Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka gaisa sannan yace. "Matawallen Daborah barka da dawowa gida ina fatan dai zakai kwana biyu ko kuma ka zauna kahuta haka nan." fuskar shi ɗauke da murmushi yace. "Hakane Abokina nadawo gida kenan na saka wakillai zasuci gaba dayin kasuwancin." kallan kanwar tashi yayi cikin so da kauna yace. "Ina nan da dan nawa munazan tawa akan maganar aure." cikin jin dadi Sarauniya Zulaiƙa tace. "Yaya kenan kamar kasan wannan abun dashi nike kwana nike tashi araina, dafatan kadawo gida lfy ya hanya.?" "Alhmdullh nasameku lfy." da lfy lau suka amsa
Kallan Saifulislam yayi yace.
"Kangiwan Daborah Saifulislam Sarkin adalci Kadimulislam kaji abinda nike bukata awajen ɗan nawa shine aure ko kaima shi zaɓi ne.?"
Rausayar da kanshi Saifulislam yayi yace. "Banda wani zaɓi da zanma Malik ya kamata ya zaɓa da kanshi daga cikin dangi ko cikin gari kamar kowa hakan zai tabbatar da gata da kauna da muke nunawa ɗan namu saidai inkai mashi zaɓi falillahil hamdu." ya gama maganar yana nazartar halin da ɗan nashi yake ciki, shima Matawallen kallan Malik din yayi yace.
"Kai nike sauraro Malik kace kana da zabin da kayi wacece.?"
jiyayi gaban shi ya buga addu'a kawai yakeyi cikin sarkewar murya wanda yana fara magana Saifulislam yasan cewa Malik baida wani zabi da yayi tunda bai taɓa yimashi karya ba, cigabada da cewa yayi. "Allah yataimaki Matawalle ina san a karamin lokaci sannan anan cikin gida zan fidda wadda zan aura a cikin Daborah."
itako Sarauniya Zulaiƙa rantane ya bata kilan ma Zahara'u ce zai fidda a matsayin matar tasa, a zahiri ko cewa tayi. "Katabba ta Malik.?" gyaɗa kai yayi baice komai ba, Matawalle ne yace.
"Shikenan duk d haka nan da sati ya kamata inji daga gareka, in kuma babu da kaina zamuje gidan baffan mu Sarkin Musulcin ka zabi mata." cikin zakuwa da jin dadi Sarauniya tace.
"Kwarai kuwa Yaya kaga kaina ya kulle na manta dacan gaskia da yayi mata."
shima Saifulislam cikin jin dadi ya kalli abokin nashi yace. "Hakan za'ai sai dai abashi lokacin kamar yanda ya bukata." da haka sukaci gaba da firar su ta aminnai kuma abokai sai dai rabi duk akan kasuwanci ne, daga bisani Malik dake jinshi a takure yaima su Huzaifa alamun su tashi su tafi hakan kuwa akayi saidai Matawallene ya tsaida su shiga yai dakin shi ya ɗauko wata katuwar leda da makiman ta yaba Malik babbar sannan yaba su Yazid tasu tsarabar ya mikama Huzaifa yace ya kaima Zahara'u tata sannan ya gaida ta godiya sukayi mashi sannan suka tafi dan Yazid shi ya anshi ta Malik ya rike sukaci gaba ta tafiyar su ba maicewa komai a cikin su.....


tare suka shiga sashen Malik suna shiga suka iske komai a gyare sai kamshin daya gama addabar su na turaruka iri iri dan lumshe idanun shi MalikusSaif yayi sannan ya bude bayan ya zauna kallo yabi falon dashi yasan, Bahijja tazo tai aikin ta na marece, mikama shi ledar shi Yazid yayi cikin gayya yace. "Kadaiji abinda Matawalle yace mutun sai ya bada himma."
wani matsiyacin kallo ya aikama Yazid saida yasa Huzaifa ya haɗe nashi zancen, tashi yayi baice masu komai ba ya faɗa daki bathroom kawai ya faɗa yafara wanka yana fidda huci mai zafin gaske bin toilet din yai da ido yayi ganin komai a gyare tsab, cikin ranshi ko yana yaba kalar tsabta ta Bahijja gata karama amman akwai tsabta, samun kanshi yayi da murmusawa wanda tunda sukaje wajen Matawalle baiyi murmushi ba saima son ɓata mashi rai da suke sonyi amman yana tunawa da Bahijja sai yaji sauki aranshi yana fitowa yafara yima kanshi tambayoyi saidai bamai bashi amsoshin tambayar shi cewa yake, wai miyasa nike yawan tunawa da Bahijja? Miyasa nike tausanta? Miyasa intana tare dani nike kasancewa cikin nishaɗi?....ire iren waɗan nan tambayoyin ya dinga jefoma kanshi su amman ba mai bashi ansar su...


