Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

horemu damu bautama Allah shi kadai kada muhada shi da wani a wajen bauta, sannan *Annabi Muhammadu* yazo mana da haske kuma waraka baiyanan na yazo mana da littafin gaskia wato *Alqur'ani* sannan a cikin sa ko wane waraka yake, a cikin sane aka sanar damu yanda zamu bautama ubangijin mu *Allah SWT* wanda ya halicce ni ya halicce ku da sammai da kassai da komai da kuke gani, sannan ya wallafa mana sallah shine abinda zamu dingayi wajen bauta masa, wannan kuma ta hanyar *Annabi* *Muhammadu* ya iso zuwa garemu, shine manzon da babu wani bayan shi sai dai kafin shi anyi mazon ni, suma akan abu ɗaya suke magana shine bautama Allah shi daya kada ahada shi da wani a wajen bauta, saidai idan mutun ya yarda da *Allah* amma bai yarda da *Annabi Muhammadu* ba ko kuma ya yarda da *Annabi* *Muhammadu* bai yarda *Allah* tabbas imanin mutun bai cika ba,kuma bai cikin musulmai da musulunci sai kayarda da dukkan su da sauran annabawa da kuma mala'ikun sa, wannan shine cikar *IMANI* da shiga cikin addinin musulunci, kaji waye *Annabi Muhammadu*, farin jakkada farin wata sha kallo mai haskake duniya da abinda ke cikin ta." baki ɗayan su suka saki wani irin sanyayyen numfashi, Sarki Baidulƙais ne yace......





_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*




Episode 65&66




"Lallai Jamra wannan addini akwai abubuwan al'ajabi a cikin shi ke duk ina kikaji wannan abubuwan?" dariya tayi mai dan sauti tace. "Wajen Bahijja duk anan naji komai danma yarinya ce batai zurfi ba wajen sanin addinin nata da hukunce hukuncan sa saidai akwai wasu bayi daka rufe a cikin wannan gidan yarin su Tasi'u tabbas sunayin addinin su duk da kasancewar suna karkashin daular wannan Masarautar saidai sun barranta da abinda muke bautamawa, sunayin addinin su a sirrince kamar yanda wasu daga cikin bayinmu suma suka anshi wannan addinin cikin sirri, inaga kaimasu hakuri a fiddo su, sucigaba da koyar damu wannan addinin dan musamu haske mai tarin yawa da waraka a cikin al'amuran mu." dan nazari Sarki Baidulƙais yayi yace. "Tabbas Jamra kingani kuwa harna manta da rayuwar bayin Allahn nan ancutar dasu, saidai mun nemi afuwar su, Sarkin Yari a fiddo mani yaran nan." da toh ya amsa ya tafi, sannan Jakadiya tace. "Ya shugaba na zanso insanar dakai saban sunana da na dade ina sirrintawa." murmushi yayi yace. "Jamra kenan aikece shugaba a wannan fannin, sannan harkina da wani suna da kika boye sama da shekaru arba'in ban sanki dashi ba?" cewa tayi ai sunan bai dadeba saida na shiga wannan addinin mai haske sannan na samu wannan suna." "inajinki wane sunane wannan tace. "Sunana Aisha shine sunan dana ansa lokacin da Bahijja ta lakana mani addinin ta." murmushi Baidulƙais yayi yace. "Sunan kuwa da dadi yake Jamra daga yau zamuna kiran ki hakan." cikin jin dadi tace. "Godiya nike ya shugaba na." cikin zolaya yace. "Nifa dami zaki dinga kirana?" murmushi tayi ta lissafa mashi sunayen musulmai tace. " a cikin su zaka zabi wanda yai maka ya shugana." murmushin ya sake yimta yace. "Na zabi suna nai daraja na farin jakada Annabi Muhammadu." Jakadiya ce ta ida da (SAW) sannan tace."yana daya daga cikin ladabin kiran sunan shi, ku ida sa Sallahu alaihi wasallam, kamar yanda ya fadakar Allah zai aminta da mutun sannan ya saka albarka a cikin lamarin mutun." kowa ya zabi sunan da yake so inda Sarkin zagi yace, Aliyu galadima yace Abubakar, Sarkin yari yace Umar, Sarkin fada yace Usman, sai dogarawan Sarki wani yace Abdullahi, wani yace Ahmad da haka suka gama zabar sunaye masu daraja da kima a duniyar musulunci, koda Sarkin yari ya dawo dasu Tasi'u haka Sarki Baidulƙais ko ince Sarki Muhammad a halin yanzun yasa aka kaisu cikin sashen shi wani bangare anaci gaba da basu kulawa ta musamman, wannan kenan




