Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu ashe rabuwar mu alkhairy ne a gareni rayuwa kenan, da wannan tunanin Bahijja ta shiga dakin su ta bude wata koɗaɗɗiyar tukunya ta iske dumamen tuwo yanka ukku ta dauki ɗaya ta zuba tafaraci ta ajema iyayen ta sauran, tana ɗauko lomar farko zataci Yarima Malik ya faɗo mata arai murmushi tayi ita kanta tayi mamaki a zahiri ko cewa tayi Allah Sarki Ya Malik kaine kafara ciyar dani abinci cikin aminci ba tareda tsoro ko shakkar wani abu ba, Allah yasaka maka da alkhairi yasa kafi haka, da haka dai Bahijja harta gama cin abincin ta hakanan taji tana cikin farin ciki aranta.....

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Washe gari sa safe Sarki Danwar ne keta shiri zasu koma Masarautar su daga Raifasu saida ya samu ya gama ɗaura Sarki Baidulƙais bisa gadar zare sannan yace zai koma Masarautar shi dan ya huta haka Sarki Baidulƙais yai masu sha tara ta arziki sannan yasa akai masu rakiya suka tafi Masarautar Ƙaisu, shiko Baidulƙais izuwa yanzun baida tunani sai matsalar dake neman kunno mashi kai musamman tsakanin shi da Sarrilƙus baida tunani sai abinda zai faɗama Boka Sarrilƙus a wani sashe na zuciyar shi ko yana bakin cikin rasa hannun shi da yayi yana maijin zafin cin kashin da Yarima Malik yaima shi a cikin dubun nan mutane....


Masarautar Daborah kuwa, Binta keta wankin kayan Sarauniya Zulaiƙa tin safe take abu guda bata kareba sai marece liqis sannan ta nunkosu ta kawoma Sarauniya Zulaiƙa har daki ta aje sannan taci gaba da yimata gyaran dakin ta tana gamawa ta tafi madafa dan ganin abinda uwar tuwo ta girma Sarauniya, ana gamawa tasa bayi suka ɗauko atare suka kaima Sarauniya Zulaiƙa, koda suka aje cikin gadara tasa Binta ta zuba mata abincin tanaci sannan ta ɗaura kafarta kan Binta kamar kullin tanai mata tausa, can Binta taji Sarauniya Zulaiƙa tace. "Ke Binta ina baiwar ƴarki."? Cikin sanyin murya tace. "Ranki shidade nabarota gida." girgiza kai tayi tace.
"kice kango dai koma dai minene inasan kijama ta kunne karta kuskura inga kafarta ta shigo cikin Masarautar nan ta tsya can turakar bayi ina fata kin fahimta."? "To ranki shidade Bahijja nagodiya da karamci, Allah yakara maki girma da lfy." itako Binta tana mamakin lamarin Sarauniya Zulaiƙa yanzun ance mutun da lafiyar shi yaita zama waje ɗaya koda yake aita huta da aikin wahala, ba wanda ya kuma cewa komai saidai kowa da abinda yake sakawa a cikin kokon zuciyar ta ji sukayi ana sanar da zuwan gimbiya Salsabila matar Waziri Dammur Mahaifiyar su Huzaifa, fuska sake Sarauniya Zulaiƙa ta tareta a tare suka zauna itako Binta kanta kasa tagaida ta a wulakance ta amsa, gimbiya Salsabila ce tace "Allah yataimaki Sarauniya ta, nazo intayaki murnar kare wannan kadararren Yakin da aka jazamaki." "hmmm kedai bari Umman Zahara'u ai da kike ganin wannan Yakin ba kadai ya sosa mani rai ba Allah dai ya kyauta gaba." "Ameen ai wannan baiwar da kashin tsiya take wlh."cewar gimbiya Salsabila.
"sosai ma kuwa shiyasa kullin nike neman tsarin Allah kada ta rabeni bare ɗana ko mijina ai yarinyar da kike gani kamar mayya take." da sauri Binta ta kalli Sarauniya Zulaiƙa sannan ta sadda kanta tanaci gaba da danna mata kafarta ga kirjinta nai mata kuna tanaji ana tsinema ƴarta, gimbiya Salsabila ce tace. "Ina ɗana yasha gajiyar Yaki karkiso kiga yanda Zahara'u ta ɗaga hankalin ta da ana Yakin nan sai addu'a take mashi."murmushin jin dadi Sarauniya Zulaiƙa tayi ta fahimci gimbiya Zahara'u tana ji da Yarima Malik cewa tayi. "Allah Sarki ƴata ƴar albarka ai ita da Malik hadin Allah ne, fatadai Allah yakara hada kansu da hankulan su." da Ameen gimbiya Salsabila ta amsa sannan sukaci gaba da firarsu rabi duk akan Yarima Malik sukeyin ta.


➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Dan kuwa Masarautar Waisu akwana atashi har Sarki Lahazu yakai kwana ukku da mutuwa, kuma ba laifi jikin Yarima Haishir yai sauki sosai tinda har yana iya tashi da kanshi ya zauna sai dai tunda ya samu labarin mutuwar mahaifin shi bai kara samun sukuni a cikin zuciyar shi baida buri daya wuce ya ɗauki fansa ga Sarki Baidulƙais dan yafara cire Bahijja a cikin zuciyar shi ya ɗauki dangana damuwar shi, bai wuce Sarki Baidulƙais da Masarautar Raifasu, kullin saiyayi kuka daya inya tuna da mahaifin shi ita kanta gimbiya Ƙamariyya bata hakura ba kullin da irin mugun nufin da take dashi aranta game da gimbiya Yazira acewar ta mijin tane silar rasa mijin ta itama saita ɗauki mataki akan matar shi...wannan kenan.

_Masarautar Daborah_


Shi ko Yarima Malik yana gama shiryawa zaije wajen Yazid dan yanaso ya mike kafar shi su dan zagaya cikin Masarautar Daborah da kewayen ta dan hutawa saiga wata baiwa tazo ta gaida MalikusSaif sannan ta sanar mashi da kiran da Sarauniya Zulaiƙa take mashi a sashen ta, bai wani ɓata lokaci ba yakama hanya ya tafi yana zuwa ya isketa kishingiɗe cikin wata bakar alqabba, bayi nata yimata fiffita amsa mashi sallama sukayi sannan ya zauna kowace baiwa saida ta kawo gaisuwa wajen Yarima sannan suka basu waje cikin kulawa Sarauniya Zulaiƙa ta kalli Yarima Malik tace......




