Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Masarautar tamu albarka sayyidina rasulillahi."

"Ameen ranka shidade gaskia munatayaka murnar wannan aure da aka daura fatan Allah yabaku zaman lfy, Allah yasa abokiyar arziki ce.

"Ameen Ciroma Sarki ya amsa, ai insha Allah gimbiya Aisha abokiyar arziki ce."
Cewar Sarkin zagi.

Haka akaita hidima cikin Masarautar Raifasu.

Hakama a cikin Masarautar wajen su Jakadiya Aisha sai hidmar su sukeyi, saida tasha ado iya ado sai tsokanar ta akeyi ana gimbiyar Sarki Muhammad, saidai tayi dariya tana mai jin dadi da farin ciki.

Ranar dai haka akai hidima kowa yana murna musamman bayi dake ganin Allah ya basu gimbiya mai tausayin kowa, ba karamar gimbiya Yazira ba, wannan yasa sukaita murna samun Yanci da matsayi sunsan wahalar su ta kare a cikin Masarautar Raifasu.


Yau takama alhamis su Sarki MalikusSaif suka gama hada kayansu dan tafiya Masarautar Runo.

Tunda MalikusSaif ya shigo sashen Gimbiya Bahijja ya isketa sai kuka takeyi, bakaramin tashin hankali ya shiga ba, da sassarfa ya isa wajen ta ya rungumota a jikin shi cikin tsausayawa ya dinga bubbuga bayan ta a hankali yana shafa kwantaccen gashin kanta yace

"Haba Nurol Hayat, sai yaushe zaki daina wannan kukan? Kinaso in tafi cikin zullumi da tunani, haba tawan kidaina kuka kinji!"

"Share kwallan idanun ta tayi tace.
"Ya Malik kaifa kace bazaka kara yimin nisaba."
"Haba tawan ba jimawa zamuyiba kinga ba dadi ace banje ba, kidaina kuka zancema Abbuh nafasa tafiya sai inzauna wajen gimbiya ta haka yai maki.?"

Shiru tayi tana kallan kyakkyawar fuskar sahibin nata cikin sanyin murya tace

"Nahakura kaje Ya Malik dan Allah kakulaman da kanka kaji Yayan Bahijja."

Murmushi mai fadi yayi har saida hakoran sa suka bayyana

Ya rankwafo ya manna mata kiss bisa cikin ta yace.
"Shikenan kanwar Malik Allah yaimaki albarka keda babyn mu."
"Ameen habibi na."
"Yawwa Hayati albishirin ki."

Cikin zumudi tace.
"Goro." rausayar dakan shi yayi yace
"Fari ko ja?"
Ɗan juya fararen idanun ta tayi tace.
"Fari kyal."

"Tom tashi inkaiki wajen Umma ki zauna a can harsai ranar da Ya Malik dinki zai dawo."

Wani irin sanyin dadi taji ya ratsata daman batasan kadaici, yanzun zataje gun Umman ta.

Batasan sadda ta rungume shi ba tana murna.
"Habibina nagode Allah yatsare man kai inason ka Ya Malik."

Shiko saijin dadi yake don farin cikin Bahijja shine nashi, da haka dai ya kamata suka shiga daki daman ya hada mata kayan ta suka tafi sashen iyayen Bahijja.

Sunzo shiga kenan suka hadu da Sarauniya Zulaiƙa tayo bankwana da surukanta.

Cikin sakin fuska take kallan yaran nata gwanin burgewa tace.

"Yawwa Abdulmalik daman yanzun nike cewa za'a rako 'yata gun Umma kafin mudawo shikenan ko ka kyauta kuwa."

Cikin ladabi Bahijja ta gaida Sarauniya, Zulaiƙa.
Riko hannun ta Sarauniya tayi suka shiga cikin falon gidan Binta da sallama a bakin su, cikin farin ciki ta amsa masu.


