Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

share garken dawakai, yana zuwa Sarkin dawaki ya taso yakawo gaisuwa sannan ya aje mashi kujera ya zauna, shima Abdulmajid dake aiki aje aikin shi yayi yazo zai duka kenan MalikusSaif ya mike cikin girmamawa yace.
"Barka dA rana Abba ya aikin." tsayawa Abdulmajid yayi yana mamakin sanyin hali irin na MalikusSaif bai ɗauki duniya da faɗiba sannan bai kyamar bawa saɓanin mahaifiyar sa, koda yake halin mahaifin sane, wannan dalilin yasa Abdulmajid ke kaunar Malik yakejin shi tamkar ɗan da ya haifa, cikin sakin fuska yace. "Lfy lau Yarima, ya fama da jama'a."

"Lfy lau MalikusSaif yace, cikin girmamawa Malik yace. "Daman inasan zanyi wata magana dakai inba damuwa." cikeda gamsuwa yace. "Badamuwa Yarima."
zama sukayi bisa wata shimfida yace. "Abba daman akan Bahijja ne abubuwa na faruwa, shine nazo dan inbaku hakuri akan abun da Ummu ta aikata dan Allah kuyi... Katse shi Abdulmajid yayi ta hanyar hade hannayen sa yace. "Dan Allah yarima karkace zaka bani wani hakuri bakai komai ba, kuma kai ɗana ne, duk laifin Bahijja ne da batayi hakuri ba ta zauna matsayin da Allah ya ajeta ba, amman baku da wani laifi, na rokeka kada kasake cewa zaka bada wani hakuri Abdulmalik."

Rausayar dakai yayi yace. "Ya Bahijja Allah yasa ba abinda ya same ta." cikin jin dadi yace "bakomai mungode da kulawa Allah ya biya yasaka da alkhairy." "Ameen Yarima yace, sannan ya mike yaima Abdulmajid sallama ya tafi, sai dai ba haka ya soba, yana isa side ɗinshi bathroom ya wuce ya fara wanka

Haka rayuwa taci gaba da kasancewa a cikin Daborah tsakanin Sarauniya Zulaiƙa da bayin nata, inyau bata wulakanta suba, gobe zata wulakanta su, saidai suyi jimamin a cikin zuciyar su suyi hakuri

Bayan kwana ukku, Yarima Malik ne kwance saman tafkeken gadon shi ya kudundune sai kyakyarwa yakeyi da kagan shi kasan baida lafiya dan jikin shi ya tsananta sosai, sallama Huzaifa ya dinga dokawa amman shiru bakowa tunda ga falo yafara cewa Yarima kana ina, jin shirun ne yasa ya nufi bedroom ɗin shi, jin numfashi nafita yasa shi shiga da sauri ya iske MalikusSaif kwance yana fidda numfashi da kyar, hayewa yayi saman gadon ya taɓa goshin shi yaji shi kamar wuta dan zafi, murya na breaking yace. "Yarima baka lfy shine baka sanarwa kowaba, sannu." baice komai ba, sai kara jan blanket da yayi yakara rufe jikin shi yana rawar sanyi, da sauri Huzaifa ya fita ya shige sashen Matawalle yana shiga ya iske matar shi gimbiya Abida zaune tana hutawa, yanda taga Huzaifa yatabbatar da ba lafiya, cikin kulawa tace. "Lafiya Huzaifa mike faruwa?" da ɗimauce yace. "Matawalle nanan." batace komai saita shi da tayi ta shiga cikin wani ɗaki, badajimawa ba suka fito tare, sanye yake cikin doguwar jallabiya, yace. "Huzaifa bissmillah zauna." "aaa ranka shidade, ba lafiya, Yarima baida lafiya yana kwance yanzun haka." kasa magana yayi da sauri ya fita, har gudu gudu yakeyi, yana shiga sashen shi ya wuce dakin MalikusSaif, tundaga bakin kofa zaka fara jiyo kyakkyarwar da hakoran sa keyi suna dokuwa da junan su, yana hawa bisa gadon ya tallabo shi, murya na rawa yace. "Abdulmalik sannu kaji sannu ɗana." baisan komai akecewa ba, yana ganin dai mutane sai dai bazai iya gane wake kanshi ba, ga zuciyar shi dake bugawa ba daidai ba, shigowar gimbiya Abida, yasa Matawalle yace. "Kije kutaho da mai magani maza kutafi Huzaifa, baki ɗayan su,sun rasa abin yi, shiko Matawalle sake rufe MalikusSaif yayi.

