Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ace munba Sarki Baidulƙais hadin kai akan wannan kudirin nashi na da gargaza karfin iko na Sarauniya Zulaiƙa dan haka inaso nan da kwana ukku kuci gaba da hada gangamin Yaki sannan zamu haɗu da Jaruman Masarautar Raifasu dan yakar Jaruman Masarautar Daborah dan haka inasan kowa ya dag, kunsan dai suwa muke niyar tunkara wannan karon so nike inga kun kawo mani kan Yarima MalikusSaif shine kadai abinda za'ayi ana kasa rayuwar Sarauniya Zulaiƙa." cikeda gamsuwa Sarkin Yaki da Jama'ar shi suka tafi dan fara shirin zuwa Masarautar Daborah......

~Masarautar Waisu~

A wajen Yarima Haishir kuwa cikin kankanin lokaci kamanin shi sun sauya gimbiya Ƙamariyya ce ta tsaya tana ba ɗan nata kulawa ba karamin takaici ne ya kamata ba, danko Sarki Lahazu baida lokacin ɓatawa kullin yana wajen Jaruman shi dan ganin suna karbar horo na musamman wani bima har dashi ake gwajin dan ya ɗauki alwashin saiya kashe Yarima MalikusSaif da Sarauniya Zulaiƙa sune kadai matsalar shi a duniya musamman da yazo ya nakasa mashi rayuwar ɗa ya sauya mashi kamanni, wannan dalilin yasa kullin cikin shiri yake ba dare ba rana abu guda kawai sukeyi a cikin Masarautar Waisu.......

```Masarautar Daborah```


A wajen Sarauniya Zulaiƙa kuwa zaune take tare da Waziri Dammur mahaifin Yarima Huzaifa suna shawarar yanda zasu fiddo da Sarkin Yakin ta duk kunya da dana sani sun addabi rayuwar Sarauniya Zulaiƙa, shima kanshi yarasa mafita, cewa yayi. "Ya kamata mukai masu ziyara sai mu bukaci zaman sulhu ko shawara da Sarkin Yakin shi kadai in yaso daga baya sai a fddo dasu Lurwan inaga hakan zaifi kinga cikin ruwan sanyi mungyara wannan kuskuren ba tareda Sarkin Yaki ya gane komai ba, kinsan halin shi akwai saurin fushi."
kaɗa kai tayi alamun ba damuwa, tashi sukayi sukaje filin da ake ba Jaruman ta kulawa ta musamman dan ba laifi ta hada Jaruman dan dai ba duka ta saka ba sun ɗauki kashi daya a cikin hudu, wannan karon kuwa Yazid ne dan Sarkin fa'da ke bada gwaji na musamman dan aikin su kenan sallah kadai ke ta dasu, danko koda Sarauniya Zulaiƙa taje itama cigaba daba Jaruman ta gwaji tayi haka suka wuni sunayi daga karshe ta wuce sashen ta dan hutawa kafin gobe taje wajen Sarkin Yaki kamar yanda Wazirin ta yabata shawara.


A turakar bayi kuwa Binta ce ke jifgar uban wankin ta dan tajima bata samu lokacin kanta ba bare ta wanke kayan dattin ta ita dana mai gidan ta Abdulmajid haka tayi tagama sannan tai sallah ta samu abin sakama bakin salati taci, sannan ta fita ta cigaba da rabama sauran bayi aikin su, itama tafiya tayi nata aikin kamar yanda tasaba.

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Suko sunci uban gudu har sungode ma Allah har Allah yasa suka bar yankin Masarautar Waisu baki ɗayan ta yanzun sun iso magamar hanya, inda suka hau wadda zata sadasu da Masarautar Daborah wadda tayi gabas kenan wannan karon tafiya suka dinga yi cikin sassarfa itako Bahijja sai murna takeyi zata ga Umman ta da Abban ta, shiko MalikusSaif wani irin farin ciki yakeji yau gashi ya dawo da Bahijja zataci gaba dayi mashi hidima kamar yanda aka alkawalta mashi tun tana ƴar jaririyar ta.