Samun waje sukayi suka zauna.
"Ummun Bahijja sannun ku, ɗana ashe tafiya zakuyi?"

Cikin jin kunya MalikusSaif yace.

"Eh Umma."
"Allah yasa kuje lfy ku dawo lfy?"
"Ameen Umma"
"Yaww Umman Malik, daman nace bari inkawo maki 'yata kafin muje mudawo sai ta zauna wajen ki."

Cikin jin dadi Binta tace.
"To Ummun Bahijja bakomai fata Allah yasa kudawo lfy."

Ameen ya rabbil alameen.cewar su baki ɗayan su.
Sai a lokacin Bahijja tagaida Umman, cikin kewar yarta da kaunar ta amsa, har zasu tashi sukaji maganar Abdulmajid yana cewa.
"Yau kuma manyan baki mukayi a gidan namu gaskia ansamu albarka kenan.

Yana isowa ya zauna.
Suka gaisa da Sarauniya Zulaiƙa.
Cikin kulawa MalikusSaif ya gaida surukin nashi, nan sukayi sallama.
Har Sarauniya Zulaiƙa ta mike taji anrike ta, ganin yanda Bahijja ta marairace sai taji ba dadi, wani irin tausayin ta yakara kamata.
"Ummu na dan Allah ke kitsaya wajena kada kitafi."
"Ayyah 'yata kiyi hakuri kwana ukku zamuyi insha Allah ki zauna wajen Umma kinji kidaina damuwa."

Gyada kai tayi alamun gamsuwa.

Shima Sarki MalikusSaif jiyake kamar karya tafi, haka sukaita satar kallan junan su, kowa yana turawa junan su sakwanni, d haka dai sukayi bankwana, nan Binta da Abdulmajid sukayi masu rakiya, suna fita kowa ya hadu wadan da za'ayi tafiyar dasu.

Matawalle, Kangiwa, Galadima, sai Yazid da Huzaifa, da Sarauniya Zulaiƙa haka kowa yahau dokin shi suka kama hanyar tafiya Masarautar Runo dake cikin birnin Gambia.

_Masarautar Waisu_

Baki daya tagama karadewa da maganar Sarki Haishir inda wasu ke ganin suyi mashi bore su tsige shi bisa mulki wasu naganin aje a kashe su shida mabiya bayan shi, kasancewar sunfi su yawa, saidai duk lalacewar sunsan Sarki Haishir Jarumi ne zai iyaja da kowa a cikin su.

Shiko ganin rabi da kwatar manyan fa'da duk sun juya mashi baya yasa ya kalli Galadima yace.

"Mi zakace akan mutanen da suka kasa yima shugaban su biyayya?"
Cikin girmamawa yace.
"Ranka shidade inaga tinda basu fahimci manufar muba mi zai hana kasa a taramaka su, muje wajen Gurfanai kace ya kare kansa daga cutarwar d mukeso muyi mashi, kaga inya kare kansa sai mubarsu da addinin su shine na gaskia."

Jinjina kai yayi yace
"Tabbas Galadima kayi hikima haka za'ayi.
Bai kasa aguiwa ba ya tada dan aike zuwa wajen Waziri Juru kamar yanda suka shawarta.

Koda sakon Sarki Haishir ya iske Waziri Juru ba karamin mamaki yaiba, yasan abinda bai yuyuwa dan bai taba ganin Gurfanai yayima kanshi komai b, saidai wata zuciyar na nuna mashi cewa zai iya.
Cikeda gadara yace.
"Kace mashi mun amince da marece a hadu wajen Gurfanai."


_Masarautar Raifasu_

Sarki Muhammad da amaryar shi gimbiya Aisha suna zauna a katafaren falon shi, sunacin kayan itatuwa, hankali kwance, cikin kaunar junan su, wanda yanzun yasan ya zama cikakken mutun kuma ya tababtar da yai aure, yana godema Allah da ni'imar da yaimashi cikin kulawa yace.

