Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga dan haka yanzun burina zai cika wajen darkake kaf ahalin RAIFASU, na rantse da Gurfanai fansa ga jinin mahaifina Sarki Lahazu.!"


➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿


Bayan kwna ukku, ba laifi jikin Sarauniya Zulaiƙa yai sauki dan ba karamin kulawa mijin ta ke bata ba sai dai kullin idanun ta suna zirarar da hawaye, na bakin ciki da fargabar abinda gimbiya Salsabila ta gaya mata, duk lokacin da Yarima Malik zaizo gaida ta takan nuna shi da yatsa alamun bata son ganin shi, wannan dalilin yasa Safulislam ya hana MalikusSaif zuwa duba ta, shikam zuwa yanzun har ya rame kamar mai ciwon hawan jini duk yayi duhu tsabar tunanin halin da Ummun shi ke ciki yakeyi da yanda bata son ganin shi ko kadan, gashi yana kokarin cire Bahijja a cikin zuciyar shi amman kullin kamar ana kara dasa mashi so da kaunar ta, yana san ya daina son ta dan farin cikin mahaifiyar shi amman abu yaki tura maimakon ya ragu saima karuwa da yakeyi, zaune yake tun safe yake sa ran ganin Bahijja amman ba alamin ba, har sha biyun rana bata shigo ba, wani irin kuna zuciyar shi ke mashi ta azazzale shi da son ganin kyakkyawar fuskar ta, zugum yayi yana nazarin rayuwa maganar zuci yafara yace.
"Bahijja karki ga banbaki amsaba, kisani inayin hakane dan mahaifiya ta, sai yanzun nagane dalilin dayasa mahaifiya ta taki yarda kika sance hadima ta Bahijja ashe wannan alakar take gudu, sai dai ni nadauka tausayin ki nikeyi Bahijja a matsayin ki na yar uwata, ashe sonki yaimani illah Bahijja inaji a jikina son da nike maki bakiman kwatan kwacin shi Bahijja, amman ba yanda na iya dole in girmama ra'ayin mahaifiya akan komai Bahijja saidai kisani ina sonki ina kaunarki."

Jiyayi andafa shi, da sauri ya waigo ganin Huzaifa da Yazid akan shi, ido ya zuba masu, hannu Huzaifa yasa yana goge kwallan da suke shatata a cikin kwayar idanun shi, yace. "Kayarda ko Malik son Bahijja ke dawai niya dakai ko.?"
murmushin karfin hali yayi, mai ciwo yace. "tabbas Huzaifa na farka daga nauyayyen baccin da nikeyi ashe haka so yake Huzaifa ina son Bahijja sai dai ra'ayin mahaifiya yafi karfin in juya mata baya, na kauda kaina akan son Bahijja amman na gaza ya zanyi Huzaifa.?" ya ida maganar tare da wasu irin zafafan hawaye wanda baisan suna sauka a bisa kuncin shi ba.


Share mashi kwallan fuskar shi yayi yace. "Kayi hakuri insha Allah komai zaizo da sauki, zaka samu Ummu da sanyin hali, kuma ka yawai ta addu'a insha Allah soyayyar dake tsakanin ka da Bahijja zata zama alkhairi a cikin wannan Masarautar kayi hakuri Yarima."
ji sukayi ance.
"tabbas Huzaifa hakane duk abinda kukace akan kunne na, Yarima Malik na son Bahijja sai dai baza muyi jayayya da lamarin ubangiji ba saidai kasani Abdulmalik mahaifiyar ka tana cikin yanayi wannan lalurar da kaga tana ciki, labarin soyayyar dake tsakanin ka da Bahijja taji shi, har yana neman saka mata ciwon zuciya, sai dai kaje kasamu mahaifiyar ka ta yafe maka."
da sauri ya iso wajen Kangiwa ya rungume shi yace.
"Abbuh kayafeman ba daga gareni bane bansan haka ta faruba Abbuh." bubbuga bayan shi yayi yace.
"Nasani Yarima dan Adam bai wuce kaddarar shi kadauki taraiyarka da Bahijja daga Allah, ka daina damun kanka ɗana."
haka suka dinga bashi baki jiyayi zuciyar shi ta sauko ya samu sukuni, tafiya sukayi shi kuma ya shiga cikin daki.


