Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shekara inda fa'da ta cika da mutane kama dasu Dagaci, Ciroma, Majidadi, Sarkin Taska, Sarkin Rumbu, Galadima, Matawalle, Kangiwa, Sarkin fa'da, Ɗan iya Ɗan buren, da dai sauran jama'ar fa'da, shiru ne ya karade wajen kowa yana jiran yaji hukuncin da Sarki ya yanke akan rabon da akayi, gyara alqabbar shi ya ɗanyi nan Sarkin zagi yafara cewa.

"Gyara zaki gyara gimtsi Allah yakara lfy da nisan kwana."

Shiko Sarki MalikusSaif cewa.

"Alhmdullh anyi budget yanda yakama ta saidai a cikin wannan bojet din da akayi inasan Sarkin Rumbu, a dibi abinci kama dasu shinkafa alqama, gero, masara, dawa, wake, da sauran kayan masaruhi na yau da gobe a rarrabawa talakawa na, da sauran bayi kowa ne abashi isashshen abinci, gida gida bansan a nuna banbanci kuma ba lallai sai wanda ke zaune a cikin Masarautar nan ba, aaa duk jama'ata dake kalkashin ikon mulkin Masarautar Daborah."

Kara rusunar da kai Sarkin Rumbu yayi yace.
"Umurnin ka abin tunkaho agareni Allah yataimaki Sarki mai adalci."

Sake waigowa yayi ya kalli Sarkin Taska yace.

"Kai kuma Sarkin taska, duk inda aka raba abinci, za'aba kowa kudi a kalla foam ashirin."

Kallan juna Kangiwa da Matawalle sukayi suna hango girman kudin dayace a bada bayan kayan abincin, gaskia MalikusSaif mutun ne mao tausayi kuma bai tsoron talauci, maganar shice ta sake katsemasu tunanin da sukeyi cewa yayi.

Ina Majidadi?"
"Allah yakara lfy gani nan biyayya ga umurnin ka dole ne."

Jinjina kai ya danyi yace.

"Idan umurnin bai saɓama dokokin ubangiji ba Majidadi, sannan wannan tafiyar tana kalkashin kulawar ka, ka tabbatar ko ina an raba, anbada akai, kuma sauran kananan Masarautun mu a aika da kayan abincin ga kowane hakimi ya tabbatar sakon ya isa ga al'ummar annabi."

"Insha Allah wannan hakkin yana wuyana zamu kiyaye."

"Masha Allah, saidai nasan daga cikin ku wasu zasuce ai wannan dokar bata a cikin wannan Masarautar, daga yau inasan a rubuta wannan dokar a cikin tsare tsare wannan Masarauta, za'adinga rabawa bayi da sauran jama'ar mu kayan abinci da kudin cefane, fa'da taba Sarkin kasuwa iko adinga barin bayi suna cin kasuwar Zursu akalla sau ukku a sati, duk da babbancin da takeyi a karshen sati, sannan ina gargaɗar mai kula da abincin bayi a madafa, za'a dakatar da bawa bayi abinci kullun, kamar yanda aka saba.
Saboda yanzun anbasu abincin da zasu dinga sarrfawa, amman za'a dinga basu abinci sau biyu a sati, ranar Juma'a da ranar litinin, kuma inasan Majidadi ya tabbatar a cikin abincin a saka masu wadatattan nama, da kuma kifi."

Kowa na fa'dar nan saida yai mamaki gaskia komai na Masarautar Daborah ya sauya, ada bawa baida wannan gatan, abincin da ake basu ko dadin kirki baida shi, ga wulakancin yau daban na gobe daban.

Inda wasu kecewa dan ya auri baiwa shiyasa ya canza tsarin, inda wasu ke ganin daman can MalikusSaif mutun ne mai tausayi da sanyin zuciya, cikin masu wannan tunanin kuwa harda Matawalle da Kangiwa, shiko Abdulmajid mataimakin limamin fa'da ne a halin yanzun, zaune yake amman kwalla na zirara a bisa kunci shi, ganin yanda bayi suka samu yanci suka samu shugaba adali mai son talakawa da bayi, ashe daman da gaske ne akwai ranar da bayi zasu zama cikakkun 'yaya kamar kowa? lallai inkam harba mafarki yake ba, a zahiri ne hakan ke faruwa lallai ya tabbata, cewa Bayima 'Ya'yane.


