Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tazo tafara yanke cibi kallan Sarki MalikusSaif tace.
"Ranka shidade sa ayimani kiran Mairo."
da sauri ya tafi ita kuma ta kama Bahijja ta zaunar da ita bisa wata leda dake shimfiɗe a ƙasa,cikin tausayawa tace.
"Sannu ƴata."
gyaɗa kai kawai ta iyayi mikomata ɗan tayi tace taimashi addu'a, ansar shi tayi tana ta kallan shi sai taga yana kama da Ya Malik ɗinta, addu'ar tayi mashi sannan ta aje shi gefen ta dan bata da wani cikakken karfi,ansar shi Jakadiya tayi ta bata macen haka ta yimata itama addu'ar tana maijin kaunar 'yayan nata a cikin zuciyar ta,Mairo ce ta shigo ɗakin sai farin ciki takeyi ansar ƴar Jakadiya tayi sannan Mairo takama Bahijjar domin taimaka mata ta kimtsa jikin ta,itako Jakadiya gyara yaran tafarayi.
Koda labari ya riski Sarauniya Zulaiƙa lokacin tana sashen Saifulislam itada Matawalle, Huzaifa ne daya gama sheda masu sai farin ciki yakeyi,itako Sarauniya Zulaiƙa sujudur shukr tayi harda kwallan daɗin ta, danko Saifulislam yakasa furta uffan saida murmushi da yakeyi hakama Matawalle baice komai ba sai alhmdullh shine abin da yace,kallan Huzaifa Sarauniya Zulaiƙa tayi tace.
"Kana da kyautar foam ɗari Huzaifa,jinjina kai yayi alamun gamsuwa yace.
"Godiya nike ranki shidaɗe."
fita yayi ya tafi sashen MalikusSaif,kafin kace kwabo baki ɗaya labarin haihuwar gimbiya Bahijja ya mamaye ko ina cikin Daborah harma da wasu sassan na daban duk anji,murna wajen bayi ko ba'acewa komai, da sauran Royal family ɗin,hakama wajen Binta da Abdulmajid kuwa murnar da sukayi bata misaltuwa hakama su Saude kowa sai sa albarka yakeyi.

