Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sansanin bayi kuma daga yau ita zata dinga gyaraman sashena da kula da komai daya dan ganceni dafatan kagane."?
"Angama Gurfanai ya kara girma ka hita lfy.'' haka ya tafi, jin kowa yai shiru hakan yasa Yarima Haishir ya kalli MalikusSaif yace. "Abokina ko bakujin dadine."? "Aaa cewar Huzaifa.
wayan cewa MalikusSaif yayi yace. "Ya bayan rabuwa abokina tun a Masarautar Ƙaisu ranar da akayi bikin gamji wajen bauta."
kallan sakarai Yarima Malik yai ma Haishir, shiru yayi yana nazari saidai ya kasa tuna komai nuna MalikusSaif yayi da yatsa yace. "Kwarai kuwa,Yarima Ƙamar ko."? Koda MalikusSaif yaga Haishir ya bashi sani da wuri hakan yasa yace. "Kwarai kuwa." rungume Malik yayi yana murna yace.


"Ɗan Sarkin buzaye shi yasa ka boye mani kanka dan insha wahalar ganeka kenan gashi na gane da wuri."
Dariya sukayi baki dayan su sannan MalikusSaif yace.
"Kaga wannan kanina ne Nurda shike bi mani."
ba karamin mamaki ya kama Haishir a iya sanin shi Ƙamar baida dan uwa amman sai yace kilan ɗan uwan mahaifin shine haka suka taɓa fira kowa yana jin dadin ganin ɗan uwan sa musamman Haishir da yake ganin Yarima Ƙamar ne ya kawo mashi ziyarar bangirma,
"Zakuyi kwana biyu ko."?Murmushi MalikusSaif yayi mai ɗauke da ma'anoni iri iri sannan yace. "Eh kwana ukku zamuyi maka."
dan ɓata rai Haishir yayi yace. "Ina laifin sati biyu."kallan juna sukayi sannan Huzaifa yace. "Ai muna a hanya ne wata rana zamu sake dawowa." shikenan cewar Yarima Haishir, suna kara taɓa fira kowa ya tashi su suka wuce masaukin su dan hutawa shi kuma ya tafi wajen mahaifin shi ya sanar dashi yayi manyan baki

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

A Masarautar Daborah kuwa ba abinda ya sauya komai sai kara ƙamari yakeyi yana tsananta musamman a wajen Binta yauma tana komawa ba abinda tafara yi sai share share da gyara ma Sarauniya Zulaiƙa ɗakin ta, tana gamawa taje tafara ma Sarauniya tausar kafarta kamar yanda ta saba, zaune suke kowa yai shiru da alama akwai abinda suke saƙawa a cikin zuciyar su, itadai Binta mafarkin da tayi na ƴarta ne ya addabi zuciyar ta, ita ko Sarauniya Zulaiƙa a duk lokacin da taga Binta sai taji mugun haushin ta sai taga akan ƴarta ne ɗanta ya tafi yabar ta wai neman Baiwa hakan kesa taga kamar zubda martaba ne da daraja a idon duniya ace Yarima kamar MalikusSaif yatafi neman baiwa kuma ƴar bayi lallai kam dole hakan ya taɓa darajar Masarautar Daborah, jin shirun yai yawa hakan yasa Binta ta ɗago ta saci kallan Sarauniya ganin kallan kiyayyar da take ai kamata kadai tasan ta tsaneta fiye da tunanin ta, sadda kanta tayi dan tagama tsorata tace.
"Ranki shidade ina neman alfarma a wajenki."?
Kallan ta tayi alamun inajinki, "daman ina san kimin izini zan kaima Abdulmajid ziyara." ɗauko gwaiba tayi ta faraci cikin izza da gadara kamar bada ita ake magana ba saida Binta ta fidda rai, sannan tace. "Zaki iya zuwa bance ki jimaba sannan da marece ki samo bayin da zasu gyarama Saifulislam lambu."

"angama ranki shidade Allah yataimaki uwar dakina uwar marayu Allah yakara girma Binta nagodiya." cikedq murna ta tashi ta, tafi turakar bayi dan shiryawa......