"Gimbiya ta baki ganin munyima Saifulislam laifi har muyi aure bamu gayama Sarki MalikusSaif ba."

Murmushi tayi tace
"Allah yataimake ka, ba dadi kam amman ai lokacin ne ya kure kuma kaga sunsha gaganiya damu kada abun yaimasu yawa."
"Kema kinyi magana, amman yakamata watara mukai masu ziyara."
"Gaskia kam, saidai mubari idan yarmu Bahijja ta haihu sai muje kamar zaifi."

"Kwarai kuwa Allah ya sauke ta lfy."
"Ameen ya Allah."
Cigaba da cin kayan itatuwan su sukayi sai kuma yace.
"Yawwa gimbiya kinsa Jakadiya sun raba kayan abincin da za'a rabama bayi.?"
"Eh ranka shidade tunjiya anbi kowane bawa da kayan masarufi sunata godiya Allah yakara sutura."

"Ameen ya rabbil alameen."cewar Sarki Muhammad.
A cikin taskar bayi kuwa duk inda kaje ba abinda akeyi sai sam barka d mulkin Sarki Muhammad, musamman ma gimbiya Aisha, da suke ganin ita takawo wannan tsarin na tallafawa kowane bawa na Masarautar wanda zuwa yanzun suke kara ganin lallai kam *BAYIMA **YA'YANE.*

Haka kuwa akayi ita kesa Sarki Muhammad yin aikin alkhairi tun tana Jakadiyar shi har zuwa yanzun da Allah yasa tazama matar shi.

_Haka akeson mutun ya kasance mai sa aikin alkhairi bana sharri ba. Hausawa nacewa ba'a mugun Sarki sai mugun bafade Allah yasa mudace🙏_


A cikin Masarautar Daborah kuwa ba kadan Wazirin Sarki MalikusSaif ba ke kulawa da nauyin da aka barmashi ba komai yana tafiya yanda ya kamata.

Hakama wajen Binta da Abdulmajid ba karamin kula suke ba yarsu ba dana abinda ke cikin ta, musamman Mansura hadimar itama tana iya kokarin ta, ba karamin kyau Bahijja tayiba duk da tana kewar Ya Malik dinta, amman tana samun kulawa wajen iyayen ta hakama wajen kanwar mahaifiar ta Saude.....



_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
And
Comment
Pls


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 125&126

*Na sadaukar da wannan page ɗin ga Malamai magada Annabawa,da ɗaliban ilimi*👍🏻

_Kofa buɗe take ga wanda zaiyimin gyara musamman wannan page din a tuntubeni ta wanann no 07034464517 sai najiku_ 🥰



_Masarautar Waisu_


Da marece kuwa kowa ya samu kiran Sarki Haishir zuwa wajen katan icccen Gamji wanda yake cikin Masarautar kowa yana jiran yaga abinda zai wakana a wajen abin bautar nasu.

Iccen Gamjin dai ya share sama da shekaru dubu biyu yana cikin Masarautar Waisu wanda sukema lakabi da Gurfanai, tun kaka da kakanni suke bautar iccen Gamji acewar su shine abin bautar su ma'ana Gurfanai.

Kowa ya fito harda Waziri Juru da tawagar shi, Sarki Haishir kawai suke jira da sauran jam'ar sa, ganin shiru sunki fitowa hakan ya samu damar yin yan maganganu wasu na cewa Sarki Haishir ya tsorata ne shiyasa baizo ba ai daman sun san Gurfanai shine addinin gaskia.suna cikin hakan kuwa kamar samara suka hango jama'ar Sarki Haishir suna zuwa inda suke.

