Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka dan taɓa yana maijin kaunar dan nashi a cikin zuciyar shi.....


Itako Bahijja tana komawa gida kwantawa tayi tana mamakin yanda Yarima duk ya sauya mata lokaci guda aranta ko cewa tayi kodai yana cikin ɓacin rai ne, wata zuciyar ce tace. ''Miye damuwarki kedai tunda kinsamu ruwa ai shikenn tana cikin tunani taji an taɓata da sauri ta zauna tana kallan mahaifin ta murmushi ta sakar mashi tace. "Abba harka dawo."? "Eh najiraki baki dawo ba Allah yasa ba wani abun kikayi ba." da sauri tace. "Abba ba abinda nayi narasa wajen da ake dibar ruwan shine na shiga lambu ashe na Yarima ne." da sauri yace. "Ke ko Bahijja ba kiga yanda wajen yakeba baiyi kama da inda bayi ke shiga ba, kikiyaye." "toh Abba shine yabani ruwan ma na diba." murmushi yayi yace. "Allah sarki Yarima yanada kirki saidai ki daina fita sai kinsan wurare." "toh Abba kasan abinda yafi burgeni." "Aa ƴata minene fadama Abban ki." "Abba Masarautar nan ta burgeni sosai, musamman wajen wannan takobin wai minene anfanin ta.?" cikin kulawa yace. "tarihin takobin Barri yanada mahimmanci a cikin wannan Masarautar shike nuna karfi da iko na Daborah ta ɗauki saman da shekaru dubu huɗu da kafuwa a cikin Masarautar nan." cikeda mamaki tace. "Wai ai akwai kyau abin, Abba yau naga wasu maguna masu kyau sun burgeni." cikin kosawa yace. "Na Yarima Malik ne shike kiwon su, kinga ƴata kiyi hidimar gaban ki bansan ace ga abinda kikayi kinji ƴata.?'' kaɗa kai tayi tace toh Abba." tashi yayi ya tafi wajen aikin shi ita kuma ta fita cikin turakar bayi ta shiga gidan Ladidi zata duba ta kasancewar bata lafiya.

