Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai tsaye sashen Kangiwa suka isa.

Anan suka iske Sarki Abu-Jalal da Sarauniya Zulaiƙa sai Saifulislam suna tattauna yanda lamarin zai kasance, jin sallamar sune ya katse masu lbrn da sukeyi, amsa masu sallamar sukayi da kallo suka bisu, har suka zauna, cikin kiɗima Sarauniya Zulaiƙa tace. "Yaya andace kuwa?"

Murmushi mai sanyi yayi sannan yace. "Alhmdullhi andace kanwata kwantar da hankalin ki."
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani wasai a cikin zuciyar ta.

Sarki Abu-Jalal ne yace. "Uhmm ya kukayi dasu Kawu.?"
ya ida magabar yana kallan Galadima cewa yayi.
"Ranka shidade Allah yataimaki Sarki mai adalci Sarkin Runo mai kishin musulunci da musulmai, munje munga iyayen yarinyar nan Idris ya amince zuwa anjima za'akai kayan shaidin domin shaidawa dangi, sannan ansaka ranar biki nan sa sati ɗaya masu zuwa."

Murmushi yayi mai faɗi sannan ya kalli Matawalle yace "kaje yanzun a hado kayan shaidi kamar yanda akema kowace ƴa' itama ai mata komai a nunawa duniya Bahijja tazama cikakkar 'ya."

Cikin gamsuwa Matawalle ya mike tareda Zulaiƙa suka wuce sashen ta, nan suka haɗa kaya masu yawa harda alewa da goro da dabino da kayan sawa masu masifar kyau, da kudi sai sarkar Jawhar da Sarauniya Zulaiƙa takara sakawa tace abawa 'yarta Bahijja.

_Lol 🤣 yau Bahijja ce take kira da 'ya, Allah gwani, Sarki buwayi gagara misali._

Haka Matawalle ya tashi yaje shida Sarkin gida sai Sarkin fa'da mahaifin Yazid kenan sai Waiziri Dammur haka suka ɗunguma aka kai kaya kamar yanda suka alkawalta, bakaramin dadi iyayen Bahijja sukaji ba.

Da mangrib angama sallah Saifulislam ya tashi yayi wa'azi akan hassada da ƙeta bayan yagama ne yasa aka raba alewa da goro na shaidin saka bikin Yarima Malik da Bahijja, baki ɗaya masallaci ya dauki surutu kowa da abinda yake faɗi,sai kallan kallo akema juna tsakanin su Huzaifa da Yazid da Lurwan, suna mamaki dan basuji labarin haka ba abakin Yarima Malik ba, shi kanshi Yarima ko motsi yakasa dan al'ajabi ana tashi daga masallaci suka hadu da abokan nashi, nan suka fara tsokanar shi har suka isa sashen shi suna mashi tsiya wai angon Bahijja, shiko sai murmushi yakeyi saidai ya kasa gazgata hakan sai yaga kamar mafarki yakeyi, Huzaifa ne yace. "Abokina ashe ka kusan angwan cewa, wayaga Yarima MalikusSaif anzama ango."
"Uhmmm." shine abinda ya isa furtawa sai smile dayake saki.
Dawud ne yace. "Aikuwa nan da sati ɗaya kace zamusha shagali."

Baki ɗayan su suka saka dariya, shidai nashi ido yana karajin kaunar Bahijja na ratsa jini da ɓargon jikin shi...

A cikin Masarautar kuwa a turakar bayi labari yagama karaɗe ko ina ansaka ranar bikin Yarima Malik da Bahijja kowa na fadin albarkacin bakin shi wasu najin daɗi wasu kuma na bakin ciki, inda masu Sarauta ke ganin Yarima Malik ya auri baiwa hakan kamar zubda kimane da darajar Masarautar Daborah, inda ta ɓangaren bayi ke ganin hakan tamkar ɗaukaka darajar sune a idon duniya yau ga ƴarsu zata zama gimbiya kuma cikakar 'ya.

