Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bahijja ta koma falo ta hade kai da guiwa tana kukan zuci, shiko MalikusSaif rasa abinyi yayi hakan yasa ya shiga bathroom ta watsa ruwa ya dauko wata lallausar jallabiya fara ya saka a jikin shi, sannan yaɗan shafa turare, kadan mai sanyin kanshi harya ya hau gado ya kwanta sai kuma yaji wata irin azabbar yunwa ta murde shi lokaci ɗaya, dan raban da yaci abinci tu. na dare, ga shi baisan cin abincin da Bahijja zata kawo mashi a halin yanzun, dan yana fushi da ita, gashi kuma bai iyacin kowane abinci cikin kwanciyar hankali kuma yasan yanzun Bahijja tana fushi dashi ta tafi gida jin yunwa na neman yi mashi illa baisan ya diro bisan gadon ba ya nufi falor yana fitowa ta wani corridor inda zai sada shi da babban falorn shi yaji shesshekar kuka da sauri ya isa wajen Bahijja ce ya gani tana aikin kukan ta, jiyayi kirjin shi ya buga da karfi, ya dafe kai yace. "Kanwar nan tawa baidai rigima ba, a zuci yake faɗar haka, sake hade rai yayi yace.
"Wai daman baki tafi gida ba?"ji tayi zuciyar ta ta tsinke da taji muryar Yarima ɗago jajayen idanun ta tayi ta ganshi tsaye ya harde hannuwan sa, dan aje guiwowin ta tayi akasa tace.
"Ya Malik kayi hakuri karka juyamin baya kaji Yayana?."
samun kanshi yayi da shiga damuwa fiye da ta ta baya, cikeda kulawa ya kalleta yace.
"Ki daina kuka kinsan bansan wannan kukan naki kinji? tashi kije ki sama ma yayanki abinda zaici."
ya karashe maganar yana murmushi itama murmushin tayi alokacin Allah kadai yasan irin a zabar da takeji wani irin masifaffan ciwon ciki ne takeji ya murɗe ta, ɗan danna bakin ta tayi tana cije lips a hankali ta yunkura zata tashi sai kuma ta koma ta zauna, cikin kulawa yace.
"Yadai miya same ki kanwa ta.?"
Kasa magana tayi sai dai nuna mashi cikin ta da takeyi, cikeda damuwa yace. "Ciwon ciki?" daga mashi kai kawai ta iyayi, wani irin tausayin ta yaji ya da baibaye shi, ce mata yayi "sannu Kanwar Malik, bi asannu ki tashi kije gida ki huta kinji karki kuma zuwa aiki sai kinji kin warke kinji?" sake ɗaga kai tayi alamun toh, dafa wata fila tayi dake tsakiyar falon zata mike a hankali ta tashi, ji tayi wani bala'i wanda tunda take duniya bata taɓa jin makamancin saba, tana kikewa taji cikin ta kamar ana mata ruwan alurai sai tsirar ta akeyi ga zafi tanaji kuma ya ɗaure mata tamau, a hankali ta daga kafar ta, ji tayi cikin ya sake murɗewa da karfi, bata san ta fadi kasa ba, cikeda wahala ta fasa uban kuka murya a sarke tace. "Ya Ma..lik... zan mutuhh." ararrabe tayi maganar kuma tana jan kalmomin karshe, ganin Bahijja kasa tana birgima ba karamin tsora ta MalikusSaif yayi ba, da sauri yai kanta ya dagota cikin tashin hankalin da ba'asa mashi rana yace......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم


_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*


Episode 69&70



_Wannan Page din Sadaukarwa ne ga yan team MalikusSaif da Bahijja kuyi yanda kukeso dashi🥰 Yarima Malik yace in gaida ku, ya yaba da kaunar ku agare su_ 😘💔