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم




Episode 43&44



"Malik?'' ɗago kyakkyawar fuskar shi yayi mai hade a kwarjini ya kalli mahaifiyar shi cikin nutsuwa yace. "Naam." fuskar ta ɗauke da murmushi tace. "Ya kamata ace zuwa yanzun kayi aure kazama cikakken mutun kamar kowa kaduba kaga kullin kara girma kakeyi mu kuma munaja baya a matsayin kana magajina Sarkin gobe ya dace kayi iyali kaima kaga zuriar ka."
Shiru MalikusSaif yayi yana mai nazarin maganar mahaifiyar tashi, itama da idanu tabishi ta fahimci baisan zancen, dan murmaswa yayi wanda yakara fiddo mashi da kyawun shi sannan yace. "Toh zanyi insha Allah."atakaice ya bata amsar bai kuma cewa komai, koda ta fahimci baisan maganar cikin kulawa ta mahaifiya wadda takeyima ƴayan ta tace. "Shikenan daman maganar kenan zaka iya tafiya." tashi yayi sannan yace. "Kihuta lfy Ummu." tafiya yake tamkar maijin tausayin Ƙasa, sanye yake cikin wani yadi baki sai sheki yakeyi yai bala'in amasar fatar MalikusSaif kasancewar shi farine ga sajen fuskar baki sai shining yakeyi yayi luf dashi gwanin ban shi'awa hulace ya saka a kanshi baka mai sirkin golden kanshi sai ɗaukar ido yakeyi yanda sumar shi ke kyalli, sannan ya ɗaura golden din alqabba wadda takara fiddo da ainihin nasabar shi da tsantsar kyawun shi, duk inda ya gama gifta bayi ne keta kawo gaisuwa cikin ladabi da girmamawa, shiko saidai ya ɗaga masu hannu wasu kuma yai kamar baigan suba, da yake Yarima Malik mutun ne mai kwarjini kuma shi baida girman kan nan da yayan Sarakai keyi, kuma baida ɗagawa da nuna shi wanine mutun ne mai kyakkyawar alaka da talakawan su har zuwa bayi saidai bai fiye san magana ba, kasancewar baisan yawan hayaniya, ta gefen sashen mahaifin shi ya wuce wanda ya gaji da kayatuwa kowane sashe dake cikin Masarautar Daborah zagaye yake da filawowi masu matukar ɗaukar hankali dayake Masarautar tanada girman gaske koda wajen bayin Masarautar ne kaje shima wajene mi matukar kyau da tsaruwa baka cewa bayi ke rayuwa a wajen har kasuwa ke akwai cikin turakar bayi, sannan gida jene jere tunda ga iyayen bayi har sauran bayin kowa yanada nashi masaukin, shiko MalikusSaif ba inda ya wuce sai wani kayataccen lambu mai ɗaukar hankali ba abinda babu a cikin lambun tunda ga kayan marmari da koramu guda ukku ruwa sai gudana yakeyi gwanin ban shi awa, daga gefen babban lambun Masarautar Daborah, nan ne inda Yarima Malik ke ciwon dabbobi da tsuntsye sai kuma wani babban wajene ba abinda ke ciki sai dawakai kala kala hadimai nata basu abinci wasu kuma anai masu wanka tsakiyar lambu wata irin kerarriyar wukace da akayi aka kafeta a jikin wukar anrubaTakobin Barri wanda wannan taswiyar wukar da aka kera kusan duk inda kayi cikin Masarautar Daborah itace alamar tambarin Masarautar Daborah, kasancewar Wukar Barri wukace mai dinbin tarihi wanda akanta ake yawan kawoma Masarautar tasu farmaki wannan dalilin yasa suke ba takobin barri mahimmancin gaske ta ɗauki shekaru aru aru a cikin wannan Masarautar ta Daborah wannan kenan kadan daga cikin tsarin Masarautar Daborah sannan suna da arziki musamman tarin dukiya da ta shahara a fagen kasuwanci da iya kare martabar ta musamman a wajen abokan gaban basu da tsara kaf a ƙasar Gambia.

Koda MalikusSaif ya isa cikin lambu cikin kankanin lokaci an gama gyara inda yake da zama kishingiɗawa yayi yana nazarin maganar da mahaifiyar shi taimashi duk da yasan shi baida wannan ra'ayin a halin yanzun kuma awajen shi hakan ba wata matsala bane.....

