Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ace yanzun zanyi ido hudu dashi bako shakka saina sauke kanshi kasa.!"

Kallan kallo aka shiga yi tsakanin Yarima Malik da Huzaifa, kowa yai shiru yana mamakin irin kalaman da Sarki Baidulƙais ke faɗa, ga tarin kiyayya nan kwance a kan fuskar shi.

Huzaifa yace. "Kaga ko na manta in gaya maka muna godiya da masauki da aka bamu yau dinnan zamu wuce,

Ba karamin mamaki Baidulƙais yayi ba, jin sunce yau zasu tafi saida ya nuna rashin jin dadin tafiyar su a zahiri.
Murmushi karfin hali yayi yace.
"Ya kamata ko satine kuyi mani gaskia."
"karka damu zamu sake kawo maka ziyara akwai wani fatauci da zamuyi shiyasa." cewar Huzaifa, fuska sake ba yabo ba fallasa, Baidulƙais yace.

"Bakomai saidai ina san inbaku sako ku kaima yayan ku Sarki Danwar, sannan ku gaida gida naji dadin wannan ziyara da kuka kawo mani."

"Ba komai." cewar Huzaifa. jinjina kai Sarki Baidulƙais yayi, alamun gamsuwa sannan ya fita.
suma ida haɗa kayan su sukayi bada jimawa suka fito dan tafiya, Sarki Baidulƙais ya aiko Jakadiya ta basu wata takarda tace Sarki yace a kaima Sarki Danwar, amsa Huzaifa yayi nan suka kara ban kwana da Jakadiya tana masu fatan alkhairi da samun nasara.
haka suka hau dawakan su suka tafi kowa da abunda yake sakawa a cikin zuciyar shi.


Haka sukayi tafiya mai ɗanyi nisan gaske, Yarima Malik ne yace. "Ina kake tunanin zamu soma neman Bahijja."?Shiru Huzaifa yayi, yana ɗan nazari sannan yace. "Allah yataimaki magajin gobe a ganina mufara dubawa ta yankin Ƙaisu kilan a dace, tunda kaga sunfi kusa da wannan Masarautar."
haka suka dinga tafiya ba tareda Yarima Malik yace komai ba.



Masarautar Waisu kuwa Bahijja ce suka gama aikin da gimbiya Ƙamariyya ta saka ta, tana gamawa ta tafi sansanin bayi masaukin da aka bata ita da wasu bayi zama tayi tana ta nazari, ta saka wannan ta kwance wancan ba abinda takeso irin taga ta samu damar guduwa dan bata yarda da Yarima Haishir ba ko kadan, rasa mafitar da tayi, hakan yasa ta kwanta ta rasa mike mata dadi a rayuwar ta, bacci ne ya soma ɗibarta tana cikin bacci tayi mafarkin gata a cikin wata sahara ba kowa a wajen da alama mutanen wajen sun mutu, itama taimako take nema saiga wani saurayi saman doki da takobi a hannun shi, mika mashi hannu tayi tana cewa kataimaka mani, zuwa yayi ya kamo hannun ta ya ɗagota a bayan su kuma wasu ne saman dawakai da kibiyoyi sunata halbo masu dan dai basu samesu ba haka sukaita gudu saman doki cikin kankanin lokaci a kaimasu rina aka zagaye ko ina, can sukaji wani mutun nacewa ina zaka kaita, daga gefen su wani ya zare wuka zai kashe wannan saurayin da ya ceceta!
da sauri ta mike zaune tana karanta adduo'i a bakinta sai zufa takeyi tana yan kalle kalle bata amince da mafarki takeyi ba saida taji wata baiwa tace mata, tafito ta anshi abincin ta a madafa inda bayi ke ansar anbinci sannan ta mike jikin ta duk yai sanyi dan tsoro duk ya gama addabar zuciyar ta.