"Kitashi Bahijja dan Allah karda ki tafi ki barni sannu Bahijja ta!, mikikaci yai maki illa kanwata."?
baki ɗaya jikin Bahijja yai sanyi numfashin ta ne yafara daukewa idanun ta na kakkafewa, baƙin cikin idanun tane suka juye ɗib baka ganin alamar su, zuciyar ta kuwa ta daina halbawa, a ruɗe MalikusSaif yasa hannun shi bisa hancin ta yaji bata numfashi, agigice ya girgiza ta da karfi yace.
"Bahijja karki tafi kibarni kanwa ta kita shi dan Allah bansan wannan wasan Bahijja.! "
ya ida maganar zuciuar shi na halbawa da karfi kamar zata faso ƙirjin shi ta fito ƙasa dan razanar da yayi, ɗaga hannun ta yayi ya saki gani yayi ya faɗi kasa kamar marar rai, bai san sadda ya saɓe taba da gudu yayi cikin falon shi da ita saman kafat ya kwantar da ita, yana kiran suna ta kamar wani zautacce, dai dai lokacin Jakadiyar Saifulslam ta shigo shiko MalikusSaif wasu zafafan kwalla ne suka wanke mashi fuska wanda baisan suna zuba ba, da gudu Jakadiya ta iso ta duka ganin yanda Yarima Malik ya ruɗe gashi a zahiri Bahijja bata numfashi dukawa tayi tana girgiza Bahijja, da sauri Malik ya kalli Jakadiya yace. "Samo mani ruwa Bahijja ta zata mutu dan Allah kitai makamin wlh ina sonta ki taimaki rayuwar Bahijja!"
tsoro ne yaka ma Jakadiya ganin yanda Yarima Malik ke kwalla wanda baima san suna zubowa ba a cikin idon shi, da gudu ta dauko ruwa tafara yayyafa ma Bahijja shi kuma wani mafeci ne ya dauko yana fiffita mata, tun lokacin da Jakadiya ta shigo cikin falon Huzaifa da Yazid suka shigo jin kalaman da Malik ke furtawa yasa sukayi cirko cirko suna kallan ikon Allah, anshe ruwan da Jakadiya ta dauko yayi bai san sadda ya sharama Bahijja shi ba, wata irin ajiyar zuciya ta sauke, tana kuka a hankali maicin zuciya, shiko a kidime ya dinga cewa.
"Bahijja tashi kinji kanwata karki tafi kibarni ina kaunarki, kanwata ina sonki, ke tawace kece yar uwata Bahijja,bazan iya rayiwa babu keba kanwar Malik, dan Allah ki tashi Bahijja.!"
ya ida maganar da raunanniyar zuciya.
ita ko bishi bishi take kallan MalikusSaif, maganganun shi sama sama take jinsu, suko su Huzaifa kallon junan su sukayi sannan sukayi ma juna murmushi shida Yazid, sai lokacin suka iso wajen suka tsaya, ganin Bahijja na neman sake rufe idanun ta, cikeda tsoro ga tarin fargaba daua addabi Yarima Malik da sauri ya ɗago ta, ya sake kwantar da ita kasa, Jakadiya ce tace.
"Yarima ka daina damuwa aita samu sauki tunda komai ya dai dai ta."
a rude ya kalli Jakadiya idan shi duk sun rine sunyi kamar gar washi yace.
"Haba jibi fa yanda take juye juye ko anbata wani abu taci, dan Allah kitaimaka mata wlh inason Bahij.....jin maganar Huzaifa shiya katsema Malik sauran kalaman shi yace. "tasamu sauki Yarima kaje ka gyara jikin ka." mamaki ne ya kama MalikusSaif daya kafe Huzaifa da kallon tuhuma, a ranshi ko cewa yayai kamar ya in gyara jikin na?, kallan Jakadiyar su yayi ganin ya jinjin mashi sannan tace.
"kaje ka wanke jikin ka ya ɓaci Yarima." a hankali yabi jikin shi da kallo abin mamaki farar jallabiyar daya saka, sai hannun shi daya tallabo Bahijja duk jini ya bata sh, bude idanun shi yayi ya kalli Bahijja dake jikin Jakadiya kwance ta dafe marar ta, sunkuyar da kanshi yayi duk nauyin su Huzaifa ya cika mashi ido, tashi yayi yace. "Sannu Bahijja Allah ya baki lfy."
Bakaramin mamaki sukayi yanda sukasan Yarima Malik da kyankyami amman ko ajikin shi, ga jinin menses(MP) ya ɓata mashi jiki amman baiji komai ba saima sannu da yake jeroma Bahijja, shiga yai daki, suko su Huzaifa fita sukayi acewar su kafin abokin nasu ya gama abinda zaiyi, itako Jakadiya kama Bahijja tayi tabi ta wata hanya da ita suka bar sashen Yarima Malik, bangaren ta takai ta, ta taimaka mata ta kimtsa jikin ta, wasu kayane ta bata ta saka, wa'ancan kuma ɗauraye su tayi ta shanya, ita kanta Jakadiya tai mamakin girman Bahijja koda yake yanayin halittar tace kace takai shekara sha takwas, sha tara,amman baki ɗaya shekarar ta sha biyar a duniya.
suko su Yazid shashen Huzaifa suka wuce da yake cikin gidan waziri ne a falo suka zauna kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi Yazid ne yace...