Haka Huzaifa yaje ya sanarwa mai magani sakon Matawalle, akan hanya ya hadu da Saifulislam ya dawo daga masallaci, ganin Huzaifa ya wuce shi, yasan ba lafiya, kiran shi yayi hakan yasa Huzaifa dawowa yana ɗan sosa kai yace.
"Ranka shidade aimin afuwa ban kula ba." murmushi yayi yace. "Nasani Huzaifa, mike faruwa daganin ka baka cikin nutsuwar ka." sadda kanshi kasa yayi yace. "Eh Yarima ne bai lfy a gaskia yana cikin hali."

tausayin Malik ne ya rufe Saifulislam, girgiza kai yayi yace. "Allah yabashi lfy, mutafi inga yanda jikin nasa yake."

Haka suka dunguma har cikin dakin MalikusSaif, sai dai yana ganin halin da ɗan nashi yake ciki, ranshi ya bashi damuwa ce taimashi yawa, cikeda karfin hali yace.
"Ya mai jikin.?" sai a lokacin Matawalle yaga zuwan Kangiwa, da sauki gimbiya Abida ta amsa, lokacin mai magani yazo ana bashi magani a cikin ƙoƙo yana sha amman idanun shi a rufe, da kyal ya fidda numfashi yace. "Bahi-jja-aah." a rarrabe yayi maganar duk da bakowa zai iyajin abinda yake faɗa ba sai kana kusa dashi sosai daga Matawalle sai Saifulislam sukaji abinda MalikusSaif yace, kallan junan su sukayi hakan yasa Matawalle ya tashi ya fita, sashen Sarauniya Zulaiƙa ya wuce, sai dai batann tana fa'da bai isketaba, girgiza kai yayi yace. "Wannan wace irin uwace da batasan darajar ɗanta ba, wato mulki yafi ɗanta kenan, batasan halin da yake ciki ba kenan, Binta yagani yace....




_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 97&98




"Intadawo kice mata in ɗan nata ya mutu saita rungumi gawar shi."

Jitayi gaban ta ya yanke ya faɗi musamman yanda yai maganar ba alamun annuri a cikin fuskar shi, itako Binta russunawa tayi tace. "Zataji ranka shidade."

Shiko Huzaifa fita yayi yaje part ɗin shi ya haɗoma Yarima magani akan hanyar dawowar shine ya haɗu da Yazid nan yake sanar mashi komai, sannan yace. "Kaje kasanarwa Ummu da alama batasani ba."

Baice komai ba dan jikin shi yai sanyi, fa'da ya wuce dan daman daga can yake, yana komawa Sarauniya Zulaiƙa ta zuba mashu ido, dan tasan ba yanzun zai dawo ba, yanda take kallan shi alamu sun nuna ba'asi take nema, murya a sanyaye yace. "Ranki shidade Yarima bai lfy."

Wani rin daram taji gaban ta ya buga da sauri da sauri tattaro jarumtarta tayi tace.
tun yaushe?"

"Ban saniba sai dai bai cikin hayyacin shi gaskia."