***********************

Wajen Sarki Baidulƙais kuwa ya gama duk wani shiri da yake tunanin zaiyi wani ɗaki ya shiga a cikin sashen shi ba wanda ke shigar shi sai shi, yana zuwa ba inda yaje sai wajen wata kwalba ya ɗauko ya fara wasu maganganu marassa dadin saurare, wani irin hayaki ke fita a cikin kwalbar cikin kankanin lokaci wani mutun ya bayyana ba kyaun gani da fasali, Sarki Baidulƙais ne yace. "Ina san taimakon ku da aljanu a wannan lokacin inasan in dirkake Masarautar Daborah da abinda suke takama dashi."
dariya ce ta kaure kaf dakin ankai minti ukku ana yinta sannan akayi shiru magana aka fara mai ratsa kunne a kace. "Yanzun ne zaka nemi taimakon mu bayan komai ya kure maka ai inda ka kasa cimma burinka akan Bahijja komai ya lalace dan haka bamu da abinda zamu iya yimaka saida kaga karasa ta, sannan zaka nememu dan haka Sarrilƙus yace a gargaɗeka kada kasake neman wani taimako daga garemu in kunne yaji."
wata dariyar ce aka kara saki zaiyi magana kenan ya ɓace, dafe kanshi yayi ya rasa mike mashi dadi shikan shi ya san rashin cimma burin shi da baiyi ba akan Bahijja tamkar naka su ne akan mulkin shi, da dajin GAMKI baki dayan shi wannan dalilin yasa Sarrilƙus kejin haushin shi dama Masarautar Raifasu baki ɗayan ta!


*Turkashi wata sabuwa inji yan caca miya haɗa Sarrilƙus da Bahijja? Koma minene da sannu zamuga ni, muje zuwa my fans*

Haka ya gama yan surkullen shi ba wani aljanni daya kara zuwa har zoben dake hannun shi saida ya murza ammn aljani ɗan tsitu bai fito ba daya gaji haka ya fito ji yake kamar ya kurma ihu gidan yari ya wuce yasa akaci gaba da ganama su Tasi'u azaba dan baki ɗaya laifin su yake gani a dalilin sune aka ɗauke Bahijja batare da ya cika burin shi akan ta ba, haka ya koma fa'da wannan karan da kanshi yasa aka rubuta wasika zuwa ga Sarkin Ƙaisu jin shiru baice komai ba ya kara yimashi tuni akan abinda yake nema a gareshi.

```Daborah```

Koda Binta ta isa wajen mijin nata yau ba laifi ta same shi da ɗan ƙwari ba kamar koda yaushe ba, tana zuwa ta ɗauko wata leda ta bashi abinci ansa yayi yana kallan ta cikin so da tsabar tausayin ta yace. "Ummu Bahijja ina kika samu wannan abincin da har kika kawo mani shi"? Murmushi tayi tace. "Mijina kenan wanda ake ragewa ne a madafi nike kalato maka dan kasamu abinda zaka saka ma bakin salati."
ansa yayi yaci yana gamawa yafara yimata addu'a harda ƴar kwallar shi, itama jin dadi tayi ganin yanda mijin ta ke saka albarka da ameen ta amsa ɗan shiru ne ya biyo baya cewa tayi. "Abban Bahijja daman wlh inaji a jikina Bahijja na cikin mawuyacin hali dan abinda nagani ya masifar ɗaga mani hankali da ace akwai yanda zanyi da nasamu nabi hanya ko ganin zan dace in gudo da 'ya'ta."

Murmushin girma Abdulmajid yayi yana ganin gangancin matar tashi yace. "In banda abinki waya gaya maki mafarki gaskia ne baki tunanin idan ki kace zaki bita kema aka maki kije wata Masarautar kici gaba da bauta a banza a wofi ai kwara nan zaki dinga ganin dangin ki kinajin dadi, yafi ace an kamaki garin neman ƴarki ga rashin sa'a na ganin yar taki ga kin rabu da kowa naki." hawaye ne sukayi nasarar wanke ma Binta fuskar ta goge cikeda gamsuwa tace. "Hakane minene mafita"? "Kiyi hakuri inda rai da rabo ki saka wannan aranki sannan daga yanzun kisaka aranki mafarki karya ne daga yau karki kara saka damuwa a cikin zuciyar ki kinji matata."?
