Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaddarar ki, tun kina jinjirarki har zuwa yanzun."

tana gama fadar haka ta fita Bahijja na biye da ita tana kwalla, suna isa Sarauniya Zulaiƙa ta kifama Bahijja maruka har ukku tace.
"Ke wace jahilace miyasa baki fahimta zaki barman ɗana ko saikin rasa ranki, kuma ke harkin isa ki wulakan ta gimbiya Zahara'u." girgiza kai Bahijja tahauyi tace. "Ban son shi natsane shi, ni banson Yarima nadaina zuwa wajen shima baki ɗaya, dan Allah kitambaye shi na shiga ukuna dan Allah kada ku halakani.!" takarasa maganar cikin raunaniyar zuciya hatta gimbiya Salsabila taji tusayin Bahijja sai dai son zuciya yaha nata bayyana hakan itako Binta kuka takeyi harda shessheka, sawa tayi Sarkin bulala ya dinga shauɗama Bahijja duka tako ina, dukewa tayi tana kuka tana cewa. "Nace ban son danki kuma ban kaunar shi kurabu dani karku kasheni Umma Abbana kutaimaka mani zata kasheni.!"
sake wanka mata mari tayi tasa aka kaita gidan kaso aka rufeta duk jikinta yayi sahu na bugu sai kuka takeyi a gefen zuciyar ta kuwa tanajin ta tsani Yarima Malik a ranta


*Turkashi anayin ta, gashi dai Bahijja ta furta kalmar tsana wa Malik agaban Sarauniya Zulaiƙa, shiko MalikusSaif ba wadda yake so sai Bahijja, ya abin zaikaya, shin Bahijja dagaske ne ta tsani Yarima Malik har cikin zuciyar ta ko kuwa wahala ce tasa ta faɗin hakan? Muje zuwa my real fans inayinku fa irin 100% din nan*


Haka aka garkame Bahijja tana kuka ga wani irin zazzaɓi daya addabeta lokaci guda.

Koda Binta ta koma gida ko bacci kasawa tayi, shiko Abdulmajid yana ganin yanayin matar tashi sai dai baibi takanta ba, domin duk abinda yafaru yaji komai, cewa yayi ita tajama kanta, shiyasa bai nuna damuwar shiba, kukan Binta ne ya fara isar shi rai ɓace yace.

"Kin isheni d wannan kukan naki marar anfani." ɗagowa tayi da jajayen idanunta tace.
"Haba Abban Bahijja taya bazanyi kuka ba, kasan cin mutuncin da akai mata." wani wawan kallo ya aikama ta yace
"yimin shiru kema kinzama sakara kenan ko kashe Bahijja tayi ai ita tajazama kanta da ace ta tsaya matsayin ta da bata wulakanta ba, dan haka koda zata mutu ba ruwana da ita, sannan kika sake kafarki ta taka inda take da sunan ziyara ban yafemaki ba, kum ba Bahijja ba Yarima Malik saidai inban haihu da jinin Jafar ba."

Yanda taga fuskar Abdulmajid ba sauki yasata sauke ajiyar zuciya tana kukan zuci kasa kasa shigewa yayi dakin shi yana maijin zafin lamarin a cikin zuciyar shi.

Bayan wasu awanni su Matawalle ne suka iso cikin Masarautar Daborah ta kofar Kudu suka shigo ba inda suka sauka sai sashen Sarauniya Zulaiƙa, ta karbe su cikin murna da jin dadi tanaso taji daddaɗan labari,Yarima Malik ne ya duka ya gaida mahaifiyar tashi cikin girmamawa ba yabo ba fallasa ta amsa tana mai kaunar ɗan nata a ranta, bayan sun gaisa da Lurwan tai mashi barka da dawowa, waigowa tayi tana kallan ɗan uwan nata tace. "Yaya barka da dawowa." "yawwa"yace atakaice. sake kallan shi tayi da ma'anoni tace.
"Yaya ba wani labari ne." rausayar dakai yayi yace. "Akwai mana, amman anjima mu hadu sashen Kangiwa zamuje mu huta." cikeda gamsuwa tace. "Shikenan yayana Allah ya huta gajiya." ameen yace, sannan suka fita kowa yayi sashen shi.

