Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwalla takeyi ta rasa na menene, hakama wajen Bahijja kukan tafara, shiko MalikusSaif sujuda yayi yana addu'a da murna, da murmushi Abu-Jalal yabi jikan nashi mai shela ne yace.

"Jama'a ku shaida an ɗaura auren Abdulmalik Saifulislam Sulaiman Sufyan da amaryar sa Bahijja Abdulmajid Abdullahi Jafar bisa sadaki foam dari biyu tareda sarkar murjani,lakadan ba ajalan ba Allah yabada zaman lafiya da zuriya ɗayyiba."

Da ameen kowa ya amsa daga nan aka fara raba goro farare kal da alewa sai kuma dabino, baki ɗayan suka ɗunguma dan zuwa yin walima a cikin wani katafaren hall dake cikin filin Barri ba bayin ba ba masu mulki ba, ba yan kasuwa ba, ba talakawa ba, kowa ya halarci wajen sai wani makimancin waje nanne Sarki Abu-Jalal ya ware wasu jama'ar su da su Sarki Muhammad da mutanen Kangiwa haka akaje ba abinda ke yawo sai naman kaji da abinci iri iri kowa yaci yasha yai hani'an, hakama wajen su Sarki Abu-Jalal kowa yaci yasha Masha Allah, suma su MalikusSaif ba abar abokan shi abaya ba saidai shi yakasa cin komai dan ɗauki da zumuɗi gashi ya kagara yaga Bahijjar shi, da kyal yasha ruwa, ana gamawa mai shela yace, anjima bayan sallar la'asar za'ayi wasan Barri kamar yanda al'adar su take wasu dayawa sunzo ne dan kallan wasan, saboda ba kowane biki bane akeyin shi ba sai bikin Yarima mai jiran gadon mulki ananne akace za'a naɗa Sarautar MalikusSaif kowa saijin dadi yakeyi.

*dan ko masoyan Bahijja Malik can na hango su,sunata kwasar shoki dan faɗar farin cikin da masoyan su sukayi bata lokaci ne.*

Wajen Sarki Muhammad kuwa na Raifasu mamaki ya ishe shi ganin jama'ar da aka tara ba kaɗan ba ga komai anyishi cikin tsari na addini karo na farko daya halacci auren musulmai ashe haka akeyin shi lallai addinin musulunci yayi arayuwa maganar Sarki Abu-Jalal ne ya katse mashi tunanin shi atare suka tafi sashen Saifulislam da sauran jama'ar su kafin marece yayi ayi wasan Barri da naɗin Sarauta ga Yarima Malik.

Itako Bahijja tana cikin dangin ta ma'ana bayi anata murna har nafila saida Jakadiya Aisha tasata tayi da aka ɗaura mata aure, tasha kayan da Sarauniya Zulaiƙa tabata lallai haɗin saiya dace da jikin amaryar dan kuwa ankone sukayi ita da Yarima Malik, sun dace da junan su, tana jikin inna Mairo zaune anata shagali ke kyace ba baiwa ake aurar wa ba, komai yaji zam zam, dan dama Sarki Muhammad ya basu kudi zuwan shi jiya har cikin turakar bayi ya gana da Abdulmajid kowa sai shagali akeyi, sallamar da Bahijja tajine yasa ta da sauri da ɗago kanta, ganin su Zainab ne da Aisha sai Jakadiya Hajara tareda baba Saude baki ɗaya takasa rufe bakin ta dan murnar ganin kawayen ta wa'anda sukayi aikin bauta atare, sai murna sukeyi suma sun sha kyau ba laifi kamar ba bayi ba, itako Saude ta kafe Bahijja da idanun ta saboda lokacin da tana baiwa a Masarautar Raifasu, bata gani sosai ba wani sanin kwarai taimata ba saidai duk lokacin da zasu haɗu takanji ta kamar 'yar cikin ta, aiko hawaye suka fara ambaliya a fuskar Saude ko ba'a faɗa mata ba tasan Bahijja jinin tace ga kamar yar uwar ta nan tana gani, itako Mairo ko magana takasa sai kallan Saude takeyi, Bahijja ce tace .
"wai Zainab ina Baba Saude." cikin zolaya tace. "tana Masarauta mana."

Murmushi Bahijja tayi tace. "Karya ba kyau Ummi tacemin tare kuka zo tana ina."