Bayan wata biyu a Masarautar Daborah kuwa tsakanin Bahijja da MalikusSaif bakaramin shakuwa bace ta kara shiga tsakanin su, saidai duk da hakan Malik na ganin tausayin tane ke dawainiya dashi da zallar son da ɗan uwa kema yar uwar sa, wanda hakan yasa Huzaifa yai bin kwakwaf amman Malik yace sam ba sonta yake ba, hakan yasa ya bullo da wata hanya ta kula Bahijja a matsayin masoyiyar shi, shiko Matawalle yayi wata tafiya kuma akalla zaiyi wata ukku shiyasa yabar zancen maganar zabama Malik matar aure, sabida tafiyar gaggawa ne da yayita ta yan kasuwa a kasar Togo, a wajen gimbiya Zahara'u kuwa harta gaza ta gayama mahaifin Malik tana son shi hakan yasa ya fadama Sarauniya Zulaiƙa itama tayi amanna sa hakan saida Saifulislam ne yace, abarshi yai zabin kanshi saidai inya amince da gimbiya Zahara'un shikenan, cigaba da shigema Yarima Malik tayi tana bibiyar al'amuran sa

Bayan sati biyu, Bahijja ce a sashen MalikusSaif tunda gari ya waye taga yanata shiri sannan yana cikin annashuwa duk da tana shakkar Yarima Malik saidai akwai kyakkyawar alaka a tsakanin su, cewa tayi. "Ya Malik ko unguwa zakaje ne naga janata shiri mike faruwa ne.?" murmushi yayi yace. "Kanwata kenan ba inda zanje yau ranace wadda bazan taɓa mantawa dda ita ba." cikeda zakuwa tace. "Allah ya taimaki shugaba na wannan wace irin rana ce.?" murmushi yayi yace. "Yakamata ki ajeni a matsayi daya Bahijja ko yayanki ko kuma uban gidan ki, ciki wane yayi maki?" wani dadi taji a kunyace ta rufe idanun ta sannan cikin sirriyar muryar ta tace. "Yayana ne kai a haka zanci gaba da yimaka kallo Ya Malik." wani iri dadi yaji ya rasa yanda akai yake shiga wannan yanayin na farin ciki inyana tareda Bahijja cewa yayi. "Hakan yayi kanwata saidai kinsan ko wace irin ranace wannan." girgiza kanta tayi sannan tace. "Aaaa Yaya na sai kafaɗa mani." cikin jin dadi yace. "Rufe idanunki." murmushi tayi tana fiddo idanun ta waje masu saka Malik nutsuwa ya rufe, shiko ɗauko wata leda yayi ya bude ya fiddo wata sarka da jawhar da lu'u lu'u da yan kunne yace miko hannun ki." budesu tayi duk da tana baiwa amman hannun ta gwanin ban shi'awa daura mata sarkai yayi yace. "Toh kanwata bude." budewa tayi ta zuba ma hannun ta idanun ta tana mai ware idanin ta tace. "Masha Allah Yayana sunyi kyau katuka saidai mizanyi da wannan.?" murmushin ya sakeyi yace. "Nakine knwata, ina tayaki murnar shekarar zagayowar haihuwar ki Bahijja.!" sake fiddo idanun ta tayi tace. "Ya Malik daman irin wannan ranar ce aka haifeni?" gyada mata kai yay yace. "Kwarai kuwa kanwata irin wannan ranar ce na samu yar uwa kuma kanwata Bahijja yau gashi kanwata ta girma harta kai shekara sha biyar aduniya kinga dole infi kowa murna da kiyaye wannan rana wajn lissafawa kanwata inai mai