A sashen Saifulislam kuwa fitowa yayi cikin shigar kamala ta manyan mutane masu kima da daraja farar jallabiya ce ya saka sai bakin himari da bakaken takalma na Saki irin na Sarauta tafiya yake cikin nutsuwa duk inda ya gifta sai bayi sun gaishe da manyan mutanen Masarautar Daborah ba inda ya nufa sai sashen matar shi yana isowa Sarkin kofa mai kula da shige da ficen Sashe Sarauniya Zulaiƙa ne yai ma shi barka da zuwa, ya bude mashi kofa sannan ya shiga cikin katafaren falon ta wanda ya gaji da tsaruwa da kayan alatu irin na gidan Sarauta bayin da ya iske cikin falon ne suna ta aikace aikacen sune suka zube kasa cikin kulawa suka gaida shi, kai tsaye wani corridor yabi wanda zai sada shi da dakin matar tashi, yana isa ya murda kofa da sallama ya shiga isketa yayi tana karanta Alqur'ani mai girma da gani kasan ta gama sallah ne zama yayi harta karasa sannan ta shafa addua'a tashi tayi ta naɗe sallaya a hankali ta karaso har gaban shi ta zauna cikin girmamawa wanda macen kirki kema mijin ta Sarauniya Zulaiƙa ta gaida mijin ta, ya amsa cikin so da kaunar matar shi, ɗan shiru ne ya biyo baya daga bisani ya kalleta cikin kulawa yace. "Ummu Malik tun jiya naso inzo inganki da kaina kasancewar nike neman wata alfarma daga gareki, shiyasa bansa aka kiramin keba kinsan ance zuwa da kai yafi aike." murmushi ta sakar mashi bisa yalwatattar fuskar ta mai kwarjini da haiba, dan karya kanta tayi kadan tana mai rike tafin hannun mijinta tace. "Haba Abu Malik wace bukata ce wannan dahar zakace kai zakazo kasameni da kanka karka manta fa kalkashin ikonka nike kuma bautar aure nikeyi Ya Abu Malik wannan wace irn buka tace kake nema a wajen matar ka.?" ɗan shiru yayi yana tunanin yanda zata ɗauki maganar tashi saidai baida zabin da ya wuce yayi mata maganar cikin sanyin murya yace. "Ummu Malik inasan ki yarje ma ɗanki Bahijja tayi mashi hidima kamar yanda ya bukata." shiru Sarauniya Zulaiƙa tayi cikin kankanin lokaci idanun ta suka sauya tana maijin zafi a ranta dan ta tsani abinda zaisa ɗanta yai mu'amala da tsatson Jafar ita kanta da Binta kema hidima tanayi ne dan ta dinga musguna mata, gashi Saifulislam shine yazo mata da wannan bukatar mai tsananin girma a gare ta, jitayi ya murza hannun ta a hankali sannan ya sake cewa. "Ya kikace mata ta.?" faɗawa tayi saman kafadar shi tana mai maida ajiyar zuciya tace. "Banda wani iko ko yunkurin jayayya da umirnin mijina tunda haka kake bukata na amince, sai dai ina da nawa sharadin kuma ba wanda zan sanar mashi shi sai Bahijja.!"
wani dadi yaji duk da yasan halin matar tashi da wahala inba wani mugun tsananin zata ɗaura ma Bahijja ba amman ya fiso su dinga cika ɗansu burin shi a rayuwa cikin kulawa yace.
"Shikenan hakan yayi ba damuwa mata ta, kinsan dalilin da yasa na damu abar Bahijja taima Malik hidima."? Kaɗa kanta tayi alamun aaa, cikin so da kaunar ta yace. "Saboda mucika mashi burin shi tunda muke da Malik bai taɓa neman wata alfarma agremu ba sai wannan sama da shekara sha huɗu kenan ya ka mata muci ka mashi alkawalin shi wannan shine dalili."
murmushi tayi wanda ita kadai tasan mi takeji a ranta tace. "Badamuwa miji na nida Malik duk mallakin kane yanda kace haka za'ayi." cikin jin dadi yace. "Allah yaimaki albarka matata mai sharemin bakin cikin raina." da ameen ta amsa nan sukaci gaba da firar su cikin kaunar junan su da tausayi har marece yayi sannan yai mata sallama ya tafi, yana tafiya tasa aka kira mata Bahijja.


Gimbiya Zahara'u ce saman cinyar gimbiya Salsabila tana ba yar tata labari mai dadi sai murmushi takeyi cikeda shagwaɓa Zahara'u tace. "Ummi nifa gaskia ina cikin damuwa a raina." ɗago fuskar ƴar tata tayi cikin damuwa tace. "Mike damunki har haka.?" sake marecewa tayi sannan tace. "Ummi gaskia ina kaunar Yarima." cikin kaɗuwa tace. "Wane Yariman? Yarima Yazid ko kuwa...katse ta gimbiya Zahara'u tayi da sauri tace. "Haba Ummi wace irin magana kikeyi Yarima Malik nike so kuma shini ke kauna har a cikin raina Ummi." murmushin karfin hali tayima ƴar tata tace. "Amman kinsan halin Malik kina ganin zai amince da wannan zancen.?"mikewa tayi cikin kisisina ta fara juyi a gaban Ummin tata sannan tace. "Ki dubeni fa Ummi daga sama har kasa kema kinsan ba yanda za'ayi ace Malik zaice bai sona nifa tuni naga alamun soyayya ta a cikin idanun shi." girgiza kai tayi tana mamakin hali irin na Zahara'u amman sai tace. "Shikenan ba damuwa sai ki sanar ma da Abban ku nasan zaiyi wani abu akai." rungumeta tayi tace. "Yawwa Ummi haka nike sonji nagode Allah yabarmin ke." "Ameen ƴata...