_koni Jameey nima rasa amsar da zan bawa Yarima Malik nayi, sai naji Ƴan Bayima 'Ya'yane fans 1,2,3&Bayima 'Ya'yane Comment Groups sunce son Bahijja kakeyi lol😂_


Da haka ya gama kimtsawa ya koma falo ya zauna, duba table yayi yaga anjere abinci gwanin birgewa girgiza kanshi yayi a zahiri yace. "Wannan shike nuna Bahijja ba zata kuma dawowa yau ba sai gobe kenan? Amman miyasa zatayi hakan, bata iya jirana take nufi komai.?" shiru yayi ya jinjinar da kanshi bisa kushin da yake zaune yana mai rufe idan shi kamar mai bacci saidai ba bacci yakeyi ba....


A wajen Bahijja kuwa tana gama wankan ta ta koma saman tabarma ta zauna ta ɗakko ledar da Ya Malik din ta yaba ta tana budewa ta zaro idanu waje ganin wasu Yan kunne masu masifar kyau da sheki zarosu tayi tana murmushi, ajewa tayi ta kuma ɗauko wata ledar ta daban tana budewa taga gasassun kaji guda biyu wani irin kut taji yawun ta sun tsinke da sauri tace. "Allah Sarki Ya Malik amintacce mai tausayi harda nama, ga yan kunne saidai inaga ana sawa niko banda....jitayi Umman ta da Abban ta sun shigo cikin gajiya sannu da zuwa taimasu cikin rawar jiki ta nuna masu abinda Yarima ya bata, girgiza kai Abdulmajid yayi cikin gajiya yace. "Ƴata Bahijja kibi a sannu karki yarda kisaka wani abu aranki game da Yarima Malik duniya kowa ya shaida Malik mutun ne mai tausayi da imani saidai kisani kallan kanwa yake miki kuma yana tausanki ƴata kema kici gaba dayi mashi wannan kallan na yayan ki wanda kuke tamkar ciki ɗaya bansan kisa wani abu aranki kamar dangantakar zuci ban san in ganki cikin matsala arayuwa ta Bahijja." itama Binta jitayi jikin ta yai sanyi cikin tausayin ƴar tasu tace. "Hakane kuwa Abban Bahijja." itako Bahijja bata gane manufar mahaifin nata ba tace. "Toh Abba na daman Ya Malik yaya nane, kuma uban gidana ne." ganin kuruciya d taima yar tasu yawa yace. "Shikenan ƴata." aranshi ko cewa yayi da sannu zaki san minike nufi ƴata, ɗaukar ƴan kunnayen tayi ta sakala a kunnen ta,shi kanshi Abdulmajid saida yace masha Allah a zahiri ganin ƴar tashi tayi kyau iya kyau mikoma Umman ta naman tayi cewa tayi "ƴata kici mana." sunkuyar da kanta tayi tace. "Umma Ya Malik yabani abinci naci tuncan sashen shi banjin yunwa kuci." addua Binta taci gaba dayima Yarima Malik tace. "Allah yasaka maka da alkhairy Malik yabamu ikon sakanta maka da abinda kakema Bahijja na alkhairi ya haɗaka da mata tagari mai addini da sanin yakamata." da amin suka amsa sannan ta kasa musu kowa yaci suka koshi rabon da suci nama basu san iyakar shekaru ba......


