Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Matawalle ne yaimata wani irin kallo sannan tace. "Naji tunda haka ka zaba saidai bata ba dana, iyakar ta gyaran falon shi." Matawalle ne yace. "Komai zatayi abarshi a haka Zulaiƙa." bata kuma cewa komai ba, shiru ne ya mamaye wajen na dakiku sannan tace."anjima kaje kugana da Zahara'u." wani irin murmushin yake yayi wanda yafi kuka zafi yace. "Toh Ummu hakan za'ayi." shidai Saifulislam yana kallan ikon Allah yau Malik akema dole, saidai nashi ido...


Matawalle ne yace. "Abdulmalik tashi kaje Allah yaimaka albarka. " da ameen MalikusSaif ya amsa yatafi ko gaban shi bai gani sosai, Matawalle ne yace. "Yakamata kisa a saki yarinyar daga gidan kaso tunda ansamu matsaya." kallan tuhuma Saifulislam yashiga yima Sarauniya Zulaiƙa a ranshi ko yana mamakin yanda ta tsani Bahijja harhaka da zata kaita gidan kaso, lallai lamarin Zulaiƙa akwai gyara sosai....

Cewa tayi. "Shikenan badamuwa, sallama taimasu ta tafi, suko su Matawalle da Kangiwa labari sukaci gaba dayi saidai kowa da abinda yake sakawa da yanda yake kallan al'amrin Malik da Bahijja.......



Koda Sarauniya Zulaiƙa takoma sashen ta sawa tayi Binta takira mata Abdulmajid har cikin sashen ta, hakanan Binta ta tafi wajen aikin mijin ta yana cikin ba dawakai ruwa, yana ganin matar tashi saida gaban shi ya fadi dan shakka da abinda da take tafe dashi, da sauri ya tare ta yace. "Ummu Bahijja lafiyarki naganki haka?" girgiza kai tayi tace. "Ba lafiya Sarauniya ke nemanka a sashen ta, baice mata komai ba, sukatafi har cikin sashen Sarauniya Zulaiƙa, isketa sukayi kishingiɗe tasha gawala gwalai asaman wuyanta ga alqabba tada ta alfarma, dukawa sukayi su dikansu, basujima da zamaba saiga wani katan bawa ya shigo da Bahijja agaban Sarauniya Zulaiƙa yai wurgi da Bahijja, zubewa tayi gaban tana facinga mahaifan ta, dukar da kanta tayi dan ba kadan mahaifin nata yaimata kwarjini ba, jitayi Sarauniya Zulaiƙa tace "Abdulmajid uban bayi dan gadan gado, shin bakaga abun kunyar da yarka tayi ba? Shin bakaji kunyar abinda ta aikata ba? ace kamar yarka baiwa tace tana son dana mai daraja magajina Yariman Daborah, kaico kunyi asara aidaman ku kungaji asara da taɓacewa maciya amana, yan gadan bauta, kaiko cemaka akai daba maka akayi ɗana Malik zaiso yarka baiwa zaka amince, koda yake zaka iya amincewa kasancewar ku jahilai mararsa ilimi masu dakikiyar kwakwala maciya amana.!" wani irin kallo Abdulmajid ke aikama Sarauniya Zulaiƙa, yarinyar da yaima bauta tuntana kankanuwar ta, duk wani wankin ta shine tun mahaifin tana da rai yau shi take wulakantawa yar cikin shi, dan dai ya dade baisamu haihuwa ba, murmushin karfin karfin hali yayi yace. "Allah ya huci zuciyar Sarauniya uwa ga magajin gobe Yarima mai adalci, saidai kisani dan yau ka haifeshi baka haifi halinsa ba, tabbas Malik yafi karfin Bahijja kuma koni kaina bazan taba bari 'yata ta auri Yarima aiko ba'afada Malik yafi karfin baiwa kamar Bahijja, dan haka amadadina da duk wani ahalina na bayi muna neman afuwa akan abin kunyar da yarmu ta aikata."


