Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauke kanshi a cikin filin daga domin shine damuwa ta a ahalin yanzun kai kuma kaji da Baidulƙais."

"Toh cewar Haishir."

"Kaje ku hada gangami gobe zamu hadu da MalikusSaif a Raifasu saina halaka shi, kaje zan hado tawagar aljanu saidai kamar yanda suka bukata a bayyane za'ayi Yakin nidasu aga wanda zai gaza."

Take aljani ɗantsitu ya bace da Haishir.

A Masarautar Raifasu kuwa Saifulislam ne ya yara kaf Jaruman su baki ɗaya yace.
"Idan kuna Yaki da wadannan gafallalun duk sadda zaku kai masu sara d takobi ko da mashi, ku dinga fadin kalmar _Bissimillah_ insha Allahu saimun karshen su."

Haka kuwa kowa ya tashi ganin dare yafara sallar magarib d isha'i suka gabatar kowa yai gida dan hutawa kafin safiya wannan kenan.

Washe gari da safe a Masarautar Waisu suma sungama hada sahu sahu kamar ba gobe harda jama'ar Sarki Danwar sai mutanen Sarrilƙus na aljanu da matsafa irin shi, Sarrilƙus ne tsakiyar su a saman wani bijimin doki na tsafi sai Sarki Haishir da Danwar agefen shi, haka suka gama ihun su d maganganun su masu wuyar fassara saidai da alama yana jamasu kunne akan kada wanda ya ɓace yayin da ake Yaki dan kar aga gazawar su, haka sukaitama Masarautar Raifasu tsinke a hatsune.

Suma su Sarki MalikusSaif sungama shirya wa saidai rabi da kwatar Yakin bada Jarumta suka dogara ba da kalmar Allah wato ambatan sunan Allah a kirazansu harma a zahiri suma din a layi suke sunyi kowace dubara ta Yaki suna jiran tsammani ta kudu ko yamma ko arewa dan sun san bazasu iya shigowa ta gabas ba manema sa'a dan sai alummar annabi keda ikoda gabas, tafi karfin mushiriki.

Aikuwa su Sarrilƙus iya wuya sun iso bakin Masarautar Raifasu saidai kirjin shi kamar ya bare dan shakk da tsoro da yarasa dalilin jin hakan tunda yaji kalmar daya rasa ma'anarta, haka shima Haishir yana shakkar haduwa dasu Sarki Muhammad a ranshi haka suka tsaya suna shawarar ta inda zasu farmasu, Sarki Haishir ne yace.

"Murabu kashi ukku, kashi ɗaya su biyoni mushigar masu ta yamma, kashi ɗaya kuma su shiga ta arewa tareda Sarki Danwar, sai sauran kubi Sarrilƙus ta kudu kunga munyi masu zobe saimu farmasu mu cinye Masarautar baki ɗayan ta, tabar kalkashin daular musuluncmusulunci ta dawo kamar yanda take a da."

Cikin gamsuwa sukayi yanda Sarki Haishir yace masu kowa yabi shagoran su, suka shiga cikin Masarautar.


Suko su Sarki MalikusSaif suna a shirye tareda makaman su wanda suka sha ayoyin Allah da addu'oi abokan gabar tasu kadai suke jira a wannan lokacin.


Koda suka shigo cikin Masarautar ta wagar Sarki Haishir ne suka bullo cikin filin Yaki ta arewa tsaye sukayi ganin wajen tankam da Jarumai saida gaban su ya yanke ya fadi, da gudu sukayo kan su Sarki MalikusSaif suko ko motsawa basuyi ba daga inda suke suka zaro kibiyoyin su suka fara harbin su dasu Huzaifa da Yazid sai Mansur babban Jarumin Raifasu haka suka dunkule waje ɗaya suka dinga kasar su da kibiya kafin suyi rabin isowa wajen su sunkashe mutane dayawan gaske, suna isowa kowa yasa kariya suka game duk musulmin dake cikin wannan filin daga idan suka daga takobi zasu sari mutanen Sarrilƙus sai suce, bissimillahirrahamanirrahim. sai su ɗaga takobi su saramasu karaf haka karar takubba ke tashi ga tarwatsin wuta na fita sai sarar junan su sukeyi saidai cikin ikon Allah da karfin ayarshi mai girma kafin a kashe musulmi ɗaya ankashe kafirai sama da goma, haka akaita kasar Jaruman Sarki Haishir.

