Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sakannin da yake ɓatawa gani yake kara rura mashi so da kaunar Bahijja akeyi a cikin zuciyar shi har lamarin ya fara bashi tsoro, haka ya wuni ko waje bai fitowa saidai in sallah zaiyi yana dakin shi kuma ya hana kowa ya shigo sashen nashi dan yana bukatar kebewa ahi kadai.

Koda Mairo ta shigo kiran Bahijja tayi wadda ta buga uban tagumi da kaganta kasan tana cikin mawuyacin hali, kiran da Mairo ke mata ko kadan bataji taba, saida ta karaso ciki sannan ta taɓata a firgice ta kalleta, tana goge kwallan idanun ta, cikin sarkewar murya tace.
"Inna barka da safiya." kallan tsaf taimata sannan tace.
"Lfy lau Bahijja, sai yaushe zakibar damuwar nan a ranki, kiyi addu'a amman kuka ba naki bane kuma ki rike matsayin ki, 'yata, tashi muje Kangiwa na neman ki." da sauri Bahijja ta dago ta aza rinannun idanun ta kan Mairo take taji tsinkewar da zuciyar keyi yana tsanan ta, kallan tuhuma ta dinga jefama Mairo takasa ko magana, ganin yanayin Bahijja ya tabbatarma da Mairo tsantsar rudanin data shiga hakan yasa tace.
" kibar damuwa 'yata, kisani ba abinda Saifulislam zaimaki tashi muje." ɗagota tayi suka tafi har cikin sashen Kangiwa, suna isa ta duka har kasa tagaida Kangiwa ta dukar da kanta ƙasa tana maijin faduwar gaba da sauri da sauri, cikin kulawa Mairo tace.
"Ranka shidade ga Bahijja nan." kallan ta yayi yace. "Kinkyauta zaki iya tafiya."


Maida kallan shi yayi kan Bahijja yace.
"Bahijja miyasa kika daina zuwa aiki sashen Abdulmalik.?" sake sunkuyar da kanta tayi shiko nazarin ta yayi, tabbas yasan Bahijja tanada kamun kai, ga sanin ya kamata shiyasa yake sonta, cewa tayi. "Allah yakara girma da daukaka, ba abinda yahanani zuwa, banjin dadine."
cikin tausayawa yace. kici gaba da zuwa kuma kiyi hakuri akan duk abinda zaki gani keda iyayen ki Allah na tare daku, dauki wannan kwaryar furar ki kaima shi nasan baici komai ba." jitayi jikinta yafara rawa, tuna jan kunnen da Sarauniya Zulaiƙa taimata, saidai bazata iya yima Saifulislam gardama tashi tayi ta dauko kokon furar, sannan tace.
"Nagode katashi lfy, Allah yakara daukaka." da ameen ya amsa yana karajin so da kaunar Bahijja na yawo a kowane sashe na jikin shi jinta yake kamar 'yar cikin shi, tana fita takama hanyar zuwa sashen Yarima, tana isa mai kula da kofar yace, bai bada izinin kowa ya ganshi ba, cikeda mamaki tace.
"Wajen aikina nazo kuma wannan umurnine daga Kadimulislam." yanda yaga ba annuri asaman fuskar Bahijja dole yabata hanya, musamman da yaji wanda ya aikota, haka ta shige samun shi tayi cikin wasu lemon green din yadi kiran na kasar Maroco yasha aiki na Sarauta da yar gajerar alqabba milk mai sirkin golden ga hula yasa mai dan karan kyau wadda takara fiddo mashi tsantsar kyau da kamalar shi, sai wani fitinanna kamshi mai sanyaya zuciya ke tashi, kanshi yadan kwantar bisa kujerar sannan ya daura kafar shi bisa center table, yana kaɗa kafar shi amman idanun shi a rufe suke alamun mai bacci da ka ganshi kasan ba baccin yake yiba, tunani ne dayagama addabar shi, ido ta zuba mashi yanda yai mata kyau saidai ya rame idanun shi harsun dan fada ga wani irin haske da yakara yi, jin kamar mutun akan shi yasa shi fara motsa kwayar idanun shi tangaram ya sauke su saman kyakkyawar fuskar Bahijja, wani irin dukan tara tara yaji kirjin shi nayi da sauri da sauri, itama hakan take a wajen ta, dan ɗaure fuska tayi ta duka ta gaida shi sannan tace. "Barka d safiya, ga sako inji ami girma Kangiwa yace inkawo maka, furace damamma." shidai baice komai ba sai kafeta da idanun shi masu rikitar da ita yayi, yana kallan ta kamar wata bakuwa haka ta koma mashi, saita kara mashi kwarjini sannan takara mashi kyau sosai, saidai tadan yi duhu kadan da kaganta kasan tana cikin damuwa a cikin ranta, dagowa tayi ta kalleshi still ita yake kallo, da sauri ta dauke kallan ta gareshi a ranta ko cewa tayi.
"Kaida kace baka sona akanmi zaka damu dani, nima ina rokon Allah ya dasa mani tsanarka araina kona huta da azaba kodan iyayena.!" jitayi wasu kwalla masu zafi naneman kubce mata tai sauri ta mai dasu, cewa tayi.
"Zantafi yace kasha wannan furar kada yunwa taimaka illah." tana gama fadar haka ta mike zata tafi kamar daga sama taji yace....

