Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fara a saman kofa yana cewa. "Bahijja kidawo gareni kizo ki ceci rayuwa ta bazan iya bake ba Bahijja kizo ki tallafeni, rashin samun ki zai lalata mani mulkina kinji abinda Sarrilƙus ya faɗa Bahijja ina shi'awarki Bahijja, duk da Jakadiyya tana cikin dakin wajen gado amman taji abinda Baidulƙais kecewa godiya taima Allah da yasa Bahijja tabar Masarautar Raifasu tasan da zuwa yanzun Sarki Baidulƙais ya gama lalata Bahijja, shiko da kyal ya iya yunkurawa ya tashi daura mayafi yayi ya iso cikin dakin itako Jakadiyya dukawa tayi tafara gyaran dakin alamun mai aiki, yana kallan ta ya kauda kai kamar baisan da itaba, wata doguwar rigace ya ɗauko ya zira dawowa saman gado yayi ya zauna, itako Jakadiyya gaida shi tayi kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace. "Jamra ina zanga Bahijja."? Jitayi gabanta ya faɗi, cikin dakewa tace "ranka shidade sai inga gaskia Bahijja bata cikin wannan nahiyar tamu saidai ya kamata kasa a nemota kodan lafiyar ta." ta gama maganar tana yin dariyar kasan makoshi, wani irin tsaki yaja yace.
"Nan da kwana ukku zanje da kaina ɗauko Bahijja ko in mutu ko in rayu Bahijja saita dawo kalkashin ikona a wannan Masarautar ta Raifasu sai dai in ban raye kisa wannan a ranki Jamra.....

