Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa yana mai farin ciki a cikin zuciyar shi.
Haka Yarima Dawud yazo yaimasu barka da zuwa nan sukaita firar zumunci da yaushe gamo, wannan kenan


_Masarautar Daborah_

Kwana biyun nan da Sarki MalikusSaif yayi baki ɗayan Masarautar ji suke kamar ya shekara ba karamin kewar shi sukeyi ba duk da Wazirin shi yana iyakar kokarin shi.
A wajen gimbiya Bahijja kuwa ba kaɗan take samun kulawa a wajen iyayen taba, da hadiman ta.
Saidai duk da haka kullin hankalin ta nakan Ya Malik dinta.

*************************************

*WAISU*

Rayuwa tafara sauya masu komai yana tafiya yanda yakama ta domin kuwa suna fahimta addinin musulunci dai dai gwargwado tundaga tsarki sallah da abubuwan da ba'a rasaba, domin kuwa har anfara kiran sallah a cikin Masarautar ta Waisu.


_*Note* :-Naji yanda Comment dinku keta zuwa wajena akan wannan littafin na Bayima Ya'yane, yanda salon sa ke sauyawa._ _Toh masoyana haka wannan labari yazo ba inda bai taɓata ba na rayuwa kowane fanni,_ _musamman wannan page yana ɗauke da sako iri iri, sannan bawai inayin wannan book ɗin_ _bane dan cin zarafin wani ko wata ba, ko wani addini! Aaa book din Bayima Ya'yane book ne mai dinbin darasi da ilimi, sannan inasan aiman uzuri koda nikeyin shi_ _ban anbaci wani addini ba wanda za'ace ina againsing dinshi, ina fito da tsantsar gaskia,ta_ _yanda sakona zaije inda nike fatar yaje, batare da cin zarafin kowa ba, inafatan za'a fahimceni._
_Sannan idan anga kuskure a cikin wannan book aiman afuwa ajizanci ne irin na ɗan Adam 🙏_

*Kuma naji dadin yanda kuka karbi wannan littafin fiye da zatona da adduar ku agareni Allah yabar so da kauna, ni Jameey ina yinku yanda yakama ta bissalam.*


_Yar Mutan Kankia ce ❣️_


Share
Comment
And
Vote
Pls



*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 127&128



_Masarautar Runo_


Cikin katafaren falon Sarki Abu-Jalal zaune yake shida 'yayan nashi duk wanda ka gani yana cikin farin ciki,maida kallan shi yayi wajen Sarauniya Zulaiƙa yace.

"Yata yau kice a cikin Runo tareda Baffan ki,gaskia bazan musilta irin farin cikin da nikeji ba a yau ,musamman idan na ganku gaki ga ɗana ga Matawalle sannan ga Kangiwa, wannan ziyarar ta musamman ce a gareni."
Murmushi sukayi baki ɗayan su.

"Baffa ni kaina bazan iya musulta farin cikin da nikeji ba,gaskia ba abin da yafi zumunci daɗi."
Cewar Sarauniya Zulaƙa.

Inda Matawalle yace.
"Yawwa Baffa muna tafe da ƙoƙon barar mu a wajen ka?"
Maida hankalin shi yayi kan Matawalle alamun ina sauraran ka.
"Baffa muzo nemawa ɗan mu Huzaifa auren Gimbiya Hafsat."
Wani irin sanyin daɗi yaji yana ratsa dukkan sassaan jikin shi,sannan yace.
"Haba Abduljabbar karfa kamanta Huzaifa shima ɗana ne, tunda har yara sun sasanta kansu ba wani matsala a ciki domin duk abinda ya faru Gimbiya Rukayya tai mani bayanin komai."

Jinjina kai Kangiwa yayi ya kalli Sarki Abu-Jalal yace.
"Gaskia kawu saidai muce Allah yakara sutura da girma,munji daɗin wannan lamarin fata Allah yasa mana albarka."

