Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matar itace Sarauniya Zulaiƙa."? Murmushi Binta tayi tace. "Eh ita ce Sarauniya Zulaiƙa kuma mahaifiya ga Yarima MalikusSaif."
shiru tayi tana mamakin yanda ta kasance azzaluma, amman kuma ɗanta mutumin kirki ji tayi anta ɓata, da sauri ta kalli Mahaifiyar ta, tace. "Umma ina Abba." mikewa tayi tace. "yana wajen aikin shi, bari inje in dawo ƴata." ''toh Umma saikin dawo." haka Binta ta tafi wajen Sarauniya Zulaiƙa tana isa ta iske ta kishingiɗe ta rufe idanun ta, koda ta isa isketa tayi idonta rufe dukawa tayi gaban ta tace.
"Ranki shidade gani kiranki ya riskeni." bude idanun ta tayi ta watsa su kan Binta, ita kanta saida ta tsorata yanda taga sun sauya sunyi jajir kamar garwashi, a gadarance Zulaiƙa tace. "Binta mi kikayi ma Saifulislam da har yasa aka kwace Bahijja? Ko kinje kin gaya mashi wani munafuncin naku na bayi."?
Rasa abin faɗa Binta tayi tana mamki ashe bada izinin ta bane aka saki Bahijja, a kiɗime tace. " Ranki shidade ni kaina banda wata masaniya dan gane da hakan naga yasa an saki Bahijja amman ina neman afuwar ki." cikin tsawa tace. "Yimin shiru makira akwai wadan da suka kai bayi tsabar munafurci da tuggu da kunga, Kangiwa kun langaɓe shi kuma Sarkin tausayi yaji tausanku kun mallake min ɗa bai ganin kowa da ƙima sai ku kuma bai tausan kowa sai Bahijja wlh indai na cika ƴa ga Sarki Abdulhamid sai nayi maganin kaf zuri'ar Jafar da munafuncin ku na gadan gado da kuka saba, ɓace mani dagani sakarai kuma anjima kiyi maza ki hado mani bayin da zasu dinga kulawa da madafa idan za'ayi wannan kaddararran Yakin ki tabbatar da anba Jarumai na kulawa ta musamman kinanjina.!"da sauri tace "eh ranki shidade umurnin ki abun tunkaho a gareni Binta na godiya."
da sauri ta tashi ta tafi har tuntube take rafkawa tana godema Allah da yasa yau Sarauniya Zulaiƙa batasa anduke taba ko wani cin zarafin haka ta kama hanyar tafiya turakar bayi wajen wucewa ta gefen sashen Yarima MalikusSaif taga Ladidi da wasu bayi na aiki tareda Yazid da alama shi ya saka su aikin dukawa tayi ta gaida Yazid harta tafi taji wata baiwa ta risketa dukawa tayi har kasa ta gaida uwar bayi sannan tace. "Allah ya taimaki uwar bayi Yarima Malik ne ke kiranki yana ta gefen lambun dake sashen shi" ita ko tsaye tayi tana mamaki domin ba taga Malik ba sai dai taga Yazid yana sa bayi aiki, a wani bangaren na zuciyar ta kuwa tana shakka kada Sarauniya Zulaiƙa ta kamata da danta, sai dai ba zata iya kin zuwa ba, haka takama hanyar tafiya wajen MalikusSaif.