murna Allah yakaro shekaru masu albarka." da ameen ta amsa sannan tace. " Yayana wannan sarkai ta girmi darajar baiwa taya zansaka wannan bayan daraja ta bata kai nan ba." hade fuska yayi yace. "Ke mai daraja ce Bahijja mutane ke maki kallan baiwa, saidai ni yar uwa kuma kanwa ta na daukeki dan haka daga kar insake jin kalmar marar daraja abakinki ke mai darajace kanwata kuma kinfi karfin komai a wajena ki aje sarkar ki wata rana zatai maki anfani" cikin jin dadi tace. "Shikenan Yayana nagode Allah yabarmin kai, amman fa kaimani wayo." hmmm yace cikin kulawa yace. "Kamar ya nai maki wayo.?" "ehmana kasan shakaruna amman ni bansan naka ba." takarsa maganar a shagwabe, samun kanshi yayi da murmusawa sannan yace. "Kwarai kuwa naima wata yarinya wayau, saidai ki canka da kanki shakarata nawa?" diddira kafar ta fara sannan tace. "Shekarka ishirin da shidda." makale kafada yai alamin aaa, ta sake cewa da bakwai sake dage kafada tayi, naji da takwas Yayana."murmushi yayi sannan yace. "Baki canka ba kanwata shakaran Yayanki talatin a duniya, Zaro ido tayi tace. "Shekara sha biyar fa kabani." murmusawa yayi yace. "Natsufa ko?" girgiza kai tayi, zatayi magana kenan saiga Huzaifa ya shigo hakan yasa tai shiru tabar wajen ta koma baban falo wani irin kallo yake masu sannan suka zauna saman kujera suna fuskantar junan su, Huzaifa ne yace. "Yarima baka ganin abinda nike fada maka akan wannan yarinyar anya ba sonta kake ba, kafito fili kafadamani dan musan minene mafita." wani bahagon kallo Malik ya aikama Huzaifa a dakile/yace. "Nataɓa boyemaka wani abu? da ace son Bahijja nike tabbas zan sanar dakai, kuma kasan matsayin yarinyar nan." dariya yayi marar sauti sannan yace. "Shikenan daman ina tsoron kada inyi abun kunya tunda ba abinda ke tsakaninka da Bahijja a gaskia ina sonta kuma auren ta zanyi." wani irin daram daram MalikusSaif yaji dan da nan zuciyar shi ta sauya condition tana bugawa da sauri sauri, zuface ta keto mashi, shiko Huzaifa a dage yake kallan Malik yakai sakan talatin yakasa furta ko kalma daya karfin hali yayi yace. "So fa kace?" "Kwarai kuwa." kana ganin Abba zai lamunce, cewar Malik. "Mizai hana zan yan tata ne, karfa kamanta kasha fadar wannan kalmar ta Bayima 'Yayane." samun kanshi yayi da sarawa da sauri ya dafe goshin shi, cikin jin haushin maganar Huzaifa yace. "Shikenan yanzun ina bukatar hutu anjima mun hadu." cewa yayi. "Haba Yayan Bahijja kodai bazaka bani kanwar taka ba?" murmushin karfin hali yayi yace. "Kafiye surutu Huzaifa zan shiga ciki banjin dadi ne." yana gama fadar haka yai ciki shiko Huzaifa dariar mugun ta yayi a ranshi ko cewa yayi yanzun wasan zai fara....


*Toh fa komai Huzaifa ke shirin aikatawa muje zuwa my real fans, inajin dadin sakon ninku fa🥰*