Batasan sadda ta mike ba tana karanto inalillahi wa'inna ilaihir raji'un bata kuma cewa komai ba, ɗan ɗage alqabbarta tayi tana tafiya da sauri da sauri sai dai zuciyarta na duka fat fat fat harta isa cikin falon shi sannan ta nufi bedroom ɗin shi, kasa shiga tayi saboda baki ɗaya jikin ta ya mutun ganin shi rungume jikin Kangiwa ga idanun shi sunyi fari ƙal ƙal kamar marar jini, wata kwarya ce Saifulislam ya rike cikin ta zuma ce marar haɗi addu'a ya farayi yana tofawa a ciki sannan yakaranta Ummul-qur'an (suratul fatihati)da wasu ayoyi na suratul bakara sai ikilas,falaq sai nasi, da wasu ayoyi na (kunfayakunu)duk ya tofa a cikin zumar ya samu kofi ya zuba yaba shi a hankali ya sha yana kauda kanshi, kwantar dashi yayi yana jin tsananin da jikin Abdulmalik yayi har cikin zuciyar shi.

A hankali ta jefa kafar ta, cikin ɗakin ta hau bisa gadon ta tallabo habar shi tana kallan shi, cikin rarrabe war murya tace. "Sannu Abdulmalik."

Juyowa tayi ta kalli Saifulislam, zatayi magana, yai mata wani irin wawan kallo yai mata yasa takasa yin maganar da tai niyaryi, juyawa yayi ya fita tareda bugo kofar yanajin kuna cikin zuciyar shi, bakaramin haushin Zulaiƙa yakeji ba.

Ranar haka Sarauniya Zulaiƙa ta wuni wajen MalikusSaif dan ba kadan hankalin ta ya tashi ba ganin yanda jikin shi ya tsanan ta ga zafi da ya ɗauka kamar wuta, koda dare yayi Matawalle ne yazo sake duba Yarima Malik din shida Waziri anan ne suka iske Huzaifa, samun waje sukayi suka zauna suna tambayar mai jkin, cikin kulawa Huzaifa yace. "tun ɗazun yake bacci jiki yai kyau sosai."

Alhmdullh Matawalle yace, sannan ya matsa kusa da Malik yaɗan yaye mashi blanket din daya rufe dashi ganin yana tsatsafo da zufa a jikin shi, maida hankalin shi yayi kan Huzaifa yace. "Yakamta ka kwana wajen shi Huzaifa."

''To ranka shidade."
Jim kaɗan sukayi sallama suka tafi tareda Waziri, bayan sun fita da kamar minti talatin Sarauniya Zulaiƙa ta shigo tareda wata baiwa ɗauke da kokon fura sai kuma wani tire kayan marmari ne da abinci, da sallama a bakin ta, Huzaifa ne ya amsa masu, zama tayi tana kallan yanayin Malik ɗin saidai taji dadi ganin ya samu sauki ba kamar ɗazu ba, hakan yasa tace. "Huzaifa ga abinci nan inya farka kasamu yaci ko yaya ne, sannan ga fura nan karka bari yai bacci ba tareda yaci komai ba."

To Ummu cewar Huzaifa, ɗan danna mashi kafar shi tayi na mintoci daga bisani ta tafi, sai dai ta ɓangaren Saifulislam tunda ya tafi baidawo ba dan baisn in yana wuri ya dinga ganin Zulaiƙa.

A wajen Bahijja kuwa kwance take amman ta gaza bacci ji take duk jikin ta ba daɗi ta rasa abinda ke mata dadi a duniya, tashi tayi ta rabka uban tagumi tana ta tunanin da batasan dalilin shi ba, Binta ce ta farka daga baccin da takeyi, tashi tayi ta fito tsakar gida zata zagaya, saita dinga jiyo motsi a ɗakin Bahijja, a tsorace ta iske Bahijja ta buga tagumi tana kwalla sannan tayi jifa da wani kofin silba, a tsorace Binta tace. "Kanki lfy Bahijja kinada hankali.?"

samun kanta tayi da fashewa da kuka marar sauti, cikin jimami Binta takaraso cikin ɗakin ta zauna kusa da Bahijja ta riko hannun ta tace. "Kukan mi kikeyi cikin wannan taletalen daren, eyeh Bahijja?"