*****************************
Bayan isha'i Binta ce zaune ta buga uban tagumi ta rasa yanda zatayi da ranta, saibin su Mairo takeyi da idanu jitayi tace.
"Mairo kibani abinda zanci in mutu in huta da wannan rayuwar da nike ciki Mairo dan Allah ki tausaya mani." rike hannun Binta tayi tace. "Haba yaya miyasa zakice haka kidan gana da Allah yana sane da duk wani hali da muke ciki kin manta wanda yai niyar kashe kanshi ko ya kashe kanshi shin mizakice ma ubangijin ki, ki tuba zuwa ga Allah kibarma Allah komai, shi Abdulmajid yayi me da ake ninninka mashi azaba kowane lokaci kiyi hakri kibarma Allah lamarin ki a matsayinki na uwa dan Allah." cikin tausayawa Ladidi tace. "Haka maganar ki take Mairo nasan, kinada hakuri to kikara akai kuma ki jajirce ƴar uwata." batasan sadda tafara murmushi ba take ta nemi duk wata damuwarta ta yaye a cikin zuciyar ta, rungume Mairo tayi tana hawaye, tarasa kona minene, itako bubbuga bayan ta ta dinga yi da sigar lallashi.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Masarautar Waisu kuwa, Bahijja ce keta aikin ta kamar yanda ta saba, wannan lokacin a dakin Yarima Haishir take tana ta gyara gadon shi, shi kuma yana banɗaki yana wanka, sauri kawai takeyi taga ta gama aikin ta taje ta huta, tana cikin shinfiɗa zanin gado taji an riko mata kugu mutuwar tsaye tayi, taji gabanta yafara dukan tara tara juyowa tayi ta banka shi da karfin tsiya, amman ko gezau baiyi ba, hakan yasa ya banka ta saman gado yayi kanta, zillewa taji ya rike mata hannu da karfin tsiya, a wajen MalikusSaif kuwa yana zaune sai duba agogo yake yana jiran yaga Bahijja ta shigo dakin su amman ya jita shiru, tashi yayi yafara zarya yaje ya dawo yaje ya dawo, ya rasa yanda zaiyi, shiko Huzaifa kallan Malik kawai yakeyi ganin yanda ya damu kanshi akan Bahijja a cikin ranshi kuwa cewa yayi Allah yasa dai abokina ba son yarinyar nan ne ya shige shiba, inko hakan ta kasance gaskia akwai damuwa sosai, yana cikin sakar zuci yaji MalikusSaif ya taɓa shi yace. "Huzaifa inaji araina akwai abinda ke faruwa da Bahijja shiyasa bata zo dakin nan aikin taba gaskia so nike yau din nan mubar Masarautar nan." cikin kulawa Huzaifa yace. "Gaskia ne nima ina bukatar mubar Masarautar nan a yau nima nagaji da zama cikin ta,sannan karka ce haka lafiya lau Bahijja take....yana ida magana saiga wata baiwa ta shigo ta kawo masu abinci ajewa tayi ta gaida su, harzata tafi taji Yarima Malik yace. "Ke ina yarinyar dake gyara dakin nan."?
A daburce tace "ranka shidade tun dazun tazo inaji tana cikin dakin Yarima Haishir dan tajima da shiga saidai....daga mata hannu yayi ji yayi zuciyar shi na dukan tara tara, baisan sadda ya fita ba, yayi dakin Yarima Haishir, da har zai shiga sai kuma ya tsaya kasa kasa yaji kamar maganar Bahijja tana cewa "kasakeni kai azzalumi ne baka isa kaci zarafi naba." da karfi yasa kafa ya halba kofar dakin ya shiga iske shi yayi ya matse Bahijja a kirjin shi yana sinsinar wuyanta, itako ta makale bakin ta sannan tana dukan shi iyakar karfin ta, shiko MalikusSaif take idanun ta suka kaɗa sukayi jajir kamar garwashi baisan sadda ya isa ba yasa hannu ya fisgo Bahijja jikin shi kamar ƴar baby, cikin ɓacin rai baisan sadda, ya cillata gefe guda ba, sai a lokacin Yarima Haishir ya dawo tunanin shi jin yanda Yarima Malik ya shaki wuyan shi yakai mashi duka har ukku take bakin shi ya fashe da jini, a rude Yarima Haishir yace "haba Ƙamar miye laifi na dan na huta da baiwa ta."dai dai nan Huzaifa ya iso ya anshe Haishir hannun Malik ya fara tattausar Malik fisgewa yayi ya fita ya koma dakin su, shiko Huzaifa hakuri ya fara ba Haishir yace.
"Kayi hakri abokina kasan halin Ƙamar bai yarda aci zarafin mace ba daman yau zamu tafi sai kayi yanda kake so da ita kayi hakuri abokina." cikeda gamsuwa yace. "Bakomai nasan bacin raine ya kawo hakan ba komai." shima tafiya yayi ya koma masaukin su, koda MalikusSaif ya isa dakin ya gama hada komai sawa yayi aka kira mashi Bahijja koda sakon Malik ya iske ta, jitayi kamar tai fitsari dan tsoro ta rasa dalilin da yasa take jin tsoron kyakkyawan Yarima, dan haka take kiran shi, jiki sage ta iso dakin dukawa yayi tace gani, wani mugun kallo yajefa mata, fuskar shi ba alamun annuri a cikin ta yace......