Shiko Sarrilƙus ya na shigowa cikin filin Yakin neman MalikusSaif yafara ido rufe, daya tunkaro inda yake duk wanda ya hadu dashi sai ya sauke kanshi kasa da takobi,koda Saifulislam yaga irin ta'adin da Sarrilƙus keyi ga mutanen su, da gudu ya hau bisa doki da takobi ya tunkaro inda Sarrilƙus ke kashe masu mutane da jama'ar shi, shima cigaba da kashe mutanen Sarrilƙus yaci gaba dayi da ya sauke kai, sai yace, Allahu akbar.

Haka sukaita ta fatattakar Jaruman Sarrilƙus da ayar Allah.

Shiko Sarki Muhammad ana cikin Yaki yaji ya bangaji mutun juyowar da zaiyi yaga Sarki Danwar ya ɗaga takobi ya zai sara mashi da sauri ya kauce, aiko ya sari iska, cikin gafin nama ya daga takobi ya sara mashi gafen wuya, take jini ya balle, a tsorace Sarki Danwar yace.

"Baidulƙais ni zaka kashe kamar yanda ka kashe Sarki Lahazu?"

Ko amsa bai bashi babya sake sharɓa mashi takobi a hannu yace.

"Allah ya tsareni daga kaidin ku, ya tsareni da komawa Baidulƙais! Ni sunana Muhammad."

Yana gama fadin haka ya sauke kafar Sarki Danwar, sai kan idan Sarki Haishir daya kasa karawa da Sarki MalikusSaif da gudu yayo kan Sarki Muhammad zuwa lokacin kuwa Sarki Muhammad ya sare kan Sarki Danwar ya dauki kan nashi yayi wurgi dashi sai a jikin Sarki Haishir, jini ya wanke mashi fuska, haka kan yayi tsalle sai gaban Sarrilƙus.

Shima a kidime ya sauke kan wani babban Jarumin Raifasu tunda duk ya sansu, ganin kan Danwar gaban shi bakaramin tsorata yaiba, hankalin shi yai masifar tashi, ji an dafka mashi takobi aka fada yasa shi juyowa da sauri MalikusSaif rike da takobin Barri, a firgice ya fara ja dabaya dan ba abinda yake bala'in tsoro da shayi irin takobin Barri shiyasa yaso ya raba Masarautar Daborah da takobin shiko MalikusSaif cigaba da binshi yayi da takobin, jikin Sarrilƙus har kyarma yake ya cigaba daja da baya.

Jiyayi antokare shi ta bayan shi Matawalle ne rike da takobi da tagama jikewa da jinin bil'adama tsaye yayi ga firgice iya firgice ya shiga, koda MalikusSaif ya iso wajen Sarrilƙus yaima Matawalle nuni da ya bar shi dashi, haka kuwa akayi, take suka kaure da karar takubba saida hankalin mutanen dake kusa dasu ya dawo garesu, cigaba da kaftawa suka dinga, duk daga takobin da MalikusSaif zaiyi ya sari Sarrilƙus saiya ambaci sunan Allah.

Aikuwa hakan yafara tasiri dan zuwa yanzun Sarrilƙus jikin shi yafara tsuma ga jinin dake dibar shi tsoro da fargaba sun gallabe shi, shiko MalikusSaif cigaba da sarar shi yayi shima yana kawo ma MalikusSaif sara da takobi.

