Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saman doki ya fita ta kofar arewa sai dai da alama akwai inda zaitafi batareda kowa yasani ba....


_Tofa ko ina Lurwan zai tafi a sirrin ce muje zuwa dai, yanzun wasan zai soma_


A sashen Sarauniya Zulaiƙa kuwa zaune take bisa kujerar ta ta mulki wadda bisan ta take wulakancin ta a cikin sashen ta, asawa tayi aka kirama ta Abdulmajid da Binta, cikin sanyin murya wadda take a sarke tace.

"Abdulmajid.?"
ɗago kanshi yayi yana jin haushin Zulaiƙa yasan da wani wulakancin ta sake zuwar masu, a dakile yace. "Naam."

Shiru tayi ta rasa ta inda zata soma sannan tace. "Inasan insanar maku da cewa ɗana Yarima Malik yana son yarku Bahijja, duk da kasancewar ta baiwa amman yanace sai ita, ni kuma banda zabi da ya wuce ince maku kuba shi auren baiwar ƴarku."

Wani abune ya soki zuciyar Abdulmajid har saida ya rufe idanun shi sannan ya buɗe su, sun kaɗa sunyi jajir yace....


_Lol komi Abdulmajid zaicema Sarauniya Zulaiƙa, dan na fahimci shima ba kanwar sala bane😁 muje zuwa kardai ku manta kuna tareda alqalamin_ 👇



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 99&100




"Eh hakane 'yarmu baiwa ce, kuma ƴar gadon bauta, wannan dalilin yasa kullin muke mata huɗubar da ta tsaya matsayin ta, saidai kiyi hakuri ranki shidade Abdulmalik yafi karfin baiwa kowane kwarya da abokin gurbin ta, mungode da karamci."

Jitayi wani tukuƙi ya tsaya mata a bisa kahon zuciya, yana mata ƙuna yau ga Abdulmajid yasamu damar mayar mata da martani a kaikaice dan ta sanar mashi da bukatar ta, lallai ya zama dole ta maida shi tunanin shi, cikin gadara tace.

"tambayar ka da kaga nayi kaba Yarima auren Bahijja, nayine dan baku hakkin ku, bawai ina neman shawarar ku bane"

A zuciyar shi kuwa kallan ta yakeyi yana mamakin mugun hali irin na Zulaiƙa sam bata biyo halin mahaifin taba, sannan ya zama dole ya nuna mata kuskuren ta sannan tasan itafa yarinya ce akan shi, cewa yayi.

"Nafahim ta sai dai kisani a wannan muhallin kaf duniya ba wanda ya isa ya aurar da Bahijja saini mahaifin ta, shiyasa ma *Manzon Allah S. A. W yace iyaye su zaɓa ma yarsu budurwa mijin aure da kansu, idan kuma ta taɓa aure toh su bata shawara wajen zaɓar mutumin kirki,* dan haka nine mahaifin Bahijja kuma ni zan zaɓama ya'ta miji, ina kara baki hakuri dakibar wannan maganar, kibawa Abdulmalik hakuri,na rigada naima Bahijja miji, ma'ana bazata auri Yarima ba."

Wani irin daram daram taji gaban ta na duka da sauri sauri cikin ɓacin rai tace.
"Ina tunanin dakai da Bahijjar duk a kalkashin ikona kuke ko.?"

Murmushi mai ma'anoni yace. "tabbas a wajen ƙangin bauta ba, amman a wajen da shari'a tace Bahijja ikona ce harsai tayi aure sannan zata koma kalkashin ikon mijin ta, dan haka idan aikin bauta kikeso miyimaki a matsayin mu na bayi yan wahala tsatson bayi wa'anda sukayi gadon bauta, zamu iya yimaki, amman a wannan fagen na aurar da ya'ta ni Abdulmajid Abdullahi Jafar iko nane kuma hakkina ne."

Mikewa tayi tana zagaye falon tana dukan hannun ta cikin tafin hannun ta ɗaya, tanajin maganganun Abdulmajid har tsakiyar kwanyar ta, juyowa tayi tana taune lips ɗin ta na kasa tace.

