Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyeta, ganin taki shiru ya hade bakin su yafara sarrafawa cikin kwarewa, aiko wasan yafara sauya salo, jikin ta yafara kakkarwa jin yafara maza mata bobs dinta yana saki nashi kadan kadan, kwantar da ita yayi ya yara shafa ko ina na jikin ta rike mashi hannu tayi, tana shagwaɓa sai takara zugashi haka yaita romancing dinsa son ranshi har saida ya samu gamusuwa sannan ya kyaleta duk da bai kusance taba amman yaji ya samu sukuni wanka sukayi sannan suka kwanta basu suka tashi ba sai kiran sallar la'asar, alwalla yayi ya nufi masallaci, ita kuma dakinta ya rakata sannan ya fita, ana idar da sallah aka fara biki, Shaidi kamar yanda Sarauniya Zulaiƙa ta shaida ma mutanen Masarautar Daborah.....

Ranar ba karamin shagali akayi ba, akasha walima kowa sai albarka yake sawa da fatan dace da zaman lafiya mai dorewa a cikin walimar ne Sarauniya Zulaiƙa taima Abdulmajid, kyautar gida a cikin Masarautar sannan ta basu hadimai mata biyu maza biyu, murna wajen mutanen ba abin fada bane, akayi addu'a kowa ya tafi gida cikin aminci da salama.

Koda Abdulmajid suka koma turakar bayi haka Saifulislam yasa akazo akaimasu rakiya cikin gidan nasu, dangin Abdulmajid da sauran abokan arziki sukai masu rakiya, harda Idris da Mairo sai Ladidi aka dawo sabon gida kowa anbashi dakin shi da mai mashi hidima, haka sukaita godiya dab murna.


Washe gari da safe Sarki Abu-Jalal ne yakira Sarki MalikusSaif da iyayen shi, ya shaida masu cewa.
"Abdulmalik abinda yasa nace kazo kaida iyayen ka dan in tunatar dakai daga abubuwa guda ukku na farko, Kaji tsoron Allah a kowane al'amari naka.
Na biyu ka kasance maiyin shawara da mutanen kwarai idan zaka zartar hukunci, komai kaskancin mutun watakil akwai darajar a da Allah yai mashi wanda kai ba kasani ba.

Na ukku kuwa shine karka dinga nuna fifiko ko banbanci ga al'ummar ka duk daya suke da bawa da mai yanci ko talaka da mai arziki ko kuma mai mulki kadauke su daya, kuma duk hukunci da yahau mutun duk darajar sa a zartar mashi dashi, koda kuwa kaine, kamar yanda ka fada Masarautar Daborah ta zama cibiyar musulunci da aiki da shari'ar musulunci, wannan shine tunatarwa da zanmaka ɗana a matsayin ka na adali, sannan zan gaya maka kalma ɗaya zuwa biyu tal.
Ka zama mai yawan lura da kaifin basira da aiki da ilimi, karka kasance mai yawan saurin fushi da yanke hukunci idan kana cikin bacin rai, daga karshe ka zama mai kula da talakawan ka wajen ganin sun samu abin da zasuci kar su kasan ce a tagaiyare, musamman marayu ka kula da lamuran maraya Abdulmalik ka zame masu uba kuma jigon su ka kula da lamarin maraya, Allah zai kula da lamuran ka, kuma zai maka jagoranci akan mulkin ka, inafatan Allah ya dafa maka Abdulmalik yasa tunanin d muka dade munayi ya tabbata akanka."

Wasu kwalla masu dumi suka sauka bisa fuskar Sarki MalikusSaif cikin dakewa yace.
"Insha Allah Abi zan kiyayye wadan nan nasihohin naka, nagode matuka Ya shugabana."

Jinjina kai yayi alamun gamsuwa sannan ya kalli Kangiwa da Matawalle yace.

"Ta yaro kyau take bata karko, dole ku zama masu kulawa da saka hannu da kwatanci akan lamarin danku."

