tace. "Abba sai yaushe bayi zasu zama masu ƴanci? Kuma batasan cewa *BAYIMA 'YA'YANE* ba?" cikin kosawa da tambayar yar tasa yace. "Kinga 'yata kibar damuwa da abinda kikasan bakida maganin shi kuma komai yana da lokaci, kibar wannan maganar kedai kiyi amfani da abinda na fada maki.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Bayan kwana biyu Yarima MalikusSaif shida su Huzaifa da Yazid sai Lurwan a cikin Kasuwar Zursu mutane ne cikin ta daga kasashe daban daban na duniya anata cinikaiya masu sayan kayan abinci nayi, masu siyan kayan sawa, dabbobi, kayan ma'aikaci da bayi kowa da abinda yake siye, tauwagar su Sarki Haishir ne ke sayan kayan abinci, Huzaifa fane yazo wajen su shida Sarkin Kasuwa ana ansar kudin haraji, duk inda sukaje sai anbasu kudin haraji, suma saida suka basu kudi, haka sukai ta jibgar kaya kamar ba gobe wajen inda ake saida bayi kuwa Yarima Malik ne shida Lurwan yan Masarautar Ƙaisu ne sukazo suna siyan bayi saida suka sayi bayi sama da dari, har abin saida yaba Yarima Malik mamaki, hakama wajen kayan wukake na yaki suma yan Masarautar Waisu ne ke siyan kayan yaki, kananun kaya suka siya, Malik ne yaje wajen Sarkin dawakan Daborah yace, ya duba masu dawakai masu aminci a rage tsaffin dawakai a saida haka kuwa akayi, suma sun jibge uban kayan abinci cikin Masarautar wanda zasu iya kwashe sama da shekaru biyu basu sai wasu ba, intakai ta maku dai haka aka wuni aka kwana ana siye da siyarwa a cikin katafariyar babbar Kasuwar Kasar Gambia wato Kasuwar Zursu dake kalkashin Mallakin Masarautar Daborah, wanda idan akaci Kasuwa suke samun muggan kudi dama kasar Gambia baki dayan ta, shiyasa Masarautar Daborah suka kasance masu tarin arziki da dukiya mai tarin yawa tun daga gwala gwala lu'u lu'u da jawhar da azurfa harma da sauran kayan karau nayau da gobe, haka Kasuwar Zursu ta dinga cin karanta ba babbaka har akayi kwanaki ukku tanaci ana ukkun ne Sarauniya Zulaiƙa da Wazirin ta su Matawalle da Kadimulislam sukazo rangadi dan suga yanda Kasuwa keci duk da shine cinta na karshe a wannan ranar kenan....





_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم




Domin samun Audio novel dinmu, ga YouTube channel dinmu nan dan samun saukin karatu sae dae kawae ki saurara😁👇

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*
Episode 59&60




*_KASUWAR ZURSU_*


Jama'a ne keta hada hada kamar ba gobe kowa burin shi yasai abu mai mahimmanci wanda zakai shi wata shekarar idan na siyar wa darajar shi da dagu ka siyar kaima dan kaci riba mai yawan gaske, marece ne ke gaba towa inda fataken ke fara kimtsa kayan su, Matawalle ne sai Sarauniya Zulaiƙa da Saifulislam sai Waziri da Dagaci sai Zannan Daborah suke ran gadi a cikin Kasiwar ta Zursu, inda Saifulislam yaje wajen tawwagar shi dan ganin yanda suke gudanar da siye da siyawar su, yana zuwa shida Zulaiƙa duk suka zube suka kawo gaisuwa wani wajene na musamman aka basu suka zauna, dan jim kadan ma'ajin Saifulislam yazo inda yake zaune ya duka harkasa sannan ya bashi makudan kudin da suka samu sanadiyar fatauci da sukeyi kasancewar shi babban dan kasuwa mai faɗa aji a cikin kasar Gambia, lissafi sukayi tabbas yasan mutanen shi nada amana dan dukiyar da suke juyawa akalla ansamu riba kashi ukku cikin hudu, sawa yayi aka kira mashi dan shi MalikusSaif bada jimawa ba saiga shi yazo,zaunawa yayi ya gaida iyayen nashi mahaifin shine yaima Malik bayanin komai, sai dai duk abin nan Malik bai yarda sun ido hudu da mahaifiyar shiba sabda bakarmin haushin shi takeji ba, cigaba da lissafin su sukayi, kashi daya na dukiyar MalikusSaif yaba ma'aji yace ya fidda kason albashin shi, sannan ya rabama sauran jama'ar su, kashi guda kuma ya saka ta cikin jallin su, yace a sake juyawa da uwar kudin kashi guda kuma yaba Saifulislam yace kai kuma wannan itace ribar ka Abbuh, kowa ya gamsu da kasafin Malik daman Saifulislam ya kira MalikusSaif ne dan ya jarraba shi yaga ko yasan takan kasuwa dan shima yana burin gudan jinin nashi ya gajeshi, dan acewar shi ba abinda yakai fatauci ma'ana (kasuwanci) riba akaf abinda mutun yasaka gaba a wannan duniyar da muke ciki, a gaban kowa Saifulislam ya keta ribar da aka bashi ta kudi masu yawan gaske ya raba gida hudu kashi daya yace ara bama talakawa kashi daya yaba Malik kashi daya yaba matar shi, shima yarike kashi ɗaya, damkawa kowa nashi kudin yayi godiya sukai mashi sannan yaba Malik wadda za'arabama talakawa kamar yanda ya saba ya naɗa Malik a matsayin wakilin shi tako wane ɓangare, da haka Saifulislam yasa aka kawo ma yaran na shi abinci da ruwa da kayan bukata, nan yaimasu fatan alkhairy sukaci gaba da hada kayan su wanda suka saya a cikin KASUWAR ta ZURSU da sauran kayan su zasu cigaba da bin kasashe fatauci kamar yanda suka saba, da haka suka nutsa cikin kasuwar suna ganin yanda komai yake wakana cikin aminci Sarauniya Zulaiƙa ce taji wani bafade yana mata magana yace.