Yarima Haishir ne zaune a wajen mahaifin shi yana mashi maganar Bahijja, cikin kosawa Sarki Lahazu yace.
"Kaga Haishir kabar zancen wannan yarinyar karfa kaman ta baiwa ce nasa ka ɗaukota kawai dan in muzguna ma Sarki Baidulƙais badan komai ba, dan haka kabar ta tayi aikin bautar ta danshi yafi dacewa da ita"
wani irin haushin mahaifin shine ya kama shi daurewa kawai yayi yace. "Baba kaikace zaka ƴanta mani Bahijja sannan ka auramani ita, yanzun so kake inyi abinda zai kara taɓa martabar ka data wannan Masarautar."?

Karamin tsaki Sarki Lahazu yayi yana maijin haushin maganar da danshi yaima shi,marar dadin sauraro daji a fusace yace....




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 9&10



"Kaje kayi abinda kake tunanin zakayi Haishir ni kuma bazan ƴanta Bahijja a halin yanzun ba sai naga yana yin tafiyar, ni nasan abinda nikeyi dan haka zaɓi ya rage gareka ko kabar Bahijja zuwa wani lokaci muga abinda zai buyo baya ko kuma kayi abinda kake tunani zakayi, saidai tabbas zaka haɗu da fushina.!"

A gadaran ce Yarima Haishir yace ma mahafin nashi.

"Nidai nagama faɗamaka abinda ke zuciya ta, ko kaɗauki mata ki ko kuma duk abinda ya faru kar kaga laifina namayi juriya dan haka kaga tafiyata."

Bai jira cewar shi ba ya kama gaban shi, wani irin bakin ciki ne ya mamaye zuciyar Sarki Lahazu ba, ganin yanda ɗan shi ke kumfar baki akan baiwa, girgiza kai yayi yana sake sake a cikin zuciyar shi yanda zai ɓullowa lamarin Haishir.



A wajen gimbiya Yazira kuwa tana zaune a sashen ta tana shan lemun kankana wani bawa ne yazo yana sanar da ita zuwan wani mutun, tunda aka sanar ma gimbiya Yazira jikin ta yayi liqis alamun damuwa a fuskar ta cikin sanyin jiki tasa aka shigo dashi kallan bayin wajen tayi kowa yabar wajen baki ɗaya ta maida kallan ta a wajen mutumin cewa yayi. "Tuba nike uwar ɗakina tabbas rana ta ɓacewa ƴan maza an kwace Bahijja daga hannun mu sannan kuma an kashe mutane na nima saura kadan a halakani tsoro da shakka suka hana in sanar maki faruwar lamarin, tuba nike kimin aikin gafara.!"

mikewa gimbiya Yazira tayi a kiɗime ta rasa inda zata saka kanta taji dadi batasan sadda wanke shi da mari mai raɗaɗi ba, cikin ɗaga murya tace . "harka isa ka gaya mani haka in saku aikin ku gaza ai daman sun kashe ka da kowa ya huta.!"
tana cikin magana sukaji Sarki Baidulƙais yayi gyaran murya kowa saida cikin shi ya ɗuri ruwa tsoro ya addabi kowa, shiru sukayi suji mi, Sarki Baidulƙais zaice masu, a hankali ya karaso zuwa inda suke yana zagaye su hannun shi goye a saman baya, danko gimbiya Yazira take tayi jiɓi fatan ta kardai ace Sarki Baidulƙais yaji abinda suke cewa yanda yaga rashin gaskia atattare dasu hakan yasa shi yin wani shu'umin murmushi sannan yace.
"Waya ɗauke Bahijja."? Daburcewa kowa yayi cikin su da sauri gimbiya Yazira tace. "Daman na aike su daji dan su sama mani maganin shawara suka haɗo da wasu samari sun ɗauko Bahijja garin taimakon ta aka kashe mashi abokai shima da kyal yasha shine yazo yana sanar mani yanzun nike cewa zanje in faɗa maka dan kaɗauki mataki.!"


Cike da rashin yarda Sarki Baidulƙais yace ma mutumin
"katabbata sannan kasan su waye suka sace Bahijja."?

Muryar shi na rawa alamun rashin gaskia yace.
"Aaa saidai da ganin su sunyi kama da ƴan gidan sarauta ko shakka babu! ."


Murmushi yayi a ranshi kuwa yana cewa bakowa bane face Sarauniya Zulaiƙa kuma ina zatan Yarima Malik ne ya aiko aka ɗauke Bahijja dan haka nan da kwana biyu zan haɗa gangami aje a yaki Masarautar Daborah.


