Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take bai kalla ba, tabbas hakan ba kramin ɗagama Zulaiƙa hankali yai ba, tasan shirun Baffa Abu-Jalal bakaramin abu bane kwara yai magana, kowa hukunci ne yayi yafi mata da dai yaki yin magana, shiko yana shiga dakin Yarima Malik ya shigo ganin yanda ran Sarki Abu-Jalal yai masifar ɓaci cikin kulawa yace.....



_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 105&106



"Abi kayi hakuri abubuwa da dama sun faru, saidai yanzun ya riga da ya wuce anyi kuskure, kayi hakuri, tabbas indai Bahijja ce na hakura, kaga mahaifin ta shima yayi fushi akan abinda Ummu tai masu, kaga hakurin shine masalaha."

Kallan Yaro man kaza yaima Yarima Malik zama yayi saman wata ƙayatacciyar kujera sannan ya riko hannun MalikusSaif ya zaunar dashi gefen shi, ya ɗan shafi gefen fuskar shi yace. "Uhmmm bazaka hakura ba, kuma cikin kwanakin nan za'ayi komai a gama ɗana, Zulaiƙa tayi kaɗan ta kawo mani sakarci a cikin zuriya ta, zata gamu da fushina.!"

cikin sanyi murya yace.
"Abi kayi hakuri, kaga tayi komai a cikin fushi ne, shiyasa aimata uzuri." ya karasa maganar yana aza kanshi bisa kafadar Sarki Abu-Jalal.

"Hmmm dan tana uwar ka ko? ni da kake ganina banda gwani duk ɗaya suke a wajena kaf ''ya'yane zaneta sai inyi ba ruwana da mulkin ta ko wani matsayin ta bansan shashancin banza kuma dole in nuna ma Zulaiƙa kuskuren data tafka, sannan zansa Abdulmajid ya aura maka Bahijja, nayi hakane dan in nuna ma Zulaiƙa cewa *bayima 'ya'yane* shiyasa ban nunama Abdulmajid komai ba, nafison da kanta zata gyara kuskuren datayi a baya sama da shekaru talatin koma fiye da haka."

"Abi kaga wannan abun banjin...."yimin shiru Abdulmalik nagama magana ba'aimin musu, kasa ido kai kallo ko kuma kaima inhaɗa da kai."

"Uhmmm."
yace a gajarce dan baijin daɗin abinda ke faruwa tashi yayi ya shiga bathroom shi kuma Sarki Abu-Jalal, wani kayataccen ɗaki ya shiga a cikin sashen Yarima Malik, yana shiga shima bathroom ɗin ya shiga yayi wanka sannan ya shirya cikin shigar alfarma ta Sarakai kamar kullun ga sai baza kamshi yakeyi fitowa yayi, lokacin ana kiran sallar la'asar a falo ya iske Yarima Malik ya gama shiri cikin wani fitinannan yadi mai ɗan karen kyau milk ne baki ɗayan shi, sai hula daya murza ma kanshi kirar yar barno, ga gashin keyar shi tayi lub kamar wani balarabe, sai kanshi mai sanyi yake fiddawa, a tare suka tafi zuwa masallaci, shiko MalikusSaif tunda ya sako kafar shi ta dama waje cikin farfajiyar Masarautar Daborah sai yake ganin kamar ya shekara bai fito waje ba, komai ya sauya mashi takara yimi shi kyau na musamman ga iske dake busowa na yanayin damuna da aka fara musu, komai yayi lib gwanin ban shi'awa hakanan yaji yana smile a fuskar shi mai yalwa da kyau, duk inda zasu wuce sai bayi da hadimai sun zube sun gaishe dasu Yarima sannan sun mashi ya karfin jiki haka yaita amsawa har suka iso bakin shiga masallaci, suna zuwa kuwa dai dai lokacin aka kabbara sallah, cikin nutsuwa suka kabbara sallah, har aka gama ga kafadar MalikusSaif gata bawan shi Ashir sai gefen damar shi kuwa Sarki Abu-Jalal ne, ana gamawa suka dinga musabaha, yana mikoma Ashir hannu ya rungume Yarima yana kwallan jin daɗi shima rungumar sa yayi ba wani kyama a tsakanin su, dan son talakawa da Yarima yake dashi da saukin hali ya wuce tunani, Allah yai mashi jinkai a cikin zuciya, shiko Abu-Jalal sai murmushi yakeyi a ranshi yana cewa kaine Abdulmalik daman na daɗe da gayawa Sarki Abdulhamid cewa kaine kuma zakazo a cikin a halin mu dayardar Allah yau gashi duk alamu sun bayyana hakan, haka dai suka fito waje sukaci gaba da gaggaisawa, nan suka haɗu dasu Yazid baki ɗayan su suka ɗunguma, sai sashen Kangiwa, Sarki Abu-Jalal yace zai tsaya wajen Saifulislam, hakan yasa su Yarima Malik suka wuce sashen Huzaifa suna yar fira a hanya.