Tashi zaune Sarauniya Zulaiƙa tayi ta mike tana taku cikeda kasaita, tana tafiya tana zagaye su suko sai binta da idanu sukeyi, wani mummunan mari ta wanke Abdulmajid dashi har sau ukku, lokacin su Huzaifa da Yazid sun rako Malik kara ba mahaifiyar tashi hakuri, baki dayan su saida sukaji jikin su yayi sanyi, saboda Abdulmajid koda yake bawa mutun ne da Allah yaima kamala, wanda mutanen Masarautar tundaga bayi har masu mulki suke mutuntawa, dattijo ne dayakai shekaru tamanin da bakwai a duniya, rike kuncin shi yayi yana mamakin karfin hali na Zulaiƙa, koda ya zauna da mahaifin ta wanda shine tsaransa bai wulaknta shi kamar haka ba sai yar cikin shi cikin gadara tace. "Kai harka isa ka kalli kwayar idona kace amadadin ahalin ku, ku harwani ahaline daku, dahar zaka fadamani hakan?" itako Bahijja batasan ta kafce da wani malalacin kuka ba, ganin irin bala'in da ta saka iyayen nata a ciki, da sauri su Huzaifa suka karaso sunaba Sarauniya hakuri, daga masu hannu tayi alamun suyi mata shiru haka kuwa akayi danko Malik yakasa furta komai dan al'ajabi gaskia lamarin mahaifiyar shi sai ita, cewa tayi. "Kai Baru zonan yimasa bulala hamsin." Malik ne yace. "Ummu kiyi hakuri ninajaza masu wannan abun ni yakamata ki hukunta ba Abba ba."da sauri ta waigo ta matso kusa da shi tace. "Wato Abba har ankai wani matsayi da zaka kira Abdulmajid da Abba ashe ya haifeka, bansani ba, toh wancan matsiyacin ba ubanka bane, bawan kane wanda bai wuci kasaida shiba, ko ka salwantar da rayuwar shi, sannan kajini da kyau Malik bawa ba dan uwanka bane bakai ba hada jinin taka da bawa, dan haka inma mafarki kake kafarka Abdulmalik." muryar shi na rawa yace. "Ummu ba haka bane karfa kimanta Bayima 'Yayane, suma mutane....


Jin karar saukan bulalan da Baru ke zabgama Abdulmajid ne ya katsema Malik zancen da yakeyi, a fusace yai kan wannan bawan da niyar dakatar dashi, jin munanan kalaman da mahaifiyar shi tayi yasa shi tsayawa. "Ka kuskara ka isa wajen nan Malik bani bakai." haka akaita zabgama Abdulmajid bulalai su Binta da Bahijja sai kuka sukeyi, Allah Sarki Abdulmajid tun yana iya daurewa har yakai ga yafara kara dan zafi ga jikin tsufa daya taso mashi, haka aka zube mashi bulalai sunfi sittin jikin shi duk yai jini dan azaba, sannan takoma kan Binta itama saida akaimata bulala talatin hakama Bahijja sannan taci gaba da cewa.....



'Dan haka kujama tsinanniyar 'yarku kunne bata ba ɗana inba haka nan ba, bada jimawa zaku bakunci al'amarin da baku taba tsammani ba, ina fatan kun fahimta."?

Binta tace. "Zamu kiyaye, kuma komai agaban idanta ya wakana nasan bazai fatan hakan ya sake aukuwa ba, muntuba uwar dakina Allah yabaki nasara." dan jijjiga kai ta danyi sannan taimasu nuni da subata waje, haka suka tafi dan Abdulmajid yakasa furta komai dan bacin rai har bai ganin gaban shi, haka suka koma cikin taskar bayi rai bace kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi....


Itako Sarauniya Zulaiƙa tana waigowa taga basu Malik ba alamun su, bakin ciki yasa sun fita, ba inda Malik ya sauka sai sashen Kangiwa har cikin ɗakin shi ya same shi yagama karatun alqur'ani mai girma, kamar karamin Yaro haka Malik ya fada saman mahaifin nashi yace. "Abbuh kataimaki iyayen Bahijja yau Ummu ta wulakanta su taci zarafin su, har Abdulmajid mahaifin Bahijja da mahaifiyar ta da ita kanta Bahijjar ta buga Abbuh Ummu na neman sakamani ciwon zuciya."