tana zuwa ta iske shi zaune saman shinfida gefen shi kuma Yazid ne cikin girma mawa Binta ta zauna ta gaida Yarima gani tayi ya ɗanyi mata duhu kadan, aranta ko cewa tayi Allah Sarki Yarima komu ba musan taya zamu sa kanta maka ba, gashi ka dawo mana da ƴarmu, tabbas nasan kana fuskan tar matsala a wajen mahaifiyar ka sai dai laifin mune mu muka jamaka hakan, karfin hali tayi tace.
"Allah ya taimaki Yarima kiran ka yasameni, inaimaka barka da dawowa Masarautar Daborah sai dai Binta ba tasan taya zata fara godema ka ba, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi."
Murmushi Yarima yayi yace. "Umman Bahijja basai kun gode mani ba nine zan godema ku sannan Allah shine abin godiya da yadawo damu cikin aminci, ina Bahijja."?
Rausayar dakai Binta tayi tana mamakin karamci irin na MalikusSaif.
Cikin jin dadi tace.
"Tana gida, dan Allah kai mana godiya wajen Kadimulislam yasa an saki Bahijja.
Jinjina kai Malik yayi yace.
"Yima kai ne karki damu, ya jikin ta da sauki ko."? "Eh da sauki na barota tana bacci." haka nan ya samu kanshi da murmusawa ya rasa dalilin da yasa yake jin dad, idan yaga Bahijja cikin aminci, a zahiri ko cewa yayi ki gaida mani ita." sannan ya bata wata leda cike da kayan marmari yace takai mata, sannan ta gaida mashi da Abban Bahijja, haka ta amsa tana godiya sannan ta tafi ranta fas tana sama MalikusSaif albarka....

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿
A wajen Sarki Lahazu kuwa shima ya gama shiryawa tsaf shida Jaruman shi da sauran hadiman shi da zaiyi tafiyar dasu, sannan yayi sallama ga matar shi gimbiya Ƙamariyya, kowa ya hau saman dawakan su, Yarima Haishir ne kawai suke jira shima bada jimawa ba ya fito yai sallama sa Mahaifiyar shi, sannan suka kama hanyar tafiya Masarautar Daborah.......

***********************************
Koda Binta ta koma haka ta iske Bahijja tayi wanka harta gyara masu mahallin su, tana zaune ita da Mairo dan suna ba Bahijja kulawa ta musamman Binta na da wowa Bahijja ta ganta da sannu da zuwa taima Umman ta sannan tace. "Umma amman kin dawo da wuri, ko kunan Masarautar baku dadewa wajen aiki."? Murmushi tayi ma yar tata, tace. "Ƴata kenan ai Bacci kawai ke dawo damu gida, yaudin ba aiki sosai kinsan Masarautar tamu ba wani kwanciyar hankali ne da ita ba suna shirin Yaki ne."
da sauri Bahijja ta ware idanu tace. "Umma Yaki kuma miya jawo Yaki ana zaman lafiya.?"
"Yata kenan saboda ke za'ayi wannan Yakin." cike da mamaki tace. "Umma saboda ni fa ki kace niko minene nayi da za'ayi Yaki akaina bayan ba kowa yasan da zama na a cikin wannan Masarautar ba sai waɗan da suka jima a cikin ta."
Murmushi Binta tayi tana kallan yr tata tace.
"ta yaro kyau take bata ƙarko, akan ki ne za'ayi Yaki, uban gidan ki Baidulƙais ya aiko da sako ga Sarauniya Zukaiƙa yace, zai Yake ta saboda
ta karya alkawali ta ɗauke ki kinji dalili."
dafe baki Bahijja tayi tace. "Wlh Umma Ya Malik a Masarautar Waisu ya same ni saboda Yariman Masarautar ya kwaceni a hannun wasu ashe shima so yake ya lalatamani rayuwa shine fa Yarima da yaje Masarautar ya ganni ya amso ni har saida akayi kashe kashe sannan muka iso nan na bani ya zanyi, Umma inko har a kaina za'ayi wannan Yakin zan shiga matsala." cikeda tausayin ta tace."kiyi hakri Allah na tareda ke kinji ƴata kuma insha Allah mune da nasara a wannan Yakin." da Ameen ta amsa a ranta ko tausayin Yarima Malik takeyi taga daga dawowar su zasu afkama makiya, ji tayi Umman ta rike mata hannu ta ɗaura mata leda a hannun ta tace. "Yarima yace akawo maki kici yana gaidaki." wani irin dadi taji tace "Umma Ya Malik aminci ne a gareni nagode ma shi, Allah ya basu nasara." ita da Mairo da Ameen suka amsa......

