Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matsayin ta na baiwa kuma hadimar shi." Kaɗa kai kawai ta iya yi alamun hakane kamar mai tuna wani abu ta tashi da sauri tace. "Bazan bar Bahijja ta kusanci ɗana ba amatsayin baiwar sa hadima asalina ma bansan tana fitowa cikin turakar bayi zuwa cikin Masarautar nan, na yafe mata duk wata hidima amatsayin baiwa na ƴan tata afagen bauta tai zaman cikin dangin ta bayi wannan shine hukuncin dana yanke mijina."
murmushin yake ya saki domin yaga tsantsar kiyayyar Bahijja a cikin kwayar idan Zulaiƙa baisan yai mata musu tana cikin wannan halin na ɓacin rai, cewa yayi. "Bablaifi saidai kibar wannan zancen sai kin kara samun nutsuwa ba'a yanke hukunci cikin fushi."zata sake magana ya ɗaura mata yatsan shi saman lips sannan ya tashi ya mikar da ita tsaye yace. "Muje falo najiyo sallamar Waziri kilan ruwan ya tsaya musan yanda za'ai da waɗannan mugayen a tare suka fito suka samu Waziri zaune falo suma zama sukayi sannan Sarauniya Zulaiƙa ta kalle shi tace. "Miye labari Waziri miye abinyi a halin yanzun."? Cikin girmamawa yace. "Ranki shidade ina tsammanin waɗan nan mutanen sun gaza yanzun tuggun su ya koma kansu wannan shi'ake kira da ƙaiƙayi koma kan mashe kiya saidai kisani a shirye muke da mu kara Yakar su matsawar sun nuna hakan a zahiri." cikeda gamsuwa tace. "Baka ganin munyi asarar Jaruman mu."? "Eh hakane kam amman kuma ai sunfimu asara tunda nasu sun lunka namu sau ukku saidai yanzun wa'anda suka rage bai wuce kashi ɗaya ba ya kike tunanin zuciyar su nai masu ƙuna, sannan sun rasa manmayan mutanen su mufa? daga karshe sun ɓuge da Yakar junan su ya kike gani labarin zai kaya bayan sun koma Masarautun su."?
Wani shu'umin murmushi Sarauniya Zulaiƙa ta saki wanda tunda aka fara Yaki shine karin farko da tayi murmushi mai ɗauke da ma'anoni iri iri tace. "Da kyau Waziri shiyasa kake da mahimmanci sosai musamman a cikin Masarautar Daborah yanzun.....
ji sukayi anshigo da gudu kamar an halbo shi Lurwan ne rike da takobi wadda ta gaji da shan jinin ɗan Adam dukawa yayi yace. "Allah ya taimakeki wuta ta tashi a cikin tsohon gidan tarihi na *Surƙu* wannan daga abokan gabarmu, saidai bami kasa a guiwa ba mutanen mu nacan suna kokarin kashe ta." da sauri suka mike suka fita wuta ce ta gama kera ilahirin gidan tarihi mai ɗimbin tarihi a cikin Masarautar Daborah da gudu su MalikusSaif suka cigaba da kashe ta sa kyal ta mutu itako Sarauniya Zulaiƙa da sauri da bankaɗa kofar suka shiga saidai bataci kayan su masu daraja a wajen su ba, tana fitowa ta dafe kirjinta can kuma sukaga an wurgo wani abu cikin kwalba ya faɗa saman kwanon gidan tarihi inda Takobin Barri take ajiye, bin inda aka halbo abin MalikusSaif yayi yaga Mutanen Sarki Baidulƙais ne, take suka rabu kashi biyu wasu suka tunkare su da takubba da kibiyoyi wasu kuma suka cigaba da kashe wutar da aka tada masu a gidan adana tarihi na *BARRI* ciki kuwa harda MalikusSaif ake kokarin kashe wutar, suko su Yazid da Lurwan suketa kasar jama'ar Sarki Baidulƙais.......



