Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Adam sai dai wanda yafi wani tsoron Allah shine yafi dan uwan sa, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya da numana ga riko amana musulmai basu kansance maciya amana ba ko ta'addanci, saboda addinin ya horemu da zaman lafiya da yan uwan mu, harma da sauran mabiyan addinai saboda farin jakada Annabi Muhammad (SAW) yace,mu zauna dasu karmu cutar dasu, da haka kadai duniya ta tabbatar da cewa addinin Musulunci addinine mai aminci kuma na gaskia, Allah yasa mudace🙏```


Koda Sarki Muhammad ya koma, fa'da ya wuce anata fadanci, basu san hawa ba basu sauka ba kawai sukaji saukar mashi ya kafe ta gefen kan Sarki Muhammad dake saman kujerar shi ta mulki bakaramin tsorata sukayi ba, haka magatakarda Usman ya
zare takardar da aka halbo sannan Sarki ya bada ikon karanta wannan wasikar kamar haka.


_Tabbas kafadi jarabawar mu Baidulƙais yau kaine kaima makiyan mu mubaya'a ka anshi addinin su sannan ka kone kayan tsafin mu tabbas ka tsammaci gamuwa dani bada jimawa ba maci amana Sarrilƙus ke magana, hhhhuuhhh!!."_


Kallan yan fa'dar shi yayi yace.
"Sakarai dashi marar imani mun riga da munce Allah kuma insha Allah mune da nasara, limamin fada yasa yayi musu addu'a kowa ya tashi, kiran Tasi'u yayi yace ya same shi sashen shi wanda yanzun ya kasance babba a cikin Masarautar Raifasu, har Sarkin malaman Raifasu ya naɗa Tasi'u cikin girmamawa yace. "Angama ranka shidade Allah yataimake ka." wani irin dadi yaji da yaji ance Allah yataimake ka inda dane saidai a hada da wani katan icce wanda tuni yasa aka kone shi, kuma bai tsinana ma kanshi komai, lallai kam ya tabbata sunyi shirme yanzun suke akan addinin gaskia, shi yasa Sarauniya Zulaiƙa suka dinga cinsu nasara a wajen yaki a she riko sukayi da igiya mai karfin gaske tunda Tasi'u yace Allah yataimake shi sai yanemi damuwar shi ya rasa gaba daya haka ya koma cikin sashen zuciyar fas da ita.

**********************************

Masarautar Waisu koda Sarki Haishir ya koma gida ba karamin ta'ajjabi ya shiga ba ganin Sarki Baidulƙais ya amshi addinin musulunci duk yanda yake tsanar shi yau gashi ya karbi addinin musulunci gaskia ya zama dole su dakilar da Sarki Baidulƙais tunda wuri tunkan daular musulunci tai karfi a cikin Masarautar Raifasu, da haka yaita sake sake sannan ya kira Sarkin Yaki yace. "Akashe sati biyu ana hada gangamin Yaki dan darkake Sarki Baidulƙais da tawagar shi baki dayan ta
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Bayan kwana bakwai, Bahijja ce takoma bakin aikin ta kamar yanda tasaba, yau dinma ba wani aikine zatayi ba, sai yan goge gogen da ba arasa ba, tana cikin goge center table Saifulislam ya shigo shida Jakadiyar shi dukawa tayi ta gaida su cikin kulawa suka amsa ta, Jakadiya ce ta tambaye ta karfin jikin ta, a kunyace tace da sauki, dan bakaramin kunyar su da nauyi su takeji ba, hatta Malik wasan boya take da shi duk da yasan kunyar shi takeji sai dai yace kunya mirinɗa bazaiso ta takura kanta ba, Jakadiya ce taima MalikusSaif magana, ba da daɗewa ba ya fito sai farin ciki yakeyi rungume mahaifin nashi yayi suka gaisa cikin so da kauna, Bahijja ce taba su waje dan ganawa da junan su, saidai taki yarda su hada ido da Yarima Malik din, haka ta fita waje dan mike kafarta, Saifulislam ne ya kalli MalikusSaif cikin kulawa yace. "Yarima nafahimci kafara maida iyayen ka abokan wasan ka, ko?" cikin nutsuwa yace. "Abbuh kayi hakuri zaka sameni mai maku biyayya zan fidda."
"daka ta Yarima bawai fiddawar ka muke buka ta ba bansan karamar magana dan haka nan da kwana ukku kafin Matawalle ya dawo ka tabbata kasan abinyi ina fatan ka fahimta."
"toh Abbuh insha Allah bazan baka kunya ba." "Allah yaimaka albarka, ina Bahijjar ta tafi ne?" sunkuyar da kanshi yayi yace. "Inaga tafita da kashigo." "shikenan bari inje inada bakin da zan gani."
"sai anjima." haka suka tafi.
itako Bahijja tana ta yawan ta taji wata baiwa tace mata gimbiya Zahara'u na kiran ta, batace komai ba ta maye mata baya suka tafi sai dai ta rasa dalilin da yasa gimbiya Zahara'u zata kirata, suna isa ta isketa kishin giɗe bisa wata kujera sai cika take tana batsawa wani matsiyacin kallo ne ta watsama Bahijja dukawa tayi ta gaida ta, karkada kafarta tayi cikin gadara gimbiya Zahara'u tace.


