Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi mashi, Hajara saiki taya ta, ko.?"
Murmushi yayi sannan ya rausayar dakai alamun to."

Basu wani ɓata lokaci suka shiga kitchen dake cikin sashen Yarima Malik suka fara aiki, kad
ɗan kaɗan sai Bahijja ta saki murmushi ta rasa koname takeyi, duk abinda takeyi Jakadiya na ankare da yanayin ta

Shiko Matawalle tashi yayi yace. "Abdulmalik kaci abinci, bari inje indawo." sake rausayar dakai yayi alamun to.

Kallan Sarauniya Zulaiƙa Matawalle yayi yace."inasan ganin ki, a sashe na."

Mikewa tayi yana gaba tana maye mashi baya.
Suko su Bahijja sun gama sakwara ta gama mulmuleta sun saka a foodflask, sannan sunyi miyar agushi taji kayan kamshu da ganye, da naman kaza, sai kamshi takeyi, itama zubawa tayi a kula da flat sannan ta jere saman tire a tare suka fito ita da jakadiya har falon,ta aje bisa tattausan kafat dake malale gwanin ban shi'awa, shi dai Malik da idanu yake raka Bahijja saita zamar mashi kamar wata bakuwa, saidai ba kowa a falon duk sun fita Yazid ne ya rage shima tana zubama Yarima abinci yafara ci, yace bari yaje ya dawo, haka yafaracin abincin shi saidai ko kaftawa baiyi sai kallan Bahijja yakeyi itako duk ta takura sai take ganin shi kamar wani bako, yanda ya kira sunan ta saida tsikar jikinta ta mimmike ji take yafi kowa iya ambatan sunan nata muryar shi na rawa cikin sanyi yace.
"Bahijjaah."
A sanyaye ta ɗago kanta ta sauke shi saman kyakkyawar fuskar Yarima, cikin zazzakar muryar ta tace. "Naam."

"Miyasa kike gudu na.?"
Sadda kanta tayi kasa tace. "Ba gudun ka nikeba Ya Malik." "minene.?"
"am am daman bakomai." tana yan kame kame tayi maganar.
Rausayar dakan shi yayi yace. "Baki sona ko Bahijja?" sadda kanta tayi take taji wani irin kwarjini da haibar sa ta lullube a hankali ta rausayar dakai, saidai ta kasayin magana.

Shima baikara cewa komai saidai yakasa cire idon sa kanta, dan bakaramin daɗi da wani irin sanyi yakeji yana ratsa shiba a cikin zuciyar shi sai faman murmushi yakeyi.

Itama sai smile takeyi tana son ta kalleshi amman takasa, ta gefen ido ta saci kallan shi batasan yana ankare da itaba, idanun sune suka sarke dana juna take suka sakarwa junan su sanyayyen murmushi mai ma'anoni iri iri na masoya sai dai kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi, wannan kenan.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Runo kuwa Sarki Abu-Jalal ne tareda Lurwan yana gaya mashi duk abinda ke tafe dashi, cikin mamaki yace. "Wato ita Zulaiƙar ce ta hana Abdulmalik din auren baiwar, bataji sakona ba kenan.?"

Shiru Lurwan yayi sai kuma yace. "Ranka shidade yanzun haka yana kwance bai lfy.?"
"Shikenan naji daɗi da kazo mani da wannan zancen Lurwan yau ba sai gobe ba, zamu koma dakai inganema idona abinda ke faruwa dan haka tashi ka shirya mutafi, haka kuwa a kayi, da Sarki Abu-Jalal da Yarima Dawud, sai Galadima da Sarkin dawakai sai dogarawan shi guda hudu haka suka kama hanyar tafiyaa Masarautar Daborah bisa dawakan su, na alfarma sunsha ado iya ado.