_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم





_Dedicated this page to all Masoya na son so nike maku son fisabilillah_



Episode 39&40



Haka su MalikusSaif suke ta faman kashe wuta amman kamar ana kara rura ta sai kara hauka takeyi, kamar ana sama ta fetir haka take hauka, danko Sarauniya Zulaiƙa ta gama fita hayyacin ta ganin asarar dake shirin samun su, suko su Malik sunyi iyakar yinsu har sun fallawa Allah, ana cikin haka suka ga wani haske ya fito daga cikin ɗakin ya dira ƙasa sai sheƙi yakeyi, danko mamaki ya gama kama kowa, _*Wukar*_ *_Barri ce_* ta keta walauniya, ta kafe cikin ƙasa wani irin dadi ne ya rufe Sarauniya Zulaiƙa da sauri ta isa wajen takobin Barri, takai hannu zata ɗauke ta hasken Wukar ya haske mata idanu har saida ta rufe idon ta, MalikusSaif ne ya iso wajen ya duka ya kama wukar ahankali hasken ya fara disashewa ɗaukar ta yayi, ya rike yana mamakin yanda akai takobin Barri ta fito daga cikin ɗakin da aka adana ta, wanda ta kwashe sama sa shekaru dubu huɗu a dane,cikin kankanin lokaci wutar ta mutu kamar ta tsafi suko su Yazid sai fafatawa sukeyi da jama'ar Sarki Baidulƙais ganin sun kusa karar dasu hakan yasa mutanen Baidulƙais suka koma bakin layi wanda yai masu iyaka dasu MalikusSaif , cikeda tsawa Sarauniya Zulaiƙa tace. "Baidulƙais dame kuke takama dashi a cikin Masarautar Daborah in Yaki kukeji yanzun aka fara saidai na haneku da kona mani wurari masu dinbin daraja agareni! Baiwa ce ta gagare ka kuma ka karya alkawali inda ka kasa ansar Bahijja yanzun muke da galaba a kanku sai ku kama gaban ku idan kuma baku gaji da artaba damu ba, sai acigaba daga inda aka tsaya ina tsammanin hakan yai maka kaida tawagar ka baki ɗayan ku.!"


Shiru Sarki Baidulƙais yayi yana jin wani irin bakin ciki a zuciyar shi yana ji yana gani yai asarar farin cikin shi Bahijja sannan wannan shike nuna mashi rabuwar su da Sarrilƙus yazo tunda ya kasa yima shi abinda ya umurce shi shekara da shekaru zaiyi magana kenan, sai ga Wazirin Sarki Lahazu yazo gaban Sarauniya Zulaiƙa yace.
"Muna mubaya'a ga wannan Masarautar taki mai dinbin tarihi, Ya Zulaiƙa yanzun muke ganin gangancin da mukayi, muka hada karfi da karfe da makiyan mu, muka yake ku, yau gashi soyayya ta zama kiyayya kuma kiyayya ta zama soyayya, ina san kisa aranki Masarautar Waisu ta barranta da kawo maku hari ko Yakar ku yanzun mungane matsalar daga inda take, Sarauniya Zulaiƙa ki sani yau zamu koma Masarautar mu cike da bakin ciki a cikin zukatan mu, an kashe mana Sarkin mu! Kuma shugaban mu, ya kike ganin wannan lamarin zai kasan ce? rikic da ku kuwa ɓata lokaci, akan mutanen da basu damu damu ba, bayan anyi walkiya munga haske ga makiyan mu nan,ashe makiyan mu na tare damu na rantse da Gurfanai sai mun darkake Masarautar Raifasu koda hakan yana nufin za'a karar da ire iren mu a cikin kasar Gambia dama duniya baki ɗaya.!"

Yana gama faɗar haka ya juya a fusace ya tafi dai dai wajen Sarki Baidulƙais ya tsaya sunai ma juna kallan kallo cikeda tsana marar misaltuwa harya wuce sai kuma ya dawo ya ɗaga takobin shi kamar zai sare wuyan Sarki Baidulƙais, sai kuma ya ɗaura ta a gefen saman wuyan shi yana huci yace.
"Ba yanzun zamuyi yun kurin kashe kaba Baidulƙais saika gama shakar bakin cikin duniya sannan kasani na rantse da Gurfanai ran Sarki Lahazu fansa ne a garemu koda zamu kare baki dayan mu kasa wannan a ranka da Masarautar Waisu kake magana.!"
fuszar da iska yayi sannan suka tafi shi ta tawagar su da gawar Sarki Lahazu wasu kuma suka ɗauki Yarima Haishir saman doki suka sashi sai nishi yakeyi sama sama ba kadan yakejin jiki ba....