Indo ce tace. "Gatanan gaban ki."
Tana ɗago kai kuwa ta sakar mata murmushi tana rungume ta tace.
"Baba Saude nayi kewarki."
Sai a lokacin ne Mairo ta samu ta mike tana rungume yayar tata tana hawaye, idanu su Zainab ke binsu itako Bahijja kallan inna Mairo takeyi ganin ta rungume baba Saude tana kuka, tasan dai koda tabasu labarin ta basu santa ba, bata gama mamaki ba saida taga Umman ta tafito daga ɗaki wajen Abban ta, taji ta saki wani tire dake hannun ta, da gudu tayi kan Saude ta rungume ta, tana kuka mai tsuma zuciya, kallan kallo akema juna tsakanin Jakadiya Aisha da Bahijja kowa yana mamaki, muryar Abdulmajid ce ta katse masu hanzari da sukaji yana cewa. "Wanike gani kamar Saude."
Sai a lokacin suka saki juna tana share kwalla tace. "Nice Abdulmajid."

Dukawa yayi shima kwallan na shatata yace. "Allah mungode maka wannan lamari kai kaɗai kasan dalilin haɗa fuskokin mu dake Saude na ɗauka kin rasu."

Cikin kankanin lokaci dangin su labari ya bazu Saude ta dawo aiko haka akaita zuwa nan suka zauna ta kwashe labarin ta tas ta basu taci gaba da cewa. "Lokacin da akabiyomu mun dawo rakiyar fatauci ga mutanen Saifulislam, kowa ya bazama dan tsira da ranshi, lokacin ne aka kamamu nida Yahayya, ba inda muka tsinci kanmu sai kasuwar bayi anan aka siyar damu zuwa Masarautar Raifasu, saidai wahalar dana sha ce tasa na rasa ganina harna wani lokaci mai tsawo, koda Bahijja tazo Masarautar mu aikin bauta duk da ba ganin ta nike ba nakanji ta kamar jinin jikina, har Allah yasa tabarmu ta dawo asalin ta tabbas munsaba kuma akantane muka dawo bisa turbar addinin mu da ake mana ta tsiya sai mun daina shi wanibi muyi wani bima mu aje, kunji takaitaccen labarina."

Sharce kwallan idanun su sukayi inda Abdulmajid ke cewa. "Allah kaɗai yasan dalilin zuwan Bahijja Masarautar Raifasu tazama haske komai ya gyaru Allah mungode maka muna kewarki Saude yaka mata ki zauna cikin dangin ki."

Rausayar dakai tayi tace. "Idan uban gidana ya yarje mani nima zanso hakan."
Jakadiya Aisha ce tace. "Ikon Allah insha Allah zai aminta Saude."
Allah yasa duk suka amsa.
Saude ce tace. "Ya Abdulmajid ina Ba'ba da Baffa."

"Ayyah sunjima da rasuwa wajen shekaru ashirin kun ɓata da shekaru biyar suka rasu."
Iyayen sune da Saude da Binta da Mairo su ukku ne a wajen iyayen su uwar su daya uban su ɗaya, shi kuma Abdulmajid shida Idris da Ladidi duk uwa ɗaya uba daya suke saidai dukkan su yan uwane daga tsatson Jafar suke auren zumunta ne akai masu.
Kwalla ta goge tace. "Allah yaimasu rahama."

Da ameen suka amsa, riko hannun Bahijja tayi tanajin so da kaunar ta.
Sallamar Hajia Kubra ce ta katse masu firar su, cikin girmamawa aka tareta nan ta gayama Abdulmajid cewar za'aki Bahijja wajen iyayen Malik, bai musaba yace Allah yatsare, sake feshe ta da turaruka tayi sannan ya riko hannun da Saude suka tafi rakiya sai Jakadiya Hajara, bayine suka rufama Bahijja baya wa'anda zasuyi mata hidima saman kayataccen dokine na alfarma aka sa ta hau a hankali aka tafi da ita sashen Kangiwa.

Suna tsayawa da sauri wani dogari yazo ya rikema Bahijja sirdi a hankali ta sauka bisa dokin Jakadiya ta rike hannun ta har cikin katafaren falon Saifulislam rike da hannun Bahijja itako ta sadda kanta cikin alkabba da taimata rufa baka ganin fuskarta sosai, jitayi Jakadiya ta zaunar da ita bisa wani lallausan kafat saidai a hankali takeji gabanta naɗan faduwa kaɗan kaɗan, shiko Abu-Jalal baki yaki rufuwa dan ganin anshigo da ƴar tashi, wani farin ciki yakeji yau na musamman, basu jima da zama ba saiga Yarima Malik dasu Huzaifa cikin shiga ta alfarma suma zama sukayi fuskar fal da annuri, itako Bahijja tanajin kanshin turaren daya daki hancin ta tasan Yariman tane yazo bata ida sakankancewa da hakan ba saida taji yace "barka da rana Abi."