"Gaskia ne kawu cewar Saifulislam.

Shima Matawalle murmushin karfin hali yayi yace.
"Insha Allah zamu dinga kulawa."

"Allah yasa cewar Sarauniya Zulaiƙa.
Sai kuma yace.
"Yata yau dinnan da azuhur zan koma mahaifata domin inkula d alummar da Allah yabani jagoranci akan su."

Fuska ta kwabe kamar zatai kuka tace. "Baffana sai inji inama ka zauna taredamu."
"Uhmm yar Baffa kenan ko ban tareda ku zuciya ta na taredaku 'yata kedai ki kula d yarki d kyau Allah yaimaku albarka."

"Ameen Baffa." ta ida maganar cikin mutuwar jiki kwalla na zirarowa a idanun ta.

"Abi zanyi kewar ka sosai, saidai ina kaunar ka a kullun."
Rausayar dakai yayi yace.
"Haka yake a cikin zuciya ta Sarki MalikusSaif dan Saifulislam jika ga Sulaiman na Salis, ina sonka dana, ke ka kiramin yar tawa mugana."

Murmushi yayi haka ya tafi sashen gimbiya Bahijja a zaune ya taddata tasha ado da kwalliya ta saka sarkar azurfa da yabata jitayi an rungumota lumshe ido tyi dan kamshin turaren sa kadai yasa tagane shi, kiss yaimata a goshi ya kawo bakin shi saitin kunnen ta cikin rada yace.
"Hayati."
"Uhmm."
Shine abinda ta iya furtawa.
"Muje zakiyi bankwana da Abi dina."
Mikar da ita yayi ya dauko alqabba pink color dayake kayan jikin ta light blue ne ya azamata bisa kaya sai murmushi suke ma juna hannu cikin hannu suka tafi sashen Kangiwa, sunzo shiga ta zame hannun ta murmushi kawai yayi da sallama a bakin su suka ida shiga zata zauna kasa Sarauniya Zulaiƙa tai sauri ta riko ra, kusa da ita ta zaunar da ita sai kunya takeji, a hankali ta gaishe su kowa ya amsa cikin farin ciki Sarki Abu-Jalal ne yace.

"Yata ya bakunta?"
Sadda kanta tayi kasa tana murza yan yatsun hannun ta, tace.
"Lfy lau Abi."

Sake kallan ta yayi yace.

"Toh Bahijja kinga yanda nauyi da girma yahau akan mijin ki, ina fatan zaki dinga daura shi bisa turba dan ya samu sauki wajen sauke nauyin dake kanshi."

''Insha Allah Abi zan iya kokarina."
Anutse tayi maganar.
Murmushin jin dadi Sarauniya Zulaiƙa tayi tace.

"Ai Baffa inaji a jikina Bahijja zata zama haske a cikin wannan Masarautar zata taimaka ma mijin ta sosai."

"Insha Allah kuwa Ummu Malik zasu inganta addini sosai a cikin Masarautar Daborah, Allah yaimaku albarka."

Cewar Kangiwa.

Galadima ne ya shigo da Yarima Dawud suma zama sukayi akaci gaba da hira, Sarki Abu-Jalal ne yaci gaba dacewa.

"Kai kuma saik kara sa hakuri a cikin zuciyar ka sannan ka kula da nauyin iyalin ka, Allah yaimaku albarka."

"Ameen suka amsa baki ɗayan su.

Yar fira suka dingayi sallamar Sarki Muhammad ne da Aisha ta katse masu firar su, kusa da Sarki Abu-Jalal ya zauna cikin kulawa yace.

"Yata aiko naji dadin ganin ki, dan muyi bankwana."

Da sauri ta dago kanta tace. "Abba tun yanzun zaku koma?"

Murmushi yayi yace.
"Ai mun jima sosai kinga akwai nauyi akaina kwara kuma mukoma."

Rausayar dakai tayi a kunyace tace.
"Hakane Allah yatsare yakaiku lfy, kuma naga sako nagode Allah yakara girma."