Koda suka tafi Sarki Baidulƙais ya sauke ajiyar zuciya dan yasan yanzun zasu fara artaba da Yarima Haishir, a zahiri ko cema Sarauniya Zulaiƙa yayi.
"Zulaiƙa kenan Jarumtar ki ta burgeni sannan taurin kanki yana bani mamaki, wato kin anshe Bahijja ko bayan kece kika bani ita, shin bari in tambaye ki, ina tunanin ki ya tafi da har zaki bar mayuwancin zaki a cikin dabbobi lokacin da yake bukatar cin abinci? nasan baki da wannan amsar!
Ni Baidulƙais bari inbaki amsar da kaina! Kamar haka Bahijja take a wajena kisa aranki Bahijja sai ta dawo kalkashin ikona, sannan karki dinga jin kanki yana kara girma wai Sarki Baidulƙais ya samu matsala da aminina Sarki Lahazu kinajin dadi gaba da ƙullu tsakani na da zuriar shi, kisani ni Baidulƙais ban yarda maka maina ba, akanki ko wane lokaci takobi na tana sage a kafaɗa ta bazan sauke taba har sai ranar dana cimma burina a cikin wannan Masarautar taki."


Murmushi Sarauniya Zulaiƙa tayi tace.
"Ban shirya jin wannan sakarcin naka ba, danni ba sakara bace, Kamar ka! Dan haka yanzun nan nabaka nan da minti talatin kubar mani Masarauta ta, tunda kun gaza kunji kunya, kuje can kuci gaba da Yakar junan ku, Masarautar Daborah tafi karfin ku, sannan Bahijja tafi karfin ka, kasani duk wani bawa dake cikin wannan Masarautar tawa sunfi karfin ka, dan haka kar in kuskura in sake ganin wani maikama dakai ko mutanen ka a cikin Masarautar Daborah."


Shiko Sarki Danwar sai jin dadi yakeyi ganin an ɓata da Sarki Baidulƙais dasu Yarima Haishir, ga anci galabar shi ya kasa ansar Bahijja yasan yanzun ba karamin artaba zasu kwasa tsakanin Yarima Haishir da Baidulƙais ba, tahowa yayi ya dafa kafadar Sarki Baidulƙais yace. "Abokina kwantar da hankalin ka, karka damu ya kamata mu tafi dan musan abinyi kaga abinda ke gaban mu ba wannan zancen ba, Sarauniya Zulaiƙa gaskia kin birgeni saidai kisani na barranta da artaba da wannan Masarautar dan lamarin ta abin al'ajbi ne da fatan zaki ƙarɓi kokon barata."