A wajen mai jego kuwa angama kimtsa su da yaran ta,gwanin burgewa sanye take cikin doguwar riga mai saukin nauyi tayi kyau dan dai taɗan rame kaɗan, haka Sarauniya Zulaiƙa ta aiko hadimai da akwatuna ukku ba abinda ke ciki sai kayan jarirai, sai guda kuma kayan ɗaka ne ciki,haka baiwar Sarauniya ta kawosu tareda hadiman su, godiya suka hauyi inda gimbiya Bahijja tace.
"Mansura abasu tukwici na foam talatin."
rusunawa tayi cikeda biyayya sannan ta tatafi dan cika umurnin uwar ɗakin ta,suma godiya sukayi mata sannan suka tafi, itako Bahijja baki ɗaya tana tunanin Ya Malik ɗinta iya sanin ta raban data kagan shi tun jiya da dare data fara naƙuda gashi har gari ya waye ankusa a zuhur,sihirtatta ajiyar zuciya ta sauke,maganar Jakadiya ce ta dawo da ita tunanin ta,maganin nono ne ta bata tace tasha,ba musu tasha haka ta kwanta dan gajiya.
bayan sallar la'asar Sarauniya Zulaiƙa ce dai aminiyar ta Hajia Kubra dasu gimbiya Salsabila sai gimbiya Abida sukazo duba ƴar tasu,suna shiga cikin ɗakin gimbiya Bahijja suka iske gimbiya Zahara'u da gimbiya Bilkisu tashi sukayi suka tari iyayen nasu bayan sun zauna Sarauniya Zulaiƙa ta riko hannun Bahijja tace.
"Sannu 'yata Allah yaimaki albarka sannu."
Jinjina kai tayi tace.
"Yawwa Ummu."
ɗaukar 'yayan tayi baki har kunne sai murna takeyi haka tai masu addu'a nan ta mikama jama'ar ta,haka suka gama duba ƴar tasu sannan suka mike,sukai ta bada kuɗin barka Mansura ke tarama uwar ɗakin tata itako saida tayi godiya,haka akaita shigowa har dare,ana sallar isha'i Sarki MalikusSaif ya shigo tareda aminan nashi,ɗakin ta ya shiga ya iske Mansura gaida uban gidan nata tayi sannan ta fita wani irin ƙayataccen murmushi yayi ya isa wajen gimbiyar tashi,itako shagwabe fuska tayi raurau kamar zatayi kuka,shiko murmushi yai mata sannan ya hawo bisa gadon yace.."haba Hayatina kiyi hakuri na tuba banzan sake ba kinji kanwar Malik."
"Uhmmm Ya Malik duk yaufa bangan kaba."
"Yi hakuri tawan jama'a sunyi yawa shiyasa amman kina cikin zuciyar Habibi ɗinki kinji gimbiya ta."
kara marairacewa tayi zatayi magana,ya haɗe bakin su waje ɗaya wani irin hot kiss yake mata yana sarrafa lips dinta,itako takasa ko motsin kwarai sunjima a haka saida ya tabbatar da haɗe duk wani korafin ta sannan ya zare bakin nasu a hankali yace.
"Karkiyi fushi ya Yayanki kanwata."
ya ida maganar yana rike kunnen shi alamun ban hakuri,gyaɗa mashi kai tayi tana murmushi, ɗaukar 'yayan nashi yayi yana smile lokaci guda sannan yafara yimasu addu'oi da huɗuba,kallan ta yayi yace.
"Habibti kinsan mi nasa masu?"
"Aaa Habibi ban sani ba."
Kallan namijin yayi dake hannun damar shi yace.
"Wannan Abduljabbar na saka mashi sunan Kawuna Matawalle, wannan kuma na sama ta sunan Umma Fatima."
da sauri ta kalle shi tace.
"Haba Habibi ai dakasa sunan Abbuh da Ummu."
girgiza kai yayi yace.
"Kinsan dalilin dayasa na saka masu wannan sunan?"
girgiza kai tayi
cewa yayi.
"Kinsan Kawu na bai taba haihuwa ba,kuma kinsan irin son da yake mani,shiyasa na saka sunan sa,nasan Ummu da Abbuh zasuyi farin ciki,ita kuma Umma da nasa,nasane dan inƙara karfafa masu guiwa susan cewa suma iyaye ne kamar kowa kuma inasan sunan fil'azal kodan sunan ɗiyar maki (SAW)."
Murmushi tayi tace.
"Allah ya rayasu yai masu albarka."
Ameen yace tareda manna mata sanyayyen kiss a goshi, sai a lokacin yace. "kinga kun mantar dani ina tareda dasu Huzaifa,kuɗin ne rayuwa ta shiyasa nike manta kowa da komai."
Murmushi tayi tace.
"Muje akai masu 'yayan nasu."
haka suka fito shi ya ɗauki namijin ita kuma macen ta ɗauka atare suke jefa kafar su,suna fitowa Huzaifa yafara zolayar su yana cewa.
"Takawar ku lfy Sarki MalikusSaif majnunun gimbiya Bahijja."
Itadai murmushi kawai tayi samun waje sukayi suka zauna sannan suka anshi yaran nan kowa yaita addu'a tareda fatan alkhairi, nan abokan MalikusSaif sukaita bada kuɗi Mansura ke ansa inda gimbiya Bahijja ke godiya nan MalikusSaif ya gaya masu sunayen su,kowa yasa albarka dan ba kaɗan sukaji daɗi ba,musamman da sukaji ansa sunan Mai girma Matawalle,da haka kowa ya tafi yana sam barka, wannan kenan.