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 23&24



"Miya hadaki da Yarima Haishir, har haka ta shiga tsakanin ki dashi."? Yanda yai mata maganar ne yasa takasa ko motsin kwarai ta rasa me zatace mashi, tana ɗagowa taga ya banka mata harara bata san ta sunkuyar da kanta kasa ba, muryar ta na rarrabewa tace. "Ba ba komai aiki naje shine ya rikeni amman....hannu yasa saman lips dinshi alamun tayi mashi shiru, hakan kuwa akayi jitake kamar ta kurma ihu ta huta dan ta tsorata da abinda ke faruwa da rayuwar ta, ji tayi yace. "Kina sakaki da rayuwar ki, kinsan halin shi yaka mata kidinga kula da kanki kefa mace ce, mai hadari kinsan yanda kike mahimmanci a wajen iyayenki da makusantan ki, dan kina baiwa ba hakan ke nuna baki da ƴanci ba amatsayin ki na ƴa mace."
sai kuma yayi shiru kamar ba shiba ji yake kamar ya bugeta dan dai yasan ba laifin ta bane fin karfin ta yayi, addu'a kawai yakeyi akan abinda ke damun shi ba abinda yake gani sai halin da ya tadda Haishir yana shirin cin zarafin karamar yarinya mai karancin shekaru kamar Bahijja, ji tayi yace. "Bahijja kukan me kikeyi."? Jin yanda ya ambaci sunan ta sai taji kamar yafi kowa iya fadin sunan kamar shi ya raɗa mata shi, samun kanta tayi dacewa. "Bakomai kawai ka tunamani da iyayena ne da asalina da masu kaunata da gaskia."
kamar bazai kuma cewa komai ba sai kuma yace. "Zaki iya gane iyayenki a halin yanzun."? Da eh ta amsa saidai tace. " da na manta suna Masarautar da aka ɗaukoni amman daga baya Yarima Haishir shine ya ansoni hannun wasu mutane daga Masarautar Raifasu shine yace zai kaini wajen iyayena a Masarautar Daborah sannan zai maidani wajen Ya Malik dina." ta karasa maganar tana kuka mai tsuma zuciya, shi kanshi yai mamaki dan baiyi tsammanin zata iya tuna sunan shi ba, duk da yasan da wahala idan bata manta da kamannin shiba, tausayinta ne yakara kama shi cikin zuciyar shi, cewa yayi ki daina kuka Bahijja Ya Malik dinki ya dawo gareki kuma sai ya mai daki wajen iyayenki da izinin Allah, a zahiri cewa yayi. "Zaki iya gane Ya Malik dinki."? Shiru tayi tana goge kwallan da suke zarya a kumatun ta tace. "Gaskia banza iya gane shiba sai dai har yanzun ina ganin yanayin shi amman ba sosai ba."
wani irin ƙayataccen murmushi ya sakar mata itako a zuciyar ta cewa tayi. "Ohni Bahijja wannan mutumine kamar mai aljani jibi yanda ya saki ranshi danma wannan mayafin bai bari aga fuskar shi sosai tana cikin sakar zuci taji yace. "Bahijja."? Wani irin faɗuwar gaba taji ɗagowa tayi ta aza mashi idanun ta masu matukar kyau da sheki tace. "Naam" cikin sanyin murya wadda lokaci guda tazo mashi yace. "Kinaso kiga Ya Malik din ki da Umman ki."? Cikin zumudi tace. "Eh sai dai nasan baka sansu ba na fidda rai da kasance wa tareda su ni baiwa ce aikin bauta nasani." jiyayi jikin shi yai sanyi basarwa yayi yace. "Yau zakiga Ya Malik dinki."
sakin baki tayi tana kallan shi, shi kanshi yasan mamakine ya addabi zuciyar ta ko kaftawa batayi, shiko hannu yasa ya yaye mayafin fuskar shi, ya aza idanuwan shi masu kama da madara asaman fuskar Bahijja, take numfashin Bahijja yafara rage aiki, kanta ya kulle takai minti goma takasa ko aza idanun ta akan fuskar MalikusSaif abubuwa da dama suka fara yimata yawo a cikin kwakwalwa, ba abinda ya faɗo mata arai sai lokacin da Baidulƙais ya rabota da iyayen ta, muryar Umman tace ta dawo mata a kunne sadda take cewa Bahijja kiyi hakuri kin rabu da duk wani farin ciki tabbas kin rasa gata Malik aminci ne a gareki, gashi kece fansa a gareshi, Allah ya kareki ƴata yatsare maki mutuncin ki da addinin ki......
Wasu zazzafan kwalla ne suka dinga zarya afuskar Bahijja nuna MalikusSaif ta dingayi da yatsa ko magana takasa, da kyal taja kafa ta isa wajen MalikusSaif batasan sadda ta ɗaura kanta a guiwar shi ba ta rushe da kuka mai cinrai tace.
"Ya Malik ashe zan ganeka a rayuwa ta lallai kam Umma kinyi gaskia da kikace Ya Malik shine aminci ne a gareni tabbas na dade ina tsammanin wannan rana ashe amintacce na zaizo gareni." wani sabon kukan ne tasake rushewa dashi, hannu Malik yasa zai fara bubbuga bayan Bahijja sai kuma ya fasa dago haɓarta yayi yace. "Bahijja kidaina kuka tunda kika barmu daidai da rana daya Ya Malik dinki bai taba mantawa dake ba, yau zakibar wannan Masarautar kinji."ɗaga mashi kai tayi shiko Huzaifa kwalla ne ya goge na farin ciki, haka MalikusSaif ya fara lallasar Bahijja har tayi shiru zaiyi magana sukaji anbanko kofa a fusacea tare suka kalli kofar Yarima Haishir ne tsaye ya gama kulewa ya fara jifarsu da mugun kallo mai cike da fassarori kala kala.....