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

A Masarautar Waisu kuwa Sarki Haishir ne zaune a saman kilisar shi anata fadanci kowa yana bada shawara akan abinda suka sa gaban su, Sarki Haishir ne yace. "Daman ina san in sanar maku da cewa akwai cin kasuwa da za'ayi a Kasuwar Zursu dake yammacin Masarautar Daborah zanso Sarkin taska da uban bayi da su hallari kasuwar dan siyo mana bayi da zasu kula da wannan Masarautar tamu, kunsan munyi asarar rayukan jaruman mu ba musan iyakar suba dan haka nikeso kuje kusamo mamu nagar tattun bayi masu karfi dan cimma wani buri namu na musamman wanda kowa keda shi a cikin zuciyar shi ya kamata ku fara shirin tafiya daga nan zuwa jibi ina fatan Gurfanai ya taima keku kuma ya baku nasara." da amin kowa ya amsa sannan Sarkin taska ya tafi neman Sarkin bayi dan sufara shirin tafiya Kasuwar Zursu.....

**********************************

A Masarautar Daborah kuwa koda yar aiken Sarauniya Zulaiƙa ta isa gidan Abdulmajid iske Bahijja tayi kwance tana bacci, ba kowa cikin gidan da alama suna wajen aikin su, zuwa tayi ta tafara bubbuga ta jitayi ana bugata a cikin bacci, a hankali ta fara bude idanta ta sauke su a kanta da sauri ta tashi tanai mata kallan ko lfy, ganin yanda Bahijja ta kafeta da idanun ta, masu saka mutun kushu'i cikin da burcewa tace. "Daman Sarauniya Zulaiƙa ke kiranki yanzun nan." wani irin daram taji gaban tane ya fadi dakewa tayi tace. " ai bansan inane sashen nata ba."cikeda mamaki baiwar tace. "Muje mana sai innuna maki." mikewa Bahijja tayi hakanan takejin faɗuwar gaba sai fat fat gaban ta keyi har suka isa sashen Sarauniya Zulaiƙa bata kara cewa komai ba, da idanun ta tabi sashen Sarauniya Zulaiƙa tana mamakin irin tsaruwar shi musamman ginin wajen daya kawatu da korayen ganye ga sai kamshi wajen keyi na damina a hankali ta shiga cikin falon kanta kasa take jefa kafarta da takejin duk tai mata nauyi, tunda Bahijja ta shigo Sarauniya Zulaiƙa ta kafeta da idanun ta masu firgita wanda ake kallo mamaki takeyi yanda tai wannan girman kamar yar shekara sha takwas a duniya, ita ko Bahijja hakanan taji jikin ta yana bata ana kallan ta a hankali ta ɗago kanta sukayi ido hudu da Zulaiƙa ganin irin kallan da take jifarta dashi ne yasa tai saurin sauke kanta kasa, harta karaso gaban Sarauniya Zulaiƙa dukawa tayi kasa ta sunkuyar da kanta sannan tace. "Allah yataimaki uwar gijiyata kiranki ya sameni Allah yakara girma da nisan kwana."
itako a watse tace aranta kaga munafukar yarinya da iya zance dake zaki yanke kwanan nawa, a zahiri kuwa kallan kaskanci taci gaba da wurgama Bahijja ita dai kanta na ƙasa ta kasa ɗago kanta ta kalle ta, ji sukayi an ajeyi faranti yadan yi kara da sauri Sarauniya Zulaiƙa ta kalli Binta a kaskance tace. "Bakida hankali ne zaki saki faranti haka so kike ki fasaman kunne ko me.?" a daburce tace. "Tuba nike ranki shidade bansan ya kubu cemin ba." itako Bahijja rufe idanta tayi ganin ana wulakanta mata uwa a gaban idan ta ganin halin da Bahijja ta shiga yasa Sarauniya Zulaiƙa tace.
"Sakara dake jahila bace mani da gani kada in halbaki." koma wa tayi gefe tana kara bata hakuri sai satar kallan Bahijja takeyi tana tsoron zuwan da tayi wajen Sarauniya aran tako cewa tayi Allah dai yasa yarinyar nan ba zuwa tayi nema naba aiko da na shiga ukku na, tunkan ta ida sakar zucin da takeyi taji Sarauniya Zulaiƙa tacema Bahijja......