"Yayi kyau sai dai bazan takura maka a halin yanzun ba Abdulmajid kaje nan da kwana biyu kayi tunani ina sauraran ka, koba komai an huta da ƙangin bauta, ya kaji wannan labarin.?"

ta karasa maganar tana shu'umin murmushi mai ma'anoni, shiko Abdulmajid baki ɗaya Zulaiƙa a tafin hannun shi take, saboda yafita shekaru kusan tsaran mahaifin tane, sai dai kawai ya kyaleta, shima irin murmushin da tayi yayi yace."Shikenan ki huta lfy."

Baijra cewar taba ya fita itama Binta har zata bishi Sarauniya Zulaƙa taa tsaida ta, wani kaskantaccen kallo taima Binta sannan tace. "Uwar bayi matar Abdulmajid jikar Jafar kinga irin taurin kan mijin ki ko? Arziki na binku kuna gudu, miyafi ranku kuga 'yarku ta ɗaukaka ta auri ɗan Saifulislam Sulaiman sannan magajin Sarauniya Zulaiƙa Abdulhamid Abduljabbar na II, sannan magajin wannan Masarautar ta zama 'yantatta harku? Amman girman kai da wauta suna neman hanabshi, ina san ki kara jaddadama shi ni Sarauniya Zulaiƙa ba shawarar shi nike nemaba Umurni ne! zaki iya tafiyar ki baiwa uwar bayi."

Russunawa tayi tana al'ajabin irin mugun halin Sarauniya Zulaiƙa.
cikin nutsuwa tace "mungode Allah yakara girma."

Batare da amsa addu'ar da Binta tai mata taba ta shige cikin ɗakin ta, jin ana kiran sallar zuhur, itama Binta fita tayi ta tafi gida can ta iske Abdulmajid yana ta faman faɗa itadai Bahijja wanke wanke takeyi duk ta tsorata dan zuwa yanzun ba karamin jin shakkar mahaifin ta takeyi ba, Mairo ce ta shigo cikin sanyin rai tace.
"Haba Ya Abdulmajid kayi hakuri komai zaizo cikin sauki fushi ba naka bane kodan darajar ɗan ta."

Cikin fushi yace."Yimin shiru Maryam, bazan ba Yarima Malik auren 'yata ba, shi daban mahaifiyar shi daban, wlh ya zama dole in koyama Zulaiƙa hankali kartayi anfani da wata dama na tana uwar gijiyar mu, ta dinga cimana zarafi."

Shiru tayi dan talura ranshi ya ɓaci sosai, ita dai Bahijja ko motsawa takasayi dan tsoro da yagama buwayar ta a cikin zuciya, sai dai taji ɗan sauki a ranta da taji Sarauniya Zulaiƙa ce da kanta ke nemawa Ya Malik dinta auren ta,wani side na zuciyar ta kuma cike yake da tsoro tasan inda har Abban ta yace aaa to Allah kaɗai zaisa ya sauko.

Jinya yakira sunan ta ne ya dawo da ita cikin duniyar tunanin data lula, amsa tayi ta taso da sauri sannan ta duka cikin yin kasa da kanta tace. "Abba gani."

Kallan ina hankalin ki da tunanin ki ya tafi yai mata, sannan yace.
"Kina aikin me, kuma ina hankalin ki ya tafi da bazaki amsa kiran da nike maki wajen sau ukku ina kiran ki."

rausayar da kanta tayi tareda goge kwallan da suka gangaro mata. a saman kyakkyawar fuskarta cikin sanyin rai tace. "Abba kayi hakuri banji ba."


"Kinajina inasan inkara gargaɗarki da kiyi gaggawar fidda Yarima Malik a cikin zuciyar ki tunkan dare yai maki danni bazan bada auren 'yata ba a inda ba'asan darajar taba,bare ƙimar taba, in kina takamar Abdulmalik na sonki kuma yana kaunar ki, ai tunda kika rasa soyayyar uwar miji kinsara rabin soyayyar ɗanta, dan haka ban lamince ba kuma ban amince ba inafatan kin fahimta.?"

rausayar dakanta tayi tana kokowa da kwallar da suke neman ziraro mata, cikin sarkewar murya tace. "To Abba nagode.''

Cikeda gamsuwa yace. "tashi kije lokacin sallah yayi."
Tashi tayi ta shege ɗakin ta tana kwantawa bisa tabarmar dake shimfide a cikin ɗakin, wani irin kukane ta fashe dashi mai tsuma zuciya, ta rasa kukan me takeyi na rashin amincewar Abba ne ko kuwa tausayin shi takeyi, dan tasan zuwa yanzun tafara ba zuciyar ta hakurin rashin Ya Malik, sai dai tasan abune mai wahala ta hakura da shi cikin ruwan sanyi, jitayi an taɓamata baya, a sanyaye ta dago da rinannun idanun ta masu kama da garwashi ga kwalla masu ɗumi yana sauka bisa kuncin ta, Inna Mairo ce ta janyota jikin ta, cikin sigar lallashi tafara bata hakuri, tace.