Bayan kwana bakwai, a cikin Masarautar Raifasu abubuwa sun kankama su Tasi'u zuwa yanzun sun dawo cikin hayyacin su har Sarki Muhammad ya yanta su, wanda yayi hakan ne dan yaye masu bakin cikin da suke ciki a cewar shi an cutar da rayuwar su akan abinda basuji ba basu gani ba, yau kam kusan mutun sama araba'in suka amsji addinin islama, saidai duk wannan abin gimbiya Yazira taki tayima mijin nata mubaya'a tana adawa dashi hakan yasa ya fita shirgin ta ya cigaba da rayuwar shi cikin tsafta dan a halin yanzun yafara mantawa da wata rayuwar tsafi da sukayi da Sarrilƙus sannan duk ya kone kayan tsafin su, kuma zuwa yanzun su Tasi'u suke basu ilimi na addinin musulinci tundaga sallah da hukun hukuncen ta hakama azumi, da zakka da dai sauran su, a hankali suke basu hukunce hukunce kasancewar su bakine a cikin addinin, zuwa yanzun bakaramim mutunta Jakadiya Sarki Muhammad keyi ba acewar shi tazama abun koyi a garesu, wannan kenan


A wajen Huzaifa kuwa yana lambu yasa aka kira mashi Bahijja tana zuwa ta gaidashi cikin kulawa yace. "Bahijja niko inasan intambayeki wani abu.?" fuska a sake tace. "Inajinka ranka shidade." rausayar da kanshi yayi sannan yace. "Yama sunan wannan saurayin naki?" da sauri Bahijja ta kalle shi cikin inkina tace. "Aibanda wani saurayi ranka shidade." "aaa Bahijja miyasa waya hanaki?kodai Malik ne?" girgiza kanta tayi cikin ladabi tace. "Aaa Abba nane, kuma ina baiwa ina kula samari." dai dai nan da Yazid da Lurwan sai Yarima Malik sun shigo cikin tafkeken lambun nasu dan shakatawa suka hangi Huzaifa, Yazid ne yace. "Jibi Huzaifa sai dariya yake da alama soyayya yakeyi nifa ina zargin shi kamar ya fada cikin tarkon so?" wani mummunan faduwar gaba ta riski MalikusSaif har saida ya dafe kirjin shi, ji yayi kamar ya juya ya koma dan baiji zai juri ganin Bahijja da Huzaifa a wannan yanayin, cikin kula Yazid yace. "Yadai Yarima naga ka dafe kirji ko baka lafiya ne?" girgiza kanshi yayi alamun aaa, shiko Huzaifa da tun shigowar su ya gansu yana sane ya fadada dariyar shi irin wanda duniya taima dadin nan, itama Bahijja jin maganar da Huzaifa yai mata yasata yin murmushi mai dan sauti, lokacin su Yarima Malik sun iso cikin fara'a Huzaifa yace.....





_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*



_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم


_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*


Episode 67&68


_*Wannan page din sadaukarwa ne ga dukkan masoyana kusani, sakonnin ku, suna isowa agareni sai dai ince rabbi yabar kauna son so nike maku son fisabilillah*_ ❣️