A zahiri ko bai amince da gimbiya Yazira ba, duk da baiji abinda suke cewa ba saidai yaji tace aikin da tasa su.....
koda yake da sannu komai zai bayyana nuna su yayi da yatsa yace. "Minene sunan ka."? Da sauri yace. "Sunana Wadir."yace da Sarki Baidulƙais jinjina kai yayi sannan yace.
"Kasa a ranka muddin nasa meku da karya ko cin amanata na rantse da gurfanai saina halaka ka, ke kuma Yazira kinsan abinda zan iya kinsan abinda bazan iyaba kiyi fatan baki da hannu akan lamarin Bahijja duk wanda nakama da hannun shi a ciki tabbas nikaina bansan kalar hukuncin da zamma shiba kikiyaye gaba."

Jikin ta na ɓari tace to.

A fusace ya fita ba inda ya wuce sai fa'da yasa aka haɗa mashi taron gaggawa da yan fa'dar sa, tun kan a hallara ya kasa tsaye ya gaza zaune, sai zagaye yakeyi ya rasa mike mashi dadi tunda Bahijja ta ɓace Baidulƙais ke cikin damuwa kullin sai yasa anje anemo Bahijja amman ba amo ba labarin ta......

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

Suko su MalikusSaif da Huzaifa ba inda suka tsaya sai wajen wata bishiya nan suka zauna dan hutawa Yarima ne yace. "Huzaifa kana ganin zamu iya gano Bahijja daga nan zuwa jibi."?
"Eh insha Allahu za'a ganta ni nafi zargin ta da Masarautar Ƙaisu." shiru MalikusSaif yayi yana nazari ɗauko wasikar da Sarki Baidulƙais ya basu sukai ma Sarki Danwar yayi ya buɗe ya fara karanta ta kamar haka.


_Daga Sarki Baidulƙais zuwa ga Sarki Danwar ina san inyi haɗin guiwa da Masarautar ka da tawa ina fatan zaka bani aron mayaka kamar yanda muka saba a tsakanin mu dan in fuskan ci Sarauniya Zulaiƙa da jama'ar ta ina sauraran ka daga Masarautar Raifasu_


Rufe takardar Yarima Malik yayi yana yaga takardar bayan ya faɗawa Huzaifa abinda ta kunsa sannan yace. "Huzaifa tabbas koda Bahijja ta dawo garemu Ummu bazata taɓa raga mata ba, musamman yanzun da tasan natafi neman Bahijja."

Wani irin tausayin Yarima ne ga kama Huzaifa, cikin sanyin murya yace. "kwarai kuwa Yarima ni kaina nasan muna cikin damuwa marar iyaka fata dai Allah yasa muganta dan mu koma da wuri kafin Sarki Baidulƙais ya ɗauki mataki akan Masarautar mu dan ahalin yanzun ita yake zargi a zahiri, kana ganin zuwan mu Masarautar Ƙaisu zai mana anfani."?

Ajiyar zuciya mai karfi Huzaifa ya sauke yace.
"Baida wani anfani wannan wasikar kadai ya isa ya wanke Masarautar Ƙaisu daga zargin ɗaukar Bahijja saidai mutafi Masarautar Waisu raina na bani Bahijja nacan."


"Ko miyasa?."cewar Huzaifa, murmushi Yarima yayi yace. "Ka manta da Yarima Haishir a kayi yaƙi kuma muka kama su yaga Bahijja zai iya riketa kodan ɗaukar fansa, ko kuma cima wani buri nashi na daban nasan waye Haishir shida Husbarul halin su ɗaya wannan dalilin yasa nace Bahijja tana Masarautar Waisu inaji a raina."


