Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaga sunfimu dubarar Yaki, ashe ba dukan Jaruman subane gaskia munyi kuskure da muka shigo baki ɗayan mu, kaga mutanen mu sun kashe jama'arta da yawa dayake ba duka bane amman kamar bamu kashe suba, gaskia ya kmata musan yanda zamu dakile wannan yakin sai zuwa anjima."


Wani banza kallo Sarki Lahazu yaima Sarki Danwar yace. "Kabar wannan maganar ma ba wani Yakin da zamu yanke saidai yanzun so nike musamu, akashe wannan shegen ɗan iskan yaron dan na fahimci kusan shi kejan ragamar wannan Yakin gaskia MalikusSaif ya cika Jarumin gaske."
Sarki Baidulƙais yazo yace. "Ku kwantar da hankalin ku yanzun haka munada kusan kashi ukku a cikin Jaruman mu, dan haka yanzun abinda nikeso daku kowa ya shirya zamunemi inda bayi suke dan ɗaukar Bahijja kunji abinda zamuyi." cikin gamsuwa kowa ya amince,wani kaskantaccen kallo Sarki Lahazu yaima Baidulƙais a zuciyar shi ko cewa yayi hmm yaro kenan kaɗauka zan tayaka ne ɗaukar Bahijja ai ina ganin Bahijja saida kaga bani ba Bahijjar dakake ikirari saidai koni ko kai.....


A wajen su Yarima Malik kuwa ana cikin gabzar Yaki, wani bakin Jarumi ya sari Huzaifa a hannu aiko take jini ya balle,koda Malik yaga an sari Huzaifa jini ya ɗibe gadan gadan yayi kanshi da takobi zai sauke kan Huzaifa shi kanshi ya fidda rai da angama sare mashi, aiko Malik yai kukan kura ya tsaga mutumin biyu rigijib ya faɗi kasa a mace, cikin sassarfa Malik yazo ya kama Huzaifa jini na zuba yabi ta wata hanya ya shige dashi wani gini da alama wajen adana kayan tarihi ne ya zaunar da Huzaifa wani farin kyalle Malik ya ciro a aljihun shi ya ɗaurema Huzaifa hannun shi cikin tausayawa yace. "Sannu Huzaifa ka zauna nan zaifi tsaro kaga ba kowa yasan da nan din ba, sannan inna samu dama zan kawo maka Bahijja ka boyemani ita kaga mutanen nan sunfimu yawa daman Allah na dafamana munacin galaba akan su." dakyal Huzaifa yace. "Shikenan abokina ka kula da kyau inna samu sauki zan dawo filin Yaki." girgiza kai Malik yayi alamar Aa sannan yace. ''Kai zaman ka kacigaba da yimana addu'a rike wannan takobin bani kibiyar ka." yana ansa ya tafi yana maijin tausayin aminin nashi abinka da yasan ko ina dayake Masarautar suce ta wata hanya ya bullo ya dinga sakin kibau sai gawar mutane aka gani kasa birjik danko Yazid yasha mamaki duk da yayi tunanin Malik ne kamar aljani sukaji da diro tsakiyar su, daga wata katanga aiko ya zaro takobi yaci gaba da artaba da magauta, suna cikin Yaki kawai yaji sun haɗe da Yarima Haishir warewa sukayi kowa yacigaba da nuna bajin tarshi akan ɗan uwan shi baki ɗaya hankalin Sarakuna ya koma kan su Malik musamman Sarki Lahazu da gaban shi ke faɗuwa yana tsoron kada akashe mashi ɗa, haka aka dinga barin wukake ji kare karaf karaf tarwatsin wuta na fita tsakanin Malik da Haishir kamar an dakatar da Yaki kallo ya koma wajen su MalikusSaif da sauri Sarauniya Zulaiƙa ta iso ganin Yaki ya dakata ta ɗauka ankarar mata da jama'a, saidai tayi mamakin ganin Malik da Haishir ana gabza uban Yaki, cikin gayya Malik ke ranwa da Haishir so yake yagama wahalar dashi, shiko harya fara sikewa dan yagama yarda MalikusSaif gwarzone kuma Jarumi wanda ya kware wajen iya sarrafa takobi musamman kibiya, yanda yaga yanata zukewa yakasa samun shi da takobi hakan yasa Haishir yai kamar zai faɗi aiko ya taɗe MalikusSaif y faɗi kasa da sauri Haishir yai kan Malik da har su Yazid zasu shiga aiko Sarauniya Zulaiƙa ta ɗaga mashi hannu dan ta sadakar da ran ɗanta tunda yakai kasa shiko Malik ko ajikin shi yaƙi tashi saida ya bari Haishir ya iso ya daga takobi zai cakama Malik yasa kafa ya halbar da Haishir ya mike ya ɗauki takobi ya wurwurata ya cillama Haishir aiko Sarkin Yakin Lahazu yazo zai kare Haishir take ta sauke kanshi sai kasa ko shurawa baiba bakaramin tsorone ya kama Haishir taɓa wuyan shi yayi yaga bashi aka kashe ba cikin tsoro Jaruman su Baidulƙais suka koma saman layin da yaraba iyaka suka tsaya dasu Yazid zasu bisu Yarima Malik ya hanasu suma cikin jama'ar suka koma saidai suma anmasu asarar rayukan mutanen su.......