Cikin tausayin dan nashi yace. "Abdulmalik karka damu, har yanzun Zulaiƙa batasan mike mata ciwoba saidai akwai wata rana da nike jiye mata ranar da zatayi dana sani marar anfani, dan haka kadaina damuwar kanka duk abinda ke faruwa ina sane da komai, Malik bazan yi magana ba, amman akwai ranar kin dillanci kaje kaci gaba da addu'a Abdulmalik in Bahijja alkhairi ce arayuwar ka Allah ya tabbatar hakama in Zahara'u ce itama Allah yatabbatar saidai duk da Bahijja ke baiwa inasan ta saboda kwawawan dabiun ta da kamala saidai mumika lamarin wajen lillahi wahidir kahhar." wani sanyi yaji jin kalaman mahaifin nashi da haka Malik ya kwanta bisa gadon Saifulislam da tunani iri iri a cikin zuciyar shi har bacci barawo yai awan gaba dashi, yana ganin ɗan nashi samu bacci ya sake rufeshi da wani tattausan blanketa yai mashi addu'a ya fita zuwa falorn shi da bai rabuwa da baki masu zuwa naiman alfarma wajen Kadimulislam......


Koda Abdulmajid suka koma cikin madaidaicin gidan su na bayi zama yayi bisa tabarmar su takaba, yana mai aikama Bahijja kallo mai dauke da sakonni iri iri wani mugun bakin cikine ya turnike shi, cikin fada yace. "Kingani ko Bahijja baki godema Allah da ni'imar da yaimaki ba, kin jazamana wulakanci da gori awajen yar danai haihuwa da kamar ta, yau an duke ubanki a gaban idon ki, an duke uwarki agaban idonki anci zarafin duk akan dan ta, Allah yasani inason Abdulmalik saidai wajibine ko kinki ko kinso tunda ba ubanki bane ki rabu dashi daga yau indai ba cika ɗa ba shegeba kuma na haihu daga tsatson Jafar dan Abdullahi baki ba MalikusSaif koda hakan yana nufin ajalinki Bahijja, dan haka kisaka wannan aranki.!"


Wani mummunan faduwar gaba ya mamaye ta saidai kwarjini da jinn nauyin wulakancin da ta zajama mahaifan ta ya girmi tai jayayya akan duk wani hukunci da suka zartar akanta, sadda kanta tayi tace.......





_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم


_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*


Episode 81&82




"Abba kayafe mani nasan nayi babban kuskuren dangan ta rayuwa da ta Yarima saidai zaka sameni mai yawan kauda kai aduk abinda bai shafeni ba kamar yanda kake bani shawara a matsayin ka na mahaifina.!"
takarasa maganar kwalla na sintiri a saman kuncin ta, Binta ce ta dungureta cikin bacin rai tace. "Yimana shiru kina magana kamar mutuniyar arziki da ace kinsan ciwon kanki ai dabaki kai kanki matsayin da Allah bai kaiki ba."
"Umma kiyiman aikin afuwa....Abdulmajid ne ya katseta ta hanyar daka mata mummunar tsawa yace.
"Karya kike Bahijja baki saduda ba, dan a zahiri ga tarin kaunar Yarima nan a fuskar ki, kina kuka ne kawai dan ancima iyayen ki zarafi, amman ba abinda ya ragu cikin idanunki, dan haka ki sani ni Abdulmajid koda nike bawa, ni ba raggo bane kowa yasani a cikin wannan Masarautar ni Jarumi ne kuma ban tsoran abokan gaba, koda afagen fama ne, kowa ya shaida hakan, hawan Sarauniya Zulaiƙa ne daga mulki ya kassara martabar bayi sabanin mulkin Sarki Abdulhamid, itama kanta tasan ubanki ba lusari bane kuma ni inada wadatar zuci, kisa aranki indai daga tsatson Jafar kike wlh Bahijja ya zama dole ki tsaya matsayin ki baki ba Yarima Malik, kema 'yace koda kike baiwa haifarki akai ba daga sama muka tashi muka ganki ba, zan kara maimaitaki kalma ta karshe badan kaunar da muke maki ba Bahijja a matsayin ki na 'yar mu wadda tazo da kalubale iri iri a cikin wannan Masarautar wlh da saina saba maki kamanni dan haka fidda Yarima a cikin ranki shi zaisa kiguji fadawa a cikin fushina, sannan baki ba ɗa mai kima da daraja ke baiwa ce daga yau baki ba Abdulmalik Bahijja.!"