Baki ɗayan su suka amsa da ameen.
Sarki Abu-Jalal ne yace.
"Yakama ta Dawud ka raka Huzaifan suje sukara gaisawa da Hafsatun ,zuwa anjima da yamma."
"angama ranka shidaɗe Allah yakara girma."
"ɗan kanina zuwa jibi iwar haka kazama Sarki ko?"
cewar Sarauniya Zulaiƙa.
Murmushi yayi yace.
"Anty kenan,kice nauyi dai zai haye mani."
Murmushi sukayi ganin ya marairaice fuska,MalikusSaif ne yace.
"Wlh kuwa Kawu sai hakuri mulki akwai jidali a cikin shi fata dai Allah yakara dafa mana baki ɗayan mu.
da ameen suka amsa,sannan suka tashi kowa ya tafi masaukin shi.

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️


Sarki Haishir ne zaune cikin shiga takamala da ka ganshi kasan ya shiryu zuwa yanzun ba abinda ke ɗaga mashi hankali sai irin katubarar daya afka tsakanin shi da mahaifiyar shi,ji yake kamar yai hauka idan ya tuna da lamarin zuwa yanzun kuwa ko son haɗuwa da ita baison yi,lamarin ya zame mashi kamar me dan ko baccin kwarai baiyi hakan yasa aka kira mashi babban malamin su wanda Sarki Muhammad ya aiko masu har cikin sashen shi aka kawo da sallama a bakin shi,inda Sarki Haishir ya amsa,sannan ya bashi wajen zama gaisawa sukayi sannan ya kalli malamin yace.
"Allah yatai maki malan ina cikin matsananciyar damuwa na aikaita ayyuka na alfasha kafin in shiga cikin wannan addinin malan gashi yanzun ina son in tuba ya zanyi.?"
Murmushi wannan malamin yayi yace.
"Wannan abun mai sauki ne Abdullahi, kofar tuba tanada yawa fiye da tunanin ka,zaka iya tuba."

Kallan shi Sarki Abdullahi yayi wanda aka fi sani da (Haishir) yace.
"dan bakasan irin alfashar dana aika ta bane shiyasa kake zaton haka,amman bari kaji abin dana aikata."

Jinjina kai malamin su yayi yace.
"Basai ka tunowa kanka a siriba Sarki Abdullahi kasani addinin mu bai lamunce ba idan Allah ya rufama bawan shi asiri shi ya tonawa kansa ba,kasani ka aika ta laifin ka wanda ba wanda ya san kayi sai Allah kuma bai tona maka asiri ba,dan haka kaima ka rufawa kanka asiri basai ka gayama kowa ba,abin da akeso shineka tuba zuwa ga Allah sannan kasa a ranka ba zaka kara aikata wannan zunubin ba ko makaman cin shi,indai kayi haka kana sakankancewa Allah zai karba, bako shakka Allah zai gafarta maka zunuban ka baki ɗayan su."
Numfashi ya fidda tareda sanyayyar ajiyar zuciya sannan yace.
"Alhamdulillahi Malan taya ake tubar?"

"ka yawaita maimaita kalmar Astagfrillah wa'atubuilah, da kuma maimaita kalmar Allahumma gafirli zambi,kaga waɗan nan sune kalmomin da zaka lazumta insha Allah gafarar Allah zata wanzu a gareka fata Allah ya gafarta mana baki ɗayan mu."
"Ameen ya rabbi."
haka Sarki Abdullahi yaita maimaita Astagfirillah a cikin zuciyar shi.

Wajen Gimbiya Ƙamariyya itama hakan take duk abubuwan da suka aikata sun sha mata kai ta rasa mafita,itama kamar yanda Jakadiya ta sanar mata fatawar da malamin su yaba Sarki Abdullahi, haka itama ta dinga istigfiar tana neman tuba zuwa ga Allah maɗaukakin Sarki.