Cikedangamsuwa Huzaifa yace. "Nima naji na aminta da hakan saidai kana ganin zuwa Masarautar Waisu zai kaimu tsawon kwana nawa.?"
tashi Yarima Malik yayi batare da yaba Huzaifa amsaba suka hau dawakan su saida sukai tafiya mai nisa sannan ya kalli Huzaifa yace. "Idan ka ɗebe mani daga inda kai mani wannan tambayar zuwa nan zamu iya ɗaukar kwana biyu zuwa na ukku zamu isa Masarautar Waisu fata dai indace da Bahijja dan zuwa yanzun narasa gane wane irin tausayin Bahijja nikeyi minene matsayin Bahijja a gareni baiwa ta ko kuwa kanwata kuma ƴar uwata saidai na baka wannan damar da ka sama mani wannan amsar koda ba yanzun ba abokina." dariyar shakiyanci Huzaifa yaima Yarima Malik yace. "Nifa ina ganin kamar son Bahijja kakeyi." wani mugun kallo yaima Huzaifa na karaina ni baice komai ba sukaci gaba da tafiya shima Huzaifa murmushi kawai yayi ya basar yasan halin mutumin nashi komai kaɗo mashi yakeyi yanzun kuma yan miskilanci ne akanshi a kowa da abinda yake tunani da haka dai suka nemi hanyar da zata sada su da Masarautar Waisu......



_Masarautar Daborah_



A wajen Sarauniya Zulaiƙa kuwa ba abinda ya sauya kullin bata da ƙuduri daya wuce taga ta halaka Abdulmajid dan ita a ganin ta wannan gazawa ne ace kamar ita Sarauniya Zulaiƙa! ace ɗanta kuma magajin ta yaje neman baiwa, yau din ma sawa tayi a kaima Abdulmajid bugun mutuwa ko ɗaga hannun shi bai iyawa itako Binta aikin wahala tasa ta ga zazzaɓi mai zafin gaske tanayi hakan yasa tafara amai saidai hakan baisa an ɗagama Binta ba duk tsufanta,
a wajen Ashir kuwa kullin sai ya zubda kwalla gashi duk lokacin da yai yunkurin gayama Sarauniya Zulaiƙa shine yaje Masarautar Raifasu sai ta hana shi yin magana yau dai ya ɗaukar ma kanshi alqawali koda zai rasa ranshi sai ya fidda Sarkin bayi Abdulmajid daga cikin ukubar da yake ciki shida Uwar bayi Binta da haka ya tashi ya tafi fa'da dan ganin Sarauniya Zulaiƙa inda take tattaunawa da ƴan fadar ta kan sakon da Sarki Baidulƙais ya aiko mata na artba dashi a watan gobe dan fuskan tar a bokan gaba wanda wannan a wajen ta ba komai bane.

_Masarautar Waisu_

Shiko Yarima Haishir koda ya koma dakin shi zama kawai yayi yana tunanin inda zai ɓullowa mahaifin shi wani ɓangaren na zuciyar shi na ganin ya farma Bahijja dan biyan bukatar shi, wani kuma nace mashi kwara ka kara hakuri ka aureta zaifi saidai abinda ya sani duk rintsi saiya biya bukatar shi akan Bahijja da wannan tunanin ya kwanta kamar mai bacci yana sake sake a cikin ranshi iri iri masu wuyar fassar.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿
A gidan yarin Raifasu kuwa su Tasi'u ne suke ta karbar azaba marar kyaun gani wani waje ne aka ware su na musamman ana gana masu azaba, tun suna ganin zasu iya ɗaukar azabar da ake masu har suka fara saduda, ba arziki suka amsa laifin da ake tuhumar su, duk da hakan abanza a wofi ba abinda aka fasa dan gane da azabtar dasu, danko Uwani Uwar bayi kullin sai Sarki Baidulƙais yasa an mata bulala ashirin sau biyar a rana, kullin saita ɗauki bulala ɗari kamar jakka tun ana bugun ta tana gaza wani bima har zawo take saki kuma a saka ta kwashe shi da hannun ta tanaji tana gani ta zama kaskantattar baiwa marar ƴanci a cikin bayin Masarautar Raifasu idanko ta dawo ɗakin da aka ajeta wata tsohuwar ƴar duniyar baiwace ta hana Uwani sakat ko kuka hana ta take, wani lokacin ma, haka zata zauna Uwani ta murza san ranta tanaji tana gani bata iya cewa uffan dan tsoro tagama karɓar ukuba gun Sarkin horon da Sarki Baidulƙais ya naɗa sannan inta koma makwancin katuwa ta kiɓa wani bima da Uwani take fillo in dare yayi ta hanata bacci saidai tayi ɓarawo batare da tasani ba haka rayuwa tai tayima Uwani juyin kwaɗo daya faɗa ruwan cikin zafi.....