Bayan kwana biyu a wajen Binta da kyal Sarauniya Zulaiƙa ta matsa mata akan taje taga yara,da batai niyar zuwa dan kunya da kara,amman bata iya musu da ita hakan yasa ta shirya ita da dangin ta suka tafi da shatara ta arziki har sashen gimbiya Bahijja, murna wajen Bahijja kuwa bata faɗuwa dan ganin dangin nata haka aka karra masu,sannan Sarki MalikusSaif ya shigo ya gaidasu cikin mutuntuwa nan sukaima junan su barka sannan ya wuce fa'da, suma basu wani jima ba suka ba Jakadiya kayan da suka kawo tareda magungunan gyaran jiki,wanda tuni Jakadiya ta jima tana gyaran Bahijja da kayan gyaran jiki na ainahin tsumin Masarautar Daborah wanda kuwa harta fara warkewa abinta,suko sallama sukayi masu kowa ya tafi cikin farin ciki.

A sashen Kangiwa kuwa shida aminin shi kuma ɗan uwan shi Matawalle suna zaune suka aika Ladidi taje ta kawo masu jarirai haka kuwa ta kawo su,koda Matawalle yaga jikokin nashi farin ciki gunshi abin ya wuce a zayyana haka sukai masu addu'oi musamman Khadimulislam dake jin wani farin ciki na musamman.
Matawalle ne yaba ladidi wata leda yace.
"Wannan ki kaima 'yata,wannan akwatin kuwa na takwara nane,sai wannan ledar kuma ta mata tace, Allah yai masu albarka."
Da ameen suka amsa haka ta amshe su suka tafi ita da hadimai sannan aka mai dasu wajen mahaifiyar su,nan ta bata kayan lokacin ta iske su tareda Sarauniya Zulaiƙa sai Sarki MalikusSaif, aiko amsa sukayi sunajin dadi,ledar suka buɗe saiga diamond a cikin ta, kowa yaji dadin kyautukan Matawalle,haka akaita kawo kayan alkhairi ta kowane sashe saidai sambar ka.

**********************************

ɗan sakon Sarki MalikusSaif ne ya isa Masarautar Raifasu,har cikin fa'da yana isa yakai gaisuwa wajen Sarki Muhammad, sannan ya anshi takardar da ya bashi yafara karantawa.

*Assalamu-alaikum*
*Dafatan sakona ya same ku cikin aminci,ina mai* *shaida maku Allah ya albarkace nice samun karuwa ta ya'ya* *ansamu mace da namiji,ina fatan alkhairin Allah a gareku,bissalam.*

Wani irin farin ciki ne ya kama Sarki Muhammad sannna yace.
"Sarkin gida aba bakona masauki."
rausayar dakan shi yayi yace.
"Allah yatai maka yau zan koma daga nan Masarautar Runo zan wuce."
Cikeda gamsuwa Sarki Muhammad yasa akayi mashi shatara ta arziƙi,sannan ya tafi,shiko koda ya koma sashen shi sanarwa gimbiya Aisha wani irin farin ciki tayi tace.
"Ranka shidade yaushe zanje inga yar tawa?"
murmushi yayi yace.
"Jibi ana gobe suna sai in haɗaki da hadimai saiku tafi."
wani farin cikine ya mamaye mata zuciya batasan ta rungume mijin nata ba tana jin daɗi.
***********
Masarautar Daborah kuwa.....


_Yar Mutan Kankia ce_ ❣️


Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 129&130


🔚🔚🔚 🔚 *END* 🔚🔚🔚🔚


*__Alhamdullilah!Alhmdullilah!!Alhmdullahi bini'imatis salihat, narasa ta ina zanfara godema Allah daya bani aron lokaci mai tsada dahar na ida kammala wannan book ɗin nawa mai ɗinbin ilimi da farin jini na BAYIMA_ 'YA'YANE_* *_wanda na kwashe sama da_ _watanni ina typing ɗin shi,tun daga Book one har zuwa Book two,duk_* *_da haka masoyana basu gaji dabin wannan littafin ba duk da watannin da muka kwasa munayin shi_* *_da hutun da mukaje, gaskia bansan da wane baki zan godema Fans ɗina ba,saidai ince Allah ya_* *_biya maku bukatun ku na alkhairi,tabbas ni Jameey Yar Mutan Kankia naga masoya na ban mamaki_* *_daga wurare daban daban saƙon ninku yaita zuwa gareni ta kowane fanni musamman yanda kuke_* *_bani ruwan Comments daga sassa daban daban na Media rabbi yabar kauna ameen_* 🙏