Hutu suka tafi tunda sunki dawowa filin da'ga wannan ya nuna ma su Malik sun tafi hutu suma zama sukayi cikin kankanin lokaci Binta da sauran bayi suka fara kawo masu abincin da zasuci da ruwa shi kuma Abdulmajid su suka shigo da bayi maza suna ɗauke masu ciwuka suna basu taimakom gaggawa kamar yanda Sarauniya Zulaiƙa ta umurta haka suka samu waje na musamman suna ajesu ana samu magani, haka suma wajen Sarki Baidulƙais Jamra ce da sauran bayi suka dinga kawo masu abinci sunaci da ruwa sunaba Jaruman su kulawa saidai tunda Allah yasa ta shigo Masarautar Daborah idanun ta kesan suga Bahijja saidai bata gantaba, can ta hango wata dattijuwar mata da alama uwar bayin Masarautar ce da kaganta kaga Bahijja hakan yasa taji cewa Mahaifiyar Bahijja ce tanaso tagan ta amman ba dama dan batasan Sarki Baidulƙais yai zatan akwai matsala tasan mutun ne shi mai basira da saurin gano abu, basarwa tayi taciga ba da abinda takeyi har akai la'asar, kowa ya huta.....



A wajen su Malik kuwa zaune suke suna shawarar yanda zasu bullowa abokan gabar su, wannan karan Saifulislam ne da Waziri Dammur zasu ga ragamar Yakin kallan su Yarima Haishir sukayi sukaga sun linkasu yawa sau biyu, Saifulislam ne yace. "Abinda ya bani mamaki ga mutanen nan yawan Jaruman su, dagani hadin guiwa ne." "Malik ne yace. "Abbuh harda ƴan Masarautar Waisu inda muka ɗauko Bahijja sai yan Masarautar Ƙaisu da alama sunyi hadin guiwa ne yana gama fadar haka yasha ruwa, cikin kulawa Yazid yace "wai ina Bahijjar dan bazamu yarda arabata da iyayen taba a karo na biyu ba."cikin jin ddin maganar Yazid, Malik yace. "Tana turakar bayi kasan basu san sirrin Masarautar nan ba, ba lallai su iya gane wajen ba, sun cikin magana saiga Sarauniya Zulaiƙa tace. "Yakamata ku sake gyara jama'ar mu nasan halin mutanen nan ba kirki suka cikaba zasu iya far mana munanan." haka kuwa akayi kowa ya tashi suka sake gyara sahu wannan karon kashe biyu aka bari aka tura ɗaya cikin tsakiyar Masarautar dan bada kulawa ta musamman...suma su Haishir sungama kimtsawa sunsa bayin su sun shiga cikin Masarautar Daborah cikin sirri sun nemomasu turakar bayi suka dawo suka shaidama Yarima Haishir, yanzun so suke sai Yaki ya nutsa sannan su tura tawaga ɗaya suje su ɗauke Bahijja su gudu da ita, da wannan shirin suka shiga cikin sahun Yaki, a wajen su sakin Yakin Daborah kuwa suna fitowa a gidan Yari suka fara shiri dasu Lurwan kowa ya shirya suka haɗa tawaga guda suka tsaya gab da fa'da suna jiran Yaki ya kamre kafin su shiga cikin filin da'ga, aikuwa wannan karon Sarki Baidulƙais shine yasa Sarkin busa ya buga kugen Yaki aka sake gamewa a karo na UKKU saibama juna wuta akeyi wannan karon kua Saifulislam ne cikin Jarumai da tawagar shi ana fafatawa sai fille kan maza yake kamar ruwa haka yake kisar su hakama Dammur ba'a basar su abaya ba, dan sun kashe mutane ba kadan ba suma ankashe nasu ba iyaka koda Sarauniya Zulaiƙa taga anata kisar jama'ar ta tahowa tayi zataba Wazirin ta kibiya dan tasan shima gwanine wajen iya halbi da kibiya ji tayi an buga mata gefen mashi a ciki dafe cikin ta tayi a fusace ta zaro takobi a jikin ta ta daɓama wanda ya sareta sai a jikin Sarki Baidulƙais, da sauri taja baya tana kafe takobin ta a saman kasa sannan suka dinga aikawa junan su da shu'umin kallo, wani irin tsawa Sarki Baidulƙais yayi ya afkama Zulaiƙa itako takobi tasa ta kare kanta sannan sukaci gaba da fafatawa, duk yanda yaso ya caka mata wuka taki yarda saita zille yayi mamakin kallar Jarumta ta Sarauniya Zulaiƙa bakaramin iya sarrafa takobi take ba, wani wawan sara takowa Baidulƙais ta same shi a kafaɗa jini ya fashe har tsurtuwa yakeyi, da sauri yai baya shiko Sarki Danwar na ganin haka ya shiga yacigaba da fafatawa da Sarauniya Zulaiƙa cikin kwarewa suke kaima juna sara, koda Yarima Malik ya waigo yaga Mahaifiyar shi na artaba da Sarki Danwar da sauri yabar abokin gabar