Jitayi bugun zuciyar ta ya tsaya na wucin gadi ga wani katan abu ya tokare mata kirji ta kasa furta komai saidai kwaranyar kwalla da idanun ta keyi, gyaɗa ma mahaifin nata kai kawai ta iyayi, dan dagani bai iya fushi ba duk da baitaba nuna fushin sa akan taba sai wannan lokacin....Mairo kanwar Binta da Ladidi kanwar Abdulmajid sune tsaye idanun su yai shaɓe shaɓe da kwalla ganin halin da yan uwansu ke ciki musamman da sukaga duk jikin su jini alamun bugunsu akayi, duk da kaf Masarautar Daborah tundaga turakar bayi har cikin Masarautar kowa yasamu labarin abinda ke faruwa tsakanin Bahijja da Yarima Malik, wasu naganin kwadayine irin na Bahijja kuma dan tana takama ita kyakkyawa ce, wasu naganin ai tausayin tane yaja yake sonta da kuma kyaunta, tunda ya sota tunkan ta zama mutun da haka dai kowa yaita fadin albarkacin bakin shi akan lamarin Mairo ce a zauna gefen Abdulmajid tace.
"Yaya dan Allah kayi hakuri karka yankema yarinyar nan hukuncin da yafi karfin ta." cikin fushi ya waigo yanaima Mairo wani irin kallo mai ma'anoni yace.
"Yanzun Maryama dan nace bata ba Yarima shine hukuncin mai tsauri bayan kowa yasan itadin baiwa ce shiko Saraki ne mai Sarauta? Kufa mata haka kuke baku fiye yin tunanin da zai fishsheku ba, dan haka wannan maganar haka take ba sauyi." Ladidi ce tace.
"Haba yaya ka kara duba lamarin dai." mikewa yayi ya kalle su yana tamke fuska yace.
"Kuji da kyau, ni kaina Uban Bahijja ba abakin komai nike ba bare Bahijja, dan haka ni bazan taba bada 'yata ba a inda ba'asan darajar taba, na kashe wannan maganar a cikin bakunan ku, ni Abdulmajid nace ba 'yata ba Yarima Malik!!!"



```Turkashi nan fa akeyin ta kunji abinda Abdulmajid yace daga gafe guda kuma ga kudurin Sarauniya Zulaiƙa uwa uba ga abinda Saifulislam yasama ranshi, sannan ga halin da Yarima Malik yake ciki hakama Bahijja,cikin su kowa zai hakura da dan uwan shi, sannan Malikussaif zai auri gimbiya Zahara'u? Hmmm har abin yasani smile😁 kudai kubiyoni dan jin yanda zata kaya a cikin wannan littafi mai dinbin darasi da al'ajabi wato (Bayima 'Ya'yane) yan karin magana sukace Wasa farin Girki nan ma haka abin yake muje zuwa my real fans🥰```


Yana gama fadan maganar shi ya fita daga gidan rai ɓace, kuka ne ya kufcema Bahijja mai ciwo, Mairo ce ta kwantar da ita a saman cinyarta tana lallashin ta danko Binta itama tashi tayi tabarmasu dakin ta koma tsakar gida tana mai jin haushin ɗiyar tata.


A wajen Malik kuwa keyar shi Matawalle ya tisa gaba, suka tafi gidan waziri, suna isa bakin gidan suka tsaya, kofar sashen yace.
"Kaje ku gana da Zahara'u sannan bance kai mata wulakanci ba, kaji yanzun nan Yazid zai taddaka sai kutafi tare." sadda kanshi Yarima Malik yayi yace.
"toh Kawu baka da matsala dani zaka sameni mai yawan yimaka biyayya." cikin jindadi yace. "Allah yaimaka albarka." "Ameen ya Allah."
da haka yatafi yabar shi, bada jimawa ba, saiga Yazid yazo, gaisawa sukayi sannan suka shiga cikin gidan Waziri Abdullatib wanda akema inkiya da (Waziri Dammur) suna shiga hadiman dake bakin kofa suka zube suka kwashi gaisuwa, har cikin katafaren falon gidan aka kaisu, zama sukayi saman kujerun dake falon na alfarma shiru ne ya biyo baya nadakikai, Yazid ne yace.