Jin Sarki MalikusSaif yaci gaba da cewa.
"Ina mai kara tunawa yan uwa masu arziki da ku fidda zakka kada ku shafa'a domin ita zakka tana tsarkake dukiya, kuma tana kawo buɗi ta kowane fanni, sannan ita zakka ya kamata in zaka fidda ta kafara ba makusantan ka, idan suna da bukata, in kuma sun wadatu, kabawa makotan ka, idan ba bukatar hakan agaresu, to kabawa talakawa masu bukata, sannan ita zakka anfison a dinga badata a dunkule ga mabukata, kada kudinga rarraba ta kuna rowar fidda ta, idan kuka badata a dunkule tana iya yuyuwar wanda aka ba, Allah yasama wannan zakkar albarka shima zuwa shekara ya fidda yabawa wani, kunga ansamu albarkar ubangijin talikai, inafatan za'a daure a dinga fidda zakka yanda ya kamata, kuma kuje ga malamai sukara yi maku cikkaken bayani akan zakka, Allah yasa mudace."

Baki ɗayan su suka amsa da Ameen.

Sarkin aiken Daborah ne ya shigo ya zube ya kawo gaisuwa wajen Sarki, ɗan Zagi yace.

"Sarki ya amsa meke tafe dakai.?"
"Ranka shidade kayi bako daga Masarautar Raifasu."

Cikin kulawa Sarki MalikusSaif yace.
"Yimashi iso."

Mikewa yayi ya fita jim kadan suka dawo tare, suka duka, sake kai gaisuwa sukayi, aka ansa masu, sannan Sarkin aike ya tashi ya tafi, shi kuma Sarkin zagi ya kalli bakon yace.



_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 119&120



"Ɗan samari mike tafe dakai?"

"Daga Masarautar Raifasu sakone daga Sarki Muhammad yace inkawo ma Sarki MalikusSaif."
Mikoma MalikusSaif takardar yayi yasa hannu ya karɓa, budewa yayi yafara karantawa kamar haka.

_Assalamu-alaikum_

_Fatan alkhairi inafatan sakona ya sameku cikin aminci Allah yasa haka ameen._
_Ina mai shaid maku halin da muka fuskan na baraza daga Sarrilƙus zai yakemu cikin wannan makon, muna bukatar talafi daga Jaruman Masarautar ka, nagode daga Sarkin Raifasu zuwa ga Sarkin Daborah."_


Lunke takardar yayi yace.

"Gaskia kam ina da wannan tunanin a cikin zuciya ta, waigawa yayi gafen damar shi yace.

"Ranka shidade Kangiwa kaji abinda Sarki Muhammad yace, Sarrilƙus yasake dawo masu da albishir din yakasarsu cikin wannan makon, yanada kyau mu tashi tsaye da addu'oi sannan muyake shi baki daya a nade tarihin wannan mutumin."

Cikeda gamsuwa Saifulislam ya kalli ɗan nashi yace.

"Allah yataimaki Sarki mai adalci hakan ya kamata ayi, sai mu fidda lokaci domin tafiya Masarautar."

"Hakane da Matawalle da Huzaifa da Yazid sai Kangiwa ku hudun nan ku zaku hada Jarumai aba kowa ragamar Jaruman da zai wakilta, ni kuma a hadani da wasu Jaruman, waziri Dammur zaici gaba da rikon Daborah kafin Allah yasa mudawo sai ayi sabon nadin makuman fa'da da yawa wasu suna bukatar hutu a ciki kuwa harda Waziri, sai Ɗan maliki wanda wancan ya rasu, zaa nada sabo duk sai ayi bayan mundawo."

Kowa yaji dadi musamman waziri dan ba kadan yake bukatar hutu ba, shiyasa MalikusSaif ya aika da takaddu a Masarautun dake cikin arewa masu gabas na Gambia domin shaidin nadin sabbin makarrabai da zaiyi ga kuma matsalar Sarrilƙus ta bujiro masu shiyasa ya maida naɗi sai sun dawo Raifasu.

Kowa kuwa ya amince da maganar Sarki MalikusSaif, cikin kulawa yace.

"Aba bakon nashi masauki ya huta kafin ya tafi su kuma zasuyi tafiyar nan da kwana ukku, sawa yayi akai mashi kiran Sarkin Yaki ya shaida mashi a tara Jarumai afara abinda ya kamata, sannan ya sallami zaman kowa ya mike suna fadin albarkacin bakin su, su Kangiwa kuwa filin barri ya wuce aka tara Jaruman sula fara rabasu kowa da commendor dinsu, aka fara gwaji kamar ba gobe.