Amsawa yayi cikin girmamawa.
Jakadiya Hajara ce tace. "Ranka shidade ga amaryar Abdulmalik tazo kusa mata albarka."
Shiko MalikusSaif ta wutsiyar ido yake kallan Bahijjar yanda take sakin asirtaccen kamshi ga wani so da kaunar ta duk sun dabaibaye shi, duk da baiga fuskar taba tana rufe da albarka.

Shiko Sarki Abu-Jalal murmushi ya saki yana kallan Kangiwa yace. "Alhmdullhi Saifulislam yau kaga ƴar muko? Abdulmalik ne da yin aure Allah yaimaki albarka ƴata, Allah yasa ki zama alkhairi a cikin wannan zuriyar tamu Bahijja." da ameen suka amsa kowa yanajin daɗi, Kangiwa ne yace "gaskia kam Kawu ai Bahijja yarinyar kirkice insha Allah kowa zaiji daɗin zama da ita."

"Allah yasa ya bada zaman lafiya." cewar Matawalle.
"Gaskia kam ni kaina zaman da tayi a wajena nasan ta da hakuri ga mutunta na gaba da ita."
Cewar Sarki Muhammad wato (Baidulƙais).
Hakanan Bahijja taji zuciyar ta ta karye danko a mafarki bata mance mai wannan muryar ba.
Cikin sigar zolaya Sarki Muhammad yace. "A bude ma iyaye muga ƴar tamu ko."

Jakadiya Aisha ce ta saka hannu a hankali ta ɗage hular alqabbar fuskar Bahijja ce ta bayyana, a tare kowa yace. "Masha Allah tubarakallah, musamman Sarki Abu-Jalal, danko Sarki Muhammad faɗuwar gaba yaji Allah yasani ya kaunaci Bahijja duk da a jahilce ya sota amman yasan tana da mahimmanci a rauwar shi baki ɗaya, saidai kuma yanzun kaunar ta juye jin ta yake kamar yar cikin shi.

MalikusSaif kuwa ko kaftawa baiyi akan Bahijja tun yana kallan ta a boye har yakasa boyewa cewa yayi.
Aranshi Allah na godemaka da kaimani baiwar auren Bahijja, kasa ta zama alkhairi ga rayuwa ta.

Sarki Abu-Jalal ne yace. "Masha Allah sannu ko ƴata Allah yaimaki albarka."
A hankali ta buɗe labban ta masu kyau da sheki tace. "Ameen ." ba kowa zaiji tace ba.

Sake kallan Jakadiya yayi ya miko mata wasu kuɗi yace "ga wannan Hajara na gaisuwar iyayene taje ta huta kinji."
Haka kowa yaita bada kuɗi, inda Sarki Muhammad ya bada sarkar azurfa ta tambarin Masarautar Raifasu yace. "Ga wannan takice ƴata sarkace mai matukar anfani a rayuwar Masarautar Raifasu na sadaukar maki da ita, don ke alkhairi ce arayuwar mu Allah yaima aurenki albarka Bahijja."
Sai a lokacin ta kalli fuskar Baidulƙais tabbas ta gasgata cewa shine saidai yanakara manyan ta kuma ya kara zama kamili, a hankali tace. "Nagode Abba."
Sunan da rakirashi dashi baisan hawaye sun ziraro mashi ba, yan nasihohi akai masu kamar yanda suka saba akan aure daga bisani akace amaida Bahijja gida, wajen tashi ne sukayi ido cikin ido da sahibin nata, murmushin so da kauna ya sakar mata itama ta maida martani suna cikeda da so da shauƙin junan su,wannan kenan.