*Nikodai Jameey nace anya MalikusSaif wannan alqawalin baisha karaba? Amman muje zuwa muga yanda zata kaya a cikin Masarautar Daborar......*


Koda masu bibiyar su MalikusSaif suka ga sun ɓace masu bat hakan yasa suka juya dan gayama Sarki Lahazu halin da ake ciki.

A wajen Abdulmajid kuwa yaudai da sauki dan anrage dukan su kasancewr batasu akeba a halin yanzun ta shirin Yaki Masarautar Daborah takeyi tanajiran isowar abokan gabarta a kowane lokaci, a wajen gimbiya Zahara'u kuwa wato kanwar Yarima Huzaifa ƴa ga Wazirin Daborah zaune take a cikin kayataccen dakin ta sai kwalliya takeyi tanasan taje takai ma Sarauniya Zulaiƙa ziyarar ban girma haka baiwar ta ta gama taya ta shiryawa sannan suka tafi sai wannan ɗaukar kai takeyi tanajin ta kamar wata Sarauniya Zulaiƙa baki daya haka taita yauki harta isa sashen Sarauniya Zulaiƙa tana isa ta iske Binta nata aiki, doɗe hancin ta tayi ta watsar da miyau cikin kyama ta raɓa Binta ta wuce wajen Sarauniya Zulaiƙa tana zuwa ta rungume ta sannan suka gaisa cikin so da kauna, cikin kilbibi gimbiya Zahara'u tace.
"Ummu wai har yanzun Yarima na baidawo ba gaskia Ummu dana tuna baiwa yaje ɗaukowa sai naji natsani komai, inashi ina ɗauko baiwa." takarasa maganar a shagwabe itako Sarauniya Zulaiƙa cikin kulewa tace. "Kedai bari Ƴata ni kaina ina da nasanin wannan baiwar da uwarta kin gani ni kadai nasan abinda zan masu idan suka dawo."sake marere cewa tayi tace. "Ummu kafana yaimani tsami inaso adanna mani ita."
wani kallo Sarauniya Zulaiƙa taima Binta ba shiri ta aje aikinta tazo haka gimbiya Zahara'u ta aza kafarta saman cinyar Binta da gayya ita kuma taci gaba da danna mata kafar, suna ci gaba da tsinema Bahijja albarka a gaban ta sai cimasu fuska akeyi amman a haka ta cigaba da danna ma gimbiya Zahara'u kafarta har saida ta ɗauke dan kanta, cikin yanga ta mike sai yaƙuna takeyi tace. "Ummu zan tafi in huta bacci nikeji." cikin so da kauna Sarauniya Zulaiƙa tace. "Kiyi bacci mai dadi ƴar albarka, kikula da kanki kyakkyawar ƴata." haka ta tafi sai yauki takeyi....


Da marece likis gari yai sanyi bakaji komai sai kaɗawar iska wajen yayi kyau yana fidda sanyi ba mai cutar waba Bahijja ce zaune saman wani dutsi a cikin daji gefen ruwa tana jefa dutse a hankali cikin nutsuwa baki daya ta shige duniyar tunanin abubuwan da suka dinga faruwa da ita, tana ta alajabi wai itace zata koma cikin Masarautar su wajen iyayen ta, jibtake kamar tai tsuntsuwa taganta jikin Umman ta, tana cikin tunani taji zazzaƙar muryar MalikusSaif ta daki dodon kunnen ta batasan sadda ta ɗan rufe ido ba sannan ta bude su a hankali ta azasu saman kyakkyawar fuskar shi mai shagaltar da ita daga kallan shi, duk da ba wani murmushi yaiba sai taga yakara mata kyau fiye da zatan ta wata leda ce ya mikama ta yace. "Tunanin mi kikeyi ne haka, ga abinci kici kada yunwa ta kamaki."