"Ameen ya rabbi, yata bakomai."

''Naso ku kara jimawa, saidai dole muyi maku uzuri."

Murmushi yayi jin Sarki Abu-Jalal yace.
"Gaskia kam dole muyima Abu Bahijja uzuri,amman kuma sai anjma zaku wuce ko?"

"Yanzun haka mungama shiri bayin muma suna woje mu suke jira."

Mamaki fal a ransu, musamman Zulaiƙa.

Sarki Muhammad ne yace.
"Daman jiya mahaifin Bahijja yazo mani da gaggarumar wata magana akan wata baiwa ta Saude, yace min kanwar matar shi ce Binta, sun rabune sakamakon samamen bayi da aka kawo masu suna kan hanyar dawowa daga fatauci, ya nemi alfarma da inbar Saude cikin ahalin ta."
Murmushi mai faɗi Saifulislam yayi yace

"Tabbas shekarun da suka shude ansamu wannan matsalar ankama mana fatake, kadan ne suka tsira, saidai kana ganin zaka iya barin Sauden a cikin ahalin ta."

Rausayar dakai yayi yace. "Mizai hana Kadimulislam? Karfa kamanta nasan daci da zafi na rashin zuriya, wannan dalilin yasa nace na yan ta Saude kuma zan barta cikin yan uwanta."
Kallan juna akayi tsakanin Saifulislam da Zulaiƙa jin abinda Sarki Muhammad yace, saiya tuna masu kashe ɗanshi Husbarulƙais, MalikusSaif yayi a wajen Yaki.

Cikin karfin hali Sarauniya Zulaiƙa tace.
"Masha Allah kayi kokari Allah yabar zumunci."

"Ameen ameen suka amsa baki ɗayan su.

Jakadiya Hajara da Saude suka shigo tare, zama sukayi, Sarki MalikusSaif ne yace.

"Alhmdullh munji dadin wannan lamari da yau kika samu yanci wajen uban gidan ki za'abarki cikin ahalin ki sai mukara godema Allah."

Wasu kwallan dadine suka rufe Saude share idanun ta tayi tace.
"Nagode ya shugaba na, dana samu wannan darajar agareka na samun cikakken 'yanci kuma zakabarni wajen dangina, Allah yakara girma da ɗaukaka."

"Ameen."
Cewar Sarki Muhammad.

Haka dai aka danyi bankwana duk suka mike zasuyi mashi rakiya, Saifulislam yace. "Abokina har yanzun kofa bude take inkana bukatar wani taimako musamman wajen wannan hatsabibin Sarrilƙus."
Murmushin jin dadi yayi yace.
"Inagodiya duk da har yanzun bamuji wani lbr ba, saidai in bukatar hakan ta taso zan sanar maku, Allah ya dauramu akan azzulumai makiya addinin musulunci."

Ameen ya rabbi cewar Matawalle. Rungume juna sukayi suka kara musabaha.

Itako Bahijja tana rungume da Ummin ta Jakadiya Aisha suna bankwana sai kwalla sukeyi,MalikusSaif kuwa nade hannun yayi ya sarkafe yana kallan yanda Bahijja ke kuka dan Jakadiya zata tafi irin rabuwar uwa da yarta, tausayin sune ya kama shi.

Haka suka dunguma sukai masu rakiya, sannan suka hada masu shatara ta arziki su Tasiu duk sun hau dawakan su, hakama Sarki Muhammad da Jakadiya Aisha suka kama hanyar tafiya Raifasu.


Haka kowa ya koma gida ba dadi dan sun shaku da Sarki Muhammad, sallar azuhur aka kira kowa ya tafi masallaci akayi sallah, sannan suka dawo sashen Kangiwa inda Sarki Abu-Jalal yagama kimtsawa kamar yanda ya shaida masu da azuhur zai tafi, shiyasa duk suka wuto dan su kara bankwana da Baffan su, haka sukaita yima junan su sallama, danko MalikusSaif harda kwallan shi, dan ba karamin so yakema Abi dinsa ba, haka suka fito shida jama'ar shi, sukayi masu rakiya kowa ya hau dokin shi, sannan suka tafi.

