Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko zama bataiba tace.
"Abdulmajid ka dubi girman Allah ka amince kabawa Yarima auren nan."

Cikeda mmaki yake kallan Sarauniya Zulaiƙa yarasa abinda ya sauyata cikin kankanin lokaci, murmushin kasan makoshi yayi sannan yace.
"Yanzun haka gobe za'asaka Bahijja baiko kamar yanda nafaɗa maki kuma kinsan haramun ne neman aure cikin neman aure,kuma koba dan haka ba,ni Abdulmajid banji zan iya ba ɗanki auren ƴata Bahijja kibar wannan maganar dan bata taba yuyuwa kema kinsani."

Hayayyaƙo mashi tayi cikin faɗa tace. "Kada kagaya mani maganar banza Abdulmajid kada kayi anfani da wannan damar kaci zarafina, karfa kamanta kai bawa nane kuma bawan ubana hakama duk zuriar ku bayina ne akalkashin ikona kuke akwai wanda ya isa kaf zuriar ku, yayi gangamin aurar da baiwa ba tareda ikona ba da sanina ba?"

tsuke fuskar shi yayi ba alamar wasa dan ya gwammaci koda Zulaiƙa zatasa a sare mashi kai yau saiya faɗi abinda ke cikin ranshi cewa yayi.

"Uhmm Zulaiƙa kenan, ni bawan mahaifin kine tabbas ko tantama babu karda kimanta a haife na haifeki koda nike bawa nida mahaifin ki Sarki Abdulhamid tare muka tashi shekarunmu ɗaya ni nai mashi hidima sai dai baitaɓa wulakanta niba, har Allah ya azurtashi dake bai taɓa ƙyarata ba, amman saike ƴar ciki na! bayan kinsan badan ina bawanki ba, da ba yanda za'ayi kidinga cin zarafina har haka, a haka kike ganin zan ba ɗanki auren Bahijja, koda zaki sare kaina ni Abdulmajid bazan bada auren 'yata ba inda ba'asan darajar taba."

Cikin zafin rai Sarauniya Zulaiƙa ta wanke Abdulmajid da wani mummunan mari marar dadi, dai dai lokacin kuwa Matawalle ya shigo dan sanar da ita kiran da Baffan su Abu-Jalal ke mata, tsaye yayi jikin sa har rawa yake ganin Zulaiƙa tasa hannu ta mari dattijon daya haifesu dan kawai yana bawa.

Shiko Abdulmajid kuncin shi ya rike, yana mamakin yanda Zulaiƙa take cin zarafin shi duk sanda taga dama lokacin da taso, rai ɓace yace.

"Nikika mara akan hakkina dan nace bazan baki auren ya'ta ba shine zaki mareni?."
a fusace tace.
"Eh na mareka ko zaka rama ne?"
a harzuƙe Abdulmajid ya ɗaga hannu zai rama sai kuma ya tsaya bai rama dan Allah ya horema Abdulmajid tarin zuciya yace.
"Uhmmm Zulaiƙa kenan kinci darajar ɗanki da mijinki badan haka ba, wlh saina nuna maki jiya na yau bace, ni nafi karfin wulakanci duk da nike bawa, kece bakisan daraja taba, amman dan uwanki yasani tinda yanaimani kallan mahaifi wanda yake abokin mahaifanku, sai dai kisa. aranki *bayima 'ya'yane* Zulaiƙa."

cikin fushi tace.
"da ka ida abin da kai niyar yi da sai kasha mamaki harka isa ka faɗaman magana son ranka dan kana tsaran mahaifina dole ka dawo hayyacin ka kasan matsayin ka na bawa, bashi ke nuna kaimani gadara ba, ni Zulaiƙa ba ɗaukar raini kuma gobe goben nan za'ayi baikon wannan watsatstsiyar baiwar da Malik, daga bisa in gogeta ta koma 'yantatta tafita daga datti na bauta."

rai bace ya gwada ta da yatsa wanda baisan sadda ya gwada taba yace.
"kinyi kaɗan Zulaiƙa duk duniya ba wanda ya isa ya aurar da Bahijja saini uban ta,sannan da kike maganar datti eh naji ƴata datti ce,dan haka kije ki samu mai tsafta ki haɗa ɗanki da ita,badai yata ba dan mai tsafta sai mai tsafta kuma datti dai mai datti,dan haka na kiyaye ki da sake cin zarafina kona iyalina wlh bauta ba hauka bane,kuma kema kinsan ni Abdulmajid nafi karfin raini koda nike bawa ke kinsan ba aimani wargi ina fatan kin fahimta?"

ta buɗe baki zata maida mashi martani kenan sai sukaji muryar Matawalle yace.