Itako Bahijja tana tsakar gida tana wanke kayan ta, kawai taji anfado mata a jiki, a tsoro ce ta waigo sai taga Salame, cikin zolaya tace.
"inkika karyani fa, kin fiye ganganci da yawa Allah kuwa."

"Uhmm kinji dan kar inma Yarima asara dai zakice, kaga masoya amaryar Malik sai dubu ta taru Allah ya nuna mana sati mai zuwa musha shagalin bikin Yarima MalikusSaif da amaryar sa gimbiya Bahijja."

Ɗan duka takaima Salame a baya cikin bugun zuciyar ta da taji yana hauhawa a lokaci ɗaya jin kalaman Salame, hakan yasa tace......




_Yar Mutan Kankia ce ❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 107&108



"Ki rufamani asiri Salame karkisa Sarauiya tasa akamani amaida ni gidan Yari."
Bahijja tayi maganar a tsorace.

"Uhmm kinji wlh dagaske nike an maku baiko ke da Yarima."

Jitake kirjin ta na zafi zuciyar ta kamar ta faɗo kasa dan tsoro taji ya lullube ta a cikin zuciyar ta, tarasa dalilin jin yanda zuciyar ta ke duka da sauri da sauri, magana zatayi sai taji Mairo tace.

"Zonan 'yata."
Tasowa tayi tazo ta zauna kusa da innar tata, tana zama tace. "Yata kinsan ita rayuwa duk yanda tazo maka haka kake ɗaukar ta Bahijja, kuma Allah shike tsarama bawan sa komai, namu shine bi, a yanda tazo mana, dan haka inasan kizama mai yawan biyayya ga iyayen ki, ki saurara kiji me zance maki da kyau, mahaifin ki Idris yayi maki baiko keda Yarima Abdulmalik nan da sati mai zuwa za'a ɗaura maki aure."

Wani irin bugawa taji gabanta nayi saidai ta rasa na minene, a wani ɓangare na zuciyar ta kuwa tanajin wani irin sanyi daya mamaye mata kasan zuciyar ta, wani irin murmushi ne ya suɓuce mata,da kyal tace.
"Inna naji abinda kikace Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
"Ameen." cewar Mairo.

Itako Bahijja jitake duk da kunya da nauyi ya dabaibaye ta gata kagara a sallameta,ta shiga cikin ɗaki kota samu saukin da takeji a cikin zuciyar ta, saiga Ladidi da sauran dangin Abdulmajid da dangin Binta sukazo da kayan baikon Bahijja daga gidan Idris suka ɗauko su, ana zuwa Bahijja taga anata shigowa da uwayen kaya take taji jikin ta yasake yin sanyi, batasan sadda ta mike ba, suko sai tsokanar ta sukeyi suna cewa, amaryar Yarima, gimbiya Bahijja, itako da gudu ta faɗa cikin ɗaki saman tabarma ta kwanta, tarasa mi takeji a cikin zuciyar ta, haka akaita shigowa ana ganin kayan da aka kawo na baikon Bahijja, bayine keta zuwa ganin kaya, zama sukayi suka fasa alewa da goro sai dabino da sauran kayan makulashe aka rabama dangi kowa saisa albarka yakeyi, abinda suka bari kayan sawa na 'yayan Sarakai sai sarkar Jawhar da azurfa da aka sakoma Bahijja, haka kowa ya koma gida suna sama lamarin albarka.

Bayan kwana ukku a wajen Yarima Malik kuwa ba karamin farin ciki bane ya mamaye mashi zuciya ba, zaune suke a cikin lambun sashen shi daya ƙayatu da kayan more rayuwa, kallan Yazid yayi yace.
"Yazid niko inasan ganin Bahijja ya za'ayi.?"
"su Yarima ankamu dayawa gaskia ne."ya karashe maganar da sifar zolaya.