Koda aka maida Bahijja, a turakar bayi suka wuce da ita, anan Jakadiya Hajara ta kawo mata kayan bukata, wanka ta shiga ta sake shiryawa wannan karan cikin wani matsiyacin material ne tasaka milk sai ratsin mint green, ba karamin karɓarta shigar tayi ba, Bayan sallar la'asar daga kowane ɓangare sai shiri akeyi domin kowa yasan ya halacci naɗin Sarautar da za'aima Yarima MalikusSaif da kuma kallan wasan Barri, cikin kankanin lokaci kowa ya gama shirin sa hakama a wajen Yarima Malik shirye yake cikin wasu dakakkun kaya na saki kirar pakistan lemon green sai ratsin kwalliyar orange color a jikin su kaɗan, hula shi ya murza itama ta Sarauta tasha ado da kwalliyar zaiba ruwan gold, sai takalman sa suma golden color ne sai baza kamshi yakeyi haɗuwa iya haɗuwa kam Yarima MalikusSaif ya haɗu gashi sai wani murmushi yake saki abin dai kam ba'a magana.

A wajen Bahijja kuwa har turakar bayi Sarauniya Zulaiƙa ta aika mata mai gyaran jiki taci gaba da aikin ta kamar yanda ta saba, itama sanye take cikin wani dakeken lace lemon green da ratsin fari a jikin shi, sai alkabba itama, lemon green da ratsin orange da takalman ta masu cover suma lemon green, tsayawa faɗin haduwar da Bahijja tayi ba karamin kyau tayi ba, haka aka dinga fesheta da turaruka masu sanyin kamshi, ana gama shiryata wasu bayi ne na musamman daga cikin hadiman Sarauniya Zulaiƙa sai Jakadiya Hajara sukazo ɗaukar Bahijja, haka suka tafi da Mairo sai Jakadiya Aisha saman wani kayataccen doki fari sol na alfarma ba'inda aka wuce da ita sai sashen Sarauniya Zulaiƙa cikin kayataccen falon ta na alfarma, a gaban Sarauniya aka ajeta, itama ta gaji da haɗuwa ga gwala gwalai a jikin Sarauniya ba abin nema bane, kallan ƴar tata ta dingayi cikin shauƙi da kauna, cikin kulawa tace. "Yata inafatan kinci abinci.?"
Dan rausayar dakan ta tayi sannan tace. "Eh naci."
Badan ta yarda ba tace. "Hajara ki kaita ɗakina ba kowa a ciki abata abinci taci inta gama za'aje filin Barri." da toh Jakadiya ta amsa, sannan suka tafi.

Haka aka kawoma Bahijja abinci mai rai da lafiya, sai wani kula a cikin shi farfeson yan shilane na tantabaru sun dafu sosai, sai turirin kamshi sukeyi, duk da ba wata yunwa bace ta addabi Bahijja sosai ba, amman taji sun burgeta, zuba mata Jakadiya Hajara tayi ta aje mata tace. "Yawwa 'yata kici, kinga wannan haɗin yanada matukar anfani a cikin wannan Masarautar, kici sosai kinji, gyaɗa kai Bahijja tayi, sannan a hankali tafara ci, hakan yasa suka bata wuri, saida taci sosai, bakaɗan naman yan shilar nan ba sukai mata dadi ba, daukar dafaffiyar madarar da aka zuba mata a kofi tayi tasha markaɗaɗɗiyar aya sai kuma nikakken dabino da kwakwa, cikin madarar sai kamshi takeyi, a hankali ta surɓa baki ɗaya jitayi daɗin madarar ya gauraye mata bakin ta, batasan tasha fin rabi ba, sannan tayi gyatsa, Alhmdullh tace, dan raban da taci abinci irin haka harta manta.

Jin sallamar Jakadiya, tayi tareda hadiman Sarauniya, haka suka kimtsa kayan da taci abinci, sannan aka kara gyara mata kwalliyar ta, kamota Mairo tayi suka fito, lokacin Sarauniya Zulaiƙa sungama shiryawa ita da yan uwanta da abokan ta sai matan abokan Saifulislam, duk sun gama kimtsawa kowa ya hadu iya haduwa saman dawakai na alfarma suka hau sauran hadiman su na binsu a kafa, haka suka ɗunguma sai katan filin Barri, lokacin kuwa su Yarima Malik sun isa bada jimawa sai yabawa akeyi da irin kyau da angon yayi tareda abokan sa, baifi minti biyar ba afara wasan Barri ba, su Bahijja suka iso wannan karan hannun Bahijja na cikin na Sarauniya Zulaiƙa, tinda suka tinkaro filin Sarkin zagi yafara koɗa ta, yana cewa barka da zuwa gimbiya Bahijja, ƴa ga Sarauniya Zulaiƙa angaishe ki, gimbiyar Daborah jinin Abdulmajid ƴar lelen Binta, barka da zuwa filin Barri amaryar Yarima MalikusSaif gaba lafiya baya alkhairi takawarki lfy bango majinjinar marayu buhun sikari mai dadin ɗandano zamanki lafiya gimbiya Bahijja."