A wajen Bahijja kuwa kwance take tana bacci, juye juye tafara, tana cewa. "Ya Malik ina sonka kada kagujeni ina kaunar ka Ya Malik dina kaine jigon rayuwa ta." cikin bacin rai Binta ta tafkama Bahijja uban bugu tace.
"tashi sakara dake baki da hankali ko Bahijja.?" a firgice ta mike tana murtsuka ido cikin magagin bacci take kallan iyayen nata, Abdulmajid ne yace. "Mikeke cewa, Yarima kike so ko?"
kame kame tafara tayi raurau da fuska tace.
"aa Abba bakomai."
wani wawan kallo ya banka mata yace.
"kinci gidan ku, nace dan dibar albarka ni zakima tijara, Yarima Malik zaki so uban gidan naki, kinsan fitinar da kikeson sakamu a ciki kuwa.?"
"Abba kayi hakuri bansan sadda hakan tafaru dani ba." kwashe ta da wani irin lalataccen mari yayi yace.
"Zan ballaki baki san sadda kika fara son MalikusSaif ba ko? Bakisan akan Yarima Malik ba Sarauniya Zulaiƙa zata iya halakaki ba? Ko kin haukace ne zakice kina son Yarima Malik? toh ki bude kunnuwanki da kyau kiji wlh blh duk tsuntsun da ya janyo ruwa shi ruwa ka doka, bazan iya jure ukubar da za'a gana maki ba, sai dai banda zabi tunda ke kika jefa kanki a halaka, wannan rayuwar ma ka tsaya matsayin da Allah ya ajeka ma kana shan wahalar mutanen karshen zamani bare ka wuka iyakar ka, kina baiwa inake ina Yarima, gaskia Bahijja baki mamu adalci ba, amatsayin mu na bayi zaki jamana wulakanci duk gargadin da nike maki ya tashi a banza a wofi kenan kinmin halacci nagode kin kyauta."
rike hannun mahaifin nata tayi tana kuka mai sosa zuciya, fisgewa yayi ya fita yana kwallah, gamuwa yayi da Mairo da takasa karasowa, da kyal itama ta shigo tana kwalla, dan ta san halin da Bahijja ta jefa kanta, a ciki na ukubar rayuwa zuwa tayi tacigaba da yima Bahijja faɗa har kanta ke juyama mata dan kuka, gashi ji take kamar ana kara rura wutar son Yarima Malik a cikin zuciyar ta, itako Binta cewa tayi
"bazan maki baki ba Bahijja sai dai kisani duk kalar cin kashin da akayi mana dake zamuyi koke, shiyasa Zulaiƙa taki yarda ki rabi danta ashe ta hango abinda mu bamu gani ba, ashe soyayya zaku kulla keda Yarima, dan haka in barci kike ki farka, gwara koda zaki mutu ki rabu da son Yarima a cikin zuciyar ki." ita dai Bahijja takasa magana sai aikin kukan da take yi.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

A Masarautar Raifasu kuwa su Jakadiya da Tasi'u ne suka gama shirin su tsaf, a sashen Sarki Muhammad ban kwana yai masu sannan ya hada su da hadimai hudu maza biyu mata biyu da dawakai shida kowa yahau guda, guda suka kama hanyar tafiya nahiyar Daborah

***********************************

Da yammacin ranar alhamis ranar ne Allah yasa Sarauniya Zulaiƙa bakin ta ya bude suna zaune da Saifulislam ta saki wani irin marayan kuka mai tsuma zuciya cikin disasshar muryar ta tace.
"Ya zanyi ina zansaka raina, dama mutuwa nayi da ganin wannan ranar yau Yarima ne zaiyi soyayya da baiwa!? daman itace matar da yaitai mana wasa da tunani wajen fitarwa ya batama dan uwana lokaci! Saifulislam kaga abinda ɗanka zai mani? tabbas Abdulmalik ya zama butulu ya zama korarre, kuma barrantacce a wajena wlh saina.....



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*



Episode 77&78




Dakatar da ita Saifulislam yayi ranshi ya sosu ya gama ɓaci a fusace yace.
"Karki kuskura kima ɗana baki! kawai dan yaso baiwa, ita baiwar ba mutun bace da zaki dinga wulakanta bayi kina cin zarafin su?"