Bayan sallar isha'i kamar yanda Matawalle ya faɗa haka kuwa akayi baki ɗayan su suka hadu sashen Saifulislam, cikin kulawa Matawalle yace. "Kangiwa munje sai dai ba abinda ya sauya domin kuwa basu dai daita kansu ba, ko kuma ince bai zaɓi kowaba a cikin dangin muba." shi dai MalikusSaif yana kasan kafat yanajin su, wani irin abune ya soki zuciyar Sarauniya Zulaiƙa wani irin kallo ta dinga jefama MalikusSaif, cikin ɓacin rai tace.
"karya kake Abdulmalik ace kaje har cikin Masarautar Runo ka kasa fidda mata, nidai nasan dangina ba munana bane, nan ma kaki 'yar uwarka Zahara'u mikake nufi wlh zan saba maka."
da sauri Matawalle yace. "Umurni daga Sarki Abu-Jalal yace abar Yarima ya zabi wadda tai mashi kinsan halin Baffan namu, nidai bani cikin wannan sabgar dan haka namu ido Zulaiƙa." mikewa tayi tace. "Miyasa Baffa ke irin wannan abun indai ni na haifi Abdulmalik wlh bashi ba baiwa kuma dole nan da sati ɗaya a ɗaura mashi aure da Zahara'u koda kuwa zai mutu.!"
kamar aradu taji sautin Saifulislam suna ratsa kunnuwan ta, jitayi jikinta ya mutu cewa yayi.
"Kinyi kaɗan Zulaiƙa duk duniyar nan ba wanda ya isa yaima ɗana auren dole Bahijja ya zaɓa kuma ita zai aura.!"

Buga table tayi dake gefen ta tace.
"Ban lamince ba Kangiwa ace ɗana magajina ya auri Baiwa." cikin ɗaga murya da ɓacin rai yace. "Waya gaya maki magajin kine? kyawun ɗa yagaji ubansa dan haka Abdulmalik bai gaji Sarauta ba, Fatauci ya gada kuma shi yasani dan haka ba ruwan. attajiri dan ya auri baiwa koda ba 'yan tattabace, kije can ki nemi wanda zai gajeki a cikin 'yayan dangi sannan ki aura masa 'yar Sarakai nidai ɗana baiwa yake so kuma dakaina zan 'yantata ya aureta sai dai inban haihu ga jinin Sulaiman ba."
Matawalle ne ya dakama Zulaiƙa tsawa yace.
"Baki da hankali ne mijin ki kike ɗagama murya? Ko kin haukace, kuma kin manta abinda Baffan mu yace, uban mu fane, anya Zulaiƙa baki so zuciyar ki da yawa ba? Ko kinmanta sumafa Bayin nan 'Ya'yane.?"
"Aaa Yaya a wajena bayi ba 'yaya bane dan basu cancani yanci ba,da ɗana ya auri baiwa gwara in mutu."
rai ɓace yace. "Shikenan tunda ba'a isa dake ba" ficewa yayi yabar wajen baki ɗaya, shiko MalikusSaif a hankali yace. "Ummu dan Allah ki kwantar da hankalin ki indai akan wannan zancen ne na hakura." mikewa Kangiwa yayi yace. "Ba hakurin da zakayi Abdulmalik inasan in gwadama uwarka halin duniya in bacci take yaka mata ace ta farka tunkan dare yai mata." cikin fushi tace. "Kangiwa kadaice ɗanka saiya auri baiwa ko? Sannan kace bazai gajeni ba ko? Nidakai mu zuba mugani." da sauri Yarima Malik ya rike mata kafa, da karfi ta warce kafar ta, cikin jin haushin shi tace. "Ka kuskura ka kara rikemin kafa ko naganka a sashena saina t.....a harzuke Saifulislam yace.
"Kika kuskara kikaima ɗana baki saina wankeki da marukan da bazaki sake ganiba a duniya sakarai dake marar tausayi da imani mai son zuciya tir da halinki Zulaiƙa."

nuna kanta tayi da mamaki tace. "Ni zaka mara Kangiwa.?"
"kwarai kuwa haukanki ko gigi yasa ki furta wata kalma marar dadi ga ɗana kigani, dan akan ɗana ba abinda bazn iya aikatawa ba." shi dai MalikusSaif ji yake kamar ya kurma ihu ganin iyayen shi na sa'insa akan lamarin, hakuri ya dinga basu, itako Sarauniya Zulaiƙa tafiya tayi har juwa takeji tana ɗibarta...

