Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kadan daga cikin tarihin Masarautar Runo.


Sunkuyar da kanshi MalikusSaif yayi yana mai yaba tsari na Masarautar Runo, dan yaji ABU-JALAL ya shiga cikin zuciyar shi kamar mahaifin shi haka yakejin shi, cikin girmamawa yace.
"Godiya nike ranka shidade Allah yakara girma da ɗaukaka." hannun shi Abu-Jalal yasa bisa kan MalikusSaif yace.
"Ɗana insha Allah saika zama jigo ga makaskanta mutane a cikin Masarautar ka dama kewayen ta, sannan zaka zama haske tsakanin duhu, zaka zama silar warwarewa tsakanin karya da gaskia Allah yaimaka albarka ya kareka daga makiyanka ɗana inaji a jikina akwai babban al'amari a tare dakai Abdulmalik, dan haka yanzun zakuje ku huta zuwa safiya zamu sake ganawa, Sarkin gida akaimin ɗana cikin sashena abashi masauki na musamman, Matawalle kuje ku huta, ya sunan abokin tafiyar taku.?"
ɗan taɓe fuska Matawalle yayi yace "Lurwan, sannnan ya kuma cewa. "Ranka shidade dan kaga ɗan ka shine zaka yada Matawalle ina laifin kabari inkai shi Masaukina tunda inada shashena."
murmushi ABU-JALAL yayi yace. "Aa a sashena zai zauna kafin agyara mashi nashi masaukin kai dai kaje naka,kaida bakon ka."
mikewa sukayi suka tafi Sarki Abu-Jalal yana karajin son Yarima Malik na kara ratsashi ta kowane sashe na jikin shi, saidai rabi tausayin sane yafi rinjayar shi, dan yasan yana fuskantar kalubale musamman a magauta da suka saka Masarautar Daborah a gaba dan cimma burukan su akanta.

Koda MalikusSaif ya shiga sashen SARKI ABU-JALAL wani irin sanyi yaji yana ratsa shi hakanan yaji wani irin aminci ya dabaibaye shi ya samu nustuwa cikin zuciyar shi, Yarima Dawud ne yakai shi cikin wani katafaren daki daya ƙayatu da kayan alfarma na SARAKAI wani irin kafcecen royal din gado ne fari kyal yanata ɗaukar ido yana sheki, cikin sakin fuska Yarima Dawud yace.
"Abokina ga ɗakin ka, ka huta yanzun ka shiga kayi wanka duk abinda zaka bukata akwai shi a cikin wardrofe." murmushi MalikusSaif yayi duk da yau yafara ganin Dawud sai yaji tamkar ya shekara suna tare, sai dai yai mashi kama da Matawalle kwabo da kwabo musamman yanayin maganar su iri ɗayane, fuska sake Yarima Malik yace.
"Nagode Kawu na, sannu da kokari." dafa kafadar Malik yayi yace. "Kacancanta Abdulmalik, bari inbarka ka huta." tafiya yayi shiko MalikusSaif rage kayan jikin shi yayi sannan ya shiga wanka.

A wajen Sarki Abu-Jalal kuwa yana tasowa da daga fa'da lokacin yamma yayi sashen shi ya wuce da zugar fadawan shi Sarkin zagi sai koda shi yakeyi, yana zuwa bakin shiga part din nashi suka dakata, sannan yai masu sallama Sarkin zagine ke cewa.
"Shigar ka lfy,Allah ya sadaka, da mafificin alkhairin wannan daren, ya kare damarka da haggun ka, angaishe da shugaba adali SARKIN RUNO."
haka ya shiga cikin ni'imtaccen sashen nashi ɗauke da sallama a bakin shi, ba kowa cikin sashen hakan yasa ya shiga cikin kayataccen ɗakin shi danyin wanka ya huta.