"tabbas Zulaiƙa kintabbata mahaukaciya ashe tsaurin kanki yakai harki sa hannu ki mari Abdulmajid, koda yake bawa bakisan darajar shi bane? kuma a hakan kike ikirarin kina son yaba ɗanki auren ƴarsa?lallai kin haukace wannan kayan kunyar badani Matawalle ba za' a kwashe taba."
haɗe hannayen shi yayi yace.
"Abdulmajid dan Allah kayi hakuri tabbas kunyarka yasa nakasa haɗa ido dakai kayi hakuri dan Allah."

Murmushi yayi mai ɗauke da ma'anoni yace. "Allah yaimaka albarka Matawalle, koda yanzun dana haihu inna ganku nakanji dadi, nasan da Allah ya albarkace ni da haihuwa tabbas dana haifi tsarar ku, amman hakan ma nagode, yau gashi mutun mai daraja kamar ka yabawa bawa kamata hakuri, lallai hakan kaɗai ya isa asan darajar bawa, bakomai nayi sai dai kasani bazan bawa Malik auren Bahijja ba wannan alqawali ne koda zan rasa raina."

Jijjuya kai Matawalle yayi alamar gamsuwa,dan yasan Abdulmajid yanada hakuri sai dai bai ɗaukar raini wannan dalilin yasa bai shiga sabgar kowa, kallan tsana Matawalle ya watsama Zulaiƙa sannan yace.

"In kinga ma cinkasar taki, kizo Baffa Abu-Jalal na neman ki a sashen Kangiwa."

"Haba Yaya ya zanyi ,kaga abinda wannan bawanbke faɗa mani ka taimaka mani wlh zan iya wulakanta wannan daƙiƙin bawan wand.......bata karasa zancen taba taji wani azaba taccen saukar mari a kuncin ta,a kiɗime ta kalli Matawalle da yatsa ya nuna nata rai bace yace.
"Ke ɗin banza keɗin wofi kar kin isa ki dinga yima mutane magana son ranki wacece ke?Abdulmajid ba tsaran mahaifin bane wlh kika kara aibata shi saina baki mamaki sakara marar hankali mtsw."
itako ta rike kunci batasan sadda tafara kwallaba yau itace ɗan uwanta ya mareta akan bayi, har yake nuna haushin shi akanta, zatayi magana kenan taga ya fita dan inyace zai tsaya tabbas baisan abinda zaiyi kan Zulaiƙa ba.
shiko Abdulmajid cikeda mmaki a fuskar shi, jin ance Sarki Abu-Jalal ne yazo, ashe shine dalilin dayasa ta kirashi dan batasan yasan abinda ke wakana kenan, murmushi yayi baiyayya nanne, itako takasa motsi.

Juyawa yayi zai fita yaji amon muryar ta tace.

"Karkaji Baffana yazo kasamu wata dama ta daban, kasani ba fashi akan ƙudurina zuwa gobe zaka ba ɗana auren ƴarka."
juyowa yayi yace.
"ai zaki iya aurar da ita ai mallakin kice ita ɗin."
ya ida maganar yana murmushi mai ma'anoni,zuciyar tace ta tsinke tace.
"dan Allah Abdulmajid ka taimakeni bansan Baffana yasan wannan zancen ka dubi girman Allah."
Baice komai ba ya jijjiga kai, tareda murmushi, tunawa yayi sadda suke zuwa Masarautar Runo shida mahaifin ta wajen Sarki Abu-Jalal idan yai laifi har baisan su haɗu saboda mutunne wanda baida wasa ko kadan, saidai akwai mutunci, rausayar dakai yayi yace. "Allah yajikan ka aminina Abdulhamid da kana raye tabbas ƴarka bata isa taci zarafina ba."
haka ya tafi yana jin ƙuna a cikin zuciyar shi duk da ba wannan ne karon farko ba da Zulaiƙa ke wulakanta shiba ba tareda tadubi farin gemun dake fuskafuskar shiba...