"Ke baiwa wai mike tsakanin ki da Yarima na?" da sauri Bahijja ta kalleta tace. "Bangane ba wakenan?" tagama maganar tana watsama ta wani mugun kallo wanda batama san tanayin shi ba, bakaramin baci ran gimbiya Zahara'u yayi ba ganin wulakantaccen kallan da Bahijja ke aika mata amatsayin ta na baiwa, rai bace ta mike ta wanke Bahijja da gigitaccen mari cikin fushi tace. "Ke harkin isa kicemani baki gane ba, Yariman ne zakice baki gane ba kin gane mani matsiyaciyar yarinya." batace mata komai ba dan takaici sai dai dafe kuncin ta da tayi, cikin isa tace. "Badake nikeba.?" a dakile Bahijja tace. "Bansan inda yake ba nima." cikin bacin rai takira wata baiwar ta tasa ta dukan Bahijja, haka taita zab gama mata bulala itako cewa tayi batasan inda yake, jin bugun yafara wuce gona da iri yasa Bahijja rike bulalar da baiwar ke dukan ta ita tace.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*



Episode 73&74




"Kar ki kuma buguna! minayi maki da zaki dakeni!." mikewa gimbiya Zahara'u tayi da niyar faskama Bahijja da sauri ta duke ta bugi iska, rai ɓace gimbiya Zahara'u tace. "Kina hauka ne har kin isa ni gimbiya Zahara'u insa adukeki ki rike bulala wanene ubanki a cikin wannan Masarautar da har zan saka abu ke ki hana!" wani irin takaici ne yagama rufe Bahijja, tace
"Ubana ba kowa bane face mutumin kirki mai wadatar zuci dan haka duk abinda zakimin kada ki kara saka iyayena, kuma daga yau kijini da kyau baki da iko ko izinin cin zarafi na tunda ba'akalkashin ikon ki nike ba!" wani wawan mari ta kaima Bahijja aiko ta rike mata hannu tace. "Kul na haneki kada ki kuskura kiyi gigin mari na." maganar Huzaifa ne ya katse su, isowa yayi wajen ya naima Zahara'u wani irin kallo sannan ya kalli Bahijja yace.
"Wuce ki koma bakin aikin ki karki damu kiyi hakuri."
"Ya Huzaifa yanzun baiwar zaka dinga ba hakuri wannan matsiya ciyar yarinyar?" wani mugun kallo ya watsa mata cikin fada yace.
Eh baiwar naji bakisan matsayin taba shiyasa kike fadin hakan nan gaba kadan zaki sani, kuma kike maganar baiwa ce, ki rike wannan a ranki Bayima fa 'Yayane! na haneki da zalinci."