_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*



_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم




Episode 47&48



"Ke wama kike.?" a ɗarare tace. "Bahijja!"
ta ida maganar kirjin ta na dukan ukku ukku.
Cikeda gadara Sarauniya Zulaiƙa ta kalleta ta watsar sannan tace. "Miyasa kikeson ki dinga shiga rayuwar Yarima? Ko har yanzun bakisan banbancin dake tsakanin ki dashi ba.?" wani irin faduwar gaba Bahijja taji jikin tane ya fara kakkarwa cewa tayi. "Ranki shidade nasani ni baiwar sace...wani irin raza nannan mari ta kwaɗama Bahijja cikin tsana tace. "Uban wa ya faɗa maki kece baiwar Malik ko daman kinsan zaki fara yi mashi hidima.?" wasu zafafan hawaye ne masu dumi suka wanke fuskar Bahijja, cikeda da shakkun Sarauniya Zulaiƙa tace. "Ranki shidade ba wanda ya faɗa mani nasan duk wani bawa dake cikin Masarautar nan Yarima na iko dashi Allah ya huci zuciyar ki."
tsaki tayi a zuciyar ta ko cewa tayi, wannan algungumar yarinyar badai iyayi ba da iya magana kamar Akku jaraba, mtsw wannan wane irin masifane? A zahiri ko cewa tayi. " ki bude kunnan ki da kyau kijini.?" a sanyaye tace. "Allah yataimakeki hankali da jina suna gareki, ganina ne kaɗai ya gagara kwar jinin ki Allah ya kara maki girma."
"daga yau zaki yima ɗana Malik hidima saidai kisani inada sharuɗan da zan gindaya maki."

Itako Bahijja al'ajabi ya addabe ta tana mamakin wane irin abune har haka sai kace ita tace sai taima ɗan nata hidima yanzun wane sharadi za'a bata Allah yasa kada acutar da ita, ji tayi tace. "Kullin ranar duniya, kitabba ta karfe bakwai kina sashen Malik kuma bance ki fara aiki ba har saiya fito sannan zaki fara gyara mashi dakin shi, sannan ki tabbtar kin kula da abincin ɗana kamar ranki, kuma karki kuskura ki bari doguwar magana ta dinga haɗaki dashi saboda bai san takura, keko da ganin ki zakiyi naci kamar mayya, sannan dole kisan abinda ze taɓa mashi zuciya dan ki kiyaye, sannan kisa aranki duk abinda ya samu MalikusSaif dake zanyi koke saboda kece mutun ta farko da zata fara yima Malik hidima a matsayin baiwar shi, inaga kilan kwakwalwar ki na dauka.?" jinjina kai Bahijja tayi tana mamakin wannan lamari taya zata iya irin wannan hidimar, haɗa ido tayi da Umman ta, taga tanai mata alamar tayi magana, da sauri tace. "Insha Allah zan kiyaye ba zaki sameni da karya sharuɗɗan da kika faɗi mani ba."
wani shu'umin murmushi Sarauniya Zulaiƙa tayi tana mai jinjina kai, sannan ta kara da cewa. "Kitabbatar duk safiya kafin kije Sashen Yarima sai kin biyo tanan, hakama idan kin tashi daga aiki idan zaki wuce gida." sake rankwafawa Bahijja tayi tace. "Umirnin ki abin tunkaho agareni zan kasance mai biyayya agreki uwar gijiyata." cikeda gadara da izzah tace.
"Kin kyauta ma kanki yarinya, zaki iya tafiya." godiya Bahijja ta kuma yi sannan ta tashi duk ranta ba dadi tana kallan mahaifiyar ta sai dai ba damar suyima junan su magana, a haka ta tafi sai zugin marin da tai mata takeji yana ratsa ta, kamar wadda aka fara mari a ranar haka ta dingaji harta koma gida ta zauna tana tunanin halin da zata shiga a cikin Masarautar data kasan ce abun alfaharin ta kuma mahaifar ta, wasu kwallane taji sun fara bin kuncin ta da sauri ta share, tashi tayi ta ɗauro alwalla tafara sallah.