Itakuwa Zulaiƙa zaunawa tayi Jakadiya Hajara dake share kwallar idanin tane ganin wulakancin da Zulaiƙa taima Abdulmajid, yasa tace.

"Ranki shidade kiyi hakuri, kije kada Baffa ya jiraki."
rausayar dakai tayi alamun gamsuwa duba agogo tayi taga har karfe tara ya gota, hakan yasa ta yunƙura ta mike atare suka tafi, tanajin tsoro da shakka a cikin zuciyar koda suka isa bakin shiga side ɗin Kangiwa tsayawa tayi kamar bazata shiga ba sai kuma ta shiga har cikin falon da sallama a bakin ta, amsawa sukayi baki daya suna kallan ta, yanda taga suna kallan ta saita kara shan jinin jikin ta a tunanin ta ko Matawalle ya gaya mashi abinda ya faru, kirkiro murmushin karfin hali tayi a saman fuskar ta sannan ta tafi da sassafar tana rungume Baffan nata kamar dai yanda tasaba in suka haɗu, shima shafa kanta yayi yanajin dadi ganin kyakyawar ƴar tasa cikin shagwaɓa tace.

"Baffana nayi kewarka sosai."
Cikin so da kaunar 'yar tasa yace. "Bawani nan tun ɗazun na aika a kiraki dayake kinyada Baban naki shine sai yanzun kikazo."

Hakanan taji faɗuwar gaba musamman da suka haɗa ido da Matawalle da irin kallan da yai mata, sauke kwayar idanun ta tayi, sannan ta janye jikin ta a jikin Baffan nata sannan tace.
"Ayyah Baffa inata zumuɗin inzo shine kasauka wajen ɗanka kamanta dani."
Ɗan taɓe baki yayi, dan ya lura akwai yar matsala a tsakanin Kangiwa da Zulaiƙa yanda ya gansu take yagane akwai matsala a cikin zuriar shi, murmushi ya kuma yi yace
"kinsan shi ɗana ne kuma aminina, ke kuma ƴata ce, kuma ƙawata ce, kinga ai zanso in kasance da aminina ko." baki ɗayan su suka saka dariya, shiru ya sake gauraye wajen sai dai shi Abu-Jalal kaf yana nazartar kowa, a cikin su.

gyaran murya yayi hakan yasa suka maida hankalin su akan shi, cikin girma da dattako yace. "Niko ina ƙanina Abdulmajid."

Daram daram haka Zulaiƙa taji gaban ya faɗi har fat fat fat zuciyar keyi a cikin kankanin lokaci, Saifulislam ne yace.
"Yana turakar bayi Baffa."

Kallan Zulaiƙa yayi wadda duk ta gama hada gumi dan shakkar yayan mahaifin nata yace. "Yata baki lfy ne naga kina gumi, ni kuwa yau ɗan sanyi nikeji duk da munyi tafiya."

Girgiza kai tayi still tana lalubo murmushin daya kaura a saman fuskar ta, sake cewa yayi.
"Uhmm baki kyauta minba Zulaiƙa."
Murya na rawa tace."Baffa kayi hakuri minayi.?"

"Ace har yanzun kina mulkin Daborah amman kinbar Abdulmajid a matsayin bawa, yana aminin mahaifin ki, wanda ya share sama da shekaru saba'in yana aikin bauta a cikin wannan Masarautar gaskia bakima kanki faɗa ba dakai kanka Kangiwa duk laifin kune harda kai Matawalle ai kunfita hankali da hangen nesa."

Ɗan rusunawa Kangiwa yayi wanda Abu-Jalal yake yaya ga mahaifiyar shi yace. "Kayi hakuri Kawu, kasan mu ba ma zauna gida bane."