yanda yai maganar yasa ta ɗan saki murmushi har saida hakoran ta suka bayyana, shima mayar mata da martani yayi, ya rasa dalilin da yasa farin cikin Bahijja ke saka shi nishadi da jin dadi tun tana ƴar kankanuwar ta, itako mamaki lamarin Ya Malik dinta ke bata, wai kar yunwa takama ni ai tuni aikin gama ya gama Ya Malik tunda na kasance a baiwa saidai in godema Allah, duk da a zuci take maganar ta saidai duk sunji abinda tace, Huzaifa ne ya kalli Malik take yaga tsantsar tausayin Bahijja a cikin kwayar idanun shi, shima ƙada kai yayi alamar tausaya wa , itako cigaba dacin abincin ta tayi har lumshe ido takeyi dan ba kadan takejin dadin shi ba, har ta karasa ta wanke hannun ta, sake mikomata ruwa yayi ta ansa a ranta ko cewa tayi ohni Bahijja kaga inacin abinci dan danan nacinye ba sabanba, Allah dai yasaka maka da alkhairy amintaccen Yarima kaceci rayuwa ta da yanzun bansan a wane hali zan shiga ba, haka tagama shan ruwan ta sannan suka gabatar da sallah, sukaci gaba da tafiyar su, dan gab suke da su karasa cikin Masarautar Daborar tunda suna hange ganuwar garin nesa dasu sosai, haka sukaci gaba da sassarfa da dawakan su kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi.


A cikin taskar bayi kuwa wata baiwa ce ke zaɓo bayi mata, zata kaisu wajen Jakadiyya tana cikin zaɓen su ta ɗauko harda Zainab saida tagama tsintar bayin sannan suka tafi sashen Sarki Baidulƙais suna isa Jakadiyya ta kwashe su sai madafa suka fara aikin abinci dan tarbar baki daga Masarautar Ƙaisu, haka sukai ta shiri kai kace biki za'ayi danko wajen Sarki Baidulƙais ya gama duk wani shirin da zaiyi dan tafiya Masarautar Daborah daman jiran isowar Sarki Danwar yakeyi dan su ida haɗa mayakan su a tuta ɗaya Masarauta ɗaya dan cimma wani buri nasu wanda kowa ya addana shi a cikin zuciyar shi batare da ya sanar ma ɗan uwan shi abinda ke cikin zuciyar shi ba, abinda suka sani suna san su wargaza mulkin Sarauniya Zulaiƙa dama Masarautar Daborah baki ɗayan ta, haka kowa ya gama kimtsawa itama Jamra tana cikin sashen Baidulƙais da bayi angama gyara komai antsara shi da marece aka fara shelar isowar Sarki Danwar da tawagar shi ba karamin dadi bane ya ratsa zuciyar Baidulƙais dan baiyi tunanin zai ansa goron gayyatar shi ba duk da kasancewr suna da kyakkyawar mu'amala da juna, cikin farin ciki Sarki Baidulƙais ya taro Sarki Danwar har cikin sashen shi aka kaishi suka zauna da manyan Jaruman shi da yazo tare dasu cikin kankanin lokaci aka fara gabatar masu da kayan abinci, haka sukai liyafar ban girma sannan aka fidda sauran Jaruman da Sarki Danwar yazo dasu kowa yaci ya sha, aka basu masauki domin su huta kafin a ida basu kulawar da gwajin da ya dace kafin zuwa jibi su ɗauki hanyar tafiya Masarautar Daborah, suko su Sarki Baidulƙais haka sukai ta shawarar yanda zasu shafe babin Sarauniya Zulaiƙa da duk wani abu da take takama dashi......