"Huzaifa miza kace gami da lamarin Yarima Malik da Bahijja.?"
murmushi yayi yace. "Yazid kenan dukan mu ba yaro nidaman tuni nasan MalikusSaif son Bahijja yakeyi shike ganin kamar tausayin ta yakeyi akwai tausayin amman soyayyar tafi karfi, itama tana son shi saidai kwarjini yake mata."
gyada kai Yazid yayi yace. "tsoro ya kamani Huzaifa gaskia akwai abin firgitarwa a cikin al'amarin nan musamman a wajen Ummu nasan muddin tasan halin da MalikusSaif ke ciki wlh akwai matsala, har tausayin su ya kamani.!" ya ida maganar da raunan niyar murya, rausayar da kai Huzaifa yayi yace.
"ai dole sai dai kana nan zaice ba sonta yake ba, yakasa gane yanda so yake." dariya Yazid yayi yace "in banda abinka taya MalikusSaif zaisan wani so bayan bai taɓa yin shiba."
hakane kam cewar Huzaifa, Yazid ya kuma cewa. "Kai naga kana sonta ya za'ayi kuma ga aminka yana sonta."murmushi yayi mai dauke da ma'anoni sannan yace.
"Daman ina nuna mata so dan inga yanda Yarima taya zan so abinda MalikusSaif keso bayan nasan tun Bahijja na kankanuwar ta Yarima Malik ke son ta taya zanso abinda nasan shine farin cikin abokina."
"shikenan Allah yakawo mana mafita a cikin al'amarin nan amman rikicin da zai wanzu shi nike tsoro."cewar Yazid.
"wlh kuwa kasan fa Zahara'u na bala'in son MalikusSaif takeyi sai dai bai sani ba, koma ya sani soyayyar Bahijja tari ga tai mashi illa a halin yanzun baijin kira, shiyasa ma bantaɓa yi mashi maganar taba, ba wanda zai haɗani da amini na."
murmushi Yazid yayi yace.
"Lallai kam kace soyayyar maso wani akeyi kenan." cikeda mamaki yace "kamar ya Yazid?"
"eh mana aini duk duniya ba wadda nike so kamar Zahara'u." murmushin jin dadi Huzaifa yayi yace "Allah ya hada hankalin ku aiko da nafi kowa murna."
da haka sukaci gaba da firar su, hadimai ne keta shigo masu da foodflask dauke da kayan abinci suna jerewa a gaban su, ga kayan marmari gefen su, baiwar Huzaifa ce tayi saving din su, suka fara cin abinci su, kowa na sake sake a cikin zuciyar shi......