Washe gari tunda safe Bahijja tagama shirin ta, ɗaukar madubin hannu tayi tana mai kallan kanta ganin yanda yan kunnen ta keta walauniya suna sheki wani irin dadi taji tana smile ta kalli Umman ta tace.
"Umma nayi kyau ko.?"
ji sukayi ance aidaman ke kyakkyawa ce ƴata baki ɗayan su suka juya suna kallan kofar shigowa makimancin gidan nasu Mairo ce tashigo fuskar ta ɗauke da fara'a da gudu Bahijja ta faɗa saman ta tana jindadi tace "Innah barka sa safia." "yawwa, ƴata dole zaki tambayi Yayata ko kinyi kyau kinsan dai ba faɗa maki zatayi ba, amman ke kyakkyawace waya baki wannan yan kunnen.?"
murmushi tayi sannan tace. "Ya Malik ne ya bani." shafa gefen fuskar tayi tace. "Aiko sun miki kyau Allah ya saka mashi da alkhairy." "ameen." cewar Binta, da haka suka fita tare kowa ya kama hanyar tafiya wajen aikin shi, kamar kullun yauma Bahijja saida taje sashen Sarauniya Zulaiƙa, ta iske wawan Sarki wanda Sarauniya tasa kullin saiya shidema Bahijja bulala goma da safe hakama sa yamma inta tashi, a gaban Binta ake dukan Bahijja saidai bata d tacewa garin bugun tane tasa hannu tana karewa ya dukan mata yatsa wani irin razanannar kara ta saki, har saida ya gama dukan ta sannan ta tafi wajen aikin ta kamar yanda ta saba, bakaramin radadin hannun ta takeji ba ga wani irin zugi da yake mata hawaye tai tayi tana kukan zuci, haka ta shigo cikin sashen Yarima Malik, itako tana shigowa falan taga ba kowa samun wani wuri tayi ta buga uban tagumi tacika ga da rurun ta san ranta dan abinda akai mata yaɓata mata zuciya, a wajen Malik kuwa zama yai gefen gado tunda yai sallah yagama karatun alqur'ani mai girma yake lazima, a hankali ya dinga jin sautin kuka, kamar yana karuwa kuma yasan kaf Masarautar Daborah ba bawan da yake shigowa sashen shi daga Jakadiya sai Bahijja da Ashir sai wata baiwa Zainura itama abunci take kawowa zuwan Bahijja ma tadaina saidai takan taya ta kawo mashi abinci, jin shashshekar kukan tai yawa hakan yasa shi fitowa yana bin inda yake jin sautin na tashi, a hankali yake tafiya har ya iso tamfatsetsen falon da take zaune bama tasan ya shigo ba, jin kamshin da ya daki hancin ta yasa tagane isowar MalikusSaif a hankali ta ɗago rinanun idanun ta da suka dishe dan kuka, tana ganin shi ta duka ta gaida shi, bai amsa ba sai ya zauna saman kujera cikin kulawa yace. "Bahijja kuka da safe har haka lfy.?" a kiɗime tace. "Bakomai na taho ne na faɗi shine na buge hannu na yake min zugi da zafi." yanda takarasa maganar irin ta yara idan anduke su suna maida bayani haka ta gama maganar tanaci gaba da kukan ta kasa kasa, wanda yake kuna ran Yarima Malik fiye da zato ko tunanin mai tunani rufe idan shi yayi sannan ya sake budewa cikin sigar lallashi yace.
"Bana faɗa maki ba ki daina guje guje ba, kinfara girma fa Bahijja akalla kin shiga shekara sha biyar kin zama babba daga yau kidaina wasan nin yara kinaji na." a hankali ta ɗaga kanta alamar toh, cikin tausayawa yace. "yanzun ki zauna ku huta kada kiyi aiki kinga hannun ki na ciwo, kijira in lokacin cin abinci na yayi kije ki ƙarɓo yau shine aikin ki." "toh Ya Malik, amman ko gadone zan iya gyara maka."
da yace aa tabar shi sai ya tuna ba agyare yake ba, kuma inta gyara mashi yanajin dadi, mikewa yayi yace. "ɗauko ledar nan kishigo ciki ki gyara." tashi tayi ta ɗauka tabi bayan shi har cikin dakin ta bashi yace ta aje bisa kujerar dakin, zama yayi kan kujera yana kallan ta itako cigaba tayi da gyara mashi tafkeken gadon shi, harta kammala, shiga tayi bathroom ta haɗa mashi ruwan wanka, aranshi ko cewa yayi lallai Bahijja kinfara hankali ashe, kinsan abinda ya dace keyi basai ansa kaki ba, tana gama haɗa mashi ta duka tace. "Ranka shidade angama kashiga wankan." samun kanshi yayi da murmusawa sannan ya mike ya shiga ita kuma ta fita zuwa madafa, wajen hada mashi abinci kamar yanda ta saba, aiko ba bata lokaci sungama hada komai ta gama jera komai, sannan ta tsaya jiran shi yana gama shirya zaman shi yayi cikin dakin jin shirun yai yawa yasa ta yin sallama, amsa mata yayi tana shiga ta duka tace Ya Malik abinci ya kammala, cikin kulawa yace, ta zubo mashi wanda zai iya ci takawo mashi, haka kuwa akayi, har daki ta kawo mashi saukowa yayi kasa, ita kuma ta koma gefe kallan ta yayi yace. "Mikomin wannan ledar ta kusa dake." a hankali ta tashi ta mika mashi karɓa yayi yafara fiddo kayan ciki ya sake kallan ta yace....