"Ranki shidade Sarki Haishir ya aikoni yace, ingaishe ki sannan in roka mashi gafarar ki da 'yan tuwa amatsayin ɗa a wajen ki." shiru Sarauniya Zulaiƙa tayi tana kallan shi cikeda mamaki tana nazarin maganar wannan bafaden na Waisu, da yake Sarauniya Zulaiƙa kwararra ce wajen fahimtar dan Adam tun daga gaskiar shi ko akasin hakan, rausayar dakai tayi cikin gamsuwa tace "Na amsa sai dai kace tuni na yafema Masarautar sa da jama'ar shi, amman yanci saina duba yuyuwar hakan nagode." ba haka wannan bafadan yaso jiba dan suna da tasu manufar da sukeso su samu a wajen ta sai dai wannan karon basu da niyar cutar da ita ko yakarta, godiya yaima ta sannan suka kama hanyar tafiya shida tawagar su zuwa Masarautar tasu ta Waisu.....

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A wajen jama'ar Sarki Danwar kuwa suma sun gama komai nasu sai dai sunsayi kayan makami da yawan gaske haka suka gama duk abinda zasuyi sannan suka kam hanyar komawa gida, atakaice dai ranar KASUWAR ZURSU ta kwashi dan Adam fiye da tunanin mai tunani har yamma liqis sannan kasuwar ta watse kowa ya kama gaban shi sai kuma wata shekara, duk da yan Daborah sukan kasa kayan su na yau da kullin wanda suke bukatar siyarwa na yau da kullin amman ta gefen kasuwar, saboda ita Kasuwar Zursu tana ɗauke da gate gate sama da shidda tana gama ci, Sarkin kasuwa zaisa kwaɗo a kulleta sai aje makullin cikin kayan adana tarihi na Masarautar Daborah sai kuma wata shekara wannan kenan......