Yaki yai Yaki kura tai kura baka ganin komai kasa sai kan Jarumai musamman na Sarki Haishir zuwa yanzun kuwa Sarki Muhammad da Haishir sun jigata junan su, sannan Sarki Muhammad ya yanki Haishir a cikin shi jini keta shatata kasa, amman a haka yake kare kanshi, shi kanshi Sarki Muhammad yaga banbaci da yake yaken daya sabayi da wannan Yakin yasan cewa ayar Allah ba abin wasa bace, yanda yaga duk yawan jama'ar Sarrilƙus amman sun kashe fiye da rabi.

Wani irin dadi yaji ya lullube shi ya dinga godema Allah dan yasan Yakin nan taimakon Allah ne kawai a cikin shi.

Shiko Sarrilƙus ganin MalikusSaif na niyar kashe shi, baisan sadda ya ɓace ba, aikuwa duk mutanen shi wa'anda ba mutane ba suma sukayi ɓatan dabo.

Koda Saifulislam yaga haka wani shu'umin murmushi yayi, ya kalli Lurwan da jikin shi yai fafata da jinin kafirai, koda ya kalleshi take yagane manufar shi, wani usur ne ya busa saiga wasu mutane tururuwa sun shigo cikin filin Yakin hannun su dauke da kwalabe da ruwa a ciki wannan karon ko Yazid ne commender, suko Sarrilƙus ganin da gaske ba mai ganin su ga hannun shi jini keta zuba amman duk da haka mutane basu ganin saukat jinin cikin gaifin nama yakaima MalikusSaif sara da takobi ya yankar mashi hannu.

"Hasbunallahu wani'imal wakil."

Shine abun MalikusSaif yafada dan yaji yakan da akai mashi amman bai ganin Sarrilƙus, wani shu'umin murmushi yayo ganin yanda MalikusSaif kejin yakan da yai mashi.

Haka suka dinga kashe mutanen Sarki Muhammad, suma cigaba da kashe wa'anda Allah yasa basu bace ba, ashe rabi da kwatar mutanen Sarrilƙus duk Aljanu ne, shiko Sarki Haishir ganin yanda Sarrilƙus ke kashe mutane wani dadi ne ya lullube shi, shima cigaba da yakin yayi.

shiko Sarrilƙus wajen Sarki Muhammad yaje ya daɓa mashi takobi a kugu, jin wani yar duk jikin shi ya dauki zafi yace.

"Lahaula wala kuwata illa billah."
A fusace Sarrilƙus yace.
"Kada ka kara furta wannan kalmar akaina kuma sainayi ajalin ka, maci amana."

Shiko da yakejin zafin ya ragu yace.
"Kabayyana kanka inka cika Jarumi, kuma ta Allah ba takaba, fasiki mashirki wlh saina kashe ka da izinin Allah."

Sake dabawa Sarki Muhammad takobi yayi.
Rike hannun shi yayi yace.
"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un."

Dai dai lokacin Sarki MalikusSaif da Saifulislam suka iso wajen, dan alamu sun nuna Sarrilƙus ke yankar Sarki Muhammad.

Shiko Sarrilƙus yana ganin su MalikusSaif sunyo inda yake ya sake daga takobi ya yanki MalikusSaif da ita.

Dai dai lokacin Bahijja dake bacci ta farka da inalillahi wainna ilahirrajiun. Da sauri Mansura ta iso wajen tana tambyar ta ko lfy.

Murya na rawa tace.
"Mansura raina na bani akwai abin dake faruwa da Ya Malik dina."

"Haba ranki shidade kada kice haka addu'a zamuyi masu ba wannan tinanin ba.

Haka ta dinga kwantar mata d hankali, tashi tayi tai alwalla tana gayama Allah kukan ta.

*FILIN DA'GA*

Shiko MalikusSaif ambatan sunan Allah.

Kwalbar hannun ya watsa inda yakejin dariyar muguntar Sarrilƙus aiko wata uwar kara ya kwada wanda saida kowa ya dakata da Yakin da sukeyi har wani girgiza wajen keyi.