A wajen Yarima Malik kuwa yana cikin bathroom yana gyara jikin shi, hakanan sai yaji smile ya suɓu ce mashi a cikin zuciyar shi ko cewa yake.
"wayyo 'yan mata na ashe angirma anzama manya kenan, Allah yarayamin ke Bahijja ta Allah yaima rayuwar ki albarka Kanwar Malik, Allah Sarki sai dai kinashan wahala kanwata!"
ya gama maganar cikin raunin murya cikeda fa tsantsar tausayin Bahijja a cikin zuciyar shi, da haka yai wanka ya gama tas, sannan ya fito ya shafe jikin shi da mai masifar kamshi da laushi, ya bude wardrofe ya zaro wasu kaya sky green mai ratsin baki, ya saka sannan ya feshe jikin shi da turaruka, a zahiri ko cewa yayi
"dole in wada taki da kaya saboda bukatar yau da gobe kanwata." yana gama abinda zaiyi ya saka takalman shi black sannan ya daura agogon hannun shi itama black, ya saka hular sarauta wanda 'yayan Sarakuna ke sawa itama black fitowa yayi ya koma cikin lambu gefen wata korama yana kallan yanda ruwa ke guduna ga tsuntsaye nata shawagi a sararin subuhana da saman ruwan gwanin burgewa, wani irin yanayi wanda a gareshi bako ne ya dingaji yana ziyar tarshi akan Bahijja, ga wasi wasi da zuciyar shi ke mashi wata tace son Bahijja kakeyi wata kuma tace aa tausayin ta kakeyi Malik, har dai wadda tace sonta yakeyi tafi rinjayar shi, Huzaifa ne ya fado mashi arai dan tsaki yaja yace. "tunda har Huzaifa yana son Bahijja dole koda son ta nikeyi indauki kaddara nasan waye Huzaifa, bazai cutar da rayuwar Bahijja ba." ɗaga hannun shi yayi ya kalli gabas yace.
"Ya Allah ga baiwarka nan ka jiɓinci lamarin ta Allah katabbtar da alkhairin dake cikin rayuwar Bahijja, Allah katai maki rayuwar Bahijja kasata sahun mutane masu daraja."
ya shafa, yana mai jin dadi a cikin zuciyar shi sanyin koramar ne ya fara kaɗa shi kasan cewar shiddan yamma ya karato hakan yasa ya tashi ya koma falon shi ya zauna kafin lokacin sallah yayi ya tafi masallaci sannan yana son yaje yaga mahaifiyar shi yana zama yaji yunwar dazun ta dawo mashi sabuwa fil, dan harya manta da batun abinci, tashi yayi ya bude wasu foodflask da Bahijja ta aje mashi, yaga dashishine akayi da miyar ganye taji bandadden kifi, budewa yayi ya zuba, gefe guda kuma ga madarar shanu nan dafaffa, bissimillah yayi yafara cin abinci baiyi cikoli biyar ba lafiyayyu yaji sallamar abokan nashi, amsa masu yayi suma sukaja kujeru suka zauna ba mai magana a cikin su turo masu kular abincin yayi alamun su zuba suci Yazid ne yace.
"Yanzun muka gama cin abinci Yarima kaidai kaci daman harka dan saki." kallan Yazid yayi ba yabo ba fallasa sannan yaci gaba da cin abincin shi, su kuma suna dan taba yar fira, dan Huzaifa yasan yana fara yima shi maganar tabbas bazai ida cin abincin ba kuma daga ganin abokin nashi ya kwashi yunwa.