Wani ƴar yar haka takejin tsikar jikin ta na tashi a hankali duk taji idanuwan mutane sun mata yawa, ga wani kirari da takeji, ta cikin alqabba ta hango Ya Malik ɗinta yana ta kallanta sai murmushi yakeyi a zuciyar ta kuwa cewa tayi "lallai Ya Malik da anganka ansan kafi kowa murna itama murmushin ta saki, ji tayi Sarauniya Zulaiƙa tace.
"Yata karki buɗe fuskar ki, sai in ankiraki kinji ko?"
Gyada kai tayi tace."toh Ummu."

Gefen haggun ta ta kalla ta cikin alqabba ta hango wani waje ya hadu iya gwargwado Umman tane ciki sai Abban ta da sauran yan uwanta ba laifi shaƙi kantane irin su Mairo Ladidi da Saude, sai Baffa Idris dinta da sauran yan uwanta su Tasiu da sauran bayin su na Raifasu.

A wajen su Abu-Jalal kuwa zaune suke da sauran Sarakai da sukazo murnar naɗin Sarautar da za'aima Yarima MalikusSaif sai sun Kangiwa, Matawalle da jama'ar su da sauran masu ruwa da tsaki na Masarautar Daborah da Runo shiru ya kewaye wajen, mai gabatar da wasan Barri wato Dawud shugaban mai kula gidan tarihin Barri ne ya fito yace.
"Batareda bata lokaci ba yanzun za'afara wasan Barri duba da lokaci na tafiya ga munada naɗin Sarauta, shiyasa zamu takaita wasan cikin Jaruman mu, muna bukatar mutun ukku a cikin ku duk da Yarima kunzama huɗu kenan."

Haka suka bada Yarima Yazid da Huzaifa sai Lurwan, duk suka fito suma sunsha kyau iya kyau, daga bayane Yarima Malik ya fito kamar jira makaɗa da mabusa suka fara busa suna koɗa Yarima suna cewa.

"Tashin ka lafiya Yariman Daborah angaishe ka, ɗa ga Sarauniya Zulaiƙa jinin Kangiwa Saifulislam Allah yakara girma da daukaka angon gimbiya Bahijja."

Duk kirarin da akema shi ba abinda yasa shi jin daɗi da yaji ance angon gimbiya Bahijja.

Da murmushi saman fuskar shi, ya tsaya gefen Huzaifa, yana wani kayataccen murmushi a ranshi ko cewa yayi. "Lallai kuwa su Huzaifa nasan anajin karfi kamar bijimin doki, wasan Barri, ni ko zan iya kuwa?"
Jiyayi wani bawa ya duƙa kasa cikin girmamawa yace.
"Ranka shidade ga takobin ka."
Murmushi yayi ya rike takobin sai walauniya takeyi yace. " *Sun'u* barka da zuwa wajen uban gidan ki." sunan takobin Yarima Malik kenan cikin kankanin lokaci aka buga kuge, kafin kaftawar ido Jaruman sun fara ba junan su wuta da takubban su ga kowa yanaji da karfi da Jarumta, Yarima Malik da Yazid sai kuma Lurwan da Huzaifa haka akaita artaba kowa yana nuna iyakar bajintar shi yakeyi.