Shiko MalikusSaif fargaba yaji lokaci guda ya dirar mashi a cikin zuciya musamman daya tuna dalilin shi na zuwa wannan Masarautar, komawa yayi bisa gadon dake gafen damar shi ya zauna dauke da bisimillah a bakin shi, tunanin Bahijja ne fal a cikin ranshi yai mashi katutu duk motsin da zaiyi saita fado mashi a cikin rai musamman da ya tuna kalaman da tagaya mashi na bata *SON* shi, a hankali ya rufe idanun shi, a bangare ɗaya kuma nauyin Huzaifa ne ya rufe shi nakin ansar soyayyar kanwar shi, jin sallamar da akayine yasa shi maida kallan shi wajen mai shigowa ga mamaki yaga Sarki Abu-Jalal, cikin ƙimantawa da girmamawa MalikusSaif ya dan rankwafa yana gaida kakan nashi, zama gefen gadon SARKI ABU-JALAL yayi sannan yace.
"Ɗana tashi zauna kusa da Abi dinka, tashi Yarima Malik yayi ya zauna, gefen kakan nashi, kallan shi yayi cikin kulawa yace. "Abdulmalik inafatan bakada wata matsala ko.?"
ɗan shiru yayi kamar bazaiyi magana ba, sai kuma yace.
"Eh Abi banda wata matsala." nazarin yanayin Malik ya shiga yi na dakikai sannan yace. "Shikenan Abdulmalik yanda kace saidai kasani karka ɓoyeman komai ɗana rabona dakai sama da shekara ishirin kenan raban da inganka Abdulmalik saidai kasani bantaɓa kwana ba na tashi ba tareda nayi begenka ba a cikin zuciya taba, tareda tausayin ka, kazama jajirrtacce ɗana, bangaren Jarumta kayi koyi da halin Sarauniya Yahanasu, bangaren daddako da sanin yaka mata kaikoyi da SARKI Abdulhamid, sannan bangaren ilimi kayi koyi da SARKI Abu-jabbar na II haka zalika wajen aiki da ilimi kayi koyi da Kangiwa mutumina mutumin kirki masanin addini mai hakuri da sanin ya kamata Kadimulislam bawan Allah, kaga waɗan mutanen ba kananan mutane bane, kasan misaya nike maka wannan maganar?" girgizar kanshi yayi alamun aaa, sanin halin rashin yin maganar Yarima Malik tun yana Yaro yasa baidamu ba dan baiyi magana ba danma yanzun da alama ya sauya cewa yayi. "Saboda rayuwar da zaka fuskanta nan gaba kadan Abdulmalik."sauke ajiyar zuciya yayi yace. "Insha Allah Abi zanyi duk yanda kace sai dai Abdulmalik zaiso yayi koyi da irin halin SARKI ABU-JALAL shine tauraro na dan na gamsu da kalar mulki da adalci dayake gabatarwa akan talakawan sa lallai wannan mutumin shine abin koyi na, domin yana koyi da koyawar ma'aiki Annabi Muhammad (SAW) duk wanda yairiko da ma'aiki tabbas yayi riko da igiya mai kwarin gaske, fatana a duk lokacin da Abdulmalik yayi kuskure yana neman afuwa sannan a nuna MalikusSaif hanyar tsira da zaibi dan kyautata rayuwar sa."