Itama a fusace take kallan Saifulislam da rinanun idanun ta masu kama da garwa shin wuta tace.
"Kaga Saifulislam karka gaya mani ba dadi baiwa ba mutun bace kuma matsawar Yarima Malik ɗana ne, kuma cikina ya kwanta da ya auri wannan makirar baiwar gwara inga gawar shi zai fiye mani sauki, ni za'a wulakanta a tozar ta, ace kamar ni Sarauniya Zulaiƙa ace ɗana magajin mulkin Daborah Yarima kamar Malik ya auri baiwa! hakan bazai taɓa yuyuwa ba saidai in ban raye.!"
karasowa yayi gaban ta yace.
"Saime dan Malik ya auri baiwa? Nace maki saime Zulaiƙa.?" cikin ɗaga murya ta nuna Saifulislam da ɗan yatsa manuniya tace.
"Badai jinin Sarauniya Zulaiƙa ba sai dai in dana haifi Abdulmalik an masanya mani sh, ba dai jinin Sarki Abdulkadir ba ɗa ga Sarauniya Yahanazu, jika ga Sarauniya Balkisu, jini ga Sarki Khalid ba, ba dai jinin Sarki Jabbar, dan uwan Sarauniya Maimoon uwar Sarki Jumal ba, wlh ba daini Sarauniya Zulaiƙa yar Sarki Abdulhamid ba, za'a ce magajina kamar MalikusSaif zai auri BAIWA yar wahala kamar wannan watsatsiyar yarinyar ba, sai nayi ajalin wannan yarinyar, ace magajin mulkina ya auri BAIWA!?"


Murmushi Saifulislam yayi cike da gadara yace. "Ki bude kunnuwan ki kijin da kyau Abdulmalik Saifullahilislam bai gaji Sarauta ba, kasuwanci ya gada, tun kaka da kakanni dan haka ɗana ni zai gada tunda da UBA ake ado ba UWA ba kuma uba ake gado! dan haka kijini da kyau Ya Zulaiƙa inhar Allah ya kadara MalikusSaif sai ya auri Bahijja ba makawa sai anyi, sannan idan akan wannan Sarautar zaki dinga yin kumfar baki kina tsinema yarinya dan kawai tana baiw, zaki hana ɗanki magajin mulkin ki auren ta, to ki rike mulkin ki ba abinda Abdulmalik zaiyi da mulki ki rike Sarautar ki kibar shi da son Bahijja da kuma gadon fatauci da yayi a wajen mahaifin shi saboda shine igiyar da mahaifin shi ya rike tun kaka da kakanni, kuma kowa yasan waye Saifulislam ba matsiyaci ban, kasuwanci ya rike dan haka ɗana bazai yi mulki ba kasuwan ci zai rike, inafatan kin fahimta Ya Zulaiƙa!?"


Jitayi zuciyar ta ta tsinke yau ita Saifulislam ke fadawa wadan nan maganganun akan BAIWA? Zaice danshi bazai gajeta ba, bayan ta gama dora buri kanshi shi daya tal, takawa tayi har gaban Saifulislam tace.
"Karya ne sai dai bada tsatsan Sarauniya Yahanazu yake ba, dole ya zama Sarki na *ɗari da* *casa'in da tara* a cikin jerin Sarakunan Daborah, sannan kuma ya zama *na dari biyu da* *hamsin da tara* a cikin jerin mulkin kama karya na mulkin kujarar alfarma ta Daborah, sai dai inbai numfashi wannan kuma daga Allah ne amman ba makawa MalikusSaif *Sarauta* ya gada ba *Fatauci* ba kuma ba *SARKI* ba auren *BAIWA*.!"
tana gama fadar haka ta fita a fusace shiko MalikusSaif yazo shigowa yaji artabar da iyayen nashi keyi akan shi baisan ya koma baya ba, duk abinda ya wakana ba abinda baijiba saidai baida zabi, addu'a yake Allah ya kaddara mashi tsanar Bahijja ko ya huta da wannan bala'in dake shirin tunkaro su, a cikin zuciyar shi ji yake kamar ta fashe dan takaici.