اللَّهُمَّ صَلِّ وَسَلَّمْ عَلَى نَبِيِّنَا مُحَمَّدٍ
```Dubun salati ya tabbata ga manzon rahama Annabi Muhammad (SAW) wanda Allah maɗaukakin Sarki ya aiko domin ya zama rahama ga talikai da iyalen gidan sa tsarkake da sahabban sa masu daraja da tabi'ai har zuwa wa'anda auka bada gaskia har zuwa ranar sakamako,ameen ya rabbi``` 🙏

_tabbas Allah shine abin godiya wanda shine ya bamu aran rai da lfy da ni'imomi daban daban wanda wannan bai samuyi sai domin rahamar Ma'aiki (SAW)._

*Saidai nasha amsa wannan tambayar musamman daga grps na addini ance wai Yar Mutan Kankia book ɗin nan naki kinyi shine domin wa'azine ga al'umma musamman wajen tauhidi ko kuwa kinyi shine dan wani abu na daban?*
*Amsata itace Bayima Ya'yane nayi shine domin al'umma su amfana da saƙon dake cikin shi,kuma ba sashen da bai tabo ba a kowane fanni na rayuwa, fatana Allah ya sadamu da alkhairan dake ciki sannan ya gafar ta mana kurakuren mu baki ɗaya* 🙏

```Jinjinar ban garemu a gareku masoyana musamman Bayima 'Yayane Fans grp,da sauran grps na writers da readers wanda basai na ambace suba saboda yanwan su rabbi yabar zumunci mai anfani``` ❣️