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿
Suko su Sarki Baidulƙais tafiya tai riba tunda suna hangen ganuwar Masarautar Daborah duk da dare ya fara amman zasu iya isa kafin duhu ya gauraye garin haka sukaci gaba da sassarfa a saman dawakan su....



_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم




Episode 33&34



Koda suka isa bakin Masarautar Daborah tsaya wa sukayi suna tunanin ta inda zasu shiga cikin Masarautar saboda tsayin katangun dake kewaye da Masarautar ga kuma ganuwa ya zagaye garin, Sarki Baidulƙais ne yace ma Sarki Danwar. "Kaga waɗan nan mutanen yanda sukai ma Masarautar nan tasu? naso tunda ga yanzun su san da zuwan mu amman kubamu shawara taya zamu farma su ba tare da sun san da isowar muba."? Jinjina kai Sarki Danwar yayi yace.
"Kashi ɗaya zamu sa su tuntuɗa yan uwan su in yaso daga baya sai su bude mana kofar mu shiga, haka nike ganin kamar zaifi."
cikin jin dadi yace. "Kwarai hakan za'ayi shiyasa nike san harka dakai, kana kawo mafita."
Commenders din Yaki ne suka dinga za gaye Jaruman su suna gyara masu sahu sahu iya ganin ka, dan ba karamin yawa ne dasu ba.....

****************************
A cikin Masarautar Daborah kuwa Yarima Malik ne zaune ya kasa bacci, ya rasa mike mashi dadi a rayuwa duba agogo yayi yaga dare baiba ko takwas ba tayi ba da yake yana yin damuna ne da, marece yayi sai kaga kamar dare ne yayi, mahaifiyar shi ce ta faɗo mashi arai da sauri ya mike yace. "Kai bai kamata ace har yanzun banga Ummu ba nasan ba zata zoba tunda tana jin haushi na."
mikewa yayi ya ɗauki alqabbar shi ya ɗaura a jikin shi sannan ya nufi sashen Sarauniya Zulaiƙa yana shiga ya isketa dasu Yazid sun gama shirin yanda zasu bullowa makiyan su, gaisawa sukayi da Yazid ganin Malik yazo yasa shi tafiya, zama yayi gefen ta sannan ya gaida ta kallo ɗaya tai mashi ta kauda kai,take yaji jikin shi yai sanyi sake matsowa yayi ya rike hannun ta sannan yace. "Ummu kiyi hakri akan abun da ya faru nasan ni mai laifine gareki amman bazan iya jure fushin kiba akaina dan Allah, Ummu duk abinda ki kaga ya dace kimani amman banda fushi dani." Kallan shi tayi a ranta ko cewa tayi, Malik kenan tuni karusa komai kaida ubanka ammn a zahiri ko cewa tayi. "Ya kamata kaje ka huta karka damu ai komai ya wuce."shima kallan ta yayi yana nazarin ta, dan bai yarda da ta hakura ba yasan in ya matsa yanda take cikin ɓacin rai komai zai iya faruwa,cewa yayi. "Nagode miki uwa mai alkhairi, mai tausayi kinfi kowa alkhairi Ummu Allah ya ɗauraki akan makiyan ki."
da ameen ta amsa masa a takaice, Binta ce ta shigo tai mata sallama zata tafi gida kallan ta tayi tace. "Kije kice ma Sarkin horo ya kwan to Abdulmajid sannan kice ma Abdulmajid cikin daren nan a shirya mani bayi maza guda ashirin su zasu kulaman da lafiyar Jarumai na."
wani dadi ne ya ziyarci Binta da sauri tace. "Shikenan Allah ya kara maki lfy angama." haka ta tafi cikin sauri ta isar da sakon Sarauniya Zulaiƙa, haka aka saki Abdulmajid tare da Binta suka wuce gida yana zuwa yaga Bahijja murna wajen Abdulmajid bayyana ta ɓata lokaci ne, hakama Bahijja sai murna takeyi harda kwallar ta dan murnar ganin mahaifin ta, ganin yanda ya shagala da ganin yar sa, hakan yasa Binta ta gaya mashi sakon da Sarauniya Zulaiƙa ta bata, yana jin abin da tace bai kara dadewa ba ya wuce ya fara shirya mata hadimai kamar yanda ta bukata...