Asashen Jakadiyar Saifulslam kuwa Bahijja ce ta farka daga bacci, da murmushi Jakadiya ta tari Bahijja cikin kulawa tace.
"Yata kin tashi kenan, sannu ya cikin naki?" a hankali tace.
"ya lafa yanzun bai ciwon ba kamar dazun ba."matsowa jikin ta Jakadiya tayi cikin kulawa tace.
"Yata kinga bakon al'amarin da yazo maki ko? toh ki daina kuka ba wani abu bane yakan zoma kowace 'ya mace, wannan shike nuna girma yaka maki Bahijja, sannan za'a bude maki littafin zunubi dana lada a wajen mahaliccin mu, saiki kiyaye wajen aikata laifika ya kasan ce aikin alkhairin ki yafi na sharri, sannan kullin ki samu kina wanka sau biyu ko ukku a rana, kuma yanda kikaga naimaki ɗazun haka zaki dingayi kina sawa a wondan ki gudun karya ɓata maki jiki, ba kowa akeson yasan kina wannan abun ba koda kuwa Yarima Malik ne shima dan agaban idan sa yazo maki da bazai sani ba, kinji?"
gyada kai tayi cikin sanyin murya tace. "Nagode Allah yaska a alkhairi." da ameen ta amsa, sannan tace. "akwai hukunce hukuncen sa har zuwa ranar da zai ɗauke, baki sake ganin shi sai kuma wani watan dan haka saiki rike ranar da yazo maki sannan ki dinga lissafa kwanakin da zai maki, ya kasu kashi kashi, wata daya zo ya nuna kanshi zai dauke mata, wata kuma tana yin kwana ukku, wata tana kwana bakwai, wata tana kwana goma har zuwa kwana sha biyar, shine iyakar kwana kin shi, dan haka sai ki nutsu kisan kwana ki nawa yake miki, sannan idan ya dauke akwai wankan da akeyi wankan tsarki kenan, shima zakiyi shi kamar haka." haka Jakadiya taima Bahijja bayani dalla dalla sannan tace.
"kinji yata, in kinje gida kisanar ma Umman ki koda wani abu ya shige maki duhu ita zata sanar dake kinji 'yata."
"toh Baba nagode Allah yakara girma."
"ameen 'yata, yanzun ga kayanki nan aleda na kara maki guda ukku duk da na jikin ki dan kidinga sauyawa kinji Allah yakara lfy sai anjima." "Ameen ya rabbi, nagode."
ansar kayan tayi ta tafi gida tana zuwa ta kwanta, batajima da kwanciya ba Abban ta ya shigo ganin ta kwance ga marece yayi yace.
"Yata kitashi marece yayi kuma za'a kira sallah lokaci yana gabatowa kiyi alwalla kiyi sallah kinji?"
samun kanta tayi dajin nauyin mahaifin nata bazata iya fada mashi abinda ke damun taba, sai tace toh Abba."
ganin ta yayi sukuku ya zauna gefen ta yace. "Bahijja ko baki lfy ne?" da sauri tace. "Aaa Abba inson inhutane nagaji da yawa jikina ba kwari sosai shiyasa."
rausayr dakai yayi alamin ba damuwa yace.
"Kibari inkinyi sallah sai ki kwanciyar ki ki huta kinji yar baba."murmushi tayi tace. "Toh Abbana."


Koda Malik ya gama cin abincin sa kallan abokan nashi yayi yasan akwai abinda suke tafe dashi kallan Huzaifa yayi yaɗan daga girar shi alamun lfy? Murmushi yayi mai dan sauti yace. "Allah yataimaki Yariman Daborah yayan Bahijja ranka shidade magajin gobe, Allah yakara girma, kayarda da maganar da nike maka akan Bahijja?" wani irin kallo yai masu mai dauke da ma'anoni yace.
"Kmarya wace magana kuma?" "hmm MalikusSaif kenan, kwayar idanun ka kadai tasanar mana da son da kake ma Bahijja." wani irin murmushi yayi a ranshi ko cewa yayi kwarai kuwa Huzaifa nima yau dinann nan na gasgata zuciya akan son Bahijja dana afka ba tareda na sani ba gashi na makara ka rigani." a zahiri ko cewa yayi. "Huzaifa manya kai komai so! so! so! haba ba damar inji tausayin Bahijja? naji daman ai kana sonta kaima kasan bayan da za'ai kaso abu nima inso shi" murmushi yayi yace. "Hmmm koda nace banso." da sauri Malik ya kalle shi yai murmushin kasan mako shi, yace. "Bahijja dai kanwata ce nabaka ita kaje kanemi so sannan zan ƴan ta maka ita." rausayar dakai yayi yace "MalikusSaif kenan abokina na kaina waya gaya maka Bahijja na sona bayan kwayar idanun ta sun fito fili sun nuna kai take so." girgiza kai yayi tace. "tayaya bayan kullin takan ceman yayan Bahijja kaga mubar wannan maganar wai yaushe Matawalle zai dawo."
"hmm ka fidda matar ne koda yake aiko Jakadiya shaidace gani ga Yazid kowa yasan Bahijja kake so."
rausayar da kanshi yayi yana nazarin abokan nashi anya dagaske Huzaifa yakeyi ba son Bahijja yake ba duk a cikin zuciyar shi yake wannan sake saken zaiyi magana kenan suka sinkayi kiran sallah baki dayan su suka mike kowa yayo alwallah suka tafi masallaci kasancewar Saifulslam shine limamin masallacin na Daborah sai in bainan imam na biyu wato limamin fada kejan sallar suna gama salla kowa ya kama gaban shi.