A Masarautar Raifasu kuwa koda sukaji dan aiken su shiru bai dawo ba ga kusan kullin da kalar siddabarun da Sarrilƙus ke zuwar masu dashi hakan yasa suka fara shirin Yaki na musamman wanda raban dasuyi gangami irin shi tunda sukayi Yakin ansar takobin Barri danko Sarki Muhammad da kanshi yake bada horo da sauran manyan Jaruman shi.

A wajen Sarki Haishir kuwa suma kam abin ba'acewa komai haka sukaita mugun nufi da kudiri akan Masarautar Raifasu danko Sarki Danwar Masarautar ya koma ya tare shida Jaruman shi sai zuga Sarki Haishir yakeyi, suna zaune a cikin lambun Waisu sunata tsara yanda zasu darkake jama'ar Sarki Muhammad, ba tareda sun damuba ko tuno alakar dake tsakanin su a can baya, kawai sukaga Aljani ɗantsitu ya bayyana da wani bakin takobi na bakin karfe sai walauniya takeyi, Sarki Danwar kuwa saura kadan ya gudu Sarki Haishir ne ya rikeshi ya kalli Aljani ɗantsitu yace.

"Barka da zuwa dagani akwai babban albishir da kazomani dashi."

Wani masifaffan dariya ya kece dashi yace.

"Yawwa halakakke tabbas kai na hannun haggun mune kaga wannan takobin da kake gani Sarkin Gamki yace inkawo maka shi da ita zaka sauke kan wannan maci amanar azzalumi makiyin mahaifin ka."

"Hhhahhhhahhh! tabbas yau Sarrilƙus ya wanke mani bakin cikin dake cikin zuciya ta, saura kadan zan sauke kan makiyina sara mafi muni."

"Kwarai kuwa nan da kwana ukku zamu maida Raifasu ta zama tarihi a cikin ƙasar Gambia."

Wani irin dariya suka saki baki ɗayan su daganan Aljani ɗantsitu ya ɓace.

"Kai Gaskia mutanen nan bala'i ne jibi yanda suke abubuwa wannan karon ba shakka Sarki Baidulƙais ya zama tarihi."

Wani shu'umin murmushi Sarki Haishir yayi na gefe n baki mai ma'anonk iri iri bai kuma cewa komai tashi yayi suka fita wajen Jaruman su sukaci gaba da bada gwaji.


Washe gari da safe Bahijja ce da baiwar ta Mansura a kitchen tana hadama sahibin nata kayan buɗa baki, jajjagen kayan miya Mansura tagama na tarigu da wadatattar albasa, wata tukunya ce ta silba kan wuta keta fidda daddan kamshi sai siraci ke fita a cikin ta, bude tukunyar tayi zabbine a ciki dankwala dankwala guda ukku sun dafu tagama tafasasu, saukewa tayi ta ta tsamesu cikin wani kwano, saida suka tsane sannan ta ɗaura kasko tasa mai da wadatattar albasa, bayan yayi zafi tafara soya naman zabbi.

"Mansura ita soyaman su, kiyimani jar suya kinji."

"Toh ranki shidade."

Wucewa tayi tafara Fara gyara mangwaron ta ta wanke shi fes sannan tayi slide dinshi ta hada mango juice ta zuba suger kadan da flavor, ta juge a jug ajeshi gefe tayi.

Wata karamar tukunya ce ta daura ta juye madara ta dafata ta saida ta dafu sannan ta aje ta gefe ta dauko mazarkwaila da zuba a wani ta juye madarar ta rufe.

Itako Mansura tanagama soya naman, Bahijja ta dauko tukunya ta zuba mai kadan da wadatattar albasa saida yai zafi ta zuba kayan miya ta dinga motsawa juye soyayan namanta tayi ta motsa sannan tasa spices da albasa mai lawashi ta juya suka hade jikin su, sannan ta rufe bayan minti biyar ra bude sai kamshi ke tashi ruwan kayan miyar ya shiga cikin naman, cikin wani foodflask ta juyeshi.

Itako Mansura tuwon jar dawa ne ta sauke sannan tafara ɗaureshi a leda tana sawa a foodflask.
"Kai Mansura kinga tuwon nan harnaji shi'awar shi, ashe zai kyau har haka."