*Toh masoyan MalikusSaif da Bahijja yaudai gasu sun hadu a zahiri bari muga taya za'ayi MalikusSaif ya iya fita da Bahijja a cikin Masarautar Waisu😁 nidai nayi 🏃🏻‍♀️Daborah inga wainar da ake toyawa.....*


A wajen Sarauniya Zulaiƙa kuwa zuwa tayi wajen Mijinta iskeshi tayi yana nafila zama tayi gefen shi ya gama abinda yakeyi yana gamawa ya waigo ya kalleta ya ɗauke kanshi gefe daya, cikin damuwa Sarauniya Zulaiƙa ta kama haɓar shi ta juyo da shi suna facing juna cikin sanyin murya tace. "Abu Malik dan Allah kayi hakri banyi tunanin ranka zai ɓaci har haka ba." banza da ita yayi ya mike ya koma saman gadon shi, ya kwanta kamar mai barci, itama sake binshi tayi tace. "Haba Mijina dame zanji tafiyar MalikusSaif ko kuwa fushin da kakeyi dani koda abokan gaba kasan kaine ke kwantar mani da hankali a lokacin da nike cikin damuwa."cewa yayi "naji magana ta wuce saidai kisani kama Jaruman ki da kikayi bakaramin tsautsayi bane ko wane lokaci za'a iya kawo maki hari daga makiya."
shiru tayi ta rike kanta komai ya kulle mata cewa tayi. "Hakane kam ga MalikusSaif ya tafi balle ya kula da komai ga abubuwa sun rudemani sannan uwa uba, bansan mi zancema Sarkin Yaki ba da Lurwan, gaskia inajin nauyin su mijina."
Ɗan taɓe baki yayi yace. "Wannan shine illar yanke hukunci cikin fushi ya kamata ki gyara Allah ya kyuta." ganin yanda Saifulislam bai ba zancen mahimmanci yasa Sarauniya Zulaiƙa tayi shiru tarasa ta inda zata fara fiddo dasu Lurwan, a sanyaye tace. "Abu Malik yanzun ba abinda kake bukatar inmaka."? Cikin kosawa yace. "Bakomai fata dai Allah ya taimakeki akan makiyan ki." da Ameen ta amsa a sanyaye ta tafi ba inda ta tsaya sai fa'da....


Itako Binta harta dangana dan takara sama ranta ɗaukar duk wani kalubale da zasu fuskanta a wajen Sarauniya Zulaiƙa dan tasan da ba abinda taimasu dan gani take zuwa yanzun kiyayyar suce ke kara ruruwa a cikin zuciyar Sarauniya Zulaiƙa, zama tayi saman wani dakali tana tunanin rayuwa, Bahijja ce ta faɗo mata a cikin zuciya addu'a tafara yi mata tace.
"Allah na rokeka idan da rabo Allah ka maido mani ƴata gareni, kasa Yarima MalikusSaif ya dawo cikin aminci koda bai dawo da Bahijja ya Allah kada kaba makiya ikon nasara akan ɗana Malik, ya Allah ka tsareshi daga sharrin makiya shike ɗebemani kewar Bahijja Allah ka tsare mani shida Huzaifa Allah na rokeka ta ida maganar tana kwalla shafawa tayi sannan ta tashi ta tafi sashen Sarauniya Zulaiƙa danyin aikin ta......