MalikusSaif ne ya daura kanshi bisa cinyar mahaifin shi baisan sadda yaji hawaye masu dumi na ɗiga a saman fuskar shiba, cikin kukan zuci yace "Abbuh dolena in hakura da Bahijja kaddara ta rabamu kuma kaddara tasa haka zata gama rayuwar ta cikin ukuba a matsayin ta na baiwa, Abbuh kayi hakuri da hali irin na mahaifiya ta, sannan kayafeman zanyi iya kokari na inga narabu da Bahijja kodan mahaifiya ta."

Murmushin manya yayi yace. "Yaro kenan da baka godema Allah ba akan ni'imar da yaimaka ba, wannan fa kamar jihadine Malik, saboda ta hanyar yin wannan auren da kake gani Allah zaisa mahaifiyar ka ta daina wani zalinci ta hanyar haɗa iri da bayi zaisa mahaifiyarka tasan kimar bayi harta ɗaukeso a matsayin 'ya'ya sannan su samu 'yanci ya kake ganin kalar wannan nasarar Abdulmalik?" shiru yayi a ranshi ko yace hakane kuwa sai kuma yace. "Aini bansan inaganin Ummu a cikin mawuyacin hali."
cewa yayi. "Komai zai dai daita Abdulmalik." rausayar dakai yayi alamar gamsuwa, cikin son ɗan nashi yace. "Kaje ka kwanta kahuta, sai dai inasan inasar dakai cewa Sarki Baidulƙais ya karbi addinin musulunci." duk yanda hankalin Malik yaɗan bar jikin shi saida ya nunajin dadin shi sosai, cikin jin dadin zancen yace. "Abbuh nan yazo ne ya anshi musulincin.?" girgiza kai yayi ya labartama shi abinda ya faru,wani irin fari cikine ya sake rufe Yarima Malik yana kara godema Allah da suka anshi addinin musulunci, kuma abin dadi ta hannun Bahijja, cewa yayi.
"Alhmdillh Allah abin godiya saidai muci gaba da addu'a Allah yakara tabbatar damu bisa hanya madaidaiciya" cikin so da shaukin da uba yakema ɗan nasa yace "Ameen Abdulmalik."tashi yayi yace "Abbuh zanje inhuta Allah yakara girma nagode da kulawa." murmushi mai fadi yayi yace. "Allah yaimaka albarka." "Ameen Abbuh cikin jin dadi ya tafi nashi side din..

Bayan kwana biyu a wajen Sarauniya Zulaiƙa kullin kalaman Saifulislam kedawoma ta sabo a cikin kunnuwan ta tasan inyai magana ba wasa gashi batasan yanda zatayi ba ta rasa mafita, shiyasa kullin take kara gallazama Binta a zaba hakama a gidan yari canma Bahijja bata tsira ba, da bala'in da ake gana mata

Sashen MalikusSaif kuwa yana zaune a cikin falon shi, saiga su Huzaifa da Yazid sun shigo da sallamarsu juyowa yayi yana kallan kofar shigowa, amsawa yayi ya maida kanshi kasa dan Allah yasani wani irin nauyin Huzaifa yakeji, samun waje sukayi suka zauna fuskar su ɗauke da annuri, Huzaifa ne yace...

"Haba MalikusSaif tare tace haka shine kayi tafiya dukan mu, ba wanda yaji ko labari kuma yau kwanan ka biyu da dawowa saida muka hadu da Lurwan yake cemana kundawo! anya tare yace haka.?"

Murmushin karfin hali yayi su kansu suna ganin Malik sunsan ya faɗa sosai tabbas yana cikin yanayi, cewa yayi. "Kayi hakuri Huzaifa wlh mugun nauyinka nikeji kaima kasan in lfy ya zanyi tafiya baku da labari, kunsan dole inyi tafiyar nan daku, gaskia bansan da wane ido zan kalleku ba, dubi yanda na guji kanwar ka Zahara'u kuma 'yar uwata taya zan iya gaya maku zanyi tafiya."
sauke ajiyar zuciya Huzaifa yayi yace. "Wlh Malik banrike da komai tabbas innace banji dadi na nayi karya, dan inna ga Zahara'u na kuka nakanji tamkar in taya ta, saidai nasan baka da maganin damuwar ta, saboda kaima irin wannan yanayin kake ciki, ko nine abinda kayi shine zanyi Abdulmalik kada kadamu." murmushi yayi yace. "Naji dadi daka fahimceni saidai nayi abin kunya na guji kwanwata yanzun haka so nike inhana kaina son Bahijja wlh nakasa Huzaifa." cikin tausayawa sukace. "Addu'a takobin mumuni itace mafita Yarima." kallan Yazid yayi yace. "Kayi hakuri Yazid tuna abinda naima Zahara'u gabanka shiya hana ingaya maka zanyi tafiya duk kunyar ku dajin nauyin ku ya addabeni."
"Haba Yarima mai adalci da sanyin hali karka damu insha Allah lamarinka da Bahijja alkhairi ne." rausayar dakai yayi nan sukaci gaba da yar firar su, kiran sallar magrib ne yasa suka tashi kowa yai alwalla suka tafi masallaci