shi yayo kansu, shiko Sarkin yakin Waisu biyo bayan shi yayi da takobi yana isowa ya shiga yai tsalle ya halbe takobin Danwar ta faɗi kasa Sarauniya Zulaiƙa ta yanke shi a hannu ya faɗi cikin gafin nama ta tafi zata kashe shi, sai taji na daɓama Malik wuka a hannu da sauri ya dafe wajen ya anshe takobin hannun Sarauniya Zulaiƙa ya sauke kan Sarkin Yakin Waisu da kaushin rai yayi kan Sarki Danwar, Jaruman shi suka janye shi, Sarauniya Zulaiƙa cw takama Malik suka tafi, wata rigace ya yaga ya ɗaure hannun shi yaci gaba da fafatwa, fatan shi jama'ar su suci galaba akan makiya, koda Yaki yao Yaki komai ya hargitse haka Sarkin Yakin Daborah suia shigo ta kofar baya shida su Lurwan suka fara karo da kawunan maza dda takubba take sukaima mutanen su Haishir rina sukaira kasarsu, danko Lurwan shine na biyu a gwanayan iya halba kibiya a cikin Masarautar Daborah daga MalikusSaif sai shi, da yaja kibiya idan ya saki sama da talatin saita watse, sai ɓarar da maza yake, koda hankalin Sarauniya Zulaiƙa ya dawo jikin ta can taga Lurwan da Sarkin Yaki na kashe maza wani irin dadi taji taga tananda sauran hazikai dan yanzun sukejin kwarin su, zuwa yanzun mutanen su sun zama dai dai da jama'ar Baidulƙais koda zasu fisu sa kaɗan ana cikin Yaki Yarima Haishir suka sabe shida wata tawagar sai idan Yarima Malik da Yazid binsu sukayi dan ganin inda zasu abin mamaki turakar bayi sukayi, itako Bahijja sallah kawai takeyi tana rokarma su Ya Malik dinta nasarar Yaki tana kuka tana addu'a gashi jin shiru Umman ta da Abban ta basu dawo ba yasa tafara kuka tana tsoron kar akashe su, tana cikin addu'a taji kamae tafiya hakan yasa ta tashi ta fita zata tafi wajen Yaki taga halin da ake ciki so take taga Umman ta, tana cikin tafiya taji ankamata anjanyeta kwalla ihu tayi abanza,fita akayi da ita ta kofar gaba a cikin turakar bayin suna son su gudu da ita saiga su Malik aiko,MalikusSaif yaja wata bakar kibiya yacema babban Jarumin Sarki Lahazu yace. "Sakarta ko yanzun inkasheka." shiko ɗaura ma Bahijja wuka a wuya yayi yacema Malik ya aje makamin shi koya ksheta.....ai baibari ya karasa maganar ba ya saita kibiya ta saitin fuskar Bahijja ya kashe shi ta tsakiyar kwakwalwar shi, take yafaɗi mace ba rai, tsoro ne yakara kama su Haishir take suka sake kaurewa ture Bahijja Malik yayi a jikin shi sukaci gaba da artaba hankalin shi yayi kan makiya aiko Haishir ya sabe da Bahijja ta hanyar rufe mata baki yabi ra wata hanya shi niyar shi ya gudu bai saniba yagan shi tsakar filin Yaki, itako Bahijja tagama rudewa ganin kawuna kasa, danko wajen su Lurwan da Saifulislam baka ganin komai sai kawuna sun kashe kamar ba gobe, koda Bahijja taga sai nutswa da ita yake cikin filin Yaki batasan ta gartsa mashi cizo ba, aiko ta saki kara, kallone ya dawo wajen su musamman su Sarauniya Zulaiƙa dasu Sarki Baidulƙais, Wani irn dadi yaji yaga an amso mashi Bahijjar shi kafeta da mayun idanun shi yayi, Sarauniya Zulaiƙa ce tasa aka buga kuge komai ya lafa, kamar yanda sukayi sharadi idan har sukayi nasarar tafiya da Bahijja to Yaki zai tsaya sunci galaba, idan kuma har suka kasa fita da Bahijja a cikin Masarautar Daborah to ancisu Yaki kuma basu ba sake neman ansar Bahijja, Yaki na tsayawa alamar Yarima ya samu nasarar ɗauko Bahijja saura fita da ita cikin Masarautar Daborah, wani kululune ya tokare Sarki Baidulƙais baisan ya isoba ya nuna na Haishir hannu alamun ya bashi Bahijja, aiko Haishir ya bige hannun Baidulƙais cikin fushi yace. "Bahijja tawace kuma ni nai nasarar ɗauko ta dan haka zanyi anfani da karfina dan inga na tafi da ita Masarautar mu."wani mugun kallo Baidulƙais ya watsama Haishir a fusace yace.....



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 37&38



"Bani Bahijja tawa ce, mallakina ce, sannan ita kawo ni Masarautar Daborah dan in anshe ta koda hakan yana nufin rasa raina."
Ya karashe maganar a kausa she.