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Su Bahijja kuwa tafiya tai riba tunda har sun shigo cikin ganuwar garin Daborah yanzun ba inda suka tunkara sai kofar shiga cikin Masarautar Daborar koda Yarima MalikusSaif suka tun karo kofar shiga cikin Masarautar su, take yaji gaban shi ya faɗi ya rasa dalil, kallan Bahijja yayi yaga sai washe baki takeyi tanajin dadi yau ta dawo Masarautar su zata huta da aikin bauta tasan nan zatafi samun yanci tunda Masarautar da aka haifeta ce, shiko tsoron shi kada mahaifiyar shi ta gallazama Bahijja azaba, take ya tuna ranar da aka haifi Bahijja da yanda Sarauniya taso akashe ta tun a ranar tuna irin artabar da suka sha har Allah yasa a kabar Bahijja, ji yayi jikin shi yai sanyi, kallan Huzaifa yayi wanda shima hakan take wajen shi, koda bai gaya maka ba da kagan shi kasan yana cikin fargaba addu'a yafara yi iri iri sannan suka bubbuga kofar Masarautar Daborah, Sarkin kofa ne ya rugo da sauri dan ganin masu buga kofar, yana budewa yaga Yarima Malik ne, take ya tuna da gargadin da Sarauniya Zulaiƙa taima shi da sauri ya maida kofa zai rufe, Yarima Malik ne yasa hannu ya banka ta, da sauri Sarkin kofa ya zube kasa yana neman afuwa, koda Sarkin gida yaga su Yarima Malik da sauri ya koma cikin Masarauta ya sanar ma Sarauniya Zulaiƙa dawowar Yarima Malik, a kiɗime ta mike rai ɓace itada Waziri Dammur suka fito,
itako Binta dake aiki tanajin haka sumar tsaye tayi ko motsin kirki takasa yi , koda Sarauniya Zulaiƙa suka isa bakin kofa idanun ta suka sauka kan Bahijja da Yarima Malik cikin fushi ta nuna su da yatsa tace.




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 27&28



"MalikusSaif maza ka ɓace mani da wannan shegiyar yarinyar a cikin Masarauta ta ko baka da labarin tuni ka zama ɓarrare a cikin Masarautar nan, dan haka ku koma inda kuka fito yanzun.!"
a sanyaye Yarima MalikusSaif ya duro saman doki ya duka kasa agaban Mahaifiyar shi ya kawo hannu, zai rike hannun ta da sauri taja da baya tace.
"Karka kuskara ka taɓa ni Malik na yafe ka na barma Binta." koda Huzaifa yaga ran Sarauniya ya mugun ɓaci da sauri shima ya sauko ya duka kasa suka fara bata hakuri Malik ne yace. "Ummu dan Allah ki yafemani karfa kiman ta, Bahijja ce na ceto da yanzun rayuwar ta yabgama tarwatsewa dan Allah ki fahimceni." itako tagama fusata saidai bata iya cin fuskar Malik gaban fadawan ta cikin fushi tace. "Ke baiwa zaki sauko saman dokin nan ko saina sare kanki yanzun nan.!" ai jikin Bahijja na rawa batasan sadda ta duro ba, itako aranta cewa take na shiga ukku Bahijja wannan wace irin mata ce anya ba ɓatan kai mukayi ba mike shirin faruwa dani ne?
Itama da sauri ta duka a gaban Sarauniya Zulaiƙa, jikinta ya fara ɓari, ta kowa Sarauniya Zulaiƙa tayi tazo gaban Bahijja tana zagaye ta, duk da ta rabu da ganin Bahijja ita kanta tasan yarinyar ta girma ta haɗa duk abinda akeso wata ƴa mace ta kasance dasu, saidai kawai ta tsaneta kuma bata kaunar zuri'ar Jafar har abada, a yamutse da tofa ma Bahijja miyau ajiki, sai a idon Malik, rufe idanshi yayi yasan tabbas rayuwar Bahijja na cikin garari dan dai nan bazata dinga samun kalubale ba wajen yunkurin lalata ba, ba kamar sauran Masarautun ba,bai gama sakar zucin da yake ba yaji wata irin kara ashe Sarauniya Zulaiƙa ce ta wanke Bahijja da mari har huɗu take ta zube kasa abinka ga farar fata har jini ya kwanta da sauri Malik ya iso wajen Bahijja zai ɗaga ta Sarauniya Zulaiƙa ce ta daka mashi tsawa tace. "Ka kuskara hannun ka ya taɓa jikin wannan ƙasƙan tattar Baiwar wlh sai na tsine maka MalikusSaif."
take ya tsaya baisan kwalla sun fara suntiri a saman fuskar shiba, itako Bahijja addu'a kawai takeyi a zuciyar ta, a kiɗime ta tashi daga faduwar da tayi tace. "Tuba nike ya shuga bata Bahijja na tuba kiyafemani, Allah ya huci zuciyarki."
itako maganar da Bahijja taimata sake fusata ta tayi take ta kalli Sarkin horo tace. "Kama mani ita ka kaita cikin turkar bayi yanda uwarta Binta zata gani kaita dukan ta har saita mutu kanaji na."?