Sunyi mamaki dan basuyi zatan zasuzo inda suke ba.
Koda suka iso abinda Sarki Haishir yafara yimasu shine Sallama kamar yanda addinin musulunci ya tanada duk da yasan ba amsa shi zasuyi saidai ya sanya shakka da tsoro dankare a cikin zuciyoyin su, musamman Waziri Juru dakewa kawai yayi, sannan yayi mamakin ganin shi da bako duk da alama musulmi ne.
Cikeda da dakewa ta Waziri Juru yace.
"Ashe zakazo ai yakama ta kazo da wuri kamar yanda mukazo inhar addinin da kake takama dashi gaskia ne!
sannan miyasa katara mu nan wajen ko kazo ne dan ka tuba ka kadawo bisa burbar kaka da kakanni?"
Wani irin shekakken kallo Sarki Haishir ya banka masu wanda saida suka raina tasu gaskiar da suke gadara d ita.

Goya hannayen shi yayi bisa bayan shi yafara zagaye Waziri Juru cikin kaskanci sannan ya daga hannun shi manuniya ya nuna Gurfanai da yatsa yace.
"Ashe tambaya ta kakeyi miyasa najima banzo na, atinani na shi wannan katon iccen abin konawa nayi zatan yagaya maku dalilin rashin zuwana
Ashe dai bai faɗa maku ba?"
Takowa yayi cikin gadara ya dafa kafadar Waziri Juru ya kuma cewa.
"Kazo ka tambaye shi miyasa banzo ba nasan yana da wannan ansar tunda kuna ikirarin shi ubangijin kune!
zoka tambaye shi, ko ka tsorata ne?"

Wani irin tsalle zuciyar Waziri Juru takeyi dan yasan ko za'a kashe Gurfanai bazai iya magana ba, tun daya tashi yana bautar Gurfanai baitaba firta da dai dai da kalma ɗaya ba, bare har ya iya yimashi wannan bayanin, taya ma za'ayi Gurfanai yasan dlilin daɗewar Sarki Haishir bayan shidin icce ne kuma girke yake waje ɗaya? bai ida sakar zucin da yake ba yaji amon maganar Sarki Haishir yace.

"To nafahimta Ya Juru tunda ka gaza yima shi wannan maganar to ni Haishir zan mashi idan har yabani amsar wannan tambayar tawa na yarda zanmaku biyayya sannan zanci gaba da bin wannan addinin da mukeyi kun amince?"

Kallan kallo sukema juna tsakanin Waziri Juru da mabiyan shi sun gama saduda sunsan tabbas Gurfanai zai iya kunya tasu, kanshi ya kulle ya rasa abin cewa.
"Kada kudamu Juru ni bance idan ya kasa magana ba zakuyi addinina ba, nine zan maku mubaya'a matukar yayi magana."

Yar karamar ajiyar zuciya Waziri Juru yayi yace.
"Duk da kasan ba kowa ne lokaci yake bukatar magana ba, miyasa kake son takura shi?"
Murmushi yayi yace.
"Kada kadamu aiyau yasan abinda ya taramu sai ya wanke ku daga zargin ku da nikeyi, indai ya cika kuda shi masu gaskia ne."
Wani irin tafasa zuciyar Waziri Juru tayi baisan sadda yace na amince.
Matsawa gaban Gurfanai yayi da kyau yace.
"Gurfanai inasan ka faɗama mabiyan ka dalilin dayasa ban fito wannan wajen ba, sai yanzun kowa na sauraran ka?"
Wurin yayi shiru kowa ya kasa kunne yaji maganar Gurfanai wanda suke ikirari shine abin bauta a garesu.
Sunkai minti goma basuji ko motsin iskan wajen ba bare susaka ran maganar Gurfanai, hatta Waziri Juru ba karamin takaici bane ya cikashi, shi da kanshi ya kalli Gurfanai yace
"Magana zakayi dan ka fitar damu cikin wannan kunyar da muke shirin faɗawa Ya Gurfanai?"
Still wajen minti biyar baice uffan ba.