Aza kanta tayi saman kafaɗar shi tana jin dadi tace. "Shikenan daga nan bazan kuma yim wannan maganar ba."
canza wata firar sukayi suna cikin magana, mai kula da Abdulmajid yace lokaci yayi haka Binta ta tafi sai murna takeyi ji take kamar anbata gaggarumar kauta, tana komawa taskar bayi haka ta ɗibi bayi sukaje lambu dan yin aikin da Sarauniya Zulaiƙa ta saka ta....

Shiko Ashir kullun cikin gana mashi ukuba akeyi ga duka wanda harya fara zame mashi jinin jikin shi yau ma Sarkin horo ne ya gama dukan shi sannan yasa wawan Sarki ya zuba mashi gishiri ga ciwon jikin shi, jiyayi kamar ya mutu dan azaba duk ya gama fita hayyacin shi, haka aka ɗauke shi aka shanya shi cikin rana kamar ba dan Adam ba.


Cikin Raifasu kuwa Jakadiya ce taje wajen gimbiya Yazira takai mata bayi sunai mata aiki, har Jakadiya ta fito gimbiya Yazira tasa aka kira mata Jakadiya cikin dakin ta ta sameta zama tayi ta gaidata kallan tayi cikin kulawa tace. "Gani ranki shidade." "Jamra ina labarin Bahijja mi kikaji uban gidan ki na cewa a kanta ."? shiru Jakadiya tayi tasan manufar gimbiya Yazira akan Bahijja bamai kyau bace cewa tayi. "Ranki shidade banda wani labari akan Bahijja abinda nasani ba'a ganta ba, wasu ne suka sace ta suka gudu sa ita." haka nan taji gaban ta ya fadi da sauri tace. "Ko kinsan su waye."? Kallan mamaki Jakadiya taimata. "Ina zan sansu ranki shidade."?
"Ina nufin ko kinji maimarta ba, na zargin wasu."? "Eh to bazan iya ganewa ba saidai da gani bai wuce cikin amintattun Sarki ne zasu ha'in ce shi su sace Bahijja wannan shine gaskia."
kallan gimbiya Yazira tayi taga take ta raina gaskiar ta daman tana sane tace haka dan taga yanda zatayi, da kyal tace. "Kibar wannan maganar Jamra ban tunanin hakan zata kasance inda rabo za'a ganta ai, zaki iya tafiya Jamra in kinji wani labarin ina sauraranki." da toh Jakadiya ta amsa ta dan bata yarda da yana yin gimbiya Yazira ba, tana zatan kamar itace ta sace Bahijja dan cimma wani buri nata koma mine ta ɗaukar ma kanta saita tona ma gimbiya Yazira asiri da haka ta isa sashen Sarki Baidulƙais, itako Uwani duniya ta koya mata hankali zuwa yanzun ba karamin dukuwa takeyi ba, har kamannin ta sun fara canzawa ga uwar yunwa na addabar rayuwar ta danko tunda aka rufeta bata kara ganin keyar gimbiya Yazira ba bare tasa ran taimako daga gareta koda abincin da zata cima cikin tane, rushewa da kuka tayi mai sosa zuciya, wata muguwar baiwa ce tafara zagin Uwani tana kwasa mata mari kamar ta samu jaka tun Uwani na ihu har saida tayi shiru cikin kankanin lokaci ta kumbura mata fuska jiniko sai zuba yakeyi a bakin ta....