Itadai Bahijja tafiya tayi tanajin tsanar Zahara'u a cikin zuciyar ta, musamman da take neman wulakan ta mata mahaifi, tana fita yace. "Wlh kika sake wulakanta yarinyar rankine zai mugun baci kinaji na.?" turo baki tayi a tsiwace tace. "Haba Ya Huzaifa taya zanki wulakan ta wannan matsiya ciyar yarinyar, baka ganin yanda take shigema Yarima na, taya zan bari wata mace na raɓar shi.!" kallan kinban tausayi yaima gimbiya Zahara'u yace. "Baiwar shi face,kuma kinsan matsayin ta a gareshi?."


"Ya Huzaifa kenan minene matsayin ta a wajen shi inba like mashi da takeyi ba dan tana son shi munafuka da ita."
Murmushi Huzaifa yayi yace.
"Kincan ka dai dai Zahara'u saidai kisani Yarima Malik shike son Bahijja kuma ta cancan ta ya sota, dan haka ki kiyaye gaba."


Dafe kirji tayi tana kallan yayan nata cikeda tashin hankali tace. "Yake sonta fa kace.?"
Jinjina kai yayi alamun tabbatar mata da hakan yace. "Kwarai kuwa kingani kanwata kibar wannan maganar kedai kisan abinda kikeyi kibar wahalar dakan ki."


Faɗawa tayi bisa kushion tafara kuka, duk abinda su Huzaifa ke cewa gimbiya Salsabila najin su, ita kanta jikin ta yai masifar sanyi rike Zahara'u tayi tace. "kidaina kuka Zahra, wannan zancen banza ne taya za'ai ace wai MalikuSaif zai so baiwa maganar banza maganar wofi, ni nasan abin yi."
cikin kuka tace. "Haba Umma, taya zan samu sukuni, ace yarinyar nan tagayaman magana, itafa baiwa ce inda bai son ta, harta isa ta gaya mani wannan maganar Umma? Kinjifa abinda Ya Huzaifa yake cewa." wani irin bakin cikine yakara turnike ta, tace. "Kibar wannan kukan kada kisama kanki damuwa, yau zanje insamu mahaifiyar shi." haka taitaba gimbiya Zahara'u hakuri.


Koda Bahijja ta shiga cikin sashen Yarima Malik zama tayi bisa wani step ta fara kuka bakadan abinda gimbiya Zahara'u ta gaya mata ba yake cimata tuwo a kwarya, a ranta kuwa cewa tayi "wlh blh sainayi maganin wannan matar saina dauki mataki akanta, harta isa ta dinga wulakan tani, da take tambaya ta Ya Malik ni yar aiken tace!"

Shiko Malik harde hannu yayi yana kallan ta, cikeda mamaki ganin tana kwalla tana magana kamar zautatta, cikeda kulawa yace "lafiyar ki kike kuka kina magana?" kame kame tafara tace. "Bakomai kaina kemin zugi amman ya saki." cewa yayi "sannu Allah yasauwa ke, shine ke daga Abbuh ya shigo zaki gudu ko, kinbar Yayan ki da yunwa ko?" sosa keya tafara tace. "Am ina daga waje, ba guduwa naiba." "shikenan tunda haka kika fada." komawa yayi saman kujera ya zauna ita kuma ta tafi kitchen dan kawo mashi abinci.

************************************

Sarki Muhammad ne zaune a cikin falorn shi shida Jakadiyar shi suna tattaunawa akan matsalolin su da suka taso masu, Sarki Muhammad ne yace. "Aisha ya kike ganin zamuyi da wannan matsalar dan gaskia abin nan yana damu na." dan murmushi tayi cikin kulawa tace. "Haba shugaba na wanda yake da Allah ai bashi ba tsoro ko shakkar wani abu, dan haka kadaina damun kanka Allah yana tareda al'amuran mu." gyada kanshi yayi yace. "Hakane Aisha, gaskia saidai duk da haka sai munkara duba lamarin nan."

Sallamar da Tasi'u da yayi ce ta katse masu maganar su, samun waje yayi ya zauna ya gaishe su cikeda girmamawa, Sarki Muhammad ne yace. "Tasi'u kaji abinda ya faru yanzun minene masalaha a cikin wannan lamarin.?"