Da sallama a bakin Sarkin Runo Abu-Jalal, ya shiga cikin turakar Saifulislam asaman kujera ya iske shi, saidai dagani ya lula cikin duniyar tunani, saida Sarki Abu-Jalal ya zauna snnan ya ɗan taɓa hannun Kangiwa sannan ya dawo daga dogon tunanin daya lula,fuskar shi ɗauke da yalwataccen murmushi ya amsa, sannan suka gaisa cikeda girmamawa.

"Sanyawa yayi a kira mashi Zulaiƙa da Matawalle."
Rausayar dakai Kangiwa yayi sannan ya tashi da kanshi, yana fita sashen Matawalle ya wuce acan ya tadda Zulaiƙa da alama tasha kuka ta gaji saboda yanda yaga aminin nashi rai ɓace, ita kuma tana cewa.
"Yaya dan Allah katayani neman afuwa gun Baffa bansan yanda abubuwa sukazo mani haka ba, bansan taya yaji wannan zancen ba."

Cikin tsantsar ɓacin rai shima nashi idanun sun ƙanƙance dan fushi yace. "Dana gaya maki ba burus kikayi dani ba da mijinki irin wannan ranar nike jiye maki kenan, baki ɗauki kowa a bakin komai ba, kin ɗauka ke kinfi kowa daraja da ɗaukaka sai gashi yau an wayi gari keke nema wajen bayin da kike ikirarin sune kaskantun mutane a idanun ki."

"Haba Ya Abduljabbar kadaina tuna abinda ya wuce."

"Kaɗan kika gani Zulaiƙa indai rayuwa ce."

"Uhmmm kuzo Kawu na neman ku a sashena."
Maganar Saifulislam itace ta kashe masu zancen su wanda Zulaiƙa keji tamkar ta kurm ihu komai yai mata tsaye cak a rayuwar ta, shiko Matawalle bai kuma cewa komai ba ya maye bayan Kangiwa, itama binsu tayi tanajin wani irin ciwon kai na ɗibar ta, kamar yanda Kangiwa yabar Abu-Jalal haka ya sake iske shi saidai wannan karon yakasa zama yaje ya dawo yanata zirga zirga yana dukan hannun shi, cikin tafin ɗayan hannun nashi, baki ɗayan sukayi sallama amsawa yayi ataƙaice, sannan ya zubama Zulaiƙa idanun shi da basu da banbanci da rushin wuta, murya na rarrabewa tunkan ta duka ta gaishe da Baffan nata taji yace.

"Zulaiƙa ashe daman harkin iya isar da zaki wulakanta zuriyar Abdulmajid?"

Murya narawa Zulaiƙa tafara yan kame kame. "Baffa bawai wulakanta shi nayiba naga fa su bayine kuma......