Da sauri Yarima Malik ya rike kafar Sarauniya Zulaiƙa yace. "Ummu kiyi hakuri ni ya kamata ki hukun ta ba Bahijja ba bata san komai ba dan Allah kiyafe mata, kada ki ɗaura mata laifi." itako Bahijja bata san tafara kuka ba, tana ba Sarauniya Zulaiƙa hakuri amman a banza a wofi, haka Sarkin horo ya kama Bahijja kamar jaka ya tafi da ita dan cika umurnin Sarauniya Zulaiƙa.
Koda Yarima MalikusSaif yaga anja Bahijja antafi da ita take yaji jikin shi ya mutu, a ranshi ko cewa yayi Ummu badan ke kika haifeni ba da saina dakile duk wani zalincin ki akan Bahijja, jiyayi tace ma Huzaifa.
"Kai Huzaifa akaf cikin Masarauta ta na aminta dakai shi yasa baka da shamaki akan hudda da ɗana, ashe kaima munafuntanta kakeyi kana cin amana ta ni nasan abinda zan maku da sannu zan maganin duk wani maha'inci." hakuri Huzaifa yafara ba Sarauniya Zulaiƙa bata jira jin ta bakin su haka ta wuce cikin gadara tabar su Yarima MalikusSaif a duke ya kasa ko motsin kirki, baisan ya fara kwalla ba sai sunturi suke a fuskar shi, dan baki ɗaya hankalin shi ya koma kan Bahijja gashi takai hukuncin da za'aima ta a cikin turakar bayi kuma dokar Masarautar Daborah, jinin Sarauta bai shiga cikin turakar bayi bare ya kaima Bahijja ɗauki koda a fakaice ne, kaɗa kai ya dinga yi yana cewa"aaa Ummu ki rabu da Bahijja ni yakama ta ki hukunta ba itaba, mikewa yayi yaji juwa na niyar kada shi da sauri Huzaifa ya taroshi jikin shi suka wuce sashen Yarima MalikusSaif.


Koda Sarkin horo ya kama Bahijja ba inda ya tsaya da ita sai cikin turakar bayi duk yanda Bahijja ke cikin tashin hankali hakan bai hanata mamakin Masarautar Daborah musamman fasalin ginin ta tunda take bata taɓa ganin kalar shiba, gata da masifar yawa ga fadi komai a tsare yake, koda aka shigo da ita turakar bayi batai tunanin gun bayi bane dan wajen ya haɗu kuma ya tsaru gashi da girma kamar wani karamin gari amman duk a cikin Masarautar Daborah yake koda taga yanayin mutanen wajen hakan ya tabbatar mata da turakar bayin ne aka kawo ta bata san tafara kuka ba ganin ya kaita wajen wani icce zai ɗaure ta, gani tayi anata kallan ta kamar wata munafuka wasu taga sun ruga suna kuka wasu kuma taga sun wuce a sanyaye jitayi wasu nacewa kai ji wata budurwa can tayi laifi za'a hukunta ta nidai bantaɓa ganin taba, sai taji wata mata shiyar mata tace. "Aiko wannan daga ninta duk inda ta fito Bahijja ce ɗiyar Sarkin bayi Abdulmajid mijin Binta uwar bayi, ai tun tana ƴar shekara shidda zuwa bakwai tabar hannun iyayenta ta tafi aikin bauta wata Masarautar gaskia bako shakka wannan kyawun sai tsatsan Abdulmajid Bahijja."