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم





Episode 55&56




"An shi wannan bagaruwar da zamzam kije kici." sunkuyar da kanta tayi kasa, sannan tace. "Ranka shidade, nagode amman kabar...katseta yayi da cewa. "Idan nayi kyauta ba'acewa aa ki karɓa ni nabaki." ansa Bahijja tayi tace. "Allah yasa ka maka da alkhairy ya tsareka daga sharrin makiyan ka." samun kanshi yayi da ɗan murmusawa har gefen bakin shi yaɗan lotsa, a hankali ya ɗaga labben sa yace. "Ameen." tashi yayi ya fita falo wani corridor yabi ya shiga cikin tafkeken lambun sashen shi yana shakatawa ita kuma Bahijja madafa ta shiga dan haɗo kayan abinci


➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿


_Masarautar Waisu_


Yau jama'ar Sarki Haishir suka kama hanyar tahowa kasar Daborah dan cin kasuwa, Kasuwar *ZURSU* kasuwace da ta shara a cikin kasar Gambia musamman ake ware ranaku ukku take ci a jere cikin shekara cine takeyi wanda kasashe daban daban na faɗin duniya suke cinta musamman makwab ta irin su Cameron, Chadi, Togo, Mali, Nigeria, Niger, harma da yankin labarawa irin su Sudan Morocco dadai sauran su, shiyasa duk lokacin cin wnnan kasuwa ta kama yan Masarautar Daborah basuda zama sukan watsa mutanen su sassa daban daban na kasuwar dan bada kulawa da shige da ficcen kasuwar gudun kada akawo masu wani hari a shammace su, wannan kenan


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Suko yan Masarautar Waisu haka sukayi ta tafiya mai nisan zango dan cimma kasuwar ta Zursu kasan cewa tana)) da nisa sosai a tsakanin su...