Ranar haka Sarki MalikusSaif ya yini jiki a sanyaye sai yakeji tamkar ya rasa wani muhimmin abune daga cikin jikin shi.


Bayan sati ɗaya Sarki MalikusSaif ne zaune a fa'da anata fadanci, Sarkin fa'da ne ya shigo tareda wani mutun aka gurfanar dashi gaban Sarki, kallan tsaf Sarki MalikusSaif yayima wannan mutumin sannan ya maida kallan shi ga Sarkin fa'da, cikin girmamawa Sarki fa'da yace.



_Ƴar Mutan Kankia ce ❣️_


Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 117&118



"Ranka shidade Allah yataimake ka, kayi bako yana bakin kofar fa'da yace aimashi iso."

Ɗan jingina kai Sarki MalikusSaif yayi ba yareda yace komai ba.

Sarkin Zagi ne yace.
"Sarki yaimaka izini Sarkin fa'da, fa'da bata cika saidaku, angaisheka Sarkin fa'da."

Tashi yayi bada jimawa ba, saigashi yadawo da wani mutun.

Baki ɗayan su, suka duka suka kai gaisuwa wajen Sarki.
"Sarki ya amsa."
cewar ɗanzagi.

Shiru ne ya gauraye fa'dar baki ɗayan ta na wucin gadi, sannan Sarki MalikusSaif ya kalli wannan mutumin alamin mike tafe dashi.

Kasa yayi da kanshi cikin girmamawa yace.

"Ranka shidade sakon ka, ya riskeni kwanakin baya da suka wuce, ka aiko mani da fadawa akan bayan mako biyu inzo insameka a fa'da."


Gyaran murya Sarki MalikusSaif yayi yace.
"Miyasa kakasance azzalumin shugaba wanda baida tausayi ga talakawan sa?"


Atake yasha jinin jikin shi, duk ya rasa abinda zaice sosa kai yayi yace.
"Ranka shidade tuba nike kaimin afuwa aikin shaidan ne!"

"Uhmmm kaine shaidan din ko? Ka anshema mutane gonakin su, ga cinye dukiyar marayu a hakan duk shaidan dinne? dan haka dole ka dandani hukunci daidai laifin da ka aikata."


Zuwa yanzun rudewa iya rudewa kam yayi ta, yasan kashin shi ya bushe, kara rankwafawa yayi ya dinga bada hakuri, tsawa Sarki MalikusSaif ya daka mashi ba shiri yai shiru jikin shi nata kyarma.


A hasala Sarki MalikusSaif yace.

"Dan haka baka cancani kazama hakimin Kurgu ba, dankai azzalumi ne, Hashimu, dan haka fa'da da Masarautar Daborah ta dakatar dakai da mulkin Masarautar Kurgu sannan ansaka maka tarar foam dubu talatin, kuma ansaka maka takunkumi ba inda zaka fita a cikin garin Kurgu daga nan zuwa jibi katabbatar ka kawo abinda fa'da ta umurceka."

Hawaye nata shatata a fuskar Hashimu haka yace.

"To ranka shidade angama, amman ina neman sassauci banda wadan nan kudaden da aka bukata."

Wani kallan tsana Sarki MalikusSaif ya watsa mashi dan ya tsani azzalumi musamman mai handame dukiyar maraya yace.

"Kasaida kadarorinka daman na haram ne ka tara."


Gefen shi Sarki MalikusSaif ya kalla yace.

"Shamaki ka aika mana sunan Lurwan yaci gaba da rikon garin Kurgu a matsayin hakimi."