Shiko Yarima Malik murmushi kawai yayi dan yasan dole sai sun mashi irin wannan shakiyanci,

"Uhmmm ai sai akiramashi ita, tunda yanasan su gana."
Cewar Dawud dake shan kankana yana kishingiɗe kusa da Yarima Malik.
Yazid ne yace. "Angama Kawu, yanzun kuwa bari insaka akira mashi ita."

Sai a lokacin Yarima yasamu kwarin guiwar yin magana yace. "Da kada ka kira mana kaga yanda zanyi layya dakai."

Dariya suka saka baki ɗayan su, "kaidai ka godema Allah kodan Yarima Dawud ai nasa akira maka gimbiyar taka."

Hakanan yaji wani irin mashahurin daɗi ya lullube shi musamman da yaji yace mashi gimbiyar shi, wani yalwataccen murmushi ne ya subuce ma Yarima Malik har saida fararen hakoran sa suka bayyana ga wani irin kyau da shalki fuskar shi nayi haka dai Yazid ya tafi su koma sukaci gaba dayin firar su, wanda tun kan yanda za'a tsara shagulan bikin ne duk da Yarima yace baiso amman su Huzaifa sun nace sai sunyi hidimar su.

Koda Yazid ya fita a kan hanyar shi da zai sada shi wajen turakar bayi ya haɗu dasu Salame ita da Lawisa sun fito da botikai a hannun su da alama rafi zasu tafi, duk da akwai ruwa a cikin turakar bayi, saidai kwana ki yasamu matsala, kuma har yanzun ba'a gyara musu ba, shiyasa suke shigowa cikin Masarautar suna ɗiban ruwa, ji sukayi an masu magana, waigowa sukayi sukaga Yarima Huzaifa ne duk suka duka kasa baki ɗayan su, suka kwashi gaisuwa, cikin girmamawa, kallan su yayi sannan ya amsa yace.
"Kuje ku kira mani Bahijja, kuce inji Yarima Yazid."
Mikewa sukayi suka koma cikin turakar bayi har gidan su Bahijja nan suka tadda Abban ta shida kanin shi Idris suna lissafa wasu kuɗi da alama na hidimar da suke son suyima 'yar tasu ne, suna shigowa suka duka Salame ce tace. "Baffa barka da rana."

Batare da ya kalleta ba ya amsa mata yace. "Harkun gama rafin?"
"Aaa Baffa daman muntafi ne muka haɗu da Yarima Yazid shine yace mudawo muyi mashi kiran Bahijja."
Itakuwa Bahijja dake can cikin ɗaki take taji zuciyar ta ta tsinke dan tasan mai kiran ta, tama san da wahala Abban ta ya bari, saidai itama tana son taga Ya Malik ɗinta, bata ida sakar zucin da take ba taji Baffa Idris yace. "Ina Bahijja maza fito kije Yarima Yazidu na kiran ki."
da to ta amsa tana saka takalmin kafarta saidai tunda akai mata baiko take wasan yar buya da Abban ta, kunya da nauyin su ya isheta, koda ta fito dukawa tayi gaban iyayen nata, kallan Idris yayi yace. "Wuce kitafi amman ki kula kinji."

"Toh Baffa."
Shiko Abdulmajid shiru yayi baiso ta jeba dan yafison ko Yarima Malik zai kara ganin Bahijja sai in ankaita gidan shi, duk da yasan kiran da Yazid ke mata daga Yarima Malik ne.
tana isa ta iske Yazid ɗin kuwa dukawa zatayi ta gaida shi, da sauri ya hanata, yace.
"Haba gimbiyar Daborah ke yaka mata asaramawa kuma a dukamawa, muje angon ki kesan ganin ki."

Gyalen dake ɗaure a kantane ta jawo takare fuskar ta dan kunyar dake ɗawainiya da ita tace. "Uhmm Ya Yazid kenan." "Gimbiya Bahijja muje ko."

