Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Umman ta, koda tagama komawa tayi gefe ta zauna bacci ne ya kwashe ta, koda Yarima Haishir ya shigo cikin ɗakin da Bahijja ke bacci, zama yayi gefen ta, yana ta kallan ta kamar ya haɗeta haka yakeji ko kaftawa baiyi, gyaran muryar da yaji ne yasa shi waigawa ganin mahaifiyar shi, tana mashi wani irin kallo a sheke, cikeda gadara tace.
"Kawani tsareta da kallo mine abin kallo wajen wannan yarinyar mai kama da aljana.?"
shidai baice komai ba, ya cigaba da kallan Bahijja, itako gimbiya Ƙamariya ta gama kulewa da karfi takaima Bahijja duka tace.
"Tashi munafuka kina baiwa zakizo ki samu waje ki kwanta tashi daga yau sashena zaki koma kinai mani hidima." a firgice ta mike tana murtsika ido ganin gimbiya Ƙamariya,yasa ta dukawa tana gaida ta, dan a tunanin ta itace Sarauniya Zulaiƙa duk da taga ta canza mata kaman ni, wani mugun kallo ta kara watsama Bahijja sannan tace. "Kika wani tsareni da mugayen idanun ki kamar na mage tashi ki fita." da sauri Bahijja ta fita falo har tuntuɓe takeyi a cikin zuciyar ta ko cewa tayi wannan wace irin kaddara ce, ina zanga Ummana!.
wata baiwa ce tagani zata wuce da sauri taje tace. "Dan Allah inane Turakar bayi."? Mamaki ne bayyane a fuskar baiwar a fusace tace. "Kinji wata banzar magana ni zaki cema haka, nan bamu da turakar bayi, saidai sansanin bayi in nan ne muje inkai ki, a ɗarare tabi bayan ta, jin ankira sunan ta.
hakan ya tabbatar mata mai kiran ta tasan bai wuce Yarima Haishir, tana zuwa ta zube gaban shi, tace. "Ranka shidade, kataimaka kasa akaini Wajen Umma ta, kaga nan cikin gidan Sarauta ne kada Sarauniya Zulaiƙa tasake kamani a wannan wajen."
tausayin ta yaji yace. "nan ba Masarautar Daborah bace, sannan Umman ki bata nan, dan haka kiyi hakuri ki zauna a matsayin ki na baiwar mahaifiya ta kamar yanda ta bukata, saidai ki sani na kawoki nan Masarautar dan wani buri nawa dan haka nan da wani lokaci zakisan komi."
Wani irin matsanancin faɗuwar gaba ta dirar ma Bahijja lokaci guda.

Shiko tafiya ya fara ko a jikin shi, ji yayi tarike mashi kafa a kiɗime tace.
"Ka rufaman asiri dan Allah kada ka cutar dani ba haka mukayi da kaiba."
dukawa yayi yace.
"Ki rike addinin ki, kinga wannan Masarautar ba addinin mu ɗaya dake ba dafatan kin fahimta."? Sake fashewa da kuka tayi, ji tayi andaka mata tsawa da sauri ta mike a ruɗe gimbiya Ƙamariya ce tace.
"Ki sameni a sashen na zakiyi mani aiki."
wucewar tayi itako Bahijja sake fashewa da kukan tayi, shima haka ya tafi yanajin dadi yau gashi ga Bahijja a cikin Masarautar Waisu.......


*Masarautar Raifasu*
Da marece Sarki Baidulƙais ne yazo wajen su Yarima Malik dan duba yanda suka kwana koda ya shigo iskesu yayi zaune, shima zama yayi suka gaisa sannan yace. "Bakina ya kuka kwana inafatan baku da wata damuwa dai."?
Lfy lau muka kwana ba abinda ke damum mu mungode da kulawa."