*Niko nace tun yanzun kinfara ganin sakayyar Allah bakiga komai ba indai duniya ce ta isheki riga da wando😁*



_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*


*Dedicated this Page to Maryam Mujittafa Lawal, ina maki fatan alkhairi* 🥰


Episode 17&18


_Masarautar Waisu_


Washe gari da safe Bahijja ce ta gama shirin ta tsaf zataje wajen aiki kamar yanda mai kula da sashen Yarima Haishir ya faɗa mata tunda ta tashi baki daya jikinta ke mata ciwo ga tana fama da matsanancin ciwon kai da, tayi niyar baza taje ba, amman gudun kada tayi wani laifin, shi yasa ta tafi koda ta fita sansanin bayi ba inda ta wuce sai bangaren Yarima Haishir tana zuwa ta fara gyaran falo hankalin ta kwance take aikin ta cikin nutsuwa har ta ida sharar da takeyi, tana gamawa tayi bayan gida tafara gyarawa,cikin kankanin lokaci ta gama aikin ta zama tayi tana hutawa jin kirjin ta na dukan ukku ukku tarasa yanda a kayi taji yana yinta ya sauya, shiko Yarima Haishir yana fitowa daga dakin shi yaga angyara falo tsaf kiran wata baiwa yayi ya tambaye ta ko Bahijja ta zo, "Eh itace ta gyara komai."
wani irin dadi yaji dan baiyi tsammanin zata zo ba ya santa da taurin kai kuma bata da tsoro, da haka ya nufi dakin su Yarima Malik, yana zuwa ya kwan kwasa masu kofa bada jimawa ba Huzaifa ya buɗe mashi kofa shiga yayi ya zauna gefen gado, sannan suka gaisa, Yarima Haishir ne yace. "Ya kamata ku fito falo, azo a gyara maku dakin ku."
hakan kuwa akayi suna gama shirin su suka fito falo, zama sukayi shiko Haishir sai dube dube yakeyi ko zai ga Bahijja jin shirun yai yawa hakan yasa ya kira wata baiwa yace ta shiga ta gyarama bakin shi dakin su, fira suka fara, awajen Bahijja kuwa gyangyaɗi ne ya fara ɗaukar ta,jitayi an ta ɓata da sauri ta farka ganin mai magana yasa ta mikewa, mai kula sashen Yarima Haishir ne yace ta tashi taci gaba da aikin ta, baki ɗaya ji tayi jikin ta ya mutu ba yanda zatayi haka ta mike ta shiga cikin falon, ta rasa inda zatay, wata zuciyar ce tace mata tafara gyara dakin Yarima, ji tayi kuma wata tace anya wannan sakaran Yariman ma yatashi, ɗan karamin tsoki tayi ta kama hanyar tafiya dakin Yarima, tana wucewa su Yarima Malik su kuma suka taho zasuje wajen mai martaba, tunda ya hangi bayan baiwar dake gaban su yaji faɗuwar gaba har suka fita haka nan yaji ya rasa sukuni a cikin zuciyar shi, itako Bahijja tana shiga ta iske ɗakin a yamutse komai ya ɓaci a cikin ranta ko cewa tayi wannan ai kazanta ce, haka nan yake nuna ma mutane isa ashema kazami ne, tana aiki tana sababi harta gama gyara mashi dakin, ta rufo shi tayi ta koma falo ta zauna, jitayi kanta yafara yimata ciwo kishin giɗawa tayi bacci ne yafara ɗaukar ta.

Koda Yarima Haishir suka isa wajen Sarki Lahazu iske shi sukayi cikin sashen shi suna zuwa Yarima Haishir ya rungume mahaifin shi suko su Malik gaida Sarki sukayi, baki dayan su suka zauna sake gaisawa sukayi Sarki Lahazu ne yace. "Ɗana baki kayi daga ina."? Cikeda zumuɗi yace "Ƙamar ne Yariman Ƙaisu ya kawo mani ziyara."
kallan tsaf Sarki Lahazu yaima su Malik sannan yace. "Aikuwa sun kyauta kaidin ne baka da kirki ba inda kake zuwa tunda Yarima HusbarulƘais ya mutu baka kuma zuwa ko ina ba ."