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Raifasu kuwa Baidulƙais ne yaje ya dawo haka yaita yi bakarmin tashin hankali ya shiga ba jin Jakadiyar shi wadda take kamar aminya agare shi ta amshi addinin musulunci yasan ba karamin kalubale zai fuskanta ba wajen Sarrilƙus ba, daman gashi yai mashi tawaye, zufa keta tsatsafo mashi kamar an mashi wanka da ruwan sama, ba jimawa saiga Jamra ta shigo dukawa tayi gaban shugaban nata ta sadda kanta tayi kasa, shiko yakai yadawo haka yaita yi yana zuwa ya dan duka kadan a gaban ta yace. "Jamraaah." yanda yaja sunan natane yasa ta dagowa da sauri cikin fushi ya kwade ta da maruka har ukku saida ta fasa uwar kara da kuwa ta faɗi kasa ta saki wata irin marainiyar kara tana hawaye cikin bacin rai yace. "Jamra kinci amana ta ke kadai kika ragemin da nike gani matsayin Jakadiya ta, ta amana inji dadi yau gashi an waye gari kema kin juyaman baya na rasa ɗana! na rasa Bahijja, na rasa abu mai mahimmanci a cikin sashe na jikina, uwa uba mulkina yana barazana agareni haba Jamra sai yanzun kema zakice kin gujeni ya kikeso inyi da raina.?" sake fashewa tayi da kuka tace.
"Na rantse da wanda raina ke hannun sa na rantse da darajar wanda ya aiko domin yazama shiriya ga talikan bayi, na rantse da girman addinina tabbas na musulunta, ya shugaba na saidai kasani wannan addinin d nikeyi haskeni kuma shiriya ce ga dukan bani adama inama zaka karbi wannan addinin da hannu bibbiyu tabbas da na zamarma ginshiƙi kuma na tallafeka tamkar mahaifina ko kuma ɗan cikina, kabar wannan addinin na kaka da kakanni bai karaka da komai sai asara bayya nanna tabbas Bahijja haskece agreni shiyasa Allah SWT ya bata ilhama dahar naji addinin ta ya shiga cikin zuciyata wannan itace dangan takata da Bahijja tun tana karkashin ikon ka naki wannan addinin a sirrance, saidai yanzun duk abinda kaka damar zartar min zan dauka amma kasani Jamra bazata iya wofintar da addinin taba ta kama
Addinin da bazai anfaneta da komai ba!" cikin hasala yace "kimin shiru Jamra kina fadin son ranki akan addinina, dan kinga nabaki muhimmanci arayuwa ta Jamra da ace wanine ya aikatamin haka sa yanzun yari gida y isa barzahu dan haka yau zaki hadu da fushina Jamra!!"
sunkuyar dakanta tayi kasa tace. "Na yarda da hakan, da ace akn wani abune na daban tabbas kasan Jamra zata bada hakuri saidai kasani ya shugabana idan ka hukunta. ni ka tsaya kayi tunanin addinin da Jamra ta shiga saidai kasani Jamra bata taɓa cutar dakai da komai ba ka duba hakan cikin nazari ina sauraran amsarka ya shugaba na tabbas zansama maka mafitar dake ciki nagode!" yanajin maganganun Jamra har cikin babban yatsar hannun shi saidai baida wani zabi dayawuce hukunta ta, sawa yayi aka akaita gidan kaso yace ko abinci baice abata ba amman kada aduketa, haka akaja Jamra zasu fita da karfi tace. "Kayi nazari mai kyau ya shugaba na, batareda kasanarwa kowa wannan maganar ba.!'' Haka aka tafi da Jamra aka rufeta gidan kaso....

**********************************

Bayan sati ɗaya, a Masarautar Daborah kuwa komai ya dai daita jikin Bahijja ya warke ta koma bakin aikin ta saidai ba kadan taja baya da Yarima Malik ba, da taje tayi aikin ta zata samu waje tai zaman ta, sai inya sata wani aikin sannan zatayi dan kusan kullin sai Sarauniya Zulaiƙa ta aiko ana duba yanda take hudda da uban gidan nata, yau tana zaune tana aikin gayran falo, taji anama gimbiya Zahara'u ison shigowa sashen Yarima Malik, tunda ta shigo take wani yan fisge fisge tana shakat kamshi kamar ba mutun ba, cikeda da gadara ta samun lumbitsetsiyar kujerar ta ta zauna tanama Bahijja wani mungun kallo na kinsan sauran itadai bata damu da ita tunda taje ta gaidata bata koma bi ta kanta ba, dan taga ko amsawar ma a wulakance ta amsa cigaba da yan goge gogen ta tayi cikin isa taji tace. "Ke baiwa." da bazata jeba dan Bahijja ta tsani wulakanci duk da take baiwa tasan darajar da Allah yaimata, juyawa tayi taje ba tace komai ba, hade fuska ta sakeyi tace. "Ina uban gidan naki.?" a dakile itama tanaji da kanta tace. "Yana dakin shi." "kice gimbiya Zahara'u tana sallama." batareda da tace komai ba ta mike zuwa bedroom din Malik sallama tayi ya amsa ta atakaice ba tareda ya kalleta ba, dukawa tayi kasa cikin sanyn rai tace. "Ranka shidade gimbiya Zahara'u ke sallama dakai tana falo." hakanan yaji ranshi ya sosu, ɗago kyawawan idanun shi yayi ya kalleta yace. "Kice mata ina aiki zata iya jira ko kuma wani lokacin ta sake dawowa." magana Bahijja zatayi watsama ta wani matsiyacin kallo ba shiri tayi shiru tashi tayi taje falon jiki sanyaye ta duka tafadama gimbiya Zahara'u sakon Yarima Malik, wani kallo taimata cikin girman kai da gadara tace. "Danna man kafana." tsaye Bahijja tayi kamar bataji me tace mata sake yimata wani watsastsen kallo tayi sannan tace. "Ke wai badake nike ba!" tafiya tayi a nutse ta tunkaro gimbiya Zahara'u harta iso gaban ta, har ta duka zata fara danna mata kafar taji ance. "Tsaya kada ki kuskura kiyi mata danna!" cak Bahijja ta tatsaya jin muryar Yarima Malik wani irin dadine ya rufe ta, itako gimbiya Zahara'u da idanu takebin Malik a ganin ta kamar yaci mata zarafi, yana isowa ya samu waje ya zauna samn kayatattar kujerar shi ya daura kafa ɗaya bisa ɗaya ya harde ya zubamata idanun shi masu firgitar da wanda ake a kallo a hankali gimbiya Zahara'u ta sauke nata idanun kasa, cikin ƙarsashi da muryar sa mai dadin amo yace. "Banyarda wani ko wata a cikin wannan Masarautar yasaka Bahijja wani aiki ba, komai kankantar sa, Bahijja tana a kalkashin ikona, dafatan kin fahimta? Inkuna bukatar tausa kinemi wasu bayin wanda sukayi kama da kalar tausa amman Bahijja ba irin subace!"