Murmushi mai faɗi Abu-Jalal yayi yana mai son ɗan nashi jiyayi inama zuri'arsu su amince tabbas da MalikusSaif ya gaje shi sai dai zasuce a ɗan mace yazo kuma Masarautar Runo ba Masarauta bace da ake mulkin kama karya ba kamar Masarautar Daborah, su Sarukana ne garesu basu da Sarauniya wannan dalilin shine ya dakile kudirin Abu-Jalal akan ɗansa Malik tsawan shekaru ashirin da biyar, sauke nauyayyen ajiyar zuciya yayi sannan yace.
"Allah yaimaka albarka Abdulmalik, tashi muje falo an shirya mana wajen cin abinci, kaji nasan halinka da kawaici ka dauki kanka tamkar Abu-Jalal." murmushi yayi cikin jin dadi sai yaji inama ace ya dawwama a cikin Masarautar Runo zaifi mashi kwanciyar hankali, ba kamar inyana tare da Ummun shiba tana ɗagama shi hankali, idanun shi suka kawo ruwa yace.
"Tabbas Abi samun kaka kamar ka abune mai dadin gaske MalikusSaif yana godiya."
murmushin manya yayi yace. "Abdulmalik bazan matsamaka akan ka faɗa mani abinda ke damunka ba, saidai kasani nasan kana cikin damuwa, ba wannan ba muci abinci ɗana." da kanshi ya zuba ma MalikusSaif abinci, farin tuwon shinkafane miyar agushi da miyan ƴan ciki a gefe guda kuma farfesun 'kaji ne, haka aka ya zuba masu a flat daya suka fara cin abinci kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi.

➿➿➿➿➿➿➿➿
➿➿➿

Washe gari da safe a Masarautar Daborah Saifulislam ne zaune a falon shi dayake karɓar baki dasu Tasi'u sai Jakadiya Aisha a gefen damar shi kuwa Sarauniya Zulaiƙa ce sai Waziri Dammur, magana Saifulislam yafara yace.

"Assalamu-alaikum."
Baki ɗayan su suka da "Wa'alaikums-salam." numfasawa yayi sannan yace.
"Dalilin dayasa na taraku nan wajen ba dan wani abuba saidan muhimmin lamari daya tunkaromu inamai farin cikin sanar daku cewa cikin manyan Masarautun mu na ƙasar Gambia, ansamu Masarautar data karbi addinin musulunci wannan ba wata Masarauta bace face Masarautar Raifasu, Sarki Muhammad wanda kowa yafi sani da Sarki Baidulƙais ya anshi addini musulunci da dukkan jama'ar shi, dan haka nikeson su zama daga cikin mu kamar yanda addini ya haɗamu yan uwantaka, dole mukasance majibantan junanmu domin hadisi ingantacce mazan Allah SAW yace, Musulmi da musulmi yan uwan junane domin sashen su yana taimakawa sashe,musulmi yataimaka ma ɗan uwansa kada yaci zarafin sa ko ha'intar shi ko kuma cin zarafin sa, kunga da wannan hadisin kadai zaku san girman addinin musulunci, da darajar yan uwan taka, da haka nike cewa zamuyi haɗaka da Masarautar Raifasu domin Yakar Sarrilƙus domin yanzun shine kadai damuwar Sarki Muhammad, shi keso yai kawoma Masarautar nakasu, to bazamu laminta ba dole muɗauki mataki sosai wajen darkake wannan mutumin mushiriki da karfin ikon Allah."

Nauyayyen numfashi Sarauniya Zulaiƙa tayi tana al'ajabin lamarin fuska a sake tace. "Alhmdullh wannan labarin yafi kowane labari daɗin sauraro tabbas nida jama'a ta a kalkashin tutar musulunci ta jagoranci shugaban mu Kadimulislam munyi mubaya'a zamuyi duk wani kokarin ganin ankawo karshen wannan mutumin da ikon Allah." kallan Tasi'u tayi tace. "Naji dadi kwarai Tasi'u da Allah yasa Sarki Muhammad ya zama daga cikin mu, sannan ya maganar addinin nasu da ilimin su." a cikin zuciyar Saifulislam kuwa cewa yayi. "Hmmm dubeta sai kace mai aiki da ilimin ta, tana aiki da ilimi zata kyamaci yar uwar ta musulma dan kawai ta fita fifiko a idan mutane, kilan ma tafita daraja a wajen uban gijin ta, mtsw Zulaiƙa baki gane yare mai tsafta da sannu zaki hankalta."