_Masarautar Waisu_


A wajen su Yarima MalikusSaif kuwa, koda Yarima Haishir ya shigo yaji abinda suke cewa sannan ga kamannin MalikusSaif nan sun bayyana cikin fushi ya nuna MalikusSaif da ɗan yatsa yace.
"MalikusSaif ashe kaine kazo dan ka ha'inceni kaci amana ta ashe daman da biyu kazo cikin Masarautar Waisu, kana nufin kazo ne dan ka ɗauki baiwa ta Bahijja shine kahanani ɗanɗanar zumarta data dade tana addabata sama da shekaru masu yawa dan haka yau dinnan basai gobe ba saina cimma burina akan Bahijja, sannan baza kabar Masarautar Waisu ba da kafarka saidai kanka ya rigaka isa Daborah! kaida wannan sakaran Huzaifan nan dan haka yau din nan zan koya maka hankali kuma yanzun a gaban idanka zan ɓare Bahijja a cikin ledar ta."

Kaman nin MalikusSaif sun gama sauyawa ba karamin ɓacin rai bane ya kamashi ba jin kalaman da Yarima Haishir ke jefo mashi marassa dadin sauraro, naɗe hannuwan shi yayi ɗaya bisa ɗaya yaima Yarima Haishir nuni alamar karya fasa, ganin yayi tsaye hakan yasa Yarima MalikusSaif ya fisgo Bahijja dake tsaye bayan Huzaifa ta gama tsorata da abinda Yarima Haishir yace, yana riko hannun ta ya wurgama Haishir yace. "Gatanan inka cika Yariman Waisu hannun ka ya taɓa Bahijja." daya tsaya sai kuma yaga inbaita ɓataba tamkar ya tsorata ne baisan sadda yakai hannu zai taɓa jikin Bahijja ba, wani irin tsalla Yarima Malik yayi ya rike hannun Yarima Haishir ya murɗe saida sukayi kara wani uban ihu ya saki ji yake kamar zai mutu, dan azaba kiciniyar anshe hannun shi ya farayi ya rasa yanda zaiyi da Malik baisan sadda ya kara sakin wata azababbar kara ba shiko Yarima Malik juyo da Haishir yayi ya wanke shi da lafiyayyun maruka har hudu take jini ya balle har hakoran shi guda hudu suka fita sama da kasa, sannan yasa ƙafa ya halba shi ya fadi kasa duk jini, shiko sai kwalla ihu yakeyi hakan yasa mai kula da sashen shi yaji karar ihun Yarima baisan sadda ya shigo da gudu ba suko su Malik fiddo takubban suka fiddo da kibiyoyi suna jiran koda ta kwana sannan ya rike hannun Bahijja sarke da nashi, fitowa sukayi cikin falon Yarima Haishir nan sukayi karo da wannan bawan mai kula da sashen Haishir, wuce su yayi ya shiga dakin da suka fito Haishir ne kwance sai gunza yakeyi dan azaba, cema shi yayi ya bisu zasu gudu da Bahijja Yarima MalikusSaif ne, ai da sauri ya tashi yabisu da gudu yafara hura usur cikin kankanin lokaci jarumai sun fara hawan dawakai, da takubba sunbi su Yarima Malik, suko sai gudu suke kasa cikin Masarautar Waisu, suna cikin gudu sukaNga Jarumai sunkai ashirin sunsha gaban su aiko MalikusSaif ya ɗauko kibiya yafara halbinsu shida Huzaifa suka fara kisar su, haka sukaita ratse Jarumai har suka kai wajen dawakan su suka hau a gaba ya aza Bahijja sannan suk fara doka uban gudu cikin kankanin lokaci labari ya karade Masarautar Waisu Yarima MalikusSaif yazo ya ɗauki Bahijja haka Jarumai sukaita binsu da takubba suko sai ruwan kibiyoyi suke ma Jaruman Waisu, koda sukazo kofar fita Masarautar nan ma sama da mutun goma suka iske sun kewaye kofar tundaga nesa Huzaifa ya dinga yimasu ruwan kibiya shi kuma Malik yana kula da Bahijja koda yaga Huzaifa ya karar dasu sai Sarkin kofa wani mashine Yarima Malik ya zaro a bayan shi ya ɗana ma Sarkin kofa a saman makoshi take ya mutu, Huzaifa ne ya sauka ya bude masu kofa suka fita sai gudun mutuwa sukeyi.
Koda labari ya isa wajen Sarki Lahazu cikin fushi yace.