"Angama ranka shidade, wani katan littafine ya dauke wanda ke dauke da kaf Masarautun dake kalkashin ikon Daborah, ya rubuta sunan Lurwan a jiki sannan ya buga hatimin Daborah, su Ciroma, Galadima, wambai, Dan buran duk sun saka hannu, sannan aka wakilta yan rakiya da tsohon hakimi suka tafi Masarautar Kurgu dan nada Lurwan kamar yanda Sarki MalikusSaif y umurta.


A halin yanzun ba abinda yake son gani irin ya saita Masarautar Daborah daga azzalimai masu handama da babakere.


*Masarautar Waisu*



Sarki Haishir ne a cikin wani dakin tsafi yanata wasu surutai barkatai ba kyan ji da sauraro, wata kwarya ce girke a gaban shi jini ne ciki keta watsalniya ga hayaki yana fita da tururi na zafi, duka dakin ya turnike da wannan hayakin ga surutan nashi sai karuwa sukeyi, wata iriyar tsawace da walkiyar tsafi aka buga har kayaiyakin dakin ba zubowa wani garsakeken mutun ne ya bayyana sai kyakyata dariya yakeyi bakin shi na fidda bakin hayaki, shiko Haishir yana bude idanun shi yaga wannan mutumin shiba mutun ba kuma ba aljani ba, saida ya firgita da zai gudu yaji maganar shi kamar aradu yace.


"Ina zaka Haishir kaifa na hannun haggun mune, kasn shine dakai ya rage mana dan tuni mukai tafatali da hannun dama mabudin alkhairi da nasara, a wajen mu kuwa bamu tareda alkhairi duk wanda yabimu ya ɓata muna tareda kai yan tawagar shaidan duniya tamuce lahira kuwa ko a gidan haya munraɓa!"

Hahhahhhhhahhhh!

Duk da Haishir shi ya kira wannan mutumin saida yaji kamar ya kece da zawo dan tsoro daya rufeshi bakin shi na kyakyarwa yace.

"Ya shugaba na aikata abinda kuka umurceni naji ba wani labarine ya matsu inga mun halaka wannan matsiyacin Sarkin."


"Hahhahhhhhahhhh! ta yaro kyau take bata ƙarko, ka kusanci gyatumar taka kenan.?"

"Eh eh nayi."
Kat kat haka jikin shi ke ɓari.

"Da kyau."
Cewar Sarrilƙus wanda yake canza halittar shi a take, yaune ya bayyanar wa Sarki Haishir a tsantsar sufar shi, amon maganar shi ce ta daki zuciyar Haishir.

"Dan haka mako mai zuwa zamuyima Masarautar Raifasu dirar mikiya mu halaka komai nasu, ashafe babin rayuwar Raifasu dasu da mayaudarin Sarkin nasu, dan Faihasu na hannun hagguna bai gajeshi ba."

Wani irin sanyin dadine ya ratsa zuciyar Haishir koba komai ya kusa ɗaukar fansar ran mahaifin shi wanda shine babban burin shi.

Shima dariyar karfin hali yayi yace.
"Tabbas da burina ya cika."

Wani garin magani ne ya gani a bisa hannun shi, a kidime ya waiga baiga Sarrilƙus ba saida amon maganar shi dayake ji yace.

"Kasha wannan sannan ka kara kusantar ta, shine tukwicin ka, daga nan zakaga yanda Sarki Baidulƙais zai zama tarihi, hhhhhhahhhahh."

Jikin shi na ɓari ya tafi ya rifo dakin duk ya hada zufa tako ina, yana isa sashen gimbiya Ƙamariyya yabata wannan maganin yaimata bayanin komai, daman itama gafalallace bata dauki alfashar da sukeyi ba wani abuba, haka suka aikata masha'ar su.