"Yarima Huzaifa fa."ɗan tabe baki yayi yace. "Karka tambayeni Yazid tunjiya da daddare ban kara sakashi a idanuna ba." rausayar dakai Yazid yayi daganan kowa yai shiru da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi, ji sukayi ana sanar da shigowar gimbiya Zahara'u, ko inda take Yarima Malik bai kallaba, sanye take cikin wani dankareren Material ja, ta daura mashi bakar alqabba ta alfarma da kaganta kasan ta gaji mulki ga kasaita da jiji dakai duk lokaci daya suka mamaye gimbiya Zahara'u, hadimar tace tadan dage mata alqabbar ta sannan ta zauna a hankali cikin nutsuwa da kamala, da sanyayar muryarta tace. "Barka da zuwa Yarima na ina yini? Ya Yazid barka da wannan lokacin."
Yazid ne yace. "Barka kade gimbiya Zahara'u mun sameku lfy?"
"lfy lau tace saidai ko kadan bataji dadi ba yanda ta gaida Yarima Malik amman bai amsata ba, Yazid ne ya fahimci hakan murmushin karfin hali yayi yace.
"Yarima ana gaida ka." biris yayi da Yazid ganin yanayin Yazid ne yasa MalikusSaif ya bude baki kamar baisan magana yace. "Kina lafiya.?"

Samun kanta tayi da murmusawa dan bakaramin dadi taji ba, tace. "Lfy lau Yarima na." wani matsiyacin kallo ya watsama ta a ranshi ko cewa yayi wai Yariman ta, Yariman Bahijja dai." baki dayan su suka kafe MalikusSaif da kallan tuhuma ganin irin kallan da suke mashi ne ya tabbatar mashi da sunji duk abinda yace, nunawa yayi ko ajikin shi, Yazid ne ya girgiza kai alamun bai kyauta ba itako gimbiya Zahara'u kamar ta kurma ihu haka taji take idanun ta sun sauya kala, cewa tayi. " kafadaman tsakanina da Bahijja wa tadace dakai kuma wa kakeso?"
kallan ta yayi ya kaudar dakai dan duk sanda zaiga Zahara'u a matsayin masoyiyar shi hakan na sosa mashi zuciya bare haryayi doguwar magana da ita, ganin yanda Yarima ya kauda kai hakan yasa Yazid yace.
"Haba Zahara'u miyasa zakice haka, aikinsan kinada mahimmanci wajen Yarima ko kidaina irin wannnan maganar." fashewa da kuka tayi, hakan yasa Yarima Malik tashi ya kalli Yazid yace. "Kaga Yazid tashi muje, in kuma kananan shikenan sai kaita zama." Allah yasani Yazid na son Zahara'u so mai girma saidai baida zabi da ya wuce ya hakura, magana Yazid zaiyi cikin bacin rai MalikusSaif ya fara tafiya dan baisan bacin rai, da sauri gimbiya Zahara'u ta riko alqabbar dake jikin MalikusSaif ta duka kasa tana kwalla tace.
"Ya Malik kataimaka mani kasoni koda rabin son da nike maka ne, sannan kasani nasan ni nafi Bahijja daraja da usuli karfa kamanta Bahijjar nan fa baiwa ce."

Ran shi ya baci dan, tsananin bacin rai har idanuwan MalikusSaif sun kankance sunyi jajir ya gaji dajin kalamai marassa dadi akan Bahijja kowa yaita kiran ta da baiwa, mahaifiyar shi kawai ya cirema hula akan aibata Bahijja shima dan baida karfi ko iko akan ta, amman daga ba nan ba, kaf Masarautar Daborah da batsewar ta baiga wanda ya isa ya aibata Bahijja ba bai daga mashi yatsaba, cikin gadara ya buge hannun ta daga rikon da taimashi yace. "Kul na haneki karki kuskura wannan kazamin bakin naki yakara kiran Bahijja bare aiba tata."

Ba karamin mamaki taiba cewa tayi.
"Yanzun Yarima dan nacema wannan watsatsiyar yarinya baiwa shine harna aikata zunubi."
