Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take takamar ba ainahin baiwar Masarautar su bace ai yanada iko akanta inda shiya ɗaukota da kanshi, cikin zafi yasa hannu ya wanke ta da mummunan mari saida ta faɗi kasa dan azaba amman takiyin kuka, sawa yayi aka kira mashi Sarkin bulala yasa shi ya duke Bahijja haka aka fara dukan ta kamar jaka, shiko sakai yayi ya tafiyar shi ranshi nai mashi kuna ba abinda yake so yakasan ce da shi sama d Bahijja ga wani shi'awar ta yanaji kuma ya ɗaukarma ranshi saiya zama namiji na farko da zai fara saninta a duniya dan da gani tanada kamun kai, da wannan tunanin ya shiga cikin bathroom yafara wanka yana huci kamar zuciyar shi zata faɗo ga magan ganun Bahijja nai mashi yawo a kwakwalwa ba kamar yanda take cewa ta tsane shi bata kaunar shi, tsabar bacin rai baisan ya fara buga kanshi a bango ba faɗuwa yayi kasa sai ya fashe da kuka mai cin rai wai shi mace zata sosama rai ta wulakanta kamar haka!? shikuma yanzun yafara sa kafar bakan tama Bahijja a cikin Masarautar Waisu....


```Niko dai nace ikon Allah wannan wane irin bala'i ne gaskia Bahijja kinga takanki ga abinda Yarima Haishir ya faɗa bari muga zai iya cimma burin shi akan ki kuwa?Allah masani, muje zuwa my fans inayin kufa🤝🏻```


Shiko Sarkin bulala yana cikin dukan Bahijja taga dukan yai mata yawa daman gata Sarkin tsoron duka batasan sadda ta mike ba ta rike bulala ba cikin fushi tace.
''Dakata karka sake dukana minai maku ne waiku wa'anne kalar azzalumai ne baku da imani ne, ka kara dukana wlh saina baka mamaki sakarai dakai kaje gun uban gidan naka kace shi miya hanashi hukunta Bahijja da kanshi saikai wahalalle kai kanka baka wuce a wulakanta kaba amman kakecin zarafin wani."
Galala tabar Sarkin bulala tsaye yana mamakin kalar taurin zuciya irin tata, dan zuwa yanzun zuciyar Bahijja tagama bushewa bataki ta mutu ba ko kuma ta rayu tayi alkawali duk wanda yake neman kasara mata rayuwa tabbas zata wulakanta shi koma waye a cikin Masarautar Waisu ta fahimci basu da imani, lokacin da Sarkin bulala mamaki ya gama kashe shi na wannan baiwa mai masifar tsiya ya dubata dan cigaba da dukanta yaga bata nan baisan ya bita ba, da gudu dan ya iske ta dai dai wajen sashen gimbiya Ƙamariyya ya isketa tana tafiya, jitayi an zabga mata bulala har cikin kanta taji dukan ta tana waigowa taga mai dukan ta, batasan ta duka ba, warto katon dutsi tayi ta ɓaurama shi a saman kai take kan Sarkin bulala ya fashe dai dai nan gimbiya Ƙamariyya ta fito daga sashen ta zataje wajen Yarima, dandazon mutane tagani kiran wata baiwa tayi ta tambayeta ba'asi ta fada mata abinda ke faruwa.
isa tayi wajen itako Bahijja ganin jini na zuba a fuskar Sarkin bulala take ta ruɗe tasan shikenan kwanan ta yakare ba tareda ta kara kallan Umman taba, Jakadiya ce tafado mata arai inda take cemata Bahijja kefa baiwa ce dole zaki ɗauki hakuri wajen bauta a duk inda kika samu kanki baki da wani zaɓi....gani tayi duk bayin dake wajen sun zube kasa suna ƙarɓar gaisuwa itako takasa ko dukawa dan tsoro, itako gimbiya Ƙamariyya idanunta ne suka sauka kan Sarkin bulala sannan ta kalli Bahijja, cikeda mamaki tace. "Ke baiwa kece kika aikata wannan aikin."?