_Allah ka kiyashemu taɓewa duniya da lahira ameen ya hayyu ya qayyum🙏_


_Masarautar Daborah_

Akwana a tashi asarar mai rai yau MalikusSaif ya kwashe kwana sittin bisa karagar mulki, komai yana tafiya yanda ya kamata cikin tsari zuwa yanzun kuwa ansamu nasarori da dama a cikin Masarautar Daborah musamman harkar kasuwanci da arbakatun kasa wanda suke sarrafawa suna saye da siyarwa, hakan yakara daukaka darajar Masarautar Daborah ko ina ana shigowa cin kasuwa, sabanin da, da sau ɗaya kasuwar Zursu keci a cikin shekara.


A bangaren MalikusSaif kuwa zaune yake bisa lallausan kafat din dakin shi, shida sahibar shi, cikin tsantsar so da kaunar ta yace.

"Hayati ya kikejin jikin naki?"
Sake shagwaɓewa tayi tace.
"Uhmm Ya Malik kasala ke damuna duk banjin dadi."
"Sannu yar aljanna baby na, na wahalarmin dake ko Hayati."

Cinno baki tayi gaba takara narkewa jikin shi tace. "Uhmm nifa nacemaka banda ciki kaki kayarda."


"Uhmm nayarda yanzun muje in baki baby ko?"

Sake narke mashi tayi tana dan rigima tace.

"Uhmm da zafi fa nagaji bacci zanyi."
Maganan nata ya kwaikwaya yace.

"Muje sai inmaki tausa kiyi bacci ko tawan?"

Ta bude baki zatayi magana ya hade bakin su ya nufi bedroom da ita, saman bed ya shimfidar da ita ya rufeta da faffadab kirjin shi, cikin tsantsar so da tausayin Hayatin shi yafara sarrafa ta, slowly har saida ya kashe mata jiki likis sannan ya rabata da kayan jikin ta, ya dinga binta da salonsa iri iri, itama tana binshi da salo na daban haka suka ruda junan su daga nan suka lula duniyar masoya, ranar haka masoyan suka kara farantawa junan su kamar su hade junansu, atare sukayi wanka, ya shiryata tsaf cikin tattausan less royal blue shima yadine ya saka royal blue sai alqabba ta sarakai white suka feshe jikin su d daddan turare, a tare suka fita zuwa sashen Sarauniya Zulaiƙa, ɗaukar alqabba yayi white ya saka mata, hannun su sarke dana juna suka bi ta garden iska na ratsa jinin jikin su, har cikin sashen mahaifiyar tasu, suna shiga suka isketa tareda Binta suna tattaunawa da alama abune mai mahimmanci suke tattaunawa.


Koda suka ga yayan nasu wani irin dadine ya lullube su, da sauri Sarauniya Zulaiƙa ta mike ta rungoma Bahijja jikin ta, suka zauna bisa lallausan shimfida dake tsakiyar falon, cikin girmamawa suka gaida iyayen nasu itako Binta kunyar MalikusSaif ne ya cikata da yawa, cikin kula tace.

"Ɗana ya fama da jama'a?"

"Alhmdullh Umma, ya Abba."
"Yana gida lfy lau."

Sarauniya Zulaiƙa ce ta kalli yar tata cikin tausayawa tace.

"Sannu 'yata ya jikin naki."

Sunkuyar da kanta tayi kasa, aranta tace.
"Oh Ya Malik dan nadanyi ciwo har Ummu saida yafada mawa, a zahiri kuwa fadada murmushin ta tayi tace.
"Alhmdullh Ummu ai na worke."



Sake shagwaɓewa tayi ta jinjina kanta bisa kafadar Zulaiƙa tace.

"Ummu andafa mana dashishin?"

Murmushi tayi mai ma'anoni tace.

"Ehamana anyi 'yata da zan aika maki dashi sai gashi kun shigo, ai abinda kikeso shi za'ai maki."

Takarasa maganar tana kwantar da kan Bahijjar bisa cinyar ta, tace.

"Bari insa akawo maki."

"To Ummuna."