Wani shekakken kallo Yarima Haishir yaima Baidulƙais sannan yace. "Ina ga ka manta nace zan auri Bahjja tun tana kalkashin ikon ka daga bisa ni matarka tasa wasu, su ɗauke Bahijja dan halaka ta akai sa'a ni masoyin nazo daniyar ta na dauketa sannan na ceceta a cikin ruwan sanyi nakai ta Masarauta ta, cikin rashin sa'a Malik yazo har Masarautar mu ya ɗauke ta, kana ganin nima basai inda karfina ya kareba dan ganin na ansheta koda karfina zai kare! ya kaji nawa labarin da ka ɗauka hadin guiwar da mukayi kai muke tayawa Yaki dan ansar Bahijja yima kanmu aiki mukeyi nida Mahaifina da duk wani tawagar mu! Dab n haka inma bacci kake ni Yarima Haishir ɗa ga Sarki Lahazu ɗan Sarki Humzu nace ka farka bakai ba Bahijja." ai yana ida faɗar wannan maganar Sarki Baidulƙais ya zaro takobi ya daɓa Haishir take Yaki ya kaure tsakanin Baidulƙais da Haishir, wani shu'umin murmushi Sarki Danwar ya saki a ranshi ko cewa yayi anzo wajen ai haka nike so


_Niko ƴar mutan Kankia nace munafunci dai dodone aduk inda ake shuka shi..._


Sukaci gaba da artaba suke basu ji basu gani kowa yana da burin da ya keso ya cimmawa akan Bahijja danko rigima tai kamari , suko mutanen Sarauniya Zulaiƙa sai dai suka koma yan kallo, cikin kankanin lokaci Sarki Lahazu yasa kaf Jaruman shi sun dawo kalkashin ikon shi, suma na Baidulƙais suka koma kalkashin ikon Sarkin su, shiko Danwar gefe ya koma da tashi jama'ar yace tunda rigima takoma ta gida ta aminnai ba wanda zai shigar mawa, awajen Malik ko suna gama karar da tawagar Haishir ya duba baiga Bahijja ba take ya bazama cikin Masarautar Daborah dan neman Bahijja a rude, itako Bahijja duk ta rude, mamaki ne ya ishi zuciyar Sarauniya Zulaiƙa ta rasa dalilin da yasa su Baidulƙais ke yakar junan su akan baiwa, baiwar ma Bahijja kodai suna sonta suke dan kyawun ta kodai fasikanci suke da it? a wani ɓangaren zuciyar ta kowa tayi baiwa ce fa, taya zasu so baiwa? mtsw taya haka/ma zata kasan ce.
jin karar sarar da suke kaima juna ya maida ta cikin hankalin t, Yarima Haishir ne ya kaima Baidulƙais sara nan ya daɓa mashi wuka akafa, shiko cikin jin zafin abinda Yarima Haishir yai mashi baisan ya daɓa mashi wuka a ciki ba, take ya faɗi cikin jini face face, da gudu Sarki Lahazu ya zari takobi ya wurgoma Baidulƙais ya sameshi a gefen kafaɗa aiko jini ya fara zuba, sake zaro wata takobin yayi suka