"Kuma me kina haukane!?"
Ganin ya kawo mata wani wawan marin da baisan ya kawo shiba, yasa Sarauniya Zulaiƙa tai saurin dukewa dan Allah yasani duk iskancin ta tana shakkar haɗuwa da Baffa Abu-Jalal, tun tana kankanuwar ta, haka har zuwa yanzun tana shayin shi fiye da kima, bata ida fargabar da take ba, taji saukar marin Sarki Abu-Jalal bisa kuncin ta batasan ta saki ƙara ba dan azaba da raɗaɗi.

"Rai ɓace yace.
"Sainaci mutuncin ki, har kin isa kidubi kwayar idanuna kice ai bayine, tunkan a haife ki nasan Abdulmajid bawa ne, tunda shike tsaran uban ki, bare kigaya mani wai bayine, kodan darajar mahaifin ki, aikin ɗagama Abdulmajid bare kuma a haife ya haifeki, dan baki da ta ido dan kawai yana bawanki shine zakisa hannu ki mari fuskar Abdulmajid.!"

Zuwa yanzun kuwa ko magana Zulaiƙa takasa bare ta samu damar da zata kare kanta wajen Baffan nasu, kasan cewar tasan baisan musu ko kaɗan a rayuwar shi, ga wani firgici daya gama lullubeta musamman da taji raɗaɗin zafin marin daya aiko mata,amman ji take kamar ta kurma ihun azaba, maganar shi ta dawo da ta cikin tunanin ta.

"Dan haka ke dakika kulla tsiyarki da kayan kunyar ki, ke zakije ki gyaro komai, wlh Zulaiƙa inba hakaba zaki gamu da fushina wanda ni kaina bansan irin shiba."

Kuka ta sake rushewa dashi mai tsuma rai jiki na rawa ga zufa da tagama wanke Zulaiƙa tace.
"Baffa ka rufaman asiri nayi iyakar yina amman Abdulmajid yaki saurarona, saima cewa yake bai bada auren 'yarsa."

"Dan ya nuna maki girman haihuwa da darajar iyaye! Dan ya nuna maki iyakar matsayin ki! Dan suna bayin ki bashi ke nuna kidinga yimusu gadaraba da nuna karfin mulki ba! Dan ya nuna maki girma iyakokin ubangiji tunda ke kin riga kin rafkana kin shagala dadin mulki da girman kai yasa kin wuce matsayin ki da iyakar ki, girman kai da izzar da mulki yasa kinshiga hurumin da ba naki ba inasane da duk abubuwan da kika dinga shukawa a cikin mulkin da kika gabatar sama da shekaru talatin da biyar kenan ba wani sassauci kin maida bayi banzaye mararsa galihu musamman zuriyar Jafar Abdallah koda, Sarauniya Yahanasu taki bayi a zamanin ta bata kaikiba, tunda ita bata hana bayi haihuwa ba kefa? kinyi kutse a cikin hukuncin ubangiji shiyasa kika tsani Bahijja dan kawai anhaife ta bayan wata banzar dokarki da kika saka marar tushe da usuli harkin isa."

Dafe kanta Zulaiƙa tayi tan girgiza kai alamun aaa dan kam bata da bakin magana a halin da ta tsinci kanta a ciki taya zata fara neman afuwar bayin ta, makaskanta a wajen ta, kuma tasan yin hakan shi kadai zaisa ta kubuta daga fushin da Baffan ta yake da ita a wannan yanayin....jitayi yace.

"Dan haka kifara istigfar tunkan mutuwar ki, abin kunya ace tsatson Abduljabbar, jika ga Abu-Wakas, yar Abu-Jalal Sarkin Runo Sarkin musulunci kuma mata ga Kadimulislam Kangiwa itake yin aiki irin na jahilan farko, yazama dole ki aje al'adun kaka da kakanni tunkan ki ida rasa imanin ki, kuma billahil azim, indai kinasan inyafe maki yazama dole kije daga nan zuwa karfe shiddan yamma ki gyara komai da kanki, inba hakaba,ba cikin Masarautar ki mukeba wlh saina ci zarafin ki a gaban waɗan da kike ikirari basu da daraja kum makaskanta ne.!"