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Wajen Sarki Lahazu kuwa shima ya iso bakin Masarautar Daborah tunda ga nesa ya fara hangen dandazon mutane bakaramin mamaki yayi ba da ganin su, saida ya kusa isowa ya fahimci kayan jikin su kamar na Masarautar Raifasu, cikin kwarin guiwa ya iso, aiko suka fara kallan kallo da juna dan sunyi mamaki domin ba wanda yai zatan zai iske ɗan uwanshi awajen musamman Sarki Baidulƙais da yake ma kanshi tambayoyi mi ya kawo Sarki Lahazu wajen Yaki, sai dai baida wannan ansar, shiko Sarki Lahazu yana ganin Sarki Baidulƙais yasan abunda ya kawo dan ya anshi Bahijja, kowa ya tsaya wajen jama'ar shi shiko Sarki Danwar cewa yayi daman Baidulƙais ya gayyaci Sarki Lahazu shine ya ɓoye mani bakomai ya munafurceni kenan?
haka kowa yai ta sake sake, a cikin zuciyar shi ganin sunki yima junan su magana hakan yasa Sarki Danwar yace kowa da tafiyar shi kenan? zuwa yayi suka gaisa da Sarki Lahazu, sannan yace suyi hadin guiwa su Yaki Sarauniya Zulaiƙa da yaki yarda ganin Sarki Baidulƙais nai mashi kallan hadarin kaji, amman daga baya sai ya yarda dan cimma wani buri nashi cike da kudiri iri iri a cikin zuciyar shi, shima Sarki Baidulƙais yaji dadin tayin da Sarki Danwar yaima, Sarki Lahazu, shima zuciyar shi cike take da ɗaukar fansa, baki dayan su bamai alkhairi a cikin zuciyar shi hatta Sarki Danwar shima ya haɗa kansu ne dan ya cimma wani buri nashi akan su, shiko Sarkin kofa tashi yayi daga kwanciyar da yayi jin hani niyar dawa kai dake tashi fiye da zaton shi bude yar kofa yayi yaga mayaƙa iya ganin shi da sauri ya koma yana rike kirji da kanshi ba ɗan aike ba ya tafi ya ga yama Sarauniya Zulaiƙa a can ya iske Yarima Malik,koda suka ji sakon da Sarkin kofa ya fada masu sai da kowa a cikin su ya mike da sauri.