yana cikin tunani ba abinda ya fado mashi arai sai Bahijja samun kanshi yayi da dan murmaswa a zahiri ko cewa yayi "baiwar Allah kina cikin yanayi ga iyayen ki basu da wani yancin kansu fata dai Allah yakara tsareki Bahijja inama Ummu ta amshe ki a matsayin ƴarta, aiko dani zan maki zaɓin miji. bai ida maganar da yakeba yaji ance. "wannan wacece za'aima zaɓin miji har haka Yarima."? Yazid ne yakara sa maganar tareda zama gefen shimfidar Yarima Malik yana mai sakar mashi murmushi cikin so da kauna na aminnai, dan kauda kanshi MalikusSaif yayi cikin dakewar murya yace. "Haka kaji nace?waima yaushe kazo nan."? "Hmm Yarima kenan najima da zuwa amman ina wajen dawakai ina rangadi ne." "hakane Huzaifa fa.?" cewar Yarima Malik, Yazid ne ya bashi ansa "tun sallar asuba ban kara ganin shiba." cigaba da firar su sukayi saidai a cikin zuciyar Yazid yaso yaji maganar da Malik keyi amman yasan shi da zurfin ciki ba lallai ya faɗi komai ba.....
A cikin turakar bayi kuwa Bahijja ce ke wankin kayan ta dana iyayen ta, tanata ba su Mairo labarin Masarautar Raifasu da kalar taimakon da Jakadiyar Masarautar taimata, wani wajen suji tausayin ta wani labarin ma har hawaye suke mata, kamar wadda aka tsikara tace." "Baba Mairo wai yaushe zakije kasuwa.?"
murmushi tayi tana shafa gashin Bahijja da yayi kwance lub tace "ƴata zanje amman kibari Saifulislam ya aikeni sai intafi dake wani irin dadi taji ta rungume Mairo tana ta murna abin ta a rayuwar ta tana so tayi yawo cikin Masarautar Daborah itama ta ganema idon ta kallar kayutuwar da tayi wannan dalilin yasa kullin takeso taga ta shiga cikin Masarauta saidai Umman ta batasan tana shiga cikin ta kuma batasan dalilin hakan ba saɓanin Masarautar Raifasu ba inda bata zuwa amman banda Masarautar su kullin tana zaune waje ɗaya hakadai Bahijja taita sake sake a cikin zuciyar ta, jitayi Mairo tace. "Yata bari inje wajen aikina ki kula da kanki kinji."? "Baba Mairo saikin dawo in kinga Ya Malik ki gaidaman shi." murmushi Mairo tayi aranta ko cewa take yaro kenan ina baiwa ina gaida Yarima kamar Malik, koda yake da sannu zakisan matsayinki na hadima Bahijja, amman a zahiri cewa tayi shikenan zaiji saina dawo, daga mata hannu Bahijja tayi tana kewar Innar tata kasancewar ta kanwa ga mahaifiyar ta, wannan kenan.


~Masarautar Raifasu~


Sarki Baidulƙais ne keta burgima cikin dakin shi kamar zai mutu ba abinda ke addabar shi irin son Bahijja maitar shi akan Bahijja harta fara hanashi sukuni da walwala a cikin mutane hakan yasa ko fa'da bai cika zama ba kullun yana cikin daki yanzun ankai fagen dako Jakadiya bai cika bari tana shiga dakin shi ba hakanan, kusan kowane lokaci yana yini ba kaya jikin shi idan shiawar Bahijja takai shi karshe haka zai dinga wasa da dick din shi wani bima saidai ya sume tsabar azaba yauma kusan hakane lamarin yafara bashi tsoro hakan yasa ya shiga wani waje cikin dakin shi ya murzo zobe da habar shi dan yanzun hannu dayane dashi komai na rayuwa yafara jagule mashi, murza zoben yayi tayi amman a banza har ya fidda rai, zai fito daga dakin sai ga wani murgujejen mutun ya bayyana fuskar shi ba kyan gani shi kanshi Baidulƙais ya tsorata dan bashi ya saba gani ba, amman saiya dake yace. "Yana ganka aljani dandukununu ina aljani dan tsitu.?" wata uwar dariya ce ya kece da ita iya yinsa sannan ya sunkuyo ya kalli Baidulƙais da jajjayen idanun shi masu ban tsoro cikin daka tsawa yace. "Mikake tunanin aljani dan tsitu zaimaka bayan kagaza anci galaba kanka kayi sakaki da mulkin ka kakasa tarawa da Bahijja bayan jimawa da tayi a cikin Masarautar ka kasani Sarrilƙus ya barranta agareka sannan aljani dan tsitu bazai kuma zuwa gareka ba, dan baka da wani anfani sako daga Sarrilƙus yace kada kasake neman sa sannan nan da kwana ukku yace ka maido da karamin zoben Sarrilƙus dake hannun ka tunda kazama masaki hahhhhhahhha." haka yaita dariya har hucin wuta ke fita daga dakin aljanin cikin kidimewa Baidulƙais ya duka yafara bada hakuri saidai ina bai saurare shiba wani irin kuka ya saki yana mai rufe idan shi tsabar bakin ciki bai aune ba yaga ba aljanin ya ɓace ɓat, gunjin kuka Sarki Baidulƙais yakeyi kamar zai mutu shikenan hasashen shi ya tabbata gashi Sarrilƙus yayi mashi bore baisan ya zaiyi da bala'in dake tunkaro shiba haka ya rarrafo ya dawo a cikin dakin nashi ya kwanta kamar mai bacci a ranshi ko bakin cikine dankare ga rasa danshi da yayi galabar da akacishi ya rasa Bahijja ga gabar dake shirin kulluwa tsakanin shi da ɗan aminin shi Sarki Lahazu uwa uba kuma yau ga abin dogaron shi Sarrilƙus ya juya mashi baya, baisan ya sake sakin wani marayan kuka ba wanda shi kanshi yasan raban dayai kuka tun ranar dayabga gawar danshi Yarima Husbarulƙais, haka dai ya kwanta ga yunwa yanaji amman ba damar yaci abinci cikin natsuwa.


➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A wajen Yarima Haishir kuwa kimamin wata ukku kenan da rashin mahaifin shi harya fara dangana yau aka tashi a cikin Masarautar ta Waisu ana bikin nadin sabon Sarki duk da basuyi wata gayya ba amman anyi shagali anci ansha anyi wasanni iri iri sannan aka naɗa sabon Sarkin Waisu fa'da cike take da mutane kowa ya hallara tun daga kan dagaci galadima waziri sarkin fa'da, sarkin gida, sarkin zagi, danbirum dasu majidadi d sauran manya da kananan fa'da, nan Shamaki ya tashi ya naɗa Sarki kowa yaji dadi inda Sarkin shela ke sanar da annaɗa Sarki Haishir Lahazu Humzu a matsayin Sarkin Waisu haka sukaita addu'oin su tareda bokan su na fa'da anata Gurfanai yataimake ka Sarki yabaka nasara, da haka kowa ya watse aka raka Sarki Haishir har cikin turakar shi daya gaji da haduwa da kayan allatu na duniya itama Masarautar Waisu ta hadu iya haduwa saboda tana cikin jerin manyan Masarautu guda ukku da mlnahiyar Gambia ke takama dasu a cikin yankin ta, a wajen gimbiya Ƙamariyya kuma ana nadin ɗan nata tana murna wani ɓangaren na zuciyar ta kuwa cike yake da kewar mijin ta, saidai ba abinda ke ranta irin taga karshen Sarki Baidulƙais da gimbiya Yazira....