"Haba 'yata kidaina kukan nan addu'a kaɗai itace abinyi a halin yanzun."

Sake kankame ta tayi cikin karyayyar murya tace. "Inna nabani kinji abinda Abba yace."
Bubbuga bayan ta tayi tace. "Ya isa kibi a sannu 'ya'ta komai zai zama labari."

Haka dai tacigaba da bata hakuri duk abinda suke cewa Binta najin su, wani irin tausayin 'yarta taji yana ratsata, sai dai ita bata da abin cewa, a cikin wannan zancen, fata dai Allah yakawo mafita."

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

A wajen Lurwan kuwa tafiya tai nisa samun wani waje yayi ya yada zango yaci abinci sannan ya gabatar da sallar matafiya ma'ana (kasaru) sannan yaci gaba da tafiyar shi.


Bayan kwana biyu yau MalikusSaif ne zaune da alama wanka yayi yaɗan samu sauki sannan yafara jero sallar da baiba, yana gamawa ya jinjina bayan shi jikin gado, Huzaifa ne ya shigo tareda Zahara'u suka zauna, cikin kulawa gimbiya Zahara'u taima shi ya jiki, ba yabo ba fallasa ya amsa, sannan ya maida idon shi ya rufe kamar mai bacci, ɗan shiru ne ya karaɗe ɗakin, badajimawa ba hadiman gimbiya Zahara'u suka shigo ɗauke da foodflask, suka ajiye, sannan suka fita, kallan Yarima Malik tayi still idanun shi na rufe, buda baki tayi kamar maijin tsoro tace. "Sannu Yarima na,ga abinci kaci."
Har yanzun dai idanun shi na rufe, hakan yasa Huzaifa yace. "Kibar shi yakara hutawa anjima zaici kinga baijima da tashi ba."

Gyaɗa kai tayi alamun gamsuwa, sannan ta tashi taimasu sallama ta tafi, haka Sarauniya Zulaiƙa ta shigo duba shi wajen magrib nan ta iske foodflask jere cikin jin daɗi tace. "Huzaifa wannan fa daga ina.?"
Sunkuyar dakan shi yayi yace. "Ummu Zahara'u ce ta kawo mashi."

taji dadi, saboda tana kaunar Zahara'u sai dai yanzun lamarin yafi karfin tunanin ta, zama tayi gafen shi ta ɗan shafa gefen fuskar shi, cikin sanyayyar murya tace. "Abdulmalik."

bude idanun shi yayi ya azasu saman fuskar ta duk sun rine, a hankali ya bude baki yace. "Ummu."
taji dadi yanda ya ambaci sunan ta, cewa tayi. "Sannu Allah yabaka lfy."
"Ameen yace." sake rufe idanun nashi yayi, ita kuwa buɗe kular dake gaban ta tayi wani kamshi ne ya daki hancin ta saida ta lumshe ido, ganin farfasun zabbi yaji kayan hadi, flat ta ɗauko ta zuba mashi, sannan ta ɗauki kofi ta zuba mashi dafaffiyar madara, cikin kulawa tace. "Abdulmalik, bude idanun ka kaci abinci."

Bude idanun yayi ya sauke su bisa flat ɗin sai dai take yaji kwata kwata bai mashi ba, asalima ji yayi zuciyar shi tafara tashi, sake rufe idanun nashi yayi tareda girgiza kai alamun yako shi.

sake cewa tayi. "Ko kadan ne kaci mana antaba ciwo bacin abinci."

baice mata komai ba, saima kauda kanshi gefe da yayi, duk da yanajin azabatattar yunwa amaman ji yake inba Bahijja ta bashi abinci ba, bazai iya cinshi ba, kwarama furar da Saifulislam ke aiko mashi itakam yana ɗan sha.
Haka ta hakura ta kyale shi kiran sallar isha'i yasa suka mike, shiko Malik kabbara sallar shi yayi dan azaune yake yinta dan ko kaɗan baijin karfin jikin nashi.