A wajen gimbiya Zahara'u kuwa wata baiwa ce takaimata rahoto taga Bahijja da kwaryar fura zata kaima Malik, kuma tana kyautata zatan akwai mugun abinda ta zuba a cikin dan yasha ta malleke shi, ai bata jira ta ida maganar ba ta dauki alqabba ta zira sai sashen Yarima Malik

Cikin sanyin murya da yanayin da baisan yayi maganar ba yace. "Kanwar Malik miyasa zaki tafi ki barni kodai kindai na son yayan naki ne bayan kinsan ni mai kau...jin saukar mari yasa sauran zancen MalikusSaif ya tsaya bisa bakin shi, gimbiya Zahara'u ce ta wanke Bahijja da mari, cikin bacin rai, tace.
"Ke baiwa yar bayi 'yar matsiyata bance kifita harkar Yarima na ba, miyasa ke mayyace harkin isa kiso wanda kema kinsan yafiki daraja kina baiwa yar gadon bauta inake ina son Yarima na wlh sai....jitayi an ɗauke ta da wani irin mummunan mari, MalikusSaif ne ke nunata da yatsa, itako Bahijja mamakin karfin hali irin na Zahara'u yahana ta magana bare tai motsin kirki tasan gimbiya Zahara'u tagama raina ta koda take ikirarin ita baiwa ce, ammn tafi karfin wulakanci, maganar da Yarima Malik keyi shine ya tsaida mata tunanin da takeyi, cewa yayi.
"Ke wace irin daƙiƙiya ce!? miyasa kika gaza gane cewa ni MalikusSaif baisan ki ban kaunar ki, sai yaushe zakiyi zuciya ne kirabu dani? natsaneki Zahara'u kuma bansan ki, kinsan fuskar wa kika mara kuwa? Kinsan dinbin darajar ta da kimar ta da kuma martabar ta a wajena, ko kuwa kinsan mahimmancin ta, a wajena? Wannan fuskar da kike wulakan tawa tafimin komai a gareni, kuma jigoce a wajena haske ce kuma tauraro ce mai haskeke rayuwa ta, kuma ita ke haska cikin birnin zuciya ta, dan haka kijini da kyau Zahara'u, Bahijja itace farin cikina kuma ita nikeso kuma ita zan aura itace uwar 'yayane, dan haka kifita a cikin rayuwata Zahara'u natsaneki!" itako Zahara'u ta rike kirji da takeji tamkar zuciyar ta zata kubto ta fado kasa, dan fargaba, itako Bahijja tabbas taji dadi yanda har Yarima kamar Malik ya bayyana darajar ta agaban Zahara'u saidai bataji zata iya tarayya da Malik kodan kimarta, jitayi yace. "Bahijjaaah!"yanda yaja sunan ya kirarshi da kakkausar murya tabbas tasan ba wasa hakan yasa ta kalleshi sannan tace "Na'am Ya Malik." sake cewa yayi. "Bahijja inasan ki sanarwa Zahara'u wayeni a wajen ki.!" yanda yakafeta da idanin shi saitaji yakara mata kwarjini, sannan bataji zata iya badashi a gaban gimbiya Zahara'u kodan yanda take wulakantata akan Malik cikin dakewa tace. "Tabbas duniya ta shaida an halicci Bahijja dan MalikusSaif dan haka Ya Malik masoyina ne kuma uban 'yayana da izinin Allah inason Ya Malik so na hakika kamar yanda kikaji yana sona, Bahijja batayin son maso wani koshin wahala, koda nike baiwa, inaso ana sona, kinga ko Bahijja tafi karfin wulakanci da kaskanci, tunda tafi mai yanci komai da tarin so da kauna a wajen mutun mai daraja, kinga kenan baiwa tafi yar masu daraja, tunda ta taka inda ke baki isa ki takaba, dan haka kidawo cikin hayyacin ki Zahara'u MalikusSaif na Bahijja kuma shine zabina." buga hannun ta tayi saman table tace. "Karyane yar matsiya ta, wlh Malik nawane kuma shine mijina, kisa aranki saina watsa sihirin da kikaima shi yar wulakantattu baiwa yar gadon bauta, wadda tsiya ta kare kanku, yar matsaya t......."Ke!!! karda ki kuskura wannan kaskantaccen harshen naki ya sake aibta iyayena inba hakanan ba saina datse wannan tsinanan harshen naki wanda baisan darajar iyaye ba, ni zan iya komai akan iyayena inafatan kin fahimta?"