ɗan jinjina kai Sarki Baidulƙais yayi alamun gamsuwa sannan ya kalli Yarima Malik yayi yace. "Dan saurayi bakasan magana ne."?
Shiru Malik yayi yaki magana sai kallan shi yakeyi saida Huzaifa ya taɓo shi sannan yace. "Eh bansan hayaniya ne."
Murmushi Badulƙais yayi irin na manya har zaiyi magana sai ga Jakadiya ta shigo.
Dukawa tayi tace."Ranka shidade, Sarkin yaƙi na san ganin ka." gyaɗa mata kai yayi hakan yasa ta shigo dashi yana zuwa ya gaida su sannan yace. "Ranka shidade kaf Jaruman mu sun bin cika baki ɗaya kewayen Raifasu basu ga Bahijja ba kuma ba alamun ta." da sauri Baidulƙais ya mike duk zufa tagama wanke shi, sai zagaye yakeyi sannan yacema Sarkin yaƙi "kaje kasa Jarumai su shirya aje duk inda za'a dubo Bahijja a nemo mani ita, kasan wacece Bahijja a wajena? na rantse da gurfanai zan iya rasa komai dan inga Bahijja ta dawo a kalkashin ikona.!"

Angama Sarki mai dole sannan ya juya da sauri ya fita, dan cika umurnin Sarki Baidulƙais , shiko Yarima Malik mamaki yakama shi yanda yaga Sarki Baidulƙais ya damu, kuma mike tsakanin shi da Bahijja? da har zai ɗaga hankalin shi dan ta ɓata!
ban kwana Sarki Baidulƙais yai masu sannan ya fita rai ɓace. shiko Malik magana yafara yima Huzaifa cikin fushi yace.....



_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 5&6




"Huzaifa ya kamata mu fitoma Baidulƙais a yanda muke, mu yake shi saboda rashin kulawa a ce har ya bari aka ɗauke Bahijja.!"
numfasawa Huzaifa yayi sannan yace. "Haba Yarima bai kamata ace mun yaki Baidulƙais ba duba da shima baisan inda Bahijja take ba duk da akwai ganganci saidai kasani yakar Baidulƙais zai maida hannun agogo baya musamman a wajen Sarauniya, sannan hakan zai kara saka Bahijja cikin uƙuba da tashin hankali karfa kamanta Bahijja bata da ƴanci, abin da ya kamata shine zuwa gobe mukama hanya mutafi tunda mun tabbatar da Bahijja bata cikin wannan Masarautar,ba anfanin zaman mu daga nan sai mutafi neman Bahijja shine mafita amman kai mi kace."?


Cikeda gamsuwa Yarima Malik yace. "nima nayi wannan tunanin dalilin da yasa kaga nikeson mu yaki Baidulƙais dan in ɗanɗana mashi kuɗar shi akan wahalar da Bahijja da yayi saidai kasani wlh kuwa inhar na cika MalikusSaif saina dawo da Bahijja hannuna a duk inda ta shiga cikin faɗin kasar Gambia, sannan da hannuna zan dirkake Baidulƙais da duk wani abun da yake taƙama dashi.!" cikeda ƙwarin guiwa Huzaifa yace. "Kwarai kuwa kayi gaskia hakan ma yayi ina goyon bayan ka ɗari bisa ɗari."


Juyowa MalikusSaif yayi yana kallan huzaifa cikeda takaici yace. "saidai banga anfanin tafiyar muba gobe mizai hana mubar Masarautar nan yau din nan."?
"Bayin mu da aka garƙameta a cikin gidan yari fa su ba zamu taimake suba."? Cewar Huzaifa.
da wata irin kakkausar murya Malik yace. "Kodan su tabbas zan dawo Masarautar Raifasu in fanshe su, yanzun dai nafison inga Bahijja ta dawo a kalkashin ikona, kafin intafi zanso in sake ganawa da Jakadiya na fahimci ba abinda batasani ba akan Bahijja."

"hakane bari insa aimaka kiranta." fitowa Huzaifa yayi wani makimancin falo ya hangi wata baiwa tana aiki, kiranta yayi sannan yasa ta kira mashi Jakadiya, tashi tayi daga dukiyar da tayi sannan ta tafi, shima komawa yayi wajen Yarima suka cigaba da shawara dan nemawa kansu mafita



Masarautar Waisu....