game, cikin karfi so yake ya kashe Baidulƙais cikin kankanin lokaci Yaki ya kaure tsakanin Jaruman su kowa yana kokari akan ganin ya kashe ɗan uwan shi sai kisar junan su sukeyi a banza a wofi, shiko Sarkin Fadar Waisu ɗauke Yarima Haishir sukayi akabfara bashi kulawa ta musamman sai dai ba wanda yake kiran sunan shi sai Bahijja, a wajen Malik har wajen Masarauta yaje ba Bahijja ba alamun ta hakan yasa ya dawo ciki yana neman ta, cikin kankanin lokaci sun gama jigata junan su da sara danko Sarki Baidulƙais ya sari Sarki Lahazu sosai haka shima ya sari Sarki Baidulƙais, koda Sarki Danwar yaga suna neman kashe junan su, musamman yanda Sarki Baidulƙais ke ganin rabuwar shi da Bahijja tamkar karshen rayuwar shine yazo, sai kuma Sarrilƙus ya kara faɗo mashi a rai yasan muddin ya sake rasa ta zai iya halaka shi dan ya juya mashi baya, haka yai kukan kura ya daka uban tsalle take ya sauke kan Sarki Lahazu, rigijib ya faɗi a mace, take Jaruman Masarautar Waisu suka zubda makaman su, ganin an kashe masu Sarki, shi kan shi Sarki Danwar yaso ace Sarki Baidulƙais ne aka kashe dan yasan Sarrilƙus sai ya kawo karshen Masarautar Waisu, shi kuma sai ya kwashe dukiyar su,dan da muwar Danwar kenan, duk wanda ke wajen sai dai ya tsora ta shi kanshi Sarki Baidulƙais baiyi zatan ya kashe Sarki Lahazu ba wanda ya kasance aboki kuma aminin shi, shi kanshi yasan indai Yarima Haishir bai mutu ba sai ya ɗauki fansa akan shi ko ta wace hanya ce, tafiya yayi dasauri ya riko hannun Bahijja yavfara tafiya da ita saibdai Sarauniya Zulaiƙa batai yunkurin hana shi ba, dan bata san ganin ta a cikin Masarautar ta ita ko, sai tirje tirjewa takeyi tana kin bin shi, ganin Jaruman su sunki motsi kuma da alamu umur nine ga Sarauniya Zulaiƙa akan kadan wanda ya hana Baidulƙais tafiya da Bahijja ganin hakan yasa Saifulislam ya tafi da sauri zai anshe Bahijja, saiga su Malik ayam sun faɗo cikin filin koda idanun shi suka gane mashi Bahijja hannun Baidulƙais ai da gudu yai kan Baidulƙais yasa takobi ya datsar mashi hannun da ya rike da Bahijja dashi bungul gutun ya faɗi kasa riketa yai gam ya maida ta gefen shi ya sake ɗaga takobi yace. "Duk wanda yasan yazo Daborah dan ɗaukar Bahijja yazo ga Bahijja nan hannun MalikusSaif in kacika kai ɗane kuma Jarumi gwarzo kanaji da kanka kazo ka anshi Bahijja!." ya ida maganar da kakkausar murya.