Koda Matawalle suka isa cikin sashen shi kallan Sarauniya Zulaiƙa yayi yace. "Zulaiƙa kinga maganin damuwar Abdulmalik ko? Yanzun mike gareki gameda wannan lamarin, gashi dai baiwa itace maganin damuwar ɗan naki, ke kuma kin tsinewa baiwa, taya zaki bullowa wannan lamarin?"
Jiki sanyaye,take taji wani uban zufa ya karyo mata tace.....


_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 101 &102


_Yan team Bahijja wannan page ɗin naku ne kuyi yanda kuke so dashi, dan naga ku kecin duniyar ku da tsinke_ 🥰



"Yaya nikaina narasa ta ina zanfara lamarin nan yana ɗaga mani hankali, gashi Allah ya jarabci Abdulmalik da son baiwa, wa'anda suka daɗe suna mana zagon kasa a cikin wannan Masarautar, kuma makiyan mune su,kasan wannan."

Kallan ke yarinya ce yai mata sannan yace. "Uhumm da kindaina riko da abubuwan Kaka da kakanni da kin huta Zulaiƙa, tunda har Abduljabbar Matawalle nabar riko da wannan aƙidar kema kya ajeta."

Wasu hawaye masu ɗumi suka fara bin kuncin Sarauniya Zulaiƙa, tace.
"Yaya ya zanyi ga mahaifin yarinyar nan taurin kaine da shi."

Shu'umin murmushi yayi yace. "Zulaiƙa kenan haka rayuwa take, karfa kiman ta Abdulmajid tsaran mahaifin kine, baccin yana bawan ki taya zaki dinga cimusu zarafi, wlh da ace ke mutunci ya dace ace tuni kin 'yanta Abdulmajid kodan shekarun daya kwasa yana ma iyayen mu hidima, amman kullin burinki kici zarafin sa dana iyalin sa tir da wannan hali irin naki."

Murya na breaking tana kuka tace.
"Haba Yaya ka daina faɗan haka Kangiwa ya juya mani baya kaima juyaman bayan zakayi kome?"

Cikin jin haushin ta yace. "Nimeke gareni nifa ɗan uwan kine shiko Saifulislam mijin kine kuma Abdulmalik ɗan shine kinga yafi kowa iko dashi, sannan yace, ɗan shi fatauci ya gada ba Sarauta ba, kema kinsan shike iko dashi kuma da uba ake gado ba uwa ba, dan haka kije kisamu mijinki ya sauko, kilan saboda darajar shi da bayin nan ke gani su aminta su ba Malik auren Bahijja."


Ajiyar zuciya ta sauke tareda fesar da numfashi mai zafi tace.
"Yaya suna bayina har saina nemi alfarma wajen su?"

"Uhmmm ba sai kinje ba Zulaiƙa zaki iya aurar da Bahijja, tunda kece uban
ta ."

Fahimtar ran Matawalle yafara ɓaci yasa tace. "Dan Allah Yaya ka naima mani alfarmar su mana.?"

mamakin kalar son zuciyar ta yakeyi, tamke fuska yayi yace.

"Da tuni nayi hakan,dan haka ta inda aka hau tanan ake sauka ai bayin ki bane, kece zaki nema ko kuma kibasu umurni duk yanda kikayi sai dai kisani rasa Bahijja a wajen Malik tamkar datsewar rayuwar shi ne, ma'ana farin cikin shi, sannan kuma Kangiwa shine jigon wannan tafiyar kije ki hankalta."

"Yaya kataimaka mani dan Allah, hakan yana nufin inemi afuwar bayina.?"

"Uhmmm kanwata kenan, durkusawa wada ba gajiyawa bane, amman infa babu girman kai, abune mai sauki."

"Kinga zaki iya tafiya nidai amatsayina na ɗan uwanki shawara nike baki, kamar yanda Baffa Abu-Jalal ya umurceki duk da kinsaɓa umurnin shi."