Shiko Haishir da jama'ar shi sai murmushin mugunta sukeyi.
Matsowa yayi ya sake matsawa da kyau a gaban iccen na Gurfanai yace.
"Baka sanni ba ko?
Saboda baka iya yimaka kanka anfanin komai saidai aimaka?
Saboda baka iya turema masu bauta maka wani bala'i a yayin da yake tunkaro mu!
Saboda kasha kunyata mu a idon makiya baka bamu nasara!
Kai kanka baka tsinanawa kanka komai bare mu!
Muke sa ruwa da sabulu mu wanke ka tas, sannan mu aje maka abinci waikai ne abin bauta abin kunya yanda muka aje haka zamu ɗauke!
Baka taba bamu nasarar yaƙi ba saidai acimu a wulakan tamu a gaban duniya!
Yau gashi amsa yar karama ta gagareka miyasa?
Ko zaka iya bani waɗannan amsoshin?"

Waziri Juru ya tunkaro Sarki Haishir a fusace da niyar yai mashi wulakanci yaji daga cikin mabiyan nashi sunce.
"Kabar shi Waziri inda gaske shi Gurfanai din yake ya bada waɗan nan amsoshin muma yau munasan muga maganar Gurfanai a gaban mu dan mufita cikin kokonto!"
Jikin Waziri Juru yai sanyi likis yasan tabbas yau dai komai zai sauya tunda Gurfanai yakasa komai.
"Muna sauraran ka Ya Gurfanai ka wankemu daga idan makiyan mu."
Baki ɗaya mabiyan shi sukayi wannan magana.

Abin takaici wajen minti ashirin ko gezau Gurfanai baiyi ba
Girgiza kai Sarki Haishir yayi yace.
"Ya'akai mu muka fika katabus anya bamuyi da nasanin bata lokutan muba akan bautar kaba?"

"Karka kara jifanshi da wadan nan maganganun naka Haishir."
"Kabar shi yai magnar shi, mu kanmu a halin yanzun kanmu ya bude munga haske."
Cikin kiɗimewa ya juyo ya kalle su yace.
"Mikuke son cewa ne?
Kuna nufin kuma zakubar addinin kaka da kakanni?"
"Kwarai kuwa Juru matukar Gurfanai bai kare kansa ba."

Ɗan tafa hannu Sarki Haishir yayi kowa yai shiru sannan yace.
"Yanzun wannan shine damar karshe da zanba Gurfanai, idan har shiɗin gaskia ne, muna son yau ɗinnan yagaya mana abinda yafaru a Masarautar Raifasu duk da zuwa yanzun sun daina bautar shi, amman kilan nasan zai sani?"

Kwalalo idanu Waziri Juru yayi yasan su kansu basu san miyafaru ba bare shi da ko motsi baiyi komai sai an mashi.
"Eh yafaɗa mana muma muna bukatar sani cewar Ciroma.
Haka kuwa kowa ya maida hankalin shi kan Gurfanai nan ma ba wani magana ko motsi.
Dariyace ta subuce ma Sarki Haishir yace
"A haka zakuyi ikirarin bautar iccen Gamji busasshe wanda bai iya yimana komai!
Wanda ya kasa bamu nasara a Yaƙu nan da mukeyi!
A haka zamu bata lokacin mu akan abinda yazun in muka ga dama zamu iya sa gatari mu faskare shi tas! Sannan mu babbage sauyar shi daga bisani muƙona shi kurmus da wuta saidai ya zama tarihi a cikin Masarautar Waisu, ku zama shaida yakasa amsa tambayoyin danai mashi dan haka ni Sarki Haishir da mabiyana mun barran ta akan abinda muke bauta mawa tun kaka da kakanni na zabi addinin gaskia wato addinin musulunci, idan kunada tambayar da zakuyima addinina ga malamin addinin musulunci zai baku haske."
Aiko wajen ya kaure da surutai rabi da kwatar jama'ar Waziri Juru sukace.
"Muma bazamu sake bautawa Gurfanai ba tunda baida amfani agare mu."

zare takobi Waziri Juru yayi yace.
"Kada kuyarda da Haishir makaryaci ne."
"Kai Juru mufa ba mahaukata bane a gaban ka komai ya wakana taya zamuci gaba da bautar iccen Gamji."
"Naji amman kubari muma muyi masu tambaya in munga gaskiar su sai muyi mubaya'a, kun amince?"
Baki ɗayan su sukace mun amince.