"Haba keko aishi so ba ruwan shi da wani matsayi ko dukiya, yana zuwa ne a kowane lokaci dan haka....
Yazid ne ya katse mashi maganar d yake yi yace.
"Yau kuma kananan munje sashen ka baka nan."
zama sukayi, saidai ba kadan jikin Yarima Malik yai sanyi ba, gashi ya kasa furta ko uffan sai dai rinanun idanun shi da ya kafe Bahijja dasu, ita ko murmushi takeyi ba abinda ke bata dariya yanda Huzaifa yace, wai saurayin ta, itako ina ita saurayi tana yar karamar ta, shiko Malik wani irin haushin tane ya kama shi awani bangare na zuciyar shi kuwa ji yake kamar ya shaki Huzaifa, maganar Huzaifa ne ya dawo dashi duniyar tunanin daya lula yace. "Yan matana zaki iya tafiya ki huta dan kada kigaji da yawa sai ki kara kulaman da kanki." sunkuyar da kanta tayi alamun mai jin kunyar saurayin ta, cikin siririyar muryar ta tace.
"Barkan ku da zuwa." dukan su suka amsa banda Yarima Malik, jitayi wata irin damuwa ta addabe ta a ranta ko cewa tayi.
"Miyasa Ya Malik ke yawan sauya mani jibi yanda ya hade rai ko anbata mashi rai ne.!?"
a hankali ta saci kallan shi aiko idanun su suka sarƙe dana juna wani irin fitinannan kallo ya watsa mata mai cikeda jin haushin ba shiri ta kawar da nata idanun, jitayi kirjin ta na dukan tara tara, wanda shima hakan take a wajen MalikusSaif addu'a kawai yakeyi, ji yake kamar ya mutu dan takaici, duk abin nan Huzaifa na ankare da halin da abokin nashi ya shiga, murmushi yayi na kasan makoshi yace. "Toh sai anjima, ki saurareni."
gyada kai tayi alamun to sannan ta tafi jiki sanyaye da tarin fargaban halin da Ya Malik dinta ke ciki, maida kallan shi Huzaifa yayi kan MalikusSaif yace. "Aboki na kuyi hakuri nayi nisa cikin shaukin so, shiyasa ban baku kulawa ba, barka da rana Yariman Daborah." gyaran murya yayi a disasshe yace. "Nagode." a cikin ran Huzaifa kuwa cewa yayi haba dan gari da sannu zaka bayyana abinda ke zuciyar ka, Yazid ne yace.
"Huzaifa wai mi Bahijja tai maka?" da gayya ya kalli Yarima Malik yace. "Labarin soyayyya mana mi zatai mani da ya wuce shi!" da sauri Malik ya kalli Huzaifa wanda yakasa boye hushin shi da damuwar shi cewa yayi. "Kai kuma karasa abinda zatai maka sai labarin wani soyayya!." murmishi yayi mai dauke da ma'anoni yace. "Aikuwa kuma kasan wlh ta iya soyayya gaskia Bahijja ta musamman ce." cikeda da kosawa da zance MalikusSaif yace. "Kaga daina gaya mani wannan sakarcin, yarinya karama ina ta iya wata soyayya." ya gama maganar cikeda tsawa da tarin bacin rai, saida kowa ya kalle shi, Lurwan wanda yake binsu da idanu cikin mamaki yace. "Yarima kenan kaga yaran nan har sunfi manya iya soyayyar ma." cikin fada MalikusSaif yace. Kubar wannan maganar ta isheni hakanan sai zancen banza kukeyi." shiru sukayi suna kallan juna shiko MalikusSaif idan shi sun rine, tsabar ɓacin rai.

***********************************

A wajen su Sarki Muhammad kuwa yau ya tashi da bakin ciki marar misaltuwa saka makon kama matar shi gimbiya Yazira da yayi da wani amintaccen bafaden shi suna aikata zina, hakan ba karamin daga mashi hankali yai ba, hakan yasa ya kashe wannan ba faden nashi, sannan yasa masu tsaro a bakin sashen gimbiya Yazira kafin ya yanke mata hukunci, zaune yake a falon shi tareda Jakadiya Aisha, cikin bakin ciki yace.
"Aisha kinga sakamakon zina ko? Ashe haka mutane kiji idan aka haikewa 'yayan su? Ko matan su? Ko yayyan su? Ko kannan su? Ko iyayen su? Ko kuma wani makusan tansu? Yau ina mai bakin cikin ganin wani bisa mata ta kuma bafade na yana zina da matata da idanuna na gan su, yanzun nasan abinda na shukane nike girba na lalata 'yayan mutane da dama wanda bazan iya tunawa ba, hakama ɗana ya ketama yara haddi, yau ga wani da matata, ni kadai nasan yanda nikeji a cikin zuciya ta, tabbas Bahijja haske ce a garemu baki daya,mun godema Allah daya ƙaddara zaman ta a tare damu, akanta na daina bin matan banza sai ita kadai nike kwaɗai tuwa da ita, wanda ubangijin ta Sarki gagara misali ya dinga kubutar da ita daga kaidina, Aisha ta yaya zan tuba akan wannan dauɗar dana tara a jiki na?" ya karashe maganar fa raunanniyar murya cike da nadama.
itama hawaye ta share tabbas tasan Sarki Muhammad yayi tuba na gaskia ya saduda sosai cikin kulawa tace.
"Ya shugaba na ka daina kuka addinin mu addinine mai sauki, tabbas a matsayin ka na tubabbe tun ran daka anshi wannan addinin Allah ya yafe maka zunuban ka, sai dai kasan ance ɗan Adam ajazine, sai ka dinga istigfari kamar yanda su Tasi'u suka koyar damu ka dinga cewa. "Astagfirillahi wa'atubu ilai, ko kuma ka dinga cewa Allahumma gafirril zambi, idan ka dinga fadin haka da ikilasi kana mai sakankan cewa da karɓa Allah zai yafe maka kaf zunuban ka."