Kwalawa Mansura kira tayi saidai bata ansaba zata kuma kiran ta kenan sai suka tsinkayi sallama
Saifulislam ne ya shigo cikin falon, amsa mashi sukayi yanda yaga iyalan nashi cikin aminci ba karamin dadi yaji ba, musamman yanda yaga Bahijja da Sarauniya Zulaiƙa tamkar yar cikin ta haka ta maida Bahijja ba wani surukun taka a tsakanin su, shima zama yayi fuskar shi dauke da annuri ya kalli Bahijja dake ta sunne kai yace.

"Masha Allah 'yata jiki yai kyau Allah yakara lafiya."

"Ameen Abbuh."

Wasa da zoben gold dake hannun ta, tafara, shiko saifulislam cewa yayi.

"Ummu Bahijja mi aka dafa mana ne.?"
Itama cikin tsantsar farin ciki tace.
"Dashishine miyar ganye da kifi."

Murmushi yayi mai dauke da ma'anoni yace.
"Ummu Bahijja kenan abincin gargajiya aka tuno mana."


Fadada murmushin ta tayi tace.

"Yarka ce take son cin dashishi shine akai mata."

"Gaskia kam ta iya zaben abinci kuwa."

Itadai Bahijja murmushi kawai tayi tanajin dadin yanda surukan nata ke bata kulawa.

Haka kuwa Sarauniya Zulaiƙa ta kawo masu abincin da kanta, Mansura ta shigo masu da tiredin kayan marmari ta ajeye a gaban su.

Haka kowa yaci abincin cikin jin dadi musamman Bahijja dakeji kamar ta cinye dashishin dukkan shi ga cikin ta ya cika amman har yanzun tanajin shi'awar cin dashishin ture flat dinta tayi tana kallan Umman ta, murya a narke tace.

"Umma zansha madarar."

Itako Binta tana mamakin yanda Bahijja ke kwasar abinci sai kace wadda cikin ta ya kai wata biyar dinnan, duk da bazai wuce wata na biyu ba, miko mata tayi cikin wani cup din silver, amsa tayi ta kurba ta lumshe ido tana sha, sadda zatayi kurba ta ukku, batasan sadda ta matse hancin taba wani masifaffan amaine ya taho mata da gudu tayi toilet din falo haka ta dinga kyara amai kamar hanjin ta zasu fito, maye mata baya Sarauniya Zulaiƙa tayi ta taimaka mata ta kuskure bakin ta sannan suka dawo falon, sai sannu suke jera mata musamman MalikusSaif dakeji kamar ya hadiye ga wani irin tausayin ta
da suka rufeshi, kwantawa tayi kasan kafat din hawaye taji sun cika mata ido, ji tayi Ummu ta janyota jikin ta, tace.

"Sannu Yata Allah yabaki lafiya."

Hawayen sukai narasar zoboma ta tace.
"Yawwa Ummu na worke kinga kuma yau aman nan ya kuma dawo mani, dan Allah Ummuna ki bani magani ya tafi karya kuma dawowa."

Dariyace ke cin Zulaiƙa ta hadeta aranta kuwa cewa tayi.

"Su Bahijja badai yarinta ba, ke dake da karamin ciki ai laulauyi sai hakuri, azahiri kuwa cewa tayi.

"To Bahijja na yar Ummun ta, zan baki magani."

Takarasa maganar tana kallan MalikusSaif da yake zaune kamar andasashi tace.
"Kama ta taje daki tayi bacci kaga ta gaji da yawa."

Mikewa yayi kamar mai jiraya dagata ta mike tsaye suka tafi sashen su.

Shiko Saifulislam ajiyar zuciya ya sauke yace.

"Kinga rabo ko Sarauniya ta da raban muga jinin Abdulmalik.?"

Murmushin tayi tace

"Gaskia kam Allah dai yakara mata lfy ya raba lfy."

"Ameen ya rabbi, saidai kamar batasan cikine da ita ba ko?"

"Eh batasani ba, amman mijin ta ai yasani ina mamakin kodai bai sanar mata bane."

"Kila ina tunanin hakan nima."