Wani kallo tai mashi ba tare da tace komai ba, shiko Sarki Baidulƙais kallan Sarki Danwar yakeyi cikeda mamakin maganar shi, ke mashi yawo a cikin kwakwalwar shi yace
"Kokon bara tame kenan mi Sarki Danwar yake nufi? murmushin yake yayi yace. "Shikenan abokina zamu tafi, a sheke ya kalli Sarauniya Zulaiƙa yace zan tafi Zulaiƙa sai dai kisani akwai rina aka ba, saina mallaki Bahijja, dan haka ki saurari zuwa na." murmushi tayi ba tace komai ba haka suka kwashi inasu inasu suka tafi da mutanen su suka tafi, Sarauniya Zulaiƙa ce tasa Jaruman ta suka fara gyaran gidn tarihin da aka sama wuta, sannan suka fara ɗaukar gawar Jaruman su sukayi jana'izar su suka gama binnewa sannan suka kwashe sauran gawar wakin Jaruman su Baidulƙais suka kaisu can cikin jeji cikin wani kogi suka juye su, sannan suka dawo wani fili Sarauniya Zulaiƙa ta tara Jaruman ta ba laifi suna da yawa tace. "Ina maku godiya mai tarin yawa, da kuka jajirce cikin ikon Allah muka kare martabar Masarautar mu, sai dai kusani ni Sarauniya Zulaiƙa 'ya ga Sarki Abdulhamid daga yau bazan sake karɓar takardar gayyata ta Yaki ba, na soke shi musamman in daga wajen Sarki Baidulƙais ya iso, saboda ya karya alkawali da ace ya anshi Bahijja da yaci galaba akan mu, sai dai tunda ya gaza dole ya hakura da Yakar mu kamar yanda sharuɗdan wannan Masarautar ya gin daya a shekaru dubu ukku da suka gabata dan haka ni Zulaiƙa na soke Yaki a dalilin BAIWA, kuma a dalilin ta narasa abubuwa masu yawa musamman ma rayukan Jarumai na, saidai Allah yasa bamu nasata Sannan bamuyi asarar kayan tarihin muba, da Wukar Barri sai mu godema Allah, sannan ina san kowane Jarumi na, na basu hutun mako biyu kowa ya huta, inai ma kowa fatan alkhairi, muna roken Allah ya kara kare mana rayukan mu da dukiyoyin mu baki ɗayan mu." da Ameen suka amsa baki ɗayan su, sannan ta sallami kowa ya tafi sabgar gaban shi, itama tafiya tayi sashen ta


Koda Yarima Malik ya koma sashen shi dakin shi ya wuce yai wanka sannan yai sallah, zama yayi saman sallaya ya cigaba da lazimi yana addu'a yana gamawa ya safko dafilo kasa ya kwanta kamar mai tunani rufe ido yayi ba abinda ke mashi yawo a cikin zuciya irin yanda Yarima Haishir ya kamo Bahijja a wani sashe na zuciyar shi kuwa yana mamakin abinda Baidulƙais ke faɗa, ganin ba abinda tunanin zai mashi juyawa yayi yaci gaba da lazimi


A turakar bayi kuwa Bahijja ce kwance saman cinyar mahaifiyar ta, suna fira da ita cikin kulawa tace ma Bahijja. "Ƴata kigodema Allah daya fiddoki daga hannun waɗan nan mutanen gaskia bakaramin sa'a kikayi ba, da yanzun ba musan a wane hali zaki kasance ba Allah yasaka ma Yarima Malik da alkhairi daya jajirce ya ansoki daga hannun su, fata Allah ya kara tsaremu daga kowane sharri ya kara tsarema na Masarautar mu da dukkan musulmai baki ɗaya." "Ameen Umma, kinsan na ɗauka ankashe Ya Malik na shiga ruɗani Umma." "gaskia ne Bahijja dole ki shiga damuwa Allah dai yakara tsarema na shi cikin aminci." da ameen Bahijja ta amsa sannan tace. "Umma wai gobe ma sai kinje wajen aiki."? Murmushin girma tayi sannan tace. "Kwarai kuwa ƴata sai naje aiki." "Umma zanje inta yaki aikin nagaji da zama ni kadai in kika tafi baki dawowa da wuri fa." takarasa maganar kamar mai shirin kuka, itako Binta tarasa mi zata cema Bahijja cikin tattausar murya tace. "Ƴata kikara hutawa ki bari kema zaki samu aikin da zaki dingayi kinji, kinga Sarauniya Zulaiƙa ba tasan taga anyi yawa a sashen ta." tashi tayi ta zauna tace. "Umma kefa ke bada aikin mizaisa nima ki bani nawa." cikin kosawa tace. "Kinga Bahijja nace kibari wani lokaci ki fara naki aikin, waike aiki har dadine dashi sai kace baki sha wahalar bauta ba." marairai cewa tayi tace. "Kiyi hakuri Umma, zan zauna anjima zan baki labarin kalar wahalar da nasha a cikin Masarautar Raifasu, da Waisu." "shikenan ƴata ko kefa, kinga dama kinje wajen Mairo ki zauna kafin anjiman." shiken Umma." tare suka tashi suka tafi suna tafe suna labari har ta shiga gidan Mairo ita kuma Binta ta shiga cikin Masarauta...