"Ranki shidade mutane basu gane dadin tuwon dawa bane sai suce basucin tuwon dawa."

Dariya Bahijja tayi tana dan rike kugu alamun tagaji ga ɗan cikin ta daya fito ras gwanin shi'awa ya shiga wata na biyar kenan, cikin tausayawa Mansura ta aje mata kujera tace.
"Ki zauna ki huta kibari inkarasa."

"Hmmm Mansura kibari mu'ida tare."

Bayanda Mansura batayi ba amman Bahijja tace zata iya haka Bahijja ta kada miyar ɗanyar kubewa da kifi ta diɓa a foodflask, sannan ta samu wani kula tace.

"Mansura zuba tuwo guda shidda da wannan naman ki kaima Ummu."

"Toh ranki shidade."
"Yawwa wannan babban jug din kikaima Abbuh juice a ciki, wannan kuma da wancan kular da Matawalle ne ki kai, inkin dawo ki dibi naki."

"Shikenan angama Ya shugabata."murmushi kawai Bahijja tayi dan batasan sadda sauran bayin ta zasu daina bata wannan matsayin ba, harta daina yimasu fada zuwa yanzun.

Tana komawa bedroom dinta wanka tayi ta tana fitowa da alwalla jikinta ta saka doguwar riga pink and blue ta fesa turare ta kabbara sallar magrib, tana ida salla tafara tafara addu'a tafara tana shafawa ta mike ta ninke sallaya, jitayi an ringumeta, a hankali ta sauke ajiyar zuciya jin daddadan kamshin turaren Ya Malik, fuskar shi ya sakala a gefen wuyan ta yana shakar kamshin jikin ta, sannan ya zagaye cikin ta da hannun shi yana shafawa cikin so da tsantsar kaunar da yakema cikin nata, murya na rawa tace.

"Ya Malik sannu da dawowa, da gani ka kwashi gajiya da yawa."

"Uhmmm sosaima kuwa Kanwar Malik yunwa nikeji."

"Ayyah Ya malik muje kadan watsa ruwa sai kaci abinci."

Sarke tafin hannun su tayi dana juna kamar karamin yaro yake binta har bedroom dinshi tayashi rage kaya tayi dagashi sai singlet da boxes, janshi tayi takai shi bathroom ta hada mashi ruwan wanka, juyowa tayi zata fita ya sake rungumeta janyota yayi ya fara watsa mata ruwan wanka yana dariyar mugunta, dan ko baa fada mashi ba yasan batajima dayin wanka ba.

"Uhmmm Ayyah Ya Malik kabatamin wanka na fa."
Cinno baki tayi tana dire diren shagwaba, da saurin shi ya sake riketa yana ɗan zaro idanu waje yace.

"Haba Hayati na karki yimin asarar baby na mana na tuba, rama a jikina."
"Uhmm eh naji nima saina rama."

Zaiyi magana yaji ta dibo ruwa ta watsa mashi, cukune fuska yayi alamin mai fushi yace.

"Kai kai nike watsama ruwa lallai yau kuwa zan..."
Da sauri ya taro ta jikin shi ganin ta tafi zata fadi bakaramin tsorata yaiba jikin shi sai rawa yakeyi, itako runtse idanta tayi jinta fada jikin shi yasa ta bude idan nata ta saukesu a fuskar shi, da tsoro ya gama bayyana a cikin ta.
Murya a sarke yace.

"Nurol Hayat! kibi a sannu dan Allah zakijima baby ciwofa."

Kicinkicin da fuska tayi ta dan harare shi tace.
"Ayyah Ya Malik bama tani kake ba ko?"

Dafe kanshi yayi yace.
"Ayyah Kanwar Malik dake nake mana, haba Hayati na gimbiyata!"

Kwantar da kanta tayi bisa faffadan kirjin shi tanajin yanda yake bugu da sauri da sauri gaskia ita kanta tasan ya tsorata.