MalikusSaif ya fita yaje sashen shi, ya fara shirin Yaki wasu kaya yasa na saƙi yasa wata hula sannan ya ɗauki kibiyoyi ya saga a kafadar shi ya saka takalman fatar damisa, da sauri ya nufi wajen su Yazid akan hanya suka hadu da Saifulislam shima labari yazo mashi na isowar abokan gabar su, a tare suka isa filin da Jaruman su suke kowa ya shirya iya ganin ka da makamai, MalikusSaif ne ya tura wani Jarumi ya sanar ma Huzaifa sa isowar abokan gaba, suna zaune da gimbiya Zahara'u tanata iyayi wai Yariman ta ya dawo, yana isa ya ya gayama Huzaifa da sauri ya mike bai ɓata lokaci ba yafara shiri, cikin kankanin lokaci ya fita zuwa wajen su Malik, ita ko Sarauniya Zulaiƙa ta gama shiri tsaf kamar da ita za'ay artabar haka ta shirya ta fito cikin jar alqabba da sharɓeɓiyar takobi a hannun ta, ita da wazirin ta suka isa wajen su Yarima Malik tayi mamakin ganin yanda Malik da Saifulislam suka shirya cikin kankanin lokaci dan ba tayi zatan Saifulislam zai shiga cikin Yakin ba, Musamman yanda tasan yana fushi da ita, MalikusSaif ne yasa Jaruman su suka rabu kashi biyar kashe ɗaya yace shi zai jasu kashe na biyu Waziri Dammur sai kashi na ukku yace Saifulislam, kashi na hudu kuma yace Yazid sai kuma kashi na biyar kuma yace Huzaifa zai zama Commender din su haka suka gama shirin su kowa hankalin shi ya koma kan Yakin da suke shirin yi.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿
Wajen su Sarki Baidulƙais kuwa sun gama bin shawarar da Sarki Danwar ya basu, take suka fara haurawa saman katan gar Masarautar aiko suna shiga cikin Masarautar suka kashe Sarkin kofa sannan suka buɗe kofar, Jarumai ne iya ganin ka sukai ta kutsawa cikin Masarautar Daborah kamar basu karewa cikin kankanin lokaci suka fara sarar mutane duk wanda suka haɗu dashi a hanya, take hayaniya duk ta gauraye kaf Masarautar, shiko MalikusSaif yana jin an shigo yaja tawa gar shi suka fito, suka tari makiya koda yaga tasasar mutanen da suka shigo saida ya tsorata, dakewa kawai yayi ya fiddo wata matsiyaciyar kibiyar shi lokaci guda idan ya saketa sama da hamsin suna iya fita haka Yarima Malik ya dinga kashe mutane kamar ba gobe, suma abokan karawar tasu haka sukai ta kisar mutanen Yarima Malik, yaki akeyi marar kyaun fasali ga tasasar mutanen su Yarima Haishir sai kara shigowa sukeyi amman haka su Yarima Malik ke kara kutsa kai ciki yana sauke kan maza koda suka game janyo dalliyar takobin shi yayi da duka hannu biyu kan mai uwa da wabi ya dinga fille kan maza, kashi biyu daga cikin tawagar su Sarki Lahazu suka tunkari filin dasu Yazid ke tsaye saboda sun kasa mutanen su,kowa yasan lokacin da zai tunkari abokan gabar su, suna tahowa wajen su, tasasa guda take Huzaifa ya fiddo da kibiya saida ya buɗa ta sosai sannan ya saketa akau ya bazar da mutane masu yawan gaske, yana farawa sauran Jaruman suma suka dinga halbama abokan gabar su kibiyoyi, ba abinda kake gani sai gawar waki birjik fululu kafin su karaso wajen sun kashe fiye da rabi sadda zasu iso kowa ya ɗauko wani faifai na silba mai kwari sukayi kariya dashi, da sun taho saman dawakai sai suka kariyar hannun su, su bugi doki dashi ya faɗi susa mashi su kashe su, cikin kankanin lokaci su Yazid sun kusa karar da mutane masu yawan gaske.