Bayan wasu awanni angama sallar isha'i Saifulslam ne ya wuce sashen shi su Yazid suka tafi gidajen su, shiko MalikusSaif wajen mahaifiyar shi ya wuce a ranshi maganganun da sukayi ne dasu Huzaifa suke mashi yawo akai wasu yai dariya wasu kuma ya girgiza kai da haka har ya shiga cikin tanfatsetsen sashen na mahaifiyar...

A wajen Kangiwa kuwa yana komawa ya fidda alqabbar jikin shi ya zauna yana mai rufe idanun shi kamar mai bacci, ji yayi Jakadiyar shi tai sallama bude idanun shi yayi ya amsata, samun wuri tayi gefe ta zauna ta dukar da kanta kasa tace. "angaishe da Kangiwa Kadimulislam tabbas yau nazo maka da wani al'amari mai giraman gaske!"
gyara zaman shi yayi ya kalli Jakadiyar tashi cikeda kulawa yace....




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم


_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*




Episode 71&72



"Inajinki Hajara, mike faruwa?" sake sunkuyar da kanta tayi tace. "Allah ya taimaki mai girma Kangiwa tabbas hakar mu ta cimma ruwa Ya Abu Malik yau dai zargin mu akan Yarima ya tabbata, MalikusSaif ya afka son baiwar nan Bahijja so bayya nanne wanda ban tunani za'a shawo kanshi cikin sauki gaskia yana matukar kaunar yarinyar nan tuba nike ya shugaba na wannan shine abinda idanuna suka gane mani zahiri ba ɗini ba kuma agaban abokan sa ya furta kalmomi na so ga Bahijjar. "
numfashi ya sauke mai zafi yana mamakin lamarin cikin ilimi da hikima irin ta Saifulislam yace. "Hakane Hajara tuni nike zargin ɗana yana son Bahijja sai dai shi baisan so bane saboda kuruciya sai yanzun ya fahimci hakan, dan haka ni ba abinda zance saidai zanma shi addu'a idan tarayyar shi da Bahijja alkhairi ne Allah ya tabbatar da hakan, inba alkhairi bane Allah ya sauya zuwa mafi alkhairi, wannan dalilin yasa nike nusantar da mahaifiyar shi ta gane tsanar mutane mararsa daraja a idon ta bashi bane domin ba'asan abinda gaba zai haifas ba gashi kuwa ɗana wanda nafi kauna yana son baiwar da take ikirari ta tsana dan haka ni bazan juya mashi baya ba, nasan yin haka zaisa inrasa ɗana sannan na gargade ki ko mahaifiyar shi bance ki sanar mawa ba, zata iya shiga cikin tashin hankali da sannu zan sanar da ita komai." cikeda gamsuwa tace. "Haka za'ai Allah yakara girma.