Jitayi yana zame kayan jikin ta a hankali, batai kokarin hana shiba, harya gama shima zare kayan nashi yayi, itako rufe idanun ta tayi, tanaji yanan shafa cikin ta yana yimashi wani sanyayyan kiss mai sanyi da dadi, yana fadin kalamai masu dadin sauraro, a hankali ta bude idanta ta kalleshi tana shafa lallausan gashin dake kwance a bisa kirjin shi, lumshe ido yayi ya hade bakin su suka fara romancing din junan su, daga bisani suka fara wanka yai mata itama taimashi dan tin bata saba wanka dashi ba harta saba, zuwa yanzun, kuma ta rage tsoron sa, suna gamawa suka nade a cikin zanin wankan su ɗaya, sannan suka shafa mai suka shirya a cikin dogayen riguna iri daya dan dai shi tashi akwai ratsin cofee, a tare suka koma falo zama yayi bisa kafat lokacin kuwa har bakwai d rabi, daman azumi yayi kuma dabino kawai yaci, zuba mashi mango juice tayi ta mika mashi ansa yayi yai bissimillah ya kurba, lumshe ido yayi yace.

"Hayatiiih!"
"Uhmm Habibihh!"

Sake lumshe idanun shi yayi yanajin dadin sunan da ta kirshi dashi yace.

"Mikika zuba a lemon dinnan yayi dadi sosai.'
Murmushi tayi tace.
"Daga kaine Habibinah."

Murmushi yayi yace.
"Uhmm tunda nina kawo maki shi ko hmmm zakin hannun kine Hayati."

Dariya tayi harsaida hakoranta suka bayyana, masu dan karan haske, ga dumple dinta sun lotsa tace.

"Habibih kaci abinci kar yunwa ta kama min kai."
Rausayar dakai yayi ta zuba mashi tuwo miyar kubewa ɗanya."

Wanke hannun shi yayi a wani koko, sannan ya saka a dibi tuwon a bakin ta ya kawo mata shi, taki karba tace.

"Ayyah Sarkina kaci mana."

"Aaa gimbiyata muci tare to."
Bude bakin tayi ya saka mata, itama ta bashi.

"Masha Allah Hayati yai dadi dame ake tuwon dawa?"

Yai maganar a sufar zolaya, itama a zolayr tace.

"Uhmm da alqama saina tuka da garin shinkafa."

Dariya sukayi baki dayan su, sukanacin abincin suna shan kaunar su, zuba mashi zabbin tayi shima yaci ba laifi sannan yasha madara alhmdullh yace.

"Ita daman tuni ta koshi kwashe kayan sukayi suka kai kitchen sannan suka dawo sukaci gaba da firar su, kwantawa tayi bisa cinyar shi, yana shafa cikin ta yanajin dadi.



Bayan kwana biyu kamar yanda Sarki MalikusSaif ya umurta angama shirin tafiya Masarautar Raifasu, shiga yai sashen Sarauniya Zulaiƙa sallama yaima mahaifiyar tashi, sallamar mahaifin sune ya katse masu maganar su.
yace. "Ina ƴartawa?"

"Nasa Hajara ta kirata nan zata dawo kafin kuje kudawo, inbata kulawa ta musamman."

"Hakan yayi kyau kuwa."
Sallamar da sukayi ne yasa suka maida hankalin su kan Bahijja duk idanin ta sunyi jajir alamun tasha kuka ta godema Allah shima kanshi MalikusSaif jiyake kamar yai kukan dan baison rabuwa da iyalin nashi, zama tayi Ummu ta janyota jikinta tana dan shafa bayan ta tace.

"Haba 'yata kidaina kukan nan, addu'a zamuyi Allah yakaisu lfy yasa ayi nasara kumanya dawo mana dasu cikin aminci."

"Ameen tace murya a sarke."

Shiko MalikusSaif kallan ta yayi yace.
"Gaskia kam kibar kuka kada kijazama kanki wani ciwon."

Rausayar dakan ta tayi, tace.
"Ya Malik Allah yabada sa'a yabaku nasara Abbuh."

"Ameen ya Allah."
Suka amsa cikin tsananin tausan ta, tashi sukayi jin anbuga kugen tafiya, a taresuka mike duna waving dinsu, suka fita, MalikusSaif ne ya wuce sashen Abdulmajid, yana shiga ya iske su zaune a falo suna shan fura Binta nashan madara, da sallama a bakin shi amsa mashi sukayi zaunawa yayi ya gaidasi cikin girmamawa.

Abdulmajid ne yace.

"Masha Allah nafito kenan munai maku fatan nasara Allah yabada nasara yai jagora."

"Ameen"
cewar Binta tace. "Toh ɗana Allah yayi albarka ya baku sa'a."