"Eh hakane ya shugaba na saidai akwai wata masalaha da nike ganin zata fishemu." cikin zumudi Sarki Muhammad yace "wace masalaha ce wannan.?" "zamu rubuta wasika zuwa ga Kadimulislam munasar mashi mun karbi addinin islama sannan muna fuskantar barazana daga wajajen abokan gaba, ya sama mana mafita, a kalkashin wannan addinin da muke ciki mai tarin alfarma sai dai kada mu sake sakon namu ya sauka ta hannun wani ba ta Saifulislam ba."

Jinjina kai yayi alamun gamsuwa a lamarin, dan ya gamsu da shawarar da Tasi'u ya bada, murmushin girma Sarki Muhammad yayi sannan yace. "Kwarai kuwa dadin shawara da mutane masu ilimi samun haske da annuri a cikin lamari, dan haka za'a sa Magatakar da ya rubuta wannan wasikar, sannan kuma inaga daku za'ai wannan tafiyar Tasi'u." da sauri ya kalli shugaban nasu yace. "Damu fa kace.?" "kwarai kuwa musamman ma kai, kaga wannan Masarautar taku ce kamar gidane zaka koma, dan haka idan kukaje ba za'asamu matsalar komai takardar mu zataje hannun Saifulislam ba tareda ansamu miskila ba, ke kuma Aisha, za'aje da kene dan ki kara yima Saifulislam gamsasshen bayanin da zai fahimta dan susan muma mun tuba mun zama 'yan tattu kuma 'yaya garesu."


Baki dayan su sun gamsu da zancen shugaban nasu, haka suka yanke shawara sati mai kamawa zasu tafi Masarautar Daborah, wanda Tasi'u kejin dadi zaiga dangin shi daya kwashe sama da shekaru goma bai kara ganin suba

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Daborah kuwa Sarauniya Zulaiƙa ce da gimbiya Salsabila ta kwashe komai ta gaya mata abinda ke faruwa tsakanin Bahijja da Yarima Malik da badakalar da ta wakana tsakanin Bahijja da gimbiya Zahara'u, wata uwar zuface ke dawainiya da Sarauniya Zulaiƙa harbata ganin gaban ta zuciyar ke duka da sauri da sauri jirine ya dibeta da sauri gimbiya Salsabila ta tarota jikin ta, daidai nan Saifulislam ya shigo sashen da sauri ya iso ganin Sarauniya Zulaiƙa a sume, ruwa suka dinga shafa mata, wani irin numfashi ne tadawo dashi mai rikitarwa sannan ta fashe da wani irin malalacin kuka, shi kanshi Saifulislam ya tsora ta dan ba karamin abu bane kesaka Zulaiƙa kwalla ba a tsorace yace. "Umman Huzaifa miya samu Ummu Malik.?" kame kame tafara a darare tace. "tasamu labarin Yarima Malik na soyayya da Bahijja kuma....."kuma me? Ke waya gayamaki? Kin tabbatar.?" duk lokaci guda yake jeromata wannan tambayar saidai takasa bashi amsa tsabar kwarjini da yake mata,ganin kallan tsanr dayake watsa mata ba shiri ta bar wajen ta tafi gida a kunyace, tallabo Zulaiƙa yayi wanda takasa furta ko uffan saidai kwallan dake dawainiya da ita, tana girgiza kai alamun Aaa, saman gado yakaita ya dnga lallashin ta, Yarima Malik ne ya shigo sashen saidai jin kamar shasshekar kuka yasa shi banka dakin ya shiga, wani irin tsoro ne yakama shi ganin yanda mahaifiyar shi ke kuka, da sauri ya karaso yakai hannu zai kamata, Sarauniya Zulaiƙa ta nunashi da yatsa da kaga fuskarta tabbas kasan tana cikin tashin hankali bayya nanne saidai takasa magana, ganin yanda take ta nuna Malik da hannu hakan yasa Saifulislam, yace. "Abdulmalik wuce kabar dakin nan, kasame ni sashena da daddare, ina san magana dakai mai mahimmanci." gyada kai yyi alamun toh, shima kwallan ya goge ya fita, yana mamakin dalilin da yasa Ummun shi ke kuka har haka.