Cikin dakewa Bahijja tace. "Ranki shidade bansan sadda na aikata hakan akan shi ba."sawa tayi kowa yabar wajen sannan ta kirasu zuwa sashen Yarima Haishir a falo ta zauna nan Bahijja ta duka cikin fushi gimbiya Ƙamariyya ta mari Bahijja tace. "Kina baiwa zakima Sarkin bulala haka ko kinsan ba karamin musiba kisa saka kanki a ciki ba."? jin abinda gimbiya Ƙamariyya tace ya karama Bahijja kwarin guiwa tace. "Ranki shidade Bahijja baiwa ce wadda take kalkashin ikon wata Masarautar dan haka a halin yanzun Bahijja ba tada zaɓi tsakanin rayuwa da mutuwa! rabon Bahijja da farin ciki kilan tun ban wuce ƴar shekara biyar ba karfa ki manta ni baiwa ce ina baiwa inani ina jin dadi.?"
jitayi kanta yai mugun saramta, a zuciyar gimbiya Ƙamariyya kuwa cewa tayi, anya wannan yarinyar ba aljana bace ganin ko ajikin ta, sawa tayi aka kira mata wawan Sarki tasa yafara dukan Bahijja jin ihu yasa Yarima Haishir fitowa ganin abinda ke faruwa yasan saida yasa kowa ya bar part din shi, isowa yai wajen mahaifiyar tashi ganin tafara tambayar ta dalilin fasama Sarkin bulala kai, da sauri yace.
"Ninasa ya duketa, kibar komai hannuna Umma, kallan wawan Sarki yayi yace ya tafi, zama yayi ya kalli Bahijja ganin yanda idanunta suka sauya ita kallan kaskanci tai mashi taki sauke idanta akan shi, shine ya kauda nashi idon, sannan yace ma Sarkin bulala ya tafi zai neme shi, sannan kuma da kanshi zai hukunta Bahijja, haka Sarkin bulala ya tafi jiki ba kwari yana shakkar Bahijja a zuciyar shi, yana cewa kodai aljana ce wannan yarinya daman kyaunta yayi yawa kilama gamo nayi a lambu ba ainahin baiwa bace.
itako gimbiya Ƙamariyya sawa tayi Bahijja ta tafi sai anmeta haka ta tafi duk jikin ta nai mata zafi.........


Washe gari da safe mutanen Sarauniya Zulaiƙa ne suka isa Masarautar Ƙaisu, haka Sarkin yaki da Lurwan suka yi basaja suka shiga cikin Masarautar suna neman Yarima Malik da Huzaifa saida suka yini cur ba alamun su hakan yasa suka tafi suma dan kaima ƴan uwan su sako, koda suka koma zama sukayi suka huta har marece, Sarkin Yaƙi ne yace masu Lurwan su shirya su koma Daborah dan sanarma Sarauniya Zulaiƙa, sungaza wajen nemo Yarima Malik haka akayi kuwa washe gari da asuba sunayin sallah suka kama gaban su dan komawa Masarautar su....

*************************

Itako Bahijja baccinta kawai take kwas, uwar bayin Masarautar ce tazo ta kirata binta tayi har sashen Sarki Lahazu, karon farko kenan d Bahijja taga Sarki gab da ita a cikin Masarautar Waisu, dukawa tayi ta gaida shi kallan ta yake yana aiyana abubuwa a zuciyar shi cewa yayi. "Baiwa a garin yaya kika jima Sarkin bulala ciwon irin wannan."?
Muryar Bahijja na rawa tace. "Ranka shidade so yake ya kasheni kuma ba abinda nayi tuba nike."
Juyawa yayi ya kalli Sarkin bulala yace. "hakan.?" da eh ya amsa yace. "Yarima ne ya bani izini."shiru Sarki yayi sannan yace ma Sarkin bulala ya basu waje, godiya yayi sannan ya fita.
Sake kallan Bahijja yayi yace"agarin yaya''!?sadda kanta tayi kasa sannan tace. "Tabbas kalamai na girmi bakin Bahijja a matsayina na baiwa indan gata Yarima da wannan maganar saidai ba yanda na iya."