Ameen ya rabbil alameen, bai jimaba ya fita sai filin Barri ya iske kowa ya hau doki, Sarkin dawaki ne ya rike mashi sirdi shima ya hau sannan Sarkin kofa ya bude masu kofa suka tafi.

Bayan awanni hudu, Masarautar ba laifi kowa yana hada hada waziri ne yasa aka fara raban kayan da Sarki MalikusSaif ya bari, haka aka raba har turakar bayi kowa saida ya samu da kudade, hakama duk anba hakimai su rabama talakawan su kowa sai murna yake yana sanbarka da addu'a ga sugabanin su.


Washe gari da safe, Bahijja ce ta tashi dakyal dan tunda MalikusSaif ya tafi Masarautar Raifasu takejin jikin ta wani iri ba karfi ko kadan ga faduwar gaba dakeji, takasa samun natsuwa a cikin zuciyar ta, Mansura ce ta shigo cikin bedroom din da Bahijja take a cikin sashen Sarauniya Zulaiƙa, da sallama a bakin ta, dukawa tayi gefen gado wajen gimbiya Bahijja tace.

"Barka da safiya uwar ɗakina." "yawwa Mansura ya gajiya."

"Alhmdullh,daman Sarauniya ce tace intambayeki mi kike bukatar a girka maki?"

Shiru Bahijja tayi kamar mai nazari wasu kwalla taji sun zubo mata wanda ita kanta batasan dalilin zuwan suba, a hankali tace.

"Kunun gyada yaimin."
Shima din bawai dan tana bukatar shanshi ba, aaa dan dai Ya Malik yace ta dinga shan shi.

Cikin girmamawa Mansura tace.
"Angama Allah ya taimaki gimbiyar Daborah."

Mikewa tayi ta wuce bathroom ta hadama Bahijja ruwan wanka, sake dawowa tayi tace.

"Allah yataimaki uwar magajin gobe, angama hada ruwan wanka ranki shidade."

Itadai Bahijja idanu ta zubawa Mansura wai ita zatace ma uwar magajin gobe, ɗan dako zuwa duniya baiba, sukama sani ko macece, tunda yanzun mulkin Daborah ya koma na maza zallah, hmmm lallai Mansura ban fatan ɗana yai mulki a rayuwa ta.
A zahiri kuwa cewa tayi.
"Sannu Mansura."
Mikewa tayi saidai itama ta fahimci uwar dakin nata batayi wani murna ba dan tace mata hakan.

Tashi tayi ta shiga wankan ta.
Haka al'amura sukayi ta wanzuwa tsakanin gimbiya Bahijja d Sarauniya Zulaiƙa bakaramin shakuwa ceba ta shiga tsakanin suba, komai itake ma Bahijja itada jakadiya Hajara sai kuma Mansura, wani bi da kanta take rakata wajen Binta su gaisa da iyayen ta, ganin yanzun cikin nata yana kara girma kamar bana budurwa ba, wata bakwai amman kai kace ya shiga watan haihuwar shine.

A Masarautar Raifasu kuwa Jarumai ne sahu sahu iya ganin ka, duk angauraye su dana Daborah ana raba masu kayan Yaki, kowane team da leader dinsu, duk wanda kagani yana kasashi na yin Yakin dan zuwan su Sarki MalikusSaif a kalla yau kwanan su biyu, amman da sukaba ma Jaruman Raifasu gwaji sai suka ga da shirme sukeyi basu iya komai ba a fagen Yaki ba da dubarun Yaki, amman alhmdullh zuwa yanzun kam an samu gamsashen gwaji wajen su Sarki MalikusSaif dasu Huzaifa, lokacin salla ne ya tashe su suka wuce masallaci daga nan kowa ya tafi gida dancin abinci domin suna sa rai zuwa gobe ko jibi Sarrilƙus zai zo yakar su shida jama'ar shi.

Koda su MalikusSaif suka koma sashen Sarki Muhammad zama sukayi kowa yana fadin albarkacin bakin shi akan Yakin maigrma Kangiwa ne yace.

"Insha Allah sai mun wargaza Sarrilƙus a doron kasar nan, da girman ayar Allah zamu halaka shi."

"Da yardar Allah kuwa."
Cewar maigirma Matawalle.

MalikusSaif ne yace.
"Yawwa Ina alqami da warƙa abani inturama Sarrilƙus d sako."

Sarki Muhammad ne yace.


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 121&122




"Allah yataimaki Sarkin Daborah, mi zakace wannan mushirin kin?"