Suna ganin haka dukkan Jaruman su MalikusSaif sukaci gaba da wurgi da kwalaben hannun su suna fashewa tas tas tas, sai ihu d kururuwa wajen keyi komai rawa yakeyi, MalikusSaif ne ya anshi kwalbar hannun Saifulislam ya sake jifa kwalbar sai a jikin Sarrilƙus hayaki keta fita a jikin su.

Take suka dinga bayyana saida jikin su kamar an babbaka su da ruwan zafi, a wahalce Sarrilƙus yafara ɗaga hannu alamun ban hakuri ya saduda jiki na rawa yace.

"Kada ku kasheni MalikusSaif na tuba na janye Yakin nan kada ku kasheni kunfi karfina.

Baidulƙais kace su kyalemu kasan kai namu."

A fusace Sarki Muhammad ya figi takobin Barri dake hannun MalikusSaif ya dabawa Sarrilƙus yace


"Yimin shiru matsayaci kaskantacce sunana Muhammad ba Baidulƙais nina barranta daku, kaje can kanemi gafalalle irin ka."

Ga jikin shi sai darewa yakeyi dan azaba, ga takobin Barri na ratsa jinin jikin shi, aiko su Yazid suka ci gaba da kasar Jaruman Sarki Haishir da Sarrilƙus kamar kiyashi shiko Sarrilƙus sai yankar shi Sarki Muhammad keyi ganin kamar bai wani abun kirki yasa MalikusSaif ya anshe takobin hannun Sarki Muhammad ya sauke kan Sarrilƙus dashi take duk wani matsafi da aljanun da yake sarrafawa sukaita faduwa a mace, ganin haka yasa Sarki Haishir ya zube kasa da guiwowin shi ya zubda makaman shi hakama sauran jama'ar shi da suka rage duk sukai jifa da makaman su, alamun sunyi biyayya.

Suma suna ganin haka Sarki MalikusSaif ya daga masu hannu alamun su dakatar da Yakin suma ajewa sukayi.


Kanshi sunkuye kasa alamun bakin ciki da tarin shakka suka addabi rayuwar shi ganin lokaci ɗaya Sarrilƙus ya zama tarihi ankashe shi da jama'arshi, cikin jin kunya yace.

"Kaicona ni Haishir ɗan Lahazu bamuda nasara duk Yakin da akeyi dan haka na barranta da sake yin Yaki daku, na rokeku kuyi mani lamani ni da sauran jama'a ta, mu koma Masarautar mu danci gaba d rayuwar mu."

Murmushin jin dadi Sarki Muhammad yayi yace.

"Kun zama bayin mu, kunga girman ayar Allah ko? Kunga girman addinina na musulunci ko? Yau gashi kun wulakan ta a idon duniya wannan kadan daga cikin addinina, kuma addinina mai karamci ne."

Wasu kwallane suka zoboma shi yace.
"Nagani nidai kubarni intafi bazan kara kawo maku hari ba."

Sarki Muhammad zaiyi magana kenan, MalikusSaif ya ɗaga mashi hannu yace.

"Kaje amman da sharadi karka kuskura ko inuwarka mugani a cikin Raifasu baka ba Masarautar nan, kaje can da kafircin ka, kaji da kanka, inafatan ka hankalta."

"Naji sharadin ku, kuma na amince."

"Uhmmm ka kyauta."

Tashi yayi shida sauran jama'ar shi suka tafi rai ɓace.

Suko su Sarki MalikusSaif wucewa sukayi kowa yaje yai harkokin dake gaban shi, lokacin sallah ne yayi sukayi salla suka kara godema Allah.