Cikeda kwarin guiwa yace. "Faɗi koma mene."
cewa tayi.
L"Ranka shidade so yake yaketa mani haddi shiyasa ni kuma naki yarda wannan shine dalili."
Murmushi kawai yayi yace a zuciyar shi wato ni Yarima zai cima mutunci kenan ni zai wulakanta ashe da gaske yake nida shi muzuba mugani!
A zahiri kuwa kallan ta yayi yace. "Baiwa da ace zamu biyema kyaun ki da son zuciya, nikaina uban Haishir zan iya neman ki, sannan idan aka biyema Masarautar da kika fito ko dan Sarauniyar ki zamu iya halaka ki, saidai a halin yanxun nafison ki rayu ko dan wani dalili saidai ban hanaki kare mutucin kiba, zaki iya tafiya."
magana Bahijja zatayi Sarki Lahazu ya hanata ta hanyar ɗaga mata hannu sannan ya nuna mata hanya tanaji tana gani ta tafi, a bakin hanya ta iske Sarkin bulala kallan banza tai mashi sannan ta tafi shima yana ganin hakan ya tafi ranshi ba dadi tana zuwa dakin su kwantawa tayi ta saki kuka mai sosa rai tana mamakin irin halin Masarautar ta da Sarauniyar su, kumi Daborah ta kunsa da yasa ba'a ganin bayin Masarautar da kima share kwalla tayi ta tashi tafara sallah tana kai kukan ta wajen Allah



_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



*Wannan Page din naki ne Nanarh Aysher kiyi yanda kikeso dashi* 🥰


_Jinjinar ban girma ga yan Bayima Ya'yane Comment grps ina yinku Allah yabar kauna_ 😍


Episode 13&14




~_Masarautar Daborah_~


Binta ce a sashen Sarauniya Zulaiƙa tana aikacen aikacen ta kamar yanda ta saba shekara da shekaru yauma haka tai mata komai sannn ta koma gefe tana jiran isowar uwar ɗakin tata, takai minti talatin sannan Sarauniya Zulaiƙa ta fito daga cikin ɗakin ta, tana fitowa da sauri Binta ta kwanta flat haka Sarauniya Zulaiƙa tabi ta kanta ta wuce har ta isa mazaunin ta, haka Binta ta sake tashi ta iske Sarauniya Zulaiƙa inda take zaune, gaban ta tasake dukawa tayi zaman rakuma haka Sarauniya Zulaiƙa ta ɗaura kafufuwan a saman kafaɗar Binta, a sheke ta kalleta tace. "Baiwa uwar bayi ko mijin naki ya mutu."?
Wani irin faɗuwar faba ya kama Binta dan rabon da abar mijin ta ya kwana gida harta manta karfin hali tayi tace. "Aaa ranki shidade saidai banda wannan masaniyar, ina rokon ki da kitaimaka mani, kisa abar Abdulmajid yana kwana gida ko sau ɗayane a sati in kikaiman hakan zan rage raɗadin da zuciyata kemani, na rokeki uwar gijiya ta.!"


Murmushin jin dadi tayi dan tai zatan, hakan tanasan duk wani farin ciki ya rabu da rayuwar Binta harta mutu dan ta tsani zuri'arsu musamman ƴarsu, kuma yanzun ta huta da ƙuda fatan ta kada MalikusSaif yasamu nasarar karɓo Bahijja, sake kallan Binta tayi cikin mugun ta tace.