*Daman haka duniya take in zakayi ramin mugunta gina shi gajere gudun wata rana kaine a ciki! wannan ya tunaman makircin Galadima Hamza da yanda ta kasan ce dasu a cikin Izzah Ko Mulki masoyan Izzah Ko Mulki recall this😁lol anayi munajin nice🤣......Muje zuwa my fans yaudai tsokana nikeji 😂*


Shiko Sarki Baidulƙais har ya gama zama da Jaruman shi yasa sunfara haɗa gan gamin yaki ba kama hannun yaro yanzun sakon Sarki Danwar yake sauraro yasan shi kadai zai iya taimaka mashi tunda Sarki Lahazu sun samu saɓanin ra'ayi da shi, yasan haushin shi yake ji dan ya hana ɗanshi Yarima Haishir, auren Baiwar shi Bahijja.



Danko Sarkin Yaƙi ba inda sukaci burki sai wajen bishiyar dasu Huzaifa suka yada zango, zama suma sukayi dan hutawa kasancewar inuwar nada sanyi sosai shiyasa matafiya ke yada zango kafin suci gaba da tafiya, suna cikin magana Sarkin Yaƙi yaga takardar ƙasa da alama yaga ta akayi sawa yayi aka tattaro ta aka haɗata sannan suka karanta duk da bakomai suka gane ba saidai sunga ansa hadin guiwa dan yaƙar Sarauniya Zulaiƙa a watan gobe hakan ba karamin ɗaga masu Lurwan hankali yaiba, sake duba takardar Sarkin Yaƙi yayi yaga ansa zuwa ga Masarautar Ƙaisu, tashi yayi yace.
"Inasa ran Yarima Malik yana Masarautar Ƙaisu dan ɗauko Bahijja tunda kunga bata Masarautar Raifasu dan hka kungama alamun sahun dawakan su nan ku tashi bayan su, amman mubi kudu ita zata sa damu da Masarautar Ƙaisu daga nan sai mucimma Yarima Malik ko ya kuka gani."
kowa ya gamsu da maganar Sarkin Yaƙi haka suka kama hanyar zuwa Masarautar Ƙaisu sun san kilan su dace a wannan karon.....

```Nikam da nace iska na wahalar da mai kayan kara ko za'a hade tsakanin su Yarima Malik da Sarkin Yaƙi?```

A wajen Bahijja kuwa tana wajen gimbiya Ƙamariyya tanai mata aiki, shara da gyaran daki sai sanwa da take zuwa madafa anayi da ita saidai kullin fatan ta samu hanyar da zata bar Masarautar Waisu takeyi saidai Yarima Haishir ya saka mata ido ko motsi tayi akan idan shi takeyin shi.

*Masarautar Daborah*

Koda Ashir ya isa fa'da dukawa yayi yakai gaisuwa wajen Sarauniya Zulaiƙa, Sarkin Zagi ne yace an gaisheka amintaccen bawa duk da ba a fiye yarda daku ba amman kai din ba laifi, Ashir mike tafe da kai Sarauniya Zulaiƙa ta amsa."


Dukar da kai yayi ya rasa ta ina zai fara ga shi zuciyar shi tafara halbawa da sauri da sauri yasan muddin ya faɗi shine yaje Masarautar Raifasu ya tabbata Sarauniya Zulaiƙa tana iya sawa a kashe shi sai dai baida wani zaɓi daya wuce ya faɗi gaskia koda kuwa zai rasa ranshi, yasan kin faɗar zai kwashi hakkin a'lumma da yawa, gashi ya baro su Tasi'u a Raifasu suna karɓar a zaba da ukuba, duk a sanadiyar zuwan shi, nan kum ya jefa iyayen Bahijja cikin tashin hankali.....bai ida tunanin da yake ba yaji Sarkin Zagi ya sake daka mashi tsawa yace. "Kai bawa idan baka da abin cewa zaka iya tafiya wajen Sarauniya Zulaiƙa ba wajen wasan yaro bane jaruman ma sai wanda ya shirya!"