Afusace ya daga hannun shi sama da niyar wanketa damari sai kuma yafasa rai ɓace yace. "Kinci sa'a MalikusSaif ba mabigin mata bane da kinsha mamaki sannan kijini da kyau Bahijja tafi karfin wulakan tatta, koda take baiwa ahaka naga baiwa na fito na shaidama duniya, ni Abdulmalik Yariman Daborah baiwa nike so kuma ita zan aura, dan haka kiyi gaggawar zuwa kicema iyayenki da ita kanta zuciyar taki ta daina son MalikusSaif dan Malik yaimaki nisa, inafatan kin fahimta.?"

Baya baya Zahara'u tayi tazata fadi amintacciyar baiwar ta ta tarota jikin ta, rai bace numfashi na sarkewa tace.
"Bakama so nane Abdulmalik kake gaya mani wannan maganar.?" "kwarai kuwa Zahara'u sadai kisani inai maki so na yan uwanta ka, kuma karki yarda kiyi kuskuran aurena Zahara'u! nabarki lfy."

tafiya yayi yabarta nan kasa sai gunjin kuka takeyi, kamar ranta zai fita, Yazid ya dinga bata hakuri, yana lallashin ta duk ya shiga damuwa ba karamin tasayin ta yake jiba sawa yayi wata baiwarta ta kama ta suka tafi daki, har zai tafi daidai fita daga part din sukayi taho mu hade da Huzaifa, kallan abokin nash yayi yace.
"Harkun tafi da wuri haka, ya kamata gaskia ka koma mugaisa ina Yariman.?" murmushin karfin hali yayi zaiyi magana kenan, sukaji kukan Zahara'u, da sauri Huzaifa ya wuce ciki shiko Yazid fita, yayi ranshi yai mugun baci.

************************************

Yana komawa sashen shi bathroom ya shiga yayi wanka ya saka wasu fararen kaya marassa nauyi sannan ya dan kwanta dan hutawa saidai yarasa mike mashi dadi a duniya duk abubuwa sun cakude mashi.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
A Gamki kuwa aljani dan tsitu ne yakai Sarki Haishir wajen Boka Sarrilƙus gurfane yake a fadar Sarrilƙus da alama 'yan tashi akeyi cikin wata razananniyar murya wadda saida kaf illahirin dajin Gamki ya amshi amon wannan muryar yace.
"Barka da zuwa wannan Masarauta tamu ta tsatsubar tsafin mallakin Gamkin Sarrilƙus amadadina da dukkan jama'ata munai maka murnar shigowa cikin wannan tafiya, domin tsira, sannan duk wani lamarin ka zamuyi maka dafa'i dasu, sai dai zamu baka wannan farin dutsin na kyaren nan inkana da wata matsala ka danna shi, aljani Bunjuri shine mamallakin wannan dutsen ma'ana bawan wannan dutsin zai bayyana gareka, saidai munada sharadi, shi wannan dutsin jini yake bukata ta hanyar hakewa 'ya mace, amman ba budurwa ba, dan haka anaso ka kusanci tsohuwar ka, da ka aikata haka ba mahalukin da ya isa yaci galaba akan ka, sannan zamu kasance tare dakai."
duk da Haishir ke kafiri na gidan gaba, dayaji Sarrilƙus yace saiya kusanci mahaifiyar shi yaji wani irin tashin hankali da kasala sun dabai baye shi sun mashi daurin goro baiji zai iya aikata hakan shi kanshi yasan abin bamai kyau bane bare kuma ace akan mahaifiyar shi zai aikata hakan!. Nazarin Sarrilƙus ya tsaya yi na dakiku ya fahimci damuwar Haishir cewa yayi
"Kana nufin baka iya bin umurnin mu.?"
eh yace, dariya Sarrilƙus yayi yace.
"Gashi mun danganta bukatarmu da ita kuma aljani Bunjuri yaji komai ba makawa a sauya wannan kaddarar saidai kasani rashin aikata hakan tamkar rasa rayuwarka ne da tata baki daya, ya kaga tamu bukatar?"
shiru yayi gashi baiji zai rasa ranshi yana ganiyar mulki ba, sannan ita kadai tarage mashi bazaiso ya rasa ta ba, ganin bai magana ba yasa aljani bunjuri ya mikoma Sarrilƙus wani garin magani, ansa yayi yace.