Haka suka tafi sai taji banbarakwai idan ana danganta ta da sunan gimbiya, Bahijjar da tasani mai yawan aikin bauta wai ita yau za'aima inkiya da gimbiya lallai kam akwai aiki kenan, tasan da wahala ma tasaba, ita aikin bauta kawai tasani, da wannan sake saken zucin har suka iso cikin tamfatsetsen falon da Yarima Malik yake saidai bai nan ta wata kofa sukabi suka shiga can cikin lambu, aiko can suka hango shi wannan karan kam harda Lurwan da Huzaifa, suna ganin su suka fara yima Yarima Malik shakiyanci, Dawud ke tare mashi, suna zuwa takoma gefe ta takure duk nauyin su ya addabeta, shiko ta gefen ido yake aikamata wani irin kallo mai ɗauke da ma'anoni iri iri wanda shi kaɗai yasan abinda ke cikin zuciyar shi, sallama sukayi masu suka basu waje, kowa na faɗin albarkacin bakin shi, itako Bahijja kamar marar gaskia takasa kallan Yarima Malik bare su hada ido dashi, ita kanta tana mamakin kanta, shiko sai murmushi yakeyi mata jiyake kamar ya haɗeta ya huta, cikin tattaro Jarumtar shi yace.
"Amaryar Malik, ranki shidade gimbiya Bahijja, ina kawo gaisuwa."

Sunkuyar da kanta tayi kasa tana murmushi sai takeji kamar muryar shi ta yau tafi kowace daɗin sauraro a cikin kunnuwan ta, jitayi yace.
"Uhmm wato kunyata kikeji kenan ko?"
tafin hannuwan ta,tasa tana rufe fuskar ta dasu, dasuke zarazara gwanin burgewa shiko da idanun shi masu firgitar wa ya rakata, yarasa miyasa bai gajiya da kallan kyakyawar fuskar Bahijja.

Sanyayyar ajiyar zuciya ya fesar sannan yace.
"Ɗago fuskarki,ki kalli ma'abocin so da begenta karkimin rowar ganin kyakyawar fuskar ki mai sakamin nutsuwa a cikin zuciya ta, kanwar Malik."

Sai a lokacin ta ɗago fuskar tata tana satar kallan shi ta wutsiyar ido, karaf idanun su suka sake sarkewa dana junan su, ta sake sadda kanta.

"Kidaina jin kunyata Bahijja kinzamo wani sashe na jikina, kin zamo haske a cikin al'amurana kece silar dai da ita komai Bahijja na kwashe sama da shekaru ashirin inasan ganin na daidai ta mahaifiya ta da dangin ki Bahijja amman hakan baisamu ba sai ta silarki, kinga kinzama jigo gareni sannan kinzama silar da mahaifiya ta tagane gaskiya da sanin darajar talakawan ta, Bahijja ina kaunar ki tun kina jinjirarki Allah ya jarabceni da sonki har zuwa yanzun da nike fidda wannan numfashin ina kaunar ki dan Allah ki soni koda rabin yanda nike sonki ne."

Hakanan taji tana murmushi mai sauti kuma kanta na kallan ƙasa takasa hada ido da Ya Malik dinta mai kaunar ta ji tayi yace.

"Kina sona Bahijja."
ske rufe fuskar tayi tana murmushi.
dafe kanshi Yarima MalikusSaif yayi yace. "Uhmm kunya kunyarki tai yawa kanwar Malik, nan da kwana huɗu zan rabaki da wannan masifaffar kunyar taki."