"Hakan ba abin damuwa bane Baiwa ɗiyar bayi jikar bayi uwar bayi, gaskia kin yi sa'a ku kuma haka zaku karata a bauta kenan? ɗan karamin tsoki taja sannan tace. Zaki iya zuwa madafa dan kawo mani abinci na fatan dai kinsa anyi mai dadi." da eh Binta ta amsa haka ta tafi madafa bata jima ba ta dawo da abinci a hannun ta ita da wasu bayi duk suka aje gaida Sarauniya sukayi sannan suka fita, haka Binta ta zauna gefen Sarauniya Zulaiƙa ta zuba mata abinci ji take kamar ta faɗa a cikin abincin raban da taci abinci yau kwana ukku kenan saidai ruwa su Mairo ke sammata a abinci idan sun anso a madafa shima ɗan kadan wani bima saidai ta kaima Abdulmajid ita kuma ta kwana da yunwa, tunda Sarauniya Zulaiƙa ta ɗauki cokali yawun ta ke gudawa itako Binta ta gama shagala da kallan abincin , Sarauniya Zulaiƙa na ankare da Binta kuma tasan tana bala'in shi'awar abincin saida tabari tayi nisa akan kallan abincin duk da shi Binta ke kallo amman hankalin ta nakan mijin ta tasan tabbas yafita bukatar abincin.
bata gama tunanin da takeyi ba taji ansheka mata wani abu mai zafi a jikin ta da sauri Binta ta mike tsaye sai kyarma takeyi baki ɗaya abincin da tazuba ma Sarauniya Zulaiƙa ne ta watsa mata ajiki har saida hannun ta ya ƙone gashi harda miya a cikin abincin sake dukawa Binta tayi ta sadda kanta ƙasa tana hawaye masu ciwo ga zafi ya isheta duk ta ƙone amman haka ta dinga ba Sarauniya Zulaiƙa hakuri kamar wata uwar ta cewa tayi.
"Yiman shiru mayya ƴar mayu kinzo kin tsareni da mugayen idanun ki so kike in kware kenan ko."? girgiza kai Binta ta shigayi cikin sarkewar murya tace. "Aaaa bahaka bane bansan ina kallanki ba ranki shidade tuba nikeyi uwar marayu ki taimaka ki ƴan tani a cikin amintattun bayin ki zuwa yanzun kimin aikin gafara na tuba."
Sake daka mata tsawa tayi tace. "Keda samun ƴanci sai a lahira idan anayi ke harkin isa ki zama amintattar baiwa bayan kunyi gadon cin amana, ɓaceman dagani, kuma nan da minti talatin ki maida hankali ki dawo aikin ki kwashe kwanukan kije ki cinye mayya kawai jikar mayu."haka Binta tagama gyara wajen sannan ta fita da kwanukan madafa taje takai su, uwar tuwo ce takira Binta tace tasamu leda ta juye ta tafi dasu, da tace aaa bata so haka ta matsa mata sabida bala'in tausan Binta takeji haka ta tafi ba inda ta wuce sai wajen mijin ta, ta bashi abinci yaci kamar mayunwaci yake cin shi itadai ta ɗaukar ma ranta koda yunwa zatayi ajalin ta bazata ci wannan girkin ba sabida akan shine akaci mutuncin ta kuma tasan idan ta gayama Abdulmajid abinda ya faru ya fita zuciya, shima bazai ciba, amma batasan yunwa ta nakasa mata miji daman kullin cikin ukuba yake da haka tai mashi sallama ta koma wajen ƴan uwanta bayi ta kwanta kafin ta koma aiki tana kwance tafara tunani zuwa can Bacci ya kwashe Binta, koda Mairo ta shigo da ɗaurin fanke da aka raba masu zama tayi tana jiran Binta ta shi dan suci tasan bataci abinci ba gani tayi Binta ta tashi a firgice alamun tsoro atare da ita riketa Mairo tayi cikin tsoro tafara tambayar ta ko lafiya.?


Sai fidda jiɓi takeyi a hankali tafara gane Mairo numfasawa tayi sannan tace. "Mairo wani ne zai ketama ƴata Bahijja haddi sai cewa takeyi intai maka mata dan Allah Mairo kisama mani hanyar da zan gudu dan inceci rayuwar ƴata Bahijja.!"