Bahijja ce kwance saman simintin dakin da aka bata ita da wasu bayi guda ukku, ba abinda takeyi sai tsantsar tunani da ya addabi rayuwar ta, tambayoyi tafara jefo ma, kanta tana sakar zuci, tace
Yanzun ni Bahijja daman ba wajen iyayena za'a kaini ba? Ashe wannan mugun yariman daman zalintata zaiyi? Minene ribar kawoni nan? Kuma mi zan mashi? Nashiga ukk ga uwar nan tashi wai ni zan dinga yimata hidima, yanzun shikenan ni a aikin bauta zan karata bani, nan bani can kamar wata ranwa, ya zanyi da raina nasan ba yanda zanyi in gudu daga wannan Masarautar tabbas dana gudu....haka ta dinga sake saken zuci tana hawaye, jitayi anda fata a firgice tadawo daga dogon tunanin da ta ninkaya, ɗago jajjayen idanun ta tayi ta aza a saman fuskar wata matashiyar baiwa, jitayi tace taje Yarima Haishir na neman ta a sashen shi, jitayi baki lakkarta ta tsinke jikinta yai masifar sanyi batasan dalili ba, tashi tayi ta fita saidai tsayawa tayi tana tunanin ta ina zata fara neman sashen Azzalumin Yarima haka taimashi laƙabi, waige waige tafara gashi ba kowa baki ɗaya wajen kuma part ukku ne tarasa wanda zata shiga, rufe ido tayi tafara addu'a sannan ta shiga Part din dake kallan ta, tafiya ta dinga yi kamar wadda kwai ya fashema wa a cikin ciki a ɗarare take koda ta shigo wani makimanci falo wanda yagaji da haduwa da kayan Sarauta, nan ta tsaya tana sakar zuci nan zata tsaya ko kuwa shiga zatayi rasa mafita tayi hakan yasa Bahijja tabi wani ɗaki da yake gefen haggun ta tana shiga taji shiru, hakan yasa ta ɗan karasa daga ciki tana magana taga Gimbiya Ƙamariyya wani mugun kallo tabi Bahijja dashi ba shiri tayi baya kiranta Gimbiya Ƙamariyya tayi sannan ta fara jefama Bahijja tambayoyi. "Mikikazo yinan? Da haka zaki fara yiman aikin? Ko kuwa harkin samu damar shigo mani ɗaki kina baiwa marar ƴanci, da gani baki da hankali.!"


A tsorace Bahijja tafara kame kame sannan ta duka kasa tace. "Ranki shidade kimin aikin afuwa, bansan nan ne ɗakin kiba, kirana akayi shiyasa nazo nan."?
Cike da gadara Gimbiya Ƙamariyya tace.
"Waya kiraki ko ance maki Gimbiya Ƙamariyya ce ta aiko akiraki ne."? Da sauri ta girgiza kai sannan tace. "Aaa ance mani Yarima ke kirana." da sauri Gimbiya Ƙamariyya ta mike jikinta na rawa tace. "Wato daga zuwanki harkin fara bibiyar rayuwar ɗana ko."? Baki ɗaya mamaki yagama kama Bahijja a zuciyarta ko cewa tayi kamar ya bibiyar sa nike, buɗe baki tayi zatayi magana, taji Gimbiya Ƙamariyya ta wanka mata mari tace.
"Wato harma kinada ikon da zaki yiman gardama k? toh kashinki ne zai bushe sha sha sha." itadai hawaye kawai takeyi sannan taji Gimbiya Ƙamariyya tace. "Tashi kibani waje kidawo anjima dan jin irin aikin da zaki dinga yimani.


Itako Bahijja fita tayi ta sake tsayawa farfajiyar parts din saidai ta rasa inda zata shiga ga tsoro duk ya kamata tai zatan zata sake haduwa da wata kuma daban dan taga ƴan gidan Sarauta basu da imani da wannan tunanin ta tafi tana cewa, rana zafi inuwa ƙuna tafara tafiya kenan taji ance. "Ke ina kuma zakije da bakiyi niyar shigowa ba." tsayawa tayi taji jikinta nai mata wani irin zafi shikenan tasan ta shiga halin ha'ula'i a hankali ta juyo dan ganin mai kiranta.....