A wajen Yarima Malik kuwa cikin bedroom dinta ya isketa itama da alama sallah tagama tana addu'a gefen ta ya zauna cikin kulawa ta kalli dan nata tace. "Yarima kagu jema Ummun ka ko?" rankwafawa yayi ya daura kanshi bisa kafadar mahaifiyar tashi yace "haba Ummu kidaina fadan haka mana." cikeda kaunar dan nata tace. "Ehmana yau kwana biyu baka nemi mahaifiyar kaba kasan halin dana shiga kuwa?"
kwantawa yayi saman sallaya ya daura kanshi bisa cinyar Ummun tashi yace. "Kiyafeman Ummu banjin dadi bane shiyasa."
Cikeda da damuwa tace. "miyasame ka?" "ciwon kai ne." wani irin tausayin shi taji tace. "Allah yakara lafiya mai anfani." "Ameen Ummu na mahaifiya ta mai share hawayena Allah yabarmin ke."da ameen ta amsa sannan tace.
"sati mai zuwa Matawalle zai dawo ina fatan ka fidda matar daya umurce ka ko?" tambayar da tai mashi sai yaji kirjin shi ya buga tabbas yana tausayin halin da mahaifiyr shi zata shiga intaji yana son Bahijja sai dai zai kokari ya fidda ta aran shi kodan farin cikin mahaifiyar shi cewa yayi "Allah yakaimu lokacin Ummu."
"Ameen duk da haka koda ace a cikin gida ne ka fidda mata, yana da kyau kabi kawun ka kuje wajen Baffan namu dan kasan dangin ka."
"toh Ummu haka za'ayi." "Allah yaimaka albarka." "ameen Ummu na." shiru ne ya biyo baya kowa da abinda yake sakawa a ranshi, ita fatan ta MalikusSaif ya zabi gimbiya Zahara'u, shi kuma hankalin shi na wajen Bahijja yana jimamin halin da take ciki, haka ta dinga shafa sumar kanshi, tashi yayi ya jawo kwaryar fura ya fara yasha, ya gama sannan yace.
"Ummu bacci nikeji saida safe."
"toh ɗan Matawalle Allah yatashe mu lfy."
"ameen Ummu Malik." murmushi tayi tana karajin kaunar dan nata itama shirin kwanciya tayi ta kwanta.


Koda ya koma sashen shi wanka kawai yayi ya saka kayan bacci sai dai ya gagara ko runtsa idanun Bahijja kawai yake gani cikin halin daya barta addu'a yafara yimata da fatan samun sauki.
itama anata bangaren zuciyar ta taji ta azazzale ta da son ganin Ya Malik dinta ko bacci ya gagare ta ba ita ta samu bacci ba sai gaf da assalatu, danko MalikusSaif bisa sallaya yake kwance da alamun nafilfili yayi daganan bacci ya sace shi.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Washe gari da safe ya kama Juma'atu babbar ran, ranar da kowa ne musulmi yake ta shirin tafiya masallaci dakin Allah, a cikin Masarautar Raifasu ma Sarki Muhammad ne ya fito wanka da alama harda wankan tsarki yayi na juma'a dan zuwa yanzun komai ansar masu hatta wankan tsarki an koya masu shi mazansu da matan su, kuma kowa saida yayi na shiga addinin musulunci hakan yasa Sarki Muhammad ya shirya cikin fararen kayan shi sai kamshi yake bazawa, ya kama hanyar tafiya masallaci shida jama'ar shi.

Koda sukaje Masallaci Tasi'u ne ke huɗuba, saboda Allah yaima Tasi'u tarin ilimin addini ko a Daborah yana cikin limamai masu jan salla a babban Masallacin na Daborah, haka ya dinga huɗuba kan ridda da hukunci wanda yayi ta, hikimar yin wannan hudubar kuwa saboda yasa zukatan mutanen da suka musulun ta su kara rike addinin su da mahimmanci su manta da addinin da suka gada kaka da kakanni da haka aka kabbara Sallah Sarki Muhammad ne a sahun gaba da sauran tawagar shi, danko kafaɗa da kafaɗa yake da wani bawa, wanda in ahanya ne ko cewa akai yabi hanyar da Sarki Muhammad yabi ada bazai iya ba saboda kaskancin wannan bawan amman da yake shi addinin musulunci ba ruwan shi da Sarki ko gwamna ko shugaban kasa ko talaka da attajiri ko kuma wani mai yanci ko bawa duk daya suke wajen wahidir ƙahar Sarki buwayi gagara misali, haka suka cakuɗe a cikin Masallacin nan domin ganawa d ubangijin talikai, suna gamawa Sarki Muhammad ya mikama wannan bawan kusa dashi hannu sukayi musabaha sannan ya mika Sarkin fada dake gafen haggun shi hannu suka sakeyin musaba kowa ya tafi gida cikin aminci.


```Allah Sarki rayuwa haka addinin musulunci yake addini mai karamci baida kyama ko nuna fifiko akan wani cikin dan

Please Login or Register in order to submit comment