**********************************

Washe gari da safe, a wajen Lurwan duke yake a cikin fa'dar alfarma ta Sarki Abu-Jalal ba karamin karrama shi akayi ba, cikin kulawa Sarki Abu-Jalal ya kalli Lurwan yace.
"Abokin Abdulmalik sannu da hanya ya jikan nawa yake.?"

Fuskar shi ɗauke da murmushi yace. "Yana lfy, ina fatan nasame ku lfy."

Rausayar dakai yayi sannan yace. "Alhmdullh."
Ɗan nazarin yanayin Lurwan Sarki Abu-Jalal yayi, ranshi ya bashi kamar ba lfy, cikin kulawa yace. "Inafatan ba wata damuwa ko Lurwan.?"

Girgiza kai yayi sannan yace. "Ba arasaba, sai dai ina san zanyi magana da maigirma Sarkin musulmi Sarkin Runo."

Murmusawa yayi yace. "Sarkin gida jekaba Lurwan masauki ya huta a tabbatar anba shi abinci da kayan bukata."

Rusunawa Sarkin gida yayi, sannan Abu-Jalal ha kalli Lurwan yace. "Jeka huta kaci abinci."
"Toh yace sannan yaima Sarki Abu-Jalal godiya yabi bayan Sarkin gida suka tafi...

_Ko miye hikimar zuwan Lurwan wajen Sarki Abu-Jalal, sannan wace magana zaiyi da Sarki Abu-Jalal?_

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Bayan kwana biyu, asarar mai rai, kwanaki nata raguwa, ranar kuwa akata shi da tashin hankali a cikin Masarautar Daborah, misalin karfe biyu na rana kasancewar ranar Juma'a ne antasu masallaci duk musulmin da kagani fuskar shi cikeda annuri na murnar wannan rana mai alfarma a duniya musamman wajen musulmai.

Jakadiya Hajara ce ta fito daga sashen Yarima Malik da gudun ta, tayi sashen Kangiwa sai dai bata same shi ba, kasancewar shine liman yana masallaci bai kaida dawowa ba, yakan tsaya yaima wasu karin karatun alqur'ani da hadisai sai anyi la'asar suke tashi da anyi sallah kowa ya kama gaban shi, shi kuma yana anfani da wannan damar wajen ziyartar dangin shi dana matar shi, duk da kasancewar shida Zulaiƙa auren zumunci ne akai masu, dan dai sun hadu a 'yayan mata zir shida ita, koda Jakadiya ta iske bai nan, batai kasa a guiwa ba ta wuce wajen Sarauniya Zulaiƙa, aiko ta isketa dasu gimbiya Salsabila da gimbiya Abida sai Binta dake ma Sarauniya Zulaiƙa tausa, yanda sukaga Jakadiya yai masifar ɗaga masu hankali, da sauri duk suka mike da alamar tambaya hatta Binta saida ta tashi, numfashi ta sauke cikin kiɗimewa tace.
"Ranki shidade MalikusSaif Yarima jiki ya tsanan ta."

Ai batajira jin karshen zancen Hajara ba suka dunguma su dukan su, wannan karan kuwa harda Binta harta fara kuka dan harga Allah tanajin Yarima tamkar ɗan cikin ta, a hanyar su ta tafiya ta hadu da Matawalle dasu Yazid yanda sukaga suna yar tsere take saida zuciyar Matawalle ta buga dan tunran da yai fushi da Zulaiƙa bai kuma waiwayar suba, maye masu baya sukayi, suna shiga suka tadda Yarima yana ta amai baki cikin shi harda sirkin jini, kuka suka hauyi ita kuma Sarauniya Zulaiƙa ta rungume shi jikinta ga idanin shi sun kakkafe sunyi haske kyal dasu, koda Matawalle ya kalli fuskar Malik yasan ba wani abune ke damun Malik ba damuwa ce kawai, zuwa yayi ya ɗago shi shida Huzaifa suka kama shi sukayi dashi tafkeken falon shi na alfarma bisa kafat suka kwantar dashi, suna mashi fiffita, kallan gimbiya Abida yayi yace. "Jeki gida cikin dakina ɗauko mani wata bakar jikkata kiyi sauri," haka ta juya da gudu ta tafi.