aiko take ido ya raina fata tasan kashin ta ya bushe tabbas zargin da takeyi ya tabbata nan ne dai Masarautar su da take ikirarin ankaita wajen Umman ta dan ta huta da aikin bauta d azaba ashe yanzun zatansan tana aikin bauta da wahala a matsayin ta na baiwa marar ƴanci, aibata gama sakar zucin da take ba taji bulalai na ɗawainiya ga illahirin jikinta tunda take duniya bata taɓajin duka irin wannan ba mai masifar zafi gata da tsoron duka kuma an ɗaureta da igiya, kwalla ihu tayi ta fara kuka mai sosa zuciya cikin kankanin lokaci anfara taruwa dan ganin wanda ake hukunta wa da sauri su Mairo da Ladidi suka iso wajen ɗan jigum sukayi suna kallan kyakyawar budurwar da ake duka ita ko sai kuka take tana gayama Allah yakawo mata ɗauki, Mairo ce ta taɓa Ladidi tace. "Ke Ladidi wannan ba Bahijja bace kiduba da kyau ƴar muce ake duka, aiko cikin rudewa tace, itace Mairo mun shiga ukku ina ma Bahijja bata dawo wannan Masarautar ba a matsayin baiwa ba kilan da tafi samun sauki a rayuwar ta." kuka suka rushe dashi..... A wajen Binta kuwa da kyal ta ida abinda Sarauniya Zulaiƙa tasa ta ji take baki ɗaya batajin dadi zuwa tayi wajen Sarauniya Zulaiƙa ta duka tace "Allah yataimaki uwar dakina, nagama abinda kika sakani saimi zanyi yanzun."
shu'umin murmushi Sarauniya Zulaiƙa tayi tana kaɗa kafa ta kalli Binta tace. "Ayya Binta karki damu kinga ma komai yanzun kije gida ki huta da marece kin ida aikin ki kinji uwar bayi." mamaki ya gama kama Binta itadai ba taga Malik a shigo ba bare tasa ran ganin Bahijja gashi yau uwar dakin nata tanajin tausanta cikin jin dadi ta mike tace. "Nagode uwar dakina Allah yasaka da alkhairy." da murmushi takara bin Binta, itako jikinta na kyarma ta tashi zata tafi dan zumudi, ji tayi ta kirata wani kwano ne tace ta ɗauka taje taci abinci takara samun kwarin jikin ta, itako Binta dan dadi batsan takara zubewa ba tayi godya a ranta ko cewa tayi inhar Bahijja ta dawo ita zanba wannan abincin taci, Allah Sark ƴata, umurni ta bata tace taje, haka ta kama hanya ta tafi turakar bayi saijin dadi takeyi tunda Binta ta shigo cikin turakar bayi taga mutane zagaye, ta gani tasan ba wanda ake wulakantawa sai Abdulmajid ya fado mata arai jitayi gaban ta ya faɗi haka ta dinga kutsawa dan ganin irin azabar da ake ga nama mijin ta, har ta isa wajen da ake dukan, dasu Mairo tayi karo sai garzar kuka sukayi tambayar su ba'asi tafara bin hannun Ladidi tayi taga wadda ake duka batasan tasaki kwanon abincin hannun taba, karar yasa kowa hankalin shi yadawo gare ta harda Bahijja da tafara laushi haka ta aza idanun ta saman fuskar Binta, itama Binta kallan ta takeyi wani mummunan faɗuwar gaba ce ta ziyar su lokaci ɗaya musamman Binta data kwalla mata kira tace. "Ƴata Bahijjaa!!!" a sume ta fadi, itako Bahijja tunda taga Binta ta kasa ɗauke idanta akanta tana ganin ta tasan Mahaifiyar tace, tana ganin ta faɗi kasa sume tace. "Ummaa!! Dan Allah kitashi kada ki mutu kibarni dan Allah Umma." suko su Ladidi sukayi kan Binta suka dinga sama ta ruwa harta farfado, danko Sarkin horo ko aijikin shi haka ya dinga dukan Bahijja kamar ba gobe Binta na farfadowa ta tashi kamar mahaukaciya ta ruga ta kankame Bahijja a jikinta sai garzar kuka sukeyi su dukan su, baki ɗayan su Sarkin horo yaci gaba da dukan su rabi da kwatar bayin dake wajen suka dinga kuka dan tausan su Binta itako Bahijja ta rike hannun Mahaifiyar ta tana kuka mai tsuma zuciya.