Murmushi sukayi nan suka dinga labarin yanda komai na Daborah ya sauya, haka suka dinga jin dadi.


Koda su MalikusSaif suka koma gida suna shiga falo ya dagata sai bedroom, kwantar da ita yayi sannan ya rage mata kayan jikin ta, wani irin tausayin yaji bathroom ya wuce da ita yadan watsa mata ruwa masu dan sanyi sannan ya saka mata riga da sicket marar sa nauyi a tare suka kwanta bisa gado yasa hannun shi yana shafa lafaffan cikin ta, cikin so da begen abinda ke kwance a cikin nata yace.

"Sannu Norul Hayat babyn Ya Malik na baki wahala ko?"

Bari in maki addua zaki samu sauki."
"To tace mashi haka ya dage rigar tata ta dinga yimata addua bisa fatar cikin nata har wani irin bacci mai dadi yai gaba da ita, a hankali ya zame jikin shi a nata ya sake lullube ta da blanket ya tofa mata addua sannan ya nufi fada cikin tsantsar tausayin hasken rayuwar tashi, haka aka dinga fadanci amman kaf hankalin MalikusSaif na kan gimbiyar tashi.


Haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin aminci komai yana tafiya yanda ya kamata.

Bayan wata ɗaya cikin Bahijja ya shiga wata ukku kenan, zuwa yanzun kam laulayin ya rage sosai, bakaramin kyau cikin yaimata ba, tayi fresh takara haske gwanin burgewa, zaune take falon ta tareda Manaura hadimar ta, suna yar fira jefi jefi ita da uwar dakin tata, Bahijja ce ta kalli Mansura tace.

"Mansura wai nikam ina labarin Maimuna."

Murmushi Mansura tayi tace.

"Ranki shidade tana turakar bayi yanzun ta daina aiki."

"Allah Sarki, ya kamata kam."
"Mansura dauki kular abincin nan kije dashi gida kunci."

Godiya ta hauyima uwar dakin tata, cikin kulawa tace.

"Ki godewa Allah ai wannan niimar ubangijine."

"Hakane, Allah yakara lfy yasa ki haihu lfy uwar gijiya ta."

Murmushi mai fadi tayi dan taji adduar da Mansura taimata.

Sallama tayi ta dauki abincin ta tafi.


A Masarautar Raifasu kuwa Sarki Muhammad ne da ciroma sai ɗan buram da galadima sai dagaci suna tattaunawa akan tattalin arzikin Masarautar, sai sukaji wata iriyar kara ta karade falon Sarki Muhammad ga wani irin guguwa da ta addabi wajen duk da kasancewa falon rufe yake ko alamun kura baka gani komai tsaf yake, amman cikin kankanin lokaci falon ya gama hargitsewa, wata kibiyace aka halbo ta soke bisa kushin din da Sarki Muhammad ke zaune, baki daya wajen suka fara addua a hankali wannan guguwar ta lafa, sannan Sarki Muhammad ya dauki wasikar ya mikama ciroma ita, dake kusa dashi ansa yayi yafara karantawa.


_Baidulƙais kenan kana tunanin ni Sarrilƙus na manta dakaine inko har haka ne kayi kuskure dan haka kajini da kyau nan da mako daya zan darkake duk wani abu da kuke ikirari dashi maci amana, daga Sarkin Gamki."_

Murmushi yayi yace. "Hmmm kunji ko na fada maku Sarrilƙus baisan tausayi ba, kuma bai yafiya saidai ta Allah batasu ba, insha Allah mukeda nasara."

"Gaskia kam yacika azzalumi."
Cewar galadima.

Murmushin manya yayi yace. "Asa magatakarda ya rubuta ma Sarki MalikusSaif da Kangiwa wasika akai masu yanzun nan kar abata lokaci."


Bayan kwana biyu, Sarki MalikusSaif ne zaune a fa'da shida jama'arshi sunata bojet din

Please Login or Register in order to submit comment