Zatayi magana Yarim Malik yace.
"Kikiyaye dan haka ɓaceman dagani karki saman ciwon kai." da sauri Zahara'u ta duka tace.
"Yarima karkamin haka kafadama ta nice zabinka kadawo cikin hayyacin ka, kai nikeso kaima kace kana sona Yarima na." tabbas baiso takaisu haka da Zahara'u ba saidai yazama dole ya farkar da ita daga nauyayyen baccin da tayi kodan mahaifiyar shi tasan cewa Allah shike haɗa zukatan mutane, dan haka susan kaskantattar da suke ikirari ita yake so kuma ita ya zaba, a kaskance yace.
"Nagama magana kuma bazan ha'inceki ba, koba komai ke yar uwatace dan haka ki tsaya matsayun ki, amman kisa aranki Bahijja nikeso kuma ita nike kauna." tanajin haka ta fita da gudu tana kuka.


_Allah Sarki Zahara'u ai haka abin yake son maso wani koshin wahala, Allah yasa muso masu sonmu dan Allah 🙏_

Kamar jira tana fita Bahijja tasa kai zata fita, baisan ya riko hannun taba da sauri yace. "Bahijja kisani kece gubar da kika dade kina wahalar da zuciyar MalikusSaif, saida taimin illah sannan na farga, yau gashi akanki MalikusSaif da duniya tagama yarda da cewa Jarumine kuma mai nagarta yau gashi ya susuce ya zama raggo ashe ba kowa bangare mutun ke kasancewa ba jajirtattace ba kuma Jarumi, sai gashi a fagen sonki na zama raggo mafi muni nakasa takuba komai akan sonki Bahijja dan Allah kisoni ko rabin son da nike maki ne.!"


Ita kanta sassan jikin ta sun karbi kalaman Malik kuma tana son shi tana kaunar shi, amman a halin yanzun bataji zata iya furta kalmar so a gare shi tayi hakan ne dazun saboda gimbiya Zahara'u, kuma yanzun zata kishine dan daukaka darajar iyayen ta da ake wulakantawa kullin ba dare ba rana wasu kwalla ne suka ziraro mata a hankali ta goge sannan ta fuskanci MalikusSaif tace.
"Kayi hakuri Ya Malik tabbas naso inkasance dakai, saidai a halin yanzun kasani ba sonka a cikin zuciyar Bahijja na hakura dakai kaje ka cika burin mahaifiyar ka, nima incika burin nawa iyayen ko sun huta da ukubar da suke fuskanta, dan haka Ya Malik ka fidda Bahijja a cikin zuciyar ka, sannan kamanta da rayuwar Bahijja, dan a halin yanzun Bahijja bata sonka.!"
wani daram yaji a cikin zuciyar shi bakin shi na kyakyarwa yana so yayi magana amman wani kululu ya tokare mashi wuya, itako bata jira cewar shiba ta fita da sassarfa tana share kwallan dake zirarowa a saman fuskar ta masu ɗumi, shiko dabas ya zauna bisa kujera da kyal ya furta kalmar Bahi-jj-aaah...in breaking word yake rabasu jiyayi kanshi yana sarama shi da karfi da karfi, baisan hawaye sun fara sintiri ba saman kyakkyawar fuskar shib mai yalwa da kwarjini uwa uba haiba da kyau da sauri yai.......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*