Koda YarimaMalik ya koma sashen shi zama yayi kasa bisa kafat ya hade kai da guiwa yana kwalla Bahijja ce ta shigo cikin falon ta gaida MalikusSaif saidai bai amsa taba, hakan yasa ta wuce ciki domin yin aikin ta tasan yana cikin tashin hankali mai yawa, saidai duk aikin da takeyi hankalin ta na wajen Yarima Malik, tana gama gyara dakin ta, taji sallamar gimbiya Zahara'u a sirace ta aje aikin ta fito cikin wani corridor sai dai ta amsa sallamar a takaice, zama gimbiya Zahara'u tayi saman kujera tace. "Yarimana mike damunka har haka, dan Allah kadaina damuwa inkana cikin damuwa ina shiga cikin mawuyacin hali." shiko MalikusSaif ko kallan ta bayi ba, da sauri Bahijja ta koma kitchen tamanta da kayan marmarin da MalikusSaif yace ta kawo mashi, hankalin ta yai masifar tashi ganin Malik cikin wani hali.

Cigaba dacewa tayi. "Dan Allah masoyina kaimin magana wlh inason ka ina kaunarka Yarima na tunbansan kaina ba nike kaunarka kaima nasan kana sona." dagowa yayi da jajayen idanun shi kamar garwashi ya watsa mata wani irin mugun kallo mai cikeda tsana yace. "Ke fitarmin daga gida, tashi kibani waje." dukawa kasa gimbiya Zahara'u tayi tace. "Dan Allah Yarima na wlh bazan iya rayuwa ba muddin kace baka sona ina sonka ina son ka." ya bude baki zaiyi magana kenan sukaji karar faranti kasa, Bahijja ce tasaki farantin kayan marmari jikin sai kyarma yakeyi bata san ta saki wani irin kuka ba, shi kanshi mamaki yakeyi miyasa Bahijja kuka har haka, itako gimbiya Zahara'u cikin ɓacin rai tace. "Ke dan uwarki miyakawo ki nan masoya na magana zakiso ki fasa mana kunnuwa da kara wai ke waye ubanki dami kike takama dashi ne eyeh.?"


Shiko MalikusSaif ran shine yasake baci jin yanda gimbiya Zahara'u take wulakanta Bahijja, juyowa yayi da niyar wanke ta da mari sai ya tuna tarayyar dake tsakanin shi da Huzaifa cikin tsananin bacin rai yace.
"Ba kowa bace face baiwar Allah mai kamala, nutsuwa, kamun kai, dan haka karki kuskura kisake zagin Bahijja musamman a gaban idona!"
ya ida maganar ta kakkausar murya.
"yayi Yarima dole kace haka akan wannan shegiyar kuma wlh kai nikeso kuma kai zan aure saina illata wannan matsiyaciyar kasa a ranka ni matarka kace.?" wani irin abune ya dira cikin kunnuwan Bahijja jin kalaman da Zahara'u ke fada da gudu ta fita ta baya tana kuka mai sosa rai, shiko MalikusSaif da ido yabi Bahijja yasan ko wannan wulakancin da Zahara'u ke mata dole tayi kuka, bai kuma cewa gimbiya Zahara'u komai ba dan kanshi yafara sara mashi, itako ganin yaki magana, yasa ta kwashi kafarta tana kuka ta fita, abakin kofa ta hadu da Huzaifa yana kallan abinda ke faruwa, raɓashi tayi ta wuce tana watsama shi wani mugun kallo, shigowa yayi yace.
"Kaga abinda ke faruwa ko Yarima sai dai ina baka hakuri akan abinda Zahara'u taimaka Malik." cikin karfin hali Yarima Malik ya dafa kafadar abokin nashi yace. "Wannan ba damuwa bane Huzaifa ai Zahara'u kanwata ce kuma naimata uzuri sai dai ina cikin mawuyacin hali abokina Ummu bata magana saidai zubar hawaye kawai takeyi."