Yarima Haishir ne ya haɗe hannuwa ya kafeta da wani shu'umin kallo, maida kanta tayi ƙasa sannan ta iso wajen shi tsayawa tayi tarasa me zatace mashi, a hankali tace. "Bansan inda zan shiga bane.....katseta yayi yace. "biyoni." tsaye tayi tana bin shi da kallan tsana, waigowa yayi ya sake kallan, wani kallo ta aika mashi sannan tabi bayan shi wani ɗaki ya shiga, ita kuma ta tsaya bakin kofa yana shiga ya zaune gefen gado yana jiran shigowar ta shiru har ya fara gajiya, hakan yasa ya shiga bathroom dan watsa ruwa, har yagama ya fito, itako Bahijja da tagaji da jira juyawa tayi zata tafiyar ta.
shiko daga ya kara duba dakin bai ganta ba hakan yasa ya leka ya hango Bahijja harta kusa fita daga falon da take, wata baiwa ce yasa ta kira mashi ita, sannan ya koma cikin ɗakin shi yana tsane ruwan dake kanshi bada jimawa ba saiga Bahijja ta shigo tsaya wa tayi bata bata da niyar zama ko dukawa, wani murmushi yayi mai ɗauke da ma'anoni iri iri sannan yace. "Ke baiwa zoki shafa mani mai." yitayi kamar bata jishi, jin yanda tayi shiru yasa shi sake yimata magana. "Bakiji me nace maki ba."? Karasowa tayi duk tsoro ya addabe ta a cikin zuciya, muryar ta na breaking tace. "Banjiba gani." wani kallo ya bita dashi hakanan taji gabanta ya faɗi, mikomata kwallabar mai yayi yace. "Shafamani a jikina." itako kin amsa tayi tana mashi kallan tuhuma tace. "Waimi kake nufi dani kace zaka kaini wajen iyeyena, mi zaisa kasani aiki, a wane matsayi nike ciki a wannan Masarautar mikake nufi dani."?
Kallan mamki yake mata yanda take mashi magana son ranta sai kace ba baiwa ba mikewa yayi yana zagaye ta itako suman tsaye kawai tayi, bata gama tunanin da take ba taji ya salgafo mata wuya, da sauri ta banke shi ta koma baya tace.
"Kada kasake taɓamani jiki." murmushi yasa keyi sannan yace. "Kina baiwar kuma baiwa ta ko kinsan dalilin dayasa na kwatoki daga hannun mugayen mutanen nan."? Girgiza kai tayi alamar aa, cikin jin dadi yace. "Saboda ina sonki, tunran da nafara ganin ki wajen Sarki Baidulƙais naji na kwaɗata dake naji inason ki sance a kalkashin inuwata in ɗanɗani zumarki." wani mugun kallo tai mashi, shi kanshi saida yaji gaban shi yafaɗi amman ya dake, cikeda karfin hali Bahijja tace. "Ina neman tsarin Allah daga kaidin ka Yarima ba abinda zaka iya yimin sannan kasani ni ban sonka dan haka ni ba baiwar ka bace ka maidani wajen iyayena ko ka maida a salin inda ka ɗauko ni, sannan na tsane ka koda hakan yana nufin ajalina.....wanka mata mari yayi cikin fushi yace. "Kina baiwa zaki gayaman waɗan nan maganganun baza ni Yarima Haishir zaki cema haka tunda nike ko gardama baiwa bata taɓa yimin ba saike!
Dan haka kisani saina ɗanɗani zumarki, duka duka nawa kike da zaki mani gardama, in har kina son inbiki ta lalama ki tabbatar kin amince ki aureni shikenan kinga kinzama ƴantatta kuma Gimbiyar Waisu, ya kika gani baiwa ta."?