Rausayar dakai yayi alamun gamsuwa, itako Zulaiƙa tarasa abin cewa.
Sake kallan ta yayi yace. "Za'a yanta shi Zulaiƙa kafin inkoma gida, zuwan nan da nayi akwai muhimmiyar maganar data kawoni amman zan nemeku akanta sai Allah yakaimu gobe."

Cikin fargaba tace. "Baffa lokacin mu nakane yanzun kagaya mana."
Girgiza kanshi yayi alamun aa, sannan yace. "Yanda nace haka za'a bari Allah yakai mana rai."
Baki ɗayan su suka amsa da Ameen, sake cewa yayi.
"Kangiwa wai Abdulmajid har yanzun Allah baisa ya haihuwa bako?"

Sake juyawa cikin Zulaiƙa yayi tarasa dalilin dayasa Baffa Abu-Jalal ke kawo zancen wannan matsiyacin bawan, duk da tasan akwai kyakyawar alaka a tsakanin shi da Abdulmajid yana cikin amintaccen bawan su kuma baida shamaki a cikin Masarautar Runo, ji tayi Matawalle yace.
"Aaa Baffa aikuwa ya haihu shekaru goma shabiyar da suka gaba, ƴarsa nanan harta zama budurwa ma."

Wani sanyayyen murmushi Abu-Jalal yayi yace.
"Allah maigirma Sarkin Sarakuna mai iko akan komai mai raba mulki sadda yaso kuma ya kwace sadda yaso, mai azurtawa kuma shike ɗaukaka bawa lokacin daya so, Allah Sarki wannan kadai ya isa bawa yaji tsoron Allah, yau ga Abdulmajid da 'yar cikin sa, haihuwa batazo mashi ba saida tsufa yakama shi, Allah yaima rayuwar ta albarka, har naji ina kaunar yarinyar a raina ina ma Abdulmajid yabani ita dana tafi da ita Runo na 'yantata in aurama Yarima Dawud ita."
da sauri Sarauniya Zulaiƙa ta kalli Baffan nasu duk mamaki ya isheta duk da tasan bada ita yake ba amman sai taga kamar da ita yakema shagube tafara tunanin ko su Kangiwa sun faɗa mashi komai, sai dai yanda taga suma fuskokin nasu ɗauke suke da mamaki hakan yasa tasan baisan zancen dake tsakanin Bahijja da MalikusSaif ba.
Jitayi yace. "Saidai so da kaunar da yake mata bazai iya rabuwa da itaba cikin sauki ba, Uhmm Zulaiƙa ƴata kina mamaki kinji nace zanbawa kanin ku Dawud auren baiwa da ace Abdulmajid zai bani itako?"

Sai a lokacin ne Sarauniya Zulaiƙa tace. "Gaskia kam Baffana ina kanina ina auren baiwa."
"Hmm Zulaiƙa kenan ba wani abu bane ai *BAYIMA 'YA'YA'NE* kamar kowa, kuma nasan Abdulmajid mutunne mai ilimin addini tabbas yarsa zata kasance mai tarbiya."

Wani sanyin ne ya ratsa Saifulislam yana mamakin yanda Baffa Abu-Jalal ke yabon tsatson Jafar makiyan Sarauniya Zulaiƙa, aran shi ko cewa yayi kodai yasan Abdulmalik yana son Bahijjar? Anya wazai gaya mashi, sai yace labari ne ya kawo haka shima cewa yayi.
"Aiko Kawu kasan yarinyar har bauta taje wata Masarautar ta daban, haka ya kwashe labari tas ya gayama Abu-Jalal har musultar da sukayi ba abinda bai gayama Abu-Jalal ba.

Sauke ajiyar zuciya yayi yace. "Masha Allah haka akeso Allah yakara mana imani."

Ameen suka amsa, shiko ya kawo labarin darajar baiwa, saboda Lurwan yaje mashi da zancen Yarima baiwa yake so, duk da baisan wacece baiwar ba, yasan yanda suke tsanar bayi, yayi shinfiɗa ne cikin ilimi da gogewa da hikima kafin zuwa gobe yasanar dasu maƙasudin zuwan shi, sannan yaga baiwar da iyayen ta.
Azahiri kuwa cewa yayi. "Inasan inga jikin ɗan nawa."
Matawalle ne ya mike tareda gyara alqabbar shi sannan yace. "To Baffa."