"Kayi hakuri abokina insha Allah zamuji abinda ke damunta kadaina damun kanka." gyada kai yayi alamun toh, sannan Huzaifa yace. "Kaga naga Bahijja na cikin tashin hankali ka tuntubi damuwar ta nasan abinda Zahara'u ne taimata amman ka bata hakuri." sake rausayar dakai yayi, shiko Huzaifa a cikin zuciyar shi cewa yayi, lallai wannan lamarin akwai ban tsoro Bahijja ta afka cikin son Malik, hakama Zahara'u, uwa uba Umma taje tayi subul da baka taga yama Ummu Yarima Malik nason Bahijja gaskia akwai matsala, ni nacema Zahara'u hakane dan ta cire Yarima Malik a cikin zuciyar ta, ashe na tabka babban kuskure inalillahi wainna ilahir rajiun, dafa shi Malik yayi yace. "Lafiya Huzaifa?" "Bakomai sai anjima zandawo."fita yayi shi kuma Malik bin hanyar da yaga Bahijja tabi yayi abin mamaki bata cikin gidan fita yayi ta baya, can ya hango Bahijja ta game kai da guiwa tanata kuka mai sosa zuciya, zama yayi saman wata kujera ta silba, ita kuma tana kasan green carpet din ciyawar dake kwance a cikin lambun yayi kore shar dashi gwanin ban shi'awa, maida hankali yayi kanta yace.......





_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم




_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*


Episode 75&76



"Bahijja kuka kuma? mike damunki kiketa kuka har haka?" jitayi numfashin ta ya tsaya na wucin gadi, a hankali ta ɗago rinannun idanun ta ta kalle shi, sai dai tabbas kasan yana cikin yanayi, cewa tayi.
"Ya Malik mi wannan take zuwa tanayi wajen ka.?" jin tambayar Bahijja yayi banbarakwai, baice komai ba, sake cewa tayi. "Natsane ta Ya Malik bata kauna ta kullin burin ta taciman mutunci.!"
sai alokacin MalikusSaif yace. "Kibar damuwa ai kanta taimawa."
"Ya Malik." kallan ta yayi alamun ina sauraranki tace. "Kana sonta kuma itace zaka aura?" samun kanshi yayi da murmusawa, itako aran ta cewa tayi, wato har murmushin jin dadi kakeyi saboda son da kake mata, ashe haka so yake na kamu da son uban gidana a matsayina na baiwa, na shiga ukku ni Bahijja wace irin kaddara ce wannan ya zanyi?
jitayi yace. "Akwai yanda zakiyi kanwar Malik." wani irin daram gaban ta ya buga lokaci ɗaya, tamke fuska yayi yace. "Kin kamu da son Huzaifa ko? Ai daman nasan shi zaki so bani b.....maganar da tayi ce ta katse mashi zancen da yake yi, da sauri tace. "Aaa Ya Malik ba haka bane, tun ina yar kankanuwa ta ka koyamin abu mai mahimmanci a cikin zuciya na sabo dakai har bayan nabar Masarauta ta na kanyi kuka a duk lokacin da natuna da asalina dakai Ya Malik, tun ina jinjirata ka tseratar dani daga halaka, anso aketamin haddi kazama jigo agareni ka tseratar dani, anso akwace ni amai dani inda ba'asan daraja taba, inda addini na da mutunci na ke barazana da rayuwa ta,amman ka fito ka yaki makiya akan darajar baiwa, kai ka tabbatar min cewa bayima 'ya'yane kuma mutane ne masu daraja! Ya Malik kaine ka shayar dani ruwa mai daɗi lokacin da nikejin kishi mafi muni! Ya Malik kaine kafara ciyar dani abinci mafi daraja, sannan ka nunamin matsayina da daraja ta, ta 'ya mace, wadda akaima wadan nan alkhairan minene laifin ta dan ta afka cikin wani rami wanda ba wanda zai iya fiddo ta, sai wani mutun mafi daraja agareta, wanda ya zama fitila agreta, minene laifina dan na zubda kwallah ga wanda baisan ganin nawa kwallan! Minene laifin Bahijja dan tace Ya Malik dinta take so.!?"
wani irin mummunar faduwar gaba yaji ta ratsa shi duk da ya daɗe cikin kogin kaunar Bahijja sai dai yana fargabar hatsarin da zasu afka a ciki! Murmushi tayi mai ciwo taci gaba da cewa. "Tabbas Ya Malik kanai mani kallan sakarai mahaukaciya wadda batasan abinda take ba ko? a matsayina na baiwa marar 'yanci zan kalli mutun mai daraja kamar ka Yariman Daborah ince shi nike so, lallai ni kaina da kaina na kira da kaina mahaukaciya! Ya Malik ban san so ba, bansan abinda ake kira so ba, amman Bahijja na sonka, Ya Malik ina sonka, duk da nasan bazan taba kasancewa dakai ba sai dai kasani ni Bahijja kaine amintacce na akoda yaushe kazamo mani fitila mai haska mani gaba na Ya Malik!"