Wasu zazzafan hawaye sukai nasarar wankema Bahijja fuska ta rasa mizata ce ma Yarima dan bata shakkar gaya mashi bakaken maganganu a cikin zuciyar ta, dan data rayu ko ta mutu duk dayane a wajen ta, tasan dai kaddara ce ta raba ta da iyayen ta da Ya Malik dinta, saidai tagaji da yawan Masarautu da takeyi a matsayin ta na baiwa marar ƴanci, tanata sake saken zuci taji Yarima Haishir ya sake rungume ta jikin shi da karfi ta ingije shi saidai duk yanda taso ta kwace kanta ta kasa, jitayi yana neman fara shafar mata jiki da karfi ta sake tureshi go gezau daman ba kaya a jikin shi, baki ɗaya jikin Bahijja ne ya ɗauki mazari ta rasa yanda zatayi da Haishir batasan ta saki wata uwar karaba shi kanshi saida ya tsorata hakan yasa ya saketa da sauri tayi waje tana kuka tarasa yanda zatayi da rayuwar ta, Jakadiya ce ta faɗo mata arai da irin huɗubar da take mata a zahiri ko cewa tayi. "Wayyo Baba Jamra inama ace kina kusa dani ina bukatarki ya zanyi miyasa duka yan Sarauta suke azzalumai masu cin zarafin mata? Miyasa Bahijja batada sa'a a rayuwa! tabbas inama ace mutuwa nayi da na huta, inama ace banzo wannan duniyar ba, wayyo Allah na kakawo mani ɗauki, tabbas Babata kin faɗi gaskia da kika fayyace mani komi akan mutunci na, shine daraja ta!
Jitayi wata baiwa ta taɓata da sauri ta waiga murmushi taimata tace. "Nabaki tsoro ko? Kije Gimbiya Ƙamariyya tana kiranki a sashen ta."
tana gama faɗa mata sakon ta tafi,itako Bahijja tsaye tayi harta manta da ta haɗu da Gimbiya Ƙamariyya goge fuskar ta tayi sannan ta kama hanyar tafiya wajen Gimbiya Ƙamariyya.....


*Raifasu*
Koda kiran, bakin Sarki Baidulƙais ya riski Jakadiya, tahowa tayita samesu zaune a falo dukawa tayi ta gaishe su, Yarima Malik ne ya amsa mata a taƙaice sannan yace."Jakadiya bani labarin Bahijja da abinda kikasani dangane da Bahijja da kalar alaƙarki da ita."?
Kallan shi tayi tana nazari kuma tana bukatar ganin fuskar shi amman ba damar hakan buda baki tayi tace.....





Ƴar Mutan Kankia ce❣️


Share
Comment
And
Vote

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 7&8




"Bahijja haifar tane kawai banba na ɗauketa 'ya' itama ta ɗaukeni Uwa saidai baiwa ce ga Sarki Baidulƙais, sannan kuma yarinya ce mai tarin ilimin Addinin ta duk da tana baiwa hakan baisa ta fasa gabatar da ibadun taba, takanyi a boye tun inajin haushin ta ni kaina kasancewar ba addinin mu ɗaya ba, saidai zaman da Bahijja tayi cikin wannan Masarautar har zuwa yanzun da tabarta batai zaman jin dadi ba ko kadan kullin cikin azaba take da kalubale hakan yasa nike tausaya mata yarinya ce mai karancin shekaru bata wuce sha ukku zuwa sha huɗu amman tana da girman jiki hakan kesa anai mata kallan cikakkiyar budurwa, har mutuncin ta naimata barazana dan ma kariyar ubangiji da kulawar da Allah yasa nike mata da tuni labari ya canza, kaji labarin Bahijja."


Ajiyar zuciya Yarima Malik ya sauke ya naima Allah godiya da yakare Bahijja daga kaidin azzalumai jin yanda kowa yai shiru yana binta da kallo yasa Jakadiya ta kalli Yarima tace. "Minene haɗin ka da Bahijja?Allah yasa ba cutar da ita zakayi ba dan har nafara dana sanin gaya maka abin da nasani dangane da Bahijja.!"
takarasa maganar cikeda tsoro, kallan ta Malik yayi ya tabbatar da Jakadiya tana cikin alhini da rashin yarda akan su hakan yasa ya ɗebe mayafin daya rufe fuskar shi.

kallam kyakkyawar fuskar Malik Jakadiya takeyi ko kaftawa batayi ta rasa inda ta taɓa ganin shi bata san tace ba "tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya tsara halittar wannan kyakkyawan saurayi waye kai mutun ko aljan? miyasa kadamu da tambayar Bahijja na rokeka ka fiddani cikin kokwontan da nike ciki a halin yanzun.! "
hakanan yasamu kanshi da murmusawa wanda hakan yasa Jakadiya takara gayama ubangiji tana al'ajabin irin kyawun saurayin dake gabanta

Dan sauke sanyayyar ajiyar zuciya yayi cikin kamala yace.
"ni mutun ne kuma nazo nan ne dan in ɗauki Bahijja, nine wanda naturo bawan da Sarkin ku, ke nema har aka kama mani sauran bayi da Bahijja suna ansar horo, a cikin gidan kaso! a takaice sunana Yarima MalikusSaif ɗa ga Sarauniya Zulaiƙa uban gidan Bahijja." suma ne kawai Jakadiya batai ba, tasan makiyin Sarki Baidulƙais ne tabbas tasan anbar baya da ƙura saidai bata da tacewa tunda tagaya mashi komai karfin hali tayi tace.