*Fatan alkhairi agareki ta wajena Pharteemarh Kankia bazan ce komai ba agareki Allah ya biya buƙata Ameen🙏*

```Albishir a gareku Masoya na,ina mai shaida maku insha Allah zakuji Yar Mutan Kankia ɗauke da sabon Book ɗin ta,wanda zai sakaku nishaɗi a cikin zuciyar ku``` 🥰


*DABORAH*

Yau take sunan gimbiya Bahijja baki daga ko ina duk sun hallara anata shagalin suna kai kace wani gagarumin biki ne sukeyi musamman wajen Sarauniya Zulaiƙa dake jin farin ciki marar misaltuwa a cikin zuciyar ta danko jariran Abduljabbar (Hassan)kenan da abokiyar tagwaicin shi Fatima (Hussaina) suke a sashen Sarauniya Zulaiƙa tun da safe inna Mairo da gimbiya Aisha (Jakadiyar Baidulƙais) a da, suka kawo mata yan jikokin nata cikin shiga ta alfarma da suka ƙawatu gwanin ban shi'awa.

Wajen Sarki MalikusSaif kuwa kwarya kwaryar walima ya haɗa tagani da faɗa kowa ya hallara tun daga manyan fa'da da hakiman shi da sauran al'ummar dake kalkashin ikon Masarautar Daborah,haka akaci aka sha kayan abinci iri irina alatu da more rayuwar duniya haka sukaci sukai hani'an danko bayyana farin cikin su Kangiwa da Matawalle bata lokaci ne musamman MalikusSaif dake jin shi ya zama Baba haka yaita jin dadi har kunne.

A wajen gimbiya Bahijja kuwa sanye take cikin wani irin dakakken leshi na gani na faɗa pitch color ta sha kyau iya kyau ga sarkar gold dake sanye a bisa kyakkyawan wuyan ta sai yan hannu da zabba kana ganin ta zaka san tana cikin farin ciki mai tarin yawa a cikin zuciyar ta, dangin tane keta shiri zasuje wajen Walimar da Sarauniya Zulaiƙa ta haɗa ma jikokin nata tagani ta faɗa, ɗunguma zuwa babban Hall na sukaBarri nan ne zasu yi walimar,gimbiya Aisha ce rike da hannun yar tata har cikin katon hall wanda yake cikeda mutane kowa yana ta farin ciki tun daga bayi har masu Sarauta, wajen gimbiya Salsabila taba gimbiya Bahijja waje ta zauna bisa wata ƙayatattar kujera ta gani ta faɗa,haka Sarauniya Zulaiƙa ta shigo da aminiyar ta Hajia Kubra sai gimbiya Rukayya yar Sarki Abu-Jalal wadda ita kaɗai ce tazo a cikin yan Masarautar Runo sai gimbiya Abida ɗauke da kyawawan jarirran nasu,haka suka zazzzauna duk wanda kagani kasan yana cikin annashuwa da farin ciki,haka kowa ya hallara hatta gimbiya Zahara'u da gimbiya Bilkisu duk sunzo kowa yasha kaya na alfarma bada jimawa ba aka fara gabatar da Walima bayan buɗe taro da addu'a dayima yaran da aka haifa kyakkyawar Addu'a wanda Saude ce ta gama gabatar da addu'ar sannan ta koma gefen Binta ta zauna haka akaci abinci marai da lafiya iri iri.

_danko yan Bayima ya'yane fans grps suke rabama jama'a kaji da drinks domin taron nasu ne,dan kuwa misulta farin cikin da masoyan Bahijja Malik ke ciki bata lokaci ne dan bakin su kamar farar auduga dan haske na farin ciki da suke ciki, haka sukai ta hidima saida suka tabbatar da kowa yaci yai hani'an._

bayan anagama walimar Sarki MalikusSaif da Yarima Huzaifa sai Yarima Yazid da Yarima Lurwan suka rako abokin nasu, yasha kayan na alfarma kalar kayan dake jikin ɗan nashi Abduljabbar,itama gimbiya Bahijja shigen kalar kayan dake jikin yarta Fatima su tasa sai abin yaba da kala kowa nata yabawa da saka albarka,Sarki MalikusSaif yazo ya miƙa sakon godiya ga jama'ar su da nunajin daɗin shi marar adadi gun talakawan sa ,da haka kowa yayi addu'a sannan aka watse cike da jin daɗi a saman fuskokin su.

Washe gari da safe gimbiya Aisha ce a sashen Sarauniya Zulaiƙa suke ban kwana zasu koma Masarautar su,bakaramin jin daɗin ta Sarauniya ta nuna ba,sannan tai masu fatan alkahiri,sashen Binta ta wuce itama ban kwanan sukayi sannan taje gun Gimbiya Bahijja tana zaune tagama feeding ɗin yaran ta ta miƙama Mansura da wata hadimar ta Zakkiya,koda ta shigo cikin farin ciki gimbiya Bahijja ta rungume Babar tata,tanajin tace.
"Haba Ummi na ace kunyi aure da Abba shine baki aikomin ba nayi fushi."

takarasa maganar tana marairai cewa murmushi tayi tace.