sosa keya yayi yace. "Ranka shidade ina kewar abokina har yanzun." girgiza kai Sarki Lahazu yayi yace. "Tabbas ɗana basai kafaɗa ba har gobe ina tir da halin Sarauniya Zulaiƙa Yakin nan ya taɓaman zuciya yanda baka zato fata dai Gurfanai ya kara ɗaura mu akan makiyan mu." sudai su Malik basu ce komai ba, sai kallon juna sukeyi basu jima sosai sukai ma Sarki Lahazu sallama suka tafi ba inda suka wuce sai wajen gimbiya Ƙamariyya suna zuwa bayin dake wajen ne suka zube kowa ya kawo gaisuwa tashi tayi daga kishin giɗar da tayi tana kallan ɗan nata cikin kulawa tace. "Yarima baki kayi ne."? Zama yayi gefen ta yace. "Eh Umma Yarima Ƙamar kenan da kanin shi Nurda sun kawo mani ziyara ne zuwa gobe zasu tafi." fuskar ta sake tace. "Sannun ku da hanya gaskia kun kyauta haka akeso zumunci nada dadi saidai ya kamata kuba abokin naku shawara yayi aure haka nan." ɗan gyaran murya Yarima Malik yayi sannan yace. "Badamuwa zamu bashi ai dagani ma kamar ya samu wadda yake so." numfasawa gimbiya Ƙamariyya tayi tace "bawa fa yace yana so ina shi ina baiwa kuma."? take Yarima Haishir ya sauya fuska yace. "Haba Umma zan ƴanta, tafa miye daga ciki dan naso baiwa."? tsaki tayi bata kuma cewa komai ba suma su Yarima Malik basu ce komai ba kowa da abinda yake aiya nawa a cikin zuciyar, da haka sukayi mata bankwana suka tafi masaukin su.....


Suna isa sashen su zama sukayi a falo Yarima Malik ne yace. "Huzaifa nifa harna fara gajiya har yanzun ace ba muga wani abu dan gane da Bahijja ba yau fa kwanan mu biyu da zuwa gobe zamu wuce Daborah anya Bahijja naraye."?
Cikin tausayawa Huzaifa yace.
"Haba Yarima insha Allah Bahijja na raye bata mutu ba."
murmushin karfin hali Malik yayi mai kama da kuka yace. "Gaskia ne Huzaifa ni kaina inaji a raina Bahijja na raye, kaga Huzaifa indai yau ta kare ba muga Bahijja ba, bai kamata muci gaba da zama cikin wannan kaskantattar Masarautar ba, jibi yanda nakoma a ƴan kwana kin da mukayi a wannan Masarautar haba Huzaifa ya zamuyi yanzun nasan mahaifan ta suna cikin tsananin kewar ta sosai, ji sukayi ana koɗa Yarima Haishir alamun gab yake da shigowa a cikin falon da suke zaune shima zama yayi gefen su, yace. "Kuyi hakuri abokai na na tsaya wajen Umma wai ba zanso baiwa ba kuji minene aibun baiwa."?
Huzaifa ne yace. "Bata da wata matsala ko kadan."
Cikin jin dadi Haishir yace. "yawwa nima dai haka nagani Nurda." suna ta zancen auren baiwa sukaji tari daga bayan su, ba ƙaƙƙautawa, a fusace Yarima Haishir yace. "Wake mana tari anan wajen."?
Ba'a bashi ansa ba,shiko Yarima Malik sadda kanshi yayi kasa yana nazari, baki ɗaya tunanin shi yayi kan Bahijja dan bai san a kowane hali take ba a halin yanzun, shiko Haishir a fusace ya tashi ya tafi inda ake tarin ya iske Bahijja kwance a saman kujera tana bacci ta kware, daka mata tsawa yayi yace. "Ke Bahijja tashi waya baki ikon kwan tawa a falon nan."
yanda sukaji ya kira sunan *Bahijja* baki ɗaya su Yarima Malik suka mike jikin shine ya ɗauki kyarma a hankali suka tako zuwa wajen Yarima Haishir, itako Bahijja ta makale jikin ta duk tsoro ya gama dirar mata a cikin zuciya jin yanda ya kwaɗa mata tsawa dan ba tayi mamakin yanda bai kai mata duka ba, shiko Yarima Malik tunda ya aza razanannun idanun shi masu rikata mai kallo akan kyakkyawa fuskar Bahijja,kaftawa baiyi baki ɗaya yai mutuwar tsaye ganin Bahijja a gaban shi kamar a mafarki, itako a hankali ta fara buɗe idanun ta harta buɗesu tangaram ta azasu saman fuskokin su ɗaya bayan ɗaya take kallan su har idanun ta suka sauka saman fuskar Malik, batasan gaban ta ya faɗi ba, da mugun karfi, duk da ba taga fuskar shi sosai ba, sake daka mata tsawa Yarima Haishir yayi yace. "Bazaki mike ba kika kafe mutane da waɗan nan idanun naki masu kama dana aljanu.!"