*Allah Sarki,haka rayuwa take duk abinda mutun zai aikata matukar mutun ya tuba zuwa ga Allah tareda tsarkake zuciyar shi ba shamaki Allah mai jin roƙon Allah ne zai gafar ma bawan sa,muna roƙon Allah ya gafarta mana ya jikan mu da dukkan al'ummar musulmai mamatan mu da rayayyun mu ameen ya Allah*


➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

*MASARAUTAR DABORAH*

Gimbiya Bahijja zaune cikin garden ita da hadimar ta Mansura ta kishingiɗa ga tarin kayan marmari a gaban ta, suna ta fira da Mansura kamar wasu kawaye ba wani banbanci a tare dasu,suna cikin fira saiga wata baiwa tazo da duƙa ta kawo gaisuwa wajen gimbiya Bahijja fuska sake ta kalli baiwar tace.
"Baiwar Allah mike tafe dake?"
dukar da kanta tayi tace.
"Ranki shidaɗe ina neman alfarma agareki."
cikeda kulawa tace. "wace irin alfarma ce faɗi karki damu."
"Allah ya taimaki uwar ɗakina ina neman alfarmar kayan abinci domin abincin da aka raba mana namu ya kare tun shekaranjiya."
Jinjina kai Bahijja tayi tace.
"Baki da matsala,Mansura kuje keda ita kicema Sarkin rumbu nace yaba ta kayan abinci,sannan kice ya sameni a sashen Umma."
"to ranki shidade angama."
har sun juya zasu tafi gimbiya Bahijja tace.
"Mansura ki taddani sashen Umma inkin dawo."
"to uwar ɗakina ki huta lfy."
tafiya sukayi ,ita kuma gimbiya Bahijja haka ta koma sashen Umman ta isketa tayi zaune bisa sallaya da alama tayi salla ne zama tayi gefen ta,cikeda kulawa ta kalli yar tata,wani irin tausayin tane ya kamata ganin yanda cikin ta ya tsufa tace.
"Sannu Bahijja daga ina kike ɗazun na shiga ɗakin ki baki nan?"
Kwantawa tayi bisa cinyar Umman ta,tana ɗan lumshe idanun ta tayi tace.
"Umma munje lambu ne."
"Tom ina Mansurar take?"
"na aikesu wajen Sarkim rumbu ne."
Jinjina kai tayi sannan tace.
"Yawwa Bahijja kina shan maganin ki dai ko?"
ɗan haɗe rai tayi dan Allah ya sani harta gaji da shan magungunan da ake bata hakanan cewa tayi.
"Eh Umma nasha."
"Ki dinga kula kinga idan Ummun ku ta dawo nafison taga kin canza sannan duk maganin da takawo maki ace kin shanye su baki ɗaya da wanda Mairo ta kawo maki."
"Uhmmm." shine abinda Bahijja tace ta maida idanun ta ta rufe saidai ba wanda take kewa irin Ya Malik ɗinta,Allah yasani ba kaɗan tayi kewar shiba a cikin zuciyar taba, jin sallamar Abdulmajid shi yasa ta buɗe idanun ta ta kalli Abban nata sannan ta zaune tace.
"Abba na barka da rana."
"Yawwa ya'ta ya jikin naki?"
sunkuyar da kanta tayi tace.
"Alhmdullh."
Jinjina kai yayi sanna ya bata wata leda yace.
"ga tsaraba 'yata."
amsa tayi tace.
"Nagode Abbana."
buɗewa tayi kayan kasuwa ne irin su yalo rogo mangwaro sai faru ,ba karamin daɗi tajiba haka ta fara cin rogon ta cikeda farin ciki.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Bayan kwana ukku yau takama Juma'atu babbar rana ,a ranar ne bayan an sauko daga masallaci akeyin naɗin Yarima Dawud, kowa sai farin ciki yakeyi anata kai kawo ga tarin jama'a daga sassa daban daban na nahiyar Gambia kowa yayi ƙur adaka kana gani kasan taron ya tara manya mutane na daga Sarakuna da masu arzkiki da manyan yan kasuwa hakama talakawa da sauran bayin Masarautar duk ba'a barsu a baya wani dankarere filine da jerin dawakai akalla sunkai guda bakwai duk sun sha ado iya ado daka gani kasan