"Yi hakuri 'yata kada kiyi fushi da iyayen ki,lokacin munga hidima tai maku yawa kunata ɗawainiya damu,kuma kema kina da juna biyu shiyasa Abban naki yace kada asanar maku idan kin haihu saimuzo muga yar tamu."
Sake rungume gimbiya Aisha tayi tana jin son ta har cikin zuciyar ta tamkar mahaifiyar ta wadda ta haifeta haka takejin Ummin ta,cewa tayi.
"To Ummi na hakura fatana Allah yasa albarka nayi farin ciki marar misaltuwa a cikin raina Ummi."
Itama jin dadin take ganin hankalin yarta Bahijja ya kwanta takara kyau mai ban mamaki a haka suka taba yar fira tana wasa da jikokin nata daga bisani sukayi ban kwana da junan su,inda Bahijja da ɗauko wasu kaya na Sarakai tace akaima Abban ta,da wasu kaya masu kyau tace akaima indo da Zainab sai kuma taba Umminta wani leshi da sarkar azurfa,ba karamin murna Gimbiya Aisha tayi ba,da haka sukayi ban kwana suna kewar junan su a cikin zuciyar su rakiya tai masu suka kama hanyar tafiya Masarautar Raifasu cikin aminci.

Bayan sati ɗaya a cikin fa'dar Masarautar Daborah kuwa tamkam take da ɗan Adam daka gansu kasan ana gabatar da muhimmin abu ne, kowa yasha ado na alfarma a jikin su gwanin burgewa Sarki MalikusSaif ne zaune bisa karagar mulkin shi da sauran yan fa'da inda Shamaki yafara naɗin mukarraban fa'da ba tareda bata lokaci ba yace.
"Fa'da ta naɗa Huzaifa Abdullatib a matsayin *Wazirin Daborah*,sai Yazid Muhammad a matsayin *Sarkin fa'da*, Lurwan Zaid *Hakimin Kurgu*, Adam Kabir *Magatakarda*, Yusuf Hassan *Majidaɗi* haka dai akaita naɗi mukamai a cikin fa'da nan aka gama limamin fa'da yayi addu'a kowa sai sam barka sukeyi domin anji daɗin naɗin da akayi da haka fa'da ta tashi suka wuce Masallaci salar la'asar.

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

*WAISU*

Mutane ne zaune duk wanda kagani fuskar shi cike take da alhini da bakin ciki,musamman Sarki Abdullahi da idanun shi sukayi jajir dan halin daya tsinkayi kanshi a ciki,Sarki Muhammd ne keta tausar shi yana bashi baki,haka akaita zuwa ana mashi gaisuwar rashin mahaifiyar shi da yayi gimbiya Kursiyya wadda ciwon ciki yai ajalin da asubar safiyar yau alhamis,saida marece likis sannan Sarki Muhammad yaima Sarki Abdullahi sallama shida Wazirin shi suka kama hanyar kowama Masarautar tasu.

**********************************

*RAIFASU*

Koda suka isa cikin Masarautar lokacin ana isha'i direct masallaci suka wuce sukayi salla ana gamawa kowa ya wuce sashen shi, koda Sarki Muhammad ya shiga sashen shi bai jima da zama ba aka sanar da shigowar gimbiya Aisha,a bedroom din shi ta iske shi cikin so da tausayin da macen kwarai kema mijin ta ta tareshi tanajin daɗi,shima haka cikin kulawa tace.
"Sannu da zuwa mijina ya hanya?"
"Alhmdullh gimbiya ta,ya yar tawa take?ansha suna."
Murmushi tayi tace.
"tana gaidaka har kaya taban tace inkawo maka."
Cikin jin daɗi yace.
"Nagode Allah yai albarka."
"Ameen ya Allah."
Cikin kulawa tace.
"Tun la'asar muka dawo ban tadda kaba."
"Eh munje Masarautar Waisu kinsan mahaifiyar Sarki Abdullahi ce ta rasu."
Cikin alhini tace.
"Allah yai mata rahama."
da ameen ya amsa,daga nan ta haɗama mijin nata ruwan wanka,ta taimaka mashi ya kimtsa sannan suka kwanta dan ba kaɗan yakejin daɗin zaman shi da matar tashi ba wadda yakema inkiya da yar aljanna.
Haka rayuwa tacigaba da wanzuwa cikin Masarautar Raifasu cikin aminci da salama.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

*RUNO*

Sarki Abu-Jalal ne da Sarki Dawud sai Rukayya da sauran iyalan shi,suketa farin ciki da jin daɗi,musamman Sarki Abu-Jalal da yaji yanda aka gabatar da sunan jikokin mashi musamman da yaji ansaka sunan Matawalle sai albarka yake sawa da sam barka,ranar har dina ta girma ya haɗa da iyalan nashi,kowa yana jin daɗi a cikin zuciyar shi.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*DABORAH*

Bayan wata ɗaya Sarki MalikusSaif ne zaune a fa'da, inda Sarkin gida ya shigo da wani bako ya kawoma Sarki Abdulmalik saƙo daga Masarautar Waisu,mamaki fal a fuskar Sarki Malik,amsa yayi da kanshi ya karanta ta kamar haka.