Ajiyar zuciya yayi ya rufe idanun shi kamar mai bacci yaci gaba da ambatan kalmomin da Jakadiyar shi taga yama shi, a hankali yana samun nutsuwa a cikin zuciyar shi.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Waisu kuwa yau Sarki Haishir ne da kanshi ya shirya ya tafi Masatautar Raifasu, bai isaba sai da dare sakaliya lokacin kowa yayi bacci bakajin motsin komai, hakan yaba shi ikon shiga sashen gimbiya Yazira tana bacci, taji andanne ta,an rufe mata baki sannan yai mata yankan rago duk shure shuren da takeyi hakan baisa Sarki Haishir ɗagama gimbiya Yazira ba, saida ya datse kanta daga gangar jikin ta, sannan ya daddatse kafafunta da hannayen ta, ya samu takarda ya ruba sako da jinin ta, ya aje saman gangar jikin ta, jin kiran salla yayi a cikin Masarautar Raifasu ba karamin mamaki yaiba, hakan ya tabbatar mashi da cewa Sarki Baidulƙais ya anshi addinin musulunci kenan, wani irin bakin ciki ne ya tokare mashi kahon zuciya, ganin sanyin asuba na kara karatowa yasa shi silalewa ya fice daga cikin Masarautar, haka aka kabbara salla sai dai har yanzun akwai wa'anda basu karbi addinin musuluncin ba a cikin su, sai dai iyayen Zainab da Indo kawayen Bahijja suma sun musulin ta.

Koda gari ya waye har kusan karfe biyu ba gimbiya Yazira ba alamun ta haka Jakadiya tace ma Sarki Muhammad aje a dubata haka akayi kuwa, suna zuwa suka iske anmata kisan gilla bakaramin tashi hankalin suka yiba, abin mamaki ganin takarda sukayi, jiki na rawa Sarki Muhammad ya dauka ya bude yafara karantawa kamar haka


_Idan bacci kake kafarka dan na fahimci kayi nisa, ka dauka alkawalina karyane ka kashemin mahaifi! kasa na manta da zancen ka to kasani da Sarki Haishir kake magana kaga kadan daga cikin aikina ga kan matarka nan ka dinga shan ruwa dashi, sannan ka saurari zuwana nan ba da dadewa ba, yanda na kashe matarka Yazira da hannuwa nima haka zan maka kisan gillar da yafi nata muni sha sha sha......_