*kuyi hkr nayi manu resend din na jiya wlh Ina busy ne shiyasa har sae da aka gayaman na kura*

Episode 85&86





Yun kurawa yayi ya mike ya fita daga sashen nashi ba inda ya wuce sai wajen Matawalle akayi sa'a ya iskeshi bisa shimfidar wani tausassan kafat na alfarma ga hadiman shi kewaye dashi sunata yima shi hidima ahankali ya maida duban shi kan Malik yanda yaga damuwa kwance a fuskar shi hakan ba karamin daga hankalin Matawalle yai ba, koda ya iso da sallama abakin shi wuri ya samu ya zauna gefen Kawun nashi, yana zama Matawalle yaba hadiman shi umurni dasu basu waje, kowa ya watse bisa umurnin Matawalle, tashi yayi daga kishingidan da yayi sannan ya kalli dan nashi cike da kulawa yace.
"Yarima koban tambaye kaba kana cikin damuwa gayaman damuwar ka ɗana.?" dan rausayar dakai MalikusSaif yayi sannan yace.
"Kawu ina cikin damuwa tabbas, kataimaka mani kaba Ummu umurni tabari in auri Bahijja Kawu zan.....ɗaga mashi hannu yayi rai bace yace. "Miyasa ka nace saika auri baiwa?" cikeda mamaki Malik ya kali Matawalle yace. "Kaima harda kai Kawu.?''

"Kwarai kuwa Yarima wannan wulakanta nasaba ne da martabar wannan Masarautar da watsama tsatson Sarki Abduljabbar kasa a ido, bare a ce a zamanin Sarauniya Yahanasu ne kai wannan katobarar da lamarin bazai dadi, kasan yanda wannan ahalin namu suka tsani bayi musamman tsatson Jafar kuma wannan baiwar dakake ikirari 'yace a cikin zuriar Jafar take kakan Abdulmajid, shi kuma Abdulmajid ai shine mahaifin Bahijja taya hakan zai yuyuwa, dan haka kabar wannan zancen ka shirya gobe iwar haka inje dakai Masarautar Shugaban jagoran musulunci ka zabi mata daga cikin 'yayan ɗiyan kakan ka."

Mamaki yagama rufe Yarima ganin yanda Matawalle ya sauya lokaci guda ya koma bayan mahaifiyar shi,lallai dole yasan abin yi saida bazai iya gardama da Matawalle ba duba da darajar da yake dashi a wajen shi, sake rausayar dakai MalikusSaif yayi yace. "Shikenan Kawu sai dai kasani ba wadda nikeso sai Bahijja ina laifin bawan d aka 'yanta shi dan wata masalaha, ka duba wannan lamarin kudaina daka ta Sarauniya Yahanasu da ra'ayinsu shekaru dari nawa da shuɗewar su yaka mata ace izuwa yanzun mun canza wasu tsare tsaren mubar riko da abinda kaka da kakan ni sukayi akwai cigaba yanzun musamman wajen addini amman Kawu kace zaka biye tsare tsaren wannan Masarautar akwai damu...."kaga Abdulmalik Saifulislam ban tambaye ka wannan zancen ba kuma inkace zaka wulakanta Sarauniya Yahanasu tabbas tamkar kakan ka Abdulhamid ne kai mawa domin kaka ce a wajen mu ka kiyaye, sannan umurni nike baka ka shirya gobe ne zamu tafi inyaso tsakanin Yazid da Huzaifa ko Lurwan kasamu wani yaimaka rakiya mutafi tare zaka iya tafiya."

Cikin girmamawa Yarima Malik ya tashi ya tafi sashen shi yana sake sake dan nemawa kanshi mafita.....