shi ko Baidulƙais ganin hannun shi Ƙasa take ya kara tsora ta da lamarin MalikusSaif , cikin tsoro ya rike hnnun shi jini na zuba, kallan Jaruman shi yayi alamun su tafi su afka ma Yarima Malik aiko wajen goma suka tunkari MalikusSaif, yasa takobi ya sauke kan na farko na biyu ma haka cak suka tsaya, shima ganin za'a karar mashi da Jarumai yasa yace sudawo a fusace ya wulla Bahijja kusa da Baidulƙais yace. "Ga Bahijja nan inka isa ka sake kama daidai da ɗan yatsan ta na rantse da Allah sai dai uwarka ta haifi wani Bahijja tawa ce kuma mallakina ce ni kadai, danni kadai Allah yasa tazo duniya dan haka nafi kowa kaunar Bahijja zan iya karar daku a kan Bahijja.! "
Wani irin daram daram Zulaiƙa taji ta rasa gane manufar zancen Yarima Malik kar dai ace Malik baiwa zai so


*Nikodai Jameey nace haka najeli _BAYIMA_ _'YA'YANE_ fans nacewa wai Malik son Bahijja yakeyi ammn baisani ba ya ɗauka tausan ta yake, ni kodai nace bari musa👀muga yanda zata kaya muje zuwa my fans son so nike maku wolh lol🤣*


tsaye Sarki Baidulƙais yayi ya kasa ko motsi yana mamakin maganganun MalikusSaif shi ko yasan ko giyar wake yasha bazai iya ansar Bahjja ba a halin yanzun, hakan na nufi anci galaba kanshi kenan ya ya rasa Jaruman shi masu yawan gaske, gashi fushin zuciya tasa ya kashe aminin shi, yanzun ga bainsan halin da Yarima Haishir ke ciki ba, yanzun shikenan MalikusSaif ya anshe mashi Bahijja bayan kusantar ta shine dawwar mulkin shi anya zai iya rabuwa da Bahijja kuwa? haka dai yai ta sakar zuci, ana cikin haka a sheke da ruwan sama kamar da bakin kwarya kowa ya gud ya samu mafaka ruwa ne ake mai yawan gaske haka Yarima Malik ya damka Bahijja hannun Binta sannan ya tafi ya ɗauko Huzaifa ya nufi sashen shi dashi da Yazid itako Sarauniya Zulaiƙa sai maimaita maganar MalikusSaif take a cikin zuciyar ta, shi ko Sarki Baidulƙais kamar gunki ko motsi ya kasa yi sai dai Jaruman shi ne sukazo suka jashi suka samu mafaka dan jiran daukewar ruwa, haka mutanen Sarki Lahazu suma gawar Sarkin su suka dauka suka nufi inda akeba Yarima Haishir kulawa ta musamman.....