*********************************

Bayan wata biyu a Masarautar Daborah kuwa Bahijja ce, a cikin makimancin gidan su tana ɗinɗima abincin da mahaifiyar ta tadawo da shi jiya da daddare domin su samu abinda zasuci da yamma tana gamawa ta zubama Abban ta yaci itama ci tayi sannan suka ajema Umman ta nata, tashi tayi taje cikin makimancin botikin su da suke tara ruwa dan bukata taga ba komai ciki ga mahaifin ta na bukatar ruwa kallan shi tayi tace. "Abba babu ruwa a gidan nan." tashi yayi da niyar ya ɗaukar botikin dan shiga cikin Masarauta ya sama masu ruwa, rike botikin tayi tace. "Abbana kabari inje insamo mana kaga daman ban taba zuwa ba yau nima sai inmike kafaɗa." ba tareda Abdulmajid yayi tunanin komai ba yace. "Shikenan ƴata ki kula da kanki saikin dawo kinji.?" cikin jin dadin yau zata shiga cikin Masarauta tafara murna tana mai ɗagama mahaifin nata hannu ta tafi fita tayi daga cikin kofar turakar bayi ta shiga cikin Masarautar sai kalle kalle takeyi da kaganta kasan bakuwa ce a cikin Masarautar Daborah duk layin da tabi saita tsaya tana al'ajabin haduwar wajen musamman gine ginan Masarautar wanda rabi da kwatar shi duk da farar tsakuwa ce akayi shi sai wasu kuma da jan gargari, ga fantin Masarautar Maroon ne da ratsin light brown, tana cikin tafiya dai daina wani waje inda zai sadaka da sashen royal family wani irin zanene aka sassaka na takobi da wani irin butun butumi na kanki sai mutun agefe rike da takobi ansan Takobin Barri a jikin ta kana gani kasan Masarautar ta shara a fagen yaki da makiya, haka ta dinga tafiya ga yanayi ne na damuna komai shar gwanin banshi'awa ga jerin filawa tabi ko ina musamman iccen inibi da ruman shine kewaye da wajen, murmushi Bahijja ta dinga yi tarasa kona mene tanajin dadi tana mamaki irin tsaruwar Masarautar Daborah a ranta ko cewa take gaskia bantaɓa ganin Masarautar data burgeni ba kamar wannan Masarautar kama hanya tayi tabi wani ɗan lungu saita tsinci kanta wani irin makimancin lambu da wata iriyar korama dayabi ta cikin lambun take iskar wajen ta dinga ratsa dukkan sassan jikin Bahijja ga kamshin kayan marmari iri iri ga tsuntsaye sai shawagi sukeyi a cikin lambun, daga wani waje taga manya manyan maguna da alama suma kiwon su akeyi saijin dadi takeyi a ranta tana cewa gaskia wannan waje akwai dadi ga kayan dadi iri iri ni ko inama zan samu ruwan indiba, cigaba da kutsa kai tayi cikin lambun hankalin ta kwance take tafiyar....shiko Yarima Malik yana fitowa daga wanka ya shirya yaska wani coffen yadi mai ɗankaran kyau sai ya sa hula da takalmi su kuma baki turaruka ya shafa, yana fitowa daga cikin dakin shi kasancewar ba wanda yake bari yana shigar mashi daki a cikin bayi iyakar su falo suna hidima, shiyasa yabi ta hanyar baya yanasan yaje wajen mahaifiyar shi, yana bi ta wani corridor ya shiga cikin lambun dake sashen shi yana shiga ya nufi wajen magunan shi dan Malik yanasan kiwo bai rabuwa da kiwon dabbobi iri iri tun daga nesa ya hangi wata baiwa tana wasa da magen sa, bakaramin mamaki ne yakama Yarima Malik ba a iya sanin shi ba baiwar dake shiga cikin lambun sashen ba tareda wani dalili ba, a hnkali ya dinga takowa kamar baisan tafiyar haka yake takowa cikin nutsuwa, itako ta shagala da wasan d takeyi da mage tana cewa ƴar kyakkyawar mage ta dake zantafi gidan mu ina sonki, jin kamshin daya daki hancin ta shi ya katse mata wasan da takeyi waigowar da takeyi taga kafar mutun daga kafar shi tafara bi da kallo har saman kyakkyawar fuskar shi mai dauke da kwarjini da haiba wani irin faduwar gaba ne ya riske su lokaci guda gaban sune ya dinga halbawa da sauri sauri, itako Bahijja ko motsin kirki takasa kuma takasa sakin magen hannun ta bakin ta na rawa ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya mai hade da kiɗimewa tace. "Ranka shidade barka da yamma, ina tuba bansan nan nazo ba.....ɗaga mata hannu yayi yanaji kirjin shi na halbawa da sauri da sauri ya rasa kona mene, take ya sake haɗe fuskar shi yace. "Mikikeyi nan.?" a rude tace. "Ruwa nazo samu." a dakile ya kara cewa. "Nan wajen dibar ruwane."? dagowa tayi takara kallan shi gani takeyi kamar ba Ya Malik dinta ba aiko suka hada ido cikin ido da sauri ta sauke nata, shi kanshi yasan Bahijja tanada mahimmanci a rayuwar shi jinta yake tamkar jinin shi, da sauri tace. "Bansan wajen ba hanya ne ya biyo dani tanan wajen, ina neman afuwa." bai kuma cewa komai ba binta kawai yayi da ido saiyaji wani irin tausayin ta a cikin ranshi, yanda yaga duk ta ɗarare, samun kanshi yayi da cewa "Bahijja!" ita kanta saida taji faɗuwar gaba, shima mamaki yayi dan baisan ya ambaci sunan taba, da na'am ta amsa, rasa abin cewa yayi kamar mai tuna wani abu yace......