Gimbiya Zahara'u ce ta fito falo sanye da doguwar riga, a jikin ta, tana shigowa ta iske Huzaifa da Mahaifin su zaune da alama fira suke taɓawa inda yace ma Huzaifa. "Baka ganin maganganun MalikusSaif akwai abin dubawa a cikin su."? Shiru yayi yana kallan Mahaifin nashi sannan yace. "Ni banga wani abun dubawa ba cikin maganganun shi ba Abba."
"Hmm yaro kenan sai inga kamar yarinyar nan Bahijja akwai wani al'amari a tsakanin su." saurin tarar shi Huzaifa yayi yace. "Abba karfa kaman ta hadimar shi ko ince itace zata dinga yimashi hidima wannan shine alaqar kuma fa baiwar sace." cikeda gamsuwa Waziri Dammur ya kaɗa kai yace hakane. Itako gimbiya Zahara'u cewa tayi. "Haba Abba miya hada Yarima na da baiwa ai sai ƴar sarauta irin shi ba wai baiwa ba ni wlh wannan maganar ma harta sosa mani rai." cikin fushi Huzaifa yace. "Waya saka bakin ki a cikin wannan maganar bansan sakarci da karambani." turo baki tayi cikin shagwaɓa tace. "Kaga yaya Huzaifa dan nasa albarkacin bakina aiba laifi bane." mikewa yayi ya tashi zai kwabdeta Waziri yace. "Haba kai da kanwar ka, ke kuma kin cika surutu ki daina shiga maganar manya." "toh Abba." shiko Huzaifa tashi yayi ya shiga dakin shi yanajin ranshi na mashi zafi musamman inya tuna da maganar Abban su baiso yaji ana wannan zancen gudun kada wani abun ya kuma faruwa."



A wajen Malik kuwa yana farkawa daga bacci yayi alwallah yafara nafilfili saida yagama sannan ya tashi ya fito falo wata irin yunwa ce yaji ta taso mashi kamar zata halaka shi a daddafe ya zauna gashi ba kowa a sashen nashi duk ya sallami bayin shi ganin dare ya fara, haka ya tashi yaje saman wani table yaga kayan marmari ya dauko wankewa yayi yahauci kamar wanda bai taɓa cin abinci ba haka yake jinshi ci yake kamar yana zubewa kasa ganin basu rika shi yasa shi tashi yana cewa bari inje wajen Abbuh kilan in samu abu mai nauyi inci, wata zuciyar tace mashi kodai kaje kaima Ummu maganar Bahijja, yanzun inda ace yanada sahihiyar hadima da bai zauna har yanzun ba tareda yaci abinci ba duk da bai zauna ba, hakadai ya isa wajen Saifulislam yana sake sake a ranshi sallama yayi yaji shiru hakan yasa ya gane yana dakin shi ba inda ya wuce sai wajen kulolin abinci, yayi sa'a da tuwon shinkafa, bai wata wata ba ya ɗauka ya zuba yafaraci yana cikin ci Saifulislam ya fito daga dakin shi, mamaki yayi ganin yanda Malik ketacin abinci, zama yayi yana murmushi yace. "Yau Yariman Daborah ne kecin abinci irin haka mike faruwa ɗana."? Ruwa yasha yace. "Abbuh yunwa taimin illah gaskia ya kamata zuwa gobe kasa Ummu tabani hadima ta." shiru yayi yana kallan Malik da mamaki dan yasan ba lallai bane Sarauniya Zulaiƙa ta amince da kudurin Yarima Malik ba, kama hannun Malik yayi yace.......





_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*

_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم





Episode 41&42



"Haba Jarumi na farin cikina saurin mi kakeyi har haka baka ganin mahaifiyar ka bata gama hucewa ba akan wannan Yakin ba, kabari sai komai ya lafa sannan saika tunkare ta da wannan maganar."