Da marece MalikusSaif d Saifulislam, Huzaifa da Sarki Muhammad ne sukayima dajin gamki dirar mikiya suna shiga cikin dajin akayo wurgi dadu woje da sun taho zasu shiga cikin dajin sai a sake wurgi dasu, Saifulislam ne yasa Huzaifa miko mashi ruwa a cikin silka, yafara karatun alqur'ani mai girma suratul fatiha, ikilas, falaq da nasi ya karan ta ya tofa cikin ruwan sai ayatul qursiyu da ayoyin kunfayakuni, ya tofa cikin ruwan ya dibo a hannun shi ya watsa a cikin dajin har sau ukku baki ɗaya dajin gamki aka hau kuwa da ihu ga wani irin girgiza da itacen dajin keyi saida jijjigar da karar ta kai tsawon minti talatin sannan ta lafa haka suka shiga cikin dajin gamki har wajen tsafin boka Sarrilƙus, suka iske wani katan abu shiba mutun ba kuma ba aljani ba fuskar mutun hannun kadangare, kafar mage sannan yanada katan bindi da wani uban karci karci a jikin shi yana ganin su ya taso masu haikan tamkar zai kashe su, cikin gafin nama MalikusSaif ya ɗaga takobin Barri ya tsashi biyu, ihu ya kwala ya juye ya koma kafcecen maciji, ruwan addu'a Saifulislam ya watsama shi, take ya dinga burgima yana surutai marassa kan gado yace.

"Sainayi ajalinku kun halaka mu kun kashe mana shugaba yanzun so kuke ku kashe mana dodom tsafi....
Sauke kanshi MalikusSaif yayi, take ya mutu, bisa duten kuka suka hau wani abune zaune bisa kujera kamar kare, kuma shiba dilaba, yana ganin Sarki Muhammad ya diro bisa kujerar zai cakume shi yaja da baya.

Dariya ya kece da ita harsaida runfar da suke ciki ta kwashe a hargitse yace.

"Kaci amanar mu Baidulƙais baka gaji mahaifin ka Gursu ba, dakai za'a hada kai akawo karshen Sarrilƙus da dajin Gamki saidai kada manta mun maka halacci."

Wani bakin cikine ke tokare Sarki Muhammad idan suka kirashi da Baidulƙais wata uwar tsawa ya banka mashi yace.

"Idan bakin ka ya kara kirana da Baidulƙais saina datse shi Allah yakareni da zama daku kuma kaima yau kwanan ka sun kare Mesuzu kaida da duk wani kayan tsafi ku."

Sake tasowa yayi zai rike Sarki Muhammad, cikin gafin nama,
Saifulislam ya watsa mashi ayoyin Allah kurmus wuta taka mashi da bukkar tsafin su baki ɗaya komai ya kone kurmus.

Wani irin haske ne ya bayyana cikin dajin Gamki sabanin duhu, koraye tsanwaye shar sukayi linkif gwanin ban shi'awa ainahin dajin Gamki ya dawo kamar da duk matsafan cikin shi da suka hana mutane sakat, yanzun Allah yakawo karshen su cikin ikon shi da kudurar shi murna wajen su Sarki Muhammad ba'acewa komai baki ɗayan su suka koma cikin Masarautar Raifasu.


Bayan kwana biyu su MalikusSaif ne suka fara shirin komawa Masarautar su, zuwa yanzun ba karamin shakuwa ta shiga tsakanin su da Sarki Muhammad ba, ga tsarin Masarautar Raifasu ya burge MalikusSaif matuka komai sunayin shi cikin tsari yanda yakama ta, komai nasu yana tafiya akan shariar musulunci, hakan kuwa ya kara burge MalikusSaif sosai.


Kowa ya shirya Jarumai da sauran mutanen Daborah duk sun saman dawakan su.



Bankwana sukayi da Sarki Muhammad sannan suka tafi cikin farin ciki a zukatan su.


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Comment
And
Vote
❣️Pls



*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 123&124




A Masarautar Daborah kuwa tunda suka dawo akaita murna dajin dadi ganin yanda sukayi nasara akan kafurai, godiya sukaima Allah SWT daya kawo masu karshen Sarrilƙus.