"Ranka shidade na rokeka kada ka bayyana kanka a wajen Sarki Baidulƙais akwai damuwa zai iya sawa a halaka bayin ku dake cikin Masarautar nan.!"

Huzaifa ne yace. "Kada kidamu Jakadiya baki cancanci haka ba a wajen Yarima Malik ba, bai zo nan bane dan niyar ɗaukar fansa ga Sarki Baidulƙais ba, yazo dan ya dauki Bahijja, saidai hakan bazai samu ba, duba da baida masaniya akan ɓacewar ta."


Wasu hawaye masu ɗumi sukayi nasarar saukowa a saman fuskar Jakadiya gogewa tayi sannan taji dadin abinda Huzaifa yace,Yarima Malik ne yace.

"Naji kina ambatan addinin Bahijja minene dan gantakarki dashi."?

Sake share kwalla tayi sannan tace. "Eh na karɓi addinin Bahijja tun tana gidan Yari, saidai kusani nabarranta akan addinin da uban gidana Baidulƙais keyi, kaji hadina da addinin musulunci."
wani irin tausayin Jakadiya ne yakama Malik cewa yayi. "Ki kwantar da hankalin ki Jakadiya kisani zan dawo kema kuma bazan barki ba cikin wannan kazamar Masarautar fatana ki boye addinin ki kodan tseratar da ranki da kuma darajar ki, dan haka kici gaba da addu'a yau dinnan zamu tafi domin neman Bahijja."


Cike da jindadi Jakadiya tai masu Yarima Malik godiya sannan ta tafi tana karajin kewar Bahijja a cikin zuciyar ta....


A wajen Jaruman Daborah kuwa sunci neman Yarima Malik har sun gaji hakan yasa Sarkin yaki yacema Lurwan zai turashi da wani bawa su shiga cikin Masarautar Raifasu kilan adace ko su Yarima Malik na nan, haka kuwa akayi tafiya sukayi dan ganema idanun su abinda suke bukatar tabbtar wa, bazasu so ace sun koma ma Sarauniya Zulaiƙa ba babu wani labari mai dadi ba.

_Masarautar Waisu_

Koda Bahijja ta isa wajen gimbiya Ƙamariyya isketa tayi tasha ado ta tisa kayan marmari a gaba tanaci kamar bata bukata, tana isa ta duƙa takai gaisuwa, wani irin kallon tsana ta banka ma Bahijja sannan ta watsar tace.
"Ke baiwa minene ma sunan ki."? A sanyaye tace. "Bahijja"
Cikeda gadara tace. "koma yaya kike wannan damuwar kice, ance kinje dakin Yarima daga yau kijini da kyau karki kuskura inkarajin anga wulgin ki a sashen Yarima kina ji dafatan kin fahimta."?
Da sauri Bahijja tace eh. tana jin wani irin bakin ciki a kasan zuciyar ta bata gama tunani ba, taji gimbiya Ƙamariyya nacewa akaita lambu zasuyi aiki sannan zasu wuce madafa domin aikin Abinci daga yau shine aikin ki fatan kin fahimta ko baiwa."?

Kai ta iya ɗagawa, itako gimbiya Ƙamariyya wata irin tsawa ta da kama a. Bahijja tace. "Bakiji mi nace maki ba?"
A hankali tace."Naji ranki shidade."
A wulakance tace.
"Kika kafe da mayun idanun ki zaki tashi kibita ko kuwa ni zan kaiki da kaina?"
Girgiza kai Bahijja tayi sannan tace. "Aaa, tuba nike!"
haka Bahijja tabi mai kula da sashen gimbiya Ƙamariyya, haka taba Bahijja aikin da Gimbiya Ƙamariyya ta umurce ta.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
〰️〰️〰️〰️