Tasi'u ne yace. "Ranki shidade muna basu ilimin addini a cikin abinda mukasani, saidai muna barar malamai daga cikin wannan Masarautar tamu mai albarka ta Daborah."

Murmushi tayi tace. "ta hannun wa kuka karɓi wannan addinin mai daraja.?" Aisha ce tace. "Ranki shidade munkarɓi wannan addinin ta hannun kankanuwa saidai tafi komai daraja a garemu gata baiwa amman aikin bauta bai hanata aikata addinin ta, a sirrance ba, kyawawan dabi'un ta da hakurin ta da girmama na gaba da ita, shine yasa mukayi kwadayin shiga cikin wannan addinin na musulunci, ba wata bace sai Bahijja hadimar Baidulƙais a da, wannan shine asalin ansar wannan addini na musulunci, Allah ya azirtani da shiga cikin sa, daga bisani kuma shugaban mu, ya anshi addinin musulunci har kashi ukku cikin hudu na Masarautar mu suka anshi wannan addinin sannan Tasi'u da sauran bayin ku da kuka bamu su sukaci gaba da koyar damu addini dai dai gwalgwado kinji asalin musuluntar mu." duk da Sarauniya Zulaiƙa taji dadi yanda suka musulunta sai tasamu kanta cikin hassada wa Bahijja da tazama jigo a cikin wannan tafiyar domin itace mafari, Saifulislm ne yace.

"Yanzun zakuje kuci abinci ku huta,kafin ku wuce zuwa gobe kamar yanda kuka bukata, saidai inaso kusani idan ɗana Malik ya dawo zamuzo Masarautar taku, sannan duk wani motsi da kukaji daga wannan matsafin kuyi gaggawar sanar damu, zamu sameku cikin aminci da karfin izzar Allah SWT, infatan kowa zaije dan hutawa." haka suka tafi suna maijin dadin yanda aka anshesu cikin mutuntawa.....

Daga Sarauniya Zulaiƙa sai Saifulislam da kuma Waziri Dammur, wani irin kallo Saifulislam ya watsa masu sannan yace.
"Kunga yanda Allah yake ɗaukaka darajar dan Adam wanda kake ganin matsiyaci ko kaskantacce sai kaga Allah ya daga darajar shi, ta inda ba'ai tsammani ba, yau ga baiwa yar bawa jikar bayi tattaɓa kunnen bayi wadda akema inkiya da kaskantacciya ta zama silar shiriyar dubun nan mutane, wannan wace irin daukaka ce da tafi wannan a idan duniya da wajen Allah SWT, yau Allah ya fara nuna darajar baiwa, tabbas haihuwar baiwa yai rana, wanda Allah yasa sai ya rayu ba wanda ya isa yai ajalinsa yau ga jaririyar nan da akaso a halaka saboda son zuciya Allah yasa ta rayu har tayi silarta mutane masu ƙima masuji da mulki ga taurin zuciya sun musulinta aiko bawa ba abin wulakantawa bane sannan *bayima 'ya'yane* kamar kowa tunda suma haihuwar su akayi ya kikaji wannan labarin Ummu Malik?"

Mikewa tayi cikin gadara tace. "Abu Malik kenan inasa ita baiwar ta silata taje Masarautar da har ta musulintar da wasu, da kake ikirari, kuma ai Allah ya kaddara zasu anshi addinin musulunci ta kowace hanya."

Murmushi yayi mai ciwo ganin uwar ɗanshi naima kankanuwar yarinya hassada yace.
"Kigyara zancen ki Zulaiƙa, a dalilin Abdulmalik dai tunda shine silar zuwan ta Raifasu bake ba, dan haka kisa aranki Zulaiƙa wlh bakin da Allah ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho wlh sai yayi, kai kuma kabiyema son zuciya kana zigata kujuri zuwa rafi indai rayuwa ce.....

tashi Sarauniya Zulaiƙa tayi rai ɓace ta tafi tana kara tsanar Bahijja aranta dan akan tane kaɗai Saifulislam yake iya gaya mata magana son ranshi hakama akantane kadai ɗanta yafara bijirema umurnin ta.