Itadai Zulaiƙa har kukan ma bai fita sai kwallan dake ambaliya a saman fuskar ta da kyal ta saita dakusassar muryar ta tace.
"Kayafeman Baffa bazaka sake samuna da wani muguwar ɗabi'ar ba dan Allah kayafemani Baffa."

"Yimin shiru karki sake taɓamani zuciya bakisan girman wanda kike haɗani dashi ba da bakiyi wannan abin kunyar ba, maza ki ɓacemani dagani awa ukku suka rage maki salan ki bari saina nemeki da kaina."

"Baffa....ya ɗaga mata hannu sannan yaci gaba sa cewa. "Kai kuma Kangiwa kabani mamaki ace matarka ke wannan abin kunyar, tana kalkashin ikonka kana mai bawa addinin musulunci gudun muwa amman gidan ka za'a dinga samun wannan sakarcin."

Rausayar dakan shi Saifulislam yayi cikin saukin rai yace."Kawu duk wannan abin na hana bayi haihuwa banda masaniya kasan cewar ni mafatauci ne, saidai nasan batasan tsatson Jafar amman duk da hakan ina tuni da nuna mata darajar ɗan Adam."

"Baffa duk abinda Kangiwa yace wannan lamarin haka yake."

"Tafi can kabani wuri kaima bakin ku ɗaya Abduljabbar kuke maza kuya kamata kuna kama mata wannan mulkin atafi dashi bisa turbar addini saboda raunin ƴa' mace, ya kamata ace daga ke a dakatar da mulkin kama karya, ya kasance Sarakuna za'a cigaba dayi a cikin wannan babbar Masarautar tamu mai ɗinbin daraja da tarihi, daman kece Sarauniya ta ta talatin da biyar, idan Abdulmalik yahau karagar mulki ya zama Sarki na talatin da biyar kenan, a jam'i ya kama Abdulmalik shine Sarki na saba'in kenan duk daga tsatson Sarki Abduljabbar na ɗaya ɗa ga Sarauniya Mulaika jikan Sarki Abu-Dawud, kunga ya zama dole kije ki tsarkake wannan taban da kika saka mana a cikin mulkin Daborah!"
"toh Baffa umurnin ka shine zabin mu, kahuta lfy."
wani kaskantaccen kallo yai mata baice da ita komai ba, haka ta tafi.
Jiki sanyaye Sarauniya Zulaiƙa ta koma sashen ta, wunin ranar ko runtsawa ta kasa ga rana ga ciwon kai da yake ɗawai niya da ita, haka kuwa aka kira sallar la'asar anagamwa bada jimawa ba Binta ta shigo baiwar Allah aikin ta tafara gabatarwa ta dawo cikin falo tana gogewa saidai duk abinda takeyi jinin ta na bisa hakaifa ganin yanda ran uwar ɗakin nata ke a dagule shiyasa take takatsantsan bata gama sakar zucin da take na, taji Sarauniya Zulaiƙa tace. "Umman Bahijja."

Sororo haka Binta ta dinga bin Sarauniya Zulaiƙa da idanun nata dake baiyana tsantsanar mamakin jin sunan da Zulaiƙa ta kirata dashi saɓanin baiwa ko kuma Binta wani lokacin ma har, yar bayi da uwar bayi sannan ƴar gadan wahala take kiranta dashi, shiyasa tabaje ba, a zatan ta kunnuwan tane basuji daidai ba, itama Zulaiƙa ta fahimci mamakine fal a cikin zuciyar Binta hakan yasa takara cewa. "Umman Bahijja zo."