Aje abincin gaban shi Yarima Malik yayi sannan yace. "Abbuh kaima kasan Ummu bazata saurareni ba kai nikeso kaimata wannan maganar." "hmm Malik kenan kasan abubuwan danai ma mahaifiyar ka kuwa ko kasan da kaina na shiga cikin turakar bayi na kwanto Bahijja wannan wane irin zubda darajane ban mata ba, wannan dalilin shi zaisa bazan kara yimata maganar Bahijja ba zata ga kamar ina anfani da matsayin da nike dashi a wajen ta ina yanke mata hukuncin da nike so, amman ka gwada intaki yarda zan mata magana muga yanda za'ayi sai dai ina jan kunnen ka Malik ka jajirce wajen yima mahaifiyar ka biyayya karka yarda wani abu yasa kace zaka bijire mata kanajina."? Eh Abbuh shikenan zan mata magana da kaina nan da jibi insha Allah." murmushi yayi yana shafa sumar kan MalikusSaif yace. "Ameen ɗana Allah yaimaka albarka." da Ameen ya amsa yanajin dadin kasancewa da mahaifin shi.......

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A wajen su Yarima Haishir kuwa suna isowa Masarautar su, ba inda suka wuce da gawar Sarki Lahazu sai wajen gimbiya Ƙamariyya tunda aka shigo da gawar jikin ta ke rawa duk tsammanin ta Yarima Haishir ne aka kashe a sanyaye ta iso tana bude mayafin da aka rufeta taga mijin tane kwance, a tsorace ta mike tanaja da baya wani irin kuka ta fashe dashi mai tsuma rai tafada saman gawar shi tana kuka kamar ranta zai fita bata gama kukan da takeyi ba saiga Sarkin Yaki ya shigo da Yarima Haishir rai hannu ga Allah, da sauri ta taro shi a saman jikin ta, kamar ta ɓaɓɓa haka takasa ko motsin kirki sai kallan Haishir takeyi da kyal ta iya cewa. "Haishir karkaimin haka karka mutu kabarni kaga narasa mahaifin ka kada kaima inrasa ka ɗana ka tashi Haishir na rokeka ka bude idonka kaga mahaifiyar ka katashi Haishir.!" sake rushewa da kuka tayi tana haki komawa ta sakeyi jikin Sarki Lahazu ta sake taro shi jikin ta kamar zautatta tace.
"Mijina karka tafi kabarni na shiga ukku wayai maka haka waya kashe min kai na rantse da girman Gurfanai saina ɗauki mataki mai yawan gaske ga duk wanda ya aikata haka akan ku." Waziri ne ya shigo ciki dakin ya ɗauki gawar Lahazu suka tafi dashi zasu birne shi da kyal aka ɓanɓare ta jikin shi tanaji tana gani aka fita da gawar Sarki Lahazu, a gigice ta koma wajen Haishir mai magani ya shigo aka ɗauke shi aka fara yi mashi magani.

********************************

Suko su Baidulƙais koda suka koma Masarautar Raifasu sashen shi ya wuce ya rasa mike mashi dadi a cikin zuciyar shi, tashi yayi baisan ya saki uwar kara ba, da sauri Sarki Danwar ya shigo ya fara tambayar shi lfy, wasu kwalla yaji suna suntiri a fuskar shi, cikin mutuwar jiki yace. "Danwar ya zanyi yau nine aka ketama rigar mutinci a Masarautar Daborah na rasa abu mai mahimmanci a tareda ni ga ankashe mani Jarumai na ga ɓacin rai yasa da hannuna na kashe aminina ya kakeso inyi da raina."? Murmushin mugunta yayi yace. "Ka kwantar da hankalin ka gobe inna koma Masarauta ta zanbi hanyar da zanbi dan ganin na sasanta tsakanin ka da Masarautar Waisu ai baku cancani Yakar junan kuba, kuma kasani hatta Bahijja zata dawo gareka." wani sanyi Baidulƙais yaji a zuciyar shi baisan ya rungume Sarki Danwar ba, shi kuwa sai kudire kudire yakeyi a cikin zuciyar shi......