Su dukan su suka ɗunguma zuwa sashen Yarima Malik, sai dai Zulaiƙa ji take tamkar ta bindiga dan takaici, suna shiga sukayi bedroom dinshi, a can suka iske Huzaifa da Yazid sai Lurwan din shiko MalikusSaif ya kudun dune da blanket,da sallama aba kinsu, amsawa sukayi ganin manyan bakine yasa suka fito suka basu wuri dan gaisawa, hawa bisa gadon Abu-Jalal yayi a hankali ya yaye bargon, take farar Jallabiyar jikin shi ta bayyana sai kamshi yake bazawa, a hankali ya bude idanun shi, jin anyaye mashi bargo ga sanyi yanaji yana kakkarwa kat kat kat, idan shine ta sauke kan fuskar Abu-Jalal wani sanyayyen daɗine ya ratsa mashi cikin zuciya, sai kuma yaji wasu hawaye masu dumi sunyi nasarar zubo mashi da sauri suka rungume juna tsam tsam kamar zasu like da junan su, murya na rawa Yarima yace "Abi."

Shima kara rungume Yarima yayi yana karajin son shi na tsanan ta a cikin zuciyar shi, suko Kangiwa da Zulaiƙa ido suka zuba ganin kauna da shakuwa dake tsakanin Baffan su da Malik, wanda lokacin da Abu-Jalal ke tashen zuwa Masarautar Daborah dan duba yayan ƴan uwan shi, lokacin MalikusSaif bazai wuce shekara bakwai ba, amman yanda sukejin junan su tamkar shi ya haife shi.
Shiko Matawalle bai mamaki dan yagane ma idanin shi zuwan da sukayi da Abdulmalik a Masarautar Runo
Cikin kewar jikan nashi yace. "Sannu Abdulmalik ya jikin naka.?"


Sai a lokacin suka saki juna yana mai ɗaura kanshi bisa kafaɗar Sarki Abu-Jalal sannan yace. "Nayi kewarka Abi, jiki alhmdullhi."

rike hannayen shi yayi cikin nashi yace. "Gani gareka ɗana Allah yasa kaffara ne." da idanu yabi mutanen dake ɗakin karshe ya sauke su kan Dawud, yalwatacen murmushi ya sakar mashi,shima ya mayar Yarima Malik din martani

sannan yace. "Abi rufeni sanyi nikeji sosai." baice komai ya rufe shi, kallan su yayi ganin har goma na dare ya gota, yace. "Kuje kowa ya kwanta ni zan tsaya in kwana da jikana."

da sauri Sarauniya Zulaiƙa tace. "Haba Baffana kagafa ka kwashi gajiya kabar su Huzaifa zasu kula da komai."
Girgiza kanshi fuskar shi ɗauke da annuri yace. "Karfa kimanta wannan zuwan dan ɗana Abdulmalik nazo, dole in zauna dashi, sai dai in Allah yakaimu gobe karfe goma na safe, inasan ganin ku, anan sashen na Yarima."

Ba wanda ya kuma cewa komai harsu Yarima Dawud su galadima da sauran jama'ar Abu-Jalal sukabi Matawalle, haka kowa ta watse ya tafi sashen shi danyin bacci.

Koda suka tafi, kallan Malik yayi yace. "Sannu ɗana tashi ga maganina na taho maka dashi."

tashi yayi ya amsa yana sha ya kwanta sake rufe shi Abu-Jalal yayi, yana mai jin tausayin Abdulmalik har cikin kokon ranshi addu'a ya tofa mashi duk da yayi, tashi yayi ya shiga bathroom yayi alwalla sannan ya shinfida sallaya yahau rera karatun alqur'ani, saida dare ya tsala sannan yafara yin nafilfilin shi, can ya ga Malik yai nisa a barci ga zufa yai sharkaf alamun sauki, yaye mashi bargon yayi, sannan yaci gaba da sallar shi, yana nemawa jikan nashi zabin Allah.