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a cikin Daborah ba dadi musamman wajen Bahijja da iyeyen ta, sai Yarima Malik da yake cikin matsanan ciyar damuwa

Bayan kwana goma da wowar su, MalikusSaif kuma yai dai dai da kwanan Bahijja shabiyu a gidan kaso, Yarima Malik ne zaune bisa sallaya da alama yagama sallar walaha, a cikin falon shi yanata lazimi, jin anyi sallama yasa ya jinjina jikin bangon da yake a gefen hannun damar shi, Mairo ce ta shigo hannun ta ɗauke da kwaryar fura ta duka tana gaida MalikusSaif cikin girmamawa sannan tace. "Allah yataimaki magajin gobe furane Mai girma Kangiwa yace inkawo maka." murmushi yayi ɗan shi Malik mutun ne mai fara'a duk da bai fiyasan hayaniya ba, kuma shi baida girman kai, ba ruwan shi da matsayin ka ko kaskancin ka, zai iya sakarma kowa fuska cikeda annuri baijin komai, hannu yasa ya anshi furar yana cewa. "Sannun ku da kokari kice Abdulmalik ya gode."

Cikin jin dadi tace. "Kahuta lfy magajin gobe, har zata fita sai kuma ya kirawo ta dawowa tayi ta duka tace. "Ranka shidade gani."

A nutse yace."Wai ina Bahijja tunda na dawo bangan taba, ko bata lfy.?"
Shiru tayi kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace. "A gaskia Yarima yau kimamin kwana shabiyu kenan Bahijja na gida Kaso a kulle."

Wani irin daram haka yaji gaban shi ya yanke ya faɗi, inalillahi wa'inna ilaihir raji'un yace sannan yace. "Shine baku faɗaman ba?" "ranka shidade tayaya kasan ba wanda ya isa ya shigo sashen ka saida babban dalili." mikewa yayi yai gaba, bai kuma cewa komai ba, bayan shi tabi, ga wata iriyar yunwa yana ji, amman saiyaji ta tafi baki ɗayan ta, dan raban da yaci abinci mai nauyi harya manta saboda fargaba, direct gidan yari ya wuce masu kula da wajen ne suka zube suka kwashi gaisuwa, baiko ansaba ya shige ciki tareda sa mai kula da gidan yakai shi gun Bahijja, duk da Sarauniya Zulaiƙa ta hana kowa yaje gunta, amman kwarjini da haiba irin ba Malik yasa sun kasa yagama shi sharaɗin uwar gijiyar tasu, har bakin ɗakin ta da take kulle aka kaishi sawa yayi aka fiddo ta, a hankali ta fito idanuwan sune suka sarke dana juna da sauri ta juya mashi baya jin wani abu ya dira cikin zuciyar ta, matsowa yayi muryar shi na breaking yace.....




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 95&96




"Kanwarr Ma-li-kk mikikeyi nan!?" yanda yayi maganar take saida tsikar jikin Bahijja ta tamike tsaye wani yarrr yarr, sannan bataji zata iya kallan kwayar idon shi dan a halin yanzun jitake ta tsane shi a ranta ita kuma bata fatan taji tsanar mutumin da bai cancanci haka daga gareta ba.

Jin taki yin magana kuma da alamu kuka take dan yanajin sheshshekar kukan ta hakan yasa ya zagaya ta gaban ta yanda zaiyi facing ɗin face dinta, saidai yana komawa gaban ta, ta sake bashi baya gaban ta na duka fat fat fat da sauri da sauri wani irin abu yaji ya soki zuciyar shi data sake juyawa mi hakan yake nufi? bai sake kokarin sake binta ba saidai yace.
"Bahijjaah." yakira sunan ta yanajan kalmomin karshe girgiza kai tayi cikin muryar kuka tace. "Dan Allah Ya Malik katafi kabar wajen nan banson ganin fuskarka katafi ban bukatar wani taimako daga gareka wanda akayimin a rayuwa ta ma nagode Allah yabiyaka da aljannah."