"Umma raina yana bani Ya Malik yana cikin wani hali.!"

Rike baki Binta tayi cikeda mamaki tace. "Wato bazaki barta Malik ba ko Bahijja miyasa bakijin magana, in mahaifin ki yajiki fa mizakice.?"

Rufe bakin ta Bahijja tayi tana zaro manyan idanun ta masu sheki, dan batasan abinda bakin ta ya furta kenan ba, murya na rawa tace. "Umma kiyi hakuri, kaina ke ciwo."

Murmushin manya Binta tayi sannan tace. "Uhummm, Allah ya sauwake, kiyi addu'a ki kwanta kinga dare keyi."

Ba tareda tace komai ba tafara addu'a sai dai har yanzun zuciyar ta na duka da sauri da sauri


Koda dare ya kara tsalawa Yarima Malik ne ya sake farkawa wannan karon da ambatan sunna Bahijja a cikin bakin shi, da sauri Huzaifa ya tashi, jin Malik nacewa. "Inalillahi Ummu kada ki halaka Bahijja ina sonta dan Allah Ummu kidubi rayuwar Bahijjaah."

A kiɗime Huzaifa ya matso kusa da Yarima Malik yana salati ya riko shi, shima zaunawa ya tashi bakin shi ɗauke da salati, yana ambatan sunan Allah yana kiran "Hazbunallahu wani'imal wakil." wata iriyar zuface ta ketoma MalikusSaif kusurfa kusurfa dake jikin shi,dafa kafaɗar shi Huzaifa yayi shima da addu'a a bakin shi, a hankali Malik ya kalli Huzaifa yace. "Yaushe kazo nan."

Bai bashi amsa yace. "Sannu Yarima tashi kayi wanka." rike kanshi yayi cikin jimami yace. "Huzaifa karfe nawa a halin yanzun naga alamun dare yayi kuma banyi sallah ba."

Duba agogon hannun shi Huzaifa yayi yace.
"Karfe 1:30." ɗan guntun tsaki yayi yace. "Ko magrib banba fa Huzaifa."


Dirowa yayi bisa gadon duk da jikin shi ba kwari ga juwa yanaji kuma zuciyar shi taimashi kunci bathroom ya shiga, yafara wanka sannan ya ɗauro alwalla, koda ya fito bathroom bai tadda Huzaifa ba, brown ɗin jallabiya ya saka sai boxes da singlet, kaɗan yadan saka turare sannan ya kabbara sallar magrib jin karatun alqur'ani daya karaɗe ɗakin da murya mai daɗi, kasa kasa yasa Huzaifa shigowa haka ya gama yin sallolin sa, yana idawa yayi addu'a rabi duk akan mahaifiyar sane, akan Allah ya ganar da ita gaskia a cikin al'amuran ta, daga bisani ya koma bisa kushin ya zauna yana jinjina bayan shi da bisan kushion ɗin, dan ya gaji da kwanciya, Huzaifa ne yafara miko mashi kwaryar fura da yaki karɓa sai yaji yunwa tamkar ammashi turen ta dan rabon da yaci abinci baicewa ga lokaci sosai yasha furar sannan yace. "Alhmdullh."