A wajen Bahijja kuwa tana komawa gida ta faɗa bisa tabarmar kabar dakin su tafara rusar kuka kamar ranta zai fita tace.
"Kayi hakuri Ya Malik ban maka adalci ba nazama butulu dana furta kalmar ki ga wanda yaimani rana ya fanshi ni lokacin da rayuwa ke mani barazana ka kwaceni daga makiyana lokacin da mutuncina keneman kubuce mani sannan ka gwadani a cikin dubban jama'a kace ni 'yace yau da bakina na furta wannan kalma gareka Ya Malik, banda wani anfani kayafe mani Yayana.!"


Jitayi ance. "Tabbas ba kunya kikaji ba, koda zaki mutu dolenki ki rabu da Yarima ki tsaya matsayin ki, tunkan duniya taimaka daurin goro ko kuma ni in barranta dake dan haka wajibinki ne ki zabi daya a ciki ko rabuwa damu ko rabuwa da Abdulmalik."

A firgice ta kalli kofa Abdulmajid ne da alama daga wajen aiki ya dawo dan a gajiye yake, ta gefen ta yabi ya wuce yana watsa mata wani mugun kallo, wani makimancin daki ya shiga da alama dakin sane, itako Bahijja game kai da guiwa tayi ta cigaba da kukan ta ahankali tana mai tausayin halin da zata kasance saidai bata da zabi daya wuce tabi umurnin iyayen ta wa'anda suka fuskanci wahala da kalubale a dalilin ta, ganin kukan bazai amfaneta da komai ba hakan yasa ta tashi taje banɗaki sannan tayi alwallah ta kabbara sallah, shima Abdulmajid alwallai yayi jin antada ikima ya tafi masallaci......


Washe gari da safe Matawalle da MalikusSaif suka shirya kamar yanda ya umurce shi, zasuyi tafiya biyawa sukayi ta sahen Sarauniya Zulaiƙa sukayi mata sallama, addu'a tayi musu da fatan dacewa dan tafi so ɗanta yayi aure a cikin ahalin su, haka suka tafi wajen Saifulislam, lokacin hadiman shi nanan waje suka samu suka zauna cikin kulawa Saifulislam yace. "Matawalle da ɗansa sai ina har haka.?"

Sunkuyar da kanshi Yarima Malik yayi yana gaida mahaifin nashi, cikin so da kauna da uba kema danshi ya amsa yana mai jin tausayin ɗan nashi na ratsa shi har kasan zuciyar shi, Matawalle ne yace. "Zamuje wajen Baffan namu dan yagana da jikan nasa, daga nan saiya fidda matar aure." murmushin girma Saifulislam yayi yace. "Hakan yai kyau, kullin alkhairi muke fata, Allah ya tsare hanya agaidaman sa Kawun nawa, Abdulmalik a dawo lfy Allah yatsare." "Ameen Abbuh." da haka sukayi sallama suna fitowa ya hadu da Lurwan shima ya shirya a tare suka isa dawaki, kowa ya hau dawakan su, daman already an gyara masu dawakan nasu, sunsha kayan alfarma da ado kamar zasuyi hawan da'ba, haka suka tafi kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi.