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

_Masarautar Raifasu_


Sarki Baidulƙais ya cun kushe rai yarasa yanda zaiyi da rayuwar shi ga Sarrilƙus ya hade mashi kai kullin da kalar barazanar da yake gani, gashi matar shi gimbiya Yazira tafara hade mashi kai dantaga yanzun tsakanin shi da miskini banbancin kadan ne dan dai shi yana da Sarauta Jakadiya ce kadai ke bashi kulawa ta musamman dan da yawan 'yan Masarautar ma sunfara guduwa acewar su, kada Sarrilƙus yazo ya darkake su basu jiba basu gani ba, a wajen Jakadiya Jamra kuwa zaune take a sashen ta da alama sallah zata gabatar, tana tashi tafara sallar ta cikin nutsuwa da aminci wata baiwa ce ta afko cikin dakin, ta iske Jakadiya na salla itako bata sallame ba, har saida tagama ibadar ta sannan tayi addu'a ta shafa, sadda zata waigo wannan baiwar harta gudu, girgiza kai Jamra tayi tace. "Lallai yau dubuna ta cika, saidai banda wani zaɓi kuma duk abinda da zai faru saidai ya faru ba wanda ya isa ya hanani addini na naga falalar sa a jikin 'yata Bahijja, itako Labuda har cikin sashen Sarki Baidulƙais akai mata iso, tana zuwa ta iske shi zaune yayi jugum da alama yana cikin mawuyacin hali, zubewa tayi takai gaisuwa ba tareda ya amsa ba ya kalleta cikeda da tuhuma, sake rankwafar da kanta tayi tace.
"Ranka shidade gurfanai yataimake ka yau idanuna sunyi mugun gani." sake watsa mata wani firgitaccen kallo yayi a karo na biyu yace. "Yi maganarki baiwa." nagode shugaba na, yau Labuda taga Jakadiyar ka mafi aminci agareka tana wani addini dagani wannan shahararren addinin ne wanda babbr Masarautar nahiyr mu sukeyi shi naga Jamra nayi tuba nike ranka shidade."
mikewa yayi yaje ya dawo yaje ya dawo sake kallan ta yayi yace. "Kin tabbatar da abinda kika gaya mani.?"
"kwarai kuwa ban isa inkirki abinda ba gaskia bane ga Jakadiyar ka ranka shidade."cewa yayi tasa Sarkin gida ya kira mashi Sarkin horo, yaje ya taho mashi da Jamra, har tuntube Labuda keyi ta tafi da gudu dan isar da sakon Sarki Baidulƙais......

*********************************

A wajen Sarauniya Zulaiƙa kuwa zaune take ita da gimbiya Salsabila, suna magana gimbiya Salsabila ce tace. "Ranki shidade uwar marayu kinji babban al'amarin da nazo maki dashi?"
ba yabo ba fallasa Sarauniya Zulaiƙa tace, minene wannan albishir din Umman Huzaifa.?" cikin jindadi tace. "Zahara'u tana son Yarima Malik." wani irin kayataccen murmushi Sarauniya Zulaiƙa tayi tace.
"Wannan ai labarine mai dadin gaske haka nikeso daman kwananan kawun shi Matawalle yace ya fidda mata nan da mako ɗaya, raina na bani tabbas Zahara'u zai fidda mujira makon ya kammala muji zabin da Yariman zaiyi koya kika gani.?"
itama murmushin tayi tace. "Kwarai kuwa shuga bata hakan za'ayi shine mafita, Allah yaimana jagoranci." "Ameen ya rabbi." haka sukaci gaba da firar su cikin jin dadi da aminci.

Shiko MalikusSaif koda ya gama hutawar shi cikin lambun shi, fitowa yayi ya shigo cikin sashen nashi, ba inda ya zauna sai saman luntsuma luntsuman kujerun shi da suka gaji da tsaruwa ya ɗaura kafa ɗaya bisa can kuma ya kwantar da kanshi bisa kan kujerar ya dan rufe idanun shi, kamar mai bacci, itako Bahijja ɗauke take da tiren abinci har ta iso cikin falon baisan ta isoba, ajewa tayi gaban shi takoma gefe ta zuba mashi idanun ta tana ganin tsananin kyawun Yarima Malik tana ayyanawa aranta, shiko Malik jiyayi kamar ana kallan shi yaji jikin shi ya bashi a hankali yadan bude idan shi guda ba tareda ta gani ba, ga mamakin shi Bahijja ce keta aikin kallan shi, shima kallan ta yayi yaga sai smile takeyi tana kara zuba mashi firgitatun idanun shi, jiyayi zuciyar shi ta tsinke wani abu ya dirar mashi a zuciya, baisan sadda ya bude idanun nashi ba ya daura su kanta itako da sauri taja da baya tana rufe fuskar ta ɗan hade rai yayi ya murtuke fuska yace
"shine zakimin tsaye kamar wata bakuwa, tun yaushe kike nan wajen.?" kame kame tafara cikin siririyar muryar ta tace. "Na ɗan jima naga kana baccine shiyasa." adakile yace. "Ai ba baccin nike ba." jitayi gaban ta ya fadi, aranta ko cewa tayi kenan yaga inata kallan shi na bani." jitayi yace. "Dame kika bani?" rufe bakin ta tayi tace. "Bakomai." a kunyace ta ɗauki flat tafara zuba mashi abinci, cikin nutsuwa ta miko mashi, girgiza kanshi yayi yace. "Kici ba yanzun zanci ba." da sauri ta girgiza kai tace. "Ya Malik karufaman asiri taya zanci abinci da flat dinka." baice komai ba saima sake hade rai da yayi, shikan shi yarasa dalilin dayasa yake kyauta tawa Bahijja fiye da kima, kuma bai iya cin abinci matukar baiga taciga ba, idan tana cikin damuwa yakan rasa sukuni a cikin zuciyar shi, ɗaga rinanun idanun shi yayi yace.
"Maza ki cinye shi tas." sake kwantar da kanshi yayi ya rufe idanun shi, ita kuwa sunkuyar dakan ta tayi tafara cin abincin ta rufe idanin ta dan dadi, shi kuwa ta kasan ido yake kallan ta yana jin dadi ganin Bahijja na cikin aminci yana smile a hankali, ji sukayi ance.