Washe gari da safe,a ɓangaren Jakadiyar Saifulislam wato Hajara, zaune suke tareda Aisha, suna ɗan zantawa Aisha ce tace.......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 89&90




"Wai nikam ina uwar ɗakina Bahijja tunda mukazo gashi yau zamu koma bangan taba."

Murmushi Hajara tayi tace.
"Inake ina ganin Bahijja ai tana cikin turakar bayi, sai dai insaka akira maki ita sai ku gaisa."cikeda zumuɗi Jakadiya Aisha tace. "Danaji dadi kuwa sa akiramin ita.
toh Jakadiya Hajara tace, sannan ta fita, itako Aisha saijin dadi takeyi yau zataga Bahijja, bada jimawaba kuwa Hajara ta dawo ta zauna gefen Aisha cikin kulawa tace. "Yawwa nasa akiramin ita, insha Allah yanzun kuwa zaki ganta." takarasa maganar fuska a sake sunaci gaba da firan su.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

_MASARAUTAR RUNO_

Sarki Abu-Jalal zaune a cikin katafaren falon shi dake tsakiyar sashen shi wanda ya kawatu da kayan more rayuwa ta yau da gobe, gefen daman shi 'yayan shine mata dana 'yan uwan shi kyawawan gaske, a gefen shi na haggu kuwa 'yayan shine maza kama dasu Yarima maijiran gado dasu dagaci da sauran yayan dangi sai saman kujerar dake gefe n hannun damar shi Yarima Malik ne sai a haggu kuma Matawalle ne sauran kujerun da sukaima falon zagaye matan sa ne sai mahaifiyar shi har yanzun tana raye wadda itace matsayin kaka agaresu, kowa yayi shiru yana jiran yaji abunda Sarki Abu-Jalal zaice ɗan gyaran murya yayi ya maida hankalin kan su bayan yai masu sallama, duk suka amsa, cikin dattijan taka yace.

" ina ma kowa barka da zuwa wannan taron kamar yanda kukaji ance ina neman ku,haka abin yake nasa akiraman ku dan ingabatar maku da babban ɗa, ko kuma ince jikana Abdulmalik da baffan shi yakawo shi dan yaimani ziyara wannan dalilin yasa nace akiraman ku don in nuna maku ɗan uwan naku ya ganku kuma ku ganshi, kunsan girma da darajar dake cikin *zumunci* dan haka kunga Abdulmalik ina san duk kugabatar mashi da kanku, kuma ɗa ne ga Sarauniya Zulaiƙa ƴar Sarki Abdulhamid nasan kunada labarin ta da _MASARAUTAR DABORAH_ baki ɗayan ta."
baki ɗayan su,duk suka amsa da eh.

Jin nasabar MalikusSaif sai yasa duk sauran matan suka dinga kus kus da baki ga sai kallan shi sukeyi shiko kanshi kasa yanajin yanda kakan nashi keta jawabi, yana murza zoben azirfar dake sake a hannun shi jin ankuma magana ne yasa ya ɗago kyakyawar fuskar shi ya kalli mai magana, Yarima Dawud ne yace. "Kamar yanda kasani nine Yarima Dawud, inaimaka barka da zuwa cikin dangi a Masarautar Runo lafiya." gyada kai yayi tareda yin smile alamun ya amsa, haka kowa ya dinga fadan sunan shi har zuwa "Abdulbasir wanda shine karami a cikin jerin maza na yayan Sarki Abu-Jalal, a bangaren mata kuwa cikin isa da kasaita wata kyakkawar budurwa tace.
"Sunana gimbiya Hafsat, sannan munji dadin kasancewa a cikin mu."shidai da ido ya bita ganin tana ta wannan yatsina da gani dai ba ragi a wajen ta kauda kanshi yayi take yaji batai mashi ba, baisan wuce wuri,haka dai akai ta gabatarma junan su kansu har zuwa karshe inda wata matashiyar yarinya tace.
"Sunana gimbiya Maimoon munaimak barka d zuwa." samun kanshi yayi da murmusawa yanda tai maganar sai yaga taimashi yanayi da Bahijja duk da kana ganin ta kaga Sarauniya Zulaiƙa dan kamar copying din tace, haka kawai yaji ta kwanta mashi arai duk da bazata wuce shekara sha biyu ba a duniya, bayan sungama Sarki Abu-Jalal ya nuna mahaifiyar shi yace.
"Ga Hajjanan mamana kenan sunanta gimbiya Yahanasu, sai wannan babbar matata ce sunan ta gimbiya Mulaika, sai wannan ita kebin ta ita kuma gimbiya Marawiyya, sai ɗayar itace gimbiya Hamdiya, sune kakan ninka Abdulmalik."