Washe gari da safe Binta na zuwa wajen aiki iske ta tayi harɗe a falon ta dukawa tayi ta gaida Sarauniya Zulaiƙa kamar jira ta kira Binta tana zuwa gaban ta ta dinga kwaɗa ma Binta mari abu kamar wasa saida taima Binta mari yakai huɗu take kuncin ta ya kumbura ga jini na zuba a saman bakin Binta, amman Sarauniya Zulaiƙa bata daina marin Binta ba, su Huzaifa ne suka shigo shida MalikusSaif dan basu ba Sarauniya Zulaiƙa hakuri suka iske wannan danyen aikin, itako Binta sai shara kuka takeyi ji take kamar ta suma dan azaba, Yazid ne ya fara bata hakri tana ganin MalikusSaif ta koma kan shi dukawa yayi yafara neman afuwar mahaifiyar tashi, tunkan ya ida dukawa Sarauniya Zulaiƙa ta wanke Yarima Malik da zazzafan marika har guda ukku a fusace tace.
"Allah yawadaran wannan tsinannan halin naka Malik dan ɗibar albarka kai karasa wadda zakaso sai baiwa, kasani kuma ka saka a ranka ni dakai munyi hannun riga daga yau sai yau bani bakai na yafeka!
sannan yau zan nuna maka karshen so badai baiwa kake so ba? ke Binta maza kikarawo mani Bahijja kika bari dakika ukku takara saina halaka ki da ita kanta sakarai jahila jaka."
ita dai Binta ta tashi ta tafi kiran 'yar tata saidai tana cikin fargaba da bacin rai, haka ta isa har turakar bayi ta iske Bahijja zaune ta buga uban tagumi tana kuka mai sosa rai, Binta na zuwa ta watsa mata wani irin matsiyacin kallo da sauri ta mike saboda yanda taga mahaifiyar ta ta tana kallan ta bakaramin firgita taiba, cikin tsoro tace.
"Umma lafiya na ganki a wannan lokacin." batasan sadda ta kifawa Bahijja maruka har guda biyu ba tace.
"Uban kine! dan ubanki ke harkin isa kiyi mani wannan tambayar bayan kin gama haɗa gadar zarenki yanxun kice zaki tambayeni, kingane mani yarinya dan uban ki! toh hankalin ki ta kwanta yau kin shiga tsakanin ɗa da uwa yau ga Sarauniya Zulaiƙa ta sa hannun ta ta mari Yarima duk a dalilin ki, duk irin so da kaunar da take mashi, yau gashi kin sa kama Yarima Malik da alkhairi yaron da yake kyauta ta maki tin kina cikin zanin goyo, yau gashi kin saka shi cikin tashin hankali, yanzun sai kije ki girbi abinda kika shuka, dan ni kaina uwarki ban tsiraba daga ukuba ko azabar da Sarauniya Zulaiƙa zatai mani ba, tayimin marar dalili bare yanzun da take da hujja inake baiwa ina son Yarima! wue mutafi ja'ira kika tsareni da kallan munafunci kinbani kunya Bahijja!."
kuka mai tsuma zuciya ta sake yi, ita kanta tasan son Ya Malik daga Allah ne, da zata iya da ta hana kanta, cewa tayi. "Umma kiyafemani nasan na jefa duk wani ahalina cikin musifa." "yimin shiru baki fara kuka ba Bahijja sai sadda kikaga a gaban idanun ki, ankama mahaifin ki an wulakan ta shi sannan zaki fara kuka, wuce mutafi, haihuwa ce ta jawo mana wannan bala'in kuma bamu da abinda zamuce sai mu godema Allah."