Shiko Yarima MalikusSaif yana can tsakiyar mayaka anata fafatawa dashi wata kaca ce doguwa ya ɗauko ya wurgama wani Jarumin su ya rike ta da sun wullata sai su zabaro sama da mutun goma suja haka suka dinga ɗebe kawunan mutane, kaca kaca haka su Yarima Malik sukai ma mutanen su Sarki Lahazu, koda suka ga cikin kashi haɗu na mutanen su ankusa karar da kashi biyu d sauri Sarkin Yakin su suka busa wani usur da gudu suka koma baya, dan sake shiri, danko Sarki Baidulƙais koda yaga yanda Yarima Malik ke wasa da rayuwar Jaruman su, ba karamin tsorata yai ba shiyasa ya koma baya ko gigin shigowa baiba da yaga Yarima Malik sai ya tuno da kisan gillar da yaima ɗan shi Yarima HusbarulƘais shi yasa bai san yana haye mashi fatan shi ya samu akashe shi a wannan Yakin, lokacin da Jaruman su suka koma cikin sahu yaki ya lafa lokacin karfe goman dare, komai ya kaure abubuwa sun rude a cikin Masarautar Daborah, suko su Huzaifa tawagar da suka faɗa masu sun gama karar dasu, ba inda suka motsa inda MalikusSaif yace su tsaya basu matsa ba suna wajen sai dai suma an kashe masu mutanen su, masu yawa, a wajen Sarauniya Zulaiƙa kuwa tana can wajen adana kayan Yaki tasa anata jido makamai iya ganin ka, tana zuwa takara ba maya kanta, kura ta lafa bakajin karar komai kowa yayi bakam yana dakon abokan gabar su, koda Yarima Malik yaga haka tattaro jama'ar shi yayi yasa suka rabu kashe biyu kashin farko suka tsaya ta gabas saura kuma suka tsaya tareda shi, wajen su Baidulƙais kuwa sun koma wani fili daga cikin Masarautar Daborah, suna tsayawa Yarima Haishir yace ma mutanen su,su kasu kashi ukku su kewaye cikin Masarautar haka kuwa sukayi, jin shirun yai yawa gashi har shaɗayan dare yayi basu jin motsin mutanen Sarki Baidulƙais, Yarima Malik ne ya naɗa sabon Commender ya kwashi kashi ɗaya suka bi ta cikin lambu suka kewaye su Yarima Haishir saida suka bari sun saki jikin su, suka farajin ruwan kibau tako ina dan MalikusSaif ya kware da iya halba kibiya, rasa ta inda ake halbin su sukayi, can suka hango su Yarima Malik akan dawakai suna halbin su, suma halbin su Malik din suka dingayi har ya isa cikin su ya ƙutsa kan dokin shi a cikin su, suka dinga ba juna wuta, kashi dayan da Yarima Malik ya bari sune suka rifa masu baya suka saka su Yarima Haishir tsakiya ankashe mutane da yawan gaske, haka suma su Yarima Haishir sun kashe mutanen da Yarima Malik yazo dasu wajen su dan har sunfara murnar sun karar da Jaruman Daborah ranar haka haka suka kusa kai safe ana abu guda, danko duk inda ka wuce mutanene falala iya ganin ka an kashe kamar kiyashi, har asuba tayi ana artaba, ko sallah saidai suka dinga yinta a tsorace idan wasu sukayi sai wasu su koma cikin filin Yaki, sannan wasu su tafi suma suyi.

****************************

Koda gari ya waye Sarauniya Zulaiƙa ce tasa Sarkin Shela ya fara shela yace. "Ance kowa ne Jarumi ya koma cikin tawagar shi za'a fara Yaki a filin *JINDAZ* a cikin wannan Masarautar ta Daborah dan haka anaso cikin kankanin lokaci kowa yabi dokar da aka sanya dan fafatawa, aiko sauran Jaruman su Sarki Lahazu suka dinga shiga cikin wani katafaren fili mai girman gaske iya ganin mai kallo haka suka dinga shiga sahu sahu, saboda yawan su kamar ba akashe kowa ba dan yawa, su kansu sunyi mamakin yawan makayan da Sarki Baidulƙais ya haɗa musamman Sarauniya Zulaiƙa saida taga sun gama wucewa daga karshe taga Sarki Baidulƙais da Danwar sai Sarki Lahazu, cikeda mamki tace a ranta, miyasa mutanen keda zamba cikin aminci ashe ba Baidulƙais bane kadai, ina zamu kai waɗan nan mutanen har haka, lallai kam Allah ya dafa mana duk wadan nan mutanen da muka kashe ashe ko kwata bamuyi ba?akwai sauran rina a kaba kenan! suma su MalikusSaif sun sha mamakin ganin tsabagen yawan Jaruman da sukazo dasu, kallan kallo aka dinga yima juna tsakanin Yarima Haishir da MalikusSaif kowa nai ma ɗan uwan shi kallan hadarin kaji, suma su MalikusSaif sun gama tsara sahun Jaruman su, yanzun yakin ya zama na sulhu sai an buga kugen Yaki sannan za'a fara ba kamar na farko ba, da sukayi masu dirar mikiya, amman su Malik kowa da tawagar da yake ja, tsakanin su Yarima Malik dasu Yarima Haishir akwai tazara sosai, kowa yana jiran yaga sun sake haɗuwa da juna, haka Sarauniya Zulaiƙa ta bada izini aka buga kugen Yaki, aiko mutanen su Yarima Haishir suka tunkaro mutanen su MalikusSaif, gudu a saman dawakan su, Huzaifa ne da yan tawagar shi suka dinga sakin ruwan kibiyoyi suna kashe abokan hamayyar su, cikin kankanin lokaci suka game, aka ci gaba da fafatawa kowa nasan yaga yaci galaba akan makayan shi.