Murmushi yayi cikin girmama kakan nashi yace. "Nagode Abi da girmamawar ku a gareni ina fatan Allah yasa albarka da aminci agaremu baki ɗaya." shafa sumar kanshi Abu-Jalal yayi suka ya amsa da Ameen sannan ya sallami kowa baki ɗayan su suka fita, Yarima Dawud ne ya riko hannun YarimaMalik suka tafi wanda yake nan danan da Malik tamkar sun dade tare sai yawo yakeyi dashi sashe sashe na *MASARAUTAR* yana kai shi gidajen yan uwa da wuraren tarihi na cikin Masarautar, koda kowa yagama fita ya rage daga Matawalle sai Sarki Abu-Jalal, sunkuyar da kanshi Matawalle yayi yace.
"Baffa daman inada muhimmiyar magana data kawoni a cikin wannan Masarautar kuma zancen nan nakane." ɗan rausayar dakan shi Abu-Jalal yayi yana mai nazartar ɗan nashi cikeda nitsuwa yace. "Inajinka Abduljabbar." saukowa yayi kasa ya tankwashe kafar shi sannan yace. "Daman zuwan nan danayi nazone da Abdulmalik domin ya duba cikin 'yayan dangi ya zaɓi matar da zai aura yaka mata ace zuwa yanzun Malik yana da iyali."

Murmushi Abu-Jalal yayi irin nasu na manyan Sarakai, shi kanshi yaji dadin hakan saidai yana fatan Allah yasa a ciki a samu wadda tayima MalikusSaif dan irin son dayake mashi bazai laminci aimashi auren haɗi ba, cikeda dattako irin na mutanen kirki masu kamala da sanin yaka mata yace.
"Kunyi tunani mai kyau saidai kasani inada nawa sharadin Abduljabbar." jiyayi gaban shi ya tsinke dan bai cika son Baffan nasu na saka sharadi ba inzaiyi magana yasan halin shi kaifi ɗaya ne, cewa yayi. "Nimai biyayya ne ga duk wani sharadin ka Baffa"cikin jin dadi yace.
"Inhar kasan akwai wadda Abdulmalik keso bansan ka boyeman kuma abishi da zabin shi kar atankwashe shi, sannan idan har ba wadda taima Abdulmalik a cikin yaran nan shikenan nidai ban yarda ba kuma ban laminta ba aima Abdulmalik auren dole bs, abar shi da aikin magauta da suka tisa Masarautar Daborah a gaba, yaji da wannan tashin hankalin ina fatan kagane Abduljabbar." da sauri yace.
"Allah yataimaki Sarkin Runo Abdulmalik ya gode da wannan adalci, saidai zamuji ta bakin shi." cikeda gamsuwa ya rausayar dakai yana mai matsa yatsun hannun sa a hankali suna bada sautin kara, duk da ya tsufa sabida Abu-Jalal zaikai kimami shekara casa'in da bakwai a duniya, cikin zuriar su daga shi sai dagaci kanin shi sai kanwar gimbiya Murjana sukadai suka rage sauran duk sun rasu saidai sun bar tarin zuriar wannan dalilin yasa su Sarauniya Zulaiƙa basu iya ketare umurnin Abu-Jalal, sai mahaifiyar shi gimbiya Yahanasu da take da kimamin shekara ɗari da goma sha biyu a duniya ta tsufa damma hutu ke dannne tsufan da shekarun.......