Wata iriyar zufa ke tsatsifo ma Sarki Muhammad baice komai ba sai kiran Inalillahi wa'inna ilahirraji'un, sannan ya kalli Sarkin gida Lukman yace.
"Kasa akwashe gawar ta aje ai rami a binne kaga addinin mu ya hanemu da sallatar gawar ta, tunda bata daga cikin mu, Allah ya kyauta gaba ya tsaremu da mugunji da mugun gani, baki dayan su suka amsa da ameen sannan suka fita shida Jakadiyar shi.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Bayan kwana bakwai, zuwa yazun shigema Bahijja da Huzaifa keyi ya fara kai MalikusSaif karshe harya fara gaza sukuni ko dare inyayi da kyal yake bacci gashi duk lokacin da zai kasan ce da Bahijja sai idanun shi sun gane mashi, yauma Huzaifa ne ya shigo lokacin Bahijja na aikin ta hankali kwance, zuwa yanzun tunda Huzaifa yace yana son Bahijja MalikusSaif ya rage sakar mata fuska duk abinda zai sata zai bata umurni ne ko dariya bai mata duk da hakan na azabtar da zuciyar shi sai dai hakan shine mafita a gareshi, yana shigowa da Sallama sai dai MalikusSaif ya amsa shi a ciki ciki bai, damuwa ba yasamu waje ya zauna ya kira Bahijja, zuwa tayi ta duka tana gaida Huzaifa cikin kulawa ya zaro wani farin zobe na azurfa a cikin aljihun shi yace.
"Zobe ne na siya maki shine nace bari inkawo maki nasan zai maki kyau."
murmushi ta saki tanajin daɗin yanda Yarima Huzaifa ke bata kulawa, cikin natsuwa ta kawo hannu zata karɓa kenan Yarima Malik yai sauri ya anshe, wanda tunda Huzaifa ya fiddo zoben nan zuciyar MalikusSaif keneman fashewa cikin fushi.
"Yace ba taso Huzaifa mizatayi da zobe bayan ita baiwa ce.?" mirmushin kasan baki yayi yace.
"Dan tana baiwa sai taki saka zobe.?" a fusace Yarima Malik yace. "ince dai baiwa tace kuma a kalkashin ikona take koh? inko har haka ne ni MalikusSaif nace Bahijja bazata saka zobe ba!"
ya gama maganar a fusace, riko hannu Huzaifa yayi da karfi ya ɗaura mashi zoben sannan ya haɗe hannuwan shi yace.
"Na roƙeka Huzaifa indai kasan abinda ya kawo ka kenan dan Allah katafi anjima munhadu."
itako Bahijja ta kafe Yarima Malik da idanun ta masu shekƙi, a fusace Yarima yace.
"Kika kafeni da kallo ko baki sanni bane? ɓaceman dagani kada insaba maki.!"
da sauri ta mike tana sassafar dan tagama tsora ta da lamarin Yarima Malik, shiko Huzaifa cikin nuna fushi ya mike yace.
"Shikenan ka kora mani masoyiya ta sannan kuma ka kori amininka ko? ina nan da kanka zaka nemoni dan samun mafita sai anjima, haka ya fita, shiko MalikusSaif daki ya shiga ya hade kai wardrofe yana dukan hannayen shi jikin bango yaje ya dawo yaje ya dawo, a zahiri kuwa cewa yayi.
"Waikai MalikusSaif minene damuwarka dan Huzaifa ya bama Bahijja zobe, miyasa kakejin haushin aminin ka dan yace yana son baiwar ka? Wai kodai ka kamu kaima da son yarinyar nan ne baka sani ba?
anya baka afka cikin tarkon so ba? girgiza kan shi yayi yace, "kai bai yuyuwa, mi ruwan ka da soyayyar su? Ba kagaba itama hannun ta har kyarma yakeyi dan zata anshi zoben da masoyin ta yaba ta, tana son shifa zakazo ka saka kanka cikin abinda ba ruwanka.!"
dan karamin tsaki yayi ji yayi anturo kofar dakin nashi, da kallo yabi kofar bakin ta dauke da sallama, a cikin zuciya ya amsa ta dan laɓɓan sane kawai suka motsa kaɗan tana zuwa gaban shi ta zube bisa guiwowin ta tace.

"Ya Malik dan Allah minai maka kake mani haka, kayi hakuri banjin dadin yanda kake bata ranka a kaina, karfa kaman ta kai ne ɗan uwana kuma kace in rikeka a matsayin yaya na majibincin lamari na amman kasauya mani dan Allah idan akwai abinda nike maka wanda bakaso ka yafemani ka gaya mani wlh ko minene zan daina, ina cikin mawuyacin hali."
wata irin tsawa ya daka mata yace.
"Tashi kibani wuri kije kiyi abinda kikaga dama, sannan ki shiga hankalin ki.!" ya karasa maganar yana nuna ta da ɗan yatsa, kuka tafara tana bashi hakuri duk da yanajin haushin ta amman kukan nata na sosa mashi kahon zuciya, ji yayi bazai jure kukan nata ba, ɗaga murya yayi yace.
"Nace ki fita zan nemeki karka ɓatan rai."
jiki a mace ta fita tana kuka sosai kamr ranta zai fita, Allah yasani intaga Ya Malik dinta cikin fushi takan rasa sukuni baki ɗaya.


haka

Please Login or Register in order to submit comment