Mikomashi abinci yayi wanda ya zuba mashi cikin flat kauda kai yayi alamun ya koshi, tuwo ne yaji miyar ganye da kifi sai kamshi yake bazawa amman sam Yarima Malik yace ya koshi, haka ya kyale shi, ɗaukar tufa yayi yafaraci saidai wani irin sanyi yaji jikin shi nayi ga kykkyarwa da ta taso mashi har haɗe hakoran shi yakeyi kat kat kat, ganin haka yasa Huzaifa taimaka mashi ya maida shi bisa gado tareda rufe shi da blanket ya kara ɗaura mashi wani akai, haka Malik ya kwana ko bacci daya fara yakan farka haka shima Huzaifa dake jinya, ga amai, danko zuciyar shi jiyake kamar zata fashe dan ba abinda ya sauya akan tunanin Bahijja, danma yana addu'a, har asuba tayi a ɗaki sukayi sallah Huzaifa yajasu, dan MalikusSaif bai iya tafiya zuwa masallaci, suna gamawa ya koma ya kwanta ya kudun dune baccin wahala yai awan gaba dashi....

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Masarautar Raifasu, Jakadiya Aisha ce da Sarki Muhammad, suke zaune a falon shi, yanda suke magana kamar akwai abu mai mahimmanci da suke tattaunawa akai, ɗan gyaran murya Sarki Muhammad yayi yace.

"Aisha kina ganin hakan shine mafita.?" rausayar da kanta tayi alamun eh, sannan takara da cewa. "Shine mafita dan haka a shawara ta ranka shidade mu aikama Sarki Haishir da wasika akan ya kiyayi Masarautar mu, tunda ɗaukar fansa yake ikirarin zaiyi ai yazo ya kashe gimbiya Yazira, kaga ba kare bin damo kenan, komai ya wuce idan kuma baijiba sai muyi anfani da karfin mu iya gwalgwado mu yake shi."

Numfasawa Sarki Muhammad yayi yace. "Kinsan wani abu kuwa Aisha.?" sake rankwafawa tayi cikin ladabi tace. "Aaa ya shugabana kai nike sauraro."

"Aisha baki ɗaya wannan addinin da muke cikin sa,na fahimci addini ne mai son zaman lafiya da numana, addinin musulunci ba addini bane da yake son ta'addanci ba, kuma musulunci da musulmai ba 'yan ta'adda bane, wlh Aisha tunda Allah yasa muka anshi wannan addinin ba abinda na tsana ingani a duniya kamar jini na gudanya a kasa, uwa uba inga jinin ɗan uwa na musulmi wannan abun shike kona mani zuciya Aisha, saɓanin da, dan na kashe mutumin banjin komai, koda kuwa bada wani dalili bane, balle ma idan ana yaki jikina har tsuma yake dan kawai in kashe, gaskia addinin musulunci yayi Aisha."

Wani irin dadi Jakadiya taji yanda Allah yake kara haskama uban gidan nata addinin cikin sauki, sauke ajiyar zuciya tayi tace.

"Kwarai kuwa wannan dalilin yasa idan muka aikawa su Yarima Malik da takardar Yaki, sukekin amincewa sabida addinin su ba addini bane maison rikici ba, sannan basu taɓa kawo mana hari ba saidai mu ke kaimasu, kaga ko anan zaka gane girman addinin mu na musulunci, saidai su kare kansu dan kar mu cutar dasu, karshe kuma sune da nasara tunda muke tsokanar su, to muma haka zamuyi ma Sarki Haishir, ranka shidade."

Ɗan murmusawa yayi cikin jin dadi yace. "Tabbas hakane, Aisha."

"Ranka shidade abinda yafi bani mamaki ɗaya ne, yanda naga Sarrilƙus yayi shiru ba wani motsi kodai ya hakura?

"Uhumm, kike gani Aisha?" "eh ranka shidade."
"Azzalumi ne kuma macuci ne baida imani kuma baya mantuwa, yana sane damu, sai dai izuwa yanzun mun masa nisa sabida hasken musulunci dake jikin mu, shiko najaza tai mashi yawa, kinji dalili, amman zai dawo."