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*

_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم




Episode 35&36



Suna gamewa aka cigaba da kisar juna da takubba bakajin karar komai sai karfe yana dokuwa da juna jini ba zuba kamar ruwa wannan karon kuwa Yarima Malik nw da Yazid ke artaba makiya su kuma Sarkin Yakin Raifasu da Yarima Haishir sune ke jan tawagar su, akwai wani basamudan bawa yana cikin mutanen Sarki Danwar shike ta kisar mutanen su Malik da ya shiga fili sai ya bazar da mutane birjik dayake lokacin gari ya waye kowa na ganin gaban shi, shiyasa Yakin yafi yima kowa dadi musamman Jaruman Baidulƙais wanda basu da burin da yawuce su ɗauki Bahijja hakama a wajen Yarima Haishir burin shi ya ɗauki Bahijja ko ana ga maza ha mata, koda Yarima Malik yaga wannan bawan nata kasar mutanen su kamar ba gobe da gudu ya sukwano akan dokin shi ya tunkare shi ya janyo wata kaca a bayan shi ya wulwulata ya sargaho kan wannan bawan ji kake ya faɗi tim saman doki ya dinga janshi kasa har saida ya kashe shi yana zuwa wajen wani icce ya bugashi take kanshi ya wargaje hakan ba karamin ɗagama Haishir hankali yaiba saidai Malik bata shi yake ba yamaida shi karamin kwaro a cikin filin da'gar duk abinda sukeyi akan idanun Sarakunan su akeyin shi kowa na cikin Jamaarsu hakama Sarauniya Zulaiƙa da take jifar Sarki Baidulƙais da shu'umin kallo, Yaki yai Yaki kura tai kura bak ganin komai sai tartsatsin wuta dake fita a jikin takubban su, kowa yana iya bakin kokarin shi dan ganin ya cimma burin shi akan ɗan uwan shi, abu kamar wasa Jaruman Baidulƙais sun kusa karar da tawagar Yazid da Malik gashi ansaka su tsakiya anata sarar su, bakaramin tashin hankali bane ya dira a cikin zuciyar Sarauniya Zulaiƙa ganin an zagaye su Malik anata sara da alama ankusa karar da mutanen da suke jagoran ta, shiko Malik yagama shagala baimasan anzagaye suba, yana waigawa yaga mutanen su saura kaɗan wani sabon karfi yaji yakara kamash lokaci wani uban tsalle yayi ya sargaho kan Sarkin Yakin Ƙaisu ya haye saman dokin shi ya wullo shi ƙasa, ya haye saman dokin wukake ya ɗauko ya dinga fille kan maza shima Yazid yana ganin Malik ya tunkaro su yai tsalle ya hau saman dokin shi, atare suke kasar mutane ga kawuna kasa burjik kamar ruwa, wani irin dadine ya sake dirarma Sarauniya Zulaiƙa a cikin zuciya, suna haɗa ido da Zulaiƙa ta cilloma Yazid kibiya yana caɓewa ya dire saman doki ya dira gefe ya cigaba ruwan kibau, cikin kankanin lokaci tsakanin Yazid da MalikusSaif sun kusan cin dunun su Haishir suko Jaruman su Haishir saura kadan su karar da tawagar su Malik, Sarauniya Zulaiƙa ce taje wajen su Huzaifa ta taso da tawaga biyu, suka shigo cikin tawagar su Malik a tsorace Sarki Danwar yacema Sarki Lahazu. "Kana ganin zamuyi nasara akan wannan matar

Please Login or Register in order to submit comment