ba wanda ya dace da hawan su, sai Sarakai domin kuwa Yarima Dawud ne kaɗai ake jira a wannan lokacin, tare dasu Sarki MalikusSauf suka taho yana rike da hannun Yarima Dawud cikin shiga ta alfarma sunsha kayan Sarauta sun gaji da haɗuwa musamman Yarima Dawud wanda yasha fararen kaya kai tsaye wannan filin suka tunkara tareda zugar jama'ar su, Madawaki ne ya rike mashi sirdi ya hau bisa wani farin doki daya gaji da ƙayatuwa,sannan Sarki Malik yahau wani Doki mai yankan batta kirar dawakan Sudan, haka sauran duk suka hau direct fa'da suka isa acan suka tadda Sarki Abu-Jalal,Kangiwa,Matawalle,Galadima ,Dagaci,Ciroma,Shamaki,Magayaƙi,Wambai,Ɗanburam,Sarkin Fa'da, Ɗan Zagi,Limamin Fa'da,Maji daɗi dai dai sauran jama'ar fada da Sarakuna da sauran jama'ar arziƙi duk anzo naɗin Yarima Dawud magajin Sarki Abu-Jalal.
haka Shamaki ya riko shi aka ajeshi saman wata kujera sannan aka ɗauko kayan naɗin Masarautar Runo aka fara naɗin Yarima Dawud dashi haka Shamaki ya fara naɗa shi,Sarkin shela keta shela kowa yai shiru inda Shamaki ya ida naɗin da bashi wani cover ta gold na qur'ani sai carbi da haka aka ida naɗin Yarima Dawud kasancewar Masarautar Runo,Masarauta ce ta Musulunci wanda tayi shura wajen aiki da shari'ar musulinci.
haka Mai shela yaita shela yana cewa.
"Alhmdullh lokaci ya kawo mu Allah ya yarda yau dai gashi annaɗa Yarima Dawud a matsayin Sarkin Runo Allah yasa alkhairi ya baka ikon yin adalci,limamin fa'da ne yayi addu'a kowa ya shafa sannan Sarki Abu-Jalal da Sarki MalikusSaif sai Kangiwa da Matawalle,sai Galadima da Shamaki suka kamo Sarki Dawud akai masu runfa suka zaunar dashi bisa kujerar mulkin Runo wadda ta gaji ta ƙayatuwa shiko sai kwalla yakeyi domin nasihohin da Sarki Abu-Jalal yai mashi sune suke dawo masu sabo fil a cikin zuciya,da haka yan fada suka gabatar da kansu sannan kowa ya tafi ɗakin taron da aka gyara domin yin walima dagacan aka ɗauko Sarki bisa doki aka kaishi wajen iyayen shi mata da yayyen shi duk suka albarka,haka dai Sarauniya Zulaiƙa tai tajan kannin nata shidai ya kasa ko maganada haka aka wuce dashi side din matar shi gimbiya Sumayya akai ta murna daga karshe dai aka wuce dashi tamfatsetsen sashen shi,haka kowa yaita jin dadi su Yarima Huzaifa da Sarki MalikusSaif sukaita tsokanar shi,da haka dai aka kira sallar la'asar kowa ya tafi masallaci wannan kenan.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Sarki Muhammad ne zaune a fa'da anata fadanci kowa yana faɗar albakacin bakin shi inda ake ta budget na shekara Sarkin taska da Sarkin rumbu duk sun hallara haka Majidaɗin Raifasu yasa akaita ware kayan abinci da wanda za'akaima bayi da talakawan Masarautar duk a rubuce ake wannan budget ɗin haka suka gama komai sannan Sarki Muhammad yaba maji daɗi umurni yace.
"Kasa hadimai su ɗibi kayan abinci kamar yanda aka ware akai cikin taskar bayi da wajen Masarauta wajen talakawa a tabbatar da kowa yasamu abinci da kuɗi domin sayan kayan masarufi wanda ba'a rasa ba."
Jinjina kanshi yayi sannan yace.
"Angama ranka shidade Allah yataimaki Sarki mai adalci."
Sarkin Za'gi ne yace.
"Ameen angaisheka Majidadi Sarki ya amsa aje aita bamu daɗi a cikim Raifasu."
hakan yasa kowa ya ɗan dara sannan suka tafi domin cika umurnin Sarki Muhammad.