A hankali tafara jefa kafarta kamar wadda kwai ya fashe mata cikin ciki,harta isa da zata duka Zulaiƙa ta tarota da hannun ta tabata kujera ta zaunar da ita, itako takasa hanata ko yimata musu,dan tsoro da mamaki daya addabi Binta duk a lokaci ɗaya. wani murmushi Zulaiƙa tayi wanda ita kadai tasan dalilin yinsa tace.

"Kefa uwace Binta kuma uwar Yarima inake ina aikin bauta, bayan zaki zama 'yantatta, na yafe maki duk wata bauta da zakiyi mani Binta saidai bansan da wane baki zanfara baki hakuri ba akan abubuwan da nai maku ba."

Batasan dalilin dayasa taji jikin ta ya ɗauki rawa ba kamar marar gaskia ba,takasa furtama Zulaiƙa komai.

Sake murmushin tayi tace. "Basai kince komai ba Umman Bahijja nasan abinda kike shirin faɗa kina shakkun mijin ki ko? Ke Asabe maza kiramin Abdulmajid inasan ganin shi!.''

sake kallan Binta tayi tace. "Dan Allah Umman Bahijja kiyafeman abubuwan danai maki na roƙeki?"

Still Binta takasa furta uffan dab tsananin al'ajabi da mamaki.

Itako Asabe aje aikin da takeyi tayi haka ta tafi har inda Abdulmajid ke aiki taje gaishe shi Asabe tayi cikin girmamawa sannan ta faɗa mashi sakon Sarauniya Zulaiƙa, jinjina kai yayi alamar toh, sannan ta tafi, tana komawa ta shaidama Sarauniya Zulaiƙa gashi nan zuwa, bata damar tafiya tayi, bayan kamar minti shabiyar saiga Abdulmajid yazo, duk da taga ya bata mata lokaci bataji daɗin hakan ba, saidai kodan masalahar da take nema hakan yasa ta hakura ba tace komai ba, shiko Abdulmajid dukawa yayi zai zauna bisa kafat dake tsakiyar falo, Sarauniya Zulaiƙa tace. "Haba Abban Bahijja ga kujera ka zauna."

Girgiza kai yayi yace. "Nan ma ya isa hawa saman iriyar wannan kujerar zaisa in'iya mantawa da asalina nagode da karamci."

Murmushin yaƙe Sarauniya Zulaiƙa tayi dan tasan tabbas ya gaya mata magana,saidai bata da zabi da ya wuce ta samama kanta mafita a halin yanzun.

Ɗan gyara murya tayi cikin sanyi rai tace. "Abban Bahijja nasake zuwa a karo na ukku akan abubuwan da suka faro wannan karan da kokon barata nazo,ina fatan zata karɓi kokon barar tawa."


Rausayar dakai yayi dan duk da baisan me zata ce ba, ya fahimci manufarta,"inajinki Allah yabani iko."

"Ameen inasan inemi yafiyar ku akan abinda na dinga aikata maku da cin zarafin ku, da wulakanta nasabar ku, ina mai baku hakuri dan Allah kuyafe mani!."

Murmushin jin daɗi Abdulmajid yayi duk da yasan akwai dalilin dayasa Zulaiƙa ta nemi afuwar su kodan Baffan ta da kuma son nemawa Yarima auren Bahijja,

a zahiri kuwa cewa yayi. "Bakomai ina fatan Allah ya yafe mana baki ɗayan mu."

Wani daɗi ne ya lullubeta ganin cikin ruwan sanyi ta gyara komai, yanzun abinda ya kamata shine ta sauwake masu aikin bauta da sukeyi masu


Gyaran murya tayi cikin jin dadi tace. "Allah ya saka da alkhairi kuma yabiyaku tabbas kun kasance daga cikin mutane masu sakan ta sharri zuwa alkhairi."

Binta ce tace. "Aiba komai Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare mu yan Adam."