"Ina son Jarumai guda talatin kubi su insan ku kawo mani gawar Yarima MalikusSaif, kubisu komai rintsi komai wuya."
haka kuwa akayi, sawa yayi aka dinga kwaso gawar wakin Jaruman da aka kashe sunkai talatin cikin ranshi ko cewa yayi lallai MalikusSaif inka gaji Sarki Jabbar ba abinda baza kai ba kuma Sarauniya Zulaiƙa ba raguwa bace mace mai kamar maza kwari ke babu amman wannan karan saina yi ajalin ka, cikin fushi yayi sashen Yarima Haishir ya iske shi fuska kumbure bugun bango yayi ya kalli Haishir yace. "Wawa dakai sakarai a wannan lokacin so kake ka nuna mani cewa Yarima MalikusSaif zaiyi galaba akanka kamar yanda yayi ga Yarima Husbarulƙais lallai da baka da anfani agareni yau gashi wani banza yazo har cikin Masarauta ta ya cima ɗana mutunci, jibi yanda ya cire maka hakora kabani kunya Haishir baka san komai ba sai bin mata kayi asara, dan haka yau basai gobe ba nikeson kaf Jarumai na su haɗa gangamin Yaki zuwa Masarautar Daborah dan haka ni da uwar sa Sarauniya Zulaiƙa zanyi Sarkin Yaki maza kasa a hadaman gangamin yakin da bantaɓa haɗa irin shiba a cikin rayuwata ba.!" haka akayi kuwa dan da nan Sarkin Yaki ya fara yin abinda Sarki Lahazu ya umurce shi.


Suko su Yarima Malik basu fasa gudu ba haka sukaita kisar Jaruman da suke binsu da yake su Jaruman Waisu takubba ke garesu, suko su MalikusSaif suna da kibiyoyi haka sukai tafiya mai nisan gaske har suka isa wani waje Bahijja ce ta kwantar da kanta saman kirjin Yarima MalikusSaif ji take mararta na katsa mata cewa tayi. "Ya Malik kishir ruwa nikeji zan mutu." a rude yace. "Kiyi hakuri yanzun zamu tsaya." Huzaifa ne yaga sun tsaya shima tsayawa yayi yace. "Yarima muna cikin wannan halin ina mu ina tsaywa."? "Huzaifa Bahijja kejin kishi hannun ka akwai ruwa."? Zuwa yayi wajen dokin shi ya dauki silkar ruwa ya mikama Malik, ansa yayi yaba Bahijja ruwa, tana cikin sha sukaji mutane sun, zagaye su......kardai ku manta👇




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 25&26




Ware idanu Bahijja tayi take taji cikin ta ya sake murɗawa bata san sadda ta rike hannun Malik ba, kallanta yayi da kagan ta kasan tana cikin matsanancin tsoro a cikin zuciyar ta, a dake Yarima Malik ya kalle su ɗaya bayan ɗaya shida Huzaifa a kalla zasu kai su goma saidai kowa da takobi a hannun su, shiru ne ya biyo baya, da sauri wani katan Jarumi ya fisgo Bahijja a hannun Malik ya ɗaura mata wuka a wuya ita ko baiwar Allah baki ɗaya tagama tsurewa zawone kawai batayi ba dan tsoro daya gama addabar rayuwar ta, dukawa sukayi shida Huzaifa kamar zasu aje takubban su alamun sun mika wuya.
damko kasa sukayi a hannun su, suka mike tisa keyarsu akayi gaba Yarima Malik ne ya kafe alamun bai tafiya, wani ne ya kwada mashi tsawa yace. " zann kashe ta muddin baka tafi ba." jin haka yasa Yarima Malik ya watsa kasar hannun shi cikin idanuwan su shima Huzaifa watsa masu ta hannun shi yayi da sauri suka ɗauki takubban su suka sauke masu kai ɗaya bayan ɗaya, saida suka kusan karar dasu, suka ga wasu mutanen sun biyo su, haka yasa suka haye saman dawakan su, sukaci gaba da bada wuta iya wuta sai kace masu gudun barin kasar baki dayan ta saida sukai masu fintin kau ko hangen su basuyi tsabar gudu......