Shigewa yayi bedroom ɗinshi, itako zama tayi saman kayatattun kujerun falon shi yana jiyo sautin kukan ta har cikin zuciyar shi, sai dai yasan dole wannan ranar tana zuwa gareta ranar dana sani marar anfani kenan."

Wajen Kangiwa kuwa yana zaune falon shi, tareda wasu baki, yasa aka basu wasu buhunna da alama taimako sukazo amsa, godiya sukayi sannan suka tafi, suna fita bada jimawa ba saiga Sarauniya Zulaiƙa tayi sallama, hakanan yaji ranshi ya ɓaci dan ko muryar ta bai san ji a halin yanzun, dayake shi mutunne mai ilimi sai bai kore ta ba, kuma bai barmata falon ba, zama tayi kasa gefen kafafun shi, tafara hawaye ta rike kafar shi cikin muryar kuka mai tsuma zuciya tace.

"Kangiwa dan Allah karufaman asiri ka ceci rayuwar ɗana ka nemani alfarma wajen Abdulmajid ya aurarma Abdulmalik Bahijja karka juyamin baya dan Allah Abu Malik."

Rufe idanun shi yayi sannan ya bude yace. "Baiwar? ko kinman ta baiwa ce ita? yanzun Sarauniya kamar Zulaiƙa ce ke kuka da idanun kan Baiwa? Gaskia bazan iya zubda girmana ba, inje wajen bayina ince su aurarma ɗana kamar Malik Baiwa marar yanci yar gadon bauta kamar Bahijja, ina ai Malik yafi karfin Bahijja, dan haka kije da kanki badai da Kangiwa ba."

Mikewa yayi zaibar falon tasake cakumar kafar shi ta rike gam, hawaye na ambaliya a saman fuskar tace.
"Rayuwar Malik tafiye mani duk abinda na mallaka, banji zan juri ganin ɗana cikin mugun yanayi ka ceceni kaine mahaifin sa, kuma dole saida uba ake neman aure."

Murmushi yayi mai faɗi yana mata wani irin ƙasƙantaccen kallo sannan yace.

"Uhmmm ko Ummu Malik? karda ki manta uwa ma zata iya bare irin ki mai gadara da mulki, kinga bakin alqalami yariga ya bushe ni Saifulislam inada kunya bazan iya kallan kwayar idnun iyayen Bahijja ba, in masu wannan zancen ba, kije kisamu ɗan uwanki Matawalle, ai shima zai iya nemawa Abdulmalik aure ko ina raye ko bani raye, kinga nagama magana Zulaiƙa."

Fisge kafar shi yayi ya shige ɗaki yana sa kuba, binshi tayi tafara buga kofar yaƙi budewa, shiko wani irin daɗi ne yaji da yaga Zulaiƙa tafara saduda, daman irin wannan ranar ya dinga jiye mata, aranshi ko cewa yayi bataga komai ba."

Itako haka ta fita ta koma sashen ta, tana ta yan sake sake a cikin zuciyar ta."

Bayan sallar magarib tasa Jakadiya Hajara ta kira mata Abdulmajid da Binta su sameta a sashen Matawalle, itama can ta tafi koda ya ganta, kallan tuhuma yai mata, amman takasa magana da kyal tace.
"Yaya dan Allah nasa akiramani iyayen Bahijja katayi neman alfarma."

Murmushi yayi baice komai ba yana mamakin halin Zulaiƙa, ita dai bazata iya neman alfarmar suba kenan saita saka wani ? Amman yasan maganin lamarin ta, da ido ya bita, itako taki yarda su haɗa idon sai wasa take da zobunan gold dake sarkafe a cikin yatsun hannun ta, sallamar su sukaji, baki ɗayan su suka amsa, zama sukayi bisa kafat, sannan Jakadiya ta juya zata tafi, Matawalle ne yace itama ta zauna, yayi hakan ne dan takaima Saifulislam rahoto saboda Jakadiyar shi ce, kuma ta amana, itama zaman tayi bayan sun gaisa Matawalle ne yacema Abdulmajid yahau bisa kushion ya zauna amman yace aaa saman kafat ɗinma ya wadatar dashi, bai kuma ta kurashi ba, shiru ne ya gauraye falon ba wanda yai magana, Abdulmajid ne yace.