"Anshi wanna diba ka shaka a cikin hancin ka."ansa yayi ya shaka wani irin sarawa yaji kanshi nayi ga zuciyar shi na halbawa fat fat fat faduwa yai kasa yana makyakkyar wa ta minti goma sannan wata zufa ce ta keto mashi, daga baya yaji wani karfi ya mamaye shi, sake kallan shi Sarrilƙus yayi yace. "Zaka iya bin umurnin mu?" da sauri yace yanzun kam ina komawa zanyi abinda kukace, koda 'yata ce zanyi ai wannan ba wani abu bane."
hhhhhahhhahhh Sarrilƙus yayi mahaukaciyar dariya dan yasan a halin yznun ko cewa yayi anshi wannan Kansakalin cireman kanka ba makawa duk da yasan mutuwa zaiyi amman bazai ketare ba, bare kuma wani aiki, wata yar hisbace ta jelar doki ya dinga karkadawa bisa kan Haishir sannan aka yayyafa mashi wani ruwa aka yanka wani bakin jaki aka zuba jinin cikin wani waje, dan danan dajin ne ya kaurkaure da kara mai kama da ihu kala kala, Sarrilƙus ne yai magana dajin yai tsit, yace.
"Dangi daga aljanu sun tayaka murna zama cikakkan ɗa dan haka aljani bunjuri maida shi gida muna jiran saka mako, kafin yace zai buda baki yayi magana har sun bace saidai ya ganshi bisa gadan shi tareda wannan dutsen a gefen shi yunkurawa yayi zai tashi sai.......





_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*



Episode 83&84



Yaga wani karamin abu agaban shi wata iriyar halitta ta daban ita ba mutun ba ba aljanba kuma ba kadangare ba, tsalle yayi ya kafe a jikin wuyan Haishir harya gama shigewa cikin jikin shi ya ɓace bat, faduwa kasa Haishir yayi ya dinga burgima yana ihu harya suma bai kara sanin inda kanshi yake ba.

*************************************

A wajen Huzaifa kuwa yana shiga wajen Kanwar tashi yafara lallashin ta cikeda kulawa yace. "Haba Zahra kidaina bata ranki akan wannan lamarin, kisa Allah aranki shi zai maki komai wlh duk yanda Ummi ko Ummu zasuso ki auri MalikusSaif in Allah bai yardaba ba zaki aure shiba, hakama duk yanda baiso inke matar shice dole ya aureki Zahra saidai kisani tabbas Yarima yana son Bahijja tun bai gane sonta yake ba harya fahimci hakan dan haka kiyi addu'a wlh kanwata da zakibiye ta tawa da kin aje son Yarima a ranki kiso Yazid dan yana sonki kuma yana kaunar ki, kiyi tunani kanwata,ni mai kaunar kine bazanso inga kin tagaiyara ba." faɗawa tayi jikin shi tana kuka mai sosa zuciya, hakuri yaita bata shikan shi yanajin tausayin kanwar tashi saidai yasan Yarima Malik yana cikin yanayi bazaiso ya rura wutar dake tunkarar abokin nashi ba, shi kanshi yasan bazaiso aimashi haka ba, da haka yasamu gimbiya Zahara'u harta hakura sannan yabar dakin yana mai tsananin jin tausayin ta aranshi.


A wajen Bahijja kuwa abubuwa sun tsananta agareta sabida fushin da mahaifin ta keyi da ita, ko magana bai mata akan lamarin dan ba kadan lamarin ya sosama Abdulmajid zuciya ba, ganin irin cin kashin da Sarauniya Zulaiƙa ke masu nayau daban na gobe daban haka kullin suke fuskantar wulakanci a wajen ta, musamman Binta dakeyima Sarauniya Zulaiƙa aiki kullun saitasa andaketa an wulakanta ta, haka Bahijja kullun da kalar wahalar da Sarauniya kesata, dan zuwa yanzun ta kauracewa zuwa sashen Yarima MalikusSaif gudun zalinci dacin zarafin da akema ta da iyayenta..

Shi kanshi MalikusSaif kwana biyun da yayi baiga Bahijja ba saiya shiga cikin damuwa a ranshi yake ganin kamar ya shekara baigan taba, kowace rana kuma a kowane lokaci

Please Login or Register in order to submit comment