_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Comment
And
Vote

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 45&46



"Miki keyi da mage.?"da sauri ta saki magen aiko ta koma cikin yan uwanta cewa tayi.
"bakomai ta burgeni ne." dan murmusawa yayi sannan yace. "tashi kije ki ɗibi ruwan ki tafi." mikewa tayi kamar wadda kwai yafashe mawa a cikin ciki wata hanya tayi duk ta daburce, so tayi tasa shi dariya ganin ta rude, amman ya dake cewa yayi. "Nan zakibi."tana bin hanyar da ya nuna mata taga wani rizab na ruwa haka ta diba ta fito nan ta tadda shi inda tabar shi godiya tai mashi ko kallan shi taka sayi da sauri sauri take tafiyar zata bar wajen, taji yace. "idan zaki dibi ruwa ki tambaya akwai inda ake diba." da sauri tace. " to ranka shidade." tafiya tayi tana mamakin yanda akayi Ya Malik ya sauya a cikin kankanin lokaci haka ta tafi har cikin turakar bayi, shiko Malik ko mawa yayi cikin falon shi ya zauna sai smile yake saki yarasa kona minene yakeyi shigowa da kayan abincin shi aka dingayi jere shi akayi a saman kafat kiran wata baiwa yayi, dukawa tayi tace. "Allah yatai makeka gani." nuna mata abincin da suka kawo mashi yayi alamun su fita dashi, batai mashi musu ba dan susan baisan jayaiya suka kwashe sannan suka tafi....

Itako Binta tana sashen Sarauniya Zulaiƙa tana aikin ta hankalin ta kam ya kwanta tunda ƴarta ta dawo gareta bata d wata damuwa, Sarauniya Zulaiƙa ce tafito cikin dakin ta sanye da doguwar riga Milk mai ratsin baki a jikinta sai kuma bakar alqabba, zama tayi cikeda kasaita da sauri Binta ta iso ta duka ta gaida uwar dakin nata, a dakile ta amsa tace. "Binta inaso asa bayi su gyara lambun sashen Yarima, sai dai kinsan Yarima yana da ka'idoji baisan yawan hayaniya, karki bari suyi aikin idan yana cikin sashen shi dafatan kin gane." "eh nagane za'ayi komai kamar yanda kika umurta."

suna cikin maganar suka jiyo anaima Yarima Malik iso zuwa wajen Sarauniya Zulaiƙa yana zuwa ya zauna ya ratayo hannun shi a saman wuyan mahaifiyar shi yadan duko saitin kunnen ta yayi wata magana wadda koni Jameey banji abinda yace mata ba saidai naga tayi murmushi sannan ya zaune gefen ta yana mai tankware kafar shi, nan Binta ta gaida shi cikin sakin fuska ya amsa, fita tayi waje, riko hannun ta yayi cikin nashi a nutse yace. "Ummu ina son inba damuwa kiyi mani wata alfarma." cikin so da kauna da uwa kema ɗanta tace. "Ina jinka magajin gobe mikake so faɗama mahaifiyar ka damuwar ka." jiyayi gaban shi ya fara tsanan bugu da sauri da sauri, a dake yace. "Ummu maganar Bahijja shine nace bari intuna ma....daga mashi hannu tayi tace. "Sai yaushe zaka bar maganar wannan yarinyar wai Mali? zansa akawo maka bayi ka zaɓi hadima a cikin su." wani irin haushi ne yakama Malik murmushin yake yayi yace. "Ummu bahaka bane naga yaka mata..."kaga Malik kabar cewa haka dan haka ka'aje wannan maganar kane mi wata alfarmar ta daban ba wannan ba." mikewa yayi yace. "Shikenan sai anjima." tafiyar shi yayi baijira yaji abinda zata ce mashi ba yana fita ya wuce sashen mahaifin shi iske shi yayi zaune yana karatun alqurani mai girma, zama yayi kusa dashi ya gama kallan shi yayi cikin kulawa yace. "Yarima taki amincewa da bukatar ka ko."? Samun kanshi yayi ɗaga kanshi alamun eh, girgiza kai yayi yana mamakin karya alkawali da matar shi tayi yace. " ka kwantar da hankalin ka Bahijja zatayi hidima kamar yanda akayi alkawali a shekarun baya."cikin jin dadi yace. "Nagode Allah yakara girma Abbuh." "Ameen ɗana kada kasama ranka damuwa." labari

Please Login or Register in order to submit comment