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Koda Sarauniya Zulaiƙa ta shiga sashen ta, takai gwaro ta kai mari take haka ta dingayi ji take kirjin ta na bugawa da sauri da sauri ba inda ke mata yawo a kwakwalwa sai inda Yarima Malik ke cewa Bahijja ta wace ni kadai akan Bahijja zan iya halaka kowa kuma nafi kowa kaunar ta.....da sauri ta toshe kunnuwan ta cikin kankanin lokaci idanun ta suka sauya, shi gewa tayi cikin bedroom dinta sannan ta shiga bathroom wanka tayi tana wanke ciwon da Sarki Baidulƙais yai mata, tana cikin wanka taji muryar Saifulislam duk hankalin shi nakan matar shi yasan anjima ta ciwo so yake yaga yanda ciwon yake ita ko tana cikin wanka ta zuba ma ciwon ruwan zafi bata san sanda tace Auhhh! jin yanda Sarauniya Zulaiƙa taja dogon ihu baisan sanda ya faɗa bathroom dinba jitayi an riketa, a tsorace ta waiga taga mijinta ne bata san sadda ta rungume shiba tana kuka mai taɓa zuciya ba, bubbuga bayan ta yahau yi, sannan ya kama ciwon yaga yankan yana da girma fita yayi dakin ta cikin wata wadirofe ya ɗauko wani magani yazo ya wanke mata jikin ta daga karshe ya wanke mata ciwon dake hannun nata, itako sai kallan shi takeyi batai tsammanin zai sakko cikin sauki ba tasan halin Saifulislam mutun ne mai tsananin hakuri saidai bai iya fushi ba,wani zani ne ya dauko ya ɗaura mata sannan ya ɗauke ta ya kwantar da ita saman gado da kanshi ya shirya ta sannan ya ɗauko wani magani ya zuba ciwon kara tayi ya fara bata hakuri cikin tausayawa sannan yasa farin kyalle ya ɗaure mata ciwon,bude wardrofe din ta yayi ya ɗauko Milk din alqabba ya saka mata, cigaba da rirritata yayi yace. "Sannu Ummu Malik ya jikin.?"sake lafewa jikin shi tayi tace. "Da sauki Abu Malik, yanzun ya kake ganin zamuyi dasu Baidulƙais kaga yanda Yaki ya juye ya koma abin al'ajabi sun zo Masarauta ta dan Yakata karshe sun koma Yakar junan su harda kisa."Murmushi yayi yace. "Ummu Malik kenan ai Allah ba azzalumin kowa bane ba yanda za'ai ya bari addinin shi ya tozarta kuma kinga ko bakomai akan kankanuwar yarinya sukeso su karɓa kuma dagani ko wannan su yanada nashi kudurin na daban akan Bahijja." da sauri ta tashi daga jikin mijin ta kalln shi kawai tayi sai taji ranta ya sosu duk da tasan kan Bahijja akai wannan Yakin saidai ta tsani a ce anyi Yaki akan Baiwa.
basarwa tayi tace. "Miza kace akan ɗanka da ya dinga kumfar baki akan Bahijja cikin dubun nan mutane."? ɗan damama yayi shima yaso yai zargin wani abu amman ko saboda mahaifiyar Malik bai fatan hakan takasan ce yasan ukubar da Bahijja zata fuskanta a baya ba'ai masu komai ba, jin shirun yai yawa yasa ta sake kallan shi cikin kwarewa da karantar yanayin mutun tace. "Kaima abunda nike zargine kake zargi ko Abu Malik."? da sauri ya girgiza kai dan yasan Sarauniya Zulaiƙa akwai ɗan banzan wayo da saurin fahimtar abu cewa yayi. "Haba keko mi kike zargi aranki mata ta."? "Hmmm Abu Malik kenan wannan abun a bayyane yake kardai ace Malik son Bahijja yakeyi." da sauri yasa hannu ya rufe mata baki ya sake kwantar d ita a kirjin shi yana bubbuga bayan ta shi kanshi yana jin yanda zuciyar ta ke duka da sauri da sauri, yasan zata iya samun matsala shi kuma yana son matar shi, cikin sanyin murya yace. "Haba Sarauniya ta ki daina tunanin haka a cikin kyakkyawar zuciyarki mai tsafta wadda bata saba da zargi ba, ina Malik ina baiwa, karfa ki manta Bahijja baiwar Malik ce ba abinda zatai mashi daya wuce hidima a

Please Login or Register in order to submit comment