Washe gari da misalin karfe goma na safe kamar yanda Abu-Jalal ya umurci 'ya'yan nashi kuwa duk sukazo a sashen Yarima Malik, zaunawa sukayi, tundaga Matawalle Kangiwa Sarauniya Zulaiƙa da kuma Waiziri Dammur, basu jima da zama ba, Jakadiya Hajara wadda itama a sashen Yarima Malik din ta kwana taje ta sanarma Sarki Abu-Jalal isowar su, lokacin yagama kimtsawa yana gyarama Yarima Malik alqabbar jikin shi, bakaramin kyau yayiba a cikin shigar tashi ba, sai yafito kamar wani balarabe, a tare suka fito cikin shigar alfarma ta Sarakai, suna isowa cikin falon Sarki Abu-Jalal ya zauna bisa wata dankareriyar kujera ta Royal data gaji da haɗuwa saboda ta musamman ce a cikin kujerun dake falon, shi kuma Yarima Malik saman tattausan kafat dake baje a tsakiyar falon ya zauna ya jingina bayan shi da kafar Abu-Jalal yana facing din iyayen nashi, ɗan shiru ne ya gauraye wajen na sakanni, baki ɗayan su, suka gaishe da Abu-Jalal din cikin sakin fuska ya amsa, shima Malik, cikin ɗa'a ya gaida iyayen nashi, haka kowa ya amsa, Galadima ne ya shigo daga baya wanda yake kamar Kawu ne a wajen Abu-Jalal shima zama yayi kusa da kujerar Sarki Abu-Jalal, gaisawa sukayi da Abu-Jalal dan yana ganin girma da mutuncin galadiman shi, gyaran murya Sarki Abu-Jalal hakan yasa kowa ya maida hankali da tunanin shi wajen shi, sallama yaimasu, suka amsa da wa'alaikumussalam."

Cigaba da cewa yayi. "Dalilin dayasa nace kuzo inasan ganin ku shine babban makasudi na zuwa Masarautar nan tamu mai tarin albarka da tarihi a cikin wannan kasa tamu ta Gambia, saboda inasan in sanar daku hukuncin dana yanke ba tareda neman wata shawara ba, sai dai a wannan mahallin a matsayina na mahaifi agareku ina baku umurni ne." jingina kai sukayi alamun gamsuwa shima yana lura da yanayin kowa sannan sunsan a ka'ida idan Abu-Jalal yana magana ba'ayi saidai inshi yabaka izini sannan cigaba da cewa yayi. "Wani labari yazo yasa meni mai ban mamaki da al'ajabi, hakan yasa nakasa bawa zuciyata hakuri, har saida nazo da inganewa idanuna abinda ke faruwa da kaina.
Wani irin faduwar gaba ne yakara tsananta a wajen Sarauniya Zulaiƙa, maganar da taji ta sauka a cikin dodon kunnen tane yakara tayar mata da hankalin, "dan haka ni Abu-Jalal ɗan Abu-Jabbar na II na goyawa ɗana Abdulmalik baya ɗari bisa ɗari akan auren baiwar da yake so yayi."

Idanu waje Zulaiƙa ke kallan Baffan nata, badan tanaja da umurnin shi bane, saidan tana mamaki inda yasan wannan labarin ko shiyasa jiya yaketa yaba al'amuran Abdulmajid, duk da itama zataso hakan a halin yanzun kodan lfyar ɗanta, shi kanshi Yarima yayi mamakin yanda har Abi ɗin shi yasan da wannan zancen shidai yasa magana makamanciyar wannan bata taɓa hadasu ba, jiyayi Abu-Jalal yaci gaba da
cewa dan haka inasan inga mahaifin wannan baiwar da ake rigima dan kawai Yarima yace yana son ta, musamman ke Zulaiƙa.!"

Shiru Zulaiƙa tayi kamar ruwa ya cinyeta, shiko Abu-Jalal kallan kwayar idonta yayi yace.
"Narasa sai yaushe zakiyi fatali da irin waɗan nan ababen naku na al'ada kin ɗauki karan tsana kin ɗaurama bayin da basuji ba, basu gani ba, laifin wani ai baya shafar na wani, da al'amuran duniya basu wucewa kema da bakikai haka ba."