Ba abinda kakeji sai karar wukake da Jaruman ke dukan takobban yan uwan su, a ka'idar wasan Barri wasane da idan anayin shi duk wanda ya bari ɗan uwan shi ya kaɓe mashi wuka ta faɗi ƙasa Shikenan anfidda mutun ko kuma wanda abokin karawar shi yakai shi kasa wanwar shima anci shi wasa, wannan dalilin yasa kowane Jarumi ya bada kaimi da nuna kwarewa a harkar Yaki dan kowa yanaji da karfin shi ga kuma dubarar Yaki, haka akai ta fafatawa saidai gogan naku hankalin shi nakan Bahijja dan ba kadan ta tafi da imanin shiba, ji yayi Yazid ya dage sai kawo mashi sara yake har tarwatsin wuta ke fita a jikin takubban lokaci na tafiya saboda a cikin minti shabiyar ake son a fidda gwani a cikin su, cikin gafin nama Yazid ya buga tsalle ya buge takobin hannun MalikusSaif da sauri ya dawo cikin hayyacin shi da idanu yabi takobin wanda rabi da kwatar wajen duk an mike ana sallallami ita kanta Bahijja ji take kirjin ta na duka da sauri da sauri fatan ta gwarzon ta yaci wasan, shiko Malik jikin shi ba karamin sanyin yaiba ganin takobin shi tay kololuwa sannan ta taho zuwa kasa, danko Kangiwa dafe kai kwai yayi Sarki Abu-Jalal kuwa ko motsi yakasa yi, waigowa yai cikin zama da kwarewa da bajinta ya buga wani irin tsalle iya karfin shi sadda takobin zata dira kasa, Yarima MalikusSaif ya cafkota a hannun shi ya rike gam, sannan ya doro kasa har saida kura ta tashi wajen, sannan zuciyar shi na bugawa da saurin gaske, wani uban ihu da aka saki ya dawo dashi cikin nutsuwar shi, ita kanta Bahijja wani sanyayyen numfashi ta saki, shiko Lurwan jin ihun ne ya janye mashi hankali dan shima ba kadan ya jigata Huzaifa ba, duk yanda yaso ya wullar da takobin hannun Lurwan yakasa, ganin hankalin shi bai tareda shine yasa Huzaifa yai tsalle ya wullar da takobin hannun Lurwan, wani irin shakku da mamaki ya dira cikin zuciyar Lurwan yaso ya caɓe takobin shi saidai ta riga da tausaka ƙasa ta cake da kasa, wani irin murna magoya bayan Huzaifa sukayi ganin yayi wining Lurwan Jarumi kuma haziƙi mai takama da Jarumta a cikin Jaruman Daborah.

A wajen Yazid da Yarima Malik kuwa fafatawa akeyi wani sabon karfi Yarima keji, suna cikin fafatawa cikin azama Yazid ya kawo wata sara aiko MalikusSaif ya zille, ya wurwura takobin shi ya sake caɓeta cikeda dubarar Yaki dan yaga Yazid da gaske yake kuma inbai wasa ba shike da nasara, cikin azama yasa kafadar shi ya bangaji Yazid da karfin gaske aiko Yazid ya tafi tangal tangal, yanasan ya rike kasa da kafufun shi ganin haka yasa Yarima Malik ya buge takobin Yazid sannan ya kara kwashe shi da kafar shi take ya faɗi kasa wanwar yana faɗuwa takobin shi itama tana isowa kasa wani razanannan ihu aka saki Yarima Malik yaci gasa, yanzun shida Huzaifa za'a fafata, kowa yaji dadi dan raban da ayi irin wannan cin har anmanta tun zamanin Sarki Khamil da Sarauniya Maimoon ace an kada abokin karawa sannan an wullar da takobi a lokaci ɗaya, hannun MalikusSaif yasa ya dago Yazid suka rungume junan su, baki dayan su suko koma wajen zaman su, aka fara basu kulawa da dafaffiyar madara kowa yasha, daga bisa shugaban gidan tarihin Barri yace.
"Anasan ganin Yarima MalikusSaif da abokin wasan shi Yarima Huzaifa."

Cikin kankanin lokaci suka fito waje kowa yana yabawa Jaruman dan kowa gwanine kuma yasan kanshi, ji sukayi yace.
"Cikin minti goma akeson cikin ku a fidda gwani."

Sake kwashewa da ihu akayi wasu na bayan Huzaifa wasu kuma na bayan ango Yarima Malik.
Ana buga kuge suka game suka fara fafatawa cicin karfin su, haka akaita artaba tsakanin Yarima Malik da Huzaifa kowa jinin shi kan hakaifa yake musamman gimbiya Zahara'u dake bayan ɗan uwan ta dan tunda aka ɗaura auren Yarima Malik takarajin tsanar Bahijja aranta harda Yarima Malik din acewar ta ya cimata mutunci ya zabi baiwa kan ta, a wajen su Huzaifa kuwa ana cikin fafatawa Huzaifa yasa kafa ya taɗe Yarima saura kiris yakai kasa dan kusan mutanen wajen duk an mike tsaye harda Sarauniya Zulaiƙa can hannun MalikusSaif ya dira kasa ya dafe kasa da karfi baikai kasa ba, hakan yasa Huzaifa cikin gafin nama yazo zaisa kafa ya ingiza Yarima shiko ya rike kafar Huzaifa ya kwashe shi sai ga Huzaifa ƙasa wanwar takobin MalikusSaif wato Sun'u itace ya cake gefen fuskar Huzaifa, ihun daɗi kowa yasaki aka shigo cikin fili Jaruman suka daga Yarima Malik sama anata jin daɗi shima Huzaifa mikewa yayi ya daga hannun yarima Malik anata murna kowa ya koma ya zauna.