haka suka tafi duk inda zasu wuce tunda daga turakar bayi sai nuna su ake ana kus kus, a darare suka isa har sashen Sarauniya Zulaiƙa, lokacin Yarima Malik yana can guiwa bibbiyu yana neman afuwar mahaifiyar shi dan ba karamin tsorata yaiba ganin hankali da tunani mahaifiyar sun rabu da ita sai kwallan azaba sa fargaba takeyi, suna shigowa Sarauniya Zulaiƙa ta figi wata jibgegiyar bulalar fatar rakumi da ta jiku da jikon gidan Sarauta tunkan Bahijja ta duka Sarauniya Zulaiƙa tafara yimata ruwan bulalai da kanta, haka taita zubawa Bahijja bulala tako ina har a fuska, ita kuwa dukewa tayi tana kare kyakkywar fuskar ta gudun kartai mata illah, amman ina abun yafi karfin tunanin duk wanda ke falon itako Bahijja hartakai kasa haka Sarauniya Zulaiƙa tai binta da bugu har harbin ta takeyi tana tsine mata albarka, Binta kuwa dukewa tayi tafasa uban kara ganin Bahijja na tumurmusa ga bakin ta ya ɗaɗe jini na kwaranya, da sauri Yarima Malik yayi kan mahaifiyar tashi ganin zatayi kisan kai, saibdai a fusace ta nuna shi da yatsa tace.
"ka kuskura kace zaka taɓani dan ceton wannan wulakantar tar BAIWAR saina tsine maka albarka MalikusSaif, baka da anfani a cikin wannan zuriar tamu ka wulakanta a halin Sarki Abdurrazak na ɗaya da har kake soyayya da baiwa!"
cak Yarima Malik ya tsaya yana dafe kanshi da yake ji tamkar ya fashe, cigaba da halba Bahijja tayi itako ta dafe ciki tana kwalla dan kuka mai sauti ya gagari Bahijja.
itako Sarauniya Zulaiƙa ji tayi anrike mata hannu a fusace ta juyo da niyar taki fama wanda ya riketa da mari sai taga Matawalle dan Sarauniya Zulaiƙa Allah ya horema ta tarin zuciya Matawalle ne rike da ita yana girgiza mata kai, tana ganin shi batasan sadda ta faɗa saman kirjin Matawalle ba ta saki marayan kuka, cigaba da dan bubbuga bayan kanwar tashi yayi, yana kallan Yarima Malik da yagama fita tunanin shi tsabar bacin rai da takaici, shi kanshi jin wannan labarin ya sosa mashi rai matuka amman ance inrai ya baci hankali baya gushewa, duk abinda ke wakana aminin nashi Saifulislam yai mashi bayanin komai, zaunar da ita yayi yana lallasar ta, itako Bahijja da kyal ta zauna jikin ta duk shatin bulalai ga jini na zuba a lips dinta, Binta ta rarrafa zata kama yar tata a tsawace Sarauniya Zulaiƙa tace.
"kika kuskura kika taɓata saina sauyamaki kamanni!."
Kallan wani hadimin ta tayi tace.
"kai Laminu kaimin wannan wulakantattar baiwar gidan Yari aita dukan ta har buzun ta, tabbas hankalin MalikusSaif yai masifar tashi, har zaiyi magana sai dai Matawalle yaima shi nuni da karyace zaiyi magana, shima shiru yai baice komai ba dan ya fahimci a wannan yanayin ba abinda Sarauniya Zulaiƙa bazata iya aikatawa ba, itako Bahijja tashi tayi aka tisa keyarta kamar barauniya aka garkame ta, koda aka rufeta zama tayi kasa tana kuka mai sosa rai, ba abinda ya bata mata rai irin kalaman da Sarauniya Zulaiƙa ke dan gantata dasu, Allah yasani tana son Ya Malik sai dai kodan mahaifiyar shi dolen ta, ta hakura dashi, kodan kada aci gaba da wulakanta mata iyaye.