Dakewa Ashir yayi ya kalli Sarauniya Zulaiƙa yaga sai kaɗa kafa takeyi ko kallon shi batayi ga fuskanta ba alamun wasa ko sassauci a tattare da ita, sake sadda kanshi yayi yace. "Tuba nike aimin aikin gafara Allah yataimaki Sarauniya, tabbas ba wanda yaje ɗauko Bahijja a Masarautar Raifasu face ni, nine naje da kaina ɗauko ta.!"
duk wanda ke cikin fa'da sai da ya tsorata da jin kalaman Ashir, cikin damuwa Sarkin Zagi yace. "Kai Ashiru ka duba da kyau karka bari tausayin bawa Abdulmajid yasa kasa kanka cikin damuwada bala'i, ka tabbata kasan abinda kake faɗa? nan fa fa'da ce kuma a gaban Sarauniya Zulaiƙa kake.?"

Murmushi mai ciwo Ashir yayi yace.
"tabbas ni Ashir nine naje da kaina Masarautar Raifasu dan ganin in Bahijja....... bai karasa sauran maganar shi ba yaji an sharara mashi mari har saida bakin shi ya fashe da jini take ya faɗi kasa ɗago kanshi yayi a firgice ya aza idanun shi akan wanda ya mareshi duk tsoro ya gama cika mashi zuciya cikin tashin hankali jikin shi na kyarma yace.....




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 11&12



*Dedicated this Page to Mom Sultan kiyi yanda kike so dashi Allah yabar kauna❣️*



"Sarauniya Zulaiƙa ce ranta duk yagama ɓaci jin abinda Ashir ke cewa cikin fushi tace.

"Banyi zaton haka daga gareka ba, banyi tsammanin dakai za'aci amana taba, kaine kabada gudun muwa wajen saka ɗana ya tafi neman baiwa, gantalalla marar ƴanci to kasani yau sai kaga ne kuran ka saika ɗanɗani kudar ka tunda bakada tunani! Sarkin gida kiramani Sarkin horo yanzun nan.!"

"Angama ranki shidade Allah ya baki nasara."
da sauri Sarkin gida ya tafi aiken da Sarauniya Zulaiƙa tai mashi, bai jimaba suka shigo atare da Sarkin horo, baki ɗayan su suka zube ƙasa suka kai gaisuwa wajen Sarauniya Zulaiƙa.

Mikewa tayi tana zagaye su, sai dukan hannun ta takeyi takasa ko zama tsabar bacin rai da bakin ciki, da wat irin kakkau sar murya tace.
"Minene hukuncin bawan da yaci amanar Masarautar su."? Muryar shi na rawa yace. "Kisa shine yadace dashi ranki shidade." Murmushi tayi cikeda zalinci tace. "Kaje kaita dukansa har saiya wulakan ta ya gama shan ukubar duniya daga baya saika halaka shi kaga koba komai zai tafi ƙiyama cikin bakin ciki da tarin nadama a cikin zuciyar shi, wannan shine saka makom bayi azzalumai mararsa imani kuma maciya amana.!"

Angama ranki shidade haka Sarkin horo, ya tisa keyar Ashir suka fita, zuwa wajen bada horo, shiko Ashir sai kwalla yakeyi yana neman ɗauki wajen Allah, ita ko ajikin ta antsikari ƙaƙƙausa, har sun kusa fita fa'da ta kira Sarkin horo da gudu ya karaso, ya duka ta sake cewa ka kai shi cikin turakar bayi ka wulakanta shi na tsawon satin ɗaya sannan ka kai shi cikin gidan kaso na tsawon wata ɗaya kana gana mashi azaba, daga karshe a soke zuciyar ja'iri da mashi sannan kaimashi gunduwa gunduwa a gaban iyayen shi, kaga ko ahaka ya tafi tabbas zai tafi da bakin ciki a cikin zuciyar shi tareda tarin nadama daga baya bakin cikine zaiyi ajalin iyayen shi natsani bayi ban kaunar su ban tausayin su, kuma ba ragi ko raguwa a tsakanina dasu saboda mayaudara ne kuma maciya