"Ranki shidade gamu Allah dai yasa lfy?"
Kallan Matawalle tayi amman yai kamar bai ga tana kallan shi ba, gyaran murya tayi tace.
"Eh daman akan maganar da mukayi daku ne kwana ki shiyasa na nemeku inji ta bakin ku."

Gyara zaman shi Abdulmajid yai yace.
"Wace magana ce wannan?"
Ba karamin mamaki bane ya kama Sarauniya Zulaiƙa ba ganin rainin hankalin da Abdulmajid zai mata,amman sai ta daure tace.

"Maganar nemawa Abdulmalik auren Bahijja ko."
Shu'umin murmushi yayi yace.
"Hakane sai dai kamar tun ranar na gama gaya maki ra'ayina gaskia kibaiwa Abdulmalik hakuri nidai banji zan iya bada auren 'yata ga wanda ba tsaran ta, a matsayin ta na baiwa."

Wani irin faɗuwar gaba taji ya mamaye ta cewa tayi.

"Uhmm Abdulmajid kenan karfa kaman ta, nima din tun ranar nace maka ba shawara nike baka ba umurni ne."


Wani kallo Matawalle ya watsa mata na kinyi kuskure.
sanan yace.
"Abdulmajid tabbas ansan ancutar daku sai dai cikar mutumin kirki shine wanda akeyima sharri amman ya sakan ta da alkhairi, kayi tunani ka zama mai yawan yafiya a cikin kowane al'amarin ka."

Cewar Matawalle, shiko Abdulmajid yaji ɗan sanyi a ranshi domin tunda aka fara wannan maganar sai yanzun yaji zance mai daɗi a cikin zuciyar shi kallan Matawalle yayi zaiyi magana kenan sai Sarauniya Zulaiƙa ta anshe zancen da cewa.

"Aaa Yaya kadaina neman bama mutanen nan hakuri, domin kuwa duniya ra shaida tsakanin Abdulmalik da Bahijja akwai banbanci."

Ido kawai Matawalle ya zubama Sarauniya Zulaiƙa, shiko Abdulmajid ɗan murmushin takaici yayi a cikin zuciyar shi kuwa cewa yayi. A haka zan bada auren yata inda ba'asan darajar taba, dan kawai infarantama wasu? Kai bazan iya ba.

Azihiri kuwa game hannun shi yayi a sigar ban hakuri ya rusuna kaɗan yace.
" ranka shidade mai girma Matawalle kodan kai Abdulmajid zai iya bada auren yar sa, sai dai a halin yanzun bazan iyaba saboda wasu dalilai amman dan Allah kada ka matsa sai kaji uzurina sannan ka yafe mani ka karɓi uzurina."

Cikeda gamsuwa Matawalle ya rausayar dakai yace. "na fahimce ka Abdulmajid, kasani mu matsayin uba muke kallan ka, amman zan maka uzuri shima Abdulmalik Allah yabashi wadda tafita ya bashi ikon ɗaukar kaddarar shi."

Sauran suka amsa da Ameen dan ba kaɗan Abdulmajid yaji dadi ba yanda Matawalle ya karɓi uzurin shi, itako Sarauniya Zulaiƙa mikewa tayi cikin fushi tace.

"Haba Yaya mi hakan ke nufi ka goyi bayan su kenan?dole zuwa gobe ai baikon MalikusSaif da wannan Baiwar har wani matsayi ne dasu da za'ai masu uzuri."
kallan su Binta Matawalle yayi yace. "Kuyi hakuri zaku iya tafiya."