~DABORAH~

Itako Sarauniya Zulaiƙa kuwa bata da aikin daya wuce galla zama su Binta ukuba kullin saitasa an dukesu anci zarafin su,yauma haka tasa Sarkin horo yasa wani karfe ya ɗaurema Abdulmajid hannuwa sannan aka azama shi wani katon dutsi a saman kirji, haka akaita dukan su, wai dan Yarima Malik yatafi neman Bahijja acewar ta tsafi sukai mashi shiyasa harya tafi neman baiwa!

ranar haka aka wuni ana ganama Abdulmajid azaba kala kala kamar ba ɗan Adam, itako Binta harta kasa ko kuka dan ba karamin jin azabar da Sarauniya Zulaiƙa tasa ake masu ba, sai gab da magariba a kasa Binta ta koma turakar bayi, shi kuma Abdulmajid cigaba da bashi horo akayi na musamman wani matsanancin kuka ne Binta ta fashe dashi maicin rai tana ganin yanda ake wulakanta mata miji hakan yasa taji bazata iya jurewa ba, ta tafi sashen Sarauniya Zulaiƙa iske ta tayi zaune anata yimata fiffita, tana zuwa ta zube kasa guiwowi bibbiyu tafara bawa Sarauniya Zulaiƙa hakuri tace.

"Ranki shidade tuba muke Allah ya huci zuciyar ki, kiyafe mamu abinda mukayi maki dan Allah kimana aikin gafara wlh bamu da masaniya akan tafiyar Yarima kimana aikin rai dan Allah ki sassauta ma mijina, akan wannan hukuncin kar inrasa shi shikadai ke gareni na rokeki uwar marayu Allah yakara girma da ɗaukaka."
koda Binta tagama neman afuwa wajen Sarauniya Zulaiƙa ka kace bada ita take ba ko kallan inda take batai ba kamar ba mutun ba haka ta watsar da Binta takai minti talatin bata ce mata komai ba, haka taita dukiya tana jiran taji abinda uwar dakin tata zatace amman shiru, kuma tanasan ta tashi saidai tana shakkun abinda zatace mata tasan hakan na iya zama laifi haka dai Binta taita tsugunno daga karshe haka Sarauniya Zulaiƙa ta mike ta ƙurɓi ruwa a bakin ta, ta watsa ma Binta a saman fuskar ta,
baiwar Allah Binta, godiya taima Sarauniya Zulaiƙa.
Itako cikeda izza tasa kafa ta ingije Binta, ta wuce a binta tayi cikin dakin ta, itako Binta murmushi tayi maiciwo ta fita jiki sanyaye tana gayama Allah SWT kukan ta kamar yanda ta saba tana kwalla masu zafin gaske, haka ta koma turakar bayi tanaji tana gani tabar mijin ta a wulakance an ɗaure shi

~RAIFASU~

Washe gari da safe Sarki Baidulƙais ne yazo wajen su Yarima Malik suka gaisa bayan sun gama gaisawa, Huzaifa ne yace ma Sarki Baidulƙais. "Ranka shidade ya batun baiwar kane, an ganta."?

Kallan shi Baidulƙais yayi yana girgiza kai sannan yace.
"Tayaya kake zatan za'aga Bahijja na tabbata ko shakka babu Sarauniya Zulaiƙa zatasa a ɗauke Bahijja tabbas na turamata sakona akan ɓatan Bahijja dan sai inda karfina ya kare akan Bahijja dan ta saɓa alkawari! ta manta da cewa Bahijja a kalkashin ikona take, ba a kalkashin ikon taba! dan haka yazama dole in yaki Sarauniya Zulaiƙa kodan kwato baiwata.!"


Wani matsiyacin kallo Yarima Malik ya aikama Sarki Baidulƙais, Huzaifa ne yace.
"Ni a nawa tunanin babu yanda za'ayi Sarauniya Zulaiƙa ta sace Bahijja kodai kanada wasu makiyan na daban ne."?


Murmushi Baidulƙais yayi, cikeda da gadara yace. "Karshen kiyayya itace gaba dake tsakanina da Sarauniya Zulaiƙa dan haka na rantse da girman gurfanai saina shafe tarihin ta musamman ɗan ta MalikusSaif na tsane sh, ban kaunar shi da

Please Login or Register in order to submit comment