```Allah Sarki rayuwa wasu insuna abu kamar baza'a mutu ba, shidai zalinci dodone wayyo Bahijja Allah ya fiddaku cikin wannan halin rayuwar da kuke ciki, fans Bahijja ku kara hakuri komai zai zama tarihi bi'izinillah🙏```

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Raifasu kuwa koda gari ya waye haka Sarki Baidulƙais d Sarki Danwar suka tashi ba inda suka wuce sai wani katon fili, inda ake ba Jaruman Masarautar gwaji na musamman, a haka Sarakunan yakin Masarautun suka haɗu da Jaruman su sukaci gaba da basu gwaji suna naɗa commender na Yaki kowa sai iyakar kokari yakeyi yaga sunci galaba a wajen yakin da zasu tunkara, shiko Sarki Baidulƙais haka ya kwashe labarin kannen shi ya faɗa mashi da sakon da yabasu, murmushi Sarki Danwar yayi yace. "Ba wani sako da nagani sai na bayan nan da ka aiko mani sannan kanina baya kasar yaje fatauci tun watanni ukku da suka gabata."
bakaramin mamaki bane ya kama Sarki Baidulƙais ba, yasan koma su waye da biyu sukazo Masarautar shi sai dai koma minene wannan ba abin damuwa bane fatan shi yaga bayan Sarauniya Zulaiƙa, a zahiri cewa yayi. "Yanzun dai ba abinda nike sai inga wannan yakin da zamuje mun dagargaza daular Daborah da komai nata." shima Sarki Danwar murmushin mugunta yayi yace. "Nima mafarki na kenan ina labarin Sarki Lahazu inace ka aika mashi da sakon gayyata kamar yanda muka saba."? Dan karamin tsoki yayi yace. ''Rabu da batun Lahazu fushi yakeyi dani dan na hanasu Bahijja, sai gashi Sarauniya Zulaiƙa tasa an ɗauke ta ina mamakin yanda ya ɗauki fushi dani." Sarki Danwar ne zaiyi magana saiga Jamra da wasu bayi sun kawo masu kayan marmari zama sukayi saman shimfidar da akai masu suka fara cin kayan itacen da aka kawo masu suna kallan Jaruman su na training.....

*************************************

Shiko Yarima MalikusSaif ya kasa zaune ya kasa tsaye ga wani irin makoko ya tare mashi kahon zuciya, baisan sadda ya fita ba ba inda ya tsaya sai sashen Sarauniya Zulaiƙa, isketa yayi falo ta harde kafa daya saman daya tana kallanshi ta ɗauke kai ta watsar kamar bata gan shi yana shigowa ba bada jimawa ba Huzaifa ya maye mashi baya, shima kallan banza ta jefa mashi, da sauri MalikusSaif ya iso wajen Sarauniya yace. "Ummu ki taimaka mani kisa a saki Bahijja kada aimata lahani na rokeki Ummu." mikewa tayi tsaye tana ma Yarima kallan sakarai marar wayau tace.
"Intai makeka fa kace? Minene hadin ka da Bahijja? Ince baiwa ce kaskantatta marar ƴanci da bata wuce in saida taba."? Baki ɗaya jikin Malik ne yai sanyi murya a sarke yace. "Ummu kada ki manta sama da shekara sha hudu kinyi mani alkawali Bahijja zatayi mani hidima a dalilin haka kika bar mani ita, kinga kenan Bahijja baiwa tace kuma hadima ta....dai dai nan Yazid ya shigo dan ansar makullin store zasu ɗibi kayan Yaki turus yayi ganin abokan nashi sun dawo ga Sarauniya Zulaiƙa ranta ya gama ɓaci dajin kalaman Malik baigama al'ajabin dawowar abokan shiba, sukaji karar mari tas tas har sau biyu, danko Huzaifa ji yayi kamar ya ruga dan tsoro, Sarauniya Zulaiƙa ce ta wanke MalikusSaif da kyawawan maruka har sau biyu shiko ya rike kunci, yayi mamaki sosai, shi kanshi yasan komai Mahaifiyar shi zata iya ai. katawa dan ba karamin ɓacin rai bane ya tabata ba, dukar da kanshi yayi zuciyar shi na tafasa ya daure

Please Login or Register in order to submit comment