Sunkuyar da kanta tayi tanajin maganganun Baffan nata har cikin kwakwalwar ta fatan ta lamarin ya tsaya haka kada yaji abinda ta aika ta, duk taji zuciyar ta ta gama karewa, murya sanyaye tace. "Baffa kayi hakuri, komai ya wuce."

Kallan gefen hannun shi na haggu yayi yace. "Abduljabbar je kasa akiramin mahaifin yarinyar."

Kallan juna sukayi da Zulaiƙa, jitayi gaban ta ya faɗi musamman da ta tuna cin zarafin da tayima Abdulmajid da daddare, sauke ajiyar zuciya tayi a sirrin ce, shiko Matawalle mikewa yayi dan cika umurnin Sarki Abu-Jalal.

Koda ya fita daga sashen Yarima Malik bai ba kanshi wahala ya nufi dawaki, aiko ya taddata Abdulmajid yana aiki kamar kullin, yana ganin Matawalle yazo zai duka kasa su gaisa, hannu yasa ya riko hannun Abdulmajid ya hanashi dukawa sukayi musabaha, sannan yace. "Abdulmajid ya aikin.?"
Cikin jin dadi yace. "Alhmdullhi."

Rausayar dakai yayi, cikeda gamsuwa yace. "Kazo Baffa Abu-Jalal yana neman ka yanzun nan."
Hakanan yasamu kanshi da murmusawa cikin zuciyar shi yace Allah Sarki mutanen kirki, har yanzun baku yarda amintattun kuba, mutun mai daraja kamar Abu-Jalal shike neman Abdulmajid, sake murmushin yayi yace. "Shikenan ranka shidade, gani nan zuwa."

Sake kallan shi Matawalle yayi cikin mutuntawa yace.
"Ya kamata kazo mutafi tare kamar hakan zaifi yima Baffana daɗi."

Rausayar dakai yayi baice komai ba, suka fara tafiya kusan ajere har cikin falon Yarima Malik, da sallama a bakin su, amsa masu akayi, dai dai lokacin Sarki Abu-Jalal ya ɗago kyakyawar fuskar shi mai cikeda da kwarjini ya azasu bisa fuskar Abdulmajid, wani sanyayyen murmushi Abu-Jalal ya sakarwa Abdulmajid tareda cewa.

"Wanike gani kamar Abdulmajid Abdullahi Jafar?"

Shima murmushin yayi yanaji wani irin daɗi, cikin girmamawa ya duka yace. "Nine ranka shidade Allah yakara girma angaishe da Sarkin musulmai, Sarkin Runo Abu-Jalal, barka da wannan lokaci, Abdulmajid yana gaisuwa Allah yakara maka lfy da nisan kwana."

Hannu Abu-Jalal ya mika mashi yana ɗago shi daga dukiyar da yayi yace. "Ga waje ka zauna Abdulmajid nan duk 'ya'yan kane."

Ya ida maganar yana nuna su Zulaiƙa da sauran jama'ar dake zaune a cikin falon.

Cikeda zuhudu da gudun abin duniya Abdulmajid yace "Ranka shidade aini bazan ji daɗin zama a nan dinba, kabarni nan albarkar ka nike nema."

Murmushi mai faɗi yayi sannan ya gyaɗa kai alamun gamsuwa, shiru ne ya sake zagaya wajen sannan Sarki Abu-Jalal ya sake gyaran murya kamar koda yaushe indai magana mai mahimmanci zaiyi yakanyi hakan, sai kowa ya sake nutsuwa sunsan magana ce zaiyi mai girma.

"Nayi matukar mamaki danace akira mani mahaifin yarinyar da Abdulmalik ke nema sai naga ashe Abdulmajid ne, da ace nasan kaine mahaifin ta tabbas da banzoba da ɗan aike naturo da sakona gareku,dan haka Abdulmajid ina nemawa ɗana izinin neman auren ƴarka."