Itako Zulaiƙa cigaba da kukan ta tayi tana cewa "Yaya nashiga ukkuna kasan abinda Yarima ya aikata kuwa? Yaya inama mutuwa nayi na huta Yaya....rufe mata baki yayi da tafin hannun shi yace.
"Naji komai Zulaiƙa, kidaina wannan kukan naki kema kinsan ganinki cikin wannan damuwar zai sa ingilgiza kece jinina Zulaiƙa, mubi ɗanmu a masala dan samun saukin wannan al'amarin."
"aa Yaya ba wannan maganar dole yau din nan ai baikon Yarima da gimbiya Zahara'u." a dimauce MalikusSaif ya kalli mahaifiyar tashi.

Cikin hikima Matawalle yace. "Naji muje ciki ki kwanta anjima duk wannan maganar munyita haka yakaita har bedroom dinta shiko MalikusSaif sashen shi ya wuce yana kwalla baisan abinyi ba a halin yanzun koda Matawalle ya fito baiga MalikusSaif ba sashen shi ya bishi iske shi yai yaje ya dawo ya rasa mafita, yana ganin Matawalle ya rungume shi yace.
"Kawu tawa ta kare muddin akace Zahara'u za'a auraman,ban son ta wlh na tsaneta Kawu!"

bubbuga bayan shi Matawalle yayi cikin tausayin ɗan nasa yace. "Karka damu kai dai kabi abinda iyayen ka suka umurceka duk da mahaifin ka baisan aimaka auren dole saidai baka da wani zabi kacigaba da addu'a Abdulmalik,sannan kasani duk wani ahalin mu kaf kasosa masu zuciya da ka zabi baiwa a matsayin matar da zaka aura, duk da ilimi ya kori abubuwa da dama a cikin wannan Masarautar, amma kasani bamu da makiya maciya amana sama da bayi, yanzun gashi an wayi gari magajin wannan Masarautar shike son baiwa, kasanya wannan lamarin bisa mizani Abdulmalik?"


Shi kanshi ya rasa abin cewa saidai kwalla dake zarya a saman fuskar shi ba abinda yake tausayi irin halin da mahaifiyar shi ta jefa kanta akan bayi da yanda take nuna musu kiyayya karara a cikin idanun ta da zuciyar ta, Matawalle ne yace. "Dan haka kaima kaje ka kwanta dan hutawa zuwa anjima zan nemeka dan asamu ayi sulhu a cikin wannan lamarin mai rikitarwa." shi dai MalikusSaif sake rungume Kawun nashi yayi sannan ya shiga cikin bedroom dinshi ya kwanta

A gidan Yari Bahijja ce ke ta kuka tarasa abinda ke mata dadi tarasa dalilin dayasa ta gayama Ya Malik shi takeso bayan shi ba tsaran tabane ita kuma kaskan tattace marar galihu, yau gashi ta jefa mahaifan ta cikin kunci da fargaba, tana cikin kuka taji mai kula da ita yace tayi bakuwa, budemata kofa yayi, da kamar bazata fito ba, sai kuma ta fito abin mamaki gimbiya Zahara'u ce cikin shigar alfarma tasha alqabba, cikin gadara da nuna isa tacema Bahijja.
"Baiwa baiwa yai bayi jikar bayi tattaɓa kunnen bayi wadda ta gaji bauta da wahala marar yanci da galihu, ko zakiso jin wannan labarin mai dadin sauraro?"
rufe idanun ta Bahijja tayi tana karajin tsanar Zahara'u a cikin ranta, jitayi tace.
"Yanzun haka kwarson ki yana can nasa anata dukan shi kamar jaki ke kwarama jaki dashi tunda bai gaji komai ba sai tarin bauta." da sauri Bahijja ta bude rinannun idanun ta tana kallan gimbiya Zahara'u da take ta murmushin ƙeta, takowa Bahijja tayi tana zagaye gimbiya Zahra'u cikeda gadara Bahijja tace....





_Yar Mutan Kankia ce ❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



_Domin samun Audio novel dinmu ga dama ta samu, domin mun sama maku YouTube channel dan samun saukin karatu sae dae ki saurara ba tare da kinsha wahalar karatu ba😁👇_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*