Murmushi Sarki MalikusSaif yayi yace.

"Uhmmm zan gargade shi da inyazo yakar karya kuskura ya ɓace ko ya turomana aljanu a boye su farmana, inya tashi ya fito a bayyane ya yake mu, sannan duk wahala dul runtsi bamu lamunce mashi ba ya bace."

Baki ɗayan suka jinjina kai suna mamakin yanda Allah yaima MalikusSaif dabaru da azancin Yaki su kansu basu yi wannan tinanin ba. Huzaifa ne ya mikoma MalikusSaif takarda da alqalami, rubuta wasikar yayi ya kalli Mansur da Lurwan yace.

"Kuje kukai wannan wasikar a dajin Gamki saidai kada ku shiga, idan kunje, ku ajeta gab da shiga cikin dajin ku juyo Allah yatsare hanya."

Ameen sukace, suka tafi dan cika umurnin Sarki MalikusSaif.

Suko su Sarki Muhammad mamaki sukeyi taya shi Sarrilƙus zaisan da sakon bayan ba'a shiga cikin dajin Gamki ba.
Yanda yaga sun kureshi da idanu yasan damuwar su cikin hikima yace.
"Kudaina mamaki, aishi yace matsafine ko, kunga kuwa duk abinda mukeyi ai zaigani kennan ta hanyar tsafin shi.

"Jingina kai sukayi alamun gamsuwa, sannan suka tafi cigaba daba Jaruman su gwajina musamman.

A dajin Gamki kuwa Sarrilƙus ne da Haishir a jikin wani ruwan madubi suna kallan yanda Sarki MalikusSaif yake bada horo da sauran manyan Jaruman shi na musamman kallan Haishir yayi yace.

"Uhmm kagani ko wato Baidulƙais saida yayi gayyar Jarumai daga cikin hazikan Jaruman Gambia ko?"

Dafe kanshi yayi cikin bakin ciki yace.
"Kubar munafukai ai mukeda nasara."

Kallan gamsuwa yaima Sarki Haishir yace.
"Jibi wasu can bakin dajin Gamki sun aje wani abu sun tafi komi suka aje."

Cikin mugunta yace.
"Ka halaka su mana."
Girgiza kanshi Sarrilƙus yayi yace.
"Aaa Haishir bazan cutar dasuba, ai su yan aikene"
Buga wata katuwar ganga yayi saiga wani aljani ya bayyana da takardar a gaban Sarrilƙus ya duka yace.
"Sarkin Gamki ga sako wasu suka ajeshi."

Ansa yayi yaba,Sarki Haishir yace.
"Karanta mana wannan wasikar."

Ansa yayi yafara karantawa.


```A'uzu billahi minasshadinirrajim,
Duk da nasan bakusan abinda take nufiba, saidai kusani bin wannan sharadin shine zaman lafiyar ku, muba kayan wanki bane da zamu tsaya jiran ku har haka, sannan kuma inajan kunnan ku, bamu lamunta ba ka dinga bacewa ba kaida jama'ar ka a fagen daga inkai kacika isasshe kuma Jarumi mai takama da tsafi, ka fito ka tunkaremu a zahiri, kuma duk wuya kada ka bace, da fatan kunne yaji
```

Wani irin bacin raine ya soki kahon zuciyar Sarrilƙus idanun shine suka rine kamar wutabyace.

"Mi wannan kalmar ta farko ke nufi,gaskia na gilgiza da naji amonta a cikin kunne na."

"Nima bantaɓa jintaba saiyau kuwa dana karanta ta, kilan wani yaran ne."

"Sam ba wani yare bane akwai dai abu mai girman gaske a cikin ta, saidai wannan dagani ba Baidulƙais bane ya rubutata ba, ammn bari muga yanzun zanga wanda yai wannan rubutun dayasa zuciya ta tsinkewa."

Wani kyalene ya dauko ya shafa wani kyale baki yayi jikin madubin tsafin shi saiga su MalikusSaif sun bayyana a lokacin da yake rubuta wasikar.


Murmushin mugunta yayi saidai ya gagara jin abinda suke cewa, kallan Haishir yayi da mamaki yagama addabar shi ganin girman tsafin Sarrilƙus yace.
"Aikuwa Sarki MalikusSaif ne yacika mai karfin hali."

"Uhmm kace kuwa zan

Please Login or Register in order to submit comment