Itadai Bahijja gefen shi takoma tana kallan ikon Allah wani matsiyacin kallo take aikama Bahijja, amman saita wayence tace. "Eh daman nagajine shiyasa nace taimani." daga mata hannu yayi cikin isa yace. "Bana magana biyu fatan zaki kiyaye hakan?" gyada kai tayi tace "eh nagane."

Kallan ta yayi yai mata alamar ko lfy, neman me take mashi, tsaf tagane abunda yake nufi saidai yai masifar yimata kwarjini bataji zata iya kwakwaran motsin kirki a gaban shi, a sanyaye tace. "Daman nazone dan igaisheka!" rausayar dakai yayi yace. "Kin kyauta nagod." mikewa yayi yace. "Ina aiki kigaida Ummi." kai ta gyada tace. "Toh." komawa yayi cikin dakin shi duk ranshi ya sosu wai Bahijja zatace taimata tausa,cigaba da hidimar gaban shi yayi ya watsar da zancen.

Itako gimbiya Zahara'u tashi tayi hadimanta suka maye mata baya, saida tazo gabda Bahijja ta tsaya cikin gadara tace. "Ke watsastsa ko, harkin isa ince kiyi abu Yarima ya hanaki ko, ke yar lelen sa ko? Saina wulakanta ki." wucewa tayi nniyar ingije Bahijja da sauri ta kwace ta bata wuri, haka ta fita rai ɓace...

A sashen Sarauniya Zulaiƙa kuwa zaune take bisa kujerar ta ta alfarma wadda ta gaji da ado na duwatsun lu'u lu'u, gefen fa kuma Waziri Dammur ne zaune da alama suna magana mai mahimmanci ne a tsakanin su, a hankali Sarauniya Zulaiƙa tace. "Kaji yanda za'ayi inajiran inji abinda Matawalle zaice gameda Malik, idan ya tsaya mana wasa sai mu zaba mashi ra'ayin kanmu." murmushi yayi mai ɗauke da ma'anoni cikin kulawa yace. "Angaishe da Sarauniyar da tagagari rauwuna a cikin dokar daji, angaishe da Sarauniyar da take gilgiza kirjin maza, koda mazan Saraki ne, wannan giramnki ne anbuga dake anbarki mace mai kamar maza kwarine kawai babu, angaishe da matar Kadimulislam ƴar uwar Matawalle mahaifiya ga jarumi haziki MalikusSaif, yanda kikace haka zamuyi Dammur nagodiya." a hankali ta rausayar da kanta tanajin dadin kirarin da Wazirin ta yaimata wanda ya yaye mata kaso biyu cikin ukku na damuwar ta, haka yaimata sallama ya tafi ranshi fas


Itako Binta dake aiki tunda dazun takan juyo kadan daga cikin abunda suke tattaunawa, Sarauniya Zulaiƙa ce taimata wani irin kallo abinka da ta saba harta gane manufar uwar gijiyar tata, da sauri ta iso zuwa gareta, ta miko mata ruwa a kofi, sannan ta rankwafa ita kuma Sarauniya Zulaiƙa ta ɗaura kafarta a kafadar Binta taci gaba da yimata tausa itakuma ta kai kofin ruwa abakin ta ta surba da sake sake kala kala a cakin ranta, lokacin marece yayi gaf ake da kiran sallar magrib, hakan yasa Bahijja ta gama aikin ta da takeyi taima uban gidan nata sallama, baice da ita komai ba, ya fahimci ta tsorata da lamarin abinda mahaifiyar shi taimata shiyasa baisan yana janta ajiki gudun kada wani abun yakara samun ta duk da kullin ruruwar tausanta ke ɗawainiya da Yarima Malik a cikin zuciyar shi, haka takama hanya ta tafi sashen Sarauniya Zulaiƙa kamar yanda ta umurce ta, wannan karon ma a gaban Binta akaci gaba da shidema Bahijja bulalai a jikin ta, kamar yanda akai mata da safe, haka sarkin bulala yaita wanke Bahijja da bulala, itako Sarauniya da kiyayyar Bahijja ke kara tasiri a cikin zuciyar ta haka ta

Please Login or Register in order to submit comment