"haba kefa uwace ga kowa kuma kinsan mafarki kinsan zahiri dan Allah kada kisaka kanki a damuwa mana." hawaye ta goge ta kalli Mairo tace. "Kayya kayya Mairo tunda na rabu da Bahijja banta ɓata mafarkin taba sai wannan lokaci inajin tsoro." duk da itama a tsorace take sai tayi tunanin kwantarma da ƴar uwarta da hankali tace. " kibar faɗar haka Allah natare da Bahijja duk runtsi kuma ba abnda zai taɓa mutuncin ta sannan karki manta mufa bayi ba taimakon da zamu iya yima Bahijja face addua." cikin gamsuwa tace hakane Mairo saidai ki sani mutuncin Bahijja shikadai ne gatanta kuma shine ya rage a tare da ita ga zafin bauta kuma ga ba daraja dukan zaima Bahijja yawa fata dai Allah ya tsareta daga kowane sharri" da Ameen Mairo ta amsa sannan ta tisata sukaci fanke da kunu ji sukayi ana buga karaurawa alamun akoma bakin bauta, gaban tane ya faɗi tasan Allah ne kadai xai fidda ta wajen Sarauniya Zulaiƙa saboda ta makara sosai haka ta mike kowa yatafi wajen aikin shi......

*********************
A wajen su Yarima MalikusSaif kuwa har sun shigo yankin Waisu yanzun Masarautar suka tunkara sai jin dadi yakeyi yanaji ajikin shi tabbas zai dace da Bahijja, itako Bahijja zuwa yanzun tazama ƴar gari a cikin Waisu kusan kwanan ta goma duk wanda yai mata saita rama daga Sarki sai gimbiya Ƙamariyya ne kadai batai mawa danko Yarima Haishir tunda ta fahimci manufar shi akanta bata ganin girman shi ko kadan haka take mashi rashin kunya iya son ranta tareda da barazana zuwa yanzun ya daina neman keta mata haddi saidai ya mameta ya rugumeta ta baya haka yake mata idan ta zille ta wurga mashi harara da tsoki tace mayaudari, yau tagama gyaran dakin gimbiya Ƙamariyya kamar yanda tasaba, taji mutun ya bankata saman gado yabi yaimata ruf da ciki yana neman fara lalubarta aida sauri da zille tace. "Waikai wane kalar wawane baka da hankali ne bakasan ciwon kanka dagani ko a cikin addinin naku kai jahiline....
Baisan ya wanketa da maruka ba har ukku saida ta fasa kara dai dai gimbiya Ƙamariyya ta shigo, ta dawo daga wajen mijinta da sauri ta karaso yana shirin kwaɓe kaya zai keta Bahijja yaga ta rashin kunya ya nuna mata karshen jahilci da sauri gimbiya Ƙamariyya ta iso tafara mashi faɗa tana cewa. "Bakada hankali a dakin uwar taka zakayi zina da Baiwa koma mi taimaka saika hukun tata." a fusace yace. "Na rantse da gamji ko agabanki ne ba abnda bazan iya aikatawa balle a dakin ki dan haka nasan abnda zan mata haka yaja Bahijja da kanshi yai mata dukan kawo wuka har saida ta daina motsi sannan yasa aka kaita wani ɗaki a sashen shi yasa mai kula da wajen yace sai tayi kwana ukku sannan kuma kullin ka fiddota ta gyaraman sashena ita kadai haka kuwa akayi aka rufe Bahijja a cikin shi batama sani ba saida ta falko ta ganta a cikin shi itako tasa kama ranta saita ɗauki fansa wajen Yarima Haishir


~_Masarautar Raifasu_~


Jakadiya ce a dakinta tagama ibada iyakar abinda taga Bahijja nayi wata baiwa ce tazo kirant, tsayawa tayi tana mamakin abinda taga Jakadiya nayi duk da bata gama yarda d hakan ba koda tayi gyaran murya, saida ta shafa sannan ta mike tace. "Lafiya yan mata."? Cikin daburcewar murya tace. "Sarki ke nemanki ranki shidade"tare suka isa zuwa wajen Sarki Baidulƙais tana isa ta duka cikin kulawa yace. "Jamra mikeke boyewa a ranki naga kin sauya ba kamar daba kinzama sabuwa agreni kina kamewa daga komai namu harma da al'adun mu, anya Jamra baki tareda da lamari mai girman gaske.?"
da aaa ta amsa mashi sai cewa tayi batajin dadi ne kwana biyu, bai matsa mata daman shi bai cika san takura ba akan sanin abinda mutun ke ciki da toh ya bita sannan ya sata kawo mashi abinci....wannan kenan.