***************************************

~DABORAH~


Koda baiwar da Jakadiya Hajara ta aika kiran Bahijja tana isa gidan su Bahijjar ta isketa tana yin sikola saidai azahiri take sikolar amman zuciyar cike yake da damuwa mai tarin yawa, gashi yau ta tashi tana matsanancin ciwon ciki kasancewar watan ta yaka mata na period din ta shiyasa take abubuwa a sukuku ba wani hanzari a tattare da ita, jin nataɓata yasata juyowa a tsorace kuma take takarajin cikin nata yakara kullewa dan ta firfita ko sallama batajiba, ganin wanda ke kantane yasata sakin ajiyar zuciya lokaci guda, a daddafe tace.
"Salame lfy kuwa.?" murmushi tayi tace. "Kedai Bahijja narasa mike damunki tun ɗazun nike rafka uwar sallama amman kamar matatta wlh ki kiyayi kanki kinada karancin shekarunki kike damuwa irin wannan.?" murmushi kawai tayi tareda rausayar da kanta, bata kuma cewa komai, Salame ce tace. "Ina Kawu yake inasan ingan shi." ɗan taune lips din ta Bahijja tayi alamun tanajin jiki tace.
"Yaje gidan Baba idi kinsan dai naji ance Ya Tasi'u yazo saidai ban tabbatar da hakan ba, shine yafita." numfasawa Salame tayi ɗiyar kanwar Abdulmajid ce Ladidi, cikin kulawa tace. "Kinga idan nabiye wannan inuwar mangoran zan iya shafa'a da aikina sannan in mance sakon da aka aikoni gareki." jitayi gabanta ya tsinke bugun zuciyar yana lunkuwa Allah yasa harbata son taji ance ana kiran ta, tasan ukuba da azaba zata sha tafahimci ba wani alkhairy ga kiran da ake mata, wani bangaren na zuciyar ta kuwa tan tausan yanda dangin ta suketa bauta, abin yazamar masu gado, amman haka Allah ya tsara, a sanyaye tace. "Wake kirana Salame." numfasawa tayi tace. "Jakadiya ke nemanki a sashn ta." ɗan rufe idanun ta tayi sannan ta wanke hannun ta dake cikin botikin wanki da takeyi ta mike da kyal tace. "Mutafi ko.?" haka suka kama hanya har suka shigo cikin Masarautar suna ɗan taɗi irin na yan uwa, suna shigowa takama hanyar zuwa bangaren Jakadiya sukayi karo da gimbiya Zahara'u da alama zataje sashen Sarauniya Zulaiƙa ne baya baya Bahijja tayi dan ba kadan taji zafiba daman ga matsanancin ciwo da marar ra kemata, kafa tasa ta taka Bahijja ganin ta a duke, sannan ta sake ingizata cikin isa da gadara tace.
"Waike wace jahilace mayya ce bakida idanu koduk girman idon na facine.?" ɗan taune bakin ta Bahijja tayi a hankali ta yunkura ta mike ta kalli gimbiya Zahara'u tace. "Allah ya huci zuciyar ban kulaba." batajira cewar gimbiya Zahara'u ba ta saka kai ta tafi a hankali take tako harta iso cikin sashen Jakadiya itako Zahara'u a kufule ta gyaɗa kai ta tafi sashen Sarauniya Zulaiƙa da kudiri a cikin zuciyar ta, da sallama a bakin Bahijja ta shiga madaidaicin falon Jakadiya, tsaye tayi tana mirza idanun ta alamun suna nuna mata gizau itako Jakadiya Aisha da sauri ta yunkura ta tashi ta rungume Bahijja tsam a jikin ta lokaci ɗaya suka fara sintirin hawaye masu ɗumi da begen junan su, itadai Jakadiya Hajara da idanu ta raka su ganin kamar uwa da ƴarta, aranta ko tace idan wani yakika da yini wani saiya soka da shekara daman haka rayuwa take, Bahijja ce tace.