Nauyayyen ajiyar zuciya ta sauke tanajin ba daɗi, cewa tayi "Allah ya shiga tsakanin mu dashi." "Ameen Jakadiya ta, Aishatu mai babban suna uwar mumunai tarayya dake haske ne Aisha."
saddar dakanta tayi tana murmushi tanajin daɗin kasancewa da Sarki Muhammad, ashe haka yake da saukin kai, kodan ya musulun ta, tabbas tasan sanyi da saukin addini ne ya lullube zuciyar shi.

Cewa tayi.
"Godia nike ranka shidade, amman ai kasan dalilin mai sunan ka haske ya bayyana a duniya,har Aisha tabi hanyar tsira fata Allah yasa damu dasu a gidan aljannah."

Cikin jin dadi yace. "Ameen ya rabbi.''

Dahaka sukaita yar fira a binsu, kiran sallah ne ya ta dasu ya shiga ciki alwalla ya ɗauro ya tafi masallaci ita kuma ta shiga wani ɗaki cikin sashen shi tayi alwalla, sannan ta kabbara sallah.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Washe gari da safe Masarautar Waisu Sarki Haishir ne zaune a fadar shi tareda Sarki Danwar na Ƙaisu, suna tattaunawa suda wasu fadawan su, ƙayyadaddu, Sarki Haishir ne yace. "Idan muka tashi shiga cikin Masarautar ta kofar yamma zamubi tunda daman kofa biyu ne dasu kunga shikenan saimu farmasu, mu darkake su cikin sauki ba tareda munsamu matsala ba."

Sarki Danwar ne yace. "Ba abinda ke konanmani rai idan na tuna wai Sarki Baidulƙais ya anshi addinin musulunci, sai inji kamar in halaka shi ina karajin tsanar shi a cikin zuciya ta, dan haka babu ja da baya saimun yake su shida jama'ar shi baki ɗayan su."

Murmushin mugunta Sarki Haishir yayi yace. "Wannan dalilin yasa nabi umurnin Sarrilƙus nayi duk abinda yace,inyi dan inga karshen Baidulƙais shida jama'ar shi da,dana kashe matar shi harna fara hakura amman danaji labarin musuluntar shi sai gabar dake tsakanina dashi takara ruruwa banda buri daya wuce inga kan Sarki Baidulƙais a hannuna bisa mashi ina janshi ƙasa."

Haka dai kowa yaita tofa albarkacin bakin shi inda Sarki Danwar ke kara ruruwa gabar dake tsakanin Sarki Haishir da Sarki Muhammad, inda suke kiran shi da (Baidulƙais) ɗin shi har yanzun saboda girman sunan dake gare shi yanzun ya girme harshen su saboda kwarjinin sunan da haibar shi, wannan dalilin yasa basu son kiran shi da suna Muhammad, sai dai Baidulƙais.....