Kafin kace kwabo labarin lalurar MalikusSaif ta karade kaf illahirin Masarautar Daborah har cikin turakar bayi, Bahijja na zaune Salame tazo mata da labarin, batasan sadda tafara kuka ba mikewa tayi zata fita da niyar taje gun Ya Malik ɗin ta, har ta kawo bakin fita ta hadu da Abdulmajid, kallan ina zuwa yai mata gashi tana kuka kamar famfo, komawa tayi da gudu ta shige ɗaki tana kuka, baice mata komai ba, dan yasan dalilin kukan nata shi kanshi jin halin da Yarima ya shiga ji yake kamar yai kuka, wanda da yawa a cikin bayin su, rabi da kwatar su sai kuka sukeyi, cikin kankanin lokaci suka tafi masallaci akaita addu'a Allah yabama Yarima lafiya dan ba kadan suka tsorata da lalurar MalikusSaif ba, anan ne Saifulislam yaji ciwon MalikusSaif ya tsanan ta, sai dai lokacin baifi minti biyar ba ayi sallar la'asar ba, hakan yasa bai fita daga masallaci kiran sallah akayi sannan aka bada sallah da aka gama akayima Yarima addu'ar samun lfy a wajen mahalicci Sarki buwayi gagara misali, kowa ya tafi jiki a sage.

Koda Saifulislam ya fita daga msallaci sashen shi ya wuce ya hado magani sannan ya wuce sashen ɗan nashi lokacin har Matawalle ya bashi magani sai dai ya daina aman da yakeyi amman idanun shi a rufe, da sallama abakin Kangiwa ya shigo ya zauna yana tambayar su ya mai jiki, da sauki sukace, cikin tausayawa yace. "Allah ya sauwake yasa kaffara ne." baki ɗayan su suka ce Ameen.

Mikoma Matawalle kwalbar magani yayi yace.
"Gashi a dinga bashi sau uku a rana safe, rana da dare." toh Matawalle yace, take ya bashi, mikewa Saifulislam yayi yace. "Zan wuce Allah yakara afuwa." ameen Matawalle yace. a ranshi ko yana mamakin zuciya irin ta Saifulislam, ga tarin so da kaunar ɗan shi nan a cikin idanun shi, amman zafin Zulaiƙa daya keji a cikin ranshi ya danne tausayin shi akan ɗan shi.

Itako jikin ta yai sanyi hakan yasa tabi bayan shi tace. "Abu Malik bai kamata katafi kaga halin da ɗan mu ke ciki."

ba tareda ya waigo ba yace. "Sauki da rashin sa na Allah ne."
Fitar shi yayi bai kuma bi takanta, itako kwalla masu ciwo ta goge tasan samun kan Saifulislam agare ta abune mai wahala mutun ne mai hakuri sai dai bai iya hukunci ba.

Dawowa tayi ta iske MalikusSaif ya farka da salati a bakin shi sai dai da idanu ya dinga bin mutanen dake wajen sannan daga karshe ya sauke su kan Binta a hankali yace. "Umma ina Bahijja miyasame ta?"

da idanu sukabi inda yake kallo suka ga Binta da take tafaman kuka tamkar ammata mutuwa, wani masifaffan kallo Zulaiƙa ke mata mai ɗauke da ma'anoni kala kala, itako murya a shaƙe tace. "Sannu Yarima Allah yabaka lfy."

Bai amsaba yace. "Ki kiramin Bahijja."
Matawalle ne yai mata alamar ta tafi, hakan yasa Sarauniya Zulaiƙa batai yunkurin hanawa ba, tashi tayi ta fita, ta tafi turakar bayi....

Itako Bahijja har ciwon kai ya addabe ta, tana isa ta iske ɗakin Abdulmajid bude alamun yana nan, ciki ta shiga ta iske shi yana addu'a sai dai kanajin abinda yake cewa duk da ba sosai yake daga muryar shi sama ba, zama tayi tanajin yanda yake rokon Allah yana cewa.