Sake gode masu tayi sannan tace.
"Allah ya biyaku da mafificin alkhairin sa nagode matuka da karamci."
wasu kwalla suka dinga zuba a saman fuskarta, muryar ta na rarrabewa tace.
"Zaku iya tafiya Abban Bahijja."
Su dai basu koma cewa komai ba ta sallame su suka tafi, hakanan yau takejin wani irin daɗi ya lullubeta wanka tayi sannan ta shirya cikin shigar ta, ta alfarma ta tafi sashen Yarima Malik, wajen Baffan nata, aiko cikin sa'a ta iske shi shi kadai ya ɗan kishingiɗa yana cin iccen inabi cikin nutsuwa da kamala, amsa mata sallama yayi cikin kulawa ta zauna gefen shi saman kafat, a takure take, lura da hakan yasa yace. "Ƴata inajinki yi maganar ki, kinyi abinda na umurce ki?"
Saukar da kanta tayi
kasa sannan tace.
"Eh Baffa mun fahimci juna sosai kuma sun yafemani."

Jinjina kanshi yayi jikin kushin sannan yace.
"Kin kyauta saidai zan kara jan kunnenki ki zama mai yawan tausayi ga al'ummar dasuke kalkashin ikon ki, kada ki kasance kina gabatar da mulki na zalinci da mugun ta, duk wani ɗan Adam da kika gani a cikin duniyar nan, akwai tarin baiwar da Allah yai mashi, ki kiyaye ki nustu kuma ki hankalta, gaskia kin cutar dasu Abdulmajid ina fatan daga wannan makamancin irin wannan bazai sake faruwa ba.''

"Eh Baffa naga ishara arayuwa ta gashi mutanen da nike wulakantar wa nike kaskantarwa dan suna bayina, yau sune Allah ya nunamin ishara nike nema garesu, naga darajar su, yau nice dakai nike naimana afuwar bayina, gaskia Baffa son zuciya ne yayi nasara neman halakani, da hannayena na hana bayina haihuwa ko suna da ciki da yawa daga cikin su tsoron azaba sun saka sun cire cikin dake jikin su, wasu kuma su gudu, har Allah yasa aka haifi Bahijja, tsantsar kiyayyar da nikema iyayen ta yasa nace a halakata, da yake Allah shi kadai yasan wacece ita, Allah ya addabi ɗana da son baiwa, har rayuwar ke mashi barazana duk da kasancewar dana jarumi gwarzo mai jajircewa, ashe ita Jarumta ba ko ina ake nuna taba, ashe ɗana bazai iya nuna Jarumtar sa wajen rasa Bahijja ba! Ashe ɗana Jarumi ne amman a fagen da'ga gwani ne wajen iya sarrafa takobi, gwani ne wajen iya sarrafa kibiya sannan gwarzo ne wajen iya fille kan maza koda sunkai dubu cikin dakikai, nayi zatan Abdulmalik ta kowane fanni shi Jarumi ne, ashe banda fannin kauna da tausayi da yake ma Bahijja dan Allah Baffa kayafemani nasan nayi kuskure sannan katayani bawa Saifulislam hakuri yabari Abdulmalik ya gajeni ɓacin rai yasa yace Abdulmalik Fatauci ya gada ba Sarauta ba, kuma kasan abinda Kangiwa zai iya bai iya fushi ba, dan Allah Baffa kasa Abdulmajid yabawa Malik Bahijja, a 'yan tasu, ita da iyayen ta, naga mu'ujiza na aminta cewa *_BAYIMA ''YA'YA'NE_* Baffa."

_Wow ina masoyan Bahijja gareku kunji dai kalaman Sarauniya Zulaiƙa 🤣😂 to ina jira kubiyo Yar Mutan Kankia da bama baman Comments lol_ 🥰

Wani irin tausayin tane yaji ya lullube shi musamman da yaga tana kuka da idanun ta, kuma daganin idanun ta tabbas ta saduda tayi biyayya ɗan sauke ajiyar zuciya yayi yace.
"Zulaiƙa ko ubanjiginmu muna masa laifi ya yafe mana balle mu, karki damu Kangiwa zai hakura kamar yanda Abdulmajid suka yafe maki, sannan naimaki alkawali zuwa gobe za'ayi baikon Abdulmalik da Bahijja, wannan fagen na iyyene maza ne dan haka Kangiwa da Matawalle zasuyi komai, bazan bar Masarautar nan ba sai anmasu aure bansan ya wuce sati ɗaya zan tafi."