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

Washe gari da safe misalin karfe goma Sarki Abu-Jalal tare dasu Matawalle aka gama yin baikon gimbiya Hafsat da Yarima Huzaifa wanda za'ayi bikin su nan da wata biyu bayan babbar sallar layya hakan ba karamin farin ciki ya saka suba kowa yaji dadin wannan lamari,musamman Abu-Jalal da yakejin farin ciki na musamman.
misalin karfe biyu na rana baki ɗayan su kowa ya gama shirin shi zasu wuce gida wanda yau suka cika kwana bakwai cir a cikin Masarautar Runo,Sarki MalikusSaif ne rungume da Sarki Abu-Jalal suna ban kwana dan bakaramin kewar junan su sukeji danko Abu-Jalal harda ƴar kwallar shi dan ba kaɗan yake kaunar jikan nashi ba, baki ɗayan su suka ɗunguma zuwa Dawaki a can suka tadda Sarki Dawud da Jama'ar shi haka sukaita bankwana da junan su ji suke kamar kada a rabu,haka dai kowa yayi bankwana suka hau dawakan su,a ran Sarki Malik kuwa yana kewan Abi din shi,saidai zuciyar shi fes take zaije yaga Norul Hayat ɗin shi dan ba kadan yake kewar suba musamman babyn su wanda kullin da kaunar cikin Bahijja yake kwana dashi yake tashi a cikin zuciyar shi, da haka suka rakasu har mararraba sannan suka kama hanyar tafiya Masarautar Daborah.

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

*DABORAH*

tunda gari ya waye gimbiya Bahijja take kitchen ita da hadiman ta, suna girki iri iri na tarar sahibin nata haka suka dinga aikin su,inda Mansura ta ɗauko wasu foodflask na silba ta mikoma gimbiya Bahijja ansa tayi ta buɗe ta zuba sinasir a ciki, sake miko mata wata kular tayi ta ta juye gasassun zabbi a ciki duk aka jeresu bisa katon flat,sai jug daya anzuba mango juice guda kuma ta juye dafaffar madarar shanu a ciki, nan suka gama haɗa komai, Bahijja ce ta kalli Mansura tace.
"Mansura ki kai wannan flat ɗin a sashen Ya Malik."
"toh ranki shidaɗe."
tafiya tayi sashen iyayen ta domin shiryawa nan tabar sauran hadiman ta suna gyara kitchen ɗin da sauran sashen nata wanda yake ta baza uban kamshi yasha gyara iya gyara.

Koda Mansura ta isa sashen Sarki MalikusSaif itada wasu hadimai haka suka jere kulolin abinci cikin wani ƙayataccen falo na alfarma gwanin birgewa kamshi kawai yake ta bazawa kamar me,haka ta gama yin komai sannan suka fito ta wuce wajen uwar gijiyar ta.