Bayan awa biyar lokacin garin yayi sanyi bakajin komai sai kukan tsuntsaye da suketa shawagi a cikin Masarautar Daborah, da yake Masarautar Allah ya albarkace su da abubuwan kiwo musamman jinsin tsuntsaye iri iri, ba kalar da basu dashi, wannan dalilin yasa ake zuwa kasashe daban daban ana siyan iri, musamman central area suketa yawo suna shawagi a saman ginin wajen dole abin ya burgeka, Sarkin gida ne da wasu mutane daga nesa sun shigo cikin Masarautar hanyar sashen Saifulislam ya nufa dasu, jin ya ambaci sunan Tasi'u suna yar fira a hanya hakan yasa nagane ashe su Jakadiyar Masarautar Raifasu da jama'ar su, shiko Tasi'u sai farin ciki yakeyi ganin shi cikin Masarautar su, wanda raban daya takata harya manta sama da shekara sha biyar kenan, sai kalle kalle yakeyi gani yake kamar ansauya komai na Masarautar komai ya koma mashi sabo, ita Jakadiya Aisha tana mamakin kyau da tsaruwa irin na Masarautar Daborah aranta ko cewa tayi kodan lokacin da mukazo Yaki bamuyi yawo cikin Masarautar nan ba, gaskia taimani kyau, lallai komai a tsare yake, haka suka karasa cikin tankameman sashen Saifulislam mai kyau da tasaruwar sashen ga yaji kaya na alatu musamman na gidan Sarauta haka suka shiga cikin falon shi akai masauki a wajen da baki ke zama sannan Jakadiyar Saifulislam ta je sanar mashi da yayi baki, haka kowa ya zauna ya kwance wannan ya saka wannan a cikin ransu, sanyayyar muryar shi ce mai aminci ta karade kunnuwan su, da sallama ya karaso cikin falon, Sarkin gidane ya duka har kasa cikin girmamawa yace.
"Allah yataimaki Kangiwa Khadimulislam, kayi baki masu mahimmanci daga Masatautar Raifasu, sunce kai kadai sukeson sugani, kallan Sarkin gida yayi yace.
"Ka kyauta Mubarak aikin ka na kyau, zaka iya tafiya, zaunawa yayi bisa kujerar shi ta alfarma sannan ya kalle su cikin mutuntuwa, yana maida duban shi wajen matashin daya duka yana bashi hannu ga mamakin shi, yaga Tasi'u cikin jin dadi yace.
"Tasi'u yau kaine a mahaifa, ashe da rabon rai kanga rai ina su Nulwa.?"sunkuyar dakan shi Tasiu yayi yana mai jin radadin rasa ɗan uwan shi da yayi yace. "Allah yaima Nulwa rasuwa." cikin jimami Saifulislam yace. "Allah yaimashi rahama." baki dayan su suka amsa da Ameen, Tasiu ne yai gyaran murya yace. "Allah yataimaki Kangiwa muna tafe da babban al'amari da farko kaga wannan sunan ta Aisha itace Jakadiya a Masarautar mu, muna tafe da wani kokan bara agareku amman ance waka a bakin mai ita tafi dadi ga sakonan daga Sarkin Raifasu yace kada muba kowa sai kai wannan sakon nakane, Allah yataimaki uban gidana Kadimulislam."

Mika mashi yai ya ansa cike da alhini a cikin zuciyar Saifulislam, yana mamakin dalilin da zaisa Sarki Baidulƙais ya aiko mashi da wasika ba Zulaiƙa ba, budewa yayi yafara karan tawa.....


_Bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci, Assalamu-alaikum waharahamatullahi, wabarakatuhu, daga Sarki Muhammad Raifasu zuwa da Kadimulislam inamai sanar dakai cewa Masarauta ta da al'umma ta mun karɓi addinin islama dan haka munyi mubaya'a a kalkashin tutar musulunci ta hanyar 'yarku Bahijja lallai hudda da mutanen ku ya zama alkhairi agaremu baki, daya fatan zaka anshi kokon barata, saidai akwai kalubale da muke fuskanta a wajen Sarrilƙus muna fatan zaku kawo mana ɗauki cikin gaggawa, bissalam daga Masarautar Raifasu zuwa ga Saifulislam._