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Daborah kuwa Sarauniya Zulaiƙa ce zaune tana cin abinci kamar bata sonci dan rabin hankalin ta bakan abincin yake ba tunani takeyi kala kala. sallamar Yarima Malik tayi ɗago kai tayi ta kalle shi sannan ta maida taci gaba dacin abincin ta, zama yayi sannan ya gaida ta amsawa tayi tace. "Gwarzon Daborah ya gajiyar Yaki."?
Murmusawa yayi yace. "Yabi jiki Ummu." ɗago kai tayi tana nazarin ɗan nata cikin kulawa tace. "Meke damun ka Yarima."? Gyaran murya yayi yace.
"Bakomai kawai dai nazo ne dan innemi alfarma wajen ki." tattare komai tayi tace inajin ka wace alfarma ce. "Ummu maganar Ashir dan Allah kiyafe mashi laifi nane baida masaniya akan wannan lamarin ni na aike shi Masarautar Raifasu."

A dakile tace. "Naman ta da wani Ashir can kaman ta bansan maci amana duk yanda nike dashi."? Sosa keya yayi yace. "Hakane Ummu saidai wannan karon ɗanki ne ya ha'ince ki ki yafe mani." hannu tasa ta shafi gefen fuskar shi sannan tace. "Badamuwa komai ya wuce kasa a fiddo maka Ashir, sannan zuwa gobe ka zagaya gidan kaso a fiddo masu kananun laifi duk a yafe masu." rungume ta yayi cikin murna yace. "Nagode maki Ummu Allah yakara maki lfy da nisan kwana." Ameen ya rabbi, atare sukaci gaba da cin abincin yana san yai mata maganar Bahijja yana shakka shiru yayi har suka kammala sannan yai mata sallama ya tafi dan fito da masu laifi.


Ita ko Bahijja tana tashi da rana taga mahaifin ta na shirin tafiya wajen aiki, cikin tausayawa tace. "Abbana inama ace zan iya aikin da kakeyi da naje naimaka ka huta."murmushi yayi yana maijin dadi nuna tausayi da Bahijja tayi agreshi kama hannun ta yayi yana cewa. "Ƴata kinsan aikin da zaki mani a rayuwa ta."? Wani irin dadi taji a ranta wai yau ita ce zataima iyayen ta aiki tace. "Aa Abba wane aiki ne."? "Kiyimin alkawalin zaki mani shi."? "Eh Abba zanmaka shi insha Allahu." "yawaa ƴata haka ake so duk abinda mutun zaiyi yasa ikilasi a cikin zuciyar shi, ba wani abu bane inaso ki nisanta kanki ga duk abinda kikasan yafi karfin ki, karki sama ranki shi balle kiji ya burgeki harkiyi shi'awarshi, sannan ki rike mutuncin ki da matsayin ki a cikin wannan Masarautar wannan shine aikin da zakima mahaifin ki kuma shine alfarma ta agreki ƴata."
sake rike hannun Abban ta tayi tana wasa da yatsun hannun shi tace. "Abbana indai wannan ne baka da matsala dani zan tsaya matsayina kuma bazan manta cewa ni baiwa bace zaka sameni mai yawan yimaku biyayya." wani irin dadi yaji yace. "Allah yaimaki albarka ƴata ya kareki daga sharrin zamani." "Ameen Abba."
cewa yayi.
"Kinga idan ina biyema kaunarki agareni tabbas bazan dinga fita wajen aiki da wuriba kinga Umman ki tuni tai tafiyar ta nikam harkin sa na makara."faɗawa tayi jikin shi a shagwaɓe tace. "Abba jinike kamar inbika zanyi kewarku kamar ku zauna inta kallanku."
jamata hanci yayi yana dariya yace. "Kinga tafiya ta ƴar nema kincika surutu kikula da kanki ƴata saina dawo." haka ta dinga dagama mahaifin ta hannu harya fita cikin makimancin gidan su mai ɗauke da daki biyu sai ban daki, wasu kwalla taji sun ciko mata idanu ba wanda ta tuna sai Jakadiya Jamra a zahiri ko cewa tayi. "Baba ina kewar ki, saidai bangan ki kinzo nan ba Allah dai yasa ba kamaki akaiba kina gabatar da addini ba kema insha Allahu sai kinbar azzalumar Masarautar can da izinin Allah Baba inayi maki addu'a kullin Allah yakare mani ke, can kuma ta tuna dasu Zainab da Indo tace Allah Sarki kawaye na shikenan bankara ganin ku kenan wayyo Zainab an rabani dake muna cikin wasan

Please Login or Register in order to submit comment