Wani kara maganganun nata suka zame mashi a cikin kunnuwan shi sannan baiji zai iya nisanta kanshi da Bahijja duk da fatan shi kenan a halin yanzun, cewa yayi. "Kanwar Malik kada kice haka, kada ki hukunta Yayan ki akan laifin da ba nasa bane, ki daina wannan kukan Bahijja nasan koma miye daga Ummu ne, kiyafema mahaifiya ta."

Sai a lokacin Bahijja ta waigo tana kallan kwayar idanun MalikusSaif, wanda sun kada sunyi jajir, ita kanta saida taji wani iri haɗa idanun su waje ɗaya, sadda nata idanun tayi kasa still tears dinta na zuba a saman kyakkyawar fuskarta muryarta na breaking tace. "Ya Malik ina neman alfarma agreka."

Cikin tausayin kanwar tashi yace. "Faɗi inajinki kanwar Malik."

Murmushi tayi mai ciwo sannan ta duka kasa guiwowin ta biyu tana haɗe hannuwan ta alamun roko tace.
"Dan Allah Ya Malik kataimaki rayuwar Bahijja ka rabu dani, nayafe so da kaunar da kake mani, dan haka dan Allah katsaneni arayuwar ka, karabu dani."

Rufe idanun shi yayi saida yai kamar minti ukku ya bude su sun sake kaɗawa cikin kulawa da tausayin ta yace. "Saboda baki sona kin tsaneni ko Bahijja.?''

Sunkuyar da kanta tayi kasa tanajin girman tambayar da yaimata, sai dai bata da zaɓi dole su hakura da juna kamar yanda take tursasa tata zuciyar, cewa tayi. "Ya Malik banso takaimu a wannan fagen ba sai dai ko shakka babu a halin yanzun Bahijja ta hakura dakai banson k!...

Ɗaga mata hannu yayi yace. "Nafahimta kanwar Malik, naji zanyu yanda kikeso, sai dai kisani Bahijja tun kina yar jinjirarki nake furta kalmar so agareki har zuwa yau da nike fidda wannan numfashin a gabab ki, amman farin cikin ki shine nawa, zan nisan ta kaina dake tunda hakan kikeso amman kalmar ki bazata iya fitowa daga bakin Abdulmalik ba zuwa ga Bahijja, sannan har yanzun ina rokonki daki yafema Ummu, kuma bazan barki cikin wannan halin ba dole kibar wannan wajen.!"

Jitayi zuciyar kamar tafaso kirjin ta ta fito cikin karfin hali tace. "Rayuwar Bahijja tafi daɗi a nan gidan dan Allah Ya Malik karabu dani nan zaifiye mani daɗi da aminci."

Juyawa tayi tana nufar ɗakin da aka rufeta tana hawaye ga tarin kaunar MalikusSaif a cikin zuciyar ta tarasa mike mata daɗi, jitayi yace.

''Indai Abdulmalik yana numfashi bazai taɓa barin rayuwar Bahijja ta wulakanta ba, dan haka kidaina zubda hawayenki kanwar Malik, hakan na taɓa zuciyar MalikusSaif."

Batareda ta waigoba ta ida shiga cikin ɗaki wanda gwara cell dashi saidai taki bari su hada idanun su, garkameta akayi, yanajin hakan har tsakiyar kwanyar shi, juyawa yayi wanda inka kalli idan Malik baka fatan ku sake haɗa idanun ku a karo na biyu, ba inda ya wuce sai sashen Kangiwa.

Yana isa ya tadda shi zaune da wasu mutane suna sallama da alama baƙi yayi zasu tafi, gaisawa sukayi bayan sun tafi ya dawo gafen mahaifin nashi ya zauna yace.
"Abbuh kataimaki rayuwar Bahij.....hannun shi da ya ɗaura bisa bakin Malik shiyasa bai karasa mganar ba, cikin tausayawa yace. "Mahaifiyar ka ta rufe Bahijja gidan kaso yau kimamin kwna sha biyu ko.?" cikeda mamaki yace. "Abbuh daman kasani.?"