Waziri Juru ya kalli malamin da Sarki Haishir ya gabatar masu dashi yace
"Munasan musan minene addinin ku sannan miye abin bautar ku?"
Matsowa yayi ya tsaya agaban su yace.
"Alhmdullh naji dadin wannan tambaya da kukayi mani."
"Dakata taya zaka dinga yimana maganar da bazamu fahimta ba kace alhmdullh mi hakan ke nufi?"
Murmushi yayi yace.
"Tana nufin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai baki ɗaya."
Cikeda mamaki Waziri Juru yace.
"Godiya ta tabbata ga Allah fa kace, yiman baya ni.?"

" Ubangiji nane kuma ubangijin ku wanda ya haliccemu baki ɗaya tun muna cikin mahaifar iyayen mu daga digon maniyi zuwa gudan jini har muka koma tsoka daganan ya busa mana rai ya kammala mana halittar mu har yai sanadiyar zuwan mu wannan duniyar ta hanyar iyayen mu mata duk a cikin wata tara da kwana tara ba mai iyayin wannan sai Sarki Allah buwayi gagara misali
Shine ubanginin mu wanda ya halicci wannan iccen da kuke bauta mawa rayuwar mu a hannun shi take inyaso yanzun zai karbi rayuwar mu data iccen da kuke bautamawa."

ɗaga mashi hannu yayi yace.
"Dakata malam kace zai iya karbar ranmu harda na Gurfanai tayaya kum ai shima fa Gurfanai yakai shekaru dubu biyu a duniya taya za'ai yau kazo mana da wannan lbarin."

Murmushi yayi yace.
"Kwarai kuwa icce ne fa kuma Allah ya halicce shi dakai kanka mai magana wannan ba wani abu bane, bari ingaya maka wani abu.
Kai dakake wannan maganar yau ina iyayen ka wadan da suka ɗaura ku bisa wannan bautar da kukeyi suna ina?"
Shiru Waziri Juru yayi, can wata mata mai juna biyu tace
"Duk sun mutu."
"Miyasa wannan iccen Gamji bai hanasu mutuwa ba?
Miyasa idan baku lafiya bai yaye maku ciwo ba?
Miyasa bai fɗa maku abinda ke cikin wannan matar mace ko namiji bane, wannan ilimin ubangijina ne mai kowa da komai shiyasan abinda ke boye da wanda ke baiyane."

"Dakata miyasa kace hakan bayan kaima kanka baka san abinda ke cikin nata ba, taya zamu sani?"
"Eh niba zansani ba saboda bansan ranar da zan mutu ba,wannan ilimin na ubangiji nane, shine Ya aiko manzan sa ya sanar mana da hakan."

"Yana ina kuma taya zamu iya gane cewa shine ubangijin gaskia?"
Cewar wannan matar.

"Ubangijina yana sama ya nuna sama da yatsa manuniya, sannan yace.
Kuma shine mai kashewa mai rayawa, sannan shine wanda yake halittar mu ya rayamu, kuma shike bamu ruwan daga sama ya wada tamu da arzikin abinci daga abinda muke shukawa shike sanya mana safiya da rana da marece da dare dan yazama rahama agaremu muyi bacci muyi komai cikin sirri."
Bari in maku wata tambaya.?"