Da yamma kuwa Sarki Haishir a ɗakin gimbiya Ƙamariyya sunata aikata alfasha, abin ba kyaun gani sai dai su ko ajikin su da alama sunsaba tazame mashi tamkar matar shi haka ya maida uwar shi, wa'iyazubillah.


```Allah yaimana tsari da irin wannan fasadi, shiyasa addinin musulunci addine mai tsabta, da ace akwai digon imani a cikin zuciyar su tabbas bazai iya aikata hakan ba, kodan giraman ta na mahaifiyar shi, Allah ya ɗauramu bisa tafarki madaidaici, Ameen."```

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

Bayan sati ɗaya acan Masarautar Daborah ciwon Yarima Malik maimakon yai sauki sai kara ta'azzara yakeyi, zuwa yanzun zazzaɓin ya sauka babu shi sai dai alamun shi ya nuna banjin daɗi ko kadan yauma Sarauniya Zulaiƙa ce rungume dashi tana kuka sai kiran sunan shi takeyi, taji shiru girgiza shi tafara a ɗimauce ta kalli Yazid tace.
"Jeka kiramani Matawalle, Malik karya mutu bai ko motsi, wuce Huzaifa kutafi."

A ruɗe suka fita sukayi wajen Matawalle, a hanya suka hadu da Matawalle, da alama wajen Yarima Malik ya taho, a rude Yazid yace. "Ranka shidade Yarima."

Da sauri sukayi sashen shi wanda baida mararraba da gudu har hardewa kafafun Matawalle sukeyi dan rudewa da yayi, yana isa ya tallabo MalikusSaif yana salati, abinka da mai Ilimi sai ya fahimci kamar suma ce yayi, kallan Huzaifa yayi yace. "Ɗibomani ruwa." hawaye na digowa bisa idanun shi, a sanyaye ya zubo mashi ruwa ya miko mashi, ansa yayi ya zuba a hannun shi yana shafama Yarima a fuska sannan yasa Yazid nai mashi fiffita cikin ikon Allah kuwa yayi wata irin ajiyar zuciya yana dafe kirjin shi, ɗagowa yayi yaga Matawalle,rungume shi yasake yi cikin murya a dishe yace. "Kawu Bahijja ta mutu ko.?"

A razane Zulaiƙa ta kalli Matawalle, aiko ya watsa mata wawan kallo, cikin sanyi zuciya yace.

"Yihakuri Abdulmalik Bahijja bata mutu ba."

kamar karamin yaro Yarima yace. "Kuwa kacema Ummu kada ta illata Bahijja ina son Bahijja Kawu."


*Allah Sarki masoyan Malik kunga mutumin yakamu, da son Bahijja, lallai kuwa koya za'akaya da Sarauniya Zulaiƙa, zata zabi bukatar ɗanta dan inganta rayuwar shi? ko kuwa zata cigaba dabin son zuciyar ta dan musgunama hadiman ta? Muje zuwa my real fans*


Itako Sarauniya Zulaiƙa dafe kirjin ta tayi dayake ta lugude kamar zuciyar ta zata faɗo kasa inhar kuwa abinda taganema idanin ta da gaske Yarima Malik ya kamu da son baiwa kuma tana iya rasa ɗanta kenan? da sauri da girgiza kanta tana cewa. "Bazan iya rasa ɗana ba akan wannan jakar baiwar ba karyane wlh." a zuciya tayi maganar amman saida duk suka kalleta fuskokin su cikeda mamaki, yanda zuciyar take da tauri wato bata hakura ba kenan."

Cikin fushi Matawalle yace.
"Aikuwa baiwa tafi karfin wulakanci tunda gashi anwayi gari ɗan ki mai daraja ya kamu da son baiwa marar daraja, kwara tunkan ki rasa shi kiyarda kayan ya ƙinki Zulaiƙa."

Wani irin sarawa ne kanta yayi lokaci guda tace.
"Yaya bansan yarinyar nan amman yaje in mata huɗu zai kawo mani lokaci ɗaya zan aurar ma Abdulmalik dasu, akan ɗana ba abinda ba zan iya ba."

A fusace Matawalle yayo kanta ya ɗaga hannun shi kenan zai mareta, kuma sai ya fasa, ita kanta harta rufe idanin ta dan tasan halin Matawalle akwai ɗaukar fushi suko su Huzaifa suna ganin rai ya fara ɓaci suka bar ɗakin,falo suka koma suna al'ajabin kalar kiyayyar da Sarauniya Zulaiƙa kema Bahijja.