"Ke minake gani haka?" a firgice Bahijja ta ture flat din abincin gaban ta, jitayi baki ɗaya numfashin ta ya dauke na wucin gadi, shiko Malik tashi yayi yaje wajen Mahaifiyar tashi ranta ɓace ita da gimbiya Salsabila cikin dakewa yace.
"Ummu sannun ku da zuwa." wani banzan kallo ta aika mashi ta maida kallan ta ga Bahijja tace. "Ke baiwa waya baki ikon zama haka kina cin abincin Yarima?" komai ya gama kwancema MalikusSaif cikin ranshi ko cewa yayi, wai miyasa masu mulki suke kyamar bayi dan baiwa taci abinci na ni ba ɗan Adam bane?
Maganar da Sarauniya Zulaiƙa ta kara jeroma Bahijja itace ta katse mashi tunani cewa tayi. "Ta yani gani waya baki ikon saka 'yan kunnen *Barri*!?
ta ida maganar tana fiddo idanuwa waje ga zuciyar Sarauniya Zulaiƙa dake halbawa da sauri da sauri.
Hannun ta Bahijja tasa ta shafi kunnen ta, murya na rawa tace.
"Tuba nike ya shugaba ta kimin aikin rai na tuba." a kufule ta datsa mata mummunan mari tayi har saida ta saki ihun azaba, da sauri MalikusSaif ya taho gun Bahijja Sarauniya Zulaiƙa ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu, kama kunnen tayi tafara jan shi da karfi aiko Bahijja tafara kukan azaba, zuwa yayi yace.
"Ummi dan Allah kiganar da Ummu bata da wani laifi nice na bata shi tasaka.
" cikin tsawa Sarauniya Zulaiƙa ta saki kunnen Bahijja ta ingizata baya baya tayi ta buge kanta jikin doguwar filar dake cikin falon, dukawa tayi ta zare 'yan kunnen kunnan ta jikin ta na rawa dan tsoro daya gama dirar mata a cikin zuciya.
juyowa tayi ta kalli MalikusSaif ta nuna shi da yatsan hannun ta manuniya tace.
"Kana da hankali kuwa Yarima, kasan darajar waɗan nan 'yan kunnen na *BARRI* kuwa, angaya maka abanza suke wajen ka?"
"Ummu ai naga ba wani anfani zanyi dasu ba shiyasa na ɗauko su na batasu..."yiman shiru kar insaɓa maka wannan 'yan kunnen da kake gani ya kwashe shekaru aru aru a cikin wannan Masarautar ba mai kasancewa dasu sai Yariman zamanin, idan ya samu wadda yake so, ko wadda keda mahimmanci a wajen shi har yake ganin zai iya auren ta zai bata 'yan kunnen tasaka a kunnan ta, idan iyayen shi ko nata suka gani shikenan ansan Yarima yayi zaben matar da zai aura, sai ai mashi baiko, a mai dasu gidan tarihi wajen ajiyar kayan Barri, shine zaka rasa wadda zakaba waɗan nan 'yan kunnen ta saka sai waccen matsiyaciyar baiwar mai kashin tsiya.!"
da idanu yabi Bahijja wadda ke gefe daya tsugunne hannun ta rike da 'yan kunnen a hannun ta, rike hannun ta Sarauniya yayi yace. "Ummu nifa Bahijja na ɗauke ta matsayin kanwata kuma yar uwa dan naba Bahijja mahimmanci bashi ke nuna ita na zaɓa ba amatsayin...."kada insake jin ka hada Bahijja da jinin ka yar uwar ka! jinin ka kenan fa Yarima itako waccen 'yar gadon bauta ce, yanzun mikake nufi da Bahijja tasaka 'yan kunnen Barri kafin ita ce, wadda ta dace tasaka su a jikin ta?" dafe kanshi yayi yace. "Ummu nafada maki dan Allah kada acutar da ita, ni kaina bawani sanin mahimmancin su nayi ba sosai kawai naga ya dace inma Bahijja kyauta dan tana da darajar a wajena."