Shiru Abdulmajid yayi jin kanshi nasarawa dan baiyi zaton wannan shine dalilin kiran shi ba, abinda yasani yana cikin amintattun Sarki Abu-Jalal, ɗan rausayar dakan shi yayi cikin girmamawa yace.

"Ranka shidade kaima kasani kafi karfin komai a wajena, amman a wannan muhallin ina neman wata alfarma a wajen ka."

Kallan tuhuma Abu-Jalal yaima Abdulmajid yana mamakin wace iriyar alfarma ce wannan zai tambaye shi, fuskar shi ɗauke da murmushi yace. "Inajinka Abdulmajid."

"Ranka shidade inamai baka hakuri gaskia bazan iya bama Abdulmalik auren 'yata Bahijja ba saboda wasu dalilai."

Wani sanyi yaji duk jikin shi yai nauyi dan bai tsammaci jin hakaba daga bakin Abdulmajid, duk da yasan hakanan bazaiki amincewa ba, itako Zulaiƙa wuƙi wuƙi tayi da idanu tanajin bugun zuciyar ta naɗan fisga a sannu a sannu,

"Ko minene dalilin ka na hana Yarima 'yarka.?"
Sunkuyar dakai Abdulmajid yayi dan baisan ya haɗa ido da Sarki Abu-Jalal, cewa yayi. "Saboda mahaifiyar shi."

Da sauri Abu-Jalal ya kalli Zulaiƙa, itakuwa ta janye nata idanun daga garesu, dan tasan bata da gaskia.

"Kamarya saboda mahaifiyar shi yimin bayanin komai Abdulmajid." cikin damuwa yaima Abdulmajid tambayar.

Ɗago idanun shi yayi da suka sauya kala, ya azasu bisa fuskar Abu-Jalal, sannan yace. "Ranka shidade, mizakace ma mahaifin da ya ɗauki 'yarsa ya bada a inda ba'asan darajar taba ko kimarta dan kawai abin duniya.?"

Ɗan shiru Abu-Jalal yayi yana nazartar maganar Abdulmajid dan ya gane manufarsa, cikin ajiyar zuciya yace. "Wannan mahaifin yacika marar kishin zuci, sannan baisan darajar zuriyar saba."

Murmushn jin dadi Abdulmajid yayi sai kuma yace. "Wannan dalilin ne kadai zaisa inhana Abdulmalik auren Bahijja, saboda mahaifiyar shi batasan kimarta ba, takirata da matsiyaciya ta duketa taci zarafin iyayen ta dukan safe daban na dare daban, dan kawai muna bayi, ta tsinemana takiramu da bayi yan gadon bauta da wahala, sannan tasa tafin hannun ta ta mareni kan 'yata, daga karshe tace zata iya kashe Bahijja matukar ta auri ɗanta, da haka zan yarda 'yata ta auri ɗanta.?"

Wani irin nauyi da kunyar Abdulmajid ne suka rufe Sarki Abu-Jalal, yarasa abin cewa, da idanu ya raka Sarauniya Zulaiƙa, karfin hali yayi yace "Shikenan Abdulmajid nafahimceka kuma nasan yanda kakeji a cikin zuciyar ka, saidai inamai baka hakuri akan abubuwan da suka faru sannan zaka iya tafiya muga abinda hali yayi, duk da haka bazan aje kokon barata ba, ina neman wannan alfarmar amman bance dole ba, saboda Bahijja yarka ce kaikeda iko akanta, kuma kowa ya shaida *BAYIMA 'YA'YA'NE* ba tsintota akayi ba, yanda aka haifi kowa haka aka haifeku daga malacci ɗaya muke, ni dakaina zan ɗauki matakin daya dace Abdulmajid dan haka zaka iya tafiya nagode, saika jini."

Wani irin dadi yaji dan yasan tabbas Abu-Jalal zaiyi adalci a cikin lamarin saboda yasan darajar ɗan Adam, godiya yayi sannan yatafi zuciyar fas da ita, itako Zulaiƙa tamkar ruwa ya cinyeta ko motsin kwarai ta kasa, sallamar kowa Abu-Jalal yayi ya tashi ya shiga daki ko inda Zulaiƙa

Please Login or Register in order to submit comment