kallan banza Bahijja ta watsama Yarima Haishir taso tayi mashi rashin kunya hakanan taji Yarima Malik yai mata kwarjini ta kasa cewa uffan, tashi tayi jiki sanyaye ta gaida su Yarima Malik sannan ta tafi, ta kusa fita taji yace. "Bahijja zonan."?
Yanda yai mata maganar saida yasa zuciyar Malik ta tsinke, komawa sukayi kowa ya zauna sannan ta iso dukawa tayi tace. "Gani ranka shidade." shiru yayi kamar bai san da zuwa taba sai kaɗa kafa yakeyi yana jiji dakai dan yaga yau tayi laushi acewar shi dan ya hukun ta tane, yasa tayi sanyi da yawa taji jiki, itako sai satar kallan su Malik takeyi da ta ɗago ido sai taga sun haɗa ido sai tayi saurin maida nata kasa shiko Yarima Malik yana mamakin girman Bahijja har haka sai sake sake ya keyi a ranshi ya rasa murna ya keyi ko kuma bakin ciki yake ji a cikin zuciyar shi. maganar Yarima Haishir ne ya dawo dasu kogin tunanin da suka ninkaya cewa yayi. "Waike wace irin baiwa ce baki san kiba uban gidan ki, hakuri ba shine kika kwashi kafafu kika tafi ko a jinki ga sa'anki naimaki faɗa."?
Kafeta da idanu MalikusSaif yayi yaji me zata ce, cikin rawar murya tace.
"Kayi hakuri banjin dadine shiyasa Bahijja na tuba." tsaki yayi yace "baiwa kinajin dadi fa anjima kidawo ki gyarama bakina ɗakin su kinji."? "to nagode." nuna mata hanya yayi mikewa tayi ta tafi tana al'ajabin mutanen da tagani wajen Yarima Haishir sun mata kwarjinu shine har yake gaya mata maganganu san ranshi da tunani iri iri Bahijja ta tafi sansanin bayi abinta.....

*******************************

Suko Jaruman Daborah yau Allah yasa suka iso Masarautar Daborah ba inda suka sauka sai fa'da suna zuwa kowa yakai gaisuwa wajen Sarauniya Zulaiƙa, haka Sarkin zagi yace dasu Sarauniya ta amsa, shiru ne ya biyo baya hakan yasa Sarauniya Zulaiƙa ta kalli Sarkin Yaƙi da tambayoyi iri iri a fuskar ta ce mata yayi. "Ranki shidade mungaza muna neman afuwarki bamu samu Yarima Malik ba, ba irin neman da bamuyi mashi ba amman yayi ruwa yai tsaki, kimana aikin gafara." ya idasa maganar kanshi kasa, mikewa Sarauniya Zulaiƙa tayi tana zagaye fa'da tana isowa wajen Sarkin Yaƙi dukowa tayi gefen fuskar shi tace. "Dagaske kun gaza baku dawo da MalikusSaif ba akan aikin dana sanin da yake shirin yiba?" Bakasan kin hana Yarima Malik zuwa neman Bahijja ba kamar zubda kima da darajar Masarautar Daborah bane? Shin kanaso kace mani Sarkin Yaƙi na ya gaza dawowa da Yariman Daborah gida ba? Mikake so in kiraka dashi wawa? Ko kuwa sakarai? Marar hankali? Ko kuwa marar tunani."?

Shidai Sarkin Yaƙi ya kasa cewa komai dan mamaki da al'ajabi ganin yanda suka sha wahalar neman Yarima amman Sarauniya Zulaiƙa takasa yimasu uzuri, bai gama tunanin da yake yiba yaji ta wanke shi da mari tace. "Ni sa'ar kace ina magana kayi shiru kafara haukane."?