~"Ya Allah dan kudurarka da buwayarka ya Allah dan zatinka, ina rokon ka dan girman sittin na alqur'ani nayi tawassali da darajar suratul fatihati, da suratul bakara, Ali imran, Nisa'i, da Ma'ida ya Allah kabawa bawan ka mai yawan zunubi agare ka, kuma mai yawan tuba zuwa gareka, bawan ka Abdulmalik Allah kaba shi lafiya, ya Allah dan so da kaunar dake tsakanin ka da fiyayyen halitta annabi Muhammad SAW, ya Allah kasan ya wannan al'amrin da muke ciki yazama alkhairy agremu kabawa dukkan ɗaukakin musulmi lfy a duk inda suke ya Allah da sunayen ka tsarkakku kace mureka dasu zaka karɓa mana ya ubangijina ka karɓama adduar mu, Allah kasa mucika da imani."~

shafawa yayi tareda yin sallatin annabi sannan ya shafa da ```subuhana rabbuka rabul izzati amma yasfuna wasallamun alal mursalina walhamdulillhi rabil alameen."```


Baki ɗayan su suka shafa, waigowa yayi ya kalleta cikin kulawa yace. "Harkin gama aikin ki."
rausayar dakai tayi tana share kwalla tace. "Aaa." abinda yasa baida mu da ya tambayi Binta ba dalilin kukan taba yasan da wahala taje aiki ba tareda Sarauniya Zulaiƙa ta wulakanta taba, harya saba, shiyasa kukan Binta bai ɗagama shi hankali, sake cewa yayi. "Kin samu hutu ne?"

Murya sarke tace. "Dan Allah Abban Bahijja alfarma nake nema wajenka." yai mamakin jin wannan kalmar a bakin Binta sai yace. "Uhmm inajin ki."

"Dan Allah kabar Bahijja taje ta dubo Yarima Malik.?"

Wani wawan kallo yai mata yaci gaba da zan carbin shi, sake matsowa tayi ta rike hannun shi tace. "Wannan itace alfarma ta agareka domin Yarima yana son ganin ta kuma bai lafiya."

"Baceman dagani Binta." karo nafarko daya ambaci sunan ta kai tsaye tsawon shekarun da suka kwasa tare akalla ita kanta sunkai. Shekara arba'in tare daya ke ya jima bai aure ba, saida yakai wajen shekaru arba'in da biyu yai aure, ita kanta Binta sherkarar ta sittin a duniya wanda shi kuma Abdulmajid yake da sherkaru Casa'in a duniya ya samu haihuwar Bahijja lokacin yanada shekaru kusan saba'in da biyar, dan harya fitar da rai da haihuwa amman da yake a wajen Allah ba yanda bai ikon shi saiga shi sun samu haihuwa lokacin duk karfin su ya kusan karewa, ba mai wannan sai Sarki buwayi gagara misali.

Jiki a sabule ta mike sai dai takasa daina kukan da takeyi, wani irin tausayin Yarima Malik ya dira a zuciyar Abdulmajid take alkhairan da ya dinga yi masu ya dawo mashi sabo a zuciya Abdulmalik bai cancanci haka agresu ba, sai dai daya tuna da cin zarafin da uwar shi tai masu sai yaji tsanarta ya kara shiga cikin ran shi, duk abin nan Bahijja nanan lafe tanajin yanda Umman take neman alfarma wajen Abban ta amman yaki amincewa, batasan ta iso bakin kofa ba sai taji sun ingiji juna dukawa kasa Bahijja tayi tace.
"Yi hakuri Umma ban kulaba." batace mata komai ba ta fita ta koma ta faɗa masu sakon da Abdulmajid ya bada, saidai ba abinda MalikusSaif yace sai ya runtse idanin shi, shiko Matawalle baiyi mamaki ai abinda Zulaiƙa tayi ta cancanci fiye da haka, gashi yanzun reshe ya juye da mujiya, itako Zulaiƙa ta cika tayi fam, badan ganin idanun Matawalle ba da tasa anje ancima Abdulmajid mutunci dan tana ikirarin aisu bayin tane, zaunawa tayi dabas bisa kushin jiki ba kwari tanajin kanta na sara mata.

itako Bahijja jin kakin da Abban ta yayi alamun zai fito a cikin ɗakin shi yasa da sauri ta duka kamar mai kaye kayen kayan tsakar gida, dan ta tsorata, saidai ba aikin take ba, kallan tsaf yai mata sannan ya girgiza kai yana mamakin wai ƴar daya haifa za tai mashi wayo, cikin kula yace. "Bahijja." da sauri ra karaso kusa dashi ta tsugunna sannan tace. "Abba gani."
'tashi kije sashen Yarima Abdulmalik yana neman ki, bance ki samu waje ki zauna ba, sannan kuma kiji kiƙiji sannan ki gani kiki gani, kinaji na!"