Itadai jitayi bakin ta yai mata nauyi ta kasa magana ko kaɗan saidai jin shi da takeyi yana mata maganganu masu saka mata nishaɗi sai take gani kamar a mafarki dan tuni ta cire tsammanin sake haɗuwa da Ya Malik dinta kamar haka a tare, a matsayin baiwar sama, bare akai ga yazama masoyin ta, wasu kwalla ne masu ɗumi sukayi narasar wanke mata fuska tuno abubuwa marassa daɗi da suka dinga faruwa acikin rayuwar ta wanda ko a Masarautar Raifasu bata fuskanci makamancin haka ba, da sauri Yarima Malik ya matso kusa da ita har tanajin ɗumin fitar numfashin shi, cikin kiɗimewa yace. "Miye abin kuka, ko dai baki sona Bahijja.?"

da sauri ta girgiza kanta alamun aaa.
cikeda damuwa yace.
"to faɗama Ya Malik dinki kukan namene?"
"Bakomai Ya Malik."

Rausayar dakan shi yayi cikin sigar wasa da sangartata yace.
"Uhmm in ba komai, ɗago kanki ki kalli Ya Malik dinki sannan ki masa murmushi yagani."

Sake sadda kanta tayi tano boye fuskar ta."
murmushi yayi yace. "Uhmmm ni yaushe kanwata ta koma haka ba surutu ba rashinji, ba ƙiriniya, kanwata takara girma ta nutsu yanzun ma kunyar Ya Malik dinta takeji."

murmushi ta sakeyi har saida hakoran ta masu tsananin haske suka baiyana shiko sai ta koma mashi tamkar tv cikin kulawa yace.
muga hannun ki gimbiya ta."
Ɗago fuskar ta tayi ta kalle shi, shiko ya kashe mata ido ɗaya, tsananin kunyar shi ce take ɗawainiya da ita, shiko cikin zolayar da baisan yana da itaba yace. "kodai kin kyasa ne, faɗaman inji dagani saike ba wanda zaiji uhmm."

make kafaɗa tayi taki magana, ganin ta takura yasa yace. "toh naji muga hannun."

A hankali ta miko mashi hannun tayi sai sheki yakeyi kamar bana baiwa, shiko da idanu ya kafesu da kallo yanajin wani irin shauƙi na ɗawainiya dashi, hannun sa ya saka cikin aljihu ya fiddo wani haɗɗan zobe na diamond ya zira mata shi a cikin yatsunta da suke zara zaren gaske masu matukar kyau da sheƙi, jin yanda ya saka mata zoben yasa ta kalli yatsanta taga sai ɗaukar ido yakeyi, murmushi tayi tace. "Nagode Allah yakara bud....

"girgiza kai yayi yana mata nuni ya ɗaura yatsan shi bisa lips din shi, daga bisani ya ciro wani zoben ya mika mata, shi kuma na azurfane mai ɗan karen kyau, ansa tayi tana kallan shi, baice mata komai ba, sai mika mata hannun shi da yayi aiko tagane abinda yake nufi, itama zira mashi zoben tayi, tace. "Masha Allah Ya Malik kamar dankai akayi shi yai maka kyau"

Murmushin yayi mata yana kwaikwayar maganar ta yace. "Dagaske kanwar Malik yaima Ya Malik dinki kyau?"

Sadda kanta tayi kasa tana murmushi tace. "Eh mana yaima Yayan Bahijja kyau sosai ma kuwa."

Lumshe idanun shi yayi jin wani yar yar da tsikar jikin shi keyi musamman yanda take sarrafa labben ta masu tsananin kyau da sheƙi, buɗe idanun shi yayi a hankali ya zuba mata su, zaiyi magana sukaji, Huzaifa nacewa.
"To masoyan juna kunata tsinkar fure har ankira sallar zuhr sai a hakura ko.?"

Jitayi kamar ta nutse kasa dan kunyar Huzaifa data isheta,ita kanta batasan sun daɗe har haka ba, batare da sun kuma cewa komai ba, suka mike ta cikin falon shi ya koma Huzaifa na maye mashi baya yana mashi shakiyanci, ita kuwa Bahijja ta cikin lambun tabi ta tafi gida ranta fas batada wata damuwa.

Da marece bayan sallar la'asar Sarki Abu-Jalal ne tareda MalikusSaif sunacin abinci a tare, shida kakan nashi sai anna shuwa dajin daɗi Yarima kefaman yi, da kagan shi zakasan yana cikin farin ciki marar misaltuwa, Abu-Jalal ne ya kalli Yarima cikin tarin so da kauna yace.
"Ɗana nikam ina fatan ka gana da Bahijjar taka ko?"
Sunkuyar da kanshi yayi cikin ɗan jin nauyin kakan nashi yace.
"Eh Abi mungaisa."

"Masha Allah, harna kosa inga an ɗaura maka aure hankalina zaifi kwanciya Abdulmalik."
Murmushin jin dadi Yarima yayi yace. "Inama kazauna nan baki ɗaya karka koma gida."
"Uhmm Abdulmalik kenan ina zankai haƙkin mutane dake kaina, nauyi yaimani yawa da ace akwai wanda ya ɗauke mani wannan nauyin dana zauna dakai."

Rausayar dakai yayi cikeda gamsuwa yace. "Wannan dalilin yasa bansan mikama sam, bansan mulki Abi."
"Aiko kwara kasama ranka zama Sarkin Daborah nan da 'yan kwanaki kaɗan ma kuwa."
Wani shock ya ziyarci Yarima yace. "Abi nan da yan kwanaki fa kace?"

"Kwarai kuwa randa aka ɗaura maka aure washe gari za'aimaka naɗin Sarauta danma mungama magana da mahaifiyar ka, itama yaka mata ta huta, shekararta talatin da biyar tana mulkin Daborah tunkan a haife ka."

Sadda kanshi ya sakeyi baice komai ba, danji yake lokaci guda kanshi yana sara mashi da karfi dan bai tsammaci wannan zancen a halin yanzun ba, shi baida buri sa ya wuce ai mashi aure shida Bahijjar shi, amman za'azo a haɗa shi da jidali, ɗan gutun tsoki yaja wanda baisan yayi shiba, shima Abu-Jalal da ido ya bishi daga bisani kowa ya tashi ya nufi ɗakin shi.

A turakar bayi kuwa Jakadiya Hajara ce da aminiyar Sarauniya Zulaiƙa wato Kubra, sukaje gidan Abdulmajid akayi sa'a kuwa sun tadda shi zaune yana gyaran kaba, suna shigowa Binta da Mairo suka taresu cikin girmamawa, sannan suka kawo masu ruwa cikin gidauniya karama, bayan sun gaisane Hajara tace.
"Daman munzone da wani bukata a gareku inba damuwa."

Abdulmajid ne ya maida hankalin shi kansu kaf, daidai nan Idris ya shigo cikin gidan da wani buhun kaya har guda biyu Binta yabawa ta shiga dasu ɗaki, shima zama yayi suka gaisa dasu Jakadiya, Abdulmajid ne yace.
"Badamuwa Jakadiya munajin ku wace bukata ce wannan."

"Eh daga Sarauniya Zulaiƙa tace tana bukatar abata Bahijja takoma sashen ta na wasu kwana ki domin yimata tirin amare kamar yanda al'adar Masarautar Daborah take."

Kallan juna su Idris sukayi, "eh bamu tari numfashin kuba saidai bai kamata ace Bahijja taje gidan surukai ba, ba tareda an daura aure ba, da kun kawo kayan gyaran jikin, sai Innar ta Maryama ta dinga yimata a nan."cewar Abdulmajid.

Cikeda rashin gamsuwa Hajara tace. "Aaa abinda yasa akwai mai wannan aikin fil'azil a cikin wannan Masarautar take, kuma haɗine da akema amaren Daborah, sannan ita kanta Sarauniya ba lallai bane ace a rana taga Bahijjar ba saboda akwai maiyin wannan dilkan aikin tane kuma waje na musamman ake tanada musu."

Abdulmajid ne zai sake magana, da sauri Idris ya tare shi da cewa.
"Badamuwa Hajara, yaushe zaku tafi da Bahijjar?"
Cikin jin dadi tace."Ai zuwan nan ma saimu tafi da ita."

Abdulmajid ne zai kuma magana, sai Idris yace.
"Ba matsala ina Bahijja kiramin ita Mairo."
Mikewa tayi ta tafi cikin ɗaki, shiko Abdulmajid cikin rashin jin dadin shi yake kallan ɗan uwan nashi, shiko sai alamar yayi hakuri yake nuna mashi dan yasan halin Abdulmajid kaifi ɗaya ne in yace eh, eh ɗince hakama inyace aaa itama da wahala ya sauya,
tareda Mairo suka fito, itako Kubra sai kallan Bahijja takeyi tana yaba kyawun ta a cikin zuciyar ta, gani take kamar ba baiwa ba yanda fatar jikin ta ke shalki tana glowing sai kace wata Sarauniya, dukawa tayi ta gaidasu.

kallan ta Idris yayi yace.
"tashi kuje keda surukan naki, ki kula sannan kikara yin biyayya domin iyayen kine kinajina."
"Eh Baffa naji."
"Allah yaimaki albarka."
Baki ɗayan su, suka amsa da ameen.

Haka suka tafi saidai Bahijja na bukatar karin bayani mi zataje yi, amman ba dama haka tabisu har suka shiga cikin Masarautar, sai dai ana tunkaro sashen Sarauniya Zulaiƙa taji gabanta na faɗuwa kuma yana dukan goma goma, kallan Jakadiya Hajara tayi cikeda tuhuma, cikin sanyin murya tace.

"Saki ranki Bahijja nan ɗinma gidan kune."
Ɗan jinjina kai tayi amman jikin ta kam yaimata sanyi matuka, har suka shigo cikin tamfatsetsen falon Sarauniya Zulaiƙa, sannan sukabi ta cikin wani corridor mai bala'in kyau, sannan suka shiga wani makimanci falo, wanda baikai na farkon girma ba, saidai ya wuce da ajin wancan haɗuwa da tsaruwa, nan suka zauna bisa lallausun kujeru na alfarma, kasa Bahijja ta zauna saman kafat mai taushi, Jakadiya tace.
"Yata hawo bisa kujera mana."
sam Bahijja taki zama akai, hakan yasa suka rabu da ita, suna zaune a cikin falon sai zuba sanyayyen kamshi yakeyi, sukaji takon shigowar Sarauniya Zulaiƙa cikin falon ta wata kofa wadda zata sadaka da bedroom ɗin ta, da sauri da sauri zuciyar Bahijja ke duka tanajin tsoro shakka da kunci lokaci daya ya mamaye mata kasan zuciya, sallamar ta suka tsinkaya lokacin farko da Bahijja taji daɗin muryar Sarauniya Zulaiƙa a rayuwar ta, saboda tayi sallamar cikin sakin fuska da aminci shiyasa sai tazo mata a bazata cikin kunnuwan Bahijja, amsawa sukayi, saman wata kayatacciyar kujera ta hau mai zaiba wadda tasha ado da duwatsun lu'u lu'u, dan Allah ya albaraci Masarautar Daborah da dukiya irin su zinari azurfa, lu'u lu'u, jawhar, murjani da sauran kayan arziki na karafa, shiyasa suke yawan ado da kayan zinarai, tana zama ta zubawa Bahijja idanunta masu kwarjini, saidai ita Bahijja kasa kallonta tayi dukar da kanta cikin ƙasa cikin sanyayyar muryar ta tace.

"Yata ɗago fuskar ki mana."
maimakon Bahijja taji sanyi a ranta saitaji kirjin ta ya buga da karfi daram haka taji yabada sauti, musamman da Sarauniya Zulaiƙa ta ambace ta da sunan ɗiyar ta, jitayi ta kuma cewa.
"Haba ƴata kidaina jin wannan kunyar nifa mahaifiyar kice saki jikin ki, kinji gimbiya ta."

Sai taji wani irin take Ya Malik dinta ya faɗo mata arai da taji Sarauniya Zulaiƙa tace gimbiya ta, a hankali ta ɗago kyakyawar fuskar ta ta kalli Sarauniya Zulaiƙa, itama Bahijjar take kallo, aranta ko tana ayyana irin tsantsar kyau da diri da Allah yaima Bahijja wanda sai yanzun take gani kyaunta a zahiri, wanda bata taɓa ganin kyawun Bahijja irin hakaba sai yau, lallai dole Yariman ta ya ruɗe ashe yasan abinda ya gani, gaskia kam akwai kyau daman haka Allah yake bada baiwar sa a gidan marassa karfi sai ya aje baiwa a cikin gidajen talakawa, ajiyar zuciya ta sauke wanda tuni Bahijja ta maida kanta kasa, ita Sarauniya Zulaiƙa karfin hali tayi ta taso tazo gaban Bahijja ta kamota da hannun ta ta ajeta bisa kujera, ta zaunar da ita, saida Bahijja ta rufe idanun ta, karo na farko kenan da tahau irin waɗan nan kujerun masu masifar taushi da laushi, ajiyar zuciya ta sauke a sirrinci. a hankali tace. "Ummu da kinbarni kasan zaifi min d.....

"Hannu tasa ta rufe bakin Bahijja take taji wani irin masifar so da kaunar Bahijja ya dira a cikin zuciyar ta, musamman. data kirata da Ummu, kuma take ta tuna ranar da aka haifi Bahijja lokacin da tace aje a fille kanta dana iyayen ta, maganar Malik ce ta dawo mata sabuwa lokacin yanada shekaru sha biyar a duniya, yake cemata, Ummu dan Allah kada ki kashe ta kibarta ta zamar mani yar uwa kuma kanwata, inason ta dan Allah Ummu kibarman ita, sannan inasan a saka mata suna Bahijja!"

Sake bude idanun ta tayi da suka sauya launi ta kalli Bahijja, cikin shauƙi tace. "Tabbas Abdulmalik ya faɗi gaskia, kin zama ƴata Bahijja kuma matar ɗana mafi soyuwa a wajena, saidai kisani Bahijja kisa a ranki nan gidan kune, kuma ni mahaifiyar kice, sannan bance ki dinga zama a kasaba, domin haka zai taɓa lafiyar ki, ki zauna kowace kujera kikaga dama, komai mallakin kine kinji 'yata."
"toh Ummu nagode Allah yakara girma da ɗaukaka."
"Ameen ya rabbi."
wanda baki ɗayan su suka amsa ma Bahijja.


_Allah Sarkin dadi inji barawon zuma, yau ga Sarauniya Zulaiƙa, na kiran Bahijja da yarta harda cemata gimbiya 🤣 BAYIMA 'YA'YA'NE fans gareku, lol😂_

Wani sanyin dadi ne ya ziyarci zuciyar Bahijja a ranta ko cewa tayi. "Wai dagaske ni Bahijja, nice zan zama 'ya' kodai mafarki nikeyi ashe akwai ranar da bayi zasu zama 'ya'ya? Maganar Sarauniya Zulaiƙa ta katse mata sakar zucin da takeyi, jitayi tace. "Ke Mansura zonan?"

Wata baiwa ce matashiya tazo ta duka ƙasa, a hankali Bahijja ke kallan ta, tabbas tasanta a cikin turakar bayi, saidai basu taɓa magana ba, ba asalin baiwar Daborah bace siyosu akayi a kasuwar bayi, cikin kulawa Sarauniya tace. "Ga gimbiya Bahijja nan kidinga kulawa da abinda

Please Login or Register in order to submit comment