Murmushi yayi mai zafi yace. "tabbas koda zata kashe Bahijja bazan hanata ba, sai dai akwai ranar da wlh sai Zulaiƙa ta zubda kwalla da idanun ta."
"Abbuh kadaina faɗan haka kodan ni."

tabbas yasan irin so da kaunar da Malik kema mahaifiyar sa da yanda take kaunar MalikusSaif bazaiji dadi ba, duk da son zuciyane yasa tarufe idanta ta ɗauki zalinci yazama ado a cikin zuciyar ta kallan Yarima Malik yayi yace.
"Kada ka kasance mai son zuciyar ka Abdulmalik dan kawai son da kake ma mahaifiyar ka, gaskia na faɗa, dan haka kada ka kuma zuwar man da zancen Bahijja dan bani a cikin wannan sabgar, kuma bance kace mani komai ba, kasa aranka umurni nike baka.!"

Haka Malik yadafe kanshi na yan sakanni zuciyar shi na kuna tashi yayi ya tafi har zai wuce sashen shi sai kuma ya wuce sashen Matawalle yanda yaga MalikusSaif kadai ya nuna mashi ba lafiya, zama yayi bayan sungaisa, hankalin Matawalle yai kololuwa wajen tashi ganin Malik rai ɓace yace. "Ɗana miyafaru.?"girgiza kanshi yayi yace "Kawu kataimaki rayuwar Bahijja Ummu takaita gidan kaso."
rai ɓace yace. "Wato Zulaiƙa bataji abinda nace mataba kenan, tafiya taurin kai ko, rabu da ita tunda bata da jin magana sainayi maganin ta, da ban niyar shiga wannan sabgar ba tunda nima banson ka da baiwa, amma take jayayya da ikon Allah, sannan har Baffa Abu-Jalal yai magana amman Zulaiƙa takijin umurnin sa ya tabbata bata da mutunci." ya ida maganar rai ɓace, Malik ne yace. "Kawu kayi hakuri kuyima Ummu uzuri."
"ymin shiru Abdulmalik nida itane kuma dole yau sai Bahijja tabar gidan kaso din, sannan in matarka ce kotanaso ko bataso saika auri Bahijja."
yana ida faɗar haka ya mike ya fice haka yabar Malik jiki a mace, shima a sanyaye ya wuce sashen shi ya kwanta jikin shi yai ringis tamkar garwashi.

Koda Matawalle yaje wajen Zulaiƙa bai duba hadiman daketa aiki ba, daga gefe kuma Binta ce duke Sarauniya Zulaiƙa ta ɗaura kafarta bisa kafadar ta tana mata tausa, rai ɓace yace

"Ashe baki da mutunci ban saniba? Ashe kin raina mutane har haka? Ashe bakisan kima ba? Kintabbata marar mutunci Zulaiƙa."
duk hadiman dake cikin falon jin yanda Matawalle ke magana sun san ba lafiya a hankali duk suka fice hatta Binta wani corridor ta shiga ta tsaya gudun kada ta tafi gida kuma tayi wani laifin.

Jiki mace Sarauniya Zulaiƙa ta matso kusa da yayan nata tace.
"Haba Yaya miyafaru kake faɗan waɗan nan kalaman akaina.?"

Rai ɓace yayo kan Zulaiƙa yace. "Kisake yimin wata magana saina saɓamaki sha shasha sha harkin isa Baffan Runo ya gindaya sharuɗɗa keki bijirema umurnin sa wacece ke!?"

"Haba Yaya kabi asannu taya zansan abinda na aikata." wani wawan kallo ya aikama Sarauniya Zulaiƙa dolen ta,ta sadda kanta ƙasa duk jikin ta yai sanyi cikin fushi yace.
"Tunda kin kama makiyiyarki kin garkame dole kice bakiyi komai ba."

Wani kululune ya tokare kirjin Zulaiƙa daman akan baiwa ɗan uwanta zaizo yana ihu rai ɓace, cukune fuska tayi tace.