Wani irin dadi taji ya lullube ta batasan ta faɗa saman jikin Baffan nata ba tana kukan da batasan na farin ciki bane ko kuwa bakin ciki bane, lallashin ta ya shiga yi, a lokacin su Matawalle da Kangiwa suka shigo yanayin da suka taddasu ya tabbatar masu da komai ya wuce, zama sukayi suka gaida Baffan nasu, cikin kulawa yace.

"Kangiwa anjima kuje kunemawa Abdulmalik auren Bahijja, sannan ina neman alfarma gareka Kayafema Zulaiƙa kuma ka janye kudirin ka."

Sadda kanshi yayi tabbas yaso ya gama gwarata , saidai tunda har Kawun sa yai magana yasan komai ya kare, ɗan kallan ta yayi ta sadda kanta kasa, murya na rawa tace.
"Dan Allah Abu Malik kayafemani nayi danasani insha Allah hakan bazai kuma faruwa ba."

Rausayar dakai yayi yace. "Nayafemaki Allah yasa mugane gaskia kuma ya gafarta mana baki daya." Ameen sukace baki ɗayan su, sannan yace "Baffa kudurina kuma na janye amman fa dan kai, sannan tuni na nemawa Abdulmalik auren Bahijja, har mahaifin ta yace, ni zan zama waliyi ga Bahijja, dan haka kai Matawalle kaida Galadima kuje ku ida magana ayi baikon."

Bakaramin mamaki bane ya kama Sarauniya Zulaiƙa, arantako cewa tayi ashe duk haukan da nike daman Kangiwa ya gama komai,lallai kam Abdulmajid ya gama nuna mani iyakata.

Shiko Sarki Abu-Jalal
Cikin gamsuwa yace. "Shikenan abokina angama Allah kada yakara maimaita wannan abinda yafaru."

Ameen ya rabbi suka amsa suna cigaba da tattaunawa wannan karan kuwa akan yanda za'aima Malik ne naɗin Sarauta, har lokacin sallah yayi suka tafi ana idawa Matawalle ya nemi Galadima suka tafi jin magana.

A wajen Dawaki suka iske Abdulmajid kasancewar nan ne wajen da yake aikin shi, suna zuwa cikin girmamawa ya tarbesu, samun wuri sukayi suka zauna, Abdulmajid ne ya gaishe su, a mutunce Galadima ne yace. "Barka da rana, ya aiki."
"Alhmdullh." cewar Abdulmajid.

Cikin kulawa yace. "Muna tafe da babban al'amari a tareda mu, duk da ba sabon abu bane, munzo nemawa ɗanmu Abdulmalik izinin auren ƴarka Bahijja."

Murmushi mai fadi Abdulmajid yayi yanajin wani sanyi har cikin zuciyar domin yanzun yasan ya nemawa Bahijja gata, tunda har iyayen Abdulmalik maza da kansu suka zo neman auren ta, kamar yanda shari'a ta tanada, saɓanin da da mahaifiyar shi ke wuce iyaka, baisan sadda murmushi ya suɓuce mashi ba, cikeda kamala yace.

"Alhmdullh,naji daɗin wannan maganar taku, saidai ni banda ikon baku wannan izinin saidai kuje gun kanina Idris shine uba ga Bahijja."

Rausayar dakai Galadima yayi yana kara girmama lamari irin na Abdulmajid dan yasan Abdulmalik yazo gidan mutunci, basu kasa a guiwa ba Matawalle yace."Shikenan hakan yana da kyau, zaka iya yimana jagoranci?."