Da misalin karfe huɗu na yamma Sarki Malik da iyayen shi suka iso cikin Masarautar Daborah, haka yan fa'da suka tarosu ba inda suka tsaya sai bakin katafaren sashen Sarki Abdulmalik koda ya iso bakin kofar shiga cikin side ɗin nashi anan dogarawan shi suka tsaya,sannan ya shiga da sallama a bakin shi wani irin fitinannan kamshi ne ya daki hancin Sarki Malik har saida yaɗan lumshe kyawawan idanun shi masu matukar sheki ,koda gimbiya Bahijja taji sautin sallamar sahibin nata da sauri ta fito cikin wani ɗaki tasha ado iya ado da wani dakareren sky blue ɗin material na alfarma ta ɗaura jar alqabba wadda tasha ado da jawwahar saman kyakkyawan wuyan ta kuwa tasa sarkar ɗanyen gold na zarri sai walauniya takeyi da sauri ta isa wajen Ya malik ɗinta shiko Sarki MalikusSaif kusan suman tsaye yayi saboda wani irin razanan nan kyawu da yaga Hayati ɗin shi tayi mashi na ban mamaki buɗe hannayen shi yayi itako a ashagwabe ta faɗi saman faffaɗan kirjin shi,a tare suka saki wani irin sihirtaccen numfashi mai ma'anoni kiss ya manna mata bisa dogon wuyan ta,sannan suka tafa da tafin hannayen su,dukawa Sarki Malik yayi yana mannama cikin ta kiss cike da kewar su da yayi yace.
"Nayi kewar ku gimbiya ta, ya baby na?"
Sake rungume shi tayi tace.
"Habibi sannu da zuwa muma muna kewar ka,baby yana lfy."
ta ida maganar tana janye tafin hannun shi dake saman cikin ta,riko hannun shi tayi sannan suka shiga cikin bedroom shiko Sarki Abdulmalik sai kallan ta yakeyi ji yake kamar ya haɗiye ta,dan ba kaɗan yake kewar komai na matar tashi ba,a hankali ya buɗe labban sa yace.
"Kanwar Malikk."
Yanda yai maganar tareda jan harrufan saida yasa tsikar jikin ta ta mimmi mike. "Naam." shine abinda gimbiya Bahijja ta iya furtawa,shiko hannun shi ya ɗaura bisa kyakkyawar fuskar ta yace.
"Kinyi kyau Hayati keta musamman ce gimbiya ta,ina kaunar ki kanwar Malik."
Kwantar da kanta tayi bisa kafaɗar shi cikin sigar shagwaba wadda duk sadda zatayi ta, takan saka shi cikin shauƙi marar misaltuwa tace.
"Habibi kaine jigon kanwar Malik, komai mallakin kane mijina ina sonka Ya malik."
kamar wani karamin yaro tsam ya rungume ta,yana shaƙar daddaɗan kamshin ta,mai saka shi nutsuwa da nishaɗi a hankali cikin dubara ta zame jikin ta sannan taja hannun shi suka shiga bathroom shidai nashi ido haka gimbiya Bahijja ta fara rage mashi kayan jikin shi daga shi sai boxes ta kalle shi tace.
"Ya malikk kayi wanka ga ruwan wanka nan na haɗa maka."
A narke tayi magana dan ta fahimci da rigima ya dawo inta biyeshi haka zai tisata a gaba yana kallan ta,harya bijiro da bukatar shi,dan taga gab yake,juyawa tayi zata fito aiko ya riƙo mata hannu,tsaye tayi takasa waigowa ji tayi yana mata tafiyar tsutsa asaman dogon wuyan ta,har ya iso gabanta ba tareda yace mata komai ba,yafara zuge mata riga,da sauri ta rike aiko ya marairaice fuska yana girgiza mata kai,wani irin kwarjini yai mata dan dole ta zuba mashi ido haka ya cire kayan jikin ta kaf sannan ya zare sarkar wuyan ta,koda yai tozali dana fulanin ta wata irin nauyayyar ajiyar zuciya ce ya sauke ita kanta saida ta kalle shi a hankali ya gangaro da hannun shi ya aza saman cikin ta daya fito sosai dashi yana shafawa, ita ganin ya fara sauya salo hakan yasa tace.
"Ya Malik muyi wanka mana."
tattaro jarumtar shi yayi ya ɗauke ta aiko suka fara wankan su cikin so da kauna danko soyayya iya soyayya ansha ta kafin sugama wankan su,haka suka fito manne da junan su,nan sukayi shigar cikin wani Yadi ash color sai ratsin zaiba iri ɗaya suka saka ita tata gownt ba kaɗan suka bada color ba,haka ta kamo hannun shi suka fito falo sannan ta fara bashi lunch da kanta har saida ya ƙoshi haka sukaita firar su ta masoya masu tsantsar ƙaunar junan su.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Sarki Abdullahi ne zaune a cikin fadar shi anata fadanci kowa ne yana faɗar albarkacin bakin shi,musamman kan yanda zasu canza tsare tsaren Masarautar tasu ta Waisu takoma akan tsari da shari'ar islama,Lamamin fa'da ne sai Magatakarda da sauran malaman su,suketa kawo hukunce hukunce na addini Magatakarda da sauran manyan fa'da yana rubutawa in ya gama sai aba Sahamaki ya mikama Sarki Abdullahi yasa hannnu daga bisani Sahamki ya buga mashi hatimin Waisu haka sukai tayi basu sukabar fa'da ba sai da aka kira sallar la'asar baki ɗayan su suka ɗunguma zuwa Masallaci.
haka rayuwa ta kasance cikin Masarautar Waisu komai yana tafiya bisa tsari gwanin burgewa.