sake nuna shi da yatsa tayi tace. "Ni za'aima ɗibar albarka ni zaka wulakanta ma tarihi da nasaba ta tunda aka kirki 'yan kunnen Barri baiwa bata taba rikesu ba bare harta saka su a cikin kunnen ta, ya tabbata har yanzun bakasan waye kai ba kuma minene matsayin kaba.!" Jakadiya ce ta shigo Sarauniya Zulaiƙa ce tace. "Kiraman Sarkin bulala Hajara." da sauri ta tafi, shiko Malik cigaba da bata hakuri yayi hankalin shi yai matukar tashi, itako Bahijja duk ta tsure, gimbiya Salsabila cikin kissa tace.
"ranki shidade kiyi hakuri duk wannan lamarin anyi shine cikin rashin sani." sake ɗagama Salsabila hannu tayi cikin ƙakkausar murya tace. "Bakisan yanda zuciya ta ke kuna ba, da baki saka bakin kiba, na rasa wannan yarinyar mutunce ko aljan, tana shiga cikin lamuran iyali na, akan wannan yarinyar ɗana Malik ya tseratar da ita tun tana jaririyar ta, inama na sallame ta da iyayen ta sunbar min Masarauta ta! akan wannan yarinyar akayi Yaki wai duk saboda baiwa! jifa Ummu Huzaifa, tunda aka kirki tarihin Masarautar Daborah ina kika taɓa ganin anyi Yaki akan BAIWA? Kan wannan yarinyar mai alfarma Kadimul islam da kafafun shi ya shiga cikin turakar bayi yasa aka kwance ta, tunda kike kintaɓa ganin jinin Sarauta ya shiga turakar BAYI!?
saita dalilin wannan tsinanniyar yarinyar, yau gashi anwayi gari akan wannan yarinyar tausayinta ya cika zuciyar ɗana harya dauki abu mai mahimmancin gaske 'yan kunnen BARRI yaba BAIWA tasaka ma kunnen ta! ki auna su da takobin BARRI kiga darajar su, baiwa ta sasu, so kike ince ɗana Yarima MALIK son BAIWA yakeyi kuma itace ya zaɓa a matsayin mata!?"

numfasawa gimbiya Salsabila tayi da takaici ya ishi zuciyar ta babban burin ta shine taga Yarima Malik yaba gimbiya Zahara'u 'yan kunnen Barri ta saka a kunnen ta yau gashi an wayi gari ya bama baiwa ta saka su, amman saita dannen bakin cikin ta tace....



_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



Episode 57&58



"Anyi kuskure kam amman ranki shidade ina Yarima Malik ina baiwa? taya za'ai yace zai auri baiwa, kema aikin san ance kwarya tabi kwarya, kibar wannan zargin kuma kinga ai yace baisan haka abin yake ba."
sauke ajiyar zuciya tayi mai nauyi sannn tace. "Duk da haka dole saina hukunta wannan yarinyar bata sanya 'yan kunnen da Sarauniya Yahanazu ta kirkire su da kanta ba dan tantance ainahin alqiblar da Yariman Masarautar nan ya dosa ba."
jin shigowar Sarkin bulala sukayi zubewa yayi yakai gaisua, sawa tayi Jakadiya ta anshi yan kunnen hannun Bahijja, sannn tace.
"Kaita dukan ta harsai ta daina numfashi.!" aiko kamar jira Sarkin bulala yafara

Please Login or Register in order to submit comment