Tashi sukayi suka tafi, shiko Matawalle kallan Zulaiƙa yace.
"Ashe ba kisan kima ba? waike me kika maida dokokin addini;ne? koda kika mada Abdulmajid banza yafi karfin haka domin kaf duniya ba wanda ya isa ya aurar da Bahijja sai shi."

"Yaya..."yimin shiru wlh ko in kasa kasa dake kuma daga yau karki kara sakani cikin sashencin banzan ki, ni nasan darajar kaina."

Fita yayi yabar sashen baki ɗaya haka itama sashen ta ta wuce, itako Jakadiya Hajara zuwa tayi ta labartama Saifulislam komai, murmushi yayi cikeda takaici yace.
"Kinga mahaukaciya, ai Abdulmajid dai dai yake da duk wani zamanin ta, naji dadin wannan labari Hajara." godiya taima Saifulislam sannan ta shiga kitchen dan yin aikin ta.


Washe gari da safe, tunda gari ya waye ciwon MalikusSaid sai a hankali dan dai bai amai saidai yana fama da matsanancin ciwon kai, jiyake tamkar zai bar jikin shi, maganin da Saifulislam ya bashi ne yasha, sannan ya kwanta, koda Sarauniya Zulaiƙa tazo ta duba shi da jiki yanda taga ko magana bai iyayi shine hankalin ya dunguza fita tayi ta shiga sashen Saifulislam akayi sa'a daga shi sai ita, da sallama ta shiga ya amsa mata,samun wuri tayi ta zauna cikin gadara tace.

"Saifulislam ya maganar baikon ɗanka da za'ayi gobe, ina fatan kun gama maganar da Abdulmajid?"

Kallan ɗage yai mata yace. "Ni ɗan aiken kine?"

Jin maganar tayi banbara kwai, cikin dakewa tace. "Amman ai ɗanka ne."

"Uhmm ko? kice kisan cewa ɗa uban sa yake gado? Hmmm inko har hakane kice Abdulmalik *Fatauci* ya gada ba *Sarauta* ba, sannan koda ya auri baiwa zai ɗauke ta su tafi Fatauci, ba abinda ya haɗa magajin Zulaiƙa sarkin gobe da haɗa zuriya da baiwa, dan haka zan nemawa ɗana auren Bahijja dakai na, sai dai kisani bashi ba Sarauta, saboda ya haɗa jinin da baiwa.!"

Da sauri ta huyo kirjin ta na halbawa da sauri da sauri tasa hannun ta ta danne kirjin ta, tace. "Sai dai ba Sarki Abdulhamid bane ta haifeni ba koda bamu haɗa jini da Baiwa ba ai kaddara ce ta jawo hakan kuma duk duniya banda magajin da zai gaji sai Abdulmalik."
Murmushi yayi mai sauti yace.
"Muzuba mugani,Malik uban shi zai gada dan haka Fatauci shine gadon gidan su Kangiwa ba mulki ba, kuma ba ruwan ɗan kasuwa da kyamar bayi, su kuwa yan Sarauta bakusan daraja da mutucin bawa ba, saboda haka kije kinemi magajin da zai gajeki niko ɗana, zai gajeni dan kasuwa ya iya."

Kuka ta fashe dashi tace. "Wlh Kangiwa baka isa ka tona mani asiri ba, Malik mulki zaiyi da yardar Allah, kuma auren Bahijja a kaddara zaizo mashi dan tsira da raywar shi zan amince ya aure ta."

Murmushi yayi yace
" hakane matar Kangiwa, kinyi kyan kai Ummu Malik, kihuta lfy."

ruwa ya kurɓa sannan ya mike har zai fita saiga Matawalle ya shigo tare suka shiga bedroom din Kangiwa.