Jiyayi zuciyar shi tagama karaya tabbas yana son Bahijja so na hakika, wanda tun tana yar fitsitsiyar ta yake son ta, har xuciyar shi ta gazgata mashi hakan sai dai baiji zai furta kalmar so ga Bahijja kodan mahaifiyar shi, cewa yayi.
"Kanwar Malik kidaina kuka, kin san mahimmacin dana baki a rayuwa ta? kinsan yanda zuciya ta ke zafi duk sanda naga saukar kwallan ki, a bisa kyakkyawar fuskar ki? kukan ki na daga mani hankali kanwata keta musamman ce a cikin zuciya ta, ni nakine Bahijja ke ta Ya Malik din ce, kibar damuwa akan wannan lamarin ina tareda ke kanwata."
wasu hawayen ne suka sake wanke mata fuska a dasisashar murya ta sake kallan shi tace. "Hakane Ya Malik sai dai naga tsantsar kina a idanun ka, nasan baka sona, Zahara'u kake so, tabbas kunfi dacewa da juna tunda ita 'yar mai mulki ce kamar kai, Bahijja kuma baiwa ce dan haka baiwa sai bawa, na fahimta Ya Malik kullin bazan gajiba wajen yimaka hidima ba saboda kai alkhairi ne arayuwa ta kuma bazan taba manta halascin da kaimin ba Ya Malik.!"
goge zazzafan kwallan da suke shatata bisa kuncin ta tayi, sannan ta tashi da gudu ta fada cikin sashen shi sannan ta fita ta tafi gida.

Malik kuwa ko motsi yaka sayi yana mamakin yanda akai Bahijja itama takeyi mashi irin wannan son,da yake tunanin bakai kwatankwacin wanda yake mata ba, lallai Allah shi ne ya haɗa jinin su har haka tun batasan wace itaba, shima tun tana karamar ta, cikin zanin goyo Allah yadasa mashi so da kaunar Bahijja ashe sonta ne yai mashi illah harya ɗauka tausayin ta yake, da kyal yaja kafar shi ya koma cikin sashen nashi dakin shi ya shiga, wani bangare na zuciyar shi kuwa Ummun shi ce yake tunani, dan baisan halin da take ciki ba a halin yanzun.

*************************************

Masarautar Waisu, Sarki Haishir ne zaune bisa karagar mulki, suna ta shawarar yanda zasu dirkake daular Masarautar Raifasu, gani sukayi wani irin guguwa ta turnike cikin fa'dar baka ganin komai sai kura ko na kusa dakai baka gani kurar takai tsawan mintuna goma kafin talafa, kowa ido yai nauyi bayan kamar mintuna biyar suka fara ganin gaban su, a firgice kowa ya zabura zai gudu dan tsoron halittar da suka gani, aljani dan tsitu ne tsaye tsakiyar fa'da, cikin wata irin murya ya fara cewa.
"Kai Haishir sako daga shugaban Gamki yace insanar daku kuyi mashi mubaya'a dan dirkake Masarautar Raifasu da duk abinda ke hannun su, basu tareda mu, sannan sun barranta daga abinda muke bautamawa!"
wani irin daɗi Haishir yaji ganin Sarrilƙus ya dawo cikin Masarautar su, duk da yanajin tsoro cewa yayi. "Mun aminta da wannan kudurin naku, muma zaman da mukeyi kenan taya zamu bullowa wannan lamarin na Baidulƙais ashe faduwa tazo dai dai da zama." dariya yaita shekawa mai hhhhhhuuhhh, ya bace har zasu gudu Haishir yace.
"Kutsaya ai mun samu

Please Login or Register in order to submit comment