Sauke sanyayyar ajiyar zuciya yayi yana mai sauka bisa kujerar da yake, yayi sujuda ya gadema Allah harda kwallan dadi yayi yace "tabbas godiya ta tabbata ga Allah da ya nuna mana wannan lokaci mai dinbin daraja ga al'ummar musulunci tabbas ta hanyar wani wani ke shiryuwa yau gashi Bahijja tazama haske a cikin Raifasu da wannan addinin namu baki ɗaya, inamai jin dadi yanda kuka musulunta yau Sarki Baidulƙais ne ke ansa sunan Sarki Muhammad suna mafi daraja wanda yafi komai tabbas wannan abin alfaharine a garemu, Jakadiya mun anshi kokon bararku, darajar ku a cikin wannan addinin yafi karfin bara domin ku masu darajane, dan haka yanzun yaka mata kuje ku huta, kai kuma Tasiu kaje kaga dangi, bari inkira Hajara tabaki masauki, Mairo kiraman Jakadiya, haka Mairo taje ta kira Jakadiyar Saifulislam tana zuwa ta duka ta gaida shi, cikeda sakin fuska yace.
"Ka kawa kuma Jakadiyar Raifasu kije kibata masauki su huta saidai minene sunan ki baiwar Allah.?" murmushi tayi tana mai jin so da kaunar Saifulislam na ratsata tace. "Aisha sunana." wani irin dadi yaji yace. "Kinsamu suna mai daraja sunan uwar mumunai, Allah yabaki ikon yin koyo da halayen ta." Ameen Jakadiya tace, sannan suka tafi da Hajara har gidan ta dan bata daki domin ta samu ta huta.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A wajen su MalikusSaif kuwa sun shigo cikin babban birnin Gambia inda nanne Masarautar da Kawun Sarauniya Zulaiƙa yake Mulki suna isa cikin Masarautar da ta gaji da kayatuwa iya haduwa ga hadimai da bayi nata gittaya da alama suna aikine kasancewar yau kamar ranar aiki take a wajen su, suna shiga Sarkin gida yafara fadanci ganin su Matawalle har cikin tsakiyar fadar yakai su inda suka shiga wajene dayake tankam da fadawa kama daga Dagaci, Dan biram, Kangiwa Ɗan zagi, Sarkin Yaki, Mai yaki, Magatakarda, Limamin Fa'da, Sarkin Fa'da, Kangiwa, Galadima, Majidadi, Ɗan isa, da dai sauran manyan ƴan Fa'da sai dogarawa na gefen Sarki suna mashi fiffita, koda aka shigo dasu Matawalle Sarki yana ganin su ya saki wani irin kayataccen murmushi mai ɗauke da ma'anoni iri iri Sarkin Fa'da ne yace, barkan ku da zuwa Masarautar Musulunci ta Gambia, angaishe da Matawalle barkanku da zuwa, zama sukayi gefen su, Matawalle ne yace. "Ranka shidade angaishe da Sarkin Musulunci Matawalle na gaisuwa da ɗanka MalikusSaif muna fatan munsameku cikin aminci.?" ɗan zagine yace.
"Takawa ya amsa Matawalle yana gaisheku yanai maku barka da zuwa sannan yasa albarka ga Yarima MalikusSaif, jika ga Sarki Abduljabbar na III, _*Masarautar Runo*_ tanai maku harhaban."
wani murmushi Sarkin Runo ya saki yana mai ɗaga ma Sarkin zagi hannu alamun ya isa cikin kasaita ta Sarakai ya bude baki a hankali yace......





_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 87&88




"Ina mai farin ciki dajin dadin wannan ziyarar da kukawo mani musamman da kazo mani da jikan nawa, mafi soyuwa agreni, lallai kam Abduljabbar dole jinjina maka,domin inka biye ta Zulaiƙa abubuwa sun sha mata kai bazata iya nuna mashi dangi ba, ga Kangiwa ba mazaunin gida bane, ɗana matso kusa da kakan ka, nan Masarautar kuce baka da shamaki da komai Abdulmalik."

SARKI ABU-JALAL kenan shugaba mai adalci da sanin darajar ɗan adam ga kaunar talakawa da kimanta bayi komai kaskancin bawa, bai yarda ya wulakanta shiba dan ainahin tutar musuluncin ta kasar Gambia a cikin Masarautar Runo aka kafata shiyasa Masarautar ta zama ta musulunci, ananne Kangiwa wato Saifulislam ya kara ɗabbaka addinin musulunci a cikin Masarautar Daborah har suka rage riko da addinin kaka da kakanni, shiyasa mutanen Masarautar Daborah da ke wayenta suke mashi inkiya da Kadimulislam...
shiko Sarki Abu-Jalal shine babban ɗan Sarki Abu-Dawud, wanda ya gaji Sarauta daga kakansu Abu-Kawwas na II har zuwa asalin wanda ya kafa tutar musuluncin a cikin Masarautar Runo wato Abu-Jabbar na I shine wa ga kakan su Sarauniya Yahanasu wato Sarki Abduljabbar duk iyayen su ɗaya da Sarki Abu-Jabbar, shiyasa Masarautar Daborah da Masarautar Runo duk daga tsatso ɗaya suke, wannan dalilin yasa duk abinda ABU-JALAL zai aiwatar a cikin Daborah basu iya yimashi musu, domin ubane agare su, wannan

Please Login or Register in order to submit comment