_Daborah_

Yauma kamar kullin Abdulmajid ne a kema azaba tafi ta kullin ga ƙishi yana ji amman an hanashi ruwa, hakan yasa Binta tazo ganin mijinta, taga yafara kakkafewa ai batasan taba mijin nata ruwa ba, ranar saida Binta tasha duka kamar ganga ranar itama a ɗaure ta kwana suna shan uban sanyi ga azaba, shiko Ashir azaba tasa harya fara sauya kamanni dan wahala kullun sai an duke shi banda wahalhalu nabdaban da ake mashi


~Allah Sarkin dadi duniya kenan zalinci dai ba abun yibane Allah yasa mudace~


Yarima Haishir ne yasa aka fiddo mashi da Bahijja a cikin ɗakin da yasa aka rufeta,fiddo mashi ita akayi yasa aka bugeta sannan aka maidata cikin ɗakin nan itako bata fasa gaya mashi abinda taga damaba,ran shine yakara ɓaci, musamman da takara cema shi jahili. A fusace yace ma mai kula da Bahijja karya kara bata abinci a halin yanzun, wani irin bakin ciki ne ya takore Bahijja a ƙahon zuciya batasan tafara kwallan bakin ciki ba....

*************************

Baidulƙais ne yasa aka kira mashi Sarkin Yaki cema shi yayi." Wane shiri kukeyi dangane da wannan Yakin da muke shirin tun kara."?
"Ranka shidade ba abinda bamu shirya ba, abinda ya rage mana shine dawakai sunyi mana kaɗan sai munkaro wasu." cikeda gamsuwa yace. "Ya kamata kaje wajen Sarkin taska a ɗibi kudi a karo wasu ka tabbatar an samu masu nagarta yanda ya kamata."
''gurfanai ya kara maka girma duk abinda ya kamata za'ayi fata dai mu samu nasara akan abokan gaba." haka yasa sallami Sarkin Yaki ya tafi dan isar da sakon Sarki Baidulƙais.....



A wajen Sarkin Yaki kuwa sungaji da neman su Yarima Malik hakan yasa suka kama hanyar da zata sadasu da Masarautar Daborah

Yarima Haishir ne wajen mahaifin shi yasake yimashi maganar Bahijja, yau ma, kamar kullin Sarki Lahazu bai bashi kwarin guiwa ba musamman da yaji abinda ɗan nashi ke bukatar yi akan Bahijja, haka suka rabu da tareda wata mafita ba wannan karanma haka Yarima Haishir ta tafi ranshi ba dadi, ya ɗaukar ma kanshi bazai kuma zuwa wajen mahaifin shi akan batun Bahijja ba, da haka ya koma sashen shi da kanshi ya fiddo ta an ɗaure mata hannu yace. "Ke baiwa kin canza ra'ayi ko kuwa kina kan bakarki."?
Wani kallo tai mashi na tsana sannan tace. "Na tsane ka kuma bazan taɓa zama mallakin kaba koda kuwa aurena zakayi, dan haka kasa a kasheni in huta ban kaunar ka, kai azzalumi ne kuma maci amana."


Rufe idan shi yayi ya bude a hankali duk sun sauya kala baisan sadda ya shake mata wuya ba yace. "Ko kinso ko kinki saikin zama mallakina koda ta karfin tsiyane ƙaƙari Bahijja tafara da kyal ya anshe kanta tafara kwalla sake sawa yayi aka rufe ta cikin dakin wanda ba abinda ke ɗawainiya dashi sai uban soro fa zafi, duk da haka Bahijja batayi sanyi ba ko ta sauko akan taurin kan da ta ɗaura ma kanta akan muguwar manufar da Yarima Haishir kesan cimmawa akanta, koda aka maida ta cikin ɗakin batasan ta rushe da kuka ba dan takaici.....