Haka rayuwa ta kasance cikin aminci da kwanciyar hankali, komai yana tafiya yanda yakama ta, ta bangaren Bahijja da MalikusSaif kuwa sunata shan soyayyar su, zuwa yanzun kuwa cikin Bahijja ya shiga wata takwas bakaramin kulawa cikin ke samuba daga wajen MalikusSaif da iyeyen shi, hakama Binta tana kulawa da yarta yand ya kamata.

A wajen gimbiya Zahara'u da Yazid zuwa yanzun sunsasan ta kansu, shima Huzaifa Hafsat yar Sarki Abu-Jalal zai aura har anmasu baiko na wata biyu.

Bayan sati ɗaya, Sarki MalikusSaif ne zaune a fa'da anata fadanci, saiga sarkin gida da ɗan aiken Sarki Abu-Jalal har gaban MalikusSaif aka kawo shi, ya bashi takarda ansa yayi yaga na amincewa akan murabus dazaima ɗanshi Yarima Dawud.

Murmushi MalikusSaif yayi ya gama karantawa sannan yasa hannu da hatimin Masarautar Daborah.


Haka ya mikama shi shaidar amincewa, haka ya bi Masarautun ɗaya bayan ɗaya kuma sukayi sa'a duk sun amince.

Bayan sallar la'asar Sarki MalikusSaif ne tareda gimbiyar shi a cikin lambu suna shakatawa cikin tsantsar farin ciki ga son duniya ya dauka ya kwallafawa cikin Bahijja wanda yake wata takwas cur yayi girma ba laifi duk da kasancewar shi cikin budurwa.

Suna cikin firarsu ta masoya Bahijja ta kalli fuskar Ya Malik dinta tace.


"Habibi kaga yanda ka kara kyau kuwa?"

Murmushi yai har saida gefen bakin shi ya lotsa yace.

"Uhmmm Hayati kina bani kayan dadi dole inyi kyau nida baby na."

Itama murmushin tayi tace.

"Ayyah Ya Malik banbanci zaka nuna min ni bandani."

Ta ida maganar a shagwaɓe.

Lakatar mata hanci yayi yace.

"Ai munfiki shandadi, jibi zamuje runu nida su Abba."

Marairaicewa tayi tace

"Mizakayi haba Habibi bansan kanamin nisa fa!

Shafa gashin kanta yayi yace.
"Inasan inga Abi dina sannan zaai nadin Yarima Dawud ne."

"Uhmmm zanje wajen Baffa nima."

Kallan wautar ta yakeyi cikin basar da zancen yace.

"Niko wane suna kikesan musama baby dinmu?"
Kwantar dakanta tayi saman cinyar shi tana wasa kwantaccen sajen fuskar shi tace.

"Wayo kakeson kaimin nidai zanbika wajen Abba dan Allah Habibi."

Dafe goshin shi yayi yace.

"Naji baki bani amsa ba gimbiya ta."
Cikeda shagwaba tace.
"Sunan Ummu za'a samata."

"Shi kikeso a saka?"
Sake juyawa tayi tana facing face dinshi sannan tace.

"Uhmmm yaimani Habibi."
Shafa cikin nata yakeyi cikin so d kauna yace.

"Shikenan Allah yasa ki haifaman yan biyu."

Dasauri Bahijja ta waro manyan idanun ta cikin shock tace.

"Kanasan in mutu kenan ina ni ina haifar....

Hade bakin su dayayi dana junane yasa bata ida maganar da tainiyar yiba.

Wani irin hot kiss yake mata mai kashe jiki da zuciya cikin kankanin lokaci jikinta yai sanyi saida yai mai isarshi cikin kasalalliyar muryar shi da bata fita sosai yace.

"Hayati zaki iya kidaina fadar mutuwa kinji tawan zaki haifu lfy."

"Uhmmm duk kasamin gajiya bacci nikeji."