_Raifasu_


Yau kam ba laifi ciwon cikin daya addabi rayuwar Sarki Baidulƙais ya ɗan saki tunda harya iya zuwa fa'da dan cigaba da fa'danci sai dai kana ganin shi zakasan ya rame ba kadan ba yai baki, Sarkin Yaki ne yakawo mashi taswirar Masarautar Daborah aka bajeta a cikin fa'da ana duba yanda tsarin garin yake da cikin Masarautar baki ɗaya dan so yake wannan karon ya wargaza tarihin Masarautar Daborah harma da Sarauniyar ta baki ɗaya, haka suka haɗu shida Jaruman shi sukaci gaba da yan kulle kullen da dubarun yaki dan cimma burin su....


A gidan yari kuwa zuwa yanzun su Tasi'u sun gama fita kamannin su da ka gansu kasan yunwa kadai ma ta gama yimusu illa balle kuma kullin da kalar ukubar da ake gana masu na gobe daban ba jibi daban tun suna saka ran taimako daga wajen Yariman su har sun fara fidda rai sun gama saduda dan da yawan su sunaji inama sun mutu da sun huta da azabar da zasu dinga fuskanta ta yau da gobe.
Itako Uwani yau uwar dakin ta gimbiya Yazira takai mata ziyara sai dai badan ta duba lafiyar ta bane, taje ne dan ta gayama ta inda ta aje layar da bokan ta ya bata ta sa'a, koda Uwani taji dalilin zuwan uwar ɗakin ta, bakaramin bakin ciki bane ya takore mata kahon zuciya ba, da batai niyar gaya mata inda layar take ba, saidai gudun abinda zaije ya yadawo yasa Uwani ta faɗi inda ta aje layar tanaji tana gani gimbiya Yazira ta tafi ta barta ko tausanta ba taji ba duk irin wahalar da taimata abanza a wofi kenan ta tashi a banza ko arzikin ruwa bata da shi a wajen gimbiya Yazira bare tasa ran zata kawo mata kwanon abinci wani irin bakin cikine ya turnike Uwani batansan sadda tab rushe da kuka ba, itako gimbiya Yazira cikin ɓacin rai tace ma Sarkin horo daga zuwan ta Uwani ta cika mata kunne da kuka dan haka ya ladabtar mata da ita haka ya kama Uwani saida ya sauke mata bulala hamsin, ya cika umurnin gimbiya Yazira, sannan yai mata talatin da yamma, kafin zuwa dare yaimata wata talatin din ta bacci, haka rayuwa ta dinga zuwa ma Uwani da salo iri iri na ganin sakayya tun a gidan duniya, danko ba abinda yakara sosa mata rai kamar yanda gimbiya Yazira tasa aka duketa, tana komawa dakin da ake rufe su ta cigaba da kuka mai sosa zuciya, wata baiwa ce mai mulkin wajen takama Uwani takara naɗa mata dan karan duka, ranar da zazzabi Uwani ta kwana.


_Ayyah Uwani miye a ciki aiba kiga komai daman ance alhaki kuikwiyone kuma meshi yake bi haka duniya take_

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Ƙaisu kuwa Sarki Danwar ne a fa'da ya haɗa mutanen shi yace. "A kallah yau kwana ukku da aiko mani da sako daga Masarautar Raifasu ya kamata

Please Login or Register in order to submit comment