"Eh Abba naji."
Wucewa yayi ya nufi wajen aikin shi itako ta rasa abinda takeji a cikin zuciyar ta murna take ko kuwa bakin ciki takeji, shiga tayi ɗaki ta sako takalman ta sannan ta fito tareda sayo masu kofar gidan nasu, sannan ta tafi, a hankali ta shigo cikin Masarautar wata iriyar iska ce ke busawa tana shiga cikin sassan jikin ta, na inuwar mangwaro da a ka kewaye illahirin katangun Masarautar, a sannu take taka kafarta, harta isa bakin side din Yarima Malik, haka nan taji gabanta na dukan tara tara kamar ta fasa shiga haka taji, a hankali ta saka kafarta cikin sanyayen sashen Yarima Malik, haka ta dinga saka kafarta harta isa cikin tsakiyar falon, idanun tane suka sauka kan Yarima Malik dake kwance gefen Matawalle idanun shi rufe, sai gefen damar shi su Huzaifa, daga gefen haggun sa kuwa Sarauniya Zulaiƙa ce sai gefen ta Ummin su Huzaifa ce, sannan gimbiya Abida matar Matawalle, daga kasan kafat kuwa Binta ce tsugunne, itama Bahijja gefen mahaifiyar ta ta tsugun bakin ta ɗauke da sallama wadda tun ɗazun takeyin sallama amman hankalin bai jikin su basu san tayi sallamar ba, Matawalle ne ya amsa mata, sai a lokacin suka lura da shigowar Bahijja, sanyayyar ajiyar zuciya ce Sarauniya Zulaiƙa ta sauke ba tareda kowa yasan ta sauke ba, sannan ta cigaba da watsama Bahijja wani irin mugun kallo mai ma'anoni, sunkuyar da kanta tayi kasa tana wasa da yatsun hannun ta, cikin sanyin murya tace.
"barka da yamma ranki shidade ya mai jikin.?"

Rausayar da kafarta tayi cikin izzah ta gadara ta amsa a dakile.
Huzaifa ne ya kalli Bahijja yace. "Jiki da sauki ya samu bacci ai."

Dan satar kallan shi tayi sai taga yai mata haske sosai sannan ya dan rame saidai duk da haka yai mata kyau, sauke ajiyar zuciya tayi tace.

"Allah ya sauwake yasa kaffarane." ameen Matawalle yace.

Sarauniya Zulaiƙa ce tace. "Sai yanzun kikazo daman Abdulmalik yace akiraki."
"yanzun Abba yace inzo."
cewar Bahijja.
Ɗan taɓe baki Sarauniya Zulaiƙa tayi aranta tace. Uhmm Abdulmajid kenan da yake yanzun wajen ku ake nema zanyi maganin kune."

Juyawa Yarima yayi a hankali ya bude idanun shi ya ɗan bude a hankali sai dai bishi bishi yake kallan mutane, a hankali idanun shi suka fara washewa tashi yayi zaune ya ɗan kalli Huzaifa sai kuma ya ɗauke idon shi, jin zazzakar muryar Bahijja data karaɗe illahirin kunnen shi tana cema Jakadiya, "ga kwaryar."

Ansa tayi tace. "Abdulmalik ga furar kasha angama dama maka."

Ko kadan baijin abinda Jakadiya ke cewa ya kafe Bahijja da firgitattatun idanun shi, hakan taji ranta ya bata ana kallan ta saboda tsikar jikin ta ke tashi a hankali, kamar wani abu nai maka tafiyar tsutsa, takasa sakewa ji tayi kunnen ta ya amsa wani irin amo wanda raban da taji irin shi harta manta, da sauri ta ɗago kanta ta kalle shi yace. "Bahijjaah yaushe kikazo nan?"

Muryar ta na rarrabewa tace. "Banjima ba, Ya Malik ya jikin naka."

Samun kanshi yayi da murmusawa wani irin karfi yaji a lokaci ɗaya yace. "da sauki kanwar Malik."

Sai kuma yai shiru ganin Ummu dan yama manta dasu a cikin falon,kai Matawalle ya gyaɗa mata sannan yace.

"Ya kamata kaci abinci Abdulmalik." toh yace, kallan juna suka dingayi can kuma sai yace. "Sakwara nike so Kawu."
Cikin jin dadi Sarauniya Zulaiƙa tace. "Sannu Yarima bari insaka akawo maka."
"Aaa kibari tunda ga Bahijja tazo sai

Please Login or Register in order to submit comment