Shiko Malik tunda ya tashi hakanan yake jin gaban shi na faduwa kamar bashi ba ya rasa abinda ke mashi dadi baki ɗaya jinshi yake kamar bashi ba, kwance yake saman tamfatsetsen gadon shi yana ta juyi, ga kasala da duk ta da baibaye shi, addua'a yafara yi can kuma sai yaji bacci ya fara ɗaukar shi, can cikin bacci yaji sallamar Huzaifa a cikin karamin falon shi, bude idan shi yayi a hankali, tashi yayi zaune kamar marar lakka ya zuro kafar shi kasa, toilet ya shiga ya wanke fuskar da kanshi sannan yafara tsnewa da karamin towel, fitowa yayi zuwa falon ya tsaya bakin kofa ya harde hannu daya saman daya yana kallan Huzaifa, jin kamshin turaren sane yasa Huzaifa ɗagowa ya kalle shi wanda harya zamar mashi jiki kamshi ne yake na musamman ya wanci da haka ake gane MalikusSaif yana waje musamman idan kana mu'amula dashi, murmushi ya sakar ma Malik din juyawa yayi yakara komawa cikin bedroom din shi hakan yasa shima Huzaifa ya shigo ciki suka zauna bakin gado shiru ne ya biyo baya kowa yana sake sake a cikin ranshi, Huzaifa ne yace. "Wai mike damun ka nagan ka sai a hankali.?" sake ya mutsa fuska Malik yayi kamar baisan maganar yace. "Bakomai." ganin ya bashi amsa a takaice ya fahimci yau baijin yan magana, sake cewa yayi. "Bahijja tafara yi maka hidima kuwa.?" kaɗa kai yayi alamar Aa, sake cewa yayi. "Miyasa kake boyeman damuwar ka Yarima.?" a hankali yace. "Koda baida anfani kaji.?" ɗan ɗaga kafaɗa Huzaifa yayi sannan yace. "Hakan ba damuwa bane abokina." mikewa tsaye MalikusSaif yayi yace. "Koda ace ana neman shiga lamarin ka akan abinda baka da tsarin shi a rayuwar ka.?"
mikewa Huzaifa yayi ya dafa kafaɗar MalikusSaif yace. "Mikenan abokina, ina fahimce akwai abinda akeso ayi maka dole, mike faruwa har haka nasa komai ya wuce."
"hmmm Huzaifa kenan Ummu kesan inyi aure bayan banda wannan tsarin a halin yanzun." cikin jimami Huzaifa yace. "Hakan ya dace sai dai ya kamata ka duba wadda ta dace da rayuwar ka." kallan mamaki MalikusSaif yaima shi sannan yace. "Kaga mubar wannan maganar batada anfani a garemu shiyasa nace zata ɓata mana lokaci."


➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Washe gari da safe tun karfe shidda da rabi Bahijja tagama shirin ta cikin kayan su na bayin Daborah, ita da Umman ta suka fito sai Abban ta atare suka shigo cikin Masarauta inda Abban ta yai masu sallama sannan ya tafi wajen aikin shi, suma Sashen Sarauniya Zulaiƙa suka wuce kamar yanda ta umurci Bahijja suna shiga cikin sashen nata lokacin ma Sarauniya bata tashi ba, itako Binta cigaba tayi da aikin da takeyi kmar kullin ita kuma Bahijja samun waje tayi ta zauna tana jiran fitowar Sarauniya Zulaiƙa, ji tayi wani kafcecen mutun ya tsaya bisa kanta a hankali ta ɗago ta kafesa da idanun ta masu matukar haske da sheki, cikin kaushin murya yace. "Kwanta." mamaki ya kama Bahijja tace. "Kamar ya in kwanta?." jitayi ya zabga mata bulala ajikin ta da sauri ta mike tana sosa inda ya duketa, cikin mugun ta yace ta kwanta aiko fir taki daman ita ta tsani duka, sake shauɗa mata yayi cikin zafin rai yace.
"Sarauniya ta bada umurni ke har kin isa kikiyin biyayya."
kallan Umman tayi wanda duk abinda ke faruwa a gaban tane cikin tausayawa taima Bahijja nuni data duka haka kuwa akayi saida yai mata bulala goma, sannan yace taje wajen aikin ta kuma inta taso saitazo nan kafin ta wuce gida, rausayar da kanta tayi alamun toh dan intace zatayi magana tabbas ɓacin rai zaisa ta yin kwalla, haka ta tashi a hankali take tafiya duk damuwa ta dirar mata a cikin zuciya tana cewa haka ake nufi za'a dinga yimin kullin kenan, batai aune ba taji ta banki mutun baya tayi zata faɗi da sauri taga Yazid ne dukawa tayi ta gaida shi sannan tafara bashi hakuri, yalwaccen murmushi yayi mata yana mamakin mi Bahijja zatayi sashen Yarima, saidai bai tambayeta ba, amsa gaisuwar ta yayi sannan yace bakomai, godiya tai mashi cikin sanyin jiki ta isa wajen mai kula da shige da ficen sashen MalikusSaif gaida shi tayi sannan tace.
"Daman Sarauniya ce ta turoni ni zan dinga kulawa da aikin Yarima Malik." kallan ta ya sakeyi sannan yace. "Kin tabbatar da hakan dan shiga sashen Yarima bada dalilin ba zai jazama maki gaggarumar matsala." cikin sanyin murya tace. "Na tabbata daga umurnin Sarauniya ne." cikin gamsuwa ya wage mata kofa ta saka kai tana shiga taji wani irin dausayi mai dadi yana ratsa mata sassen jikin ta tunda ga kafarta har kwakwalwar ta, lumshe idanun ta tayi tana bin falon da take ciki da wani irin kallo ganin kayatuwar wajen da haduwar shi ya gaji dajin kayan alatun more rayuwa ga kilissai na alfarma iya ganin ka, a tsoro ce take tafiya taga wata hanya da alama nan ne hanyar da zata sadaka da dakin Yarima MalikusSaif, cikin sanɗa take tafiya har ta iso taga wasu dakuna guda ukku duk a rufe, tana san ta bude su tana shakka tasan duk inda yake tabbas yana bacci, cikin karfin hali ta tura ɗaya ga mamakin ta ba kowa a cikin dakin hakan yasa ta shiga duk da ba wani datti dakin yayi ba, amman haka tafara kakkaɓe dakin shiga tayi toilet din dakin ta fara wankewa jitayi an bankaɗo dakin a tsorace ta fito daga bathroom din ganin Jakadiya hakan yasa ta duka ta gaida ta, bude wata wardroff tayi da alama bawani anfani ake da itaba, daukar kayan aiki tayi taba Bahijja sannan takara jamata kunne tace.