"Baba Jamra inata kewarki a cikin zuciya ta ina Zainab da Indo da Baba Saude?" lokaci ɗaya duk ta jeroma Jakadiya waɗannan tambayoyin tareda goge mata kwallan idanun ta, kama hannun ta tayi ta zaunar da ita gefen ta cikin so da kaunar da uwa keyima 'yarta tace. "Ƴata kidaina kuka su Zainab sunanan duk lfynsu lou, hakama Saude." cikin jin dadi Bahijja ta kuma cewa. "Baba Jamra mikukazo yinan?." murmushi mai faɗi tayi tace. "Munzo wajen Kadimulislam dan shaida mashi cewa Masarautar mu muna kalkashin tutar musulunci tundaga Sarkin mu harzuwa bayin mu da yawan mu duk mun musulunta." wani irin farin cikine ya mamaye zuciyar Bahijja batasan ta faɗa bisa Jakadiya ba, tana kukan farin ciki, sauka tayi ƙasa tana mai sujjada ga Allah tana kara godema Allah sannan ta ɗago ta kalli Jakadiya tace. "Alhmdullh Allah yakara tsira da amince ga fiyayyen halitta wanda Allah yai duniya da lahira domin shi sannan ya aiko shi da addinin gaskia dan ya zama rahama da ni'ima ga talikai ya wadacemu da ni'imomi iri iri da tarin ilimi a cikin litattafin nan da ya zarce tunanin mai tunani ta hanyar lugga mai girma wato *ALQUR'ANI* mai girma, Baba Jamra wannan shine tunanina akanki tunda kika anshi wannan addinin tsoro ya dira cikin zuciya ta gudun kada rayuwar ki ta salwanta, dayake Allah mai rahama ne gashi yasa *MASARAUTAR* *RAIFASU* tazama haske daga duhu ba abinda zamuce sai godema Allah SWT." sake rungume ta Jakadiya tayi tace "tabbas Bahijja rayuwarmu dake ta zame mana alkhairy yau ga Sarki Baidulƙais yana ansa sunan Sarki Muhammad, Jakadiya Jamra yau tana ansa sunan Aisha Sarkin fada ya koma Umar, Galadima shine ake kira da Abubakar, Waziri shine ke amsa sunan Aliyu, intakai cemaki yau Magayaki shine Usman, miyafi wannan dadi Bahijja Allah shikadai ya cancanci agodema shi, domin ni'imar shi ta wadace mu." murmushi Jakadiya Hajara tayi tace. "Gaskia ne 'yar uwa Allah abin godiya." cikin kulawa takara kallan Bahijja dake ɗan taune lips dinta tace.
"Yata mike damunki naga kin ɗan faɗa kinyi rama, lfy?" murmushin karfin hali tayi tace bakomai, dan tasan da wahala idan Babarta tagan ta ko ada tana saurin gane damuwar ta, amman batasan tasan abunda ke faruwa."
ganin Bahijjar batasan tasani yasa bata ta kurata ba, gani tayi ta duke kasa ta rike ciki tana nukurkusa tana cewa.
"Wayyo Allah na Umma na cikina zan mutu, inalillahi wa'inna ilahir raji'un, Wayyo Allah Baba kitaimakamin." da sauri Jakadiya Hajara tayi kanta itako Aisha rungume tasake yi

Please Login or Register in order to submit comment