"Kwarai kuwa saidai bansan ko zaku iya shiga cikin asalin namu ba, yana cikin turakar bayi, kuma ku baku shiga cikin turakar ba....

Da sauri Matawalle ya katse Abdulmajid ta hanyar cewa. "Abinda yafi komai sauki kenan a wajen mu, ai kyaun 'ya abita a gaban iyayen ta duk da kasancewar Bahijja baiwa, ai dole mubita har usulinta dan kowa da nashi usulin yake takama da gadara kada ka damu Abdulmajid zamu shiga har cikin turakar bayi don nemawa ɗan mu izinin neman auren Bahijja."

Baice komai ba ya mike suma mikewar sukayi har cikin turakar bayi, da idanu sukebin tamfatsetsen wajen da yasha gini irin na da ɗinnan saidai komai a tsare yake ga gidajen bayi nan iri iri manya da kananan bayi sai hada hada suke dayake yaune ake cin kasuwar sati a cikin turakar sai huɗfa bayi sukeyi duk inda su Abdulmajid zasu wuce sai anbisu da kallo dan ba karamin mamaki bane bayyane a fuskokin bayin ba, sunsan a tarihin Masarautar Daborah jinin Sarauta basu shiga cikin turakar bayi yau gashi uban bayi tareda dasu maigirma Matawalle lallai dole suyi al'ajabi saidai fatan su Allah yasa ba wani laifin Abdulmajid yayi ba, haka sukaita kwasar gaisuwar bayi iri iri har suka isa wani makimancin gida mai ɗauke da tsakar gida da ɗakuna biyu sai zaure, tsayawa sukayi cikin zauren sannan Abdulmajid ya shiga ya sanarma ɗan uwan nashi komai, daman yasan da zancen bai ɓata lokaci ba, akaimasu iso bisa wata tabarmar Kaba aka shimfida masu duk suka zauna sannan aka kawo masu ruwa cikin kwanon gidauniya gaggaisawa sukayi, cikin rashin nuna kyama suka sha ruwan a mutunce sannan Galadiman Sarki Abu-Jalal wanda yake Kawun Sarki Abu-Jalal ne shine yafara magana yace.

"Dafatan mun sameku lfy?"
"Lfy lau alhmdullh."cewar Idris kanin Abdulmajid cigaba da magana Galadima yayi yace.
"Munzo neman izinin auren yarka Bahijja wa ɗanmu Abdulmalik."

Fuska cikeda annuri yace. "Masha Allah ai Yarima mutumin kirkine ga sadaukarwa dan haka ni Idris na bashi izini Allah yatabbatar mana da alkhairi."

Ameen ya rabbi cewar Matawalle sannan yace. "Zamuso a yau ɗinnan ayi baikon su, nan da sati ɗaya kamar yadda Baffan shi Sarki Abu-Jalal ya buƙata, sannan kada kuyi komai mu zamuyi anjima za'a kawo kayan shaidi sai kurabama dangin ku domin a shaida."

Rausayar dakai Idris yayi alamu gamsuwa yace. "Bakomai mun amince saidai muma zamuyi koda kadan ne daga abinda Allah ya horemana domin ƴarmu zataji daɗi idan taga abin iyayen ta." Matawalle zaiyi magana kenan Galadima yace.
"Ba laifi munji uzurin ku, saidai dafatan uzurin mu ya karɓu."

"Eh ya amsu Allah yakaimu satin lfy, sai a shaidama yan uwa lokacin ɗaurin auren tun yanzun."

Sake musabaha sukayi sannan suka aje ɗaurin kuɗi, da sunki amsa Galadima yace, ai na al'adane anaima kowace 'ya dole ne aima Bahijja itama 'yace kamar kowa, godiya sukayi sannan sukai masu rakiya har suka fita,cikin turakar bayi,

Please Login or Register in order to submit comment