```"Assalamu-alaikum
Dafatan saƙona ya iske ka Ya adalin Sarki mai daraja ina mai gayyatar ka zuwa ɗaurin aurena da za'agabatar sati mai kamawa,a Masarauta ta,sannan ina neman alfarma ta mahaifiya agareni kasanar ma``` ```Sarauniya ƙoƙon barata,nagode daga Sarki Abdullahi Waisu zuwa ga Sarki MalikusSaif Daborah```

Wani sanyayyen murmushi ne ya saki yanda yaga sakon Sarki Abdullahi yasan suma sun musulunta nan ya shaidama Galadima da Ciroma yace.
"Ku shirya sati mai zuwa zamuje Masarautar Waisu domin shaida auren Sarki Abdullahi."
haka kowa yasa albarka sannan ya sallami kowa,direct sashen Mahaifiyar shi ya nufa ya shaida mata komai itama taji daɗi kuma ta yarda zata zame ma Sarki Abdullahi uwa kamar yanda ya buƙata,shima Kangiwa ba kaɗan yaji daɗin wannan labarin ba,ganin cikin kankanin lokaci Allah ya shiryi manyan Masarautun su na ƙasar Gambia,godiya sukayima Allah SWT haka suka tashi kowa yayi sashen shi dan hutawa.

Bayan kwana shidda kamar yanda Sarki MalikusSaif ya gayama jama'ar shi haka suka shirya tareda Sarauniya Zulaiƙa suka tafi Masarautar Waisu basu suka isaba saida marece likis acan suka iske Sarki Muhammad da gimbiya Aisha wanda ya zama uba ga Sarki Abdullahi,suna isa akai masu tarba ta girmamawa saijin daɗi sukeyi,musamman da yaga Sarauniya Zulaiƙa ta maida shi tamkar ɗanta haka suka huta da marece suka tafi gidan amarya wanda mahaifin yarinyar yake kanine ga Sarki Lahazu mahaifin Sarki Abdullahi suka kai kayan da uwa keyi na al'ada sai murna sukeyi.

Washe gari da safe da misalin karfe goma na safe aka shaida ɗaurin auren Sarki Abdullahi da amaryar shi gimbiya Hajara, wanda Sarki Muhammad ne ya zama waliyi ga Sarki Abdullahi haka aka gama ɗaurin aure kamar yanda addini ya tanadar.

Da yamma likis aka ɗauki amarya aka kaita wajen Sarauniya Zulaiƙa tasa albarka a matsayin ta na uwa ga ango nan taima surukar tata kyauta da Sarkar murjani da kuɗi foam ɗari hakama gimbiya Aisha itama ta bada kuɗi foam hamsin sannan aka wuce da ita wajen Sarki Muhammad shima yasa albarka da kyautar shi,hakama Sarki MalikusSaif daya zama abokin ango yaima amaryar tasu kyauta ta girma,daga nan aka wuce da ita ɗakin mijin ta.
koda gari ya waye haka Sarakunan ke sashen Sarki Abdullahi suna cin abinci a tare cikin minci,nan Sarki Abdullahi ya kawo labarin Jahiliya da kalar haukan da suka gabatar kowa sai dariya yake ana tuna baya,wani kuma su ɗanyi al'ajabi har aka kira sallar zuhr atare suka tafi masallacin Waisu aka gabatar da sallah sannan suka dawo,bada jimawa ba suka shirya suna kewayar junan su,haka Sarauniya Zulaiƙa takara yima Sarki Abdullahi nasihohi wanda uwa kema ɗan ta da surukar tata,da haka sukayi ban kwana suka ɗunguma domin komawa Masarautun nasu,har akazo mararrabar hanya nan Sarki Abdullahi ya tsaya yana ɗaga masu hannu sannan kowa ya kama hanyar da zata sada shi zuwa Masarautun su cikin aminci wannan kenan.