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

Bayan kwana bakwai a Masarautar Daborah ranar ne akayi baikon Yarima Yazid shida gimbiya Zahara'u, sai Lurwan da gimbiya Bilkisu ɗiyar galadiman Daborah tareda baikon Yarima Huzaifa aka haɗa rana ɗaya duk za'a ɗaura masu aure,ranar farin ciki wajen su bai faɗo kowa yanata sakama lamarin albarka.

Bayan sati biyu da baikon su Yazid, lokacin kuwa cikin gimbiya Bahijja ya shiga wata tara cur, ba karamin kulawa Sarki MalikusSaif yake ba gimbiya Bahijja domin kullin suna tareda junan su,saidai in zaije fa'da sannan suke rabuwa da junan su shima badn yaso na,dan shakuwar da sukayi ko ada basuyi kwatan taba,kullin kara so da kaunar junan su suke,abin gwanin burgewa,yau dinma tare suke cikin shiga ta alfarma ba inda suka wuce sai sashen Maigirma Matawalle suka kai mashi ziyara acan suka tadda su Huzaifa sai gimbiya Zahara'u da matar Matawalle,zama sukayi akai ta gaisawa ana rahana cikin so da kaunar juna,gimbiya Salsabila ce tace.
"Yata ya kamata ki daina fita haka ko tafiya mai nisa kinga kinyi nauyi."
ita dai sunkuyar da kanta tayi ƙasa sannan tace.
"toh Ummi."
"aikuwa dai Ummi kwara tabi mana ɗa a sannu a daina tafiya mai tazara."
Cewar gimbiya Zahara'u tayi maganar a sifar zolaya.
Matawalle ne yace.
"Kada ku takurama Yata ai anaso a dinga motsa jiki,kuketa wani ɗanku toni ta 'yata nikeyi."
dariya suka saka baki ɗayan su, ɗan jim kaɗan suka tashi suka yima Matawalle sallama sannan suka tafi gidan Waziri Dammur suka gaida shi,haka aka karrama su, ranar da haka sukaita ziyara gidan dangi ,sannan suka tafi gidan su Bahijja aiko suka iske Abdulmajid a gida ba karamin daɗin ganin yaran nashi yayi ba,danko Binta sai tarairayar yarta takeyi ranar haka suka wuni gidan su Bahijja saida aka kira la'asar sannan suka tafi sashen Kangiwa a can suka iske Sarauniya Zulaiƙa,lokacin Kangiwa ya fito zai tafi masallaci gaisawa sukayi da ƴartasa, sannan suka wuce masallaci da Sarki Malik.
Itako Sarauniya Zulaiƙa rungume yarta tayi sukayi cikin ɗaki suma suka yi sallah haka Kangiwa suka dawo sallah suka zauna da ya'yan nasu cikin so da kauna danko Bahijja na kwance ta ɗaura kanta bisa cinyar Sarauniya Zulaiƙa itako sai rirritata takeyi tanai mata tausar kafarta tanajin tausayin yar tata da haka Bahijja tayi bacci ba ita tashi sai yamma likis, saida sukayi dinner sannan sukaima iyayen nasu ban kwana suka tafi gida,ranar ko Sarki Malik yasha shagwaba sai cewa takeyi kafar ta kugunta shiko sai riritata yakeyi hartayi bacci,can cikin dare jikin Bahijja ya tashi lokaci guda naƙuda ta tasar mata a kiɗime Sarki MalikusSaif ya farka duk ya ruɗe rungumeta yayi itako tafara ruri tana cewa.
"Ya Malik zan mutu wayyo Allah marata!"
a ruɗe ya janyota jikin yana murza hannun ta a hankali, wani irin tausayin tane yaji ya mamaye mashi zuciya, haɗe kanshi da nata yayi yana buso mata sanyayyen iskan bakin shi yace.
"Sannu Kanwar Malik Allah ya sauke ki lfy gimbiya ta, daure kinji tawan."
ɗaga mashi kai tayi a hankali kuma taji naƙudar ta ɗan lafa mata saidai baki ɗaya jitake kamar zata mutu, sake manna ta yayi jikin shi yace.
"Kanwar Malik sannu ki daure kinji bari inkira inna Mairo tazo ta taimaka maki kinji Hayati."
"to Ya Malik da zafi wlh,wayyo cikina,marata."