"Oh rigima wato gajiya nasaka maki kenan ko?"

"Ya Malik nidai...sai kuma tafasa ida maganar ta.

Shiko da idanu yabita yanda take shagwaba tana cinno dan karamin bakin ta mai tafiya da imanin shi yace

"Bakiji dani yanzun ko kanwar Malik?"

Yanda yai maganar saida kirjin Bahijja ya buga, saboda da wata irin narkakkiyar murya yai mata maganar.

A kasalance tace
"Aaa Ya Malik karkace haka."

"Tom kanwar Malik naji yanzun fadamin inake maki ciwo?"

Sake cinno bakin tayi wanda tasaba duk sadda zatayi mashi magana a shagwabe take yinta, tace.

"Bako'ina kawai inajin bacci."

Shiko kamar karamin yaro haka yaita riritata, har marece yayi ganin shidda takusa yasa ya dauki gimbiyar tashi suka shiga cikin side dinshi kai tsaye bedroom dinshi ya wuce da ita ya kwantar da ita bisa gadon shi daya gaji da haduwa, itako sai rufe ido takeyi saboda wani irin bacci dake dawainiya d ita.

Rankwafowa yayi bisan ta saidai bai saki nauyin shi akanta ba yace.

"Hayati tashi kiyi wanka kinji."
"Uhmmm."
A hankali yafara buso mata iskar bakin shi mai dan karan sanyi da dadi, ganin tana kara narke mashi yasa shi ɗaukatar ya shiga da ita bathroom.

Rage mata kayan jikinta ya fara jin yana kokarin zame mata underwires yasata saurin bude idon ta, ta rike hannun shi, a kasalance tace.

"Ya Malik dan Allah bacci kabarni"
"Kai kanwar Malik baccin ki yai yawa gaskia kibari kiyi wanka."

Zatayi musu suka hada ido, wni irin kwarjini yai mata dan dole ta kyale shi, da haka sukayi wankan su cikin so da kauna har suka gama, ya daukota zuwa bedroom ya shiryata, ya samata kaya marassa nauyi, nan suka kwanta, badan yanajin bacci ba.

Haka yaita rirritata har bacci barawo ya saceta wannan kenan.



A wajen Sarauniya Zulaiƙa kuwa zaune take a falon Saifulislam suna magana akan cikin Bahijja da yanda yai girma.


"Wlh kullin da tausayin yarinyar nan nike kwana a cikin zuciya ta, fatana Allah ya sauketa lfy."

Cewar Saifulislam.

Numfasawa Sarauniya Zulaiƙa tayi tace.

"Gaskia kam shiyasa nasa Jakadiya tafara hada kayan magani tana bata insha Allah zata samu saukin nakuda."

"Allah yasa."
"Ameen ya rabbil alameen."

Dan shiru ne ya biyo baya kowa da abinda yake nazari.

"Amman idab haihuwar tazo amaida wajen iyayen ta dan ta samu kulawa."

"Haba AbuMalik yanzun har sai anmaida Bahijja gida gani ga Hajara, kum ga hadimai zata samu kulawa."

"Kwarai Ummu Malik nasani kawai inasan a gatan ta tane, sannan a kimanta iyayen ta ai zasuji dadi, suka a darajasu badan mungazaba."

Shiru tayi badan taso ba, saidan bata iya musu dashi.

Ganin batace komai ba yasa yai shiru yace.

"Wai nikam Abdulmalik shiru ya rabu da shigowa."

"Aikuwa tun shekaranjiya inaga aikine yai mashi yawa, ga maganar zuwa Runo wajen nadin Yarima Dawud."

Murmushin manya Saifulislam yayi yace.
"Ai Abdulmalik bazaije ba."

"Saboda mi kasan Baffana bazaiji dadi ba."

"Nasani, ya zauna ya kula da matar shi da kyau zaifi, nida Matawalle sai mu wakilce shi."