Duk sukace munajin ka.
Yace."miyasa kuke ganin mutun ya mutu a gaban idan ku batareda anyanka shi da wukaba ko mashi batareda ɗigon jini ba, bakuyi mamakin hakan ba?"
Duk sukace munyi.
Yace. "Wannan ikon Allah ne."
Wa yasan matar da keda ciki kuma yasan yau zata haihu ko gobe.
"Duk sukace babu."
Yace "wannan ilimin ubangijina ne.
Ya sake nuna wannan matar mai juna biyu
yace. "Idan Allah yaso yau ɗin nan ko gobe wannan matar zata iya haihuwa, kuma inyaso yau ɗin nan a cikin mu zai iya daukar rayuwar wani ko mu dukan mu, sannan yana cikin girman ubangijina in yaso yau ɗinnan saiya saukar da ruwan sama."
Ya nuna Gurfanai yace.
"Wannan ko bai iyawa saboda shiɗin icce ne kuma abin ƙonawa ayi abinci dashi, amman ubangijina Allah wannan duk ba wani abu bane agare shi shiya halicci sama da kasa duk abinda mukeyi yanajin mu shike bamu abinda zamuci ya azirtamu da lafiya."

Jikin su yayi liqis dan sungam su, koshi kanshi Waziri Juru jikin shi yai sanyi zaiyi magana kenan cikin hukuncin ubangiji iska mai karfi ta taso ta turnike wajen hadari ya ida gangamuwa daman lokacin damina ne garin yai bakikƙirin sama tayi duhu, aka fara neman hanyar boyewa take ruwan sama ya kaure dan dole aka fara guduwa dan samun mafaka da sauri malamin nan ya riko Waziri Juru yace.
"Kaga kaɗan daga cikin ikon ubangijina tunkan aje ko ina har ya saukar mana da ni'imar shi ta ruwan sama, kaga ko Gurfanai ya gaza kuma yakasa boyewa dan kada ruwa ya duke shi, muko dayake ubangijin mu ya wadace mu da lafiya gashi mun gudu dan mu fakema ruwa,amman kuma Gurfanai yakasa fakewa."

Sannan ya sake shi kowa yasamu mafaka ranar haka akaita ruwa kamar zaici gari ga tsawa da walkiya a kaita yi, kowa ya tsorata gashi dai ruwa daga sama yake sauka kuma sunsan ubangijin musulunci da musulmai yana sama, Lallai ya tabbata addinin musulunci shine addinin na gaskia dayawan su duk sun amince.
Suma sauran sun yarda da gaskia wannan al'amarin,shiru shiru ruwa ya ɗauke amman sai karayin shi akeyi.

Wa'anda ke kula da Gurfanai suna cikin ɗakin su daga gefen katanga dake nesa da iccen kaɗan,akan idanunsu sukaga hasken wuta ya sauka akan iccen Gurfanai ya dagargaje ya ƙone ya tarwatse ga wata kara da aka saki saida kowa ya tsorata hatta Waziri dake gaban mahaifin shi bai lafiya yana kalubalantar shi akan ɗaura su da sukayi akan bautar iccen Gamji, shima yace, yasan bai iya masu komai dan haka shi yayi imani da addinin wannan malami,yai imani da Allah wanda ya saukar da wannan ruwan da kuma annabin shi, dan dole Waziri Juru yai shiru take tari ya kama mahaifin shi a gaban idan shi ya mutu.

take maganar malamin nan ta faɗo mashi a rai ganin gashi yau uban shi ya mutu ba tareda ɗigon jini ba kamar mai bacci tabbas yakara yarda da addinin musulunci.

A wajen wannan mai cikin kuwa surukar Ciroma ce ana wannan tsawa cikin ta ya juya cikin hukuncin Allah naƙuda ta kaure sai gashi ta haifo jariran ta maza guda biyu.

Lallai hakan ba karamin mamaki yabasu ba saboda acewar su wai Gurfanai yace sai nan da wata ɗaya zata haihu ko kwana ukku ba abaiba gashi ta haihu ya tabbata addinin da wannan malami da Sarki Haishir keson suyi imani dashi shine addinin na gaskia.