A kwana a tashi ba wuya wajen lillahi yau su Yarima Malik suka iso Masarautar Waisu sake sauya kamanni sukayi sannan suka shiga cikin Masarautar sarkin kofa ne ya tsaida su yafara bin cike sukace wajen Yarima Haishir sukazo, batare da ɓata lokaci ba a kaima su Yarima Malik iso zuwa sashen Haishir koda aka sanar mashi da zuwan su haka ya fito ya same su zaune a falon shi, shima zama yayi ya kafesu da kallo cikin mamaki yace.....




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 15&16



_Dedicated this page to Autar Safana, Allah yabar kauna❣️_



"Barkan ku da zuwa Masarautar Waisu ya hanya dagani kun kwashi gajiya da yawa?." ya ida maganar fuskar shi ɗauke da murmushi duk da bai wayance suba kuma yana bukatar haske a wajen su saidai bai nuna masu hakan ba, Huzaifa ne ya amsa mashi da.
"yawwa ya muka sameku."? Yarima Haishir ya kalli MalikusSaif yace. "Dan uwa yaka mata ku shiga cikin daki domin watsa ruwa kafin anjima inzo mugaisa da juna."
cikeda gamsuwa Yarima Malik yace. "Hakane mungode da karamci." shiru Haishir yayi yana nazarin wannan muryar sai dai bai iya tuna inda yasan mai irin taba kasan cewar sunyi hudda da mutane iri iri a sassa daban daban na nahiyar Gambia, hakan yasa ya basar, da tunanin da yakeyi.
Kallan tsaf MalikusSaif yake ma Haishir yana nazarin shi kozai iya tuno wani abu da yaji muryar shi abin mamaki sai ya ga Yarima Haishir ya mike yaima su MalikusSaif iso maganar da yai masu ita ta katsema Yarima Malik tunani yana gaba suna baya ta wani corridor ne sukabi suka nufi wani tankamemen ɗaki tare suka shiga sannan Haishir ya dafa kafaɗar Malik yace.
"Abokina ga masaukin kunan fata dai yai maku kyau kuma ya burgeku."? Murmushin karfin hali Yarima yayi ya kaɗa kai alamar eh sannan yace "mungode."
yanda ya furta maganar kamar an mashi dole sai kuma ta kara mashi kyau shi kanshi Haishir duk da bazai iya shaida fuskokin su sosai ba amman yaga kyawun MalikusSaif, bayan sun aje kayan su ya turo masu wata baiwa ta hada masu ruwan wanka MalikusSaif ne yafara shiga yana fitowa Huzaifa ya shiga shiryawa sukayi kowa ya maida wani farin kyalle da suke boye fuskar su dashi suna gama shiri bada jimawa Yarima Haishir ya shigo shima ya sake sabon shiri nan yai masu iso suka dawo falon shi, bada jimawa ba aka fara gabato masu da kayan abinci iri iri, sawa yayi aka zuba masu sannan yace suci abinci, da kamar bazasu ciba gudun kar yayi zatan wani abu yasa suka fara cin abincin shima ci yayi suna ƴar fira har suka gama suna cikin magana ne saiga mai kula da Bahijja ya shigo zubewa yayi ya kwashi gaisuwa sannan yace.
"Ranka shidade yaune wa'adin da kaɗibar ma wannan baiwar ya cika za'a iya sakin ta daga rufewar da akai mata."? Tunda MalikusSaif yaji ance Baiwa baisan yanda a kaiba yaji gaban shi yana bugu kamar wanda wani abu ke shirin faruwa dashi take yanayin shi ya sauya har sai da Huzaifa ya fahimci hakan a fuskar abokin nashi, daurewa kawai yayi amsar da Yarima Haishir yaba wannan bawan shi ya dawo da MalikusSaif a nutsuwar shi yace.
"Eh a sake ta sannan ta koma cikin

Please Login or Register in order to submit comment