Akwana a tashi yau ya'yan Sarki MalikusSaif suke cika wata biyu a duniya ba karamin wayau bane sukayi sunyi bulbul dasu gwanin burgewa dasu, hadimai keta yimasu hidima inda Zakiyya ta ɗauki Hussaina ta kaita wajen kakarta Sarauniya Zulaiƙa suna shiga suka isketa da yayan ta wato Matawalle ba karamin daɗin ganin jikar tasu sukayi ba wadda ke kama da mahaifiyar ta kwabo da kwabo ansarta Matawalle yayi yanajin daɗi kallan Zakiyya yayi wadda ke duƙe ta kawo gaisuwa yace.
"Ina takwaran nawa yake?"
Murmushi tayi tace.
"Allah yatai maki mai girma Matawalle yana wajen kakar shi."
Jinjina kai yayi yace.
"Ya kamata akawo mani shi yini ya gaida kakan shi."
Cikin jin daɗi tace.
"Insha Allah."
Sarauniya Zulaiƙa ce ta amshi ta tana mata wasa tace.
"Faɗima yar ma'aiki mai babban suna Allah yaimaku albarka ya'yana abin alfahari na."
"Ameen."
Suka amsa baki ɗayan su,da haka Matawalle ya tashi ya fita,a bakin kofa ya haɗu da Kangiwa gaisawa sukayi sannan ya shigo cikin sashen matar tashi.

A wajen Binta kuwa ba kaɗan take ba jikan nata kulawa ba,goye yake a bayan ta har yai bacci hakan yasa ta kwantar dashi gefen kakan nashi,shiko Abdulmajid sai farin ciki yakeyi ganin yanda albarkar Allah da rahamar sa ta wanzu cikin gidan su,yau shine yafara tara zuriya lallai kam Allah shi kaɗaine abin godiya kuma akoda yaushe,jin kiran sallar magrib yasa shi yin alwalla ya tafi masallaci akan hanyar shine ya haɗu da ɗan uwan shi Idris atare suka tafi zuwa sallah.

A wajen su Sarki MalikusSaif kuwa shida gimbiyar tashi ce naɗe a towel da alama wanka suka gama kowa na kara kaunar junan su ga wata irin shaƙuwa ce kullin ke kara tasiri a zuciyoyin su,tare suka shirya haka ya gama shirya matar shi cikin riga da sicket na atamfa da suka amsheta kamar dan ita aka ƙero su kalar fatar jikin ta saita kara kyau,shima farin yadi ne daya ƙawatu ta sakama mijin nata suka feshe jikin su da turaruka suna tajin daɗi a haka suka isa falo,hannun su sarƙe dana junan su,zama sukayi sunata yar firar su cikin so da kauna,jin ana sanar da shigowar su Yarima Huzaifa da Yazid sai Lurwan kallan gimbiya Bahijja yayi hakan yasa ta koma cikin ɗaki,a lokacin suka karaso da sallama a abakin su,fuska sake ya amsa su,zama sukayi Sarki MalikusSaif ne yace.
"Angaishe da angunan gobe iwar haka kowa an kai mashi amaryar sa wayaga su Huzaifa a ango wai akwai da'ga da gwarama."
Yakarashe maganar yana dariyar wulakanci da shaƙiyan ci,shiko Huzaifa yaƙi yin magana sai raba ido yakeyi yasan abinda ya shuka ne zai girba dan ba kaɗan Sarki Malik kema yankar Huzaifa ba,saidai yai murmushi wani bima haɗe mashi kai sukeyi suna mashi wulakanci wani ya rama wani kuma saidai yayi murmushi Yazid ne yace.
"Ranka shidade gobe da karfe tara na safe za'a wuce Runo ɗaurin auren Huzaifa, so muke sadda biyun rana zatayi har andawo da amarya sannan a ɗaura namu."

"Yayi ango Yazid na gimbiya Zahara'u wato a ɗaura naka kake cewama ko kara babu anyi angunan zamani baidai kunya ba."
Kamar jira Huzaifa yace.
"Aikuwa Yazid baisan ta ido ba shiya...
"Kai in ana maganar masu kunya wake takai wato kasamu damar yin magana ko?"
Sarki MalikusSaif ya karashe maganar yana zolayar Huzaifa,Lurwan ne yai dariya yaga an gwaleshi Huzaifa.
"Wato kai harda dariya jin daɗi aikaine limamin shaƙiyan ci."
Cewar Sarki Malik,dariya sukayi sannan ya kuma cewa.
"Allah yakaimu goben lfy kowa ya shirya da wuri Allah yasa albarka.
Ameen suka amsa baki ɗayan su.
Gimbiya Bahijja ta fito

Please Login or Register in order to submit comment