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

A wajen Sarki Abu-Jalal
kuwa cikin ikon Allah tafiya tai tafiya har sun fara shigowa nahiyar Daborah, gadan gadan suka kama hanyar da zai sada su da Masarautar Daborah

da yamma likus saifulislam ne yasa aka kirama shi Abdulmajid saboda zuwan da Matawalle yayi da rana sun tattauna al'amura masu matukar mahimmanci, wannan dalilin yasa aka kirama shi Abdulmajid, koda yazo, bisa kujera ya nuna mashi alamun ya zauna, haka kuwa akayi zama yayi kanshi kasa dan Allah yasani yana jin nauyi da kunyar Saifulislam sosai, cikin girma da mutuntuwa suka gaisa, numfasawa Kangiwa yayi sannan yace.

"Bansan ta inda zanfara ba, Abdulmajid sai dai ranar bikin dole sai dole, ina neman alfarma awajen ka."

Cikin jin nauyi yace. "Ranka shidade indai kaine zaka nemi alfarma a wajena, bazan so hakan ba, sai dai kace mani umurni zaka bani Allah yataimaki Khadimulislam."

Cikin jin dadi yace.
"Karfa kaman ta, Abdulmajid agirme ka girme taya zan iya baka umurni, kabar shi a alfarmar."
Sanyayyen murmushi yayi yace. "Yanda kace haka za'ayi."

"Naji dadin hakan daga gareka, ina neman alfarmar nemawa ɗana Abdulmalik izinin neman auren 'yarka Bahijja."
Sunkuyar da kanshi yayi kasa, sai dai take yaji tausayin Bahijja ya kama shi dan yasan halin Sarauniya zata iya wulakanta ta amman kuma Kangiwa yafi karfin wannan alfarmar a wajen shi, cewa yayi. " da Abdulmajid da Bahijja duk ikonka ne ranka shidade."

Yaji dadin zancen Abdulmajid sai dai a zahiri cewa yayi.
"Kasan dalilin dayasa na ce neman izinin auren ta? saboda kasa ai bincika maka halayen M Abdulmalik, kada kabada auren yarka ba akan shari'a ba, idan kasamu Abdulmalik da wani halin ya zama dole ya hakura da Bahijja."

Yana mamakin hali irin na Saifulislam gaskia mutumin kirkine tabbas Bahijja tayi dacen uba, dan yafi karfin suriki, cewa yayi.

"Haba ranka shidade a iya sanin mu tun da aka haifi Abdulmalik har zuwa yanzun bamu taɓa samun shi da wani mummunan hali ba, dan haka na amince kuma kaine zaka zama waliyin Bahijja."
"Murmushi yayi ya rasa ta inda zai fara godema Abdulmajid a rayuwar shi, cewa yayi. "Allah yasaka maka d aalkhairi, amman inada wasu sharuɗɗa in ba damuwa."

Rausayar da kanshi yayi sannan yace. "Eh ina jinka ranka shidade."
numfasawa Saifulislam yayi sannan yace.
"Inasan ka katsaya akan bakarka na bazaka ba Abdulmalik auren Bahijja ba, a gaban mahaifiyar shi har saitayi dana sani, kuma ta nemi afuwar ku, tasan cewa bayi suna da daraja kamar kowa kuma *BAYIMA 'YA'YANE* idan ta aminta da hakan sannan zaka bada auren Bahijja badan komai ba dan Zulaiƙa tasan darajar ta data iyayen ta, inafatan ka fahimci manufa ta.?"

Murmushin jin dadi Abdulmajid yayi dan daman abinda yakeso ya nuna Zulaiƙa kenan darajar Bahijja, amman shi ba abinda Abdulmalik ya taɓa yimasu naƙi, asalima shi abin so ne, dan yayi imani Bahijja bazata taɓa samun masoyi na gaskia ba kamar Abdulmalik, yasota tun batasan kanta ba, yake kyautata mata, ganin yanda Abdulmajid keta murmushi yasa Kangiwa yace. "Allah dai yasa sharaɗina ya karɓu.?"