dafata yayi yafara yimata fiffita da mafece duk yagama ruɗewa yace.
"yi nishi matata sannu daure kinji gimbiya ta."
Ya ida maganar a raunane ,itako duk tagama haɗa gumi dan azaba sarke hannun su yayi cikin najuna sannan yafara yimata addu'a cikin kofi ya tofa ayatul kursiyu, fatiha kafa bakwai sai addu'ar Allahumma lasahala ilamaja'altahu sahalan wa'anta tajalil'huzna izashshi'itas salahalan,ya tofa zuwa lokacin kuwa tayi nisa da kyal take nishi ba abinda take kira sai lahaula walakuwwata illabillah sake game hannun su yayi shima duk yai zufar kamar shike labor ɗin kafa mata kofin yayi alamun tasha,sha tayi saidai idanun ta a rufe suke still tana nishin naƙuda, shiko kamar yai mata kwalla lokaci guda nakudar takara rikiciwa a kiɗime yace.
"Sannu kanwar Malik insha Allah yanzun zaki haihu."
Itakam bama tajin shi jitayi cikin ta ya yamutsa mata ta da karfi tace inallahi wa'inna ilahir raji'un cikin ikon Allah saiga Bahijja ta sintilo kwakkwan ɗanta santalele dashi,yanyara kukan da yayi hakan yasa Sarki MalikusSaif ya buɗe idanun shi da suka kaɗa sukayi jajir dasu dan rikiɗa da fargaba,wani irin farin ciki ne ya lulube shi daya ga gudan jinin nashi yana ta kuka a ruɗe ya matsar da yaron gefe,ji yayi takara damkar shi da karfi tayi wani uban nishi wanda yafi na farko still bakin ta na ambatan sunan Allah, kara rungumeta yayi yace.
"Sannu kin sauka lfy gimbiya ta bari inkirawo inna Mairo, da sauri ya fito zuwa falo ya haɗu da Jakadiya wadda zuwa yanzun bata nisa dasu da sashen su saboda tunanin haihuwar Gimbiya Bahijja,yanda taga Sarki Malik hakan ba karamin ruɗata yaiba bata jira cewar shi ba ta maye mashi baya suna shiga cikin ɗakin idanun suka gane masu yan jariran ta,ta kara sunkuto kyakyawar budurwar ta jajir da ita, da sauri Jakadiya takarasa wajen ta,shiko Sarki Malik mutuwar tsaye yayi dan yai mamaki ashe ashe Hayatin shi yan biyu ne zata haifa,baisan sadda yai sujudur shukur ba yana godema Allah (SWT), itako Jakadiya shiga tayi wani ɗaki ta ɗauko kayan haihuwa tayi

Please Login or Register in order to submit comment