Episode 79&80



"Banyi mamakin jin wnnan maganar ba, ga wajen wadda batasan darajar kanta ba bare na iyayen ta, dan haka kijini da kau kuma ki fahimta amman idan kwakwal taki tana ja, daga yau kika kuskura kika kara shiga cikin gonata ba gimbiya ko Sarauniya kike sainayi kaca kaca dake, yar Waziri ko? Toh yar Sarki kike sainayi kasa kasa dake sakara dake!." a fusace Zahara'u takawo wani mugun mari a kuncin Bahijja ta rike hannun kam sannan ta wullar dashi, da yatsa ta nuna Zahara'u dashi tace. "Karki kuskara kice hannunki zai tafaɓa wannan fuskar tawa, koda take fuskar Baiwa saidai mai daraja ce, tunda mutun mafi mahimmanci da matsayi yace baisan komai sai wannan fuskar da kike ikirarin mari, dan haka ba haneki kuma na kiyayeki Zahara'u, Bahijja tafi karfin duk wani tunanin ki Bahijja tafi karfin daukar wulakancin kaskantatta irinki, masu iya hukunta Bahijja sai mutane masu mahimmanci da kima da daraja da girma, ba irin kiba marar hankali da tunani!" wani irin bakin cikine ya tokare zuciyar Zahara'u tana mamakin yanda Bahijja bata tsoranta bare shakkar ta take gayamata maganganu mararsa dadin ji da sauraro, duk da kasancewar ta Baiwa, harta ɗisa mata shakka da tsoranta a cikin zuciyar ra dan gani take kamar mai jinnu dakewa tayi tace. "Haka kikace ko? Kisani dani kike zancen saikin kwashi kashin ki a hannun ki, sakara Baiwa yar bayi sainayi ajalinki, keda Yarimana saidai kallo wlh yafi karfin ki." itadai Bahijja bata kuma cewa komai ba, saima shigewa da tayi dakin da aka killace ta haka tabar Zahara'u bude da baki tana mamakin karfin hali irin na Bahijja......


Saifulislam da Matawalle sai Malik da Sarauniya Zulaiƙa kowa ya nutsu Matawalle ne yace. "Kangiwa?" kallan shi Saifulislam yayi yace. "Na'am." sannan ya waiga gafen haggun shi yace. "Zulaiƙa.?"itama amsawa tayi tana murza zoben gold dake jikin yatsun hannun ta, kallan kasa yayi inda Malik ke zaune bisa lallausan kafat da yake shimfide a cikin falon Saifulislam yace. "Abdulmalik.?" kanshi ya kara saddawa kasa yanaji zuciyar shi nata duka fat fat amsawa yayi yace. "Na'am Kawu." cigaba da magana Matawalle yace. "Inasan kowa yabani aran hankalin shi akan wannan lamari, kaidai Malik yanada kyau ka nemi afuwa da gafarar mahaifiyar ka, sannan kaimata biyayya ka aje son wannan yarinyar da kakeyi, ka dauki kaddara maganar gaskia kasan ance kowace kwarya da abokin gurbin ta kuma kaga yarinyar baiwa ce mahaifiyar batason alaka ta shiga a tsakanin ku, nafison wannan gidan yazama gida mai tarin albarka da lumana kaga da ayi kwara kada afara, kai kanka bazakaso ace ka auri mata ba, amman tana cikin matsala da tashin hankali ba."


Shidai Malik bugun da zuciyar shi keyi sai karuwa takeyi ya rasa dalilin dayasa yake shiga cikin wannan yanayin lokuta da dama, dakewa yayi yace. "Kawu yanda kace haka za'ayi dan Allah Ummu kiyi hakuri, naji na hakura, saidai banda wani zabi da zanyi dakaina kowace ku zabamin farin cikin ki shine nawa Ummu." duk da taji dadin furucin dan nata saidai ta daukar ma kanta saita hana su Bahijja da iyayen ta shan ruwa cikin Daborah, Matawalle ne ya kalleta yace. "Kinji abinda dan naki yace amman kinyi shiru.?" murmushin karfin hali tayi tace. "Badamuwa Allah ya tabbatar da alkhairi kuma na yafemaka." godiya yaima mahaifiyar tashi saidai shi kadai yasan mawuyacin halin da yashiga cikin kankanin lokaci wani mugun jiri yakeji yana dawainiya dashi, Matawalle yace. "Kangiwa bakace komai ba.?" kallan Malik yayi yadan girgiza kai dan yafahimci danshi yana cikin yanayi amman zaisa ido yaga iyakar su, cewa yayi "Alhmdullh tunda ansamu sasanci naji dadin hakan saidai inada nawa sharadin.!" kallan tuhuma Sarauniya Zulaiƙa taima mijin nata ko kallan arxiki bata isheshi ba dan mugun haushin ta yakeji a halin yanzun cewa yayi "Bahijja zataci gaba da aikin ta kamar yanda aka alkawalta sama da shekuru shabiyar, wannan shine nawa sharadin." girgiza kai Zulaiƙa tafara,

Please Login or Register in order to submit comment