Rausayar dakai yayi cikeda gamsuwa yace. "Kwarai kuwa kullin abinda nikeso inga nasamar wa 'yata yanci duk da kasancewar ta baiwa, ai nasan daga mahalicci ɗaya muke baki ɗayan mu, da talakan da mai arzikin, da masu mulkin damu kanmu bayin shiyasa nikeson in tunatar da uwargijiya ta cewa komai na Allah dan haka na amince da duk uzurin ka."

"Masha Allah tabbas son zuciya yasa Zulaiƙa ta gafala Allah yasa wannan karan ya zama sanadiyar shiriyar ta."

"Ameen."
Abdulmajid ya amsa yaji kwarin guiwa jin Kangiwa yana cikin zancen yasan ƴarsa bazata wulakan taba, maganar da Saifulislam yai mashi ce ta katse mashi tunanin shi, cewa yayi.
"Bissimillah ga abinci matso muci."
Girgiza kanshi yayi alamun Aaa, matsa mashi yayi amma ya ƙicin kayan abincin da aka jere mashi ganin Kangiwa ya nuna rashin jin dadin shi yasa ya sha ruwa, sannan ya ɗanci iccen tufa yace. "Alhmdullhi."

Murmushin jin dadi Saifulislam yayi yasan Abdulmalik yayi dace da uba na kwarai dattijon kirki mai tsoron Allah, ji sukayi ankira sallar magrib baki ɗayan su suka tashi kafaɗa da kafaɗa suka jera suka tafi masallaci danyin sallah.

A wajen MalikusSaif kuwa zaune yake saman sallaya, yana addu'a yau kam jikin nashi da sauki sosai, sai dai daya juya sai yaga Bahijja tana mashi murmushi, shima murmushin yakeyi, jiyayi yana kewarta kwana biyun da yayi bai kara ganin taba sai yaga tamkar ta shekara biyu ne, amman wani side na zuciyar shi, nasa shi nishaɗi inya tuna da tsadaddan murmushin ta.

Bayan sallar isha'i da misalin karfe 8:30pm dai dai wannan lokacin babban bako ko kuwa ince manya baki masu matukar mahimmanci da matsayi a cikin Masarautar Daborah suka iso, tunda ga Sarkin Kofa har Sarkin gida haka suka taro su, baki ɗayan su suka ɗunguma har cikin tafkeken side din Kangiwa, lokacin da suka shigo cikin side din Kangiwa suka iske Matawalle da aminin nashi Saifulislam suna zantawa domin fuskokin su cike suke da annuri, baki ɗayan suka mike jin sallamar Sarki Abu-Jalal data daki kunnuwan su, wani irin farin cikine ya lulluɓe su take, suka taho suna mashi maraba rungume Saifulislam yayi yace. "Sannu da zuwa Baffa ya hanya."
Shima rungume shi yayi tsam dan Allah yasani ba karamin so da kauna yakema Saifulislam ba, yace. "Yawwa Khadimulislam barka dai ya muka sameku?"

"Alhmdullhi Kawu."
Sakin shi yayi sannan suka rungume juna da Matawalle suka gaisa."

ɗunguma sukayi suka shiga can cikin katafaren falon Kangiwa wanda suke sauke baki masu daraja da mahimmanci, kowa ya zauna, cikin kankanin lokaci Jakadiya Hajara tafara gabatar masu da kayan abinci da nasha, sai dai Kangiwa yace sufara shiryawa sannan haka kuwa akayi, wani tamfa tsetsen ɗaki ne daya ƙawatu da kayan alatu na musamman aka buɗewa Sarki Abu-Jalal kamar wani masaukin shine antana de shi domin shi,duk da ba shigar shi akeyi ba, amman yasha gyara na musamman, koda ya shiga haka yai wanka ya sauya kaya mararsa nauyi, sannan yai sallah, hakama wajen su Yarima Dawud kowa ya gama kimtsawa, snnan suka dawo falon, abinci Jakadiya tafara zuba musu suka faraci sai dai Abu-Jalal, madara mai dumi yafara sha, sannan ya kalli Kangiwa yace. "Ina ɗana yake?"