amana ne yau gashi anwayi gari ɗana mafi soyuwa a cikin zuciyata ya tafi ɗauko baiwa wulakantatta marar ƴanci yana magaji na ya tabbata dole Abdulmajid da Binta sai sun ɗandani kudar su inama su aka kama da wannan laifin, kash duk da haka sai naga karshen duk wani azzalumai kuma maciya amana a cikin bayin Daborah, wuce dashi kasa Sarkin bulala na gidan yarin Fatur da sauran mahukunta suita dukan shi shida Abdulmajid inasan kafin nan da faɗuwar rana a nakasa shi.!"
waziri ne ya girgiza kai yana mai mamakin yanda kiyayyar bayi ke ɗawainiya da Sarauniya Zulaiƙa zuwa yanzun ya tabbatar da kara nun kuwa a cikin zuciyar ta, Sarkin horo ne yace. "Angama ranki shidade tun a fa'da ya fara halba Ashir yana dukan shi yana cin zarafin shi har suka isa cikin turakar bayi yafara hukunta Ashir.......



Akwana atashi a sarar mai rai, tafiya tai masu Malik nisan gaske dan suna sa rai gobe da marece zasu isa cikin Masarautar Waisu haka sukaci gaba da tafiya cikin dajin Allah....


Itako Bahijja tun da gari ya waye take aiki har marece data gama wannan ake kara mata wani tana cikin aiki kiran Yarima Haishir ya sameta a gajiye ta mike ta tafi lambu inda yake shaka tawa tana zuwa ta iske shi sai cika yake yana batsewa ganin yanda bayi ke ta ɗawainiya da uban gidan nasu abin ne ya bata mamaki aranta ko cewa tayi Allah ya tsareni inma wannan wawan Yariman wannan wahalar na tsaneka ashe kaima azzalumi ne kuma mayaudari, wasu kwalla masu dumi sukayi nasarar wankema ta fuska.
Batayi aune ba jita ana gogemata fuskar da hankicif da sauri ta buge hannun shi duk bayin dake wajen nan saida suka tsorata.
Kallan daYarima Haishir yai masu yasa kowa barin wajen, gaban Bahijja ne ya shiga dukan goma goma tasan ba mutucin ya cika ba Allah yasa kada yai yunkurin taɓata bata gama addu'ar zuci ba taji ya cafkota ta faɗo jikin shi yana kokarin yaga mata sutura kwarara ihu tayi taga ba wanda ya damu daya kawo mata taimako da karfi ta ingije Yarima Haishir amman kamar wani dutse take ban kewa, saka kuka tayi mai tsuma zuciya tana kiran Umma ki taimaka mani ganin yafara sunsinar wuyanta yana san cafke libs dinta, ta bugar mashi gefen kunne da karfi bai san sadda ya saketa ba. zata gudu ya taɗeta ta faɗi cikin fushi ya mike ya fara dukan ta yana cewa.
Wacece ke, kina baiwa ƴar bayi ki nemi wulakanta ni." itako duk ta ruɗe batasan tafara maida mashi bakaken maganganu ba.
"Ni bakowa bace face baiwar Allah ni ba baiwar kaba ce, kuma kasani insha Allah bazaka taɓa narasa akaina ba, kasani akan mutucina saidai ka kasheni, kuma naji ni baiwace ƴar bayi kabari ɗan bayi irina ya nemi ƴar uwar sa baiwa! kai ɗan Sarki jikan Sarki magajin Sarki kaje kanemi ƴar Sarki jikar Sarki irinka badai Bahijja ba wlh nafi karfin ka, Yarima kazalince ni kaci amanata wlh na tsaneka.!"
baki ɗaya ran Yarima Haishir ya gama ɓaci tunda yake yarinya nawa ya lalata har dadi sukeji idan ya haɗa jiki dasu sai wannan banzar baiwar zata gaya mashi ban zayen maganganu koda

Please Login or Register in order to submit comment