"Haba Baffan Malik akan baiwa zaka dinga yimin faɗa haka wannan matsiya ciyar yarinyar. "

''Kifita idanuna in rufe ke kike mata kallan matsiyaciya amman mu a wajen cikkakkar 'yace tunda ɗan mu na sonta, kuma kikiyayi kanki kada alhakin ta ya hanaki gamawa da duniya lafiya nagaya maki, sannan inna fiddota ki sake maidata gidan yarin kiga yanda zan ɓata maki rai, wadda batasan ciwon kanta ba saikace ba uwa ba mtsw." yagama maganar yanajan tsaki ya fita, faɗawa tayi bisa kujera tana maida numfashi tana mamakin yanda Matawalle yaji wannan zancen kodai Malik zai sanar masa take tace aaa sai dai in Saifulislam ne dafe kanta tayi tanajin kuna a cikin zuciyar ta, itako Binta duk abinda akayi tanajin ta, duk mamaki ya isheta ashe akwai wanda ya isa ya gayama Zulaiƙa taji bayan mijin ta a fadin duniyar nan, rawa jikin ta yafara tana son ta fita tana shakka kada ta huce kanta, itako Zulaiƙa ganin tanajin juwa dan bakin ciki dakinta ta shiga ta kwanta.

Bayan sati ɗaya Bahijja ce kwance a cikin ɗakin su, itada Salame tana dan dannama Bahijja kafarta yau kwanan ta bakwai da fitowa gidan kaso ba kadan taji jikin ta yayi mata daɗi ba, takara samun karfin jikin ta, Salame ce tace.
"wai Bahijja yaushe zaki koma aikin ki.?" yitayi kamar bataji Salame jin yanda gaban ta ke faɗuwa tunanin Ya Malik ya dawo mata fil sabo, ta tabbata duk inda yake yana cikin damuwa, sannan koya yake da abin da zaici, ɗan karamin tsoki tayi tace. "Ni ina ruwana da zandamu kaina a kan halin da zai shiga." sake jifomata tambayar tayi, cikin kosawa tace. "Nadaina zuwa." sake jefamata wata tambayar tayi tace. "Saboda mi?" wani kallo tai mata tace. "Saboda abinda idonki ya gane maki." rai ɓace Salame tace.
"Dan na damu da damuwar ki shine zaki gaya mani bakar magana." taɓe baki Bahijja tayi tace.
"Bakida maganin da zakimin dan haka ba damuwar ki bace, kinga dan Allah kirabu dani inji da damuwa ta." tashi Salame tayi tana faɗa ta tafi, itako Bahijja tashi tayi ta dauki buta ta shiga kewaye bada jimawa ba ta fito ta fara alwallah.

A masallaci kuwa anagama jam'i dayake Kangiwa shike jansu sallah yafara nasihohi kamar dai yanda ya saba, akan darajar ɗan Adam wannan karan yayi magana cikin ilimi da sanyaya murya yace.

"Yakama ta muji tsoron Allah mu mutunta junan saboda Allah da kanshi a cikin alqur'ani mai girma yace. *Walaqadi karamna* *bani adama.* " ma'ana kuwa yace, *hakika munkarrama ɗan* *Adam*, da wannan ayar kadai ya ishi mutun yaji tsoron Allah yasan cewa mutum ba abin wulakantarwa bane tinda har Allah da kansa yace ya karrama ɗan Adam, sai kai saini zamuce zamu dinga wulakanta yan uwanmu dan kawai kana ganin kafi wani daraja da matsayi kayi anfani da wannan damar kana cun zarafin sa, toh wlh muji tsoron Allah duk wanda kagani a doran kasa yanada tasa darajar, kuma inka bibiyama yafika daraja a wajen Allah, dan haka muji tsoran haɗuwa da Allah, mu dinga ƙimanta 'yan uwan mu da darajar su mu taimaki junan mu sannan kada mubari shaiɗan ya samana son zuciyar a rayuwar mu, dafatan zamuyi anfani d wannan tunatarwa Allah yasa mudace." ameen duk suka amsa.

Nan sukayi addu'a kowa ya shafa anata musabaha duk suka fito masallacin nan MalikusSaif ya tafi wajen dawakai dan yaga Abban Bahijja ya nufi can daga masallaci...

Itako Sarauniya tana gama sallah tace.
"Kaji Kangiwa nasan wannan abun da biyu yakeyin shi, hmmm nidai bazan bari ɗana ya kasance da baiwa ba."

_Ikon Allah anya Zulaiƙa baki fara wuce iyaka ba?kodai son zuciyar taki tafara komawa jahilci_ 🤔


Koda MalikusSaif ya isa gidan dawakai ya iske Abdulmajid har yafara

Please Login or Register in order to submit comment