Shiko Matawalle iska mai zafi ya furzar yace. "Kinci sa'a ke macece Zulaiƙa kuma kinsan Matawalle bai dukan mace da saina koya maki hankali, kuma ga ɗan naki kiyi yanda kikaga dama dashi, daman mugayen halayenki ne yasa mahaifin sa ya fidda hannun shi kan ɗan shi mafi soyuwa a gareshi, baki da hankali sai dai kace ba uwa ba sha sha sha dake mtsw."
ya ida maganar yana jan dogon tsoki ya fice,ita kuwa kuka ta dinga yi tana kiran Matawalle amman yaki dawowa, zuwa tayi ta duka kusa da Yarima Malik da yake kwance idan shi a rufe amman ba bacci yake ba, kwalla na zuba a idanun shi tace.
"Abdulmalik dan Allah karufaman asiri ka daina son baiwa, ka nemi daidai kai wlh koda komai nawa zai kare zan iya rasa komai in nemama auren su, amman banda baiwa jinin Jafar na rokeka ɗana bansan rasaka Abdulmalik kaine magajina jinina ka daina san Bahijja."

Kara runtse idanun shi yana jin maganar Ummun shi na taɓa mashi zuciya, yayi iya kokarin shi amman yakasa cire son Bahijja a zuciyar shi amman yakasa har ya kwanta wannan ciwon ya yarda, da son Bahijja ajinin shi ne tun randa yasata idanun shi tana jinjirarta Allah ya dasa mashi kaunar Bahijja ta hanyar jin tausayin rayuwar Bahijja.

ganin yaki magana ne yasa ta komawa gefe tanajin ƙuna a cikin zuciyar shi, a falo Lurwan ya iske su Yazid suna gaisawa yace.
"Yajikin Yariman." da sauki sukace shima zama yayi kusa dasu kowa yana jin ba dadi aran sa, itako Sarauniya Zulaiƙa baccine yafara auwan gaba da ita, cikin bacci taji kakarin amai a firgice ta bude idanun ta, taga Yarima na aman wani abu shi ba jini ba kuma ba normal amai ba, batasan ta isaba ta rungume shi tafara kuka tana kiran sunan shi, su Huzaifa suma suna falo har baccin yafara awan gaba dasu can sukaji Ummu nacewa Abdulmalik kada ka mutu kabarni dan Allah, na amince zaka *AURI* Bahijja wlh na amince, basu san sun faɗo dakin ba, lokacin Yarima bai san inda kanshi yake ba, ganin halin da yake ciki hakan yasa Lurwan zuwa kiran Saifulislam lokacin karfe 12:30 a tare suka shigo dan raban da yazo wajen Malik Yau kimamin kwana sha huɗu kenan sai dai yai mashi aiken magunguna, yana isowa ya ingije hannun Sarauniya Zulaiƙa yace.
"Kada kikara tabamani ɗana kibari in kikai silar mutuwar sa saiki ringumi gawar sa."

Ɗaura hannun ta tayi saman kai tafara kuka tace.
"Abdulmalik karka barni, na amince ka auri Bahijja, indai zaka rayu dani ɗana."

Murmushin takaici Saifulislam yayi ya kalleta wanda suma su Huzaifa ita suke kallo da mamaki, cikin gadara yace.
"tunda wuri haka Zulaiƙa wai harkin saduda tun ba'aje ko ina ba? Kinyi kyaun kai, sai dai kisani itama baiwa tana da tata alfarmar dan haka sai kije da kanki kinemawa ɗanki Abdulmalik auren baiwa Bahijja, amman ba Saifulislam ba, inke baki da kunya ni Kangiwa nasan ƙima da darajar mutane.!"

Idananuwan ta araunane ta zubasu bisa fuskar Kangiwa tasan indai yai magana shikenan cikin sanyin murya tace.
"Ina kataɓa ganin uwa ta nemawa ɗan ta aure, ai wannan sai dangin uba."

"Uhummm ashe kinsani, aikoba uba uwa zata iyayi, wai ko kinmnta bayin kine ai kinada iko dasu umurni kawai zaki basu, ya kika wannan wasan Zulaiƙa."

Baijira cewarta ya sake ba ɗansa maganin da ya haɗo mashi haɗin zuma da ruwan zamzam yayi mashi tofi yana sha yai tafiyar shi ganin MalikusSaif ya samu bacci.

Washe gari da safe Lurwan ne

Please Login or Register in order to submit comment