Matawalle ne yace.
"Baffa kabari ka huta tukunna."
"Uhmm Abduljabbar kenan, ai wannan zuwan dan shi kadai nazo kaga dole inba abinda yakawo ni mahimmanci."

Kallan juna sukayi da Kangiwa sannan sukace. "Hakane Baffa."
Sake kurɓar madarar yayi wanda su Dawud da Galadima suke kwasar abincin su da gaskia dan sunji yunwa, cewa yayi. "Ya jikin nashi da sauki ko?"
Mamaki fal a fuskokin su, shima ya fahimci damuwar su, basarwa yayi yace. "Uhmm kubar mamaki Abdulmalik na musamman ne agreni, ya jikin nashi.?"
da sauki sukace, bai kuma magana ba, kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi.

A wajen Sarauniya Zulaiƙa kuwa tana kwance bisa lumbu tsetsan gadonta ta tashi zaune jin kiran da Jakadiyar Saifulislam kemata, fitowa tayi falo, ganin yanda Hajara keta murna yasa Sarauniya Zulaiƙa saurin tambayar ta ba'asi cikin ɗauki tace. "Ranki shidadshidade yau Masarautar Daborah na ɗauke da manya manyan baki na musamman masu matukar mahimmanci."
cikeda zumuɗi tace. "Uhmm suwaye wadan nan Jakadiya.?"

"Ranki shidade Sarkin Musulmi ne wato Sarki Abu-Jalal da kafar shi yana sashen Kangiwa."

Ai tunda Zulaiƙa taji ance Sarkin Musulmi taji 'yan hanjin ta sungame gefe guda, maimakon tai farin ciki take damuwa ta dirar mata.
Ita kanta Jakadiya ta fahimci Sarauniya batai murna ba, ta rugo ta gaya mata ne dan ta samu kyautuka kamar yanda ta saba, indai Baffan ta yazo masu ziyara wanda yafara gaya mata takan bashi kyauta ta musamman.
kallon ta Jakadiya tayi cikin damuwa tace.
"ranki shidade lafiya na ganki kin shiga damuwa.?"
a hargitse tace.
"Na shiga ukkuna Hajara ya zanyi akwai matsala ki taimaka mani!"
cikeda mamaki Jakadiya tace.
"Ranki shidade wane kalar tai makone wannan?"
cikin kiɗimewa Sarauniya Zulaiƙa tace.....


😂😂😂 *har naga yanda ƴan bayima 'yayane suka kashe kunnen danjin abinda mosiyayar tasu zatace ƴan team Zulaiƙa gare ku* 🤣😂



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 103&104




"Baffa yazo? Hajara maza ki kiramani Abdulmajid kiyi sauri ku iso yanzun nan dan Allah ki taimaka mani kaku daɗe!."
ta ida maganar zuciyar ta na halbawa dan ta shiga tsananin fargaba da tsoro.
da sauri Hajara ta fita tana sassafar ta nufi turakar bayi zata shiga cikin turakar bayi kenan ta haɗu da Abdulmajid zai fito, baya ya koma cikin girmamawa yace. "Ranki shidade barka da dare?"

Yawwa Abdulmajid cewar Jakadiya, wucewa yayi tace.
"Abdulmajid."

tsayawa yayi yajuyo baice komai ba, a nuste tace. "Sarauniya na neman ka."
Wani irin abu yaji harya gaji da wannan wulakancin ita bata iya samun shi sai shi, a haka daman ake neman aure iyayen yarinya su zasu dinga bin iyayen yaro? rashin galihu yasa yabita ba tareda yace komai ba, har suka isa cikin katafaren falon nata itako taje ta dawo ta kasa zama Allah yasani tana shakkar Baffan nasu a rayuwar ta, jin sallamar su yasa tayo kan Abdulmajid

Please Login or Register in order to submit comment