Shiru ne ya biyo baya Sarauniya Zulaiƙa ce ta mike tsaye, hakan yasa aka nutsu fuskar ta cikeda annuri da farin ciki wanda takasa boye hakan a zahiri magana tafara.
"Alhmdullhi anyi wasan Barri cikin aminci Jarumai kowa yayi bajin tar shi kuma kowa ya gamsu da yanda aka gabatar da wannan wasa dan haka batareda baɓata lokaci yanzun za'a gabatar da kyautuka kamar yanda aka saba, wata kyauta ta dauko aka fara daga Lurwan ta sowa yayi yana ta murmushi, wajen Matawalle yaje suka gaisa sannan ya bashi kyauta, sai aka kira Yazid shi kuma Waiziri Dammur ne ya bashi tashi kyautar da kuɗi, sai Huzaifa shi kuma Saifulislam ne ya karrama shi saida ga karshe aka kira MalikusSaif wajen baki ɗaya aka ɗauki kabbara ana murna zuwa yayi ya tsaya gefen Sarauniya Zulaiƙa, wani irin kallon so da kauna tareda alfahari da ɗan nata take mashi mikawa Sarki Abu-Jalal kyautar tayi shima, mikewa yayi yana sakin kayataccen murmushi yayi cikin dattako yace. "Ina gimbiya Bahijja."

tana zaune taji gabanta ya yanke dan bata tsammaci kiran ba, a hankali ta ɗago kanta dake cikin alqabba ta kalli Jakadiya ta gefe, ji tayi ta rike mata hannu a hankali ta mike suka isa wajen Sarki Abu-Jalal, kanta sunkuye, Jakadiya Aisha ce ta buɗe fuskar Bahijja daketa ɗaukar ido amman still idanta na kallan kasa, wani irin suman tsaye Yarima yayi na ɗan lokaci yana kallan kyakyawar fuskar ta mai kara mashi kaimi da kwarin guiwa Sarki Abu-Jalal ne yace.

"Anshi wannan kyautar 'yata ba mijin ki."
Cikin girmamawa ta mika hannu biyu ta karɓa sannan ta ɗan saci kallan fuskar Yarima, da sauri ta jenye nata idon tana murmushi ganin yanda yake kallan ta, yana mata wani sanyayyen murmushi daya kashe mata jiki, a hankali take taku wanda batasan tanayin shiba harta iso gaban shi, wani irin abu yaji tsikar jikin shi ta wani tashi yar yar ga kanshin ta daya gama kashe mashi illahirin jikin shi, Sarauniya Zulaiƙa ce ta riko hannun shi, ita kuma ta bashi kyautar shi ta musamman, ɗago kanta tayi a tare suka sakarwa junan su smile mai kayatarwa.

Wajen ne ya karaɗe da gunjin ihu da murna na mutane dan yanda suka kayatar abin saidai ashe Masha Allah.

Sai kyauta ta karshe da aka ba Yarima wani ingarman dokine na alfarma daya kawatu da haɗuwa iya haduwa wannan karan kuwa Sarki Muhammad Raifasu shine ya gabatarwa Yarima da kyautar dokin, haka akaita farin ciki kowa yaci yasha aka tafi zuwa fa'dar Daborah domin yima Yarima Malik naɗi, kowa ya tinkari katuwar fadar su cikin wani fili inda nanne ake naɗin Sarakuna a cikin Daborah shiko Malik shi dasu Huzaifa sashen shi suka wuce dan bakaramin zafi yakeji ba, wanka yayi ya fito ya shafa mai, mai matukar kamshi, da turaruka masu daɗin gaske, wasu fararen kayane ya saka masu laushi da kayau sun bala'in karɓar jikin shi sosai, sai digon baki a jikin

Please Login or Register in order to submit comment