Jikinshi na kyarma yace. "Ina neman afuwarki ranki shidade, bakina ya girmi kalaman da zanyi anfani dasu wajen baki hakuri." cikin fushi tace. "Sarkin gida kiramani Sarkin Yari aje a garƙame mani su, sai sunyi sati ɗaya a ɗaure badan kada makiya suyi mani dariya ba da saina sauke keka akan wannan matsayin nak! dan dai za'ace Sarkin Yaƙin Sarauniya Zulaiƙa ya gaza yaji kunya, ku ɓacemani dagani sakarkaru daku mararsa kishin zuci.!"


Haka sukai ta ba Sarauniya Zulaiƙa hakuri amman kamar bada ita suke ba , haka aka tafi dasu gidan Yari abin gwanin ban tausayi.


➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Yarima Malik kuwa yana komawa, cikin ɗakin su yafara dukan hannu yaje ya dawo yaje ya dawo, ya rasa inda zaisa kansa cikin ɓacin rai yace.
"Huzaifa jibi Bahijja yadda tazama baiwa marar ƴanci yanda ake juyata kamar ba mutun ba, jibi yanda Bahijja ke yawo da kayan da suka kama mata jiki, gaskia idan ina ganin Bahijja haka zuciya ta zata iya fashewa, Huzaifa kasan yanda na ɗauki Bahijja"?
Mamakin MalikusSaif ya gama kama Huzaifa, ganin yanda yake zance kamar zararre.
Shiko MalikusSaif ganin yanda Huzaifa ke mashi kallan tuhuma, yasa ya kule yace. "Ina maka magana kayi shiru."
Murmushi yayi yace.
"Aaa Yarima saika faɗa." " Ina jin Bahijja tamkar jinin jikina mai gudana kuma hantata ƴar uwata tamkar mun kwanta ciki ɗaya da Bahijja haka nikejin ta Huzaifa, ta yaya zanga ana wulakantata tana yawo da waɗan nan wulakantattun kayan kafurai na gane mata surar jiki yarinya karama amman ana bata aiki mai wahala,Huzaifa yau dinnan zan ɗauki Bahijja mubar wannan Masarautar.!"
Ya ida maganar yana fidda huci mai zafin gaske.
dafashi Huzaifa yayi yace. "Yau da gobe duk daya ne a wajen Allah kabari sai zuwa gobe intazo aiki wajen mu sai mu bayyana mata kanmu tana iya yuyuwa ta manta mu saboda ba wayon kirki ne da itaba sosai sadda aka raba ta da iyayen ta ba, dan ni nasan bata sanni ba, amman kwara kai saboda kasa ba da ita,kilan ta iya tunawa da kai, kuma ya kamata tasan kudurin mu ta shaidamu, sannan sai mu dauke ta."cikeda gamsuwa MalikusSaif yace.
"Tabbas kafadi gaskia abokina tarayya ta da kai akwai dinbin ilimi a ciki kana bani shawara mai kyau Huzaifa Allah ya kaimu goben lafiya." da ameen Huzaifa ya amsa, sannan sukayi alwalla kowa yai sallah suka kwanta sai dai cikin su bamai bacci kowa da abinda yake ai yanawa a cikin zuciyar shi......


Ita kanta Bahijja tana gama abinda zatayi ta kwanta saman ƴar tabarmar ta ba abinda ke mata yawo sai saurayin da tagani tareda Yarima Haishir ta rasa inda tasan kaman nin shi, ɗan guntun tsaki tayi tace. "Kedai Bahijja kin cika shirme ke dama baki ga fuskar shi ba inake ina tunanin inda kika sanshi, kibar wannan zancen ma, can kuma ta cukune fuska tace.
"wannan shegen Yariman sai nayi maganin sakarai, can kuma ta sake yin murmushi tace Allah Sarki Baba Jamra koya take a halin yanzun koya addinin ta yanzun, shikenan bani ba Baba Jamra, na rabu da ita kenan? Nan zan zauna

Please Login or Register in order to submit comment