"Amman mizai hana ni inkula da ita ku saikuje Baffa zaini zafin hakan."

"Shikenan kema ya kamata kije rabonki da Masarautar Runo tub yaushe?"

Murmushi tayi cikedajin dadi tace." wlh namanta anjima."

"Kishirya sai muje dake."

Wani irin dadine ya lullube Sarauniya Zulaiƙa batayi zatan zai amince taje Runo ba.

Mikewa Saifulislam yayi yace.

"Ita kuma Bahijja sai takoma wajen Umman ta kafin mudawo, tunda kin dage sai Abdulmalik yaje."

"Ayyah Abu Malik kayi hakuri."
"To Sarauniya ta nayi kitashi lokacin sallah yayi."

Atare suka fita shi ya nufi masallaci ita kuma ta wuce side dinta.
Haka rayuwa ta kasance komai na Masarautar Daborah yana tafiya cikin aminci da kwanciyar hankali.


Masarautar Waisu kuwa Sarki Haishir ne keta kai kawo yarasa yanda zaiyi da rayuwar shi, abubuwa sun runcabe mashi ga yarasa mahaifin shi, ga Sarrilƙus ya yaudare shi, ashe daman addinin su na bautama Gurfanai duk karyane tunda ya kasa tsinana masu komai a lokacin da suke bukatar kulawar shi, lallai ya tabbata addinin da Sarki Baidulƙais ya koma shine addinin gaskia.

Wasu kwalla masu zafi sukayi nasarar wanke fuskar Sarki Haishir.

A firgice ya kalli wazirin shi yace.

"Yazama dole mubarranta da wannan lalataccen addinin na kaka da kakanni banga tsiyar daya tsinana mana ba sai tozarci da kaskanci dole duk wanda ke kalkashin ikona yabi addinin musulunci ko kuma duk wanda yaki yimin biyayya saidai yabar mani Masarauta ta!"

Wani irin firgici yakama mutanen fa'da jin abinda Sarkin su ke fada.

Cikin bacin rai waziri yace.
"Zamuyi maka biyayya amman bazamu taɓa aje wannan addinin namu ba na gado."

Wata irin tsawa Sarki Haishir ya watsa mashi yace

"Kayi karya Juru tilas kuyimani biyayya ko kumar kaida zuriyar ka kubar mani Masarauta ta."
Cikin kankanin lokaci rikici ya barke a cikin fa'da wasu na bayan Sarki Haishir wasu kuma na bayan Waziri Juru saidai wadan da ke bayan Waziri Juru sunfi yawa, acewar su basu barin addinin su na kaka da kakanni.

Cikin tsananin fushi Sarki Haishir y zare dallelen takobin shi ya daga murya yace.

"Narantse da girman addinin dana gasgata a yau dinnan duk wanda yai jayayya da umurnina sainayi ajalin shi ko kuea yabar mjn Masarauta ta"

"Karya kake Haishir yanda kake takamar Masarautar Waisu, takace haka muma muke takama, na rantse da Gurfanai da girman rawanin kakana Mudwu saidai kayi ajalina ni Waziri Juru da duk wani mabiyina bamu barin addinin mu na gado."

Yana gama fadan haka yasa kai shida mabiyan shi sukabar fa'dar rai bace.

Wani irin shu'umin murmushi Sarki Haishir yayi wanda shi kadai yasan ma'anar shi.


Bayan kwana biyu a Masarautar Raifasu
Wajene tamkam da dan Adam abin ba'acewa komai saidai da alama wani muhimman abune ake gabatarwa.

Sarki Muhammad ne cikin shiga ta alfarma bakinshi yaki rufuwa ga yan fadanan kama dasu Dagaci, Galadima, Matawalle, Shamaki, Ciroma da dai sauran su, anata yima Sarki Muhammad murna, shiko cikin farin ciki yace.

"Nagode Allah yasaka da alkhairi yakara daukaka wannan

Please Login or Register in order to submit comment