"Ki nutsu kisan abinda Yarima keso da wanda baiso ina fatan kinji abinda Sarauniya ta faɗamaki.?" da sauri ta rausayar da kanta sannan tace. "Eh naji." taɓe baki Jakadiya tayi ta tafi Sashen Saifulislam domin duba bayin dake sashen nashi ita ko Bahijja cigaba da aikin ta tayi saida ta tabbtar da tagama gyara ko ina na dakin sannan tayi turaren wuta tagama ta rufo dakin haka ta shiga wanda ke kusa dashi nan ma ta gama gyarawa, tana zuwa wanda ke kallan su sai taji faduwar gaba ta tabbata Yarima yana cikin wannan kuma ya zama dole saita gyara shi, a hankali tafara tura kofar gaban ta na dukan tara tara da sauri, rufe idanun ta tayi sannan tayi sallama cikin siriryar murya, ta shiga sai dai bata ga kowa ba, batai wata wata ba tafara gyaro kewaye, tafito ta kwashe wata alqabba da tagani saman kujera ta linke jitayi kamar motsi hakan tasa kara duba gadon still bata ga komai ba saidai wani bargo mai ɗan karen taushi da laushi zuwa tayi tafara janye bargon a hankali idanta na saman glass din madubi tana kallon kanta a ciki, shiko Yarima baccin shi yake mai rai da lafiya jiyayi kamar ana ja mashi bargo, a hankali ya fara bude idon shi cikin gafin nama ya fusgo hannun ta ya janyota da karfi aiko ta kwaɗa ihu jinta jikin mutun shiko jin muryar mace saida ya tsora ta bai san ya rufe mata baki ba da hannun shi a hankali ya ida bude idan shi tan garan sai kan fuskar Bahijja, itako tagama tsurewa da sauri ya janye hannun shi, ita kuwa direwa tayi ƙasa,jikin ta na rawa ta sadda kanta kasa tana kyakkyarwa jitake kamar zai iya dukanta dan har ga Allah bata lura da mutun a kwance ba, sake sunkuyar da kanta tayi cikin zazzakar muryata tace. ''Allah ya huci zuciyar shugabana kayi hakuri bansan da....ɗaga mata hannu yayi ya kara haɗe fuska yaci magani a ranshi kuwa yana mamakin yanda akai har Bahijja tashigo cikin dakin shi ko hakan na nufin Ummu ta amince tai mashi hidima? a kasan zuciyar shi kuwa wani irin dadine ya ratsa kowane sashe na jikin shi yarasa dalilin dayasa idan yaga Bahijja kusa dashi yakejin nishadi a ranshi kodan yana tausanta ne oho? yau burin shi da ya dade dashi shekara da shekaru kenan zai cika yau Bahijja ce zatai mashi hidima, itako ganin yakara ɗaure fuska taji wani shakkar shi ya dirar mata a zuciya ko kallan shi takasa yi ga tsoro ya kama ta, jin shirun yai yawa gashi bai sallame taba balle taje tayi uzurin gaban ta yasa a hankali ta ɗago kyakkyawar fuskarta aiko idanun su suka sarke dana juna, wani irin dam taji gabanta ya buga da sauri ta sake sunkuyar da kan nata shiko karfin hali yayi ya sauko saman gadon yai kamar bai ganta ba, a jikin shi doguwar jallabiya ce coffe brown, haka ya tako ta gefen ta ya wuce buɗe wardrof dinshi yayi sai kuma ya rufe, itako sake satar kallan shi tayi still suka hada sake haɗa ido, zata sadda kai kenan taga ya nuna mata bathroom da kallo tabi toilet din dan tagane manufar sa, a hankali ta mike ta haɗa mashi ruwan wanka, sannan ta fito ta sake dukawa tace. "Ranka shidade nagama haɗa ruwan." baice mata komai ba ya shige bathroom, itako kamar jira take har sauri takeyi tafara gyaran gadon, shiko Malik bai rufe kofar ba yana kallan ta tana laying bed, murmushi yayi wanda baisan yayi shiba sannan ya rufe kofa ya shiga danyi wanka, danko Bahijja tanaji ya rufe kofa tayi ajiyar zuciya wani irin dadi ne ya mamaye mata cikin zuciya tana mamakin yanda take shakkar Ya Malik dinta har haka,shima ya sauya mata da wannan tunanin ta cigaba da aikin ta a nutse tana gamawa tafita daga dakin duk jikin ta yai sanyi.....



_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 49&50



Yana fitowa banɗaki ya duba baiga Bahijja ba, ɗan taɓe baki yayi zama yayi inda zai kimtsa jikin sa, tsane ruwan jikin shi yayi da wani lausasan towel daga bisan wuyan shi har kan kirjin shi, sannan ya fara shafa mai a bisa kyakkyawar fatar shi mai tsantsi da tafshi ga sheki tana tayi harya gama mulke jikin shi da mai, mai ɗan karen kamshi, yana gamawa ya ɗauki turaruka ya feshe jikin shi dasu, a hankali ya tashi ya isa wajen wardrofe din shi dake jikin bango kamar baisan budewa cikin nutsuwa ya bude ta, da idanun shi masu haske da sheki

Please Login or Register in order to submit comment