Intakaice maku ba agama ruwan nan ba sai cikin dare, koda gari ya waye kamar jira mutanen Masarautar, sukayi ma wajen Gurfanai ne tsinke da niyar su kona shi tunda shi ba ubangiji bane, abin mamaki sai suka iske Gurfanai ya dagargaje yayi kurmus kamar ba'ataba yinshi ba.

Surutu yafara tashi wasu na ganin Sarki Haishir da wannan malami suka ƙona shi dansu samasu gamsuwa a cikin zuciya, nan masu kula da Gurfanai sukace ba ruwan su tsawace daga sama tafaɗa mashi suna gani yaci ya cinye batareda ya tsinana ma kanshi komai ba.

Jin maganar Waziri Juru yasasu sukayi shiru yace
"Tabbas addinin Gurfanai addini ne na karya ya kasa kare kanshi balle ya karemu yauga mahaifina ya faɗaman gaskia shima ya aminta da addinin musulunci kuma yace Gurfanai iccene yau gashi kowa ya gani, ga mahaifina ya mutu a gaban idona,ba tareda nasani ba bare inga daidai da ɗigon jini na shaidar mutuwar sa dan haka ni Waziri Juru nayi imani da addinin musulunci."
Ji sukayi Sarki Haishir dake tunkaro wajen dan yaga abinda ke wakana yace
"Alhmdullh nagode ma Allah daya nuna maku gaskia."
Ana cikin haka saiga ciroma da jarirai a hannun shi yace
"Nima na amince da wannan addini yau ga jikokina a hannuna matar ɗana ta haihu cikin dare."
Kowa yai mamaki a iya sanin su saura wata ɗaya ta haihu sai gashi ta haihu jiya har ya'ya biyu.

Nan dai baki ɗayan su sukayi imani da addinin musulunci, suka runguɗa zuwa fa'da nan malamin da Sarki Haishir ya kira ya basu kalmar shahada kowa na maimaitawa ya sake yimasu bayani akan addinin musulunci da imani da Allah da manzon sa kowa yai imani.
Yace abashi takarda ya rubuta sako zuwa Masarautar Raifasu aka akaika dan aike yatafi.

Sarki Haishir ne yace
"Mungode akan ƙoƙarin dakayi wajen nuna mana gaskia tabbas addinin musulunci addini ne mai tausayi duk irin muguntar da mukayi maku hakan bai hana Sarki Muhammad kin amincewa da zuwanka Masarautar muba duk da munkasan ce makiyan shi"
Cikin kulawa Tasi'u yace.
"Ai ba Sarki Muhammad keda wannan karamcin ba daga addinin mune, bisa koyarwar fiyayyen halitta annabi Muhammad SAW."
Nan Tasi'u yaci gaba da yimasu bayani daki daki dai dai gwargwado, haka ya zauna cikin Masarautar Waisu."

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

A wajen su Sarki MalikusSaif sun sauka cikin Masarautar Runo bakaramin farin ciki bane ya mamaye Sarki Abu-Jalal ba, musamman dayaga ɗan lelen nashi haka akaita kawo gaisuwa wajen su MalikusSaif daga fa'da ba inda suka nufa sai katafaren falon Sarki Abu-Jalal daya gaji da ƙayatuwa da kayan alatu na more rayuwa tayau da kullin, kowa ya samu waje ya zauna cikeda farin ciki marar iyaka, Sarki Abu-Jalal ne yace.

"Naji daɗin wannan zuwan da kukayi yauga 'yata cikin Masarautar Runo gaskia bansan irin farin cikin da nikeji ba, Allah yaimaku albarka."
Baki ɗayan su suka amsa da ameen.

Haka hadimai sukaita shigowa da abinci iri